Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
ban santa ba sannan kuma turaren da kika jin nan.
Nuruddeen ne ya saya yace inji kamshin naki shine ya fesa min a kirji ban bari ya karasa ba na ture hannunshi wallahi ba abinda kike zato bane haba ummulkhair kin 'bata min rai banyi zina Ina saurayi ba banyi bayan abunda surrayyah ta min ba, banyi bayan fitowana prison ba se yanzu da nake tare da masoyiyata, abin alfahari na, uwar 'ya'ya na?" Shiru tayi kanta kasa yace "In baki yarda ba lemme call him tunda ba mata yake dashi ba" wayan ya bud'e ya fara dannawa da sauri ta rike hannunshi In low tune tace "am sorry".
Rungume ta yayi suka sauke ajiyar zuciya a tare cikin kunnenta yace "kar ki kara plz bana so, bana son zargi ya dinga shiga tsakanin mu sbd yana 'bata aure, kin kuwa san yadda na tsani zina to tun daga randa na kalli mahaifina akan......" da sauri ta had'e bakinsu bata so sam taji zancen sbd duk waenda sukayin suna tare da mahallicinsu bata so sam ya dinga aibanta mahaifinshi bata yarda In har a gabanta ne.
Seda suka farantawa juna sukayi wanka kan suka dawo suka kwanta a manne da juna kaman zasu had'iye juna, washegari da safe aka sanar da su haihuwan nurriyyah inda ta samu d'a namiji aiko khairi tace zasu zo tunda ranar Monday zata gama last papper d'inta na first semester level 200, sati uku ne hutun Bayan sun gama wayan ne taga kiran dada.
'Dagawa tayi suka gaisa take tambayarta Abba tace ya fita da turanci da mamaki khairi tace "dada kaman turanci naji kinyi?" Dada tayi saurin cewa "nop hausa ne, na san Monday zaki gama paper in ba matsala ki roki mijinki zamu tafi taraba Abbanku ya matsa akan na komawa mahaifina watakil yanzu gaskiya tayi halinta" Khairi tace "Toh zan gwada tambayarshi Allah ya sa ya amince, da su nasreen?" Tace "a'a kin san tsarin makarantanku ba d'aya ba zamu dawo Wednesday mubi jirgin Adamawa se mu karasa jalingo a mota".
Khairi tace "sede tafiyanmu inaga zeyi daban daban sbd nuriyyah ta haihu yau da safe zamu tafi gomben watakil Tuesday" dada tace "masha Allah, Allah ya raya ya d'ayyaba, me ta samu?" Khairi tace "namiji" dada tace "d'ayyib zan kira hajiya fatima In mata barka, zan kira me jegon ma, muma wucewa be kama mu ba zamu shigo gomben kafin suna in shaa Allahu se mu wuce gabad'aya tare" sallama sukayi.
Musharraf dake tsaye a gefenta yana had'a tea duk wayan da sukayin a kunnenshi sbd a speaker wayan yake yace "gaskiya ya kamata ku waiwayi gida haka shekaru dayawa se muje tare zan d'auki leave na two weeks kinga hutun su little ma three weeks ne tafiyan yazo a daidai" Kai ta gyad'a duk fargabanta maganan mahaifin dada ne na ze tsine mata duk randa ya kuma ganinta kofan gidanshi da kuma tuna irin rantsuwar da mahaifinta yayi kan fitowarsu Allah sarki Allah ya ji kanka Abba, ko ya rayuwan su hauwa? Ta'be baki tayi suka ci gaba da abunda sukeyi.
Sunday suka had'e kayansu tsab trolley uku kowa da nashi Monday tayi last paper d'inta tuesday suka kama hanyar gombe a mota sukayi tafiyan wannan karon duk khairi ta galabaita ko don bata saba tafiya me nisa irin haka a mota bane se Allah, sun samu tarba sossai daga wurin momma gidan a cike da 'yan barka da shike tun kan nuriyyahn ta haihu ta dawo gidan da zama sbd matsalolin da cikin yayi ta bata.
