Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
fitansu daga d'akin ba jimawa sufyan ya fita hakan ya sa zuciyar musharraf ta kasa sukuni da ya rasa dalili, har yaje yayi wanka ya sauyo kaya daga bayi ya fito yaga basu dawo ba, ranshi yaji yayi wani mugun 'baci ya dinga buga tsaki wadda se da kowa ya tambayeshi ko lafiya yace 'kanshi ke sarawa ga muran da yaki barinshi na toshe mishi kirji' duk sannu sukayi mai.................
Da kai kawai ya amsa har momma ta dawo be bar kananan tsaki ba, idonshi kuwa na kan kofa kur kaman me jiran wani abu mai matukar muhimmanci, ganin basu da niyar shigowa yasa yana kallon momma yace "Ina Amrah ne? I want to ask her something" Anty zulai tace "Ai sun d'an jima da fita da yarinyar nan da su farida suka ce mai aikinku ce ya ma sunanta?" Momma tace "au wai ummulkhairi?" Hannu Anty zulai ta juya alamun bata sani ba................
Wayan Amrah momma ta kira se sukaga side bag d'inta ma a d'akin ta bari, sallaman da su Uncle nasir ke yi musu ne yasa hankalin momma ya bar kan su khairi da d'add'aya suka dinga ficewa se da d'akin ya saura su yasu tukun momma tace "ni kam Ina yaran nan suka shiga ne?" Musharraf da tunda su uncle nasir suka fara tafiya ya sulale ya kwanta tare da lumshe ido yana ta yaki da zuciyarshi da ya rasa gane abinda yake ji se kokarin controlling kanshi yakeyi amma abun na neman fin karfinshi, jin momma tayi maganan dubosu yasa ya sauke boyayyiyar ajiyar zuciya..................
Be bud'e idon ba seda yaji sallaman miemie kofan ya kurawa ido, sam momma bata lura ba sbd ita kad'ai ce a d'akin da little dake bacci, Nuri kuma suna waje da marwan, Amrah ce ta shigo daga bayan miemie se Khairi daga karshe, had'a ido sukayi a tare gabansu ya fad'i da sauri ta kau da kai zuwa wurin momma dake cewa "Ina kuka shige ne haka?" Amrah ce tace "muna daga baya muna hira ne momma"................
Momma tace "Ohk" khairi tace "sannu da dawowa" momma na murmushi tace "yauwa khairi" Amrah na kallon musharraf tace "hamma musharraf gani" Shiru ya mata yana kallon momma yace "Am starving"Β momma na shirin mikewa khairi ta mike ba wai don kanzagi ko wani abu ba kawai gani tayi be kamata sunanan momma ta dinga wani aikin na daban ba musamman ma ita da ta kasance er aiki......................
Kusan basket shidda ne na abinci a d'akin hakan yasa ta bud'e duk coolers dake ciki, bayan ta gama ta d'ago ta kalleshi shima ita yake kallo kasa tayi da manyan idanunta tana mamakin yau wani irin kallo yake mata ne oho, cikin tsiririyar muryarta tace "wanne zan zuba maka?" Shiru yayi seda ta d'ago kai tukun ya kalli abincinta ya kuma kallonta.....................
Cikin kankanin lokaci ta fahimci abinda yake nufi danbum shinkafar ta zuba mishi da sous din hantan ta d'aura akan karamin tray, a bowl ta zuba mishi fruit salad marar sanyi sbd murar da yakeyi, mikewa yayi ya zauna a hankali yana tankwashe kafa, a gabanshi ta ajiye mishi garin ajiyewa ne hannunta ya karkace saura kad'an trayn ya fad'i a tare suka kai hannu amma nata ya riga sauka hakan yasa hannunshi ya sauka akan nata......................
A tare suka d'ago kai suna kallon juna basu san wani irin abu bane ya rike musu idanun cikin na juna, sossai take kallon kwayar idonshi cikin 'batar basira wani maiko da bata san na me ba dake kwance a kwayar idanunshi, take kallo ta jima tana contemplating haka idonshi yake ko kuwa, se yau ta tabbatar da ashe haka idanunshi suke kaman an zuba ruwan zaiba.....................
