Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
rokon yafiyarshi ba don halinshi ba, don shi ba ya d'ubi girman Allah ya yafe mishi zina da yayi da matarshi dukda da yardarta, da asirinsu ya tonu kuwa me makon ya yarda se ya d'aurawa d'anshin namiji kwaya d'aya sharri har yayi zaman shekaru a gidan yari' senotorn de a shekaru biyu da suka wuce yayi sadaka da gabad'aya dukiyarshi inda ya koma talaka futuk a fad'arshi ya kwashe shekara biyu yana rokon Allah yafiya kan yazo a yanke mishi hukuncin zina, sannan ya kara da cewa matarshi kuma 'yar uwarshi fatima ta yafemishi tayi mishi takaba ko ze samu rangwami wurin Allah, inda a yau da safe aka yanke mishi hukuncin kisa ta hanyar jifa ga yadda abun ya kasance.
Da sauri khairi ta rufe fuskanta tana kuka sossai, Amrah da Miemie ma kuka sukeyi sossai yayinda momma ke hawaye tare da furta "Allahumma gafirlahu wa rahamhu, Astagfirullah" musharraf kam tunda aka fara jifan mahaifinshi ya runtse ido a hankali yace "na yafemaka Abba, Allah ya yafemaka, Allah ya amshi bakuncinka" uwar gayya nuriyyah kam yanke jiki tayi ta zube a sume.
Dukda laifin da ya musu amma gidan sunga tashin hankali sun kuma ji mutuwanshi sossai ba kad'an ba, kan kace me gidan ya cika da en uwa, a take su dadda suka kamo hanya cikin mintuna 30 suka shigo cikin gombe a lokacin har su hamma Ahmad sun kar'bo gawanshi, momma tasa hijabinta kato har kasa su hajiya Aisha duk sanye da manyan hijabai su Amrah ma na zazzaune hk dada ma, khairi kam na d'aki sossai ta tausayawa Abbansu duniya kenan, musharraf na waje cikin masu amsan gaisuwa idonshi kaman gauta tsabar ja jijiyoyin kanshi duk sun tashi goshinshi rad'a rad'a da su be ta'ba sanin yana son mahaifinshi ba se yau adu'a sossai ya dinga mishi har aka mishi wanka aka shiryashi a part d'inshi, dashi da su uncle nasir se Mamaji da bappa ne suka mishi wanka suka kwantar dashi a parlor su momma suka shigo suka mishi adu'ar ban kwana sossai tayi mishi adu'a ta roka mishi yafiyar Allah inda ta dinga furta na yafemaka hamma, na yafe maka, duk su nuriyyah ma sun mishi adu'a itakam ma duk ta fice a hayyacinta tana sonshi sossai don yafi kula da ita akan kowa a gidan suna ji suna gani aka fita dashi zuwa gidanshi na gaskiya bayan an binneshi musharraf kasa daurewa yayi ya fashe da kuka sossai.
Da kyar su uncle Ahmad suka samu ya dawo gida inda suka kira Doctor Aslam gida yazo ya duba shi don zazza'bi ne sossai ya rufeshi, alluran bacci ya mishi me karfi tare da d'auramishi ruwa don jininshi ya hau sossai.
Bayan kwana bakwai
A yau akayi sadakar bakwan Abbansu mutane dayawa daga wurare dayawa sun zo musu gaisuwa har en office d'inshi, kuma har lokacin yana kwance khairi ce ke kulawa dashi shan maganinshi, cin abincinshi, tsabtar part d'inshi dukda exams din da suke zuwa ita da Amrah, ita ke tausanshi da kalamai masu taushi don kwantar mishi da hankali sossai ta cire kunya take kula dashi, momma ma sossai mutuwar ya shige ta ko yaushe suna tare da dada tana bata kalamai, nuriyyah ta zama so silent kullum marwan na zaryan zuwa kwantar mata da hankali, Miemie ma de mutuwar ya shigeta don tayi sanyi kaman ba me hayaniyar nan ba.
Su mamaji sun koma tun bayan sadakar uku, amma kullum suna kira suji lafiyarsu haka su hamma nasir kullum se sun zo da iyalansu, su ke kawo musu abinci, a haka akayi sati biyu zuwa lokacin musharraf ya warke har ya koma office kowa ya koma normal rayuwanshi banda momma dake takaba, soyayya tsakanin khairi da musharraf ya ninka da, musharraf da kanshi ya bada shawaran a d'aga bukinsu se momma ta fita takaba wata hud'u kenan, za'a kara wata uku akan d'ayan da ya saura zuwa lokacin ma su khairi sun gama neco ba ma waec ba.
Su mamaji sun yarda da hakan kuwa, a hankali rayuwa ya ci gaba da gurgurawa lokuta dayawa ana cikin farin ciki da saisaitar rayuwa musamman wurin su khairi yau suke gama neco a yau kuma mutuwar Abba ke cika wata uku da sati biyu saura wata guda bukinsu inda baza'a fasa duk wani events da aka shirya tun farko ba, zasuyi lalle day, bridal shower, kamu, walima ranar da aka d'aura aure se dinner washegari, dukda khairi bata so ba amma ba yadda ta iya gasu amaren dayawa ita kad'ai baza tace kar ayi ba amaren sun had'a Nuriyyah, maryam, sulaimi, zainab se khairi. Mazan biyu na gida ne yayinda sauran suka kasance waje, mamaji da bappa sun zauna sun tattauna tunda suncewa sufyan ya fidda mata yaki zasu had'ashi da Afreen uncle Ahmad ya nuna yana tsoron kar abinda ya faru da kaninsu ya faru da d'anshi tunda ya nuna baya so a kyaleshi.
Haka kuwa suka hakura suka barshi don sunga illar hakan, tunda musharraf ya sa kafa ya tafi be sake zuwa ba se de waya sam be son ganin mommanshi na takaba yayi alkawarin baze dawo ba kuma se ta fita, soyayyarsu ba wadda be san dashi ba daga gida har wurin aikin hakan ke kara kular da Anty Rabi'ah musamman In tazo gidan taga yadda khairi ke kulewa a d'aki suna shan love, tayi ta hantararta kenan da gayamata munanan kalamai ba ita kad'ai ba har dada da su nabeel, kaman yau khairi na kwance a kuryan gado waya makale a kunnenta tana yiwa musharraf rigima "Allah honey nayi kewarka plz come soon am dying right here" ta bangaren shi yace "habaa rayuwata ki tausayawa bawan Allah mana, ko kina son ganin honeynki na kuka?" Cikin tura baki tace "uhm uhm" yace "am sorry nima Ina missing dinki sossai musamman wannan kunyan naki, nayi kewar idanunkin nan masu matukar kyau da tsari, nayi kewar well carved attractive lips dinkinnan baza ki gane ba baby am missing yhu more than someone can imagine".
Ya sauke numfashi kan yace "kawai ban son zuwa ne se momma ta fita takaba" tace "alright dear Allah nuna mana, ya shirye shiryen buki?" Murmushi yayi yace "Ai ku za'a tambaya wannan baby ba mu maza ba kune masu abubuwan yi amma fah na shirya mishi sossai sbd Ina so ya zama best wedding ever a gombe, huhhh dear am so tired wallahi tun safe aiki nake ban huta ba da kina nan kuma kin zama tawa da ina dawowa gida zan baje akan gado kiyi min tausa da hannayenkin nan masu taushi da albarka".
Murmushi me sauti ta sake tace "ka san ban ta'ba zata kana da surutu ba honey?" Wani sauti ya sake da ya sata jin tsikar jikinta ya zuba yace "Ai ke kika koyamin kuma se na gayaki da momma na" ya karasa da muryan da zata iya rantsewa ko little baza ta iya irin shi ba, lumshe ido tayi tace "I love yhu" cikin fisgar hankali yace "minfu mi yid'i ma boddi ha nder nberd'e am"(nima ina sonki beauty har cikin zuciyata).
Kira taji ana kwala mata hakan yasata cewa "I will get back to yhu baby, ana kirana" yace "waye?" Tace "Anty Rabi'ah" tsaki yaja don pendonshin ta fara fita ranshi sbd takurar da takewa khairi dukda ba ita ke fad'a mishi ba amma yana sane, cikin kasa da murya yace "ko menene ya 'bata miki rai ki tuna, Ina sonki zaki ji farin ciki, bye bye" ya kashe wayan murmushi tayi kan ta mike ta fito.
Ita da Afreen ta gani zaune a parlorn kasa ta duka tace "gani Anty" hararanta tayi tace "wacece Antynkin? Kije chan ki nemi Antynki munafuka, ba tun d'azu na kiraki ba? Wato se kinga dama zaki fito koh? Shege be iya samun wuri ba wallahi" Afreen tace "na rasa meyasa Anty fatima ta kasa gane munafurcin mutanen nan da gani sunan en gidan suka kai wurin bokansu na daji kiri kawai(mugayen fulani sune kiri).
Hawayen da ke kokarin zubo mata ta mayar don ganin dada da Amrah na shigowa murmushi tayiwa Amrah bata san sunji abinda su Anty Rabi'ah suke cewa ba Amrah ma ganin khairi bata nuna mata ba ysa ta sakar mata murmushi tare da ci gaba da tafiya da dada sandarta na hannunta ko kallon su Anty Rabi'ah batayi ba har suka shiga d'akinsu khairi, Afreen tace "ba kin gani ba mommy, suna shirin rabamu da en uwan mu" Anty Rabi'ah tace "kyalesu tsintacciyar mage de...." bata karasa ba se ma daka wa khairi tsawar da tayi tace "ki tashi kije ki dafamin pounded yam bana son na gari, doya zaki fere ki daka, da miyar egusi se pepper soup kan sa da kunun Aya" mikewa khairi tayi ta shige kitchen tana d'an murmushin tuna kalaman musharraf.
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
πππππ
IGIYAR RAYUWAπ
πππππ
π«ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, charity, honor and super writers)
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
Pageβ‘οΈ7οΈβ£9οΈβ£βΆοΈ8οΈβ£0οΈβ£
ππππππππ
Cikin natsuwa ta fara girkin don ita a ganinta ba wani abu me wahala suka bata ba kasancewarta me son girki, babban abunda ke damunta rashin tarbiyar Afreen tana ga se ta seta yarinyar ta kiyayeta a gidan ta rasa dalilin tarewarta a gidan tun last week, ga mamanta da kullum tana hanya, a fili ta furta "Au na manta ita da gidan pendonta!!" Tana ta sake sake tana girkin amma duk sadda ta tuna da musharraf se taji wani farin ciki wadda hakan ke kasa boyuwa a fuskanta bayan ta gama ta jera musu a dining ta shige d'akinsu tayi wanka da karamin towel ta fito d'aure a kirjinta tare da zama gaban dressing mirror ta fara shafa mai.
Tana cikin shafawa taji wayanta na ringing special ringing tone da ta sa don special man d'inta yasa ta gane me kiran seda ta ja ajinta tukun ta d'aga suka fara hira tana ci gaba da abinda take, tambayarta yayi me taje tayi nan ta gayamishi amma bata ce ga wacce ta sa ta ba, be ce komai ba don Amrah ta riga ta sanar mishi, sossai ya yabawa zuciya irin ta khairi da wata ce da se ta aibata pendonshi a gabanshi amma se ta dinga rufa musu asiri, hirar ta ne ya d'auke mishi hankali, inda take sanar dashi wai zasu koma gidan hajiya ruqayyah In ji ta achan za'ayi musu gyara na wata guda da ya saura, inda yake tambayarta karfe nawa zasu tafi tace mishi da dare driver ze kaisu.
Hakan ne ya hana musharraf kiran Afreen yaci mutuncinta, Ai ko da daren khairi da nuriyyah suka tafi da manyan akwatunansu, dada kam bata da abin cewa se godiya ga wannan bayin Allahn duk abinda tayi niyyan fad'a ko yi akansu kan ta aikata momma ta rigata, tunda tazo gidan bata komai se ci da kwanciya da kuma yawan zama da su Amrah a garden ko chan bayan boys quarters, shiyasa a duk sallollinta na farilla se ta sa mutanen nan a adu'a harda hajiya ruqayyah da ta d'auki nauyin kayan d'akin khairi gabad'aya ga na gyaran amare da zata musu.
A chan gidan kuwa hajiya ruqayyah part guda ta ware musu me komai da komai me d'akuna uku ta gayyato babbar me gyaran jikin nan Hajiya Jameela idrees daga chad don tayi mugun kwarewa a harkar se hajiya yasmeen Ahmad daga sudan duk dakuna d'ai d'ai ta saukesu se su khairi suka sauka a d'aya.
A ranar da suka zo a ranar aka fara musu abinda ya kawosu don manyan fridge d'in part din a cike suke da guzurin su hajiya yasmeen, da magungunan sanyi da infection suka fara, se gyaran fata wasa wasa kan sati biyu ya zagayo su khairi sunyi wani mugun chanzawa ga kamshi da ya mugun kama jikinsu ga wani d'an kiban da sukayi sukayi fresh dasu kaman d'anyen tomatos π
.
Toh su ci me kyau su sha me kyau ko abinda suke ci ma daban da wadda en gidan suke ci, su kwanta a Ac azo a dirje musu jiki da dilka a turarasu sama da kasa ko fita basa yi, yayinda soyayyarsu da musharraf kuwa ba'a magana kaman zasu kashe juna da love, har mamaki nuriyyah ke yi ba don ta san muryan hammanta ba da se ta karyata khairi akan irin soyayyar da suke zubawa.
Randa suka cika sati biyu a gidan a ranar momma ta fita takaba hakan yasa suka tarkata gabad'aya gidan zuwa gidansu harda hanan matar haidar da hafsa da suka saje suka zama kawaye matar haidar kam ma kusan da ita ake cinyewa da shanye kayan gyaran amaren, sossai momma tayi farin cikin ganinsu haka suna samun kulawa fiye da zatonta, ko su maryam da suma aka had'asu zuwa gidan uncle Ahamad don gyaran baza su nuna musu komai ba har ake wani kananan maganganu akan kaisu gidan hajiya ruqayyah da tayi, ta rasa me ke damun Rabi'ah wallahi har gwara zulai da dama ta san halinta ne.
Bayan an gama yiwa momma gaisuwa mutane sun tattafi khairi ta samu kebewa da dada inda suka fara magana akan gyaran jikin da ake musu se albarka dada ke sawa hajiya ruqayyah ko da ta'bi ta san jikin khairi ya chanzu balle kuma In ta wuce se kayi mintuna kana jin kamshinta, dada ne ta nisa tukun tace "Khairiyya ni kam maman hamdeeya ta san da auren nan kuwa?" Khairi tace "a'a dada" dada ta kuma cewa "Anya ma da na aikeki ki sallameta ki kuma bata adreshin gidan nan kinje?" Shiru khairi tayi hakan ya ba dada amsar tambayanta.
Cikin 'bacin rai tace "amma baki da hankali khairi shiyasa mana banga matarnan ta zo gidan nan ko sau d'aya ba, na san da ta sani da se tazo sbd mutunci irin nata, me ta miki haka da ta chanchanci wannan sakayyar daga gareki bayan duk kyautatawarta a kanmu anya rayuwa yace haka?" Shiru khairi ta kumayi hawaye na shirin zubo mata duk se bata ji daadin abunda ta aikata ba gashi ta bakantawa mahaifiyarta rai.
Dada ta sake cewa "ashe In kikayi kud'i na kanki har mu zaki iya mantawa da......." da sauri khairi tace "a'a dada kin fah san halina dada kin san abinda zan iya da wadda bazan iya ba, wallahi ba Haka kawai naki mata sallama da bata address ba, mijinta ne ya matsa yana sona dukda na nuna mishi bacin raina da kin amincewata amma se ya sameta ya kuma fad'a mata ita kuma ta kirani tana rokona In aureshi ana cikin hakan ne barin mu unguwan ya tashi, ban fad'a mata bane sbd kar ya kuma biyoni nan har yasa inyi abinda zan mutu Ina da na sani, don na san se ta fad'a mai, amma tunda ranki ya 'baci akan hakan yanzu zan samu driver ya kaini In gayamata, kiyi hakuri".
Bata jira cewar dada ba taja hijab d'inta ta fice driver ta samu ya kaita har tsohon unguwansu inda tace ya jirata ba jimawa zatayi ba, da sallama ta shiga gidan maman hamdeeya dake kitchen ne ta fito da sauri ganin khairi yasa taje da gudu ta rungumeta tana cewa "Alhamdulillah khairi ashe kuna nan garin duk na shiga damuwa da taraddadin me ya sameku? Ko kuna lafiya?".
Hawaye ne ya gangarowa khairi tace "kiyi hakuri mun saki cikin damuwa, muna nan lafiya" janta maman hamdeeya tayi zuwa parlor suka zauna ta fita ta kawo mata ruwa dukda bata ga alamun wahala a jikin khairi ba sema hutu da jin daad'i da ya bayyana amma hankalinta yaki kwanciya akan lafiyansu klau, bayan khairi ta sha ruwa ta bata labarin duk abinda ya faru da dalilin barinsu, sossai ta bata hakuri akan abinda tayi inda ta fad'a mata dalilin yin hakan.
Dukda ran maman hamdeeya yayi ba daadi amma tayiwa khairi uzuri sbd tana ganin laifinta ne, da bata nemeta akan maganan auren mijinta ba da duk hakan be faru ba, adress d'in ta kar'ba tace zata zo In shaa Allahu, ta dinga tsokanan khairi har kofa ta rakota se da tazo fita tace "banga hamdeeya ba" maman tace "suna fita da babanta zuwa gidan kakanninta kina shigowa" "Eyyah a shafa min kanta se na ganku" hannu ta d'aga mata tare da komawa ita kuma ta shige mota.
Tana sauka a mota kiran musharraf na shigowa d'agawa tayi tanacewa "baby Alhamdulillah momma ta fita takaba yaushe zan ganka?" Murmushi me sauti yayi har tana ji tukun yace "se next week dear, ya kk?" Tura baki tayi tana nufan garden tace "opps na manta ana gaisuwa tsabar kewanka da nayi, Assalamu alaikum ina yini?" Wani murmushin ya kuma saki cike da shaukin sonta yace "lafiya qalbee, ni kam ana ta maganan anyi kewata ko me aka tanada min?" Fuska ta rufe da tafin hannunta d'aya murmushi yace "awwwn I guess kunyar sarauniya ya motsa" tsiririyar dariya ta sake tana zama akan grass carpet dake gyare fes ba ko digon dotti bayan ta jefa hijabinta cewa yayi "on your data" kashe wayan yayi ita kuma ta cika umarninshi na kunnawa, tana kunnawa call dinshi na shigowa video call bata damu da sa hijabi ba ta d'auka.
Sanye take da doguwar rigar atampha blue da aka mata wata arniyar dinki da ya bayyana wuyanta sossai zuwa kan kirjinta an yiwa rigan style da plain purple chiffon kanta ba dankwali se gashinta da tayi parking daga tsakiya yana lilo a bayanta, suna had'a ido ya sake nannauyar ajiyar zuciya yana kare mata kallo dukda ta waya ne hakan be hanashi ganin freshness da shiness na jikinta ba dukda ba komai a fuskanta amma tayi mishi wani balae'en kyau ji yake kaman yaja ranan aurensu yadda ze ganta zaune kusa dashi ta zama mallakinshi.
Zaune yake a office sanye da Ash color suit da white shirt a ciki me dogon hannu ya cire na saman na cikin kawai ya bari tare da sake neck tie dinshi ash, "wow qalbee kinga yadda kika koma kuwa?" Murmushi kawai tayi mishi ya kuma cewa "an kuwa ta'ba ce miki kina da kyau?" Girgiza kai tayi yayinda da waro ido yace "Toh kinfi kowacce mace kyau a duniya,