Advertisements
Chapter 27 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   27 / 38

78K to 81K   out of 113.1K words

*Am so sorry dearies wallahi wani important thing ne ya sha min kai kwana biyu kuka jini shiru, am very sorry for keeping yhu guys waiting🙏*

Page➡️7️⃣5️⃣▶️7️⃣6️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Manyan fararen idanunta da ta waro su sbd tsoro ya ke kallo da lumsassun idanunshi da kaman an d'iga mishi zaiba, a hankali ya saketa gabad'aya yana sauke boyayyiyar ajiyar zuciya kasa tayi da kanta tana motsa lips d'inta da sukayi matukar d'auke hankalinshi shiru yayi yaki magana har na kusan mintuna 3 ganin da gaske baze yi maganan bane yasa ta cewa "Ina kwana, ka dawo lafiya?" Kallonta kawai yakeyi ba tare da ya amsa ba, baki ta tura tana jujjuya idanunta murmushi kawai yayi ya wuce ta yayi tafiyanshi abunshi.

Tana ta kunkuni har ta isa d'akinsu don abun ya bata haushi tana mishi magana ya wani yi banza da ita, a fili tace "samu ma kayi na maka magana, d'an ba kara" zubewa tayi a kan gado gefen dada, dada tace "lafiyanki ko? Irin wannan fad'owa haka" Khairi tace "lafiya dada, dada Ina kewan d'an uwana, ko me ya sameshi ya hana shi dawowa garemu se Allah" Shiru dada tayi na mintuna kan tace "hmmm Allah ya bayyana mana shi nan kusa khairi ba ke kad'ai ke kewanshi ba, adu'a zamu ci gaba da yi har Allah ya bayyana shi".

Khairi zatayi magana kenan taji an turo kofa d'aga kai tayi se taga su little, mikewa tayi tana murmushi ganin yadda suke rige rigen mata oyoyo rungume su tayi gabad'aya na seconds kan ta sake su tana cewa "muje room d'inku maza In muku wanka ku samu ku ci abinci" jansu tayi ta bar nabeel nan yana cire kayanshi sama suka haura tayi musu wanka ta bud'e sif d'insu kayansu na wanke na jere tsab ta zaro musu riga pink da jeans blue se blue hula me kyau sossai, d'akin su Amrah suka shiga suka samu Miemie na bacci Amrah na kallo a system.

Gadon Amrah suka nufa tare da tsalle akanta ihu ta sake tana mikewa zaune Khairi na tsaye se dariya take musu, "what!!!! Lallai ma yaran nan, wato ke kika turosu ko?? Toh wallahi In kama yaro anan ku ga yadda ake ribiti" Ai da gudu sukayi waje har khairi suna mata dariya itama bayansu tabi tana d'akawa Miemie duka itama a fusace ta tashi ta bi bayansu don sun katse mata baccinta me daad'i.

'Dakin dada suka shiga da gudu yayinda khairi taja baya tana musu dariya sossai ta san dada na chan tana Shari'ah bata gama dariyan ba taji ance "what's funny?" 'Dan razana tayi don bata ji zuwanshi ba se magananshi kasa tayi da kanta tana cewa "babu" kafin ya kuma magana suka sake fitowa da gudu turus suka tsaya ganinshi, had'e rai yayi yace "baku da hankali ne? Katti da ku ku zauna kuna mana gudu a gida. Yara sunayi ku kunayi?" Shiru sukayi Miemie na tura baki, Amrah na mata dariya a fakaice ganin hakan yasa ya gane Amrah ce ta nemi fad'a hakan yasa ya kama kunnen Amrahn ya murd'e da karfi ihu ta sake tana cewa "sorry Hamma" dariya khairi keyi sossai tana mata gwalo shagala yayi da kallon ta har Amrah ta zame suka gudu sama da Miemie suna mishi dariya da kallo ya bisu kan ya juyo yaga wayam ba ta nan, murmushi yayi yana shafa kanshi ya fice daga parlorn.