Khairi kam kaman ta had'iye yaron, suna zaune da musharraf suna ta kallon yaron gwanin sha'awa da sauri taga ya mike ya fita chan kuma ya dawo ranshi ba daad'i kwata kwata don fuskan nan a had'e yana zama Anty rabi da Hajiya zulai tare da Afreen da kuma sufyan suka shigo, uncle Ahmad da uncle nasir biye da su, duk zama sukayi khairi ta zame kasa ta gaida su Haka musharraf amma shi Uncle's din shi kad'ai ya gaisar ya koma yayi zamanshi tare da gaidasu Anty rabi a haka, ta'be baki tayi ba tare da ta amsa ba ta mike ta zo ta kar'bi yaron, tare da satan kallon su Uncle Ahmad dake gaisawa da su momma tace tana kallon hajiya zulai "kinga gara na kar'beshi kar ta hallakashi sbd bakin ciki abinka da juya" hajiya zulai tace "Ai ko de kinga irin abinda ake gayawa su Alhj suka ki ji gashi ko wacce da akayi aurensu tare na shirin juyewa yau ko gobe amma banda ita da ko alamun abun arzikin babu ace mutum be sonka tsakani da Allah dukiyarka yake bukata aki yarda, banza juya" tassssss suka ji saukar mari, a razane kowa ya waigo zuwa inda suke. To fah
Alhamdulillah thanks for the prayer 🙏
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Las Las
Page➡️1️⃣0️⃣0️⃣▶️🔚🔚🔚
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Gabad'aya parlorn mikewa sukayi ganin yadda yake 'bari kamar mazari dama ranshi a 'bace yake ga maganganun hajiya zulai da Anty Rabi'ah yau ba don matar uncle Ahmad bace, ba don yana ganin girman uncle Ahmad fiye da sauran uncles dinshi ba, ba don ba tarbiyar momma ba kenan da ba abinda ze hanashi yiwa matar dukan mutuwa, shiyasa ya sauke hannunshin akan d'anta da dama shine silar 'bacin ranshi tun farko, uncle nasir ne yace "musharraf wai lafiyanka kuwa?" Momma tace "me ya maka haka?" Hararan da sufyan ke mishi ne yake kara tunzura shi hakan yasa shi had'ashi da gini ya shakeshi da sauri khairi ta dafa hannunshi ganin yadda hajiya zulai ke ihun ze kashe mata d'a.
Momma ta karaso ta d'aga hannu da niyyar sauke mishi mari da hanzari khairi ta shiga marin ya sauka a fuskanta har seda ta zube a kasa tsabar karfin marin, ido ta runtse yanzu da haka marin ze sauka a fuskanshi inaa ta san komai musharraf yayi akwai dalili tana kyautata zaton ba Haka kawai ze hau dukan shi ba, da azama musharraf ya sake Sufyan yana d'agota kallon cikin idanunshi da yayi ja tayi ta runtse ido se hawaye da kirjinshi ya had'ata yana kallon momma da ta tsaya kaman mutum mutumi haka su uncle nasir ma karfin halin khairi suke jinjinawa.
A hankali ya fara magana cikin rawar murya ya bada labarin abunda aka turamishi ran aurenshi wadda yayi sanadiyar kwanciyanshi asibiti ya kara da irin zaman da yayi da khairi kan ya zo ya gane karya ne da alqawarin da ya mata ya d'aura da "na shafe wata shidda chur Ina neman me wannan numbern, har experts a harkan tracking fiye da mutum hud'u na biya amma ba'ayi nasara ba se yau a d'azu d'aya ya kira ni ya bani full details na wadda ya had'a hoton kuma sunje sun sameshi da police inda ya amsa fault d'inshi ya kuma bada details na waenda suka sa shi, and that turns out that sufyan ne ya biyashi don aikata hakan and wanchan munafukan ya nuna Afreen ita ta zo har cikin gidan nan ta d'ad'auki qalbee hotuna daban daban" yana shafa bayan khairi yace "am sorry qalbee na kasa cika alkawarinki sbd munanan kalaman da iyayensu suke jefanki dashi" kallon su Hajiya zulai yayi yace "and yhu this is my first and last warning Wallahi wallahi mata ta kara zagarmin mata se nayi mata abunda bata ta'ba tsamanni ba, ku kuka hallici juyan? Ko ku kuka h......" "musharraf" momma ta kira shi In a whisper.
