Advertisements
Chapter 15 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 38

42K to 45K   out of 113.1K words

tace "I don't think ko airport maid din nan ta ta'ba zuwa" Shiru Amrah tayi, little ta kuma rike hannun khairi tana kallonta, khairi na murmushi tace "thanks, bari In sakowa little" tare da nufan kitchen, Amrah tace "yana dining na fitar"............

Chan khairi taje ta sakowa little ta dawo parlorn a kasa kan rug ta zauna little ma tayi irin zamanta, a baki ta dinga bata har ta ce ta koshi Amrah na zaune gefe ta gama cin abincin tana kallo...........

Bayan ta gama bata ta had'a plate din Amrah da wadda little taci tayi kitchen ta had'a da kwanukan safe ta fara wankewa, biyota little tayi tana taya ta da surutu har ta gama ta share da towel me tsabta ta ajiyesu mazauninsu...........

D'akin da aka bata taje tayi alwala tayi sallahn azahar kan ta kwanta, wani bacci bacci take ji har ta fara lumshe ido taji an shigo, d'ago kai tayi se taga maryam ce tsaye tana yatsina tace "am not interested da abinda kika dafa, I want jollof na couscous with vegetable" bata jira Cewar khairi ba ta fice...........

Mikewa khairi tayi ta fito, kitchen ta shiga ta fara had'a mata dayake daidai na mutum d'aya ne in less than 30mins ta gama ta zuba a plate ta kawo mata parlorn a kan center table ta ajiye tare da jawo mata gabanta..........

Turo kofa taji anyi ko bata juya ba bugawar zuciyarta da kamshin turarenshi ya sanar da ita waye ne ya shigo runtse ido tayi don har ga Allah ita bata son encountering dashi, sallama kawai yayi maryam ta amsa, ya nufi dining.........

Kujera yaja ya zauna tare da fiddo waya ya fara dannawa ran nan a had'e har ta juya ta nufi d'akinta taji maryam tace "ruwan fah ko ni zan kawo wa kaina?" Fridge din dake gefen dining taje ta d'auki drinks d'aya da ruwa ta koma kitchen ta sa a tray ta d'aura cup tana fitowa taga maryam ta koma kan dining tana ta zuba duk da bata jin me take fad'a amma ta san da musharraf takeyi bayan ko d'ago kai be yi ba tun zaman ta balle ya tanka..............

Taje ajiye tray din taji maryam na cewa "haba ya musharraf ya za'ayi in zauna Ina ta magana kaki ko kallo na se kace baka sanni ba?" Shiru ya kumayi ta kuma cewa "ko ma menene ni de Ina sonka so kuma na aure, and am very sure zanyi nasara se na koya maka sona daga baya".............

A zafafe ya d'ago yace "leave" shagwa'be fuska tayi tana cewa "am sorry sweet......" "I said leave" ya kuma fad'a mikewa tayi tana tura baki zata wuce yace "and abincin nan wa kika barwa? Ko ke kike sayan kayan abincin da zaki sa a dafa ki tashi ki barshi a wurin? Common my friend take this food and finish it now!!!!"............

Ya karasa da d'an tsawa har khairi ma seda ta tsorata ajiye trayn hannunta tayi da sauri ta juya one step tayi taji ance "Ke!! Serve" juyowa tayi don ta san da ita yakeyi zuciyarta na bugawa ta fara zuba mishi abincin hannunta se rawa yake duk da idonshi akan waya yake amma yana kallon yadda jikinta ke 'bari bayan ta gama sa mishi ta tura gabanshi d'an daidai ta sa sam bata cika mishi ba..........

Ja yayi ya fara ci kaman baya so, tana juyowa suka had'a ido da maryam tana aiko mata da sakon harara bayan d'ura abincin gabantan kawai takeyi ba wai don tana jin yunwa ba, murmushi ne ya kubcewa khairi da sauri ta bar wurin tana murmushi sossai..........