Washegari da karfe 10 suke da papper hakan yasa tayi wankin da take da shi da wuri dayake yawanci inner wears d'inta ne yasa ta nufan chan bayan garden don shanyawa, a natse ta karasa da bucket d'inta a hannu sanye take da cotton night wear masu taushi farare wando har kasa da riganshi se ta d'aura karamin farin hijab a kai kafanta sanye da fararen silifas.

A natse take tafiya har ta isa ta fara shanyanta tunda tazo wurin take jin warin taba ta tabbatar shine bata nemi inda yake ba don bata son ganinshi dashi a yana sha, zuciyarta taji ba daad'i duk ya chunkushe, Sam bata fata ya ci gaba da shan taban nan har aurensu bata san yadda zatayi ta sashi denawa ba be bata fuska ba gashi momma ta d'aura hope a kanta tana jin idanunshi a kanta amma taki juyawa se shanyanta take yi duk da kunyan da take jin kaman zata natse amma ranta dake 'bace ya hanata denawa.

Bayan ta gama ta kama hanyar ficewa daga wurin yi tayi kaman bata ganshi ba dayake dole se ta wuce ta inda yake zaune akan wasu kyawawan kujeru green color, kan ta fita daga wurin hakan yasa tana isowa daidai inda yake ta kara kau da kai be wuci taku d'aya ta wuceshi ba yasa hannu ya rike hannunta tare da janyota baya tayi kaman zata fad'i kan kafafunshi dake mike se yayi saurin janye kafafunshi ta zauna tana rintse ido don ta d'an ji zafi In a whisper yace "sorry" Shiru tayi mishi 'bata rai ta kuma yi tana motsa lips d'inta don har lokacin be dena busa hayakinshi ba.

Bata hankara ba taji babban yatsanshi kan lips d'inta da take ta motsi dashi, da sauri ta d'aga manyan idanunta ta zuba cikin nashi karkata kai yayi looking so naughty yace "I like your lips, in munyi aure it will be my something else" juya idanunta tayi tana ture hannunshi tare da kokarin mikewa, da sauri ya maidata ta zauna yace "wai menene kike ta 'bata rai?" Kallon d'ayan hannunshi tayi ta kauda kai.

Goshi ya dafe tare da yarwa ya take yana cewa "bakya so?" Kai ta gyad'a mishi yace "Toh shikenan In shaa Allahu daga yau na dena sha amma fah se kin min alkawarin har abada baza ki sani bakin ciki ba, ba kuma zaki sani dana sanin aurenki ba, ummulkhair maganan gaskiya bazan iya ci gaba da danne abinda nake ji a zuciyata game da ke ba, kece mace ta farko da ta karya padlock da na sawa zuciyata bayan mutuwar surayyah" ya fad'i surrayahn da wani d'aci a zuciyarshi da har tana iya ganewa.

Kallonshi kawai take ta kasa magana be kalleta ba yace "ban san ta ya ba ban kuma san yaushe kika shiga zuciyata kikayi kane Kane ba ko fili kad'an na wata mace baki rage ba, khairr Ina sonki da dukkannin zuciyata Dan Allah karki ta'ba cin amanata da soyayyata, tunda aka haifeni ban ta'ba jin irin son da nake mikin nan ba akan wata mace bayan mommana".

Numfashi ne ya nemi d'aukewa khairi she just can't believe, ya Allah ji take kaman ta tashi tayi ta taka rawa yayinda musharraf ya sake yake ta fad'a mata sirrin zuciyarshi, Sam be san nata zuciyarma cike yake da tsantsar soyayyarshi ba wadda ya fara har'bawa tun daga randa ta kalleshi a Arabian estate. Magananshi ya katse ta inda ya ci gaba da cewa "ummulkhairr kin gama da zuciyata tun daga randa na ganki a area d'in su haidar wasu banzaye na kokarin keta miki haddi wadda shine kallona na biyu dake, na kasa gasgata hakan seda naga nayi iya kokarina wurin hana son tasiri daga ranan amma abun ya ci tura, na kwana cikin matsanancin zazza'bi a lokacin amma zuciyata na gareki da duk tunanina na ko kin isa gida lafiya ko baki isa ba.