Shiru yayi tare da jan hannun matarshi suka fice daga parlorn, basu karasa fita ba suka ji saukar mari har kusan kala hud'u, uncle nasir ne yake saukewa sufyan duk sanyinshi seda ranshi ya 'baci yau haka ya rufe Afreen da duka wasu irin yara ne su, seda uncle Ahmad ya gama dawowa daga suman tsayen da yayi kan ya kalli Hajiya zulai yace "ki tafi gidanku se na neme ki" waro ido sufyan yayi tare da zubewa a wurin yace "kayi hakuri dad wallahi bazan kara ba, karka hukunta mom akan abinda ba ita ta aikata ba na tuba" hararanshi uncle Ahmad yayi kan ya juya ya fice momma de bata ce komai ba amma kallo d'aya ka mata zaka san ranta a 'bace yake haka su Amrah da mai jego ma se harara suke sakewa su afreen din, wato uncle Ahmad ya san hukunta mahaifiyar sufyan ne kad'ai ze sa shi ladabta yayi nadamar gaskiya sanin yadda yake kaunar mahaifiyar tashi, ita kuwa cikin kuka da ihu ta fice daga gidan, hajiya rabi'ah ta rufa mata baya Afreen kuwa Uncle nasir yace da ita ze tafi zata ci me unguwan garinsu a gidanshi cikin sacewar gwiwa sufyan ya mike ya fice, nan momma ta kira bappa ta fad'a mishi duk abunda ya faru ta kuma tabbatar mata da hakan, inda bappa yayi alkawarin sa taheer yaje har gidanta ya ci mata mutunci kuma shima ze kirata haka diddinsu ma, hakuri ya dinga bata har taji kunya.
Bayan ta kashe suka zauna tattaunawan da su Amrah, a bakin gado ya ajiyeta shima ya zauna hannunshi na kan yatsun momma da suka fito a kumatunta cikin kasa da murya da tsantar damuwa yace "am so sorry qalbee, me yasa kika shiga? Dan Allah karki sake da na gani da ban bari ba am sorry" murmushi khairi tayi tana kifa kanta akan kirjinshi tace "mind not hayatee, bazan iya ganin wani abu ya ta'ba min lafiyanka ba da rai na da lafiyata In bari" zagaye hannunshi yayi zuwa cikinta yace "Ina sonki" murmushi me sauti tayi tace "same here hayatee".
Anan suka shantake, kwana uku da zuwansu su dada suka sauko Gombe ana washegari suna kenan, tun washegarin barinsu Abujan suka diro, musharraf da khairi ne suka je taransu mota biyu sukayi amma gidan inna zasu sauka shi kuma Abba a hotel ze kwana tunda kwana biyu kawai zasuyi, a natse matafiyan suka fara fitowa Arrivals janye da akwatunansu khairi kam kaikaya ido tayi tana tunanin idon ya fara deceiving d'inta amma abu guda kaman na farko ta gani dafa musharraf tayi tace "kana ganin abunda nake gani kuwa?" Murmushi yayi yace "surprise ni na hana a fad'amiki daidai idonki ke gani".
