Advertisements
Chapter 3 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 99

6K to 9K   out of 295.8K words

zamu fito ki ganshi da kyau. Hmmm Hausarsa sai ta
baki dariya, sakkwatanci yake”

Kamar wanda ta hadiyi kota Salame tace “umhumm”
Taro ya watse amare da angwaye suna farinciki, Zayyan da Mairama suma suna nasu.
Bayan isha ba dadewa kuwa sai ga aike cikin gidan ana sallama da Mairama. Ta Madina
tayi dariya tace idan al’amari ya kankama tukwuicinta mai tsoka ne tunda ita ta
kawota. Kunya ce ta kama Mairama taje ta janyo Salame wadda taso nokewa suka fita.

Maza uku ne a wurin. Zayyan, Hadir sai kuma wani abokin Hadir din tun kuruciya
layin gidansu ma daya Salisu. Tunda suka fito shi kuma ya kyallo Salame shima tasa
zuciyar ta lula kogin kauna.

Gaisawa suka yi a mutumce Hadir ya sake yi musu bayanin waye Zayyan da manufarsa
akan Mairama. Zuciyar Salame kamar ta fashe don bakinciki a ganinta cin fuska ne ma
suke mata. Bayan an gama bayanin Salisu yace shima fa yaga matar aure nan dai aka
hau gabatar da kai. Salame ko kadan bata yi farinciki ba. Salisu dan kasuwa ne a
kantin kwari tun da kuruciya yake da zafin nema bata sani ba yana da arziki sosai.

Mairama da Zayyan sun rabu akan cewa jibi kafin ya bar gari zai sake zuwa don a
hada shi da mai yi masa rakiya Sumaila wurin Malamijo. Idan ya tafi zai gabatar da
maganar ga magabatansa don bashi da burin a ja lokaci. Salisu ne dai bai wani sami
hadin kan Salame ba hanlinta yana kan hirar su Zayyan yace Mairama ta taya shi
neman fada.

Bayan sun tafi a cikin gidan ana ta tsokanar Mairama ta kuwa biye musu tana yi tana
sako yayarta aciki. Salame kunci da bacin rai ya sanya ta fashe da kuka mai cin
rai. Shiru kowa yayi Mairama tayi juyin duniya taki cewa komai. Ta Madina aka
sanarwa tazo itama tana tambayarta sai cewa tayi wai gida take son komawa.
Ashar Ta Madina ta kunduma mata “ke har wani gida gareku a Sumailan kike son
komawa?”

Fuskarta har ta soma kumbura tace “ni dai tafiya zanyi tsoro nake kada mu koma
Malamijo yayi fada don baiso muka zo ba”

Ba wani abu ke cinta ba face zallar kishi da kanwarta. A ganinta idan tasa su ka
koma gida Zayyan bazai san gidansu ba bare yabi Mairama shikenan kowa ya rasa.

Abu kamar wasa Salame ta tubure sosai. Ran Ta Madina a bace tace gobe da sassafe
zata sakasu a mota kuma ta kwana da sanin cewa bazata sake neman daukota ba, idan
Malamijo zai cinyeta ne a gidansa babu ruwanta. Dayake ido ya rufe maganar ta inda
ta shiga ta nan ta fice.

Mairama a daren bata damu ba sai da ta tuna Zayyan yace zai zo hankalinta ya tashi.
Har daki ta kira Salamen ta roketa alfamar ta bari su sake kwana. Kallon da bata
taba yi mata ba ta jefeta dashi wanda ya haddasawa Mairama tuhumar kanta ko ta bata
mata rai ne.

“Kinzo kin wani shige cikin danginmu sai wani cusa kai kike yi. Dadin abin dai duk
tsiyar mutum da danginsa na jini zaiyi tinkaho. Mu dai munyi sa’a muna da dangin
uwa”

Mairama sai taji ranta ya baci itama “nima ba daga sama tawa uwar ta fado ba. Idan
don nazo bikin danginku ne Allah Ya baki hakuri bazan kara ba”

“To dama waye zai gayyaceki?”

Kasa bata amsa tayi ranta a jagule ta karasa hada kayanta ta dauko wanda Salamen ta
bata na taron da akayi da rana ta saka ta mika mata. Bata damu ba ta karbe duk da a
farko niyarta ta bar mata kyauta ne.

Tasha aka kaisu suka hau
mota suna harare hararen juna. Mairama ita gorin da akayi mata ne ya bata mata rai
don bata san me tayiwa Salame haka da zafi ba. Sun isa gida kafin azahar Malamijo
yana gidan gonarsa wurin dabbobi.
Babu wanda ya aikesu bare yayi murnar dawowarsu gidan. Basu rufa awa guda ba ma
Dije ta taso Mairama tazo tayi mata aikin fura da take yi ta sayarwa saboda ciyar
da yaranta. Tana tsaka da aikin Inno ta kira Salame ita kuma aka bata surfen
masara. Haka suka yi ta aikin babu mai yiwa ‘yar uwarta magana. Mairama ke satar
kallon Salame cike da damuwa, ita kuma da sun hada ido sai ta galla mata harara.

Washegari wuraren goma na safe aka aiko wani yaro wurin Malamijo. Dan aiken da ne
ga wanda yake taya shi aikin kula da dabbobinsa. Yaron yana haki don gudu yayi zuwa
gidan ya sanar dashi wani katon san sa yana neman kasawa ya bada izini a yanka shi.
Tamkar an soki kahon zuciyarsa ya zabura zai bi bayan yaron sai ya tuna babu
takalmi a kafarsa ya koma ciki da sauri.

Lokacin da ake sanar dashi san ya kasa dan sa daya na wajen Inno mai suna Habibu
yana ji ya juya cikin gidan kafin ya ankara da tsayuwarsa. Inno tana gaban murhu za
ta hada wutar girki yazo yana haki.

“Inno yau kece a turaka?” ya tambaya babu alamun damuwa a fuskarsa sai ma
farinciki. Yaran gidan musamman masu uwaye sun san ranakun girkin iyayen nasu
saboda abincinsu yana fin na sauran ranakun auki.

“Idan bani bace uban me zanyi a nan da zafin ranar nan kwal a kaina”

Dariya ya saki har wawulunsa na gaba su ka bayyana “san Malamijo ne ya kasa Inno
yau akwai cin nama.”

Kamar wadda aka bawa kujerar hajji Inno ta saki dariyar farinciki ita ma. Su da
nama sai dabba ta kasa. Gashi ya fada girkinta sai yadda tayi kenan. Bakin dan nata
ta toshe lokacin da yake cewa ta cire musu manyan tsoka idan an soya irin na wancan
karon.

“Allah Ya sa wani ma ya kasa mu samu da yawa” ya kare da addua.

Tsaf Malamijo ya gama jin me suke cewa ya shiga tafa hannuwa “ba amin ba,
billahillazi baa min ba. Kuji min ‘yan bakinciki masu fatan tsiya. Idan ba kun
jawowa kowa wallahi mahauta zan saidawa bazaku ci ba”

Yaron sai ya kama kuka nan da nan iyalan gidan su ka cika tsakar gidan. Don kada
ayi biyu babu Inno ta fada musu sa ne ya kasa kuma wai baza’a kawo musu kamar yadda
aka saba ba. Iyaye mata suka hau jimami yaransu harda masu dan wayo suna kuka. Kuka
na gaske suke ana rokonsa ya taimaka. Shi abin nasu tsoro ya bashi ma ya ja baya ya
manne a jikin bango yan raba idanu.

“La-e-lafi qureshin wallahi idan ku mayu ne Allah Ya fiku” yace yana tottofe na
kusa dashi “ko ku matsa ko na dauko sarkin mayu yazo ya kama min ku kafin ku karasa
ni. Haba ko da naji, kullum zukewa nake jiki babu wata mamora kamar ba Ali mai
garken dabbobi ba”

Magana yake yana kallon jikinsa yadda yake sai tsayi da uwar rama ya kula Mairama
tayi murmushi abinda bata saba ba. Tun haduwarta da Zayyan take jin zuciyarta fes
babu wannan mugun kuncin na gidansu. Mamaki sosai ta baiwa Malamijo don kullum ya
tarasu yana irin wannan hade rai take abinta bata kuka bata bada hakuri kuma. Sai
yaji wani dan dadi a ransa haka kawai.

Yadikko ce ta bashi amsar maganarsa “ta ina zaka yi kiba ka tara hakkin mutane sun
fi talatin a wuyanka”

“Ta, ta, ta uwar zance nasan sai kin tanka. Indai sa ne zaku ci amma yau akan idona
za’ayi komai har rabawar don bana so ake kwarar wasu. ‘Ya’ya dai duka nawa ne”
Gidan tuni ya kaure da ihun murna ya shige ya sako silifas zai tafi gonar kafin su
ma wurin aikin naman su kwashi rabonsu su boye.

Yana fitowa yayi kicibus da sojoji biyu a kofar gidan da wani yasha shadda sai
kyalli take na sabunta. Su kuwa sojojin ya ganesu ne saboda kayan jikinsu wanda
suka yi matukar kyau a cikinsu. Sai kuma dan Ta Madina wato kanin Salame da ta aiko
rannan. Gaban Malamijo yayi wata irin faduwa baki ya soma rawa.

“Uhmm ince dai lafiya ko”
Hadir ne ya amsa fuskarsa dauke da murmushi “lafiya kalau dama akan Mairