Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
yace "lastly ban hana ki In manya na magana kina sa baki ba? And the fact of calling that crazy girl cutie ewwww" se ya dakata da maganan yana kwa'be fuska irin disgusting din nan, kan yayi ci gaba little dake hawaye sbd har yanzu be sakar mata kunne ba tace "but she's cute can't yhu........" "shut up!!!!" Ya daka mata tsawa kukan gaske ta fashe dashi hakan ya sa ya sake mata kunne tare da fasa fad'an abinda yayi niyyan fad'a................
tare da sulalewa yayi kwanciyarshi, jikin momma taje ta shige tana kuka kasa kasa don ta san in ta kuskara yaji kukanta dukan da be mata ba toh se yayi mata shi, a wurin tayi bacci momma ta ajiye abubuwan hannunta tana mikewa da ita a hannu zuwa kan two seater ta kwantar da ita, ta dawo ta d'auki traynta tayi kitchen................
Washegari🌚🌚
Da wuri khairi ta tashi yadda ta saba ta kimtsa komai na gidan tayi musu breakfast bata samu sayawa su khairi lunch box ba haka zasuyi hakuri zuwa albashinta, wanka tayi musu kan ta sawa nabeel vest da boxers ta turashi gidan Maman hamdeeya aiko mintuna kad'an ya dawo da kayansu a leda kar'ba tayi ta bud'e tare da zarowa ta fara sa musu.....................
Red plain trouser da milk riga, shine na nabeel wandon be kai kasa ba, se nabeela red trosern da milk riga se wani karamin hijab iya kirjinta sunyi kyau sossai jakansu na islamiyya ta d'auko ta cire littafin islamiyyan ta sa musu sabbi 20leaves guda uku uku da sabon pencil d'insu abinci suka ci kan suka sallami Dada khairi ta raka su har school da yake gaba kad'an da islamiyyansu sede ta baya................
Seda ta dawo kan suka karya ta tattara kwanuka ta wanke tazo ta zauna suka hau hiran rayuwa da dada, a lokaci d'aya tunanin d'an uwanta ya fad'o mata da kyar ta hana kanta kuka tayi mishi adu'a kan ta fad'a tunanin musharraf da muryanshi me sanyi da daad'i a zuciyarta tace "Allah sarki na mishi sanadiyar shiga ruwa na barshi da wahala" tuna irin atishawar da yayi tayi zuwanta se ta kuma jin ba d'aad'i ta tabbatar daren jiya beyi bacci ba...............
Tsaki tayi a fili tana bugun goshinta tace "meke damu na ne?" Wani tsakin ta kuma ja, Dada tace "lafiyanki kuwa khairyya?" Murmushi tayi tana cewa "klau Dada ba wani abu" ci gaba da hiransu sukayi bayan tayi iya kokarinta wurin cire tunanin musharraf a ranta.....................
#comment
#vote
#share
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️4️⃣0️⃣▶️4️⃣1️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
Friday
Haka kawai khairi ta tsinci kanta cikin farin ciki da ta rasa dalili har take alaqanta hakan da aikin da zata fara ne wadda ta tabbatar da yardar Allah shine rufin asirinsu, da wuri ta tashi tayi musu breakfast tana sauke breakfast ta d'aura jollof don ya zama na rana tunda bata nan, tayiwa su nabeel wanka ta shirya su cikin uniform d'insu seda ta sa musu breakfast d'insu kan ta shiga wanka tana fitowa jollof d'inta yayi ta kwashe musu a karamin cooler d'insu ta kai d'aki ta ajiye................
Cikin A shape gown material ta shirya tana sa kayan tana tunanin d'an uwa don shi ya d'inka mata, sossai gown din ya mata kyau, ponytail style tayi parking gashinta da ta manta when last ya ga kitso black silky hijab da iya karshi cinya ta saka ta zura black robber silifas d'inta, wani paper bag ta samu ta zuba d'an abinda zata iya nema In taje Chan, fiskanta fayau ba komai ko d'igon baki d'aya baza ka gani ba haka jikinta ma................
