Advertisements
Chapter 17 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   17 / 99

48K to 51K   out of 295.8K words

juya
yana kallon sama sabanin dazu da yake kallonta. Wani kululun bakinciki yaji ya rufe
shi a lokacin. Ya gama wahala ya dawo da ransa amma ya zama kaya irin haka. Zainab
dinsa abar tattalinsa ita ce haduwarsu ta farko bayan watanni zata kare a gyaran
fitsari. Kuka zuci ya rinka yi har ta gama mirgina shi ta sauya masa kaya sannan ta
cire zanin gadon ta shimfida zanin goyon Ibrahim a gefe inda ta ja shi ya kwanta.
Zama ta kuma yi ta dora kansa a cinyarta "Hadir"


Bude idanu ya sake yi sai ya ga ta duku da kanta ta sumbaci lebensa. Zuciyarsa tayi
nauyi matuka. Ga matar da yake so take son shi amma ko yatsanta bazai iya rikewa
ba.


"Ka ga alamomi zamu fara koya yadda zan rinka ganewa idan kana bukatar wani abu"


Ido ya kifta don ya nuna mata ya fahimceta. Ta gyara zama tana yawo da yatsunta a
kansa "idan kana son abinci ko ruwa sai ka juya kanka barin dama. Idan kuma bandaki
kake son zuwa sai ka juya hagu. Ni kuma sai ince abinci ko ruwa idan dama ne. Sai
ka kifta ido sau data shine eh, sau biyu kuma a'a"


Ta jima ko lokaci bata tunawa tace sai sun kwatanta. Ummansa da kanta ta dawo tace
lallai tazo taci abinci. Ko da ta diba dakin nasa ta sulale ta koma taci. Shi sai
su kunu ko koko ake bashi da ruwa. Asibitin da aka kaishi a Kano ne suka ce kada a
bashi mai nauyi har sai ya soma sabawa da sabon yanayin jikinsa. Kudin da aka nema
na gwaji da aikin da ake tunanin yi masa kuwa ko yana daukar albashi kila sai ya
shekara biyar zai tara su. Aiki a lakarsa ta kashin baya ba karamin tsada bane
dashi.


Da daddare ko keyarta basu gani ba a ciki. Hadir ya sake matsuwa cikin daren tana
rungume dashi tana bacci haka ya saki fitsarin nan ya bata musu jiki saboda bashi
da damar tashinta. Tana tashi da asuba gyaran wurin ta soma yi sannan ta goge masa
nasa jikin tayi masa alwala.


Satinsu daya babanta ya koma. Zainab ita take yiwa Hadir komai banda zuwa bandaki
saboda yayi mata nauyi. Wannan tana ganin yayi alamar take sanar da kaninsa.


Wata guda suka yi a haka babu wani cigaba kullum yana nan a yadda yake sai ma hawan
jini da ya kama shi saboda yawan tunani. A wata na uku mahaifanta suka dawo dubiya.
A lokacin ne kuma baban Hadir a gabansa da Ummansa da iyayen Zainab ya bijiro da
maganar kashe aure.


Kofin kunun hannunta ne ya subuce bata sani ba kuma bata damu ba.


"Kashe auren wa kenan?" Babanta ya tambaye shi.


"Zainab da Hadir"


Zubewa tayi a kasa ta fashe da kuka "Umma kuyi hakuri idan wani abu nayi zan
gyara."


"Ko daya Zainab. Wannan shawarar da wahala muka iya yanke ta. Zamanki da Hadir babu
alfanu sai tarin wahala. Nasan kunyi mana halacci da kawaici amma in sha Allahu
bazamu bari naku hakurin ya kare ba"


Kuka sosai Zainab ta saka tana ji suna cigaba da maganar tana ta magiya.


Shi kansa Hadir din hawaye yake fitarwa. Babansa ya sake bata hakuri "kina da
kuruciyarki ta yaya zamu barki da mutumin da bazai iya yi miki komai ba sai zame
miki nauyi. Abu na biyu Hadir ne karfinmu mu kanmu. Yana kwance yanzu mu ma rayuwar
wahala take mana ta ina zamu ajiyeki? Yau da gobe sai Allah 'yata Zainab, watarana
zaki bukaci fiye da Hadir amma aure yayi miki dabaibayi. Zaki so kulawa da kowacce
mace take muradi a gidan aurenta. Sannan ko mu iyayensa zamu iya gajiyawa balle
mata. Komai fa sai anyi masa hatta gyara kwanciya. Kudin aikinsa kuma bamu da
yadda zamuyi mu taba hada rabinsa ma. Zuwana Sakkwato uku akan maganarsa sun ce
babu kudi a barikin"


Zainab daga gaban wannan take zuwa gaban wancan tana kuka tana roko akan su barta
da mijinta. Kwarai ta basu tausayi amma basa son nuna son kansu da rashin dattako.
Hadir sai rufe ido kawai yayi zuciyarsa tana kuna sai da yaji mahaifinsa ya kira
sunansa.


