Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
Nan ma girgiza kai dada tayi tace "mahaifinsu muka tuna" inna tace cikin takaici "ji min shashanci yanzu don kun tuna umaru se ku ta mishi kuka? Ba adua ya kamata ku dinga mishi ba? Baku san kukan nan kara mishi nauyi kuke ba aduarku kawai yake bukata? Mtseww ku ci gaba In kun ga dama" ta juya ta fice.
Abul yace "Dada Allah sanya alkahiri na tayaki farin ciki sossai don Abba ba mutumin banza bane mutum ne me sanin darajar d'an Adam, yana da karamci sossai da mutunci duk yadda zan kwatanta miki shi baza ki fahimta ba se kin zauna dashi" Shiru kawai dada tayi, khairi tace "Allah sanya alkahiri" tare da mikewa ta fice, dada tace "Abulkhairi kaman 'yar uwarka bata so auren nan ba" shima ya lura da hakan sede ya ta iya aikin gama ya gama tunda an riga da an d'aura hakan yasa yacewa dada "zata so ne with time in shaa Allah".
Direct motan momma da keyn ke hannunta ta shiga ta ja ta fice daga gidan, yana tsaye yaga wucewarta dama doguwar riga sea green ce jikinta kirar kasar Oman me stones dayawa a hannu da jikin rigan gyalen ne a d'aure a kanta ko warwarewa batayi ba bare ta yafa Allah ya sa ma rigan me kaman bubu ne daga wuya har gwiwan hannunta duk a rufe suke, yanayin driving da yaga takeyi ya tabbatar mishi akwai abunda yake damunta dama jikinshi ya riga ya gama bashi, motanshi ya shiga da yake a jikinshi yake jingine bayanta yabi.
Tana parking a haraban gidan ta bud'e kofa ta fita zuwa part dinsu a kan gado ta fad'a tana lumshe ido hawaye na gangara mata Allah sarki Abbanta, bata ji shigowarshi ba se ji tayi an dafa goshinta tare da sa tattausan hannu aka share mata hawaye kamshin turarenshi ne ya sanar da ita waye tun kan ta bud'e ido a hankali ta bud'e ta zubo mishi idanuntan da suka chanza launi.
Kallo d'aya ya mata ya san ba yanzu ta fara kukan ba cikin damuwa yace "qalbee auren dadan ne bakya so?" Se ta sa mishi kuka da sauri ya zauna da kyau tare da jawota jikinshi ya rungume yana shafa bayanta a hankali ya fara rad'a mata wasu kalamai masu kashe jiki da shiga zuciya cikin hausa da turanci kai har fulatanci inda yayi mata nasiha sossai akan kin auren dadan da takeyi ya nuna mata shine mutuncinta sossai bayananshi suka gamsar da ita tayi lakwas a jikinshi Ai ko batayi niyyan hakura ba dole tayi don waye ita da zata iya fuskewa wannan lallashi.
Basu koma gidan ba suka yini soyewa abinsu se dare suka shirya zuwa dinner kawai, sun yi kyau kuwa sossai kaman ka sacesu ka gudu, suna like da juna suka shiga event center din inda suka tafi da imanin mutane dayawa tunda suka zauna be barta ta tashi ba sema wani tsare gida da ya karayi fuskanshi na nuna tsantsar kishin shi akan matanshi don gani yake kowa kallon young beautiful wife dinshi yakeyi don tayi masifar kyau fiye da amaren.
Bayan kwana uku Abba ya d'auki dada, nabeel, nabeelah, Abul, nasreen da Afreen suka wuce Abuja don ya ce shi ze rikesu bisa amana kaman shi ya haifesu don ya san dada baza ta ta'ba iya muzantar da yaranshi ba so me yasa baze iya rike nata ba, har suka tafi khairi bata nunawa dada ta sauka ba don har yau In ta tuna da wai dada tayi wani aure se taji wani irin kishin Abbansu nasreen ya kamata, bata ta'ba bari sun had'u dashi ba tun bayan auren.