Ban ji hankalina ya kwanta ba seda haidar ya kira momma sukayi magana a gabana inda yake sanar da ita lafiyanki klau har hajiyarshi ta had'aki da driver don komawa gida, khairr ban san ta yadda zan misalta miki irin farin cikin da na shiga ba a sadda momma ta nuna tana min sha'awar aurenki a lokacin na tabbatar ta ga abinda na hanga a tattare da ke, da kika amince kuwa har azumin godiya ga Allah nayi ba tare da sanin kowa ba.

Ban san ta yadda zan fad'a miki irin so da kishin da nakeyi a kanki ba amma ke sheda ce a sadda wanchan banzan sufyan d'in ya rike min hannunki, Ina fad'a miki hakan ne sbd ban son a d'aura mana aure da shakku ko wani kokonto na junanmu sbd Ina son mu zama sirrin juna, aminan juna, masoyan juna, rufin asirin juna, Ina son a duk sadda wani abu ze faru ko ya had'amu mu zauna tare muyi solving duk wani issues d'inmu tare, kin san abinda ya ninka min son da nake miki daga farko har ya kasa boyuwa?" Girgiza kai tayi tana sake murmushi da tunda ya fara maganan shine a fuskanta.

Cikin kasa da murya yace "sbd irin son da kike yiwa familyna musamman little da momma, khair Ina kaunarki har ban san adadi ba" wani irin ajiyar zuciya ta sauke farin ciki na mamaye duk zuciyarta kokonton auren wadda baya sonta ya fice daga zuciyarta soyayyarshi ya kara ninkuwa a zuciyarta irin wadda bata ta'ba ji ba don bata ta'ba yin soyayya a rayuwanta ba se daga kanshi bata fata kuma yayi breaking heart d'inta.

Kaman yadda yake mata magana cikin kashe murya itama tace "ba matsala Hamma Allah ya shige mana gaba" 'bata fuska yayi yana cewa "ban gane ba fah, ummu cewa zakiyi nima Ina sonka sweetheart" ya karasa da kashe murya kaman wata mace, da sauri ta rufe fuska tana murmushi tace "I can't hamma" da sauri yace "nop yhu can say it, oya am all ears ko bakya sona ne na miki tsufa ko?" Sauke hannunta data rufe fuskanta tayi tana wasa da yatsunta tace "haba na isa?" Yace "har ki wuce ma".

Time ya kalla kan yace "I thought 10 kuke da papper?" Kai ta gyad'a ba tare da ta kalleshi ba, yace "Ohk je ki shirya karku makara but promise me In kin dawo zaki fad'a min kina sona" Kai ta gyad'a yace "ban yarda ba fah, se kin furta da bakinki tana murmushi tace "Ohk I promise" yace "uhm uhm fah" mikewa tayi tana d'aukan bucket dinta tace "na tafi" yace "take care" wucewa tayi zuciyarta fari kal kaman auduga wani iri take jin kanta kaman tayi ta taka rawa, Alhamdulillah ta dinga maimaitawa tana jinjinawa rahamar ubangiji a garesu.

Duk wadda ya ganta a ranar ya san tana cikin farin ciki ba kad'an ba ko a school waenda suka d'an saba seda suka tambayeta ko kujeran hajji aka biya mata? Murmushi kawai take musu shine amsan amma bakinta yaki rufuwa Amrah ce tace "ni kam kode yayi proposing ne?" Da sauri ta rufe fuskanta shewa waenda suke zaune da su sukayi Amrah kam harda gud'a, kunya kaman ta nitse.

bayan sun gama papper suka fito don tafiya gida kenan me makon su ga driver se suka ganshi tsaye jingine da mota hannunshi rike da waya yana dannawa sanye yake da black jeans white shirt me guntun hannu se ya d'aura black jacket a kan rigan be wani rufe gaban rigan ba don kana ganin rubutun dake gaban fari kal d'in shirt d'inshi da aka rubuta "Just chill" da manyan bakin harrufa, kafanshi sanye da black combat shoe, 'Masha Allah' ta furta cikin numfashinta tana d'aura ido akan black silk hair dinshi da yaji gyara se sheki yake daga nesa.