"Hadir, ina mai umartarka da ka sauwakewa Zainab kada mu zama masu daukan alhaki,
ka amince"


"Kada ka sakeni, don Allah ku barni da aurena" Zainab ta fada cikin tashin hankali.


Kifta ido Hadir yayi babansa ya sake cewa " ka amince cewa kai Hadir ka yiwa Zainab
matarka saki daya?"


Wannan karon ma ido ya sake kiftawa yana zubar da hawaye. Zainab yaji ta fado a
jikinsa ta kankame shi tana kuka bata san ma me take yi ba "Wallahi ban saku ba,
babu inda zani"


Mamanta da Umman Hadir kukan suke tayata saboda tausayi.

"Zainab kiyi hakuri"


"Ba fa zan je ko ina ba ai ba da bakinsa yayi sakin ba"


Babanta gani yayi abin yana daukan lokaci an kasa rarrashinta ya tashi ya mareta.
Ta rike kunci baban Hadir yana cewa don me zai mareta "yaya take so muyi mata ne?
Duk wani bayani anyi amma da gangan taki ganewa. Ki tashi maza ki hada kayanki yau
dinnan ma zamu koma"


Karamin hauka Zainab tayi ranar har suka bar garin gashi ance ta bar Ibrahim saboda
Hadir yaji saukin rabuwa da ita shima.


Sau biyu tana guduwa Kano bayan sun koma sai da babanta yayi mata kaca kaca karshe
ya yi mata aure. Lokacin Hadir ya kusa shekara biyu a kwance. Ranar da aka kaita a
ranar ta nuna mijin da wuka tace ko ya saketa ko ta kashe shi ta kashe kanta. Bai
tsaya bata lokaci ba yayi mata saki ukun da ta bukata.


Iyayenta sunyi fushi sosai da ita ta koma wata iri ita kanta saboda tashin hankali.
Sai da kyar ta samu suka hakura bayan an sake saka mata rana da wani ma'aikacin
kamfanin man fetur a Port Harcourt. Wannan karon babanta yace idan ta sake kashe
aurenta ko taje Kano bazai yafe mata ba. Mijin nata mutumin Sakkwato ne amma a can
Port Harcourt din zasu zauna.


Ba don taso ba akayi auren. Mutumin mai suna Musa Waziri yana matukar son Zainab
shiyasa baya fushi da ita. Yana da kudi shi ya canjawa iyayenta gida ya samarwa
yayyenta maza biyu aiki a branch din gidan mansu suka samu rangwame daga kangin
talaucin da suke ciki.


Ranar da ta tare tayi kuka kamar ranta zai fita. Gani take taci amanar Hadir
shiyasa har shekaru suke tafiya tsakaninta da mijinta bata taba wata doguwar
walwala ba. 'Ya'yansa 'yan mata biyu da ya rabu da mahaifiyarsu su kadai ne suke
samun kulawarta. Wannan dalilin shi ya karawa Musa hakuri da ita da halinta na
rashin son sa. Duka wani hakkinsa tana saukewa amma soyayya da fara'arta sai yayi
watanni bai gani ba.


Hadir yana nan kwance sai gashi da suka samu kaninsa yake kaishi idan yayi ciniki a
kasuwa kudi sun samu. Gashin yana taimaka masa wurin jin dadin jikinsa saboda yawan
kwanciya. Magana ce dai da wuya yake iya hada kalma daya kwakkwara. Ibrahim yana
girma ya gane waye Hadir a wurinsa a hankali ya gudu daga cikin gidan ya koma dakin
mahaifinsa. Sannu a hankali indai ba yana makaranta ba komai na Hadir ya dawo
gareshi. Idan aka kaishi hutu wurin Zainab baya iya sati biyu ya rinka cewa Abbansa
kenan dole a mayar dashi da wuri.


A haka shekaru ke tafiya a haka rayuwar wannan iyalin ta wargaje gabadaya daga
aikin soja. Miji ya koma kan wheelchair ga ciwon zuciya ya kama shi da gaske saboda
yawan tunani. Uwa ta sake aure bisa dole amma zuciyarta tana ga tsohon mijinta
sannan dansu ya taso a wata bahaguwar rayuwa bai san komai ba tunda ya fara wayo
sai jinyar mahaifinsa.