Cikin sauri ganin bakwai da rabi tayiwa dada sallama, dada tace "Allah ya tsare ya kiyaye, ya kuma bada sa'a ki ci gaba da kula dan Allah, ki kuma rike mutuncinki kiji tsoron Allah a duk inda kike, sannan ki gujewa 'bacin ranki don kin san sakamako" a sanyaye khairi tace "In shaa Allah" ta kama hannun kannenta suka fice, napep ta tara musu don bata son suyi latti seda suka biya ta ajiye su kan ya wuce da ita GRA.................
Yana ajiyeta ta biyashi kud'in shi ta nufi gate din gidan gabanta na fad'uwa a kai a kai, knocking tayi malam d'ahe ya bud'e a mutunce suka gaisa inda yake tambayarta wurin wa ta zo ta sanar dashi itace sabuwar me aikin gidan, maraba yayi mata tare da bata hanya ta wuce, taku takeyi cikin salon tafiyanta da kaman tana tausayin kasa ta nufi main entrance na gidan a bakin kofa ta tsaya tare da knocking..................
Wata bakar buduruwa ta gani da ta san zata girme mata da shekaru masu yawa duk da baza ta haife ta ba, murmushi buduruwar ta sake mata Tace "sannu" da sauri khairi tace "Ina kwana" nuri tace "lafiya wurin momma kika zo?" Khairi tace "a'a ni ce sabuwar me aikin gidan" khairi ta d'auka zata ga nuri ta chanza fuska se taga ta fad'ad'a fara'arta Tace "Ohk sannu da zuwa bismillah"...............
Shiga khairi tayi cikin jin daad'i don bata ga alamun wulakanci a gida ba kwata kwata, a kasa ta samu wuri ta zauna tana gaida miemie da Maryam dake parlorn cikin fara'a miemie ta amsa ta yayinda ko kallo bata ishi maryam ba, nuri na kallon miemie tace "je ki kira mata momma" Miemie ta mike ta haura stairs ba jimawa se gata da momma, cikin fara'a tayiwa khairi sannu da zuwa khairi ta gaida ta, ta amsa tana tambayarta gida da mamanta, amsawa khairi tayi da "suna Lafiya Alhamdulillah" momma tana nuna khairi tace "ga fa sabuwar me aikinmu ummulkhairi sunanta"...................
Miemie ta d'aga mata hannu da murmushi itama ta mayar mata da murmushi, nuri tace "momma ina kika samu me aiki kyakyawa er fulani haka?" Momma tace "hajiya rukayya ce ta turomin ita wlh" Miemie tace "and she looks cool and innocent" momma na murmushi tace "ai itace little ke ta baku labari" wara ido miemie tayi tace "dama itace cutie? Ashe da gaskiyan little masha Allah"................
Maryam dake kallonsu da haushi da kuma mamaki ta ja tsaki, tare da mikewa ta haye sama da kallo suka bita kan miemie ta ta'be baki, momma tace "tashi ummu muje In nuna miki d'akin da zaki dinga ajiye abubuwanki" mikewa khairi tayi ta bi momma d'akin kasa dake daura da kitchen ta nuna mata ita kuma ta shige, tiles ne shimfid'e a kasan d'akin se babban katifa guda d'aya dake manne jikin inda window yake daga Chan gefe sallaya ce shimfid'e, se fanka dake ta aikin juyawa shikenan se toilet...............
Jakan hannunta ta ajiye ta fito, kanta a kasa take tambayar momma meza'a d'aura musu na breakfast ta tabbatar ba wadda ya karya a gidan, momma tace "nuriyyah nuna mata kitchen da store, ki de nuna mata abinda ya kamata" mikewa nuri tayi anan khairi ta san sunanta, bin bayanta tayi zuwa kitchen a tsanake nuriyyah ta nuna mata duk abinda ke kitchen d'in da store ta kuma nuna mata yadda zata kunna gas da electric cooker se hot plate..................
