Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
rawa da zuciyarta keyi sam ya kasa zama wuri d'aya, kai harta tsikar jikinta tashi take..
A zahiri ta san ba da ita yakeyi ba wtkl wakanshi kawai yake amma ta kasa hana gangan jikinta da zuciyarta shiga nishad'i da amincewa da ita yakeyi, bata so sam ya san idonta biyu don kar ya dena hakan yasa ta ci gaba da rufe idon har suka isa, a hankali ta bud'e ido ta d'aura akan wani katon iron blue gate da suke danna horn a gabanshi zaka rantse gidan ba'a kauye bane a cikin garin Abuja ne tsabar kyau da had'uwarshi, bata tashi sanin kyaun gidan ba seda suka shiga ciki a cikin wani tabkeken parking lot sukayi parking inda motoci kala kala a ciki sun kai goma sha biyu..
Hakan ya tabbatar mata da duk en garin Gombe sun iso don ba karamin mota a ciki Parker nasu sukayi tana mamakin bud'in da Allah yayiwa wannan family In bata manta ba Amrah ta fad'a mata su maryam kowaccensu motan kanta take hawa daga yarinya ta shiga jami'a ake mallaka mata mota, girgiza kai tayi a zuciyarya tace 'arziki na inda yake' sauka tayi ganin duk su momma sun sauka, baya ta bud'e ta d'auki little a kafad'anta tare da d'aukan madaidaicin jakan da momma ta bata tasa abubuwan anfaninta, na su nabeel daban su biyu haka na dada, ta juya da niyyan tafiya kenan taji an rike hannun jakan har hanun wadda ya riken na gogan nata, wani irin electrical shock da taji yasa tayi saurin sakewa tana kallon shi..
Ba tare da ya kalli idonta ba yace "Ai abubuwan se su miki yawa" be jira cewarta ba ya zaro trolley d'inshi ya ajiye daga jikin motan tare da bin Bayanta cikin tafiyarshi na Izza da tsantsar kasaita se kace d'an gidan saraki, manyan parts guda uku ne a gidan cikin ko wani part akwai 2rooms and parlor, 2rooms and parlor akallah hud'u hud'u banda part na tsakiyan da ya kasance babban parlor d'aya se rooms guda goma cikin wani dogon corridor, na hagun shine na Abubakar da matarshi shuwa wato diddi da bappa, se na daman na Adamu da Aslamiyya wato mamaji da dadda, na hagun suka nufa momma ce tayi knocking tsadaddan door d'in part d'in bayan haurawansu babban varender me steps biyar ko wani angle.
Mintuna biyu aka bud'e Afreen ce tsaye sanye da doguwar rigan kanti ba ko d'an kwali a kanta ihu tayi tana cewa "oyoyo momma" a take sauran kannenta da yaran uncle taheer suka taho suka rungumeta suna ihu, murmushi kawai take musu ganin oyoyo ya ki karewa yasa musharraf dake tsaye gefen momma ya daka musu tsawa "wani irin rashin hankali ne wannan bakwa ganin da baki muke!!!" Da sauri suka saketa suna juyawa parlorn su khairi suka rufa mata baya, nuriyyah dake rike da sandar dada ta taimaka mata har ciki ta ajiye ta kan kujera.
Kallon khairi musharraf yayi da ta fara nishi sbd little da ta mata nauyi gashi tana shirin zama kasa, hakan yasa ya ajiye jakan hannunshi tare da karasawa wurinta beyi mata magana ba yasa hannu ya zame little wadda yasa khairi razana ya had'u mata da irin shock d'in d'azu don fatan wuyanta da hannunshi ya ta'ba saura kad'an ta fad'a mishi amma se tayi saurin dafa broad chest d'inshi, da mugun sauri kuma ta zame hannunta tana zamewa kasa kunya kaman ta nitse ganin momma na kallonsu.