Class mates d'insu da suka fito tare ne suka fara kusasu daga masu cewa "woowwww guy d'in Chan ya had'u karshe" se masu cewa "wayyo wallahi zuciyata ta har'bu Allah yasa wannan guy d'in ya zama nawa" se masu cewa "innalillahi kinga wani guy a chan Ina ma zece yana sona wallahi da kunga yadda ake zuba soyayya don na san wanchan karshene daga ganin alama" wata kam cewa tayi "wallahi se na mishi magana ko baze amsani ba, bari ki gani ma in fara da d'aukan hotonshi ba tare da saninshi ba irin wannan guy d'in sune ake mallaka ko ta halin kaka ko da kuwa mutum ze dangana ne da malam".

Idanunta da suka fara chanza launi ta d'aga ta zubawa yarinyar da tayi maganan karshe ai kuwa se taga ta d'aukeshi hoto kanshi ta maida idonta ranta na wani irin suya da bata ta'ba ji ba a rayuwanta har wani zafi zafi yake mata, a lokacin shima ya d'ago ganin sun nufoshi yasa ya maida wayanshi aljuhu yana mikewa daga jinginuwa da yayi da motar duk cikin waenda sukayi 'bangareshi ita kad'ai zuciyarshi ke gani ko za'a kashe shi bayan ita be san ko kalan fatan waenda suke gefenta ba har ta iso karamin murmushi tayi mishi wadda ko fuskanta be gama gamawa ba ta zagaya ta bud'e front sit ta shige.

Hakan ya tabbatar mishi ranta a 'bace yake don tun daga ganin farkon da yayi mata yake tunanin ranta a 'bace yake toh me ya 'bata mata rai? Gaisheshi duk sukayi a tare kaman baze amsa ba se kuma yace "lafiya" tare da bud'e mota ya shige baya Amrah ta bud'e ta shige tana mamakin wasu matan don duk abinda suka dinga fad'a akan wanta tana ji, har ya tada motan yaji ana knocking glass saukewa yayi yana kallon faran tsiririyar yarinyar da ta mishi knocking yana jiran jin me ke tafe da ita, khairi da ta d'ago taga yarinyar da ta d'auke shi hoton nan ce se kawai ta fara hawaye shi kam ma sam be lura ba hankalinshi na kan yarinyar tace "plz handsome in baza ka damu ba ka sa min number dinka wallahi daga ganinka naji abinda turawa ke cewa love at first sight" wani d'an banzan tsaki yaja tare da figan motan yana watsa mata kura, en matan da suke wurin suka kwashe da dariya suna nunata a kunyace ta juya sumi sumi ta nufi motar gidansu da yazo d'aukanta........














#vote
#share
#comment












'Yar mutan Adamawa


🎗🎗🎗🎗🎗






                IGIYAR RAYUWA😭






                                               🎗🎗🎗🎗🎗

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, charity, honor and super writers)

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo6763

               'Yar mutan Adamawa

Page➡️7️⃣7️⃣▶️7️⃣8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Tunda ya d'auki hanya ko juyawa be yi ba balle ya ga hawayen da yayi cha'ba cha'ba a fuskanta duk tunaninshi ya tafi ga mata masu kaiwa maza kansu a wannan zamani, mazan yanzu ba kai ka fara cewa kana sonsu ba ma ya aka kare bare, mazan yanzu da basu san darajar mace ba? Ya tabbatar d'ai d'ai ne za'a samu masu bin koyarwan manzo a zamantakewar aure he just take a glance at her a lokacin da ya sha kwanan gidansu waro ido yayi a d'an rud'e yace "qalbee!! What happened to yhu subhanallah are yhu sick? Ko nayi miki wani laifi ne?" Ya karasa yana danna horn na shiga gida.