Da gudu khairi ta karasa wurin dada da take shirye cikin atampha super wax da yaji kud'i d'inkin riga da zani ta d'aura d'ankwalinta me kyau ta yane kanta da orange kashka babba idonta sanye da medicated glass fari hannunta riqe da designer hand bag kai ko agogonta abun kallo ne, sossai tayi kyau da gudu khairi ta fad'a jikinta dada ta murmushi ta d'agota "me haka khairiyyah? Look everybody here is eying you se kace ba matar aure ba" kuka khairi ta saka tana kallon idon dada tace "yanzu dada kina kallo na?" Dada tace "kwarai kuwa Godiya ta tabbata ga Allah yau gashi Ina ganin jarumar 'yata" sake rungumeta khairi tayi tana shesheka Abul yace "oh Abba kaga d'aughter d'inka kaman wata baby se afkin shagwa'ba" Abba yace "kyale min daughter tayi son ranta kaima Ai same reaction ka nuna sadda kaga maman naku" gwalo khairi ta mishi tana cewa "sannu da zuwa Abba" yana murmushi ya amsa a lokacin musharraf ya karaso ya duka har kasa ya gaidasu suka amsa a sake kan suka dunguma mota khairi de duk motsin dada a kan idonta tana mamakin ikon Allah da ta gaji da jin yadda dadan ke jefa turanci d'ai d'ai a cikin magana tace "dada dan Allah makaranta kika shiga?" Dariya Abba yayi yace "Eh tayi school na 5months" Khairi de se daad'i takeji har suka isa gidan inna, kowa ya shigo mata sannu da zuwa se yayi mamakin ganinta inna kaman zata maida ta ciki don murna amma be hana In dadan ta jefa turanci cikin magananta innan ta tsigale boko ba.
Washegari dada a gidan momma suka yini da su hajiya ruqayyah suna shan hira sossai momma tayi farin cikin ganin chanjin da ta samu sossai, gidan ya cika da 'yan suna yaro yaci sunan Abbansu musharraf mahmoud zasu na kiranshi irfan sossai kuwa su musharraf sukaji daad'in sunan inda kayanshi da na khairi kawai abun kallo ne bare a zo na momma se na sauran dangi yaro ya sha gata, Hajiya Rabi'ah da Hajiya zulai ko lekowa basuyi ba.
Washegari da safe da misalin karfe shidda su dada suka zo suka d'auki su khairi dayake mota biyu zasuyi tafiyar da ita dukda Abba ya so jirgi amma ba'a cika samun jirgi zuwa jalingo ba se kawai suka hakura zasu bi mota da de su bi jirgin zuwa yola su kuma bi mota zuwa jalingo, manyan prado ne guda biyu da suka ji kud'i fari da baki d'aya Abul, khairi, musharraf da little bakin kenan, farin kuma dada, Abba nabeel da nabeela dayake tsoffin drivers da suka san kan hanya suka samu nan da nan suka fara cin taya.
Awa shidda me kyau ya kawo su jalingo dukda sun tsaya a hanya yafi sau abunda yafi don khairi ta galabaita sossai tayi ta amai duk hankalin musharraf a tashe gashi ta kasa cin komai suna isa Abba ya cewa drivern su ya kaisu unguwa da za'a samu hotels masu kyau su samu su huta kan su nemi asibitin da za'a Kai khairi don taji jiki, magami ya kaisu suka za'bi hotel suka shiga suka biya kud'in inda har drivers d'in suka kama musu d'aki d'aya su biyu, ganin yadda khairi take lafe a jikin mijinta ko tsayuwa ta kasa yasa Abba kama musu d'aki su biyu su ma, shi shi kad'ai, Abul da nabeel suma su kad'ai, se little, nabeela da dada.
Wanka ya taimaka mata tayi duk shima ya zama wani iri kaman shine marar lafiyan ordern abinci ya bayar seda ya tambayeta me zata ci tace pepper soup d'in kayan ciki da black tea me zafi sossai haka aka kawo mata da kanshi yayi ta bata amma abun takaici tana gama ci ta kwararar, har hawayen tausayinta musharraf yayi da kyar ya samu bacci ya d'auketa yayi wanka ya shirya shima yazo ya kwanta don basu da bashin sallah, se la'asar khairi ta tashin wadda tashintan ya jawo tashinshi wanka suka sakeyi sbd zafin da akeyi suka yi sallah kan ya taimaka mata ta shirya tana ya complain ciwon kai, fita sukayi a waya ya sanar da Abba zasu asibiti driver d'aya ya d'aukesu se FMC jalingo khairi de se kallon jalingo takeyi cike da kewa, da suka zo daidai junction d'in asibitin kuwa se taji kuka na zuwa mata hango police division inda aka tsare Abbanta da kyar ta had'iye kukan.