Lumshe ido yayi ya bud'e yana juyawa da sauri zuwa wani door dake facing d'in na shigowa. Wata kyakyawar farar mata ce da khairi bata lura da ita bama seda tayi gyaran murya tana cewa "sannunku da zuwa lale maraba, ga kishiyoyina" kallonta khairi tayi tana jinjina kyaunta dukda tsufan da ya nuna sossai a fuskanta hakan be hana tsantsar kyaunta fitowa ba.
Ga fara'a da ya cika mata fuska da tsantsar annuri alamu sun nuna tana jin daad'in wanzuwarta da 'ya'yanta a irin wannan lokaci, kasa momma ta zame tana gaida ta amsawa tayi tana tambayarta ya hanya, da Lafiya klau momma ta amsa, su Miemie ma gaisheta sukayi Amrah da tun shigowarsu take lafe jikin matan tace "kawas ya kk" hararanta tayi tana ture ta daga jikinta tace "matsa min anan marar kunya, ki kwace min miji sannan ki zo kina ce min wani kawas aka gayamiki ana kawa da Kishiya ne?" Duk parlorn dariya suka saka.
Khairi da ke murmushi sossai ta kalleta tare da cewa "Ina yini, mun sameku lafiya?" Amsawa tayi da fara'a tana mamakin Ina fatima ta samo kyawawa haka, a mutunce suka gaisa da dada inda momma tayi musu iso zuwa part dinta wato inda musharraf ya shiga, d'akinta ta isar da dada inda ta had'a su Amrah da khairi dakinsun me adaje ne irin na boarding kanana na katako guda 6 anan suka samu musharraf kishingid'e a jikin gadon da ya kwantar da little..
Duk jikinshi a mace hakan yasa da ya kwantar da ita ma ya kasa fita zuwa part d'insu na maza yana mamakin wani irin sabon abu ne yake ji ajikinshi game da yarinyar nan musamman In jikinsu ya had'u hakan na bashi mamaki se kace be ta'ba sanin wata mace ba, shigowarsu ne ya sa shi mikewa ganinsu duk da trolley d'insu kowaccensu ta nufi bakin gadon da ta saba sauka bayan ta mishi sannu, ba wacce ya amsawa se idonshi da ya bud'e yana kallonsu d'aya bayan d'aya gado Amrah ta nuna mata taje gefen gadon ta ajiye jakanta tare da satan kallonshi se kuma suka had'a ido..
Da sauri ta kawar da kanta mikewa yayi ya fice tare da ja musu kofa, ajiyar zuciya ta sauke tare da yaye gyalenta ta zauna bakin gadon a lokaci d'aya duk su ukun suka fashe da dariya hakan yasa khairi kallonsu da mamaki nuri tace "Kai irin wannan soyyayya" Miemie na dariya ta fara wakar "soyayya ruwan zuma kasha kaba masoyi" Amrah kam murmushi kawai takeyi tana tuna gulmar da sukayi tayi tun isowarsu gidan, kunya ne sossai ya kama khairi kaman ta nitse da sauri ta tashi ta fad'a kofan da ta gani tak a d'akin da alamun bayan gida ne, da karfi Amrah tace "gama ki fito don ni ban miki nawa ba" suka sa dariya a tare.
Bayan fitanshi straight mota ya nufa yaja trolleynshi zuwa part d'insu yana bud'e kofan yaga su marwan da sufyan zaune a parlorn suna hira bayan sallaman da ya musu yace "hi dudes" a tare suka ce "hello kun iso kenan" Da Eh kawai musharraf ya amsa tare da wucewa corridor din da d'akunansu suke d'aki na biyu by left ya shiga wadda shine nashi, a gyare yake tsab komai na d'akin fari akwatinshi ya ajiye tare da budewa ya fiddo towel, Sam be jin daadin yadda yake shashare kakarshi da take matukar sonshi, fitowanshi daga part din mommanshi ne ya Samu gaisheta sama sama amsawa tayi tana Jan shi da wasa kaman kullum amma ya kasa amsa mata, kaman yadda ya saba dafe kai yayi yana tuna yadda suke a da, itama kenan da ta haifi mahaifiyarshi Ina ga dadda..............