Nuri tace "ki d'aura doya da kwai se ki dafa mana black tea da kayan kamshi" Kai khairi ta gyad'a nuri ta fita, store khairi ta nufa ta d'auko doya ta fara ferewa se kuma ta tuna da bata san yawan yadda zatayi ba kar tayi yayi kad'an ko kuma yayi yawa, fita tayi maryam kad'ai ta gani zaune a parlorn gabanta ta karasa tace "Anty Dan Allah ya yawan doyan da zan dafan?"...................
Tafi mintuna biyu a tsaye kan maryam ta d'ago ta watsa mata harara a tsawace tace "kinga na miki kama da sa'arki ko ta uwarki da zaki zo ki tsaya min a ka?" Baya khairi ta matsa tare da sake murmushi dukda taji zafin sako dada da tayi amma ko a fuskanta be nuna ba ta juya ta nufi komawa kitchen din kenan taji muryan momma tana cewa "lafiya khairi?"..............
Dukda taji abinda maryam din ta ce mata hakan kuma be mata daadi ba amma se ta fuske da tambayarta me take so, khairi tace "dama hajiya yawan doyan da zan dafa nake tambaya" momma tace "mu biyar ne a gida ki dafa daidai yadda kika san ze ishi mutane biyar" Da "toh" khairi ta amsa tare da shigewa kitchen din tana mamakin maryam daga tambaya, ta'be baki tayi ta fara aikinta sharp sharp ta dafa doya ta baza shi tire ta d'aura mai tare da kad'a kwai, a d'ayan hot plate ta d'aura wani tukunyan ta zuba kayan kamshi da lipton bayan man yayi zafi ta fara jefa doyan a kwai tana sawa cikin mai..................
Ba 'bata lokaci ta gama ta zuba a wani babban cooler da ta gani cikin kitchen carbonate ta d'auka ta fito ganin dining table daga chan gefen parlorn an rufe wurin da labule shara shara milk me ado sossai, kan ka haura se ka taka steps akallah hudu, bayan ta ajiye ta koma kitchen ta d'auko flask da ta zuba black tea din ta kuma kaiwa kan dining, ta kara komawa ta d'ibo plates da spoons da fork se cups ta kuma kaiwa a kan dining din ta ga roban yaji da kuma na sugar se kawai ta gyara musu zama ta kuma komawa kitchen din..................
Abubuwan da tayi anfani dashi ta wanke tana gamawa ta bud'e kofan da ta gani a kitchen din bayan na store se taga waje ne wurin akwai dakali da manyan bafs a gefe se pampo a chan gefe kasan wurin kaman ana wanke wanke idan suna dayawa, kujeran tsuguno da ta gani a gefe taja ta zauna tana tunanin rayuwanta................
Sossai take jin kad'aici tana missing su sulaimi tana missing d'an uwanta tana missing Abbanta, hawaye ne ya fara gangaro mata 'Allah ka saka mana ya Allah kayi mana sakayya' a fili ta furta hakan tana fashewa da kuka ta jima batayi kukan Abbanta ba amma abun kullum yana zuciyarta yanzu da take zaune bata komai ne suke fad'o mata..............
Daga kanta taji ance "lafiya khairi kike zaune ke kad'ai anan?" Da dabara ta goge hawayenta tare da sake murmushi tana juyowa tace "Lafiya klau momma, me za'a d'aura na rana" momma tace "shinkafa za'a yi da miya se cowslow amma yanzu ki had'awa musharraf fruit salad hope kin iya?" Khairi tace "Eh na iya" momma ta kuma cewa "kaman baki d'ibi doyan ba" a ladabce kaman de yadda take magana da momman tun farko tace "na riga na karya a gida bana jin yunwa".............