Sati d'aya mekyau suka kara tare da su dada kan suka fara shirin tafiya sunje sun yini a dukku suka gaishesu suka dawo cike da abun arziki don yanzu dadda ta sauka akan kin auren ta riki khairi kaman sauran surukanta, tare suka je gidan nuriyyah aiko khairi ta kara tsorata da ciki don ganin yadda nurin ta koma bata iya cin komai duk abunda ya shiga se ya fita musharraf ma ya tausaya mata, marwan ke sanar dasu Doctor yace In cikin yayi wata hud'u zata dena su dena tada hankalinsu.
Cike da tausayinsu suka dawo sunje gidajen uncles dinshi gabad'aya amma hajiya Aisha mahaifiyar marwan ce kawai ta yi mata tarba ta mutunci amma banda hajiya zulai, haka Anty rabi ma wulakanci kawai ta mata bata damu ba sam ko a kwalan riganta mijinta na zuwa ta nanukeshi suka wuce, sossai su Amrah suka ji haushin tafiyansu don zasuyi kewansu sossai musharraf yayi musu alkawarin zuwa Abuja next hutunsu suka tafi suka barsu da kewa.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo 6763
'Yar mutan Adamawa
Second To The last page
Page➡️9️⃣8️⃣▶️9️⃣9️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Bayan kwana biyu da dawowarsu suka je gidan Abba a parlor suka samu familyn gabad'aya zaune ana hira gidan gabad'aya an sake renovating har furnitures din an chanza kuma Abban ne da kanshi yayi yaki sam su Alhj mudassir suyi, da gudu su nasreen suka zo suka rungume khairi suna murnan ganinta bayan sunyi breaking hug din suka je zasu rungumi little da gudu tayi kan cinyar dada tana tura baki.
Dariya suka saka don sun san fushi tayi da suka fara rungume mommynta, sukayi kanta a cewarsu se sun rungume tan, da gudu ta fara zagaya parlorn suna binta, d'an karamin tsaki musharraf ya saki da su Amrah ne ba abinda ze hanashi make yarinya, khairi tace kasa kasa "sorry mu karasa" karasawa sukayi Abba na musu Sannu da zuwa haka dada ma har kasa suka duka suka gaisheshi ya amsa da fara'a haka dada ma, bayan sun gama gaisuwan ne suka mike suka zauna saman cushions.
hira suka fara khairi de se kallon dada takeyi tana mamaki dada ta dawo wata hajiya tashi d'aya ko leshin jikinta ma abin kallo ne se ta fito a marar shekarunta anan ne ma take ji wai next week zasu tafi Spain akwai abinda ze kai Abban ze tafi da ita a gwada mata aikin ido, sossai khairi ta nuna jin daad'inta tayi ta wa Abba godiya yana dariya yace "me na godiya ummulkhair bayan matata nayiwa" murmushi tayi tana dukar da kai, sallama musharraf ya musu ya fice akan se da dare ze dawo ya d'aukesu, har wurin mota khairi ta raka shi suna 'yar hiransu na masoya.
A d'akin Nasreen ta yada zango inda nan ta samu Afreen suka shiga hira suna tuna abubuwan da aka yi tayi lokacin bukin su marwa, kan ta shiga seda ta leka little a d'akin nabeela ta gansu suna wasa da kayyayakin wasan nabeelan d'akin kawai abin kallo ne an shiryashi gwanin sha'awa.