Da wannan tunanin yayi wanka yana fitowa ana knocking da yes ya amsa aka turo kofan aka shigo Zainab ce, hakan yasa ya had'e rai tam kaman hadari cikin yanga tace "barka da zuwa Hamma musharraf" cikin husky masculine voice dinshi yace "ajiye abinda aka aikoki and leave, In kuma baza ki ajiye ba yhu can leave with it and ko pim kika kara cewa you will definitely regret it" sanin halinshi yasa ta ajiye ta fice sum sum sum..............
Tsaki ya buga tare da fesa turarukanshi ya janyo wayanshi yana zama bakin gado ba don ya d'auki leave a office na two weeks ba ba abinda ze hana shi tafiya Abuja, shi ya tsani irin wannan had'uwa gida d'ayan sbd waennan mayun en matan, haka ya ci gaba da zama a d'akin yayi sallahn la'asar dukda ya san se mamaji yayi fad'a sbd a irin wannan lokaci duk mazan familyn tare suke had'uwa a shiga masallacin dake kofan gidanshi gwanin sha'awa.
A chan cikin gida kuma bayan an aiko musu abinci daga babban kitchen don a irin wannan lokaci ba wacce akeyiwa girki a part d'inta sede ayi a babban kitchen a kuma shirya shi a babban dining area dake part d'in mamaji a chan ake lunch and dinner breakfast ne kad'ai ake turawa part part, momma ta shiga ta sanar musu ga abinci an kawo maza su fito su d'iba..
Fita sukayi suna ta dariyan kunyan khairi don da kyar ta fito daga toilet d'in kuma ta kasa sakewa har lokacin haka suka ci gaba da tsokananta tun bata sakewa har ta sake suka ci abinci tana mamakin Ina su nabeel, Bayan sun gama ne su Amrah suka jaata babban parlor anan ta same su suna ta wasa da sauran yaran gidan sa'anninsu, fita sukayi zuwa part d'in mamaji...........
A nan khairi taga ashe part d'in duk iri d'aya ne shima kofofi biyar ne dashi hud'u 2rooms da parlor se d'ayan kofan kitchen ne me girma dukda be kai na bayan gidan inda ake girkin buki ba, d'aya part d'in Uncle Ahmad da iyalanshi d'ayan kuma uncle nasir da nashi iyalan se d'ayan na momma da Abbansu musharraf amma tunda abun nan ya faru bata sake sauka a part din ba, se en matan da suke sauka ciki anan suka shantake dukda khairi bata magana se murmushi, dukda ta takura amma sam ko a fuska bata nuna ba ganin yadda yawancin en matan ke yi mata kallon uku saura kwata..............
Bayan magrib suka koma part din diddi achan sukayi sallahn magrib da isha Anty Rabi'ah ce ta had'a kan yaran part d'in gabad'aya zuwa parlorn dadda ran nan a had'e ta nuna khairi da su nabeel tace "ba'a gayyata da ku ba" tare da nunawa su Amrah hanya haka suka fita ba don sun so ba, khairi de bata ce komai ba sema gyara zama da tayi tana tunanin yanayin momma bayan dawowarsu daga d'aya part d'in ranta kaman a 'bace amma sbd bata da hurumin tambayanta yasa tayi shiru gashi Anty Rabi'ah ma fuskan nan kaman bata ta'ba dariya ba.
Ita bata ma damu da wai ance ba'a gayyacesu ba dama chan su ba familyn gidan bane so akan me zata damu wurin dada suka shiga sukayi zaune a kasa a gabanta suna shan hira daga parlor akayi sallama ta mike ta fito me aiki ce da tire na abinci tace "inji momma" kar'ba tayi tare da godiya a d'akin suka ci sukayi kat suka ci gaba da hiransu har su nabeel sukayi bacci d'aukansu tayi d'aya bayan d'aya ta kaisu d'akin da aka saukesu tare da shimfide su su biyu gado d'aya, don ta lura kowacce da gadonta har little da suka fita suka bari tana bacci basu dawo sun Tarar da ita ba.
