Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
zo ta zauna da dadanku ba? Naga ita kad'ai"..............
Abul yayi murmushi yace "ba wani abu baba ai tana zama ita kad'ai" ba tare da baba ya tanka ba suka tsare napep suka shige seda suka tsaya muhammad nya suka sauke su nabeel kan suka wuce..............
****
Cike da kewar gida ya tashi don isowar dare yayi a jiya dukda a gajiye yake sbd tafiyar mota a haka ya shirya cikin 3peaces suit brown color ya zura brown cover tare da d'aura yazole wrist watch brown yayi kyau sossai gashinshi ya sha gyara...........
A gurguje ya feshe jikinshi da mix perfumes d'inshi masu tsananin kamshi, creed, mission ya d'aura da eternity a take d'akin ya bule da fitinannen kamshinshi, bud'e drowern jikin mirror d'inshi yayi kwalayen sigari ne dayawa da Liters har ya sa hannu zai d'auka se ya tuna da nasihohin momma akan cigarettes numfashi me karfi ya sauke yana kokarin fad'a da tunanin nasihohin cikin karfi ya yakice tunanin tare da d'eban kwalaye biyu da liter d'aya ya sa a brief case d'nshi..............
Da sauri ya fice zuwa kasa ya bud'e motanshi kiran Corolla LS ya shige ba wani 'bata lokaci drivern ya ja motan bayan ya kwashi gaisuwa wurin ogan nashi se da ya d'an tsaya wurin gateman suka gaisa tukun suka fice mintuna kalilan ya kaisu CBN kasancewar gidanshi be da wani Nisan kirki da nan.............
Rike da briefcase d'inshi ya shige lift zuwa floor da office d'inshi yake yana tafiya yana amsa gaisuwan wasu daga cikin kananan workers a bankin jikin office d'inshi ya tsaya inda akayi rubutu da gold a jikin wani brown katako mai kyau, tsayawa karanta matsayinshi nayi cike da mamaki "Mr. Abubakar Mahmoud Adam" daga kasa kad'an aka rubuta "Accountant general of the federation" sossai nayi mamakin ganin yana cikin board members na CBN..................
******
Federal high court
Bayan kowa ya gama shigowa da mintuna kalilan Alkali ya sa kai ya shigo a take kowa ya mike don nuna girmamawa a gareshi seda ya zauna tukun kowa ya koma mazaninshi ya zauna harda lawyers da suke sanye cikin irin kayansu na lawyoyi............
Su Khairi suna jere daga gaba gaba duk hankalinta na kan Abbanta tana kallon irin lalacewar da yayi duk ya dishe, ganin idonshi na kallon wani gefe daban yasa ta kai idanunta wurin Hauwa da mamanta ta gani zaune hankalinsu kwance da sauri ta kauda kanta tana ji akayiwa alkali bayanin case d'in da ya tara su anan inda ya nemi Barristers suyi introducing kansu...........
Wani tsamurarren bakin Barr ne ya mike "ya mai girma mai shari'ah sunana Barr mudassir qasim nine lawyern me kara" gyad'a kai Judge din yayi inda barr da su Abul sukayi hiring ya mike "sunana barr Aliyu karofi nine lawyer me kare wadda ake tuhuma".............
Barr mudassir ne ya mike ya fara kwararo bayanai da hujjojinsu inda a take ya bayyana yadda abun ya faru a yadda hauwa ta fad'a a nan bakin kogi yayi mata inda ya nuna shedarsu ta takalminshi da kuma hanky d'inshi. Zufa ne ke ketowa Barr Aliyu, khairi, Abul da Abba har baba da sulaimi, amma basu karaya ba sun mika lamuransu ga Allah................
Barr Aliyu yayi kokari sossai wurin ganin ya kare Abba inda yayi anfani da labarin da Abba ya bashi gabad'aya inda yaje da abubuwan da yayi, an nemi ganin hauwa da ta tashi ta bada labarin abunda ya faru, inda ta mike ta bada labarinsu na karya cikin kuka inda kowa ya tausaya mata ban da waenda suka san karya take, an kira dogarin sarki da Abba ya furta a cikin labarin shi inda yace shi karya Abba ke mishi kwata kwata basu had'u da ko mai kama da shi ba a ranan.............
