Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
baa" da kamar waka yayi shima murmushi na subuce mishi..............
Dangwarar da plate din Zainab tayi a zafafe tace "haba hamma yanzu don mutum ya so ka lefi ne? Wannan wani irin wulakanci ne don Allah ni ce talaucin?" Ya San abinda ta fi tsana kenan talaka da talauci ko shi da ze zama talaka ko kallo baze ishe su ba daga ita har mahaifanta, cikin murmushi idonshi akan waya yace "d'aye manna!!!!!" Wani dariyan haidar ya sa har yana ture system d'in gabanshi, a zafafe Zainab ta fice daga d'akin wulaknci kam ta shashi a kan musharraf ba kad'an ba se tayi zuciya kuma ta sake dawowa shi yasa yake kiranta "d'aye manna" wani lokacin ma har karawa yake da "an d'aye kin manne, an d'aye kin manne Allah yayi mutum marar zuciya anan" amma yau kam ta ci alwashin ko mutuwa zatayi ta rabu da shi har abada wai itace sa'anshi? Amma Allah ya isanta............
Da kuka ta shiga main parlor ba wadda ya tanka ta cikinsu se ma murnan da sukeyi d'akin nuri ta shiga da ya kasance masaukinta ta had'a akwatinta da ta taho dashi ba tare da neman mayafi ba ta fice zuwa motarta tare da fisga ta bar gidan in a very high speed..........
****
Bayan sun idar da sallahn azahar khairi ta zauna ta natsu tana tunanin da wani unguwa zata fara cikin waenda maman hamdeeya ta lissafo mata ta yi zurfi cikin tunani taji Dada na magana............
"Ni kam khairi hankalina be kwanta da aikin nan ba, Ina tsoro wani abun yaje ya sameki a inda baki san kowa ba kin san yanayin jikinki khairi" Shiru khairi tayi na en mintuna itama tana tsoron abinda dada ke tsoro sede kuma ba yadda ta iya hakan ne kad'ai mafita zatayi iya kokarinta ganin bata bar ranta ya 'baci ba wannan alkawari ne................
"Karki damu Dada adu'arki kad'ai nake bukata in shaa Allah ba abinda ze faru" "Toh khairi Allah ya sa" da Ameen ta amsa tana duba wayan dadan don kaiwa maman hamdeeya ta sa musu a chargi tun washegarin zuwansu da ya d'auke basu sake sata chargi ba kasancewar basu da charger...........
******
Tsabar dariya har hawaye haidar yayi shi ko gogan tun murmushin na biyu be sake ba sema fuskan da ya had'e ya san yanzu momma zata kirashi ta ci mai mutunci but hakan shine kad'ai option don duk cikinsu ba wacce ze iya aura kuwa har gwara hafsa ma da bata furta mishi Kalman so ba sede alama amma banda waennan marasa kunyan nan.............
Abincinshi yake ci cikin kwanciyar hankali seda haidar ya gama dariyarnshi tukun yace "baka da kyau mutumina ko kayi wanka" harara musharraf ya watsa mishi cike da haushin dariyan da yake tayin...........
Ai ko be gama cin abincin ba ya ga call d'in momma yana d'agawa tace "na gode musharraf kuma ka sameni yanzu a d'akina" bata jira cewarshi ba ta kashewarta ajiyar zuciya ya sauke tare da ci gaba da cin abuncinshi hankali kwance seda ya koshi tukun ya mike yana kallon haidar yace "zamu je ne ko inyi tafiyata" haidar yace "rufamin asiri kanason momma ta had'a dani? Ai se ta gama da kai zan shigo inyi kaman bana d'akin komai ya faru"..............
Ta'be baki kawai yayi tare da ficewa kaman ka'ida suna baje aparlon ko wacce jira take ya shigo ko kallonsu be yi ba ya nufi sama se su ne ma suka bishi da na mujiya kaman zasu cinye shi, a karshen steps suka had'u da Amrah da sauri ta juya zata gudu ya kuwa yi azamar chapke hannunta tare da murd'ewa baya kara zatayi ya wara mata mayun idanunshin nan nan take ta sa d'ayan hannun ta rufe bakinta...........
