Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
nufi sama jin zarah na cewa "kun kusa paapi?" Ya sata tsayawa da tafiyar da takeyi bata san me aka fad'a a d'ayan bangaren ba taga zarah ta kashe waya tana murna, Miemie tace "little!!" Zarah ta juyo ba tare da ta jira taji me miemie zatace ba tace "Anty Miemie paapi nah ya kusa isowa" ras gaban miemie ya fad'i murmushi kawai tayiwa zarah ta nufi sama tana cewa "dole musha nitsogin"
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
đđđđđ
IGIYAR RAYUWAđ
đđđđđ
Story & written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
âYar mutan Adamawa
PageâĄď¸1ď¸âŁ1ď¸âŁâśď¸1ď¸âŁ2ď¸âŁ
đđđđđđđđđ
Sun shigo gombe after 5 dukda a kishingidâe yake idonshi a lumshe amma chanjin iska da nishadâin da yake ji a cikin ranshi ya tabbatar mishi da sun shigo mahaifanshi tabbas a ko yaushe gida daban ne, a hankali ya budâe idonshi tare da mikewa ya zauna da kyau yana kallon window sassanyan murmushi ne ya bayyana a fuskanshi har dimple dâinshi na gefen dama ya bayyana wadda ya sani kusa yar da biro na ashe yana dariya!! Murmushin ba karamin kyau yayi mishi ba sede kash ba kasafai yakeyi ba, yana ta kallon cikin garinsu har suka isa GRA layin shiru ba kaman cikin gari da suka baro ba, horn da driver dâinshi ya danna ne yasa shi maido da idanunshi kan ash ion get dâinsu da sauri mai gadinsu ya fito yana ganin motan maigidansu ne yayi saurin komawa ya tura get din zuwa karshe inda motarsu ta kutsa zuwa katuwar haraban gidan dake dâauke da flowers masu kyau daga jikin gini inda sukayi har baya wurin boysquaters inda nan ne masu aikinsu suke wasu harda iyalai kuma shi ke ciyar dasu, Chan karshe garden ne mai kyau wadda ruwa ke bulbula yana kuma gudana, qasan haraban shimfidâe yake da interlocks masu kyau daga gefe madaidaicin part ne me parlor da dâaki dâaya se kitchen da store wadda ya kasance nashi yayinda parking lot ke facing part dâinshi cikinshi motoci ne guda uku na different companies, main house dâin kuma duplex ne da ya gaji da hadâuwa steps uku daga kasa kan ka haura kan varender din dake shimfidâe da white tiles zuwa babban parlor dake a kasa wadda komanshi ke In Ash and milk se kitchen, store da toilets guda biyu se dâaki guda dâaya. Motansu na tsayuwa tsakar gidan Zarah ta fito da gudu tayi kanshi be gama fita ba ta rungume shi karamin murmushi yayi kan ya duka yasa hannu ya dâaga ta yana juyata se dariya takeyi ajiyeta yayi yasa hannu a sit din bayan ya dâauko brief case dinshi dâayan hannun kuma ya riqe hannun âyar shi cikin tsiririyar muryanta tace âI missed you paapiâ yace âmissed yhu too my littleâ nan ta fara zuba mishi surutu kananan murmushi kawai yake sakewa ba tare da ya amsa mata ba har suka shiga cikin parlorn ya so ya fara zuwa part dinshi yayi wanka amma baze iya ba se yaga momma dâinshi da ta kasance farin cikin rayuwanshi da sallama ya shiga parlorn inda momma dake zaune cikin shiga na alfarma ta mike fuskanta dâauke da murmushi tana welcoming nashi ajiye briefcase dinshi yayi tare da karasawa ya rungume ta tana murmushi ta ture shi tana cewa âkayya Musharraf se kace a india?â Murmushi yayi sossai tukun ya langwaâbar da kanshi gefe cikin shagwaâba da yayi mugun karâbanshi yace âeww momma nayi missing naku ne fahâ tace âmuma munyi missing dinka sossai sonâ seda ta zauna tukun shima ya zauna a kasa tare da dâaura kanshi akan kafanta rigimar zarah ne ya ankarar dasu wanzuwar ta awurin duk ido suka maida kanta ta turo baki gaba tana bubbuga kafa a kasa cikin shagwaâba tace âPaapi don kaga granny shine ka manta dani koo??