Barr mudassir ya nemi ganin Abul inda ya tabbatar da fitan Abba a daidai lokacin da hauwa tace amma Abbanshi cewa yayi bari ya je yazo inda ya tabbatarwa da court ko sama zata had'e da kasa baze ta'ba yadda Abbanshi ya aikata irin abu haka ba..............
an tambayeshi yinin ranan gabad'aya yana tare da mahaifinshi inda ya gyad'a kai, Barr mudassir ya sake tambayarshi ya ga wani d'an aike daga gidan sarki girigiza kai yayi, cikin murmushi Barr mudassir ya karasa cike wa court bayani inda yace "ya mai girma mai shari'ah wannan shariah a saukake take kuma a bayyane, mai laifi da lawyern shi basu da wani hujja da ze tabbatar da ba shi ya aikata ba inda muke da manyan shedu akanshi..............
Ya tozarta mace ya wulakantata ya kuma 'bata mata rayuwa na har abada Ina rokon wannan court me albarka tayi gaggawar yanke mishi hukunci bisa laifin da ya aikata cikin gaggawa don ya zama izina ga en baya"...............
Cikin gamsuwa Alkalin ya gyad'a kai tare da rubuce rubuce inda ya tambayi lawyer me kare wadda ake kara ko yana da abun fad'a inda ya nemi alkalin ya d'aga shari'ahn sam alkali ya ki, anan take ya yankewa Abba hukuncin shekara Ashirin da hud'u a gidan yari tare da azaba mai tsanani, be gama rufe baki ba Abba ya yanke jiki ya fad'i a take zuciyarshi ta buga ya bar musu duniyan da abinda ke cikinta, dama be cika lafiyan zuciya ba tun haihuwanshi...............
Da sauri wani ya tashi ya nufi inda Abba ya ke da alamu doctor ne, hannunshi ya kama yana jin pulse d'inshi a d'an tsorace ya sa kanshi kan kirjinshi cikin tsananin mutuwar jiki ya d'ago ya kalli alkalin tare da girgiza mishi kai alamun Abba babu.........
Kaman kiftawar ido khairi ta iso wurin tare da kama hannun mutumin a firgice tace "fad'a min dan girman Allah da darajar iyayenka me ya samu mahaifina? Me ya samu Abbana?" ta karashe da ihu "I'm sorry to say se hakuri ya riga ya kar'bi kiran mahaliccinshi sede fatan Allah ya yafe mishi" a take court din ya d'auki kabbara inda khairi ta sulale ta zauna dabas kan mazaunanta....................
😭😭😭
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story & Written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Page➡️1️⃣5️⃣▶️1️⃣6️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
"Abba aaa'aa Abba kar kayi mana haka, Abba ka tausayamana innalillahi wainna ilaihi rajiun wayyyooo, wai Allah am ku taimaka ku taimakemu kuce karya kuke ko ze tashi na san be mutu ba, Wlh be mutu ba" cikin matsanancin kuka khairi ke fidda duk abinda yazo bakinta tana jijjiga mahaifinta amma inaa ba alamun tashi a tare da shi...............
Dayawa daga cikin yan court d'in sun tausaya musu ba kad'an ba don Abul ma da yake namiji kuka yake kaman ranshi ze fita, hauwa da mamanta kuwa tuni zufa ya keto musu a lokaci d'aya cikinsu ya d'uri ruwa basu kawo haka ba sam a ransu, a take hauwa ta fashe da kuka tana jin har cikin kashinta itace ta kasheshi itace ajalinshi, Maman na ganin hauwa ta fara sarewa ta kama hannunta suka fice daga court d'in............
Da kyar alkalin ya samu ya nitsar da kanshi don mutum ya mutu farat d'aya a gabanka ba karamin abu bane, mikewa yayi ya cire riganshi na alkali da hulan ya mikawa guard d'inshi a hankali ya tako zuwa kan gawan bayan yayi wayan da baifi da mintuna 3 ba, ya duka yana mishi adu'a...........
"Ku yi hakuri ku rungumi kaddara, haba baiwar Allah sai kace ba musulma ba? Kin kuwa san kukan da kikeyin nan kara mishi azaba ze yi? Haramun ne yiwa mamaci irin kukan da kikeyin nan ba'a hana hawaye ba amma banda kururuwa ki ta maimaita innalillahi wainna ilaihi rajiun zakiji sauki, Allah yaji kanshi ya gafarta mishi".........
Hawaye na zuba take girgizawa alkalin kai alamun bazai gane ba, sam baze gane ba, a daidai lokacin chairman na makabarta da mutanenshi suka iso don su alkalin ya kira kan ya zauna bawa su khairi baki, baba ne ya shige gaba akayi duk wani cike cike court ta mika gawan Abba ga family d'inshi aka d'aukeshi a motar gawa don zuwa gida a mishi wanka............
Cikin tausayawa Alkalin da wasu manya da suke nan suka shiga motocinsu wasu ma napep suka bi yayin da wasu suka hau machine me kafa biyu suka bi bayansu inda khairi da sulaimi suke motar alkalin Abul da Abba suna motar gawa............
A kofar gidansu motocin sukayi parking sede cikin tsananin mamaki suka tsaya kallon kofar gidansu garkame da katon sarka inda aka makala padlock daga karshe, da sauri Baba ya ce "mu karasa gidana a mishi wankan a chan" d'aukan Abba akayi zuwa cikin gida anan su khairi suka ga kullin kayayyakin sawansu gabad'ayansu Dada na zaune geje tana share kwallah...............
Jin mutane na shigowa gidan yasa ta mike tana dafa sandanta take cewa "Maman sulaimi Hamma buba ne ya dawo koh?" Maman sulaimi da ta daskare ganin an shigo da gawa bama ta san dada na magana ba tabbas gawa take gani ga khairi, sulaimi da Abul na ta kuka, ga mijinta nan tsaye Toh waye ya rasu? Ko de malam umaru??........
Ras gabanta ya fad'i inda ta furta "innalillahi wainna ilaihi rajiun" Dada se ta kara rud'ewa dama gashi tana ta fama da fad'uwar gaba, bata kai ga magana ba taji an fad'a jikinta bata karasa rud'ewa ba seda taji muryan 'yarta cikin kuka tana cewa "Dada am shikenan, shikenan mu kam, Dada.... daada....." kukan da takeyi ya hana maganan fitowa na kirki................
A rud'e Dada tace "menene? Menene ummulkhairi?" "Abba... Abba ya tafi dada sun kashe mana shi sun yi mana ajalinshi.... daa..." had'iye maganar tayi ganin Dada ta yanke jiki ta fad'i ihu ta kurma, Baba da ya d'ibi butoci ya kai wa mutanen waje da taburmai don suyi alwala kan a yiwa Abba wanka ya karaso da sauri yana kallon Maman sulaimi da take a tsorace daidai nan wasu mata suka shigo............
Duk en unguwan ne, ja baya yayi suka kama Dada bayan Abul ya sa mata ruwa ta de sauke ajiyar zuciya amma bata bud'e ido ba suka shigar da ita d'akin sulaimi, Gawan Abba kuma suka shigar d'akin baban sulaimin dama d'akuna biyu ne kachal a gidan se toilet da kitchen..............
A nan take akayiwa Abba wanka aka shirya shi cikin rigan kowa wato likkafani aka kira iyalanshi suyi mishi adu'a da kallon karshe, Dada, Abul da khairi suka shigo a tare suka rike mamansu a tsakiya, duk sun samu suna kuka yayinda Dada kukan yaki zuwa mata sam..............
A gabanshi suka durkusa duka inda Dada ta fara zuba mishi adu'o'i bayan ta gama ne kuka mai karfi ya kwace mata inda take cewa "Allah yaji kanka umaru Allah ya gafarta maka, yasa aljannah ce makomarka ya biyaka da gidan aljannah yadda ka taimakeni Allah ya taimakeka, tabbas ni nayi rashi na rasa miji na gari, uba na gari, uwa na gari, aboki na gari............