Shima kallon manyan eye ball d'inta dake sakashi cikin wani yanayi da be san na mene ne ba yake yana jin wani tension na building inside him, rufe kofar da akayi ne ya dawo dasu daga thoughts d'in da suka fad'a, da sauri ta kawar da kanta a kunyace tana zame hannunta, satar kallon su Amrah tayi se taga duk sallah suke da alamu momma ce ta shiga toilet................
Wani munafukin murmushi ya sake he looks so charming with it sbd be bari murmushin ya gama mamaye fuskanshi ba iyakacinta gefen baki wadda yasa dimple d'inshi na dama lotsawa, a matukar kunyace ta zame ta zauna akan plastic chair tana boye fuskanta da hijabin jikinta, wayancewa yayi ya wani basar kaman ba shi ba tare da fara cin abincinshi.....................
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
πππππ
IGIYAR RAYUWAπ
πππππ
Story and written by: fateemah Muhammad gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Pageβ‘οΈ5οΈβ£5οΈβ£βΆοΈ5οΈβ£6οΈβ£
ππππππππ
Da kyar khairi ta sake bayan wasu lokuta amma ta kasa cin abinci sbd wani fitinanniyar kunyarshi da take ji abinka da fulani, shi kam ko a jikinshi se ma yawan satan kallonta da yake, da ya gaji ma kwanciya yayi abinshi yana facing inda take zaune tare da lumshe ido, a jikinta take jin ana kallonta amma ta rasa waye ne ta kalleshi yafi sau abinda yafi se taga idonshi a lumshe....................
Tana cikin sake saken yadda zata tambayi momma labarin rayuwanta da kuma kaddaran musharraf taji an turo kofan, murmushi me kyau ta saki tana mikewa tace "sannu da zuwa mamie" mamien haidar ce tazo tana matukar ganin daraja da girman matan, mamie ma na murmushi tace "yauwa sannu ummulkhairi" gaisawa sukayi cikin mutumci, su Amrah ma suka gaisheta ta amsa musu tana tambayansu school, kusa da momma taje ta zauna suka fara irin gaisuwarsu ta kawaye..................
Nuri ce ta shigo da sallama ganin mamie yasa ta duka har kasa ta gaida ta, amsawa tayi fuska d'auke da fara'a tace "ya service?" Nuri tace "Alhamdulillah mamie mun kusa kammalawa" mamie tace "toh Allah ya bada sa'a daughter" tace "Ameen" tana kallon momma tace "momma inaga ni kam zan koma gida" momma tace "Ohk ku tafi da khairi ma sbd abincin dare" khairi na mikewa tace "toh momma, se kun dawo Allah ya kara sauki" momma tace "Ameen" sallama tayiwa mamie.....................
Suka fice tana satan kallon gadon har lokacin idonshi a lumshe yake, bayan nuri ta bi tana mishi adu'ar samun lafiya, yinin ranan gabad'aya haka tayishi cikin wani yanayi da bata san na menene ba, a chan asibiti kuma bayan fitansu khairi momma ta mike tana cewa hajiya ruqayya "zo muyi wani magana" mikewa hajjiya ruqayyah tayi ta bita..............
Mota suka je bayan sun zauna hajjiya ruqayyah tace "menene aminiya da baza ki bari mu koma gida ba?" Momma tace "hmm Ina so inga komai ya tafi yadda nake so ne ruqayyah, matsalolin musharraf kara yawa suke bazan ta'ba iya barinshi ya kara wattani uku zuwa hud'u nan gaba ba mata ba sbd lafiyanshi" hajjiya ruqayyah tace "me ya faru?" Nan momma ta bata labarin duk abinda doctor ya fad'a, seda ta sauke ajiyar zuciya tukun tace "Ina mishi sha'awar auren ummulkhairi"........................