Ta kuma tabbatar spare gado guda biyu ne sbd kar ta takura musu yasa ta kwantar dasu a gado d'aya ita kuma zata kwanta a d'aya, komawa d'akin momma tayi tayi sallama da dada akan se da safe, tana fitowa parlor taga message ya shigo wayanta "sameni mana a parlorn diddi" dukda bata san numbern ba haka taje ta d'auko hijab ta fito ita duk a zatonta musharraf ne ze sata wani aikin, tana fitowa ta kalli sufyan gayen da yayi ta kallonta a asibiti cikin had'e rai tace "gani" murmushi yayi yace "haba beautiful had'e rai sam be kar'bi fuskanki ba, In kina dariya haske kike kaman tauraro plz kar ki hana ni anfana da wannan haske" ja baya tayi tana kokarin wucewa don ganin ya Matso dab da ita bata ankara ba taji ya riko hannunta a lokaci d'aya aka turo kofa d'ayan idon da zatayi se cikin na musharraf.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
đđđđđ
IGIYAR RAYUWAđ
đđđđđ
đŤANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
âYar mutan Admawa
PageâĄď¸6ď¸âŁ9ď¸âŁâśď¸7ď¸âŁ0ď¸âŁ
đđđđđđđđ
Wani irin sharp idea ne ya fadâo mata dukda ta san it is not right a matsayinta na er talaka amma tana tsoron zargi ya shigo tsakaninta da musharraf In har ta aureshi kai ko bata auri musharraf ba ta san mutuncinta na âya mace, cikin abinda be wuce kyaftawar ido ba ta dâaukeshi da wani wawan mari tare da fisge hannunta hadâe gabas da yamma tayi, shi kuwa abun ya zo mishi out of blue, dayake bayanshi ne ke facing kofa se be ga musharraf ba, ganin tana kokarin wucewa bayan ta mareshi, shi da kowacce mace ke burin samu sbd kyaunshi irin na shuwa arab da kuma kudâin da yake dashi, don ma ya nuna yana sonta ba wai asalin so yake mata ba kawai de akwai abinda ya gani jikinta ne da ya kula ba wadda ya lura da hakan..................
Duk Laifin kanshi yake gani na kulata da yayi be danneta ta karfi ya biyawa kanshi bukata ba, cikin zafin nama ya damko hannunta tare da murdâe shi a bayanta wani dâan kara ta sake tana juyowa taji saukar hannunshi a fuskanta wadda har seda ta dena gani da ji na wucin gadi, dâago hannun yayi da niyyar sake kaimata mari yaji an damke hannun, a zafafe ya juyo yana kallon musharraf dake tafasa har fuskanshi yayi ja tsabar âbacin rai, shi karan kanshi ya manta last da yaji irin wannan ciwo da âbacin ran da yakeji daga kirjinshi har kan harshenshi.
Mamaki ne ya kama sufyan a saninshi musharraf baya shiga abinda be shafeshi ba amma gashi akan wannan banzar yarinyar ya hango abinda be taâba hangowa ba a idon musharraf tsantsar kishi da âbacin rai har rufe mishi ido yake, naushin da musharraf ya sake mishi a fuska ne ya dawo dashi daga tunaninshi zaro ido yayi yana kokarin fusge dâayan hannunshi dake cikin na musharraf amma ya kasa.................
Naushinshi musharraf ya dinga yi da hannunshi na dama shi kuma yana tarewa da na hagu ganin In be yi wani yunkuri ba fa musharraf ze iya illatashi hakan ya sa shi saka iya karfinshi ya fusge hannun tare da kaiwa musharraf naushi a fuska shima, Ai ko nan ran âyan maza ya âbaci suka fara kaiwa juna naushi sede baâa dâau lokaci ba sufyan ya galabaita abinka da wadda yayi zaman prison har ya zama kwaro a cikinsu.............