Bata ga Abul ba seda suka zo cin abinci daga gani da alamu yanzu ya tashi daga bacci "eyeee jin daad'i se yanzu ka tashi?" Murmushi yayi yace "to 'yar uwa me mutum ze yi yanzu bayan baccin ba karatu ba komai gashi Abba ya hanani d'inki" murmushi tayi kan tayi magana Abba yace "Eh ba wani d'inkin da zakayi da raina da lafiya na ga kud'i, zaman rashin karatun ma na this year ne kawai next year zakayi waec da neco In had'aka da 'yan uwanka a Nile" murmushi kawai Abul ke ta bugawa cikin jin daad'i wai yau shine ze je Nile university hmm Allah kenan, se kuma tunanin Abbanshi ya fad'o mishi adu'a kawai ya mishi ya ci gaba da cin abincinshi.
Bayan sun gama cin abinci d'akin dada khairi ta shiga ta fad'a gadonta se bacci dayake fashin sallah take se la'asar lis ta farka ta shiga ta wanko fuskanta da bakinta a bakin gado taga dada zaune bayan fitowanta tana murmushi tace "dada kinyi ta shigowa Ina bacci ko?" Dada tace "Ai ko de wannan baccin naki kaman ba na lafiyannan ba har yanzu yana nan khairi? A gidanki wa ke miki aiki?" Tura baki tayi tace "na dena fa dada, yanzu dinma don baya nan ne amma ai matsalan hamma dayawa yake In yana tare dani" dada tace "hmm to an ji me miji, ba de haka kike sake baki kiyi ta surutun miji da kawaye ba kam?" Bubbuga kafa ta fara "haba haba dada se kace wata sakarya, wannan ma fah don kene" hmming dada tayi inda suke ci gaba da hiransu na tsakanin 'ya da uwa inda har dada ta tambayeta jikinta baya tashi ko, tace tunda suka tashi ranar kamu da dare basu sake tashi ba.
Dada Tace "ranar kamunku?" Khairi ta amsa da Eh inda ta bata labarin duk abinda ya faru yadda taji a bakin su Amrah girgiza kai kawai dada tayi tace "Allah ya kyauta" anan ne ma khairi ta fad'a mata sharrin da aka mata wadda seda tayi hawaye da ta tuna, da farko dada taji tsoro sossai amma da taji sunyi resolving issue din se kawai tayi adu'ar kariya a garesu.
Se bayan isha musharraf yazo ya d'aukesu anan dada ta sa aka ma surkinta special girki suka tafi da shi bayan Abba ya bata kud'i da farko kin kar'ba tayi seda taga ranshi ya 'baci ya nuna mata kaman su nasreen take yanzu a wurinshi da ba don ma tayi aure ba da tare ze had'asu ya zama Abban triplet dariya kowa yayi aka raka su har mota suka tafi.
Ranar tafiyan su dada har airport suka rakasu su nasreen harda shagwa'ba suke mata akan zasuyi missing d'inta se ka rantse itace ta haifesu haka suna ji suna gani suka tafi, dama Khairi tayi niyyan d'aukan su nabeel kan su dawo Abba yace be yarda ba kar a raba mishi kan 'ya'ya dada ba bata goyi bayan hakan ba hakan yasa ta hakura, a airport din duk suka rabu kowa ya kama hanyar gidanshi.
BAYAN WATA SHIDDA
Rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin hukunci na Allah yau da gobe asarar mai rai, wani lokacin ayi farin ciki yayin da wani lokacin akasin hakan, inda wani lokacin ayi fad'a wani lokacin a shirya, haka rayuwa ta ci gaba da gurguzawa su khairi tana karatunta cikin mai da hankali hakan yasa take samun cin nasarar duk wani abinda tasa a gaba a school d'in inda tayi suna a department d'insu ta kasance 5pointer.
Kowa ji da ita yake musamman lecturers d'insu, a 'bangaren musharraf ma Alhamdulillah aikinshi yake cikin yarda da amana zuwa yanzu ko warin taba ma baya son ji bare a kai ga sawa a bakinshi da sunan sha Amma har yanzu d'an bakin da yayi mixing da asalin red lips d'inshi na nan, murjewa da kyau kam ya ninka na da sbd kulawar da yake samu daga qalbeenshi hakan ke sa su fad'a akan 'yan matan dake binshi.