Waro ido hajja tayi tace "'yar aikin da na turamiki?" Momma tace "ita fa ko kina ga tana da wani aibu?" Hajjiya ruqayyah tace "a'a sam se hankali da tarbiyya da na lura tana da shi kawai de gani nake kaman musharraf be so mace me wayewa ba taya za'a yi yaso wadda ko primary bata dashi, dukda tana kyau da diri kam".................
Murmushi momma tayi tana tuna abinda ta gani d'azu tace "ze so ta ne, tana da hankalin da nake tunani ita ce kad'ai zata iya fiddashi daga halin da yake ciki gabad'aya, sannan tayi karatu zuwa ss2 In kinji turancinta ma zaki rantse private school tayi" hajjiya ruqayyah zatayi magana kenan momma ta fara bata labarin khairi tun daga na iyayenta har ita kanta, wlh se da hajjiya ruqayyah tayi hawaye.................
Cikin tausayawa tace "khaih duniya!! Alhamdulillah Alhamdulillah, Allah mun gode da ni'imarka garemu" don wallahi labarin khairi imani ya kara mata, cikin tausayawa tace "ai ko na sami 'ya aminiya, na d'aukewa mahaifiyarta nauyin duk abinda uwa zatayiwa erta a bukin, sannan me ze hana In an tashi biyawa Amrah kud'in waec da zatayi nan da two weeks musharraf ya biyamata, don kin san yanzu karatu shine gatan kowa a duniyan nan"..................
Momma na murmushi tace "mun kuwa gode kuma zan fad'a mata, eh nima nayi tunanin haka In yaso bayan auren ta ci gaba da karatunta ko a wajen aikinshi ne, sannan Ina tunani su dawo gida gabad'ayansu mu zauna tare a matsayin en uwa" hajjiya ruqayyah tace "masha Allah, Allah ya tabbatar da alkhairi, ya batun Nuriyyah kuma?" Momma tace "dazu mukayi maganan da su yaya Nasir yace yana so asa bukin kawai nan da wata biyu tunda next month zatayi passing out, kinga se a had'a da nasu khairin don zuwa lokacin itama ta gama WAEC d'in"..................
Sun kara tattaunawa kad'an kan suka fito jin har an shiga sallan la'asar d'akin suka koma hajja ruqayyah tayiwa musharraf sannu da jiki tana zolayanshi wato sai abokinshi na nan yake zuwa gidan ta ko, murmushi kawai yayi bata jira tayi sallan la'asar ba ta wuce...............
Washegari
Da safe ya matsa aka sallameshi suka tattaro suka dawo gida, direct site dinshi ya nufa yayi wanka da ruwan d'umi yana jin daadin jikinshi, bayan ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya nufi parlorn momma don Allah ya gani yanzu be son kad'aicewa sbd tunanin dake cika mishi zuciya da kwakwalwa and he hate that..................
A parlor ya kwanta abinshi don ba kowa kasa, yana nan kwance yaji ana gudu a hankali ya d'aga kai se yaga little ce da wasu kyawawan yara guda biyu mace da miji masu tsananin kama da juna ga kyau da Allah ya zuba musu daga ganinsu kuma ya ba zuciyarshi kannen yarinyar nan ne don kamansu, wurinshi sukayo da gudu little ta fad'a jikinshi yayin da su kuma suka jaaa birki...........
Murmushi ya musu a tare sukace "Ina kwana uncle?" Baki little ta turo tace "he's not uncle he is paapi, paapi ga nabeel da nabeela cuties siblings" mikewa yayi zaune yana saukar da little kasa yace "morning twins, ya Dada?" Sukace a tare "tana lafiya, she said we should behave kuma mu gaisheku, and we thank yhu for everything" murmushi musharraf yayi yace "duka mu kad'ai?" Nabeel yace "yes paapi"................
Murmushi ya kumayi yana d'aukan nabeela sama yace "lets go" little ta fara diddira kafa tana turo baki tace "paapiii" Da sauri yace "shhhhhhh, oya wuce muje yawo" tsalle ta fara cikin jin daad'i ta bi shi don har ya riga yayi gaba rike da hannun nabeel, mota ya d'auka suka fice daga gidan..................