Maryam kuma ganin murmushin da khairi tayi se taji kaman da ita takeyi haushin yarinyar ya kara ninkuwa a ranta dama tunda ta d'aura ido a kanta taji bata sonta, wannan couscous din da ta saka ta yi ma kawai don ta bata wahala ne se gashi ita aka had'a da wahalan d'urawa don da d'an yawa a plate din gashi musharraf ya wulakanta ta a gabanta, takaici ne ya zo mata har wuya hawaye ya cika idonta a haka kuma ta ci gaba da d'ura couscous............

Khairi na shiga d'aki ta fara dariya don abun ya bata dariya lokaci d'aya kuma ya bata haushi ace mace tana tallatawa na miji kanta yana dizga ta, khaih Allah ya sawwake wasu matan ke bada sauran mata, ita kuwa abunda baza ta iya ba kenan koman son da takeyiwa namiji baza ta iya fara fad'a mishi ba matukar ba shi ya fara ba, tambayar kanta tayi to ma me son ne oho..........

Ta karasa da ta'be baki tana me kwanciya kan katifa juye juye ta dinga yi tana tunano maganganun da maryam ke fad'awa musharraf wani ta'be baki kawai takeyi se murmushi jefi jefi, ganin baccin ba zuwa ze yi ba ta mike ta fito, nuri da Miemie ta gani zaune kan dining suna cin abinci Amrah na kwance kan doguwar kujera tana kallo salima ma na zaune tana chat, bata ga maryam ba haka musharraf ma baya parlorn amma da alamu be jima da ficewa ba don har yanzu kamshin shi be bar parlorn ba............

Sannu tayiwa Amrah da salima, Amrah ce kawai ta amsa da "ai ke za'ayiwa sannu cutie" murmushi khairi tayi tana cewa "kema cutien zaki na cewa?" Amrah tace "tab ai dole in little ta sawa mutum suna bakwa kira kun ta fad'a da ita kenan har kuka se tayi" murmushi khairi tayi tace "Lallai little pretty, bari nayi wanke wanke, plz Anty Amrah ko kin san me za'ayi da dare?"...........

Amrah tace "Ke ma Antyn?? A'a ki kirani Amrah na plz ni ba babba bace" Ta karasa da turo baki, dariya khairi da Miemie dake dining suka sake, had'e rai Amrah tayi tace "Ke kuma wa ya sa bakin ki?" Miemie tace "oho dai kunne na ya ji kuma se naki dariya?" Khairi tace "toh yi hkr Anty Amrah fad'amin me za'ayi da dare"...........

Amrah tace "Again!! Ni de in zaki ce min Anty Toh zaki shekara magana ban amsa ba don bazan amsa ba Allah na san in bamuyi sa'anni ba sede ki girme ni" nuri ma murmushi tayi tace "cutie karki yarda ma ki ce mata Anty don I'm very sure kin girme ta, and naji momma na cewa za'ayi tuwon semo da miyan zogale da gyad'a" Kai khairi ta gyad'a kan ta karasa dining din ta fara tattare kwanukan don ta tabbatar sun gama ci...........

Bayan ta gama wanke wanke ta d'aura tuwo cikin lokaci kankani ta gama ta sassaka a leda ta shirya a cooler, seda taje tayi sallan la'asar ta dawo kan ta d'aura miya, tana cikin daka tarugu taji an rungume ta ta baya ko bata juya ba ta san little ce murmushi tayi tana juyowa tace "little pretty har kin tashi daga baccin?" Tura baki gaba tayi tace "Eh momma ce ta tashe ni wai la'asr yayi kuma ba kyau bacci bayan la'asar"..............

Khairi tace "hakane ai little pretty, yanzu kinyi sallah?" Tace "Eh, cutie kin iya zobo drink Ina so na sha kuma paapi na ma yana so, nace momma tazo ta mana wai In tambaye ki In zaki iya kiyi mana" khairi tace "worry not pretty zaki sha zobo" tsalle little ta fara cikin jin daad'i...........