Cikin kasa da murya yace "yaushe na fara wasa dake? In aikeki ki aiki wata?" Hawaye na cika idonta tace "kayi hkr Hamma musharraf Wlh momma ce tace na bari ta kai Dan Allah kayi hakuri zafi" rankwashi ya sake mata a kai tare da sakar hannunta ya ci gaba da tafiyanshi kaman ba shi ba, da gudu ta koma d'akinsu tana kuka, ta'be baki yayi tare da knocking d'akin momman yana tuna saura zahra se ya mammaketa na rashin zuwa makaranta yau be manta ba sam............
Seda yaji momma ta amsa tukun ya tura kofan ya shiga da sallama shagwa'be fuska yayi duk da kuwa yadda yake ganin 'bacin rai shimfid'e a fuskanta "me kayiwa er mutane?" Dafe kirji yayi yace "oh ni me tace na mata?".............
Harara ta zabga mishi "Musharraf wai kakanka na zama ne? Ko Ina wasa da kai" karkata kai ya kuma yi kaman yaro yace "ni fah ban mata komai ba In na mata ta fad'a mana" momma tace "kuka fa taje take tayiwa mamanta ban ma san tafiyanta ba kuma daga aikarta kai maka abinci ne".............
D'an zaro ido yayi "oh na tuna momma cewa fah kawai nayi ni de bazan auri wacce take sa'a na ba ko ma ta girme ni" zaro ido momma tayi tana mikewa "Zainab dince sa'anka ko ma ta girme ka?" Baki ya tura ya san in yayi magana ba abinda ze hana momma make keyanshi baya ya ja zuwa jikin kofa ya kuma cewa "na kuma tuna na ce mata naci kaman talau........." da azama ya fita yana murmushi ganin momma tayo kanshi, se da ya fitan tukun itama ta sake murmushi a fili tace "Allah ya shirya min kai"...........
#share
#comment
#vote
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
*An kar'bo daga Aisha tace : madallah da mataye matayen madina, waenda kunya bata hanasu da suyi tambaya game da addininsu kuma su fahimta a cikinshi. Abu dawood ne ya rawaito*
Page➡️3️⃣2️⃣▶️3️⃣3️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Washegari
Da wuri khairi ta tashi, tayi duk wani aikinta ta gama inda ta musu d'umamen tuwon jiya bayan sunyi wanka sun shirya suka zauna karyawa, su nabeel ma yau zasu fara zuwa islamiya sun shirya cikin uniform d'insu milk da brown sunyi kyau sossai, bayan sun gama karyawa khairi ta dubi dada tace "dada in ban dawo da wuri ba ko ya zakuyi da abincin rana?"...............
Murmushi dada tayi tare da cewa "karki damu kekam ba akwai sauran d'umamen nan a kula ba ki ajiyeshi kusa kawai, in su nabeela sun dawo zata d'uma mana ko kin manta ta iya hura wuta? Ni kuma se in dinga fad'a mata abinda zatayi" murmushi khairi tayi tana zura khimar d'inta tace "Toh shikenan mu mun wuce, zan tafi da su nabeela don ganin islamiyar tasu".....................
Adu'ar sa'a dadan tayi musu da fatan dacewa, suka fice se murna su nabeel ke yi, suna fita gidan Maman hamdeeya sukayi wa tsinke inda a get suka gamu da mijinta suka gaisa cikin mutunci ya fice, a shirye suka same ta so ko zama basuyi ba suka fito da kafa sukayi tattaki zuwa islamiyar su nabeel d'in inda a gaban khairi Maman hamdeeya ta cike komai har en littatafan da ba za'a rasa ba ta saya musu dama tun gida ta saya musu jaka me ABCD din nan da 20leaves kowa d'ai d'ai da pencil.............