â Yace âohh sorry sweetheart zo abunkiâ karasawa tayi ta zauna daga kasa tare da kwanciya akan kafanshi, da yake ya riga ya dâaga kanshi daga kafan momma hakan yasa shi kallonta fuskanta fal murmushi a hankali yace âmun same ku lafiya momma?â Tace âlafiya klau Musharraf ya wurin aikin naku?â Yace âAlhamdulillah momma, Ina yaran nan?â Momma tace ânuri bata dawo daga wajen aiki ba yayinda Amrah ta raka miemie school tana da 4-6â dâan âbata fuska yayi tukun yace âbut duka motocin gidan nan suna waje why?â Momma tace âhmmm sun je sun karasar da man duka rankatakab yadda ba yadda zaâayi a fita dashi filling station Ina ta son in kira azo a sa tun safe se in shaâafaâ âbata fuska yayi sossai tukun yace âhaba momma ya zaâayi a bar motocin gida duka ba mai fisabilillahi in wani urgent abu ya taso fa?â Murmushi tayi kawai sanin dâan nata yanzu wannan abu ya jawa duk âyan matatan ta fadâa sam ta manta ne sbd hidiman dawowanshi amma da ko ita bazata so yazo ya same su haka ba, dâan shiru yayi don da gaske ranshi ya âbaci, kallon fuskan zarah yayi se yaga tayi bacci dâaga ta yayi ya sata a kafadâanshi tare da mikewa momma tace âkawota kaje dining abincinka na jirankaâ yace âno momma lemme freshen up, zan tafi da ita In zan fito masjid se in tasota ta shigoâ Kai momma ta gyadâa ya dâauki briefcase dâinshi ya fice, a tsakiyar gidan ya gamu da nuri murmushi shimfidâe a fuskanta tace âya Musharraf san da zuwa, ya hanya?â Ba tare da ya saki fuska ba yace âyauwa Alhamdulillahâ ya wuce ta yayi gaba abunshi da kallo ta bishi har ya shige part dâinshi baki ta taâbe, ta san yafi sake mata akan su Miemie amma bata san wa ya taâbo shi ba daga dawowarshi ya fara cin ran nan nashi har ga Allah tausayi yake bata har ranta sbd ta san duk wani obstacles da ya shiga a rayuwanshi duk da wayonta ba har chan ba lokacin, da tunanin ta fadâa parlor bakinta dâauke da sallama. nayi mamakin ganinta me duhun fata a cikinsu, chocolate color ce ba kaman su da suke farare tas tas ba...
**
Abul be jima da kwanciya ba bacci ya kwashe shi a lokacin baban sulaimi ya shigo inda yace âIna Abulkhairi yazo ya kaiwa babanku abinci a chargi office don na tambaya aka ce kaiwa ake yiâ ajiyar zuciya khairi ta sauke kenan tun safe be ci komai ba? Tana jin Dada na amsawa baban sulaimin da âya shige dâaki ba da jimawa ba, ummulkhairi tashi ki dubo shiâ a sanyaye ummulkhairi ta tashi ta nufi dâakin nashi da sallama ta shiga ganin yana bacci yasa ta fitowa ta dubi baba tace âbaba bacci yakeyi, mi andi o somi Un, ha mi wara mi yarana mo (na san duk a gajiye yake bari na zo na kai mishi)â kai Baban sulaimi ya gyadâa ya san dole ya gaji shi da be saba da irin wahalan nan ba duk da su ba masu hali bane amma babansu be bari suyi aikin wahala sam ko yayane gwara dâan dâinkin da yakeyi ma shima don Sanaâa ne, duban khairi yayi ya san tana son zuwa taga mahaifinta ne baze hana ta ba se yace âtoh bari na turo Ummu sulaimi ta raka kiâ Kai khairi ta gyadâa shi kuma ya fice yana tausaya musu ya san In case ya fara daga wurin sarki toh se inda karfinshi ya kare ganin an kwatowa me hakki hakkinshi yana aduâar gaskiya tayi halinta kar bayin Allahn nan su wahala akan abunda yake da tabbacin ba malam Umar bane ya aikata tuna abunda umman sulaimi ta fadâa mishi yayi shigowanshi Wai an hana su nabeel wasa a waje yau da maganganu se abin ya bashi mamaki ya kuma tokare mishi kirji a yadda malam Umar yake me kyautatawa mutane da makwabta