Da misalin karfe goma sha d'aya na Safe momma ta sauko kasa zuwa d'akin Khairi a bakin gado ta same ta zaune da sauri khairi ta zame kasa, tace "sannu da fitowa momma" momma tace "yauwa khairi kin gama aikinki kenan?" Khairi tace "Eh na gama momma" momma tace "Toh khairi bari na baki labarin rayuwarmu inda zaki ji daad'in yanke shawaran da ranki ke so, ba zan miki dole ba khairi don wallahi kaman 'ya na d'aukeki, Ina so in na gama baki labarinnan ki yanke hukunci zuwa gobe.....................
Sbd Ina son musharraf yayi aure as soon as possible, kin de ji abinda likita yace a asibiti" Kai khairi ta d'aga momma zata fara bata labari daga asalin tushensu khairi tace "Amrah ta fad'amin a yayin da take min bayanin waenda na gani a d'akin asibiti jiya" momma tace "Ohk bari na fara baki daga auren da aka yi min, Tunda aka kaini gidan mijina dake Abuja en uwa ko wa ya koma muhallinshi a lokacin na gama NCE d'ina, dama tun kafin auren mamaji ya sa hamma mahmoud d'in samamin aikin koyarwa a wani secondary school.........................
Na yi good two weeks ban sa hamma mahmoud a idona ba, sam ban wani damu ba damuwa na d'aya zaman kad'aicin da nakeyi duk girman gidan ba kowa se ni kad'ai a part d'ina, daga waje kuma daga mai bawa flowers ruwa, drivers, se gateman, tunda na shiga gidan ko kofan part d'ina ban fito ba................
Abun ya isheni hakan yasa kawai na shirya a wata ranar Monday na fito dayake ina da Lettern makarantan a hannuna hakan yasa na san sunan makarantan Ina fita driver ya zo da gudu ya tambayeni Ina zan je na fad'a mishi sunan makarantan aiko be yi kasa a gwiwa ba ya d'aukeni se makarantan nayi reporting...................
Na fara aiki da kwana biyu ina zaune a parlor naji an banko kofa an shigo da sauri na mike Ina kallonshi ban hankara ba naji saukan mari hagu da dama a tsorace nake kallonshi yayinda shi kuma cikin zafi yace "Ke!! Ballagaza, wa ya baki izinin fita aiki? In ba jahilci da rashin tarbiyya ba taya za'a yi ki fara zuwa aiki ba tare da izini na ba" a tsorace nace "kayi hakuri zaman shirun ne ya isheni shi yasa nayi tunanin fara aikin kuma naga kai ka ne......" "dakata, ban miki gargad'in aurena ba Kika nace? Wato kinga mai kud'i shine zaki makale mai ko? Toh bari kiji In fad'a miki kin shigo kabarinki ne wai har kina da bakin ce mini zaman kad'aici ya isheki."..................
Shiru nayi kaina a kasa, kafa yasa ya shure ni har seda na kai kasa, nyau ya tofa min kan ya juya ya fice ajiyar zuciya na sauke, hawaye na silalo min kuka nayi sossai na share hawayena, ba yabon kai ba amma Allah yayi ni me tsananin hakuri da juriya ga zurfin ciki hakan yasa ba wadda na fad'awa kuma ba wadda nake da niyan fad'awa, bayan kwana biyu dadda(Aslamiyya mahaifiyar Mahmoud) ta kirani bayan mun gaisa take tambayata ya aiki? Ban so fad'a ba sam amma se ta matsa jin na fara kame kame, kuma kaman uwa take a gareni don diddi na(mamanmu shuwa) haihuwana kawai tayi.................
Wahalana da reno na duk dadda ce, cikin rashin makama nace "hamma mahmoud ya hanani Dan Allah dadda ki rokamin mamaji ya roka min shi zaman gidan ba daad'i" dadda tace "hanaki yayi?" Nace "eh" tace "Toh shikenan se anjima" bata jira cewana ba ta kashe wayan se lokacin naji na shiga hali na tsoro, karfa dadda tayi mishi abinda ze zo ya min abinda yafi jiya.....................