Bayan an musu interview aka turasu aji biyu don yaran yara ne masu tsantsan ilimin addini don sossai malaman suka yaba da background d'insu, Asabar da lahadi zasu dinga zuwa daga 7 zuwa 12, yayinda sauran ranakun makaranta kuma 2 zuwa 5. Cikin kwanciyar hankali khairi tayiwa Maman hamdeeya sallama inda ta tari adaidaita ta shige tana ce mishi "Arabian estate"..................
Tafiyar minti goma shabiyar ya isar dasu unguwan, unguwa ne me kyau don yayiwa khairi kyau duk ginin iri d'aya ne se roof dinne suka banbanta layi d'aya red yayinda d'ayan layin ya kasance blue shiru wurin kaman anyi ruwa an d'auke ba kowa, "d'ari da hamsin" me napep din yace da kyar ta samu ya kar'bi d'ari tana mamakin tsadar kud'in napep na gombe..............
Gashi bata iya hawa machine ba ta san da ya fi sauki amma tunda akayi wani gomna na taraba, ya hana machine a cikin jalingo shekaru dayawa bata kara hawa machine ba. She's so curios ta rasa ta Ina zata fara, seda ta shafe kusan mintuna 20 a tsaye kan ta yi shahada ta nufi house no 1, knocking tayi ta jima tsaye kan wata ta zo ta bud'e mata sanye da riga daban zani daban hannunta rike da mopper kallon sama da kasa tayiwa khairi kan ta ce "lafiya" ba tare da ta amsa gaisuwan da khairin tayi matan ba.................
A sanyaye khairi tace "dama aikatau nake nema Dan Allah ko shara da wanke wanke ne a taimaka min" harara matar ta zabga mata duk da itama er aikince amma hali irin na d'an Adam se cewa tayi "bamu bukata akai gaba" tare da rufe kofan da karfi, ajiyar zuciya khairi ta sauke kan ta wuce gida na biyu nan ma wata buduruwace ta bud'e mata amma daga ganin ta er gayu ce itama a yatsine ta amsawa khairi da basa bukata tare da rufe kofan...............
A haka khairi ta dinga bi gida gida har kusan azahar amma bata samu Ko kallon arziki ba, ga kishirwa tana ji, tsayuwarta a kofan wani gida yayi daidai da kiran sallahn da aka kwad'a daga Chan bayan estate d'in a hankali tayi knocking wani matashin saurayi ne ya bud'e mata kyakyawa sanye da shorts da vest kau da Kai khairi tayi kan ta gaishe shi, yadda yake kallonta har ya so ya razana ta a shakiyance yace bayan ta gama gaya mishi bukatanta.................
"Baby a yadda kike da kyaun nan? Ki zo kawai na kilar dake yarinya kiga irin kud'in da zaki dinga chaka a wurin manyan garin nan" yana wani kakkashe ido ya karasa maganan, da sauri khairi ta ja baya tana cewa "se anjima" tare da fara tafiya sauri sauri tana waiwayen baya ajiyar zuciya ta sauke tare da zama akan dakalin wani gida.................
Se da ta huta sossai tukun ta mike ta kwankwasa kofan gidan, wata matashiyar mata ce sanye da khimar har kasa murmushi shimfid'e a fuskanta khairi tayi saurin cewa "Ina yini?" Matar ta amsa da "lafiya ya gida?" Khairi tace "lafiya, don Allah aiki nake nema ko da baku da mai muku shara ko wanke wanke ko kuma girki ki taimaka don Allah"...............
Matsa mata matan tayi tare da cewa "bismillah" shiga tayi a d'arare ta samu kasan carpet ta zauna matar ta karasa ciki na mintuna kan ta fito da tire madaidaici a hannunta ta ajiye gaban khairin tana sakar mata murmushi tace "bismillah ci abinci kiyi sallah se muyi magana" d'an shiru khairi tayi tana tunani seda matar tace "ni musulma ce er uwarki wallahi bazan cuce ki ba" tukun khairi ta fara ci....................