Little na nan tana karatunta yayinda Abba ya sa su nabeel makarantansu class d'insu d'aya inda suka kasance kaman wasu triplet gasu ba laifi Allah ya basu ilimi, Abul de har yanzu ba abinda yakeyi daga bacci se kallo a sabuwar system d'inshi da Abba ya aiko mishi don har yanzu basu dawo ba, kuma yaki fad'a musu ko aikin idon dada anyi nasara ko ba'a yi ba.
Tafe take cikin sauri sbd makara da tayi ta san zuwa yanzu babynta ya dawo be cika rigata dawowa ba itama ta fi so ta ringa rigashin sbd shirya wasu abubuwan kan ya dawo amma yau gashi exams ya d'an Chaza mata kai bata fito da wuri ba har lokaci ya wuce sossai ga go slow da ta gamu da shi a hanya.
A hanzarce tayi horn gateman ya bud'e mata da mamaki take kallon tsakar gidan ganin ba motanshi a parking space time ta kalla tuni ya kamata ace ya tashi daga office da mamaki ta sauka ta rufe motanta ta shige cikin gidan a parlor ta samu little da gudu tazo tayi mata oyoyo rungume ta tayi tana cewa "sannu pretty yau ba karatun yamma ke kad'ai a gidan" murmushi little tayi tace "kin kira malam d'in kinji ya jikinshi mommy?" Khairi tace "wallahi ban samu kiranshi ba kinga bari nayi wanka na ci abinci se na kirashi" little tace "Ohk mommy se kin fito zan baki labarin abunda duk ya faru a school" khairi na murmushi ta haura sama har tayi wanka ta shirya cikin riga armless wadda ko cibinta be kai ba yellow da jeans blue ta sauko musharraf be dawo ba.
Abun ya matukar d'aure mata Kai ta kira kusan sau biyar kan ta gama Shiri wayanshi switch off, zama tayi tana jin hiran little ba tare da tana fahimta ba ko abinci bata yi niyyan ci ba, haka suka zauna har magrib kowa ya mike sukaje sukayi sallah a d'aki ta zauna tayi karatunta har lokacin isha tayi adu'o'inta tare da kiran layin shi ya shiga ba'a d'aga ba, sallah tayi ta idar tare da saukowa ta leka d'akin little taga tana sallah ta dawo parlor ta zauna kenan taji an turo kofa.
Da sauri ta mike ganin shine tace "sannu da dawowa" tare da karasawa tayi hugging d'inshi shima rungumeta yayi se yaga tayi saurin janyewa yace "sorry baki ganni ba, ba kuma ki jini ba wallahi munje wani office dinner ne da ma'aikatanmu a gidan wani friend dinmu and my phone was slipped from my hand ya dena yi kwata kwata, se Ina dawowan nan na biya na sayi wata".
Ba tare da ta yarda ba tace "Ohk" tare da kar'ban brief case d'inshi ta haura sama ta barshi da 'yarshi tana welcoming d'inshi, da ido ya bi bayanta se yaga kamar bata yarda da abinda yace ba haka ya haura de bayan ya had'a little da chocolates da ya saya mata a hanya, a bakin toilet ya ganta tana share hannunta da karamin towel ba tare da ta kalleshi ba tace "ruwa na toilet" a d'an dame yace "wai qalbee me ya faru ne? Look am sorry for not informing yhu shima kuma with reason am sorry plz".
Murmushi kawai ta mishi ya shige bayin ba tare da ya yarda ta aminta dashi ba, yana shiga ta ga wayanshi da ya ajiye a kan dressing mirror yayi haske, haka kawai ta ji tana son gani ta mike taje ta danna fuskan "I'm very sure zuwa yanzu ka isa gida, can I call yhu plz baby? am missing you" jiri ne taji yana neman kada ita ta sauri ta dafa jikin mirror ta zauna tana jin wani tension na building cikin kanta da kirjinta tashin hankali kenan shi yasa ya jima? Dalilin kenan da ta ji yana kamshin turaren da ba nashi ba?.