Me makon tayi shiru se ta fashe da kuka harda shesheka, Amrah dake baya murmushi kawai ta sake ta san ba wani abu bane kishi ne kawai ke d'awainiya da ita, kuma da alamu ze lalla'ba kayanshi da farko ma damuwa tayi da auren hammanta da khairi sbd sanin halinshi amma yanzu zuciyarta fes ashe hamma an iya soyayya harda wani qalbee😅

Yana parking ta fice daga motan khairi ma shirin fita take taji ya riko hannunta cikin damuwa yace "menene ummu?" Cikin kuka tace "ba kai bane ka saurari wasu" waro ido yayi shikam ma be gane inda maganan ta dosa ba hakan yasa yace "ban fahimta ba" tura baki ta kuma yi cike da rigima tace "har hoto fah ka bari ta d'aukeka, har fa cewa take ko da malam se ta mallakeka, amma tana knocking glass ka bud'e" dariya ya saki cikin dariya yace "jealousy jealousy, dama duk kukan na kishi na ne? Alhamdulillah" kukan shugwa'ba ta kara sawa da sauri ya bar dariyan da yake yace "sorry, am sorry sweetheart bazan kara sauraren kowacce mace ba bayan ke da muharramaina In shaa Allah kinji?" Kai ta d'aga yace "oya fulfill your promise" rufe fuskanta tayi da kyawawan yatsunta hakan yasa ya kurawa yatsun ido na mintuna kan yasa hannu ya sauke ya rike su cikin hannunshi yace "wallahi qalbee kina sa ni surutu dayawa In yi ta magana ki ki cewa komai".

Yanzu dinma shiru tayi ya sake cewa "shikenan tunda baza ki min magana ba you can go" ya fad'a yana sake mata hannu ganin kaman ranshi ya baci yasa tace "Ohk sorry, zanyi magana" Shiru shima yayi tace "mi yid'i ma ha nder nberd'e am" tana karasawa ta fice da sauri tana murmushi, murmushi me sauti ya sake yana shafa kanshi zuwa kirjinshi a kan lips dinshi ya furta 'Alhamdulillah' ashe ze sake farin ciki a rayuwanshi? Cikin farin ciki ya fice ya shiga d'akinshi gobe da safe ze wuce hakan yasa ya d'an shirya abinda ze bukata.

Tana shiga parlorn ta samu duk ahalin gidan zaune su nabeel ne kad'ai basa nan suna islamiyya, har kasa ta duka tayiwa su momma da dada sannu da gida kan ta shige d'aki don yin wanka, a ranar da yamma suna zazzaune a parlor ana hira yayinda momma da hamma ke kallon news khairi kuma na tsaye daga wurin dining tana taya me aikinsu shirya abincin dare, su little suna game a waya amma basu sa volume ba, nuriyyah, Amrah da Miemie kam kowacce chatting take yayinda dada ke zaune shiru tana azkar.

Sanarwa aka farayi a tv wadda ya sa su maida hankalinsu gabad'aya akai "Abun al'ajabi wani hawan Allah ne wadda ada aka sanshi farin sani sbd yadda aka dama dashi sossai a siyasar kasarnan inda mukamin da ya rike daga karshe shine mukamin senator ba kowa bane se senator mahmoud Adam, ya mika kanshi ga hukuma akan abubuwan da yayi marasa kyau har gwara da alummah ma akan iyalanshi inda yace 'ya cutar dasu mafi munin cutarwa wadda baze fad'u ba amma yana rokonsu yafiya yayi hakan ne watakil ko zasu yarda da gaske ya tuba yabi Allah su taimaka In sunji labarin mutuwarshi su yafemishi haka iyayenshi su sashi a adu'ar su dan Allah duk san duniya ne da son zuciya se sharrin shaid'an ya ja mishi abinda ya aikata a garesu, yaci amanar aure yayi shaye shaye yayi cin hanci ba kad'an ba yayi zinace zinace.

Abu mafi munin da ya aikata kuwa shine zina da matar d'anshi yana

27 / 38