Bata wani ci sossai ba ta ajiye matar ta nuna mata bayi dake parlorn taje tayi alwala a parlon tayi sallah tana idarwa matar tace "baiwar Allah kiyi hakuri kinji? Na san kina bukatar aikin nan hakan yasa bazan iya ce miki babu kai tsaye ba, ni ni kad'aice se mijina ni nake komai nawa bana bukatar me aiki kiyi hakuri ga wannan ki hau machine" ta bata five hundred a ladabce khairi ta kar'ba tana yabon kirkin matar har ranta taji daadi ba wadda yayi mata irin wannan karamcin, kin kar'ban kud'in tayi da kyar matar ta sata ta kar'ba kan ta fice....................
Haka tayi ta bi gida gida amma bata samu ba wulakanci kuwa ba irin wadda bata gani ba har ta yardar wa kanta matar Chan ne kawai me karamci a gabad'aya estate d'in, se yamma likis sannan khairi ta shige gidan karshe shi kam irin me fence d'in nan ne tana tura karamin get d'in kare ya biyota a 360 ta fito se kuma tayi wawancin barin kofan a bud'e kare kam ya fito dama ta wuce wasu biyu a gefen bolan gidan a take suka rufa mata baya................
Khairi tayi gudun da bata ta'ba yin irinshi ba a rayuwanta bata dena gudu ba har seda taga ta fita daga get d'in estate din tukun ta tsaya haki a lokaci d'aya ta fashe da kuka, ita ba gudun bane ya sata kuka se wasu matasa dake zazzaune saman mota a kofar gidan matan nan me mutunci su uku suka fara fashewa da dariya kan d'aya daga cikinsu dake danna waya ya d'ago duk da be fashe da dariya ba amma tana juyowa don kallon karnukan suka had'a ido inda ya sake wani shu'umin murmushi da ya fi kona ranta akan dariyan da sauran suke harda rike ciki..................
Seda tayi kukanta ta koshi tukun ta fara tafiya don ganin magrib ya gabato, harara ta bankawa securities din dake gadin gate din kan ta wuce, se kace su suka kar zomon😅 bata wani jima ba ta samu napep ta hau ta wuce haki kam har lokacin bata dena ba, ga kishi ga ko sallan la'asar bata yi ba...................
*******
Zaune ta ke a bakin gadon d'akin tana kallon wata kyakyawar mata da zasuyi sa'anni chocolate color ce daga ganinta er gayu ce kaman momman fatar ta kad'ai In ka kalla ka san kud'i sun zauna, less d'in jikinta kawai abun kallo ne bare gwalagawaln da suka fi komai d'auke hankali akanta, "ban san yadda zanyi da musharraf ba hajiya rukayyah rashin auren shi na mugun damu na".................
Wacce aka kira da hajiya rukayyah tace "hajiya Fatima ban ga ta yadda rashin auren yaron nan ze d'aga miki hankali ba, tunda ba neman mata yakeyi ba hasali ma Ko kallo mace bata ishe shi ba ko kin manta aure lokaci ne? Idan lokacin yin na biyun yayi ba se kin mishi magana ba, sannan idan kika mishi na dolen ma kina da tabbacin xe riqe? Baze rike ba sbd be so, wacce yake son ma kinga abinda ya faru".................
Cikin nazari momma tace "na san In har na mishi auren ze riqe amma har yanzu ban samu macen da ta kwanta min da shi ba amma Ina ci gaba da dubawa In har na samu dole in mishi don sam hankali na be kwantawa da ganinshi hakan wlh" ajiyar zuciya hajiya rukayyah ta sauke tukun tace "Toh Allah ya za'ba mana abinda ya fi alkhairi" momma tace "Ameen"................
Hirarrakinsu suka ci gaba dayi na kawaye har suka gangaro kan auren da me aikin su momma zatayi inda take fad'a mata tana neman wata ma bata san ko zata samu nan kusa ba. Suna cikin hiran aka kira sallahn la'asar suka mike suka gabatar kan momma ta fara shirin tafiya dama tun 12 ta zo, har wurin mota hajiya rukayyah ta rakata inda sukayi sallama driver ya ja mota suka fice Ina ta aikin mamakin yawan securities na gidan..................