shine don Allah ya jarabceshi âyan unguwa zasu takurawa iyalanshi? Lallai ka guji duniya da mutanen cikinta da tunanin nan ya karasa cikin gidanshi inda ya samu sulaimi zaune ta zabga tagumi yanzu dawowanta makaranta ko uniform bata cire ba take jin abunda ke faruwa dama tana so In ta cire uniform se ta shiga taji me ya hana su Abul zuwa makaranta yau dayake makarantansu dâaya kuma yau bata jira su ba dama tare suke tafiya amma yau babanta yace ta wuce kawai sbd be da kudâin napep da ze bata kuma be so ya dâaurawa malam Umar dâawainiya bayan ga na yaranshi shiyasa tun da sassafe ta fice, seda babanta ya mata magana sau biyu kan ta dawo daga duniyan tunanin da ta fadâa yace âtashi sulaimi je ki raka khairi chargi office ta kaiwa Abbanku abinciâ Da Toh ta amsa tana mikewa a sadâadâe ta karasa dâaki ta shirya cikin doguwar rigan atampha tana cikin sa hijab taji sallaman khairi wani hawaye ne ya cika idonta tana jin tausayin kawartata da sauri ta share ta fito ta samesu da ummanta tana kara mata nasiha da kyar take iya kakalo murmushi tana ganin sulaimi ta mike tace âbaba, umma se mun dawoâ jerawa sukayi da sulaimi suka fice, da kyar sulaimi ta kakaro magana inda tayi mata jaje murmushi kawai khairi tayi ta san in tace zatayi maganan ba abunda ze hanata sake kuka akan hanya, tafiya suka dinga yi kurma kurma har suka iso jalingo devision da kyar aka barsu suka shiga inda suka tsaya daga baki bakin kofa wani dâan sanda ya tambayesu âwa kuka zo gani?â Tace âMalam Umar sandaâ âau kice me babban laifi kukazo gani akwai ershi a nan?â Kai khairi ta gyadâa kanta na tsananin sarawa mutumin ze kara magana sulaimi tace âkayi hakuri Dan Allah abinci muka kawo mishi muna bashi kuma zamu wuce bata jin daadi neâ Kallon khairi yayi tukun ya taâbe baki ya nufi cikin cell yana cewa âtoh a de kiyaye don ance kama tudinu tudan abinda kayi shi zaâayi maka eheâ basu tanka shi ba se chan ya fito da Abban ganin fuskanshi kawai yasa khairi fashewa da kuka sulaimi kuwa hawaye ya silalo mata, fuskanshi a kumbure tsaban dukan da akayi mishi duk don ya amsa laifin da ba shi ya aikata ba, da kyar ya samu courage dâin yi mata murmushi yace âyi shiru mamana karki damu jarabawata ce tazo a haka in shaa Allahu kuma zan cinyeta tare da karfafawanku gareni In ku kun kasa dâauka ni da nake ciki tsundum kuma ya zanyi? Uhmâ da kyar ya samu khairi tayi shiru tare da mika mishi abincin ze dâauka kenan dâayan police dâin da tunda suka shigo be yi magana ba yace âdakata!! Budâe ki ci tukun ki bashiâ budâewa tayi ta dâiba a spoon tare da kaiwa bakinta da kyar ta ci ta hadâiye sbd kuna da ranta keyi Wai yau Abbanta ne anan wurin cikin wannan hali, bayan tayi spoon biyu se ta rufe ta mika mishi karâba yyi har sun juya yace âummulâ se ta juyo yace âki sha maganin da na karâbo miki daga kauyen Abbare n nanâ Kai ta gyadâa mishi kan suka juya suka fice har suka iso gida ummulkhairi na hawaye kukanta ya Karu ne sadda suka shigo layin unguwansu tun daga bakin hanya ake zundâensu har suka iso depon su idi shaidâan nan kam zaginsu sukayi tayi ba tare da wani shayi ba dukda ummulkhairi bata ga idi shedâan a wurin ba amma tayi mamakin wai yau âyaranshi ne ke zaginta su da suke girmamata kaman itace ogan nasu ba idi ba, âkhaih Allah ya isa mna hauwa Allah kayi mana sakayyaâ a fili ta furta hakan suna shiga cikin gidansu basu karasa shigewa ba ma khairi kam ta zube a wurin da sauri Abul da ke zaune ya taso yana ambaton âsubhanallah kamata sulaimi mu karasa da itaâ.............
