Advertisements
Chapter 8 Reading IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

IGIYAR RAYUWA Lokacin da Komai Ya Rushe by Fateemah Muhammad Gurin

Author :  Fateemah Muhammad Gurin Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 38

21K to 24K   out of 113.1K words

kaman yayi tsuntsuwa ya ganshi gombe..........

***

Ita kam momma tunda sukayi haka da Musharraf ta ajiye wayan a parlorn ta haura sama, wanka tayi ta fito da alwala tare da gabatar da walaha, tana idarwa ta shafa mai tare da shiryawa cikin wata dakkakkiyar lace black and red tare da feshe jikinta da turarukanta masu sanyin kamshi..............

Saukowa tayi hankalinta gabad'aya se ya koma ga Musharraf ta sanshi sarai In har tayi fushi da shi toh be da natsuwa sam, seda ta shiga wanka tukun ta tuna da wayan da ta bari a parlor ta san yayi ta kira, tana shirin d'aga wayan ta duba kenan se mai aikinsu hanne ta shigo da sallama...........

Zama momma tayi tana amsa sallaman har kasa hanne ta du'ka ta gaida momman, momma tace "hanne me yasa yanzu baki son zuwa da wuri yanzu past 9 fah duk wanke wanken safe na tare kin san girkin safen ma kanki yake Ina yi ne kawai amma In Musharraf ya sani kema kin san sauran"..............

Hanne kanta a kasa tace "hajiya kiyi hakuri kwanan nan duk shirye shiryen buki na akeyi yau ne ma ake kawo lefe" cikin mamaki momma tace "shine ba sanarwa hanne? Yanzu yaushe ne d'aurin auren?" Hanne tace "nan da sati biyu kuma a kaltungo zamu zauna".........

Kai momma ta gyad'a tare da yi mata adu'an zaman lafiya, hanne ta mike ta wuce tana amsawa a zuciyarta, bayan wucewanta ne momma ta shiga tunanin inda zasu samu wata mai aiki me amana da gaskiya irin hanne ko ma fiye da ita............

"Yaaa salaam" ta furta tana me kara kallon fuskan wayanta 20 miss calls na Musharraf shi da baya kiran mutum fiye da sau biyu!!! Danna kiranshi tayi amma a kashe tayi ta nemanshi bata samu ba Haka ta zauna jugum cikin tunanin wani hali yake, ita ba da gaske take mishi ba ai ko maza sun kare ta gama zama da mutum irin Mahmoud amma da gaske ta yafe mishi duk laifin da yayi mata...........

******

A yau suke da nufin barin taraba state jakukkunan kayansu guda uku suka fitar sulaimi da khairi se kuka sukeyi haka dada da ummi 'maman sulaimi' ma zaman shekaru dayawa rana d'aya ace za'a rabu da ciwo kuma zaman amana sukayi...........

Haka suna ji suna gani suka rabu baba ne ya kira musu napep shata har roadblock inda ake hawa motocin tafiya, ba su kara minti biyu ba suka wuce, sienna suka samu se suka kama back seat gabad'aya wato guda uku, khairi, dada da Abul suka zauna a sit, Abul ya d'auki nabeel inda Khairi ta d'auki nabeela................

Awanni kusan 7 ya kaisu gombe daga cikin jalingo sbd rashin hanya sam hanyar ba kyau, tunda suka hau motan drivern yake saka wa'azi na malamai daban daban akan marayu, cin hakkinsu da hukuncin masu cin kud'i da gadonsu, sossai jama'ar motan suka natsu suka ji har suka isa.................

Suna sauka tasha Khairi ta tsayar da drivern inda ta bashi labarinsu In brief, sannan ta kara da "muna so ne ka taimake mu, mu samu gida karami daidai na talaka mara tsada mu saya" girgiza kai kawai drivern keyi yana mamakin halin rayuwa seda ta kai aya tukun ya sauke ajiyar zuciya yace "kar ki damu zan taimakeku nima ina dillalancin gidaje akwai wani gida da zan sayar wa wani dama se mu je ku gani".......................

Godiya sossai suka mishi ya d'auke su a motanshi har tudun wadan fantami chan ciki suka shiga zuwa wani karamin gida me d'akuna biyu d'aya a chan ciki se d'aya a zaure gidan. gidan jan kasa ne irin ginin gomben nan filin tsakar gidan d'an karami ne sossai da karamin bayi, amma duk an shimfid'e da siminti se kitchen na langa langa.................