Haka ta ci gaba da damun khairi da surutu har ta gama aikinta har zobon, a wani farin roba ta sa ta sa a fridge, duk inda tayi little na bayanta, yarinyar ta shiga ranta sossai ta lura little dinma na sonta...........

Bayan ta gama komai ta wanke duk abinda ta 'bata ta kuma goge kan kitchen island, gas cooker da hot plate. little ta ja ta wai suje su zagaya gidan tunda bata san ko Ina a ciki ba, haka ta bita suka dinga zagayawa har garden, sun jima sossai a chan kan suka wuce boysquaters anan suka samu matar malam d'ahe inna laure  ita ke share share da goge goge a gidan da sassafe take shiga tayi komai kan gari ya gama haske ta gama ta koma bata sake lekowa se washegari...........

Gaisawa sukayi da khairi daga nan suka dawo cikin gida, a parlor suka samu momma tana kallon khairi tace "wai sannu ummulkhairi naga har kin gama ayyukanki gabad'aya, harda zobo kikayi na tabbatar wannan yarinyar ce ta saki yi dole"...........

Dariya kawai khairi tayi, momma tace "zaki iya tafiya, se ki d'ibar muku abincin a food flask, ya sunan kannenkin?" Khairi tace "nabeel da nabeela" momma tace "twins ne" khairi tace "Eh" momma tace "masha Allah ki duba store akwai gora se ki diba muku zobo zaki ga wani maroon coolar me d'an miya a ciki da karamin basket se ki sa muku abincin a ciki"..........

Khairi tace "toh mun gode" ta mike taje ta sako musu, ta fito d'akin da aka bata ta shiga ta d'auko jakanta ta fito d'ari biyu momma ta bata tayi kud'in napep godiya ta mata, tayiwa su Amrah sallama har get little ta raka ta kan ta dawo...........

A natse take tafiya kaman me tausayin kasa kanta kasa kaman ance ta d'aga kai se idonta ya fad'a cikin nashi ya sauya kaya daga manya zuwa kanana, milk jeans da maroon shirt me guntun hannu kafanshi sanye da normal shoe na maza, zaune yake saman mota shi kad'ai hannunshi rike da taba yana zuka............

"Subhanallah gentleman like him da shan taba? Be son lafiyan jikinshi ne?" A fili tayi maganan tana ji mishi takaici da haushi ta tsani taban nan kai duk wani kayan maye ma, tsintar kanta tayi da adu'ar Allah ya sa tabar kad'ai yake sha...........

Satar kallonshi tayi se taga shima ita yake kallo da sauri ta kawar da kai tana jin tafiyar na mata wuya natsuwa na neman barinta tsabar karfin kwayar idonshi a kanta.........

Shi kuwa ko a jikinshi kallonta yake shi kad'ai ya san me yake karanta a jikinta, dukda ya ga ta kasa tafiyar yadda ya kamata sabd kallon da yake mata hakan be hana shi ci gaba da kallonta ba. Allah ya taimake ta se ga napep da sauri ta tsare ta shige tana sauke ajiyar zuciya, kau da kanshi yayi ya ci gaba da shan tabanshi hankali kwance.............

Tafiyar mintuna a kalla 20 ya kawo ta gida, sauka tayi ta sallame shi ta shige gida, da gudu su nabeel suka rungumeta suna mata oyoyo ajiye kayan hannunta tayi ta tarbe su da murna itama tana tambayarsu ya school da lafiya suka amsa ta..........

Ta karasa tayiwa dada san da gida tana zama gefen taburman da take kai, nan ta fara ba Dada labarin duk abinda ya faru a ranar duk labarin little ne da yadda yarinyar ta shiga ranta se mutuncin mutanen gidan...........

Suna nan zaune suna labri har aka kira magrib suka mike sukayi sallah, yadda al'adarsu take karatu ne bayan magrib hakan kuwa sukayi seda akayi isha suka ci abinci, khairi tayi wanke wanke don akwai kwanukan abincin rana da su nabeel suka ci............

