Advertisements
Chapter 38 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 38

111K to 113.1K   out of 113.1K words

jarirai tsabar shanyewa komai na jikinta a karkace wasu sunce garsa ne ya buge ta don ko magana da kyau bata iyawa, da bakinsu suka dinga tona asirin kansu".

Abba yace "Allah kenan" Abul yace "baba gidanmu kuma ba waenda suka shiga ne se naga kaman har kwad'on da muka bari ne a jiki" Baba yace "hmmm gida kam ya gagari kowa zama duk waenda suka shiga basa kwana d'aya suke guduwa suce wai aljannu ne a gidan ba abinda ba'a mishi ba amma an kasa zama" kallon gidan su baban kawai khairi keyi kaman baza tayi magana ba se kuma tace "umma babyn waye hannunki kyakyawa haka?" Umma Tace "'yar sulaimi ce sunanta ummulkhair, tafiyan ku da wata d'aya Allah ya fitar mata da miji tayi aure na rufin asiri tana zaune a millennium suit" yadda unman tayi pronouncing seda ya sa su dariya sulaimi ce ta gyara har suka iya fahimta sossai khairi taji daad'in takwaran da aka mata, inda umma ta ci gaba tana hararan Sulaimin "yanzu ma yini ta zo mana shine kuka same mu nan, kinga gidan nan duk mijinta yayi wahalan gyare mana, ya saya wa babanku babur ya chanza mishi Sana'a Alhamdulillah kawai".

Sun d'an jima suna hira don har abinci su khairi da sulaimi sukayi  aka ci aka koshi, dukda khairi bata jin daad'i sossai ga tashin zuciya ko abincin bata iya ta ci na kirki ba, kan sukayi haraman tafiya don a yau d'in suke son shiga Baaba gaasa, kan su tafi dada tace "kuzo muje mu duba jikin su maman hauwa" baki gaba khairi ta ke tafiya ita bata ga dalilin shiga musu ba amma ba yadda ta iya haka ta karasa suka shiga musharraf na mata gwalo a fakaice hakan yasa ta murmushi tare da jefa mishi hararan wasa.

Suna ganinsu se kuma tausayinsu ya kamasu ganin yadda suka koma abun tausayi rayuwa ta musu d'aurin kazan kuku duk sun fice hayyacinsu gafara suka dinga rokansu duk suka amsa da sun yafe, khairi ce ta fara fitowa musharraf ya bi bayanta a jikin mota suka tsaya yana kallonta yace "ya akayi kikayi saurin yafemusu qalbee?" Murmushi tayi kan tace "na yafe musu ne sbd sune silar had'uwata da hasken rayuwata, muradin raina, taurarona, rayuwana gabad'aya da numfashina" juya ido yayi yana murmushin shi me kashe 'yan mata yace "tab amma wannan tauraro sa'a ne dashi duk wannan matsayi shi kad'ai?" Itama tana murmushi tace "Ai ya fi haka hayatee ya zarta duk inda kake tsammani I love him to the moon and back, i will love him to the square of infinity, I will definitely be nothing without him cos he's my oxygen" wani irin murmushi musharraf ke yi da duk wadda ya gani ze san irin shaukin da yake ciki, dafe saitin zuciyanshi yayi yace "ashhh waennan kalaman sun soke ni dayawa baby, ki bari haka kar na fad'i na rasa me tallafe ni" far tayi da ido kan tace "aka gayamaka zan iya bari ka fad'i har kasa ne? Inaaa bazan iya barin kwaina zuwa kasa ba don na san in ya fad'i rayuwata tazo karshe" kad'a harshenshi yayi kan yace "Ina sonki dayawa" ganin su dada sun fito yasa ta fasa bashi amsa.

Sama sama suka shiga sauran makwabtan kan suka tafi da alqawarin in sun dawo yini guda zatayi a gidan sulaimi su sha hiran bayan rabuwa, duk abinda sukayin nan bata ga idi ba runfar sun ma babu a wurin kuma bata tambaya ba, kallon hanya kawai sukeyi suna hira kasa kasa suna ganin yadda hanyar duk ta lalace In ba mota me kyau irin nasu ba jiggatan da mutum ze yi Allah ne kad'ai ya sani, fulanin da ke kiwo da masu tallan nono da suke wucewa jefi jefi ba karamin burge musharraf suke ba be ta'ba ganin irin hakan dayawa ba don na gombe basu cika yawa haka ba kuma al'adunsu da shigensu daban daban kasancewar fulatancin ma kowa da irin nashi.