Bayan na gama tunanuka na na tashi na shiga kitchen na d'aura ruwan zafi don yin girki, tunda nazo gidan da d'an sauran kayan miyan da kawayena suka sayo na kafa murhu, nake anfani Allah ya taimake ni ma a rayuwana na fi son mai da yaji akan komai, kuma dadda babban roba guda na yaji ta had'ani da shi a cikin gara na, toh a ranan kayan miyan yake karewa d'an wanda ya sauran nake gyarawa...................
Wani banko kofan da akayi se da na tsorata, a matukar razane nake kallonshi ganinshi da belt a hannu yana gyarawa kan inyi wani yunkuri ya rufeni da duka na fitan hankali yana yi yana maganganu a ciki yana cewa "wato had'ani da iyayena kika fara tun ba'a je ko Ina ba ko? Toh bari inyi miki me tushe yadda zaki ji daad'in kai gulma" yana cikin duka na garin kaucewa hannuna ya buge tukunyar da na d'aura se jikina Allah yasa be yi zafi sossai ba amma azabar wurin kad'ai ya isheni musamman hannun da na buge da shi d'in ganin haka yasa ya kyaleni yana huci yace "for your own information daga yau In kayan gararki suka kare ki nemi abinda zaki ci wa cikinki, tunda kince se kinyi aiki ko biyar na bazan kara kashe miki ba, wawiya jaka"..................
A ranan nayi kukan da ban ta'ba irinshi ba a rayuwana duk da haka ban fad'awa kowa ba nayi jinyar kaina na koma bakin aikina, In takaice miki khairi a haka muka shafe kusan wata biyu lokacin ni nake zuwa da kaina in sayi kayan abincin da zan ci kuma In biya kud'in mota da kaina sbd ya hana drivern shi tukani kwata kwata ma ya hana In ta'ba mishi ko mota ne, kullum In zan fita zuwa makaranta haka zan ganshi da mata kala kala ba randa na ta'ba ganinshi da mace d'aya hakan yasa nake ta adu'ar Allah ya rabani da shi da gaggawa In kuma shi ne mijina na har abada toh Allah ya shiryaminshi......................
Wata ranar laraba da har abada bazan manta ba, bayan na gama d'an girki na na dare kad'an na ci na sha ruwa, tare da shigewa d'aki shap na manta dawowana ban rufe kofan parlorna yadda na saba ba, na fito wanka d'aure da zani a kirji naga mutum tsaye a bakin kofan bayangidan yana ta layi a matukar firgice na juya da niyar komawa se ji nayi an riko ni, irin rikon da akewa 'barawo In takaice miki a ranan mahmoud yayi min mummunar fyad'e azabar da na sha Allah ne kawai ya sani.....................
Sati nayi ina jinyar kaina har asibiti naje akayimin d'inki da nurses din suka tambayeni fyad'e aka min se ce musu nayi eh, sossai suka tsinewa wadda yamin hakan ban tanka su ba har suka gama aikinsu, nan ma seda na kwana da safe na koma gida Ina iyakar kokari na wajen ganin ba wadda ya fahimci irin zaman auren da nakeyi, a haka a haka rayuwa ya ci gaba da gurgurawa duk randa ya shawu ya bugu haka ze zo ya farmin kaman dabba se ya tabbatar ko numfashi bana iyawa kan yake kyaleni In naki bud'e mishi kofa kuwa duk sadda ya kamani se yamin dukan da ko tashi bazan iya ba.................
A haka na samu cikin musharraf, cikin wannan wahalar rayuwan gashi ko nayi niyyan fad'awa wani se in kasa, don ma makarantan da nake aiki suna min uzuri sbd tausayamin da suke kullum fuska na a kumbure idona a tare da jini basu ta'ba tambayana wa yake min hakan ba sede su tausayamin suyi ta min sannu, cikin musharraf me tsananin wahalarwa ne hakan yasa na kara ramewa nayi baki kirin, har iska