Ta shirya kwanukan momma a basket din ta Adana basuyi wani hira ba suka kwanta don kowa ya gaji..........

Kwance yake kan gadon momma yana aikin  danna waya, turo kofan akayi d'ago kai yayi se yaga momma ce tace "wai ni ka zo ka min bake bake a gado bayan ka san lokacin bacci na yayi a kanka kake so in kwanta?"..........

Murmushi ya sake yana cewa "momma zan tafi jibi flight na 10 zan bi, if possible a rubuta duk abinda babu gobe se nuriyyah suje su sayo, zan basu kudin shopping dinsu a goben ma" momma tace "Ohk toh se da safe wannan kam, and Musharraf In kaje ka daure ka dinga cin abinci plz In ka dawo bana jin daadin ganin yadda kake raman nan, ko de har yanzu kana sa damuwa a ranka
ne?"............

Murmushin yake yayi yace "ko d'aya momma" jin yadda ya amsa mata a takaice yasa ta san be son maganan shiru tayi ta kudurta a ranta a gobe ita da khairi zasu mishi danbun nama, donuts da duk wani abinda ta san baze 'baci nan kusa ba ya tafi dashi kila ya taimaka mishi..........

Mikewa yayi yace "seda safe mother" tace "good night and kar a manta da alwala da kuma adu'ar kwanciya yana murmushi ya fita a zuciyarshi yace se kace little?............

A parlor ya samu su nuriyyah nan ya fad'a musu gobe zasu je shopping ko wacce ta rubuta abinda take so ze duba a goben, godiya suka mishi ya fice ba tare da ya amsa musu ba...........












#vote
#share
#comment





'Yar mutan Adamawa



🎗🎗🎗🎗🎗







                 IGIYAR RAYUWA😭







                                              🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

             'Yar mutan Adamawa

*wipe away the tears of the orphans in order to attain the pleasure of the most merciful and a house in paradise*

Page➡️4️⃣4️⃣▶️4️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Washegari

Karfe bakwai da rabi dai dai yayiwa khairi a GRA, duk gidan ba wadda ya tashi bacci kasancewar weekend ne, d'akin da aka sauketa ciki ta shiga ta ajiye bag dinta, tare da komawa kitchen ta fara dube dube duk tunaninta ya tafi kan ko me zasu ci da safen? Tana d'aura hannunta kan kitchen island se taji paper an d'aura karamin robbern tumeric a kai d'auka tayi ta bud'e se taga an sa "kiyi pepper soup na kifi, za'aci da bread se kiyi tea but na soya beans" gyad'a kai tayi kaman a wurin aka bata umarni tare da fara aikin.................

Cikin lokaci kankani ta gama tare da shiryawa a dining ta koma kitchen ta wanke duk abinda ta 'bata, tana share kitchen din taji zuciyarta ya buga gabanta ya fara fad'uwa da sauri ta juya se kuwa idonta ya fad'a cikin nashi da sauri tayi kasa da kai tare da cewa "Ina kwana?" Kaman baze amsa ba se kuma yace "Lafiya" tare da ci gaba da tsayuwarshi.............

Juyawa tayi ta ci gaba da goge kan gas se kuma taga kaman hakan be kyautu ba se ta juyo tace cikin tsiririyar muryarta "ranka ya dade akwai abinda kake bukata ne?" Juya idonshi yayi tare da ta'be baki yace "just coffee" Kai ta gyad'a ya juya ya fita, coffeen ta had'a mishi tare da sa cup din kan karamin tray fari ta fita dashi a kan one seater ta Ganshi zaune se lokacin ta samu zarafin kallonshi da kyau sbd kanshi dake kan waya...............