A bangaren Hadir rashin iya magana ya nemi iyalin Zayyan yana damunsa sai ya kwana
yana kuka idan ya tuna rasuwar aminin da ya dauka tamkar dan uwa. A irin lokutan
ciwonsa ke tashi a kasa gane kansa. Zainab ma bata taba mantawa dasu ba amma kunyar
nemansu take yi a yanzu bayan shekaru sun ja ta dan dawo cikin nutsuwarta. Bata san
Zayyan ya rasu ba haka nan bata sani ba ko shima ya dawo kamar Hadir. Mami kuwa
sunan garinsu kadai ta sani ta ina zata fara nemanta.


Babban abin dubawa shine komai na rayuwa duk yadda ka kai da matsuwa dashi sai
Allah Ya nufeka da yinsa. Mukan kwadaitu da gabatar da wani abu mai girma a garemu
amma sau tari sai wasu abubuwa suyi mana shamaki dasu. Yanayin rayuwa bai mantar da
Zainab mutanen da suka yi zaman amana ba amma halin da ta tsinci kanta yasa
damuwarta ta danne hangenta. Burinta daya ne a rayuwa...ta komawa Hadir!


**********
"Ni na kashe shi...ni nayi ajalin Zayyan..ina zan saka kaina? Hassana na kashewa
Alheran mahaifi. Meyasa nima ban mutu ba?"


Kuka ne irin na mazan da suka ga tashin hankali muraran ba labari ba. Babban soja
mai ji da jarumta shine yake zubar da hawaye kamar yaron goye.


Farfadowarsa kenan daga allurar anasiziya da aka yi masa kafin a shiga dashi
theatre. Tsahon sati biyu da kwanaki da yayi a asibitin Katsina kafin likitan da
zaiyi masa aikin kafar yazo daga asibitin koyarwa na Zaria yayi su ne a cikin halin
rashin sanin inda yake. Irin kukan da Mami tayi na fili da na zuci bazai fadu ba.
Major Mustapha soja yayanta kuma uban 'ya'yanta shine wasu cikin masu zuwa dubiya
suke kirawa hauka. Dole ace yana hauka don idan har zaka zauna dashi na minti biyar
ido biyu surutan da zaka ji yana yi kwatakwata babu ma'ana ga wanda baya tare dasu
a ranar da abin nan ya faru a dajin Liberia. Labari ne na yaki, tashin hankali da
zubar jini. Tsananin ciwon da kafarsa take yi shine musabbabin fitarsa daga
hayyacinsa har yake wadannan surutai. An tabbatar musu da cewa zafin ciwo ne kawai.


Asibitin suna kokarin dressing din ciwon amma yadda tsutsa ke fita suna cin namansa
daga ciki shi kadai yasan azabar da yake ciki. Dakin kansa wani irin wari yake yi
don kannensu maza ke kwana dashi ma. An hana Mami kwana sai dai tazo ta wuni ta
koma gida.


Kudi sosai suka kashe akan ciwon nasa. To yau dai Allah Yayi likita yazo an yanke
kafa dan abinda aka bari iya rabin cinyarsa ne. Sauran naman duk ya zagwanye saboda
infection.


Abinda yake fada ya tadawa Mami hankali. Cikin nutsuwa ta matsa kusa dashi tana
tambayarsa me ya sami Zayyan din.


"Ni ne dai nayi ajalinsa. Ashe duk mutuncin da yaron nan yake nuna min a dalilina
zai rasa ransa. Ya ceci rayuwata ya rasa tasa. Me yasa nima ban mutu ba?"


Mami ta shiga rudani aka sake kiran likita yace su kwantar da hankulansu allura
bata gama sakinsa ba. Da kadan da kadan sai da suka kwashe wata uku cur a asibitin
nan. Kafarsa ta hade wurin sai dungulmi amma ya gamu da wata sabuwar lalurar da
basu ankara da ita da wuri ba wato septicemia. Infection ne na jini da yake samuwa
daga infection a wani bangaren jiki sai kwayoyin cutar su gangara cikin jini.


Da zazzafan zazzabi abin ya fara sai kuma yawan jin sanyi. Da fari magunguna da
alluran malaria aka bashi. Yayi sati ana wannan babu wani chanji sai ma gaba da
abin ya kara. Bugun zuciyarsa sai ya kara gudu har ana gani dagowar kirjinsa, dama
ga muguwar rama da ya hada. Da likitocin suka ga babu sauki akace typoid ce. Nan ma
duk wasu allurai da magunguna sai da ya karar dasu.