Sunyi ciniki inda ya ce su kawo dubu d'ari nan ma ya rage musu sossai don sossai suka bashi tausayi, haka Dada ta cire kud'in ta mika mishi ya kirga tare da komawa mota ya d'auko musu takkaddun gidan ya damka musu Abul da khairi suka saka hannu, suka ma drivern godiya ya wuce...............

Gidan ba komai se wearing na nepa hakan ya sa Dada ta damkawa Abul 15 thousand inda khairi ta rubuta mishi abinda ze sayo musu na kwanciya da anfanin gida, fita yayi ya tafi..................

*******
Bayan yayi ta kiran momma bata d'aga ba se kawai yayi jifa da wayan cikin takaici da haushin kanshi, rayuwanshi gabad'aya na da ya shiga dawo mishi daki daki, wani irin kuka ne ya zo mishi amma yana ta kokarin mayarwa, kukan ne ya kwace mishi tuna irin ba'kar wahalan da momma ta sha a kanshi ba irin sana'an da batayi ba don ganin ta ceceshi amma se da mahaifinshi ya tabbatar ya tura shi prison tare da azaba me tsanani...............

Sossai yayi kukan tukun yaji zuciyarshi ya d'an yi sanyi a duk lokacin da ya tuna rayuwanshi na baya se yayi irin wannan kukan, mikewa yayi ya fad'a wanka se da ya share akallah 40mins a bayin tukun ya fito d'aure da sea green towel a kwankwanso da wani fari a kanshi yana tsane gashin kan nashi, a gaban dressing mirror ya yada zango tare da jan kujeran ya zauna...............

Hand dryer ya d'auko ya busar da gashinshi tare da shafa masu mayukansa masu tsada, yana gamawa da kai ya dawo jiki inda ya shafa man sama sama tare da feshe fatan jikinshi da mahaukatan turarukanshi, yana ganawa ya nufi wardrobe d'inshi ya zaro wani three quarter blue da sleeveless shirt black d'aukan kwalin cigarette d'inshi yayi da liter ya karasa inda ya hurgar da wayan shi ya d'auka tare da kunnawa..................

A tsanake ya gangara stairs d'in gidan nashi zuwa kitchen dake kasa ta kofan baya ya fita zuwa karamin garden d'inshi dake gidan a chan ya samu wuri ya zauna kan grass carpet tare da kunna tabanshi ya fara zuka, kallon time yayi almost 12 danna kiran momman yayi luckily kuwa ya samu ringing biyu ta d'aga..............

"Am soo sorry momma" ya furta cikin sanyi da shagwa'ba murmushi tayi me sanyi da har yaji tace "apology accepted" ya kara cewa "plz momma ki janye maganganunki na d'azu plzzzzzz" tace "na ki, I thought kana office oya concentrate in ur work" dip ta kashe wayan ta barshi da waya a kunne murmushi yayi tare da saukewa ya san wasa take mishi tun farko daga tune d'inta kuwa se yanzu yaji natsuwa ta sauko mishi, ci gaba da shan tabanshi yayi................

*****

Yau ne gobe ne, yau ne gobe ne tun suna sa ran ganin Abul har suka cire hankalinsu ya tashi sossai gashi su nabeel sun fara kukan yunwa, har akayi isha Abul be shigo ba mikewa khairi tayi ta fara safa da marwa, ganin takwas yayi yasa ta fara hawaye innalillahi wainna ilaihi rajiun take ta maimaitawa a zuciyanta kallon Dada dake share hawaye ba tare da tace komai ba tayi tare da cewa "Dada bari In dubowa su nabeel ko awara ne a wajen nan in zo"...................

Dada tace cikin tsoro "A'a khairi mu jira dawowan Abulkhairi d'in de" khairi ta share hawayen idonta tace "ba nisa zanyi ba, In har ban samu abu anan kusa ba zan dawo" hawayen idonta Dada ta goge tana gyad'a kai a hankali tace "Dan Allah ki dawo In baki samu ba" Kai khairi ta gyad'a tare da sa kai ta fice, bayan ta kar'bi 500 wurin dadan, bata kuwa yi nisa ba taga mai awara nan ta tsaya ta sayi na 200, ta karasa wani shago dake gefe ta sayi pure water bag d'aya sbd kama ruwa ga sallolin kansu ma duk basu sauke ba sbd ba guga a cikin rijiyar dake manne da toilet dinsun................