Khairi kuwa ganin musharraf ze iya yin kisa yasa ta Kwasa a guje zuwa part dâin dadda ta san ko ta hanashi ba hanuwa ze yi ba balle ma baza ta iya ba sbd tsoronshi da ya shigeta lokaci dâaya, da karfi ta tura kofan parlorn tana cewa âmomma ki zo, momma!! Hamma musharrafâ tana magana tana nuna waje da sauri suka mike momma tayi saurin bin bayanta ganin ta kuma kwasa a guje, suna turo parlorn suka sake salati a tare............
Da sauri momma tayi kanshi tana kamashi a lokaci dâaya tana kiran sunanshi, cikin âbacin rai ya ture hannun momma yana shirin komawa sufyan da be dena zaginshi ba, uncle Ahmad ne ya tsinka mishi mari yana cewa âbaka da hankali ne da girman ku musharraf? Me ya hadâaku haka??â A zuciye musharraf ke kallon uncle Ahmad yana ta aikin sauke numfashi yayinda hannunshi ke a dunkule, wato ubanshi son kai zeyi me yasa be mari dâanshi ba se shi...........
Sufyan ne dake zaune kasa jini na dâiga a fuskanshi yace cikin alamun kuka a muryanshi âAbba wai akan wanchan banzar yar.......â âdakata!! Wallahi ka kiyaye ni na rantse da girman zatin Allah ka sake cewa abinda zuciyata ke SO banza zan kakkaryaka a gidan nan, In kuma ka Musa ka gwada inga uban da ya tsayamakaâ...........
Shiru sufyan yayi don wallahi ya tabbatar tunda ya furta har yayi rantsuwa ba abinda ze hanashi karyashi hakan ya sashi iya bakinshi, wani irin shock khairi ta shiga jin yace âAbinda zuciyarshi ke soâ me yake nufi? Itace abinda zuciyarshin ke so? Ya Allah, Allah sa ba mafarki take ba, Momma ce ta daka mishi Tsawa âbaka da hankali ne wai musharraf? âDan uwanka kake maganan zaka karya a gabanmu? Kuma kace kaga wadda ze tsaya mai? To ni zan tsaya mai nice uban da zan tsaya mai In ka fasa karyashiâ ta kalli sufyan tare da cewa âme ya hadâaku?â...............
âMomma akan fah mai aikinkun nan ceâ kallon khairi duk en parlorn sukayi har momma, ganin irin kallon da suke mata yasa ta maida kanta kasa tana shirin fara hawaye, ta shiga uku yanzu ta hadâa en uwa kenan? Da ta sani da tun farko bata mareshi ba, wani farin dattijo me cikar kamala ne ya bayyana a parlorn yana cewa âWa ya taâba maza ne?â Ganin fuskan sufyan yasa yace âsubhanallah me ya faru?â.
âUmmulkhairi ya mara tare da murdâe mata hannu bayan bata mishi komai ba ko aka gayamishi en aikin ba mutane bane? Wallahi In baka fita hanyar matar da zan aura ba, kuma yarinyar da nake so da kauna ba zaka yi dana sanin kasancewana dâan uwankaâ baki sake en parlorn ke kallon khairi se kuma su kalli musharraf banda en gidansu da kuma Anty Rabiâah da diddi, a take kananan maganganu ya fara tashi cikin en matan parlorn harda masu zuciyar barin parlorn...........
Anty Rabiâah ce tace âyanzu fisabilillahi musharraf akan wanchar talakan ka daki dâan uwanka? Shi yaro karami ne ko be san me yakeyi ba? Ai In kaga ya mareta to tabbas da abinda ta mishi watakila ma seducing dâinshi tazo yi kaman yadda ta yi muku asiri kai da kafatanin gidanku, Allah ya kamataâ runtse ido musharraf yayi yana ji kaman shi Anty Rabiâah ke zagi wani irin zafi ne ke chakar zuciyarshi inaga ita? Idonshi ya dâaura akanta tana tsaye kanta kasa hawaye na zuba a fuskanta.............
Mamaji ne yace âuhm