Momma tace "Ohk" har ta nufi komawa se kuma tace "akwai fruits a fridge karamin nan a ciki zaki samu su cabbage, sannan a deep freezer akwai kayan miya a gyare suke a wanke blending kawai zakiyi, and naman kaza shine a blue leda, naman rago a orange leda, se naman sa a green, kifi d'anye kuma a black, suma de a wanke suke zubawa kawai zakiyi in zakiyi anfani dashi leda d'aya muke anfani da ko wani meal, se farare na tuwo su kuma wankakkun shuwaka, yakuwa, se zogale ne a cikinsu".................
Khairi tace "toh hajiya" momma tace "ki ce min momma, ban san dalili ba but duk cikin masu aikina kinfi ko wacce shiga min rai jinki nake kaman su Amrah" murmushi kawai khairi tayi itama tana jin son momman, mikewa tayi taje ta d'auko tray da roba da kuma knife ta dibo kankana, ayaba, lemu, mangoro se gwanda, a verender din ta dawo ta zauna ta fara cire kwallon kankanan tana yankawa kanana kanana.................
Bayan ta gama da kankana ta yanka sauran duk a kai kanana bayan ta gama ta duba kitchen din a fridge ta samu peak milk na gwangwani, a wurin spices ta samu foster clark da kuma wani gwangwanin sugar bayan na dining d'auka tayi ta koma ta zuzzuba wadda ze isa ta juya sossai ta d'auka ta kai fridge ta ajiye................
Ta koma wurin freezer ta fiddo kaza, da kayan miya, cikin lokaci kankani ta gama stew daad'i take ji sossai In tana girki haka take jin cikin d'in kaman nata, a tsabtace take komai har ta gama rice, tana son duba time amma ba waya hannunta balle agogo, diban kayan cowslow din tayi ta koma kan varender ta fara yankawa a natse har ta gama tayi grating carrot, kitchen ta koma ta fara dube dube har ta samu wani robber me kyau sossai ta had'a a ciki ta rufe da foil paper.................
Daga parlor taji momma na kiranta, da sauri ta fito sede ta d'anyi turus jin yadda bugawar zuciyarta ya chanza da sauri ta d'ago se idonta ya fad'a cikin nashi kallon seconds biyu ya mata ya d'auke kai, zaune yake kan one seater kafanshi zube a kan center table sanye yake da wata arniyar gezna milk anyi ado da black zare a gaba ya kafa hula black, yayi kyau sossai...................
Har ranta take mamakin na miji da irin wannan haske da kyaun, a gaban momma ta duka tace "gani momma" ta'be baki musharraf yayi a zuciyarshi yace 'karere se kace ita ta haifeta' ci gaba da danna wayanshi yayi, yana ji momma tace "kawowa Musharraf fruit salad dinshi" tana mikewa tace "Ina yini?" Ko d'ago kai be yi ba balle ya amsa, har ta wuce a bowl ta zuba mishi ta sa spoon tare da d'aurawa a kan karamin tray ta fito.............
Har ta nufi saukewa a kasa se taga ya zame kafanshi yatsotsin kafanshi dogi masu d'an kauri ta bi da ido, masha Allah kafanshi ya mata kyau, a kan table din da ya janye kafan ta ajiye, ta juya ta nufi kitchen kenan taji an turo kofa muryan little taji ta shigo da gudu tana ihun paapi, paapi, suna had'a ido ya sakar mata harara da sauri ta koma tace "Assalamu alaiikuum" murmushi ne ya kubcewa musharraf, momma da khairi jin irin sallaman da tayi kaman waka a lokaci d'aya idonshi ya sauka akan kumatunta da ya lotse sossai se fararen hakwaranta da suka bayyana kaman bata san wani abu wai shi cin abinci ba tsabar farinshi..............
Da sauri ya d'auke kai yana maidawa kan little da ta karaso tana cewa "paaapi na a yi Anty Amrah na o......."(paapi ba ka ga Anty Amrah ba ta......) maganan ya katse ne sadda idonta ya sauka kan khairi se kuma ta waro su tare da daka tsalle "cutieeeee oyoyoooo" Da gudu ta nufi khairi ta rungumeta, d'aga ta khairi tayi tana mamakin rashin nauyinta tace "oyoyo little pretty, ya kk" kallonsu yayi na mintuna kan ya d'auke kai ya maida kan fruit salad dinshi................