Sannan ko akwai gugan ba butar da zasuyi alwalan dashi, bayan ta gama sayan abinda zata saya ne ta fara tambayar mutanen wurin ko sunga wani yaro me kama da ita, kowa se yace mata a'a wani ne daga karshe ta samu yace mata ya ganshi ya tsare machine ya hau, godiya ta mishi tare da komowa gida a inda ta barsu nan ta samesu, awaran ta bud'ewa su nabeel a take suka fara ci hannu baka hannu kwarya................

Ita kam bata bi ta kan awaran ba ta d'auki ruwa tayi alwala tare da bud'e jakansu ta fiddo wani zaninta ta shimfid'a tare da tada sallah, dada ma alwalar tayi da taimakon nabeel ta tsaya kusa da khairin tare da tada nata sallahn, bayan khairi ta idar lokacin su nabeel sun gama ci tare da bajewa kan varendar tsakar gidan har bacci ya fara d'aukansu Dada na zaune gefe tana azkar adu'anta d'aya Allah ya dawo mata da d'a gida lafiya.................

D'akinsu ta nufa tare da shimfid'e bargo mara nauyi a kasa ta d'auko nabeel da nabeela ta kwantar da su a Kai ta fito ta janyo kofan sbd sauro dama bata bar kofan a bud'e ba tun zuwansu, wurin Dada ta nufa ta zauna tare da d'auko wani kullin awaran da pure water tace "Dada bismillah da nyamdu en nyama"( ga abinci mu ci)..................

Kai Dada ta girgiza tare da cewa "bazan iya ba khairi, ko wani hali d'ana ke ciki? Nima nayi kuskuren barinshi fita shi kad'ai a wannan gari da be san kowa ba, oh wani irin IGIYAR RAYUWA ne wannan? Daga wannan se wannan? Yaushe ne zanga fari a rayuwana? Iya tsakankanin zama na da umaru? Ya Allah na tuba in wani laifin na aikata a gareka ka yafemin ya Allah, ka kular min da d'ana ya Allah na tabbatar yana inda be bukatar taimakon kowa se naka ya Allah ka taimakeshi........"..............

Kuka sossai Dada ta fashe dashi khairi ma na tayata wayan Abbansu dake hannunta ne ya fara kara d'agawa tayi ganin baba ne suka gaisa inda ya tambayesu ko sun samu gida? Cikin rawar murya ta amsa mishi, a tsorace yace "lafiya?" "Abulkhairi majji(ya 'bata) baba" ta karasa da kuka "innalillahi wainna ilaihi rajiun" baba ya dinga nanatawa "ta yaya? Me ya faru? Ya akayi Kuka rabu?" Kit wayan ya mutu ba tare da ta ba baban amsa ba........................

Dada kuma bata da numbern baban sulaimi, haka sukayi zaman kurma kurma har 12 ganin sauro na shirin cinyesu ne yasa Dada ta cewa khairi "kamani zuwa d'aki" kama ta tayi har kan shimfid'ar da tayi musu suka kwanta, sun jima suna juye juye kan bacci yayi awon gaba da su.........






#vote
#share
#comment


'Yar mutan Adamawa



🎗🎗🎗🎗🎗






                  IGIYAR RAYUWA😭






                                            🎗🎗🎗🎗🎗

Story and written by: fateemah Muhammad Gurin

Wattpad:- Gureenjo

             'Yar mutan Adamawa

Page➡️2️⃣4️⃣▶️2️⃣5️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗

Three days later

Sossai suka susuce damuwa yayi musu tsananin yawa a cikin kwana ukun nan, har gwara ace mutuwa Abul yayi da irin wannan 'batan shiru shiru sun yi zaman jira har sun gaji sun yi kuka sossai suna kuma kai wa Allah kukansu, a kwana na biyu da 'batanshi khairi ta samu ta lalla'ba Dada inda da kyar ta barta ta tafi police station tayi musu bayani amma se suka nemi raina mata wayau bayan kud'in da ta basu................