Sanye yake da jallabiya coffee color me guntun hannu da ya matukar amsar fatan jikinshi, duk da be yi wanka ba amma kamshin shi duk ya cika parlorn, ganin ze d'ago yasa tayi saurin karasowa ta janyo center table ta ajiye mishi, ko kallonta be yi ba har ta juya ta fice, komawa tayi bakin aikinta Bayan ta gama goge gogen ta fice varender ta fara wanke mop din da tayi anfani dashi bata hankara ba taji an rungume ta, juyowa tayi ta d'aga ta sama "morning cutie" khairi na murmushi tace "morning pretty, ya kk?" Little tace "lafiya klau cutie Ina friends d'ina?" Khairi tace "sun je islamiyya, ke bakya zuwa ne?" Little tace "a gida malam ke zuwa ya mana da Anty miemie da Anty Amrah, ko wani weekend da yamma" kai khairi ta gyad'a tace "wa ya miki wanka?"...............

Little tace "momma tare muka sauko ma she's at the sitting room" khairi ta ajiyeta a kasa tare da kama hannunta suka fito, cikin ladabi ta gaida momma nan ta shaida mata ayyukan dake gabansu yau, da kai kawai khairi ta amsa, se misalin karfe goma su Amrah suka fita da, gabad'ayansu har little, da su salima.............

Ba sune suka dawo ba se azahar sayyaya kam sossai sukayi, a lokacin khairi ta jima da gama abincin rana har tayi donuts, naman ta ma yana wuta, da gudu little tayi kitchen da leda a hannunta "oyoyo cutie" khairi na murmushi tace "oyoyo kun dawo?" Little tace "yes cutie gashi na sayo miki tsarabar chocolate" khairi tace "aiko na gode" bata fiddo daga leda ba kawai lekawa tayi murmushi shimfid'e a fuskanta, bata kai ga magana ba taji momma na kiranta.................

Fitowa sukayi inda momma ta bata umarnin tattare kayayyakin kitchen ta kaisu wurin zamansu d'iban sayayyan ta fara da kad'an kad'an har ta gama, yau kam bata gama aikinta da wuri ba sam sbd ayyukan da suka mata yawa se bayan magrib ta gama goge kitchen a gurguje ta koma d'akin da yanzu ya zama nata duk da ba kwana takeyi a cikinshi ba, ta d'auko bag dinta ta fito...............

Momma dake zaune parlor ita da su Amrah da little tace "sannu khairi yau kam Kin sha aiki, gashi har dare ya miki bari inyi magana da driver se ya mayar dake gida sbd baza ki samu napep da daren nan a unguwan nan ba" kan khairi kasa tace "Toh na gode momma" little tace "Ayyah momma tunda da driver za'a kuma daga chan nan ze dawo In bisu mu dawo da driver?" Amrah tayi saurin cewa "Eh Allah nima zanje" momma tace "Toh shikenan kuje se kun dawo"................

Da gudu Amrah taje ta d'auko gyalenta ta gangaro don ita kam Allah ya d'aura mata son khairi ba kad'an ba, Jan hannunta tayi little ta d'auki basket din abincinsu suka fito suka wuce, har kofan gida khairi tayi mishi kwatance yana parking suka fito Amrah tacewa drivern "Dan Allah bari mu gaishe su mu zo baba Adamu" yana murmushi yace "toh 'yata" sossai yake jin daad'in aiki da su momma sbd mutuncinsu sam basa rena na kasa dasu, dukda a karkashinsu yake kuma motarsu amma se sun had'a shi da Allah akan aikinshi.............

Khairi na sallama nabeel da nabeela suka taso da gudu suna mata oyoyo itama rungume su tayi na mintuna kan ta sake su tana cewa "ga friend na maku" wara ido sukayi suna kallon Little dake makale da hannun khairi, nabeel ne ya fara cewa "hi" se nabeela ta fad'a murmushi little tayi tace "hello twins kuma kuna da kyau kaman cutie amma baku kaita ba, sunana Zarah and yhu?" Nabeel yace "am nabeel" nabeela tace "nabeela"...........

Amrah ce da ta gaji da tsayuwa tace "hi twins I'm Anty Amrah Adda khairi's best friend" waro ido sukayi har khairi kan suka fashe da dariya

15 / 38