Dada ce ta dinga kwatance har kofan gidansu sauka tayi tana kallon yadda gidan yayi mugun lalacewa da fargaba fal ranta ta shiga cikin gidan, da sallama kallo d'aya ta mishi ta san ba mace ganin yadda duk gidan tarkace ne up site down, da sauri ta karasa d'akin babanta jin ana tari daga ciki, kwance yake kashir'ban kaman macecce kallo d'aya ya mata ya fashe da kuka yana mika mata hannu da gudu ta karasa ta rike bata damu da kazantar da yake ciki ba, ta d'agoshi ya zauna yana zama ya fara rokan yafiyanta akan hukunci da ya yanke akanta ba tare da bincike ba, bakinshi ta rufe tana hawaye tace "Ina umma?" Yace "ta rigamu gidan gaskiya bayan ciwon da tayi fama da shi na shekaru uku ba ta iya ko mikewa zaune, ta ban labarin duk halin da ta saka ki a ciki ki yafemin dan Allah safiyya" mikewa tayi ta d'ibi ruwa a rijiya ta mishi wanka tsab bata ko damu da su Abba dake zaune a mota ba seda ta kimtsa shi ta fito suka shiga tare ta nuna wa Abba shi a matsayin mijinta na yanzu a hankali ta bashi labarin rayuwanta gabad'aya inda ta tambayeshi yayyunta yana kuka yace "anyi wani cikowa da ya hallaka su gabad'aya cikin dare nima lokacin bana nan na tafi kiwo shine sanadiyar kwanciya na, har 'yan gidan su umar gabad'aya ba wadda ya tsira" Abba ne ya nuna be ga anfanin zaman su ba su d'aukeshi su tafi dashi Inda musharraf ya bada goyon baya da kyar ya yarda suka d'aukeshi suka tafi basu yada zango ba se cikin jalingo kwana kawai sukayi washegari suka wuce yola sukayi komai na jirgi don tafiya da Abba dayake national ne kuma Abba ya san mutane cikin kankanin lokaci aka gama komai suka wuce Abuja se ta waya suka sallami su sulaimi akan zasu sake zuwa In shaa Allahu tunda zumunci ya kullu.

Suna isa Abuja Suka wuce da baba asibiti, khairi kam seda aka mata Karin ruwa sbd stress da yayi mata yawa ta huta sossai kan aka sallameta baba ma an bashi kulawa sossai cinkin lokaci kankani ya warware ashe ba warwarewan lafiya bane na kiran Allah ne kullum se ya roki yafiyan dada kan wata ranar juma'a ya cika wadda hakan yasa 'yan gombe kusan duk suka zo mata ta'aziyya tayi kuka sossai na rashin mahaifinta gashi yanzu ko 'yan uwa bata da.



Bayan shekaru goma

"Lastly Dr. Ummulkhair Umar Farouq" tafi wurin ya d'auka raf raf raf a hankali ta mike sanye da wani arniyar leshi da yaji kud'i blue d'inkin doguwar riga ta d'aura rigan grad dinta a kai maroon color akan kafaffen d'ankwalinta ta d'aura hulan mayafinta zagaye da wuyanta wow da kyar na gane khairi ce ba don an kira sunanta ba se na karyata, tayi wani irin cika ta kara fari sossai, murmushin da takeyi ya fito da hakirin makkanta cikin jerin fararen hakwaranta, wuwulla ido tayi tayi da kyar ta hango hayateen ta wadda shine gatanta da komai nata shi ya tsaya mata wurin cika burinta na karatu me tsananin zurfi har ya kai ga yau ta kamalla phd d'inta.

Hannunshi d'aya ya d'aga mata murmushi kwance a fuskanshi yayi wani irin kyau ya kara girma ya ajiye gemu me tsananin kyau yadda yayi style dinshi ma kawai abun kallo ne, wata kyakyawar yarinya 'yar shekara d'aya da wata takwas ce rike a d'aya hannunshi se zizzillewa take yana rike ta, murmushi tayi tana girgiza kai rigiman Arwa se ita.

Cikin karramawa bayan dogon yabon da aka yi mata aka bata kwalinta a hannu wadda ya sata zub da hawaye, komawa wurin zamanta tayi tana share hawayen fuskanta, bayan an gama taro suka fito se dube dube take ta inda zata hango family d'inta chan kuwa ta hangi Little na zuwa wadda yanzu ta koma Adda zarah don taki yarda da Little kuma In ba babanta ba rike da hannun wasu kyawawan yara biyu waenda zasuyi shekara goma goma se wata 'yar shekara biyar bayansu tana tafiya bakin nan a zum'bure da alamu laifi aka mata.

Juya kai tayi se taga dada, momma, Amrah da tayi aure da yaranta uku, se miemie ita kuma yaranta hud'u se Abul da yanzu ake shirin yi mishi aure wadda ya zama doctor Abulkhairi umar faruq gwararren likitan kashi, se Afreen itama babynta d'aya da Nasreen me fama da tsohon ciki, dada ta kara haihuwan yara maza biyu Abdulhaleem da Abdulrahim ba 'yan biyu bane. duk a tsaye wuri d'aya hannun da taji cikin nata da wannan fitinannen turaren nashi ya sanar da ita waye ne murmushi tayi tana kallonshi sadda se ji sukayi ana zuba musu ruwan pics, zarah tace "Kai mommy and paapi kunga yadda kukayi kyau ga little arwa se murmushi take zubawa".