A lokacin da bani da duka waenchan kai ka maye min gurbinsu ka bani wani rayuwa na daban me cike da soyayya, ina Sonka amma Allah da ya hallice mu yafini sonka, daga yau na maka alkawari zan ci gaba da yi maka adu'a har karshen numfashi na......."
Kuka ne sossai ya sarke ta ja baya tayi tana hawaye, Abul ma ya matso ya yiwa Abban Adu'o'i, khairi ma haka sossai ta zuba mishi tanayi tana kuka, seda aka zo fitar da gawan Abba tukun ta rikirkice musu tana kankame makaran tana wani irin ihu da ya tsorata jama'ar gidan seda kowa yayi hawaye, da kyar aka samu aka 'ban'bareta wasu maza majiya karfi su biyar suka riketa aka samu aka wuce da Abba............
A take aka mika shi gidanshi na gaskiya ba karamin jama'a yayi ba se aka ajiye batun maganan fyad'e aka ringa maimaita ayyukan alherinshi, bayan an dawo ne Abul ya samu baba yace "baba dada tace, Abba ya sha fad'a mata cewa In ya mutu be so ayi zaman makoki daga an kaishi an dawo a watse shikenan".................
Baba ya samu alkali ya fad'a mishi don ya zama kaman shugaba a wurin da kud'i da karfinshi ake komai, sossai jikinshi yayi sanyi jin yadda ake yabon halin alheri irin na malam umaru sanda se yake ga kaman shima yayi contributing wurin kashe shi duk da ya san cewa ajali In tayi kira toh se an amsa, amma kuma da ya d'aga shari'ahn da Abba be ji abinda ze buga mai zuciya ba, tabbas idan da gaske ne malam Umar be aikata abinda ake zargin shi dashi ba, guiltiness ze ci gaba da binshi har karshen rayuwanshi..............
Yana cikin tunanin ne yaji maganan baba bayan ya fad'a mishi ne ya koma wurin zaman shi ya zauna suka ci gaba da amsan gaisuwa, ba jimawa wata mota tayi parking aka fara fidda abinci da ruwa na gora da spoons a takeaway abincin yake so se aka ringa ajiyewa d'aya d'aya a gaban kowa, da mamaki Baba ke kallonsu waen nan kuma daga Ina? Ya kasa ba kanshi amsa har suka gama suka shiga da dayawa cikin gida..............
Ashe alkalin ne ganin yanayinsu na babu yasa ya kira ya bada order akan ayi sharp sharp a kawo tun kawo gawa yaga kokarinsu ma na gamawa cikin kankanin lokaci dukda ya san aikinsu na da sauri, seda Baba Yaga Alkali ya mike ya nufe su bayan sun fito ya gane daga inda abincin ya fito adu'a sossai ya mishi a ranshi dama duk tunanin yadda za'ayi yakeyi.............
Bayan kowa yaci ya sha alkali ya mike ya musu bayani akan mamacin yace be bukatar kowa ya mishi zama, so se akayi mishi adu'a a take aka watse sede duk wadda zeyi gaisuwa ya shiga ciki ya ma iyalanshi ta'aziyya..........
bayan an samu da kyar khairi ta natsu ta dawo kanta ta jima zaune wuri d'aya hannunta dafe da kanta dake tsananin ciwo kaman ze rabe sam bata cikin duniyar mutane tayi nisa sossai cikin tunaninta gabad'aya bata jin daadin komai a cikin jikinta hawaye kuma yaki tsayawa ko ta samu tayi shiru In har ta tuna irin sharrin da ya kashe mata abbanta se ta 'barke da sabon kuka...............
Da kyar sulaimi da wasu mata suka lalla'bata tayi alwala tayi azahar a kan sallayan ta zauna ta bud'e wani sabon babin kuka, bata san iya lokacin da ta d'auka ba ta de ji ana raba abinci ita ma an ajiye mata amma ko kallon takeaway d'in batayi ba, se maimaita, "Ya Allah! ka gafarta mishi. Ya! Allah ka bashi tabbata" takeyi..............