Babu wani 'bata lokaci suka samu ganin Doctor wacce macece gwaji tayiwa khairin cikin abunda be fi awa ba tayi musu congrats da samun juna biyun khairi sossai sukayi murna khairi harda kwalla tuno abunda aka gama gaya mata satin nan, da farin ciki suka dawo musharraf kam ya kasa shiru seda ya gayawa su dada suka dinga ma cikin da uwan Adu'a a kunyace ta gudu nasu d'akin.
Kulawa sossai musharraf ya ci gaba da bata ninkin a kan na da bini bini me ta ke so, me zata ci sede tayi murmushi, washegari misalin karfe tara sukayi wanka suka fito se unguwan sarki suna shigowa memory din rayuwansu na kara taryo kanshi shekara goma sha bakwai a unguwan nan abunda yake musu zafi yadda mutanen cikinta suka kasa gasgata abinda zasu iya da wadda baza su iya ba, a kofan gidan su ummu sulaimi suka parker gidan an gyara shi gwanin kyau ya dawo na zamani ba kaman na da me kyauren buhu ba yanzu harda karamin get brown, gidansu ta kai idonta ga mamakin ta yana nan yadda suka tafi suka bari se bala'e'iyar kura da zaka hango daga inda kake duk yana ya cika ko Ina zanan kuma ya ru'be.
Sauka sukayi dada da khairi suka isa kofan gidan baban sukayi knocking wata mata ce ta zo ta bud'e musu da alamu 'yar aiki ce don riganta daban zaninta daban se d'ankwali daban murmushi tayi musu kan tace "bismillahnku ku shigo" shiga sukayi ta isar da su har madaidaicin parlorn gidan umma dake zaune rike da wata yarinya 'yar shekara d'aya da kad'an ne ta mike da mamaki tace "wa nake gani haka? Kaman khairi da dada???" Murmushi suka mata alamun tabbatarwa da sauri ta ajiye yarinyar tazo ta rungume dada tare da fashewa da kuka se tatta'bata take tana kallonta da kyau, ihun kiran "sulaimi" da takeyi yasa khairi maida hankali don ganin ta inda zata fito, aiko se gata sanye da leshi green riga da skirt ta kafa d'auri da mamaki ta tsaya Kallon khairi kan ta karaso da gudu suka rungume juna bayan gama farin cikin ganin juna dada tace "da mutane fah muke suna waje" umma tace "su shigo mana sulaimi kuje ku shigo da su" fita sukayi ba jimawa suka dawo da su Abba Bayan sun zazzauna nabeel da nabeel kam suna makale da sulaimi ganin umma yasa su sakinta suka je suka rungumeta waya ta d'aga ta kira Baba tace "yayi maza ya dawo suna da manyan baki" Ai ko ba jimawa sukaji tsayuwan machine a kofan gidan se gashi ya shigo ya mikawa su Abba hannu suka gaisa seda ya je kan Abul tukuna ya gane su waye suka zo farin ciki sossai ya bayyana a fuskanshi yana hangen irin motocin da ya gani a kofar gidan da alamu da shi suka zo.
Introducing su Abba dada tayi musu inda aka kara gaisawa Baba ya d'aura da "Ai dayake Allah ba azzalumin bawansa ba, baku jima da tafiya ba gaskiya tayi halinta, wata biyu da barinku garin nan wasu marasa imani kartai suka shiga har gidan su maman hauwa suka ma hauwan muguwar fyad'e se anan ne suka san me asalin fyad'en don yanzu maganan da nake mukun nan gabanta ya ru'be ance HIV da cancer take dashi ita kuma uwar an wayi gari aka ganta a shanye kafanta da hannunta kaman na