Author : Fateemah Muhammad Gurin Category : Complete Novels
sun fito har garwashi nake sawa a wurin amma hakan be hana su fita ba" a d'an fad'ace yace "shine baki gayamin ba?" Shiru nayi, har muka isa kofan gidanmu be sake min magana ba ya juya ya fice na lura kaman ranshi a 'bace yake...........
Ashe yana barin wurin gari ya tafi ya sayo wani maganin kwari me karfi ya taho dashi, Ina shiga gida na samu babana na ya dawo da gudu na karasa na rungume shi bayan na ajiye tulun kaina, shima rungume ni yayi cikin farin ciki ya na tambaya na ya nake cikin murna na amsa, Ina satan kallon ummi dake sake mana harara a fakaice.................
Tsaraban da ya yo min ya bani na wuce d'akina cikin murna, har rana ya d'aga ban fita ba na San ba aikin da zanyi ba kuma zuwa tallah sbd baba ya dawo, sallaman yaro ne yasa na fita Ina kallonshi d'an makwabtanmu ne cikin wasa yace "Safiya 'be d'o nyaune ha yasi"(ana kiranki a waje) na san baze wuce umaru ba hakan yasa na bishi Ina kallon ummi dake ta kallona da tsana karara a fuskanta................
Ina fita na tare shi da hiran baba na ya dawo, murmushi yayi yace "ko zaki min iso?" Nace "ai In ya dawo baya ganin kowa a ranan baccin huce gajiya yake sha" yace "toh gashi Ina so muje In saka miki magani a d'akinki sbd abun kar su kara cizar min ke"............
A kunyace nace "zaka iya shiga ai ummi ce kawai ke aiki a tsakar gida" gyad'a kai yayi tare da bin bayana muka shiga da sallama duk da naga kallon mamakin da ummi ke mana hakan be sa naji ko d'ar ba don babana na gida, har d'aki na na kaishi ya bud'e maganin da niyyan zubawa kenan mukaji an fisge................
D'ago idon da zanyi don kallon wadda ya fisgen kawai naji an zuba min wani ruwa me shegen rad'ad'i da azaba a cikin idon kara me tsanani na sake inda anan take Umaru yayi kaina ganin Ina shirin fad'uwa ya d'aura ni kan jikinshi, a sama sama naji ihun ummi tana cewa "mun shiga uku malam!! malam!! Innalillahi wainna ilaihi rajiun yau naga ta kaina ni zahara'u"..................
Da gudu baba ya shigo jin ihu da salatin yayi yawa a tsorace yake kallona lafe a jikin umaru salati ya saki, ummi tace "malam kwarto har cikin gid'a safiya ta kawo mana shikenan mun shiga bakin jama'a" idona da yayi dishi dishi tare da yin jaaa na fitan hankalin se ruwa yake zubarwa nake kallon baba, da alaman yarda ze yi.....................
"Baba ba....." rufe min baki baba ya katse umaru dake shirin magana ze yi magana kenan mukaji sallama da karfi ba kakkautawa da sauri baba ya fita ummi ta rufa mishi baya, Umaru ma kama ni yayi ya tsayar tare da rike hannuna muka fito da mamaki yake kallon mama goggo zuwa lokacin duhu kawai nake gani.................
"Na zo ne In jaa kunnen karuwan 'yarka, wato karuwancin da sukeyi da umaru a waje be wadatar ba se ta Bishi har cikin gidana ran rasuwar mijina suka aikata masha'arsu, don tsabar rashin tarbiya ko kunyan gidan rasuwa bata jiba, Toh wallahi ku kiyayeni baza ku zo a rana tsaka ku 'bata min tarbiyar yarana da ke tasowa ba"..................
Da sauri baba ya dafe gini jin jiri na shirin kada shi se gumi yake had'awa take idanunshi sukayi ja, cikin lalau'be na isa inda yake tare da zamewa na rike kafanshi cikin rawan muryan nace "baba ka saurareni don Allah, ka kuma yarda dani wlh Wlh ban ta'ba aikata zina baa....." hankad'e ni da baba yayi ne yasa na dafe bakina Ina kecewa da kuka me tsanani shikenan shikenan baba ya yarda..............
Cikin fusata baba yace "tarbiyan da na miki kenan safiyya? Abinda zaki saka min dashi kenan a rayuwa? Tirr da haihuwanki daga rana irin ta yau na cire ki daga cikin 'y'yana wallahi ko kofan gidana kika tako Allah ya isa ban yafe ba kuma se na dawwama Ina tsine miki albarka idan har kika bayyana wannan munafukar fuskar taki akan nawa"...............
Cikin tsananin kuka naso In fahimtar dashi amma inaa yaki saurarena kaman daga sama muka ji muryan umaru yana cewa "ka yi hakuri ka aura min ita a haka, Ina neman alfarma don darajar annabi ka d'aura mata aure da kanka gareni ni kuma nayi maka alkawarin muddin Ina numfashi bazan ta'ba kawota ko da hanyar kauyen nan bane balle cikin garinnan ko gidanka".................
Tsit wurin yayi na mintuna tukun baba yace "muje a d'aura, wannan yarinya na tabbatar da mahaifiyarki na da rai da tayi Allah wadaran ranar da ta samu cikinki" ficewa sukayi, suka barni Ina aikin matsanancin kuka gashi bana gani............
Ina a inda suka barni har suka je suka dawo, umaru ne ya kama hannuna muka mike Ina ta kiran sunan mahaifina amma ko...... ko(kuka ne ya sarke Dada sossai tana ganin kaman yanzu duk komai ya faru.. da kyar ta samu kukan ya tsaya tukun ta ci gaba)............
Ko kallon inda nake be yi ba har muka fice daga gidan, gidansu umaru muka nufa Ina aikin kuka sam be lura binshi kawai nake Ina d'aura kafana a duk inda ya sauke ba sbd bana kallo kwata kwata duk da kuwa idanuna bud'e suke, gidansu muka shiga ya had'a kan shanukanshi duk hannunshi cikin nawa muka fice....................
*ku yi hakuri Wlh ban jin daad'i ne kwata kwata, shiyasa kukajini shiru kwnaa biyu, ku lalla'ba da wannan*
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
๐๐๐๐๐
ย ย ย ย ย ย ย ย ย IGIYAR RAYUWA๐ญ
ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ย ๐๐๐๐๐
Story and written by: fateemah Muhammad gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
ย ย ย ย ย ย ย 'Yar mutan Adamawa
Pageโก๏ธ2๏ธโฃ1๏ธโฃโก๏ธ2๏ธโฃ2๏ธโฃ
๐๐๐๐๐๐๐๐
Ko 'lau' bamu tsaya ba muka wuto jalingo, a take ya sayar da duk shanukanshi a lokacin dare ya fara yi gashi bamu san kowa ba sam be lura da idona ba yace "je ga wani dutse Chan ki zauna ki jirani kinji?".........
Girgiza kai kawai nayi ganin Ina ganin wani gefen yasa yace "me ya faru? Kar ki damu komai ze wuce ne Allah yana tare damu" a hankali nace "bana gani" zaro ido yayi yana cewa "me???" Maimaita mishi na kumayi dafe kai kawai yayi yana ambaton sunan Allah...........
Wani tsohon Abokin babanshi ya tuna dake nan jalingo yana da gida a barde way, d'anshi babba ma dillalin filaye ne, ajiyar zuciya ya sauke kan ya tsare mana machine muka hau se unguwan, da mutunci tsohon ya kar'be mu, kwanan mu biyu d'anshi ya sama ma umaru gidan nan da kuma gona inda ya biya da kud'in shanukanshi da ya sayar...............
Bamu kara ko kwana d'aya ba muka komo unguwan nan, shekarata d'aya na haifeku inda na sha wahala sossai sbd kankantar shekaruna, ban haifi su nabeel ba seda kuka shekara 12, batun ido kam mun jarraba magunguna yaki budewa se kawai muka hkr, Allah sarki umaru Allah ya rahamce ka, ya gafarta maka...........
ย Cigaban labari๐ธ๐ธ
Duk seda suka zubda hawaye sossai labarin ya girgizasu musamman Abul da khairi kusan mintuna biyar tukun baba yace "toh yanzu wai me ya kawo habun?"........
Dada tace "yace In Ina son zama a gidan cikin kwanciyar hankali In bashi 'yata tunda ni be same ni ba, da na ki shine ya fara zage zage anan na san yana bibiyar kab labarinmu sossai yaci mana mutunci daga ni har d'an uwan nashi" "innalillahi wainna ilaihi rajiun" suka fad'a a tare ummulkhairi tace "what??? Ni??? Yana yayan babanan??"............
Murmushi mai ciwo dada tayi tace "hmmm khairi abinda duniyar yanzu ta koma kenan uba ya nemi 'ya, wa ya nemi kanwa se adu'a kawai" baba yace "toh yanzu menene shwaranki" Kai tsaye tace "mu bar garin nan".............
Abul yace "haba Dada sbd shi kawai se mu tafi mubar gidanmu, makarantanmu, Sana'an mu da kuma rayuwar da muka saba da shi?" "Dole kuwa ku tafi Abulkhairi a yadda naji labarinshi tabbas be barku ba nan ma ba tsira kukayi ba kuje ku sake Gina wani sabuwar rayuwan kawai tun ba'a zo ana da na sani ba"............
"Baba toh yanzu Ina zamu je?" Cewar Abul, Haka kawai khairi ta tsinci kanta da cewa "Gombe" gyad'a kai dada tayi cike da gamsuwa don haka itama Chan hankalinta ya karkata gwara suyi nisa ko Allah ze sa su gujewa sharrin habu zuwa garesu, Maman sulaimi da tunda aka fara labarin se yanzu tayi magana tace "Toh bar mishi gidan da ya kullen zasuyi? Da kuma wani kud'i zasu tafi har su samu su kimtsa komansu?"..................
Dada tace "akwai sauran kud'in gonan nan da Abul ya bani yana jikina yanzu haka dubu d'ari biyu da ashirin, ze ishemu In shaa Allah, gidan kuma ya rike shi da Allah ai hakkin marayu ne, in mun ce se mun kwace gidan zamuyi asaran d'an kud'ad'en da mu ke da ba tare da munyi nasara ba tunda ya kwace takardun ya tafi dashi"................
Ita de khairi ta kasa magana mamaki sam ya ki sakinta da jin wannan cakwakiya da wan mahaifinta ke son had'awa da kuma ita, a zuciyarta tace tab lallai da kuwa da ya d'aukarwa kanshi. Shi kuwa Abul sam be so tafiyan ba don ba yadda ze yi ne kawai, sun tsayar akan zasu wuce washegari inda khairi ta mike jiki a sanyaye ta fara had'a musu kaya.....................
********
Sam ransu ba daad'i suka sauko daga saman cikin shirin makaranta Amrah da Zaraah sanye da uniform yayinda Miemie take sanye da doguwar rigan atampha da madaidaicin gyale kokarin sa wayanta take a cikin Side bag dake jikinta tana kuma fidda car key, kaman basa so ransu a had'e kaman ba su ba suka cewa momma dake zaune parlon kasa "mun tafi".................
A sanyaye tace "Allah ya kiyaye" tare da binsu da kallo kaman ba su ne masu fara'a da wasa ko wanni lokaci ba, zaraah ce kawai da bata san me ke faruwa ba take aikin fara'a da surutu, fita sukayi inda suka shiga motan ya Musharraf da Miemie ke zuwa school dashi be ce ya bata ba amma tunda ta fara Jami'a ya bata keyn shi kuma ke tura mata kud'in petroleum a kai a kai, har pocket money....................
Amrah ma ta iya driving don tare ya sa aka koya musu amma ya gargad'i Miemie kan kar ta sake ta bawa Amrah key ko sau d'aya ne se ya fad'a, hakan yasa In har tana da lectures d'in 8 take sauke su kan ta wuce driver se ya je ya d'auko su da motan Momma..............
Suna fita suka shige motar 'kiran End of discussion, Miemie ta ja ta nufi gate, daga wajen gate d'in wani mutumi ne baki sossai yake kama da Nuriyya komansu iri d'aya sanye yake da jumpan da daga ka gani kasan a sabonshi ba karamin kud'i ya ci ba, amma yanzu yayi datti ya kod'e sossai mutumin a rame yake kaman ka hureshi ya fad'i kanshi ba hula se gashin da ya tara abun tausayi de.................
Ko kallon inda yake basuyi ba Miemie ta ja a d'ari tabbas da akwai kura a wurin ba abunda ze hana ya bule mutumin, daga ciki kuma momma tayi zurfi cikin tunani har bata ji saukowan nuriyyah ba se ji tayi ta dafa ta, a hankali ta d'aga kai ta kalleta tana barin hawayen idonta zubowa, zama nuriyya tayi a gefenta sanye take da kayan NYSC ta d'aura after dress akai baki me buttons daga sama har kasa, tare da yana gyalenshi hulanta da jakanta ta ajiye tukun ta fara magana....................
"Har yaushe momma?" Momma tace "ban son Allah ya kamani da laifin barinku kuna abinda kukeso bayan kuma ba daidai bane, tunda ya tuba kam baza kuyi hakuri ku kar'be shi ba?" Nuriyyah tace "hmm yafiya fa kikace momma? Har ya kai a yafe mishi duk laifin da ya aikata nan? Dan Allah momma ki dena sa kanki a damuwa duk randa yazo kin san yanayin hawan jininki wadda shine sila kar ki bari yayi mana ajalinki"...................
Ajiyar zuciya momma ta sauke tace "toh naji zan dena damuwa in shaa Allah kar ki fad'awa yaynki zuwanshi dan Allah" Kai nuriyyah ta gyad'a tare da mikewa tace "se na dawo" momma tace "Allah ya tsare ya bada sa'a" murmushi sukayi wa juna kan ta wuce, motar ta da hamma Musharraf ya bata kyautanshi 'discussion continue' red color ta shige tare da jan motan ta fice Ko kallon gefen da mutumin yake itama batayi ba ta bar unguwan.....................
Seda tayi nisa da unguwar tukun ta parker tare da fashewa da kuka sossai take kukan duk cikinsu ita kad'ai Allah ya d'aurawa kaunar mahaifinta har cikin ranta amma laifinshi a garesu ba na yafiya bane har se ya je an yanke mishi hukuncin da ya dace da abunda ya aikata, nan kam dole su bishi da ad'uar dacewa da rahamar ubangiji despite manyan laifukanshi a duniya.................
Seda tayi kukanta ta koshi tukun ta d'aga waya ta danna kiran hamma Musharraf ko bata fad'a mishi ba su miemie ko zaraah se sun fad'a mishi gwara suyi magana ta fahimta da shi tunda yafi sake mata..................
*******
Shigowarshi office kenan yana zama ya jawo files files na gabanshi ya fara dubawa a tsanake yana cikin na farkon ne yaji kiran nuriyyah seda kiran ya kusa tsinkewa tukun ya d'aga da sallama a bakinshi amsawa tayi daga bangarenta ta gaidashi ya tambayeta su momma se tayi shiru ya sake cewa "bata da lafiya ne?".....................
Ya fad'a yana kokarin controlling kanshi don take yaji hankalinshi yayi mugun tashi Allah ne kad'ai ya san yadda yake son mahaifiyarshi, "a'a hamma, baba ya zo" In a very angry tone yace "what??? Ya zo? Me ya kawo shi?? And wa ya nuna mishi gidana???" Nuriyyah tace "ban sani ba wallahi yaya amma na sa me gadi ya koreshi, shine nake so ka kira momman ko hankalinta ze d'an kwanta na de yi iya kokarina"..................
Idonshi da yayi jaa ya kara kankancewa ya lumshe tare da cewa "Ohk" ya kashe wayan be kira momma ba se da ya kira gate man d'insu ya kashe mishi kashedi akan In ya kara bari mutumin nan ya shigo mishi gida wallahi a bakin aikinshi cikin tsoro ya amsa don ya san ran mai gidan nashi a 'bace yake sossai..................
Sanadin barinsu unguwan tudun wada kenan sbd baban na yawan zuwa Chan mai gadinsu na da kuma se ya barshi ya shiga, bayan duk kashedin da Musharraf ya mishi, randa ya zo last a ranan Musharraf ya sayi gidansu na yanzu suka tarkato suka dawo ya kuma kori wancan mai gadin duk kuwa da irin rokonshi da yayi tayi, a bakin driver yaji wannan labrin ai tun farko ma bai san shi bane da wlh be barshi ya shigo ba...................
Bayan Musharraf ya gama waya da gate man a take ya danna kiran momma tana zaune a inda nuri ta barta se sake sake take taji kira ya shigo wayanta tana kallon Musharraf ne taji wani tausayinshi ya rufeta, sam bata ga laifinshi ba don yace baze yafewa wadda ya lalata mishi rayuwa ya kuma jiyar dashi wahalan rayuwa ba, amma tana tsoron kar Allah ya kama ta da laifin gujewa mijin aurenta duk da kuwa ba sonshi take ko son zama da shi ba, amma hakkinshi na kanta tabbas abinda ke sata cikin damuwa kenan In har ya kusanci inda suke.....................
Da sallama ta d'aga ya amsa a sanyaye daga bangaren shi, cikin kasa da murya yace "momma me yasa kike son sa damuwa a ranki a duk sadda mutumin Chan ya matso garemu? Ba de har yanzu kina son shi ba?" Girgiza kanta kawai tayi tana mamakin halin musharraf a matsayinta na mahaifiyarshi yakewa irin wanchan tambayar? Ta san ba laifinshi ba ne haka yake birkicewa In har yaji labarin babanshi sam bata so wa kanta da 'ya'yanta irin wanchan uba ba amma ya ta iya ba laifinta bane Allah ne ya za'ba musu...........
"In Ina sonshi Musharraf laifi ne? Ko ka manta mijina ne kuma uban 'ya'ya na? Jininshi ke yawo a jikinku duk irin tsanar da kuka mishi kuwa ba yadda zakuyi da jinin nan ko ka manta har yanzu sunanka "Abubakar Mahmoud Adam?" Ku natsu ku maida hankalinku jikinku don kun yafe mishi ba abinda ze chanzu a jikinku, ku kiyaye kuma ni na riga na yafe mishi kuma In har ya sake dawowa zan bishi inda yake rayuwa muyi rayuwa tare tunda baka da manners".................
Kit ta kashe wayan, da karfi ya bugi hannunshi da table d'in dake gabanshi tare da cewa "shiiiittt!!!!!" Wlh ya manta da wa yake dealing yayi mata irin wancan tambayan, tana da saukin kai amma tana da zaafi wurin tarbiyya don shine shaida sbd yafi kowa dakuwa a hannunta kasancewar shi me fad'an duk abinda ya zo bakinshi wa mahaifinshi.................
"Goddamn it!!!!!!!" Duk randa mahaifiyarshi ta komawa mahaifinshi a ranar tabbas za'a d'auki gawanshi safa da marwa ya fara yana kiran numbernta amma sam ta ki d'agawa hannunshi ya tusa a tulin gashin kanshi idonshi na cikowa da hawaye, da sauri ya isa gaban briefcase d'inshi ya bud'e tare da d'auko cigarette ya kyasta mata liter zu'ka biyu ta kare ya jefar ya kara d'auko wani.................
#vote
#share
#comment
'Yar mutan Adamawa
๐๐๐๐๐
IGIYAR RAYUWA๐ญ
๐๐๐๐๐๐
Story and written by: fateemah Muhammad Gurin
Wattpad:- Gureenjo6763
'Yar mutan Adamawa
*this page goes to yhu sweet sis haneefa Muhammad Gurin, thanks for the support and care, yhu are such an angel dear I love yhu so much๐*
Pageโก๏ธ2๏ธโฃ2๏ธโฃโถ๏ธ2๏ธโฃ3๏ธโฃ
๐๐๐๐๐๐๐๐
Ganin yayi ta kiranta bata d'aga ba yasa yayi reporting a office be da lafiya ya tafi, tarkata komanshi yayi ya fice, ranshi a matukar 'bace wannan fushin da mommanshi tayi da shi duk baba yayi blaming sbd da be zo ba da hakan be faru ba, haushinshi yake ji har kashinshi............
Yau be taho da driver ba so da kanshi ya ja motan ya jefa ta titi, har ya isa gida ranshi tafasa takeyi ji yake