Chan se ta mike da sauri tana cewa "ya subhanallah Nabeel da Nabeela" Dada ma tace "subhanallah na manta kwata kwata dasu" wata aka kira aka ce ta kira Abul a waje Ai kuwa taje ta kirashi yana shigowa, Dada ta fad'a mishi ba'a d'auko su nabeel ba gashi past 3...............
A gurguje ya fice ya tsare napep ya hau se muhammed nya a wajen get ya samesu a raku'be gefe sunyi futu da kura da alamu sunyi wasa sun gaji yunwa duk ya cinye su, suna ganinshi suka mike suka je suka rungume shi nabeelah tace "Hamma Abul me yasa baka zo ka d'auke mu ba?? Tun d'azu muka tashi mun gaji ga yunwa"..............
Hawayen da ya cika mishi ido ne ya gangaro da sauri ya share, nabeel kam ya kalla kuma yafi nabeela wayau se yace "Hamma kuka kakeyi? Fuskan ka duk ya kumbura me ya sameka?" Nabeela bata jira amsan Abul ba tace "Hamma kace zaku je ku taho da Abba shiyasa baku zo makaranta ba, kun dawo dashi?"...............
Da sauri ya tsuguna yana fashewa da kuka tare da rungume su cikin rawan murya yace "Abba ya rasu ya tafi inda ba'a dawowa, ku ringa mishi adu'a kullum kunji?" Be jira amsan su ba ya mike yana share hawayen fuskanshi ya tsare musu napep suka hau se gida duk jikinsu a sanyaye don sun san mutuwa a karatunsu na addini..................
Duk da ba wai sossai suka sani ba amma seda sukayi kuka ganin mutane a kofar gidan baba basu san me yasa aka shiga dasu gidan baba ba amma suna ganin Khairi da dada sukaje suka rungume su suna kuka................
*****
Yana jingine da jikin glass d'in dake mamaye da office d'inshi hannunshi rike da taba yana zuka yayinda idonshi ke kallon kasa, ko yaushe ya shiga cikin irin wannan yanayin rayuwa da abinda ke cikinta yake tunawa lumshe ido yayi a cikin kwakwalwanshi yake jin ihun kukan momman shi da ya kasa d'aukewa a kunnuwanshi tsawon shekaru................
"Baba kayi hakuri ka dena dukanta haka me tayi maka?" A ko yaushe tambayar da yakeyi yiwa mahaifinsh kenan In ya sa mahaifiyarshi a gaba yana jibga tun be san kanshi ba har ya kai yayi girman da baze iya jurewa ba............
"Wallahi ka kara d'aga mata hannu se na rama mata" yana tuna irin kallon mamakin da babanshi ke mishi a sadda ya furta mishi wannan kalaman, a yayinda mahaifinshi be daddara ba a yammacin ranan ya hau dukan mommanshi duk basu ankara ba suka ji saukan abu akan baban nashi inda a take suka kaure da fad'a babanshi na dukanshi yana ramawa................
"Innalillahi wainna ilaihi rajiun Abubakar me zan gani haka? Me kake yi?" Inda tayi maganan cikin kuka da d'aukewar hankali..............
Wai waye Musharraf ne? Wani irin kalubale ya fuskanta a rayuwanshi??
Duk ku biyo 'yar mutan Adamawa ku sha labari☺️☺️
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gureen
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
*my first dedication in this book will goes to kindhearted woman, with a unique name and a very kind full habit- Sawdah-edress, Allah yasa ki fi haka, ya rabaki da sharrin makiya, ya kuma bar zumunci🥰🥰*
Page➡️1️⃣7️⃣▶️1️⃣8️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Bayan kwana uku
Yau Abba ya cika kwana uku cir da rasuwa yayinda family d'inshi suke cikin tsanani da matsin rayuwa, da ba don Allah ya basu makwabci me halin sahabbai ba da basu san inda zasu jefa kansu da rayuwansu ba............
Tunda aka watse a bayan an kai Abba an dawo, baba da kanshi ya dinga d'iban akwatunansu yana kaiwa d'akin sulaimi na Abul ne kawai ya shigar d'akinshi inda ya fitar wa Maman sulaimi da akwatin da