A zuciye ta dawo gida tana takaicin banzan hali irin na wasu daga cikin forces na nigeria, a kwana ukun da sukayin nan suna rayuwa ne a matukar takure ba abinda suka saya na anfanin gida kullum sede ta fita ta saya musu abinci shima ba wani na kirki ba, inda sukayi sa'a sun sami makwabciya me matukar mutunci da karamci maman hamdeeya, ta shigo musu sau biyu ta kuma turo musu abinci sau uku ganin yanayin rayuwansu..............

Duk da ba sanin su tayi ba, amma halin rayuwansu yana bata tausayi duk shiganta sau biyun nan samunsu cikin wani hali take, nabeel da nabeela duk sun zama wani iri kaman ba su ba masu wasa da dariya amma sun koma shiru shiru...........

**
Ta bangaren Musharraf kuwa ya ci gaba da rayuwanshi yadda ya saba na kad'aici da shan taba da ya zama mishi aboki kuma kawa da ya ji yana shiga damuwa in ya tuna rayuwanshi na baya se ya zauna ya d'irki na d'irka In ya gaji kuma se ya mike yakai kukanshi ga Allah..........

****
Yau ma kaman kullum zaman shirunsu suke ko taburma ba su da se kayansu da suke shimfid'awa su zauna ko shara gidan be ta'ba gani ba sbd ba tsintsiya, guga da sukaji ana sayarwa a unguwan suka saya se wani bokitin da ta aro musu wurin maman hamdeeya da shi suke wanka suyi alwala da guga...............

Ajiyar zuciya khairi ta sauke tare da kallon Dada tace "dada zaman da mukeyin nan ba shine mafita ba, kud'in da muke kashewan nan tafiya suke ba wadda ke shigowa In har kud'in nan suka kare a haka Toh ba karamin tashin hankali zamu shiga ba, adu'a zamu ci gaba da yiwa d'an uwa, in shaa Allahu baze fad'o kasa banza ba"....................

Ajiyar zuciya Dada ta sauke kan ta fara magana "na san hakan khairi kin rigani furtawa ne kawai ni ce ya kamata in karfafa muku gwiwa a matsayi na na mahaifiya kuma babba amma na sawa kaina damuwa wadda ya shafi har ku, ni uwa ce na fi jin zafin 'batan Abulkhairi akan rasuwar mahaifinku, ban san wani hali yake ciki ba, ban san wani rayuwa ze fad'a ba, yana raye ko mace Allah shine kawai masani" hawaye ta share kan ta ci gaba...............

"Ki shiga gidan maman hamdeeya ki roke ta ko Allah ze sa ta raka ki kasuwa ki sayomana abinda ya kamata se kuma muga sauran chanjin ko Ze ishemu Sana'a" da "toh" khairi ta amsa kan ta mike ta shige d'aki ta d'auko hijab d'inta a natse ta fice tana kallon su nabeel da suke kwance gefen Dada abin tausayi, da sallama ta shiga gidan, wata chocolate color mata ce ta amsa mata wacce na tabbatar itace maman hamdeeya sbd d'umbin fara'a..................

Da ta tari khairi dashi cikin tsokana tace "nayi fushi se yau zanga idanunki?" Murmushi khairi tayi tukun tace "afuwan maman hamdeeya ba gashi na shigo ba, Ina er fara?" Ta karasa tana dube dube "yanzu suka fita da dadynta zasu gidan kakanninta, ki karasa parlor mana bari In gama shanyan nan gani nan zuwa" cewar maman hamdeeyan, murmushi khairi ta saki kan ta nufi parlorn maman hamdeeyan..................

Duk da baza a kirasu masu kud'i ba amma kai tsaye za'a iya kiransu masu rufin asiri gidan ciki da parlor se band'akuna biyu d'aya ciki d'aya a waje, se karamin get d'insu na karfe ba kaman su khairi masu kofan buhu ba, bayan ta gama shanyan ta shigo parlorn da sallama, suka gaisa inda khairi tace "maman hamdeeya dama zuwa nayi in roki alfarma dan Allah in da hali Ina so ki rakani kasuwa In sayo mana d'an abun anfani"..................

Murmushi maman hamdeeya tayi kan tace "haba khairi raka kasuwa ne se kin ta had'a ni da Allah? Dama yanzu gama shanyan nan da nayi wanka kawai zanyi in tafi kasuwa hakan ya sa ma na aika hamdeeya gidan kakanninta, ga remote yi kallo kan na watsa ruwa se mu wuce" murmushi kawai khairi tayi kasancewarta ba me yawan magana ba....................

Bayan ta fito ne suka wuce seda suka biya gidansu ta kar'bi kud'i wurin Dada kan suka wuce, sun jima sossai inda suka saya abubuwa masu yawa kusan fiye da rabin kud'in sun sayi kananan katifu uku, buta, bucket, tukwane biyu, karamin turmi, ludayi, plates, spoons, labulaye masu saukin kud'i sossai sbd sauro, kondon kife kwanoni, murhun karfe, karamin taburma, da dai abinda baza a rasa ba.................

Ganin da d'an sauran kud'i yasa ta ware 50k ta ajiye, sauran ta auna musu d'an kwanon shinkafa, masara, wake, borkono, ta sayi maggi da gishiri, daddawa, kuka, ku'bewa busasshe da 'yan d'anyun kayan miya ba masu yawa ba se albasa.............

a wheelbarrow suka zuba duka kayan ya kaisu har bakin hanya suka samu taxi suka wuto gida, godiya sossai sukayiwa maman hamdeeya kan ta wuce, khairi ta cire khimar nata ta hau shirya duk abinda suka saya a inda ya kamata, ta saka labulayen da igiyoyin da ta saya da su, ta sa katifun tare da shimfid'e musu bedsheets da suka zo dashi a kayansu, duk abin kitchen ta shigar..............

Nabeela ta kama ta raka ta gidan maman hamdeeya inda suka samu hamdeeyan ma ta dawo da gudu 'yar yarinyar da bata wuce 3years ba tazo ta rungume khairi d'an shigowan da suka yi da mamanta har ta saba da ita sossai, juya ta khairi tayi a sama tana mata wasa sossai yarinyar ta ringa dariya tana kiran maama, da ita a hannu suka karaso ciki.............

A kitchen suka samu maman hamdeeyan tana tuka tuwo kujeran tsuguno ta jawo ta zauna kusa da ita tana cewa "san da aiki maman hamdeeya" cikin fara'a tace "yauwa ai ke za'ayiwa sannu na san kin aikatu" murmushi kawai khairi tayi tana sauke hamdeeya dake ta tsalle a cinyanta tana mikawa nabeela hannu, wasa suka fara inda khairi ta maida hankalinta kan maman hamdeeya..................

"Maman hamdeeya kina ganin wani sana'a zamuyi a unguwan nan wadda ze kar'bu?" D'an shiru maman hamdeeya tayi tukun tace "Ina ga kuyi na kayan miya, irinsu maggi, borkono, kuka, kubewa, gishiri, busasshen tattasai, daddawa, albasa, attarugu da dai sauransu ku kukulla irin na goma, ashirin da hamsin zan taya ku tallah a unguwan nan samu a san kuna sayarwa sbd su ne ba'a samun masu sayarwa sossai a layin nan"................

Cikin tsantsan farin ciki khairi tace "mun gode sossai maman hamdeeya Allah ya biyaki, mu kam muna sa'an makwabta" su hauwa da mamanta ne suka fad'o mata a take hawaye suka gangara a idonta bata san sadda ta furta "Allah ka saka mana" ba, da mamaki maman hamdeeya ke kallonta a natse cikin damuwa tace "lafiya kuwa khairi?" Share hawayen tayi kan tace..............

"Klau kawai na tuna da rayuwan mu na baya ne" "wannan ko wani irin rayuwa ne da ze saka ki kuka lokaci d'aya haka?" Ajiyar zuciya ta sauke "hmmm zan baki labari amma ba yau ba, a Ina ake sayar da itace?" "Toh shikenan, daga gidan nan ki Kirga gida d'aya, biyu, uku shine na masu sayarwa" Kai khairi ta gyad'a kan ta mike tana kallon nabeela tace................

"Nabeela 'yan dilla"(mu tafi), juya kai nabeelan tayi kan tace "Eyyah useni Adda

8 / 38