Sede duk hankalinshi na kansu yana mamakin me yasa little da bata da saurin sabon da mutane duk da tana da surutu amma ta saba da khairi a gani d'aya baki ya ta'be, yana jin little na cewa "cutie yau ke zaki min wanka ki shiryani, and feed me couse am starving" murmushi khairi tayi zata yi magana taji momma na cewa "a'a little ki je Anty nuri tayi miki duk waennan abubuwa don khairi de aiki ne da ita"..............
Khairi ta ce "momma na gama aikina gabad'aya na rana, zan iya mata" momma ta d'an wara ido ta ce "Lallai haka kike da saurin aiki?" Murmushi kawai khairi tayi tana duban khairi tace "where is ur room dear?" Little tana kallon sama tace "upstairs cutie" saman khairi ta nufa a sace ya bi su da kallo lokaci d'aya yana mamakin turancinta abinda be ta'ba zaton tana ji ba balle tayishi fluently haka, ta'be baki yayi tare da ci gaba da shan fruit salad dinshi..............
A chan d'aki kuwa wanka khairi tayiwa little se surutu take zuba mata tana amsawa kaman bata so, bayan ta shirya ta cikin kananan kaya da ta san ta fi sakawa a hankali tace "little pretty naji kina cewa ya musharraf paapi is he ur father?" Little tace "yes he's my father, momma my grandmother, And my anties are Anty nuri, Anty miemie and Anty Amrah"..............
Faduwa gaban khairi ya dinga yi da ta rasa menene dalili ko don tana mamakin kaman musharraf ne wai ya haifi 'ya kaman little ne ko me, maganan little ne ya dawo da ita daga tunaninta a hankali tace "and ur mom?".................
*SORRY* 🙏🙏🙏
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
🎗🎗🎗🎗🎗
IGIYAR RAYUWA😭
🎗🎗🎗🎗🎗
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo
'Yar mutan Adamawa
Page➡️4️⃣2️⃣▶️4️⃣3️⃣
🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗🎗
"Mamana ta rasu" cikin tausayawa khairi tace "sorry pretty Allah yaji kanta" murmushi kawai little tayi, tana shafa cikinta tare da yin puppy face murmushi khairi tayi tace "Ohk mu je ki ci abinci" suna bud'e kofa ana bud'e na d'akin momma had'a ido sukayi da wata buduruwa da bata sani ba, wani kallon banza ta watsa mata a d'age tace "who the hell are yhu?" Kai a khairi ta kawar tace "house help" waro ido tayi tace "and yhu have the guts na hawan upstairs baki san maids basa hawa nan ba".............
Little tace "o'o Anty salima I invited her here, and momma ta sani" harara saliman ta watsa wa khairi kan ta wuce ta sauka, suma sauka sukayi ran khairi ba daadi tana tunanin su waye waennan en matan gwara ma salima ta d'anyi kama da mutanen gidan amma banda maryam kuma bata ji little ta kira sunansu a cikin mutanen gidan ba...........
Little na ganin Amrah zaune parlor tana cin abinci tace "Anty Amrah see the cutie I was telling you about" kallon khairi Amrah tayi tana murmushi tace "hi cutie" murmushi khairi tayi tana tabbatarwa kanta Lallai tayi sa'an gidan aiki don duk yaran momma bayan musharraf suna da tsananin kirki haka momman ma, Amrah na sa spoonful na abinci a bakinta tace "yhu cooked?" Kai khairi ta gyad'a waro ido Amrah tayi cikin sauri ta had'iye abincin tace "wow you cooked well Amma kinyi catering school a abroad ko?"...........
Dariya khairi da little sukayi yayinda salima ta ta'be baki ta ci gaba da danna wayan da takeyi, a fili