Hararanta khairi tayi ta kuma harari yaranta na fari da suka kasance 'yan biyu suka kuma ci sunan Abbanta da Abban su musharraf ake kiransu 'mussadiq' da 'mu'allim' tace "waye ya ta'bamin 'ya?" Musu suka fara wannan na ba ruwana wanchan na ba ruwana babyn me suna Nihal wacce taci sunan dada tace "mommy ya mussadiq ne ya mareni don na kira sunanki da karfi ana event" kallonshi tayi da sauri yace "am sorry mommy" girgiza kai tayi ya san bata hakura ba wuyan su koma gida ne kawai.

Suna 'yar hira suka karasa wurin su momma se mamakin zarah da ta koma buduruwa 'yar sixteen nake wacce ke dab da fara jarabawar gama secondary da su nabeel amma yanzu basa nan suna jalingo wurin umman su sulaimi, sossai su Abba suka taya ta murna inda suna komawa gida taga surprise walima daga mijinta inda su Anty farha suka zo kusan gabad'ayansu yanzu ta haihu har uku ma, su Asma'u duk anyi aure da 'ya'ya taji daad'in ganinsu sossai inda aka ci aka sha a ranar suka juya kowacce ta koma inda take aure dukda rabinsu anan Abuja suke dama khairi na lecturing a Base university kuma anan ta yi phd d'inta anan kuma aka kara mata matsayi ta ci gaba da kayanta cikin farin ciki da jin daad'in rayuwa, sufyan ya jima da nadama inda ya roki yafiyarsu suka kuma yafe mishi ya kuma auri Afreen 'ya'yansu uku, Hajiya zulai da hajiya Rabi'ah duk sunyi nadaman abunda suka dinga yiwa khairi sbd yadda take kyautata musu.

Inda dadda da Mamaji da kuma bappa duk suka riga gidan gaskiya har inna amma duk mutuwan lokaci daban daban diddi ce kad'ai ta saura a dole ta dawo cikin gombe tare da momma a sabuwar gidanta da musharraf ya sauya mata tunda ba yadda basuyi ba ta sake aure taki kuma ba komai ya haddasa hakan ba se rashin samun jin daad'inta a auren na farko wadda take gani duk haka ne, shiyasa ta za'bi zama da yaranta har sukayi aure abunsu.


hajiya ummulkhair da Alhaji musharraf soyayyarsu na nan se ma abunda yayi gaba don sun yarda da kalman nan na true love never fade, tsohon gidan su khairi ta gina gidan marayu a wurin da niyyar ladan ya kaiwa mahaifinsu inda dada da Abul sukayi rijiyoyi da massallatai duk da niyyar ladan ya kai mishi don har gobe suna jin sonshi suna kuma alhinin mutuwanshi.




Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

Anan na kawo karshen littafin nan na IGIYAR RAYUWA abunda mukayi kuskure Allah ya yafe mana abunda muka rubuta daidai kuwa Allah ya bamu ladanshi.

Godiya me yawa a gareku:

ANNUR WRITERS ASSOCIATION.

Mu Karu da juna group: ba karya na ji daad'in kasancewa da ku sossai kuma har abada Ina alfarahi da ku na gode kwarai Allah ya bar kauna.

Ban manta da ku ba readers d'ina na queen bee, waenda suka karanta suka kuma nuna sun karanta suka kuma yi comment na gode kwarai da kaunarku.

Sauran masu karantawa without vote, comment or showing Appreciation Allah ya shirya.

Adama Aliyu duk da a karshe kika zo amma na ji daad'in comments dinki sossai 'yar garinmu Allah ya bar kauna.

My Oda half Haneefa Muhammad Gurin godiya dubu ba don ke ba da se kuyi sati uku baku samu update ba, yadda kika matsamin akan typing🙄☹️hmmm shaa I love yhu.

My blood Aisha Muhammad Gurin me karatun sirri Allah kar ya tona asiri🤭😜

Maman khalil🥰
Maman heedaya❤️
Ummu rijaaal🥰
Maman meenat❤️
Zainab Ads🥰
Hauwa Adam(jiddo)❤️
Aisha lawal shahud🥰
Salmerhalee🥰
Saadah sanusi🥰
Salmer🥰
Nagartacollection🥰
Ummu muzammil🥰
Khadija Ads❤️
Ummu Ameer🥰
Hassana S Fagge🥰
Sadiya muhammad🥰
Khadija(queen)🥰
Sadiya tijjani❤️
Maijidda❤️

Waii da ma waenda ban ambata ba duk ina yinku kuma ina sonku Allah ya bar kauna.

Lastly my wattpadians kar ku ce na manta da ku kuna raina na gode kwarai Allah ya bar kauna, big heart for yhu guys❤️❤️❤️❤️





'Yar mutan Adamawa na muku fatan alkhairi.
















38 / 38