Kuka ta saka sossai, wani irin bala'e'en kishi ne ke cinta bata ta'ba zaton tana da kishi haka ba se yau tashin hankali mijinta ya fara dare a waje sbd wata? Ta kai five minutes tana kuka kan taji motsin fitowanshi da sauri ta mike ta kwanta akan gado tare da juya ma kofan toilet baya tana ci gaba da hawaye, kallon bayanta yayi na mintuna kan ya sauke ajiyar zuciya ba haka ta saba mishi ba ya kamata tazo ta tare shi ta shafa mishi mai ta taimaka mishi ya sa kaya amma tana kwance.
Shafa mai yayi ya sa kayan baccinshi cotton trouser da riganshi me igiyar d'aurewa kawai daga tsakiya gabad'aya gaban kirjinshi a bud'e yake kara feshe turare yayi.
gadon ya hau tare da juyota a take hankalinshi yayi matukar tashi ganin hawaye na gangara a idonta a rud'e yace "qalbee me ya faru? Me yasa ki kuka?" Se kuwa ta fashe mishi da kuka me sauti rungume ta yayi a kirjinshi yana shafa mata baya har tayi ta koshi idonshi a runtse Allah kad'ai ya san me yake ji, ganin kukan yaki lafawa ne yasa shi d'agota tare da had'e bakinsu special lallashi ya dinga mata har seda ya ga kukan ya d'auke chak dukda kokarin tura shi da take yaki sakinta sam.
Yana saketa ta mike da sauri tayi bayi ta dinga tofar da nyau ranshi ya fara 'baci da wannan sabon d'abi'a nata shine ze yi kissing d'inta ta tofar da nyau? Kwanciya yayi ya rufe ido da nufin fita harkanta tunda haka ta za'ba, yana ji ta dawo ta kwanta a chan karshen gadon haka suka kwanta ta jima sossai tana juye juye shima yana kwance Shiru be tanka mata ba dukda ba bacci ya yi ba, yana ji ta mike da fita da alamu duba little taje yi, Ai ko hakan ne seda ta tattabatar ta kwanta kan ta hauro ta chanza zuwa kayan bacci ta koma ta kwanta Shiru.
Har misalin shabiyu da rabi ba wadda ya iya bacci a cikinsu don basu saba irin wannan fad'an ba tunda suka shirya basu ta'ba 'batawa sun kwana ba'a jikin juna ba, ganin kaman yayi bacci yasa ta mike ta zauna ta had'a kai da gwiwa tana me ci gaba da kukanta sossai yayi kokarin share ta amma sam ya kasa hakan yasa shima mikewa yayi ya zauna cikin taushin murya yace "ummulkhair" d'ago kai tayi dukda baya kallon fuskanta sbd kashe wuta da tayi tun kan ta kwanta amma ya tabbatar kuka take yi.
"Gayamin plz me na miki da zafi haka? Ko kina tunanin zan fara miki karya ne a zamantakewar mu abunda ban ta'ba miki ba?" Shiru tayi tana shesheka kaman baza tayi magana ba kuma se tace "yhu never lied to me but I didn't believe what you said earlier, kana smelling different perfume ba naka ba, naji hakan ne a sanda nayi hugging d'inki shigowarka and".
Se ta mike ta je gaban mirror ta d'uko sabuwar wayan nan ko samun ya duba da kyau be yi ba, ta kunna hasken har yanzu sakon na nan ta kawo mishi ta kunna mishi fuskan wayan kar'ba yayi ya karanta da sauri ya mike tsugunne akan gadon tare da sa hannu ya kunna hasken d'akin yadda ze kalleta da kyau yace "I swear to God ban san wacece wannan ba, kin san ba yadda zanyi in miki rantsuwa akan karya ko to wallahi