Hankula sun kara tashi ne ranar da zuciyarsa ta nemi bugawa shine fa aka rinka
gwaje gwaje baji ba gani. Jininsa har asibitocin koyarwa na Zaria, Kano da Ibadan
an tura domin gano abinda yake damunsa. Rashin wadatar kayan aiki a asibitocin
kasarmu ya janyo Major Mustapha ya kusa rasa rayuwarsa. Da kyar aka gano a asibitin
Ibadan aka turo musu sakamakon. Sai a lokacin aka fara treatment bayan infection
din yaci jininsa sosai har ya fara harin kayan cikinsa.
Da aka sallamo shi haka ya dawo gida kamar mutum mutumi. Yau da lafiya gobe babu.
Ya rage surutai sai ma rashin son magana da kebewa daga mutane. Idan ya kalli
kafarsa sai yaji ya tsani rayuwa gabadaya. Da bai rasata ba Zayyan bazai dawo
daukarsa ba. Da sai su gudu tare su tsira tare.


Yayi shekara a kwance. An sayar da motarsa da filinsa na nan Katsina duk a siyan
magunguna masu tsada domin samun lafiyarsa.


Wata rana Mami tayi masa zancen su Mairama sai kawai ya saka mata kuka. Taya shi
tayi don gabadaya mijin nata yanzu tamkar bashi ba.


"Da wane ido zan kalleta Hassana? Ko kinsan cewa da don ta ni ne wallahi na
gwammace na kare rayuwa a Liberia da na dawo gida na fuskanci matar Zayyan. Na zama
silar da bomb ya tarwatsa mata miji shine abinda kike so kiji na fada mata idan ta
tambayeni ta yaya mijinta ya rasa ransa?"


"Kayi hakuri Daddy ba manufata ba kenan. Kasan ya barta da ciki ga Radhiya"


Kai ya girgiza "baki san nauyin da zuciyata take ciki bane da kin kyaleni. I feel
guilty and I hate myself and.... my life. Idan zaki je nayi miki izini"


Tasowa tayi ta rungume shi tana hawaye "nima me zance mata?"


"Ban sani ba..." yace da raunin zuciya yana kara kankameta.


Kwanaki kadan da yin wannan magana wata rana da daddare suna kwance ta tuna
Fauziyya ta kwanta bata yi fitsari ba. A gidansu Major din aka basu wani bangare
dakuna biyu masu fuskantar juna. Awwab a wurin samari yake kwana har an mayar dasu
makaranta.


Ta je ta kai Fauziyya tayi fitsari ta dawo da sanda saboda kada ta tashe shi. Amma
duk da haka sai da ya farka. Inuwarta ya gani ta tuna masa da lokacin da 'yan
tawayen nan suka rinka fitowa ta baya da saman bishiyoyi suna harbinsu. Baiyi wata
wata ba ya mirgina jikinsa ya damkota. A daidai wannan lokacin jinsa yake kamar a
wancan lokacin. Kunnuwansa suna jiyo masa sautin harbi da hayaniya tartar. Wata
muguwar shaka ya kaiwa Mami ya sakar mata karfi.


"Captain na kama daya kuzo ku daure shi mu tafi dashi base dinmu" yace da dan
karfi.


Mami sai kokawa take tana son yi masa magana ta kasa saboda wuyanta da ya shake
tana numfashi sama sama. A daidai kunnenta yace


"Who sent you?"
Wahala ta fara yawa Mami duhu duhu take gani. Da kyar ta samu ta juya ta saka duka
karfinta ta galla masa cizo a kirji. Gashin kanta ya damko da karfi ta saki kara.
Daga hannu yayi ya kwada mata mari ta sake yin wata karar. Zai kuma marinta haske
ya mamaye dakin. Mahaifiyarsa ce ta shigo tare da kaninsa da suka ji ihun Mami.
Tana zuwa itama hannu ta cire ta mare shi.


"Kasheta kake son yi ne Mustapha? Sakar mata gashi"


Tamkar wanda ya tashi daga bacci sai lokacin ya kula da hannunsa da inda hannunsa
yake yayi saurin sakinta. A guje ta tashi ta fada jikin Innarsa tana kuka. Wuyanta
Innar ta lura dashi saboda farar fata yayi jawur.


"Na shiga uku ni Fatima me zan gani? Ba dai shaketa kayi ba?"


Kansa yaji ya daure wai me yake yi a dakin nan shi da suke tare da su Zayyan a
daji. Firgici da tsoro ya kama shi ya soma yunkurin sauka daga kan gadon. Innarsa
ta dakatar dashi.


"Kada ka soma matsowa inda muke wallahi." Ta kalli kaninsa "rufe min shi da safe
sai a fadawa Alh Baba kafin babanku ya dawo"


Washegari zama na musamman akayi akan abinda ya faru a daren. Mahaifiyar Mami ta
shafawa idonta toka tace 'yarta ko dai ta koma gida ko kuma a raba musu daki bazata
yarda a kasheta ba. Ko wace ma hakan zata yi shiyasa aka tattara Mami da yaranta ta
kuma gidan iyayenta.


Major Mustapha kuma ya shiga wani sabon mawuyacin mataki a rayuwarsa. Iyaye duka
sun hadu akan cewa gamo yayi a dajin nan aka shiga banka masa magungunan gargajiya,
hayaki da rubutu. Kowa yaji labarin maganin aljanu cikinsu zai bada kudi domin a
kawo su gwada. Idan ka ganshi dole ka koka in kasan waye Major Mustapha. Ya rame ya
kare sai kashi da tashin hankali. Kuma abu kadan yake tayar masa da wannan abu ya
fada cikin dogon tunani yana ganin kamar yanzu abin yake faruwa.


Awwab shine mai zama dashi sosai kafin watarana shima ya shigo daki ya nemi Daddyn
nasu ya rasa. Ya zauna jiran ko yana bandaki amma shiru. Haka akayi ta neman Major
hankalin kowa a tashe. Mami taci kuka ta more. Sai can kamar ance Awwab ya duka ya
ganshi a karkashin gado yana ta rarraba idanu.


"Mami gashi nan"


"Shhhh zasu ganmu."


Mami ta dake ta duka itama "su waye zasu ganmu Daddy?"


" 'Yan tawayen mana"
Kasa magana tayi ta tashi ta koma dakin Innarsa tana kuka. Har yaushe zasu kare
rayuwarsu a wannan yanayi? Dama haka ake auren sojan ko kuwa kaddararsu ce haka?


Sauki babu sai daga Allah. A wannan yanayin Gambonsu Mami da mijinta Harun da a
wurin Alh Baba suka zo daga Germany inda yake aiki a gidan rediyo a matsayin mai
labarai.


Sunyi bakincikin yadda rayuwa ta mayar da 'yan uwansu shine Harun ya shiga newarwa
Major da Mami visar tafiya. A cewarsa zai kai dan uwansa asibiti ne tunda babu wani
cigaba a gida. Iyayensu dai sun kyaleshi ne amma a iya tunaninsu asarar kudi zaiyi.


Abu na Allah sun tafi Germany a shekara ta uku bayan rasuwar Zayyan. A can ne
bincike ya nuna Major yana fama da Post Traumatic Stress Disorder (PTSD). Lalura ce
ta kwakwalwa da a lokacin ba'a waye da ita sosai a bangarenmu na Africa ba. PTSD
tana samuwa ne ga mutanen da suka yi gamo da mummunan yanayi ko al'amari kuma tana
tashi ne idan suka samu kansu a yanayin da zai iya tuna musu da wannan abu. Yawan
mafarkin da yake yi da kuma ji ko ganin kamar yanzu abin yake faruwa duka
alamominta ne.


Mami tambaya take ba haukacewa yayi ba aka ce mata ba hauka bane sai dai masu ita
suna bukatar tsantsar kulawa daga makusantansu don idan abu yayi yawa wasu har
kashe kansu suke yi.


A gidan Gambo suka zauna har zuwa lokacin da ya fara jin sauki. Mami ta jajirce
sosai wurin kula dashi. Daga baya ta fara tunanin kada su zame musu nauyi tace
Harun ya nema mata aiki. To aiki a wata kasar ba'a samunsa kai tsaye. Ta bukaci ko
yaya tana son neman kudi kafin su koma saboda kusan karkaf sunyi. Komai nashi ya
kare an fara shiga aljihun dangi.


Aikin nanny ya samar mata har yana tsoron fada mata sai ta basu mamaki wurin karbar
aikin hannu bibbiyu. Gidan wasu 'yan kasa take zuwa daga bakwai na safe zuwa bakwai
na yamma. Tayi su shara, wankin toilet da sauran ayyukan gida hade da raino.

Mutane da dama suna zaton da ance ka fita waje watayawa kake. Aikatuwa take
bilhakki mijinta yana kukan nakasa a gefe. A hankali masu gidan suka yaba da
kwazonta sai aka basu wani dan bangare karami a gidan.


Cikin shekarsu ta biyu Harun yaje gida abinda ta hada ta bayar aka dauko musu
'ya'yansu sauran kuma ta aika Sakkwato wurin sojan da Major ya rubutawa sako cewa a
bawa

17 / 99