*****
Ana kiran magrib tana sallama a kofan gidan da gudu nabeel ya zo ya rungumeta cikin muryarshi ta yaranta yace "Adda hato a dilli a acci amin nabeela wuli ha jungo tun nane o d'o woka"(Adda Ina kika tafi kika barmu gashi nabeela ta kone tun d'azu take ta kuka)................
zaro ido khairi tayi tare da kama hannunshi cikin sauri suka karasa ciki Ai kuwa kuka ta samu nabeela nayi rike da hannunta dada na mata fifita...................
Karasawa gabanta tayi ta rike hannunta hawaye na cika idonta tace "garin yaya nabeela?" Dada tace "wai fa cewa nayi ta hura wuta ta d'aura mana d'umamen nan ban san yadda akayi ba naji suna musu da nabeel akan yadda ake sa itace bayan wutan ya ruru kan nayi magana naji ihun nabeelan nan ma ya sa'be don Maman hamdeeya ta sa mata kamu a wurin"...............
Juyawa khairi tayi tana kallon nabeel tace "kona er uwarka kayi?" Zaro ido yayi yana girgiza kai wani hawayen na zuba mishi don haka suke in d'aya na kuka to fa dole d'ayan ma ze yi kuka "A'a Adda kawai na sa hannu Ina kokarin gyara mata itacen se kawai tayi saurin fisgewa shine bata sani ba ya d'alli hannunta d'ayan" had'e rai khairi tayi tace "me ya kai ka bakin murhun tun farko, ko yari ma jaulero mivi?"(me ya kai ka kitchen din nace).................
Cikin muryan tausayi yace "wad'u munyal Adda mi metata nastugo"(kiyi hakuri Adda bazan kara shiga ba) khairi tace "good" tana mikewa tace "Dada ha mi jula mi yaramo chemist"( bari inyi sallah In kaita chemists) da Toh Dada ta amsa. Seda sukayi sallah tukun khairi ta kama hannun nabeelan suka fice inda suka bar dada da nabeel.............
Magani aka shafamata a wurin suka kuma bata na sha don ta konu ba laifi, suna hanyar dawowa khairi ta tsaya ta saya musu taliya leda d'aya suna da d'an kayan miya se ta tafasa musu, suna shiga kuwa himar kawai ta cire ta nufi kitchen in less than 40mins ta gama musu jollof na taliya seda sukayi sallahn isha tukun suka ci anan dada ke tambayarta ya aikinfa an samu? Da a'a kawai khairi ta amsa sam bata fad'a mata komai akan tafiyanta ba.....................
Da kyar ta samu ta taimakawa su nabeel da wajibul manzeel d'insu (assignment) tsabar gajiya da bacci suna ganawa, tayi alwala ta shiga ta kwanta, sede me!!! tana rufe ido fuskanshi ya fad'o mata yana wannan shu'umin murmushin da sauri ta bud'e ido tana ambaton sunan Allah, lokaci d'aya ta ajiye a ranta don haushin da ya bata ne yasa fuskanshi ke dawo mata amma tana mamakin irin kyaun da Allah ya zuba mishi juye juye tayi tayi da kyar ta samu baccin ya d'auketa.................
#share
#vote
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️3️⃣4️⃣▶️3️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Yau kwana biyu kenan khairi na fita tana aikin neman aikatau amma bata samu ba wulakanci kam ba wadda bata gani ba amma da yake ta sawa zuciyarta neman aikin ya zama wajibi a kanta hakan be dameta ba, babban damuwanta ma kayan abincinsu da suke barazanar karewa don be wuce ya musu kwana biyu ba.................
Tare da su nabeel suke fita ta ajiyesu islamiyya ta wuce kasancewar basu shiga boko ba ta roka su dinga