#vote
#share
#comment
âYar mutan Adamawa
đđđđđ
         IGIYAR RAYUWAđ
                       đđđđđ
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
       'Yar mutan Adamawa
PageâĄď¸1ď¸âŁ3ď¸âŁâśď¸1ď¸âŁ4ď¸âŁ
đđđđđđđđ
Cikin yanayin shi na Izza da kuzari ya shimfid'e zarah a gadonshi ya nufi wardrobe d'inshi yana cire kayan jikinshi seda ya saura daga shi se boxers tukun ya janyo light green towel ya yafa a kafad'arshi ya shige bayinshi dake manne da d'akin a gurguje yayi wanka ya fito sbd magrib daya gabato cikin light brown jallabiya a hankali ya haura gadon yana Dan bubbuga fuskan zarah kaman me tada wata babba, bud'e lumsassun idanunta tayi ta zubawa mahaifin nata murmushi ta sakar mishi tana mika, yana kallonta ya furta "Alhamdulillahillazi ahyana ba'ada ma amatana......" seda tayi murmushi tukun ta amsa da "wa ilaihin nushur"...................
"Oya wakeup magrib yayi" mikewa tayi yana rike da hannunta suka fito seda ya ga shiganta main house tukun ya fice masallaci da ba wani nisa ne dashi ba.......
Duk da yunwan da yake ji haka ya zauna se da akayi isha tukun ya fito dayake hakan ya kasance al'adarshi, ya d'an tsaya wurin mai gadi da driver d'insu ya tabbatar ba wani abinda ya faru kuma ba'a musu wani cin fuska duk da ya san momma baza ta ta'ba bari ba amma yana da kyau ya tabbatar d'in.......
Da sallama ya tura kofan parlorn, Amrah da Miemie na tsaye hannunsu cikin na juna da alamu fad'a sukeyi suna d'aura ido a kanshi se suka washe baki suka maida hannun kaman irin rike juna kawai sukayi tare da zamewa kasa suka zauna suka natsu idonshi dake kansu ya kawar ya maida kan nuri dake kunshe dariya harara ya sakar mata se ta gimtse baki Momma kam se dariyanta takeyi karasowa yayi ya zauna gefenta yana shafa cikinshi ta gane Sarai yunwa yake ji amma miskilancinshi baxe barshi ya fad'a ba...........
Kallonsu Amrah tayi tace "Auta ku tashi muje muyi dinner ya Musharraf na jin yunwa" d'an baki ya turo jin Momma tace mishi yaya, ba tare da ta kalleshi ba ta nufi dining tana murmushi suma mikewa sukayi suka isa Amrah tayi serving d'insu tana hararan miemie "Ina Little?" Kallon sama Mimie tayi tare da kwala kiran "Zaaarahhh" bata ajiye numfashi ba taji an daka mata tsawa "kee wani irin iskanci ne wannan?? Ko mu sa'anninki ne zaki zauna kina ma mutane ihu a kai come on kije d'akinta ki kirata".............
Sumui sumui ta tashi ta nufi stairs Amrah se dariya take a ranta don itama In ta sake dariyan ya fita fili za ta samu rabonta, tsab ta gama serving d'insu a lokacin zarah da Miemie sun fito zuwa dining d'in kowa yayi bismillah ya fara ci.........
Seda ya tabbatar kowa ya gama ci tukun ya fara aikawa su Miemie mugun kallo suna ganin haka suka san sunyi laifi duk suka dukar da kai yana nuna su ya fara magana "duk kanku Kun sanni kun kuma san abinda zan iya da wadda bazan iya ba, Wlh Wlh yarinya ta kara fita da mota ta karar da mai bata biya filling station ta sha mai ba tazo ta ajiye mota Wlh ranta in yayi dubu ze baci"...........
Be jira yaji amsan su ba ya mike yana cewa "good night Momma am exhausted" momma tace "Allah tashe mu lafiya" Zarah ta shagwa'be fuska tace "am sleeping with yhu paapi" girgiza kai yayi "no In kin bini baza ki barni na huta ba I know yhu" a sanyaye Tace "sleep tight paapi" yace "night sweetheart" su Amrah suka had'a baki wurin cewa "good night ya Musharraf" hannu kawai ya d'aga musu yana ficewa duk suka sauke ajiyar zuciya suka kalli juna tare da fashewa da dariya lokaci d'aya..........
*************
Da kyar Abul ya samu jikin 'yar uwannashi ya lafa abun tausayi don seda ya zubda hawaye, Sulaimi ce ta share hawayen idonta tana duban Abul tace "Abba yace a fara mata anfani da maganin da ya kar'bo a Abbare last week" Dada tace "Ina yace magungunan karfi garesu? Baza su matsa mata ba In ta fara anfani da?" ..............
Abul yace "Ina ga gwara muyi anfani da shine kawai yadda Abba ya fad'a su d'an yi nisa da ita kar wani abin ya faru wadda ba za'a ji daadinshi ba tunda duk kwanakinnan ranta a 'bace yake" ba musu Dada ta dogara sanda ta shige d'aki............
Mintuna kad'an ta fito da wasu bakaken leda a hannunta tayi kiran Abul akan yazo ya kar'ba, kar'ba yayi ya bud'e dama Abba ya mishi bayanin magungunan tun da ya dawo, akwai na hayaki, na sha, na shafawa se wani kaman turare a lokacin duk suka mata banda na sha d'in se sauke ajiyar zuciya take tsabar ciwon kan da ke damunta..............
Two days later
A daddafe waennan family sukayi two days cikin zullumi da tsananin kewan jigonsu me tsananin kaunarsu kaman yadda suke kaunarshi, Kullum khairi da Abul ke kai mishi abinci safe, rana dare kuma kullum In sunje se sunyi kukan lalacewar da yayi, jikin Khairi be kara tashi ba don kullum tana kokarin anfani da magungunanta........
A yau za'a shiga court tunda abun ya faru basu ta'ba had'uwa da hauwa ko mahaifiyarta ba, ko son ganin sarki don su wanke mahaifinsu basayi, dukda sun san shi ya tsayawa su hauwa dukda akan mulkinshi irin na adalci yake amma kuma gaskiya ta shige mishi duhu suna de adu'ar Allah yasa ya fahimta ko ba jima ko ba dad'e.................
Kaman yadda suka saba tashi a ranan makaranta haka suka tashi Abul yayi shara yayinda khairi tayi musu breakfast tayiwa su nabeel wanka Abul ya shiryasu suma sukayi wanka amma se suka shirya cikin kayan gida sabanin uniform sunyi akan Dada zata tsaya gida sbd yanayinta ba saba fita tayi ba In sun ajiye su nabeel se su wuce federal high court................
Suna gama breakfast suka ji sallaman Baban sulaimi da sulaimi bayanshi ta shirya cikin kayan gida itama don baza ta iya barin kawarta ita kad'ai ba, fitowa sukayi inda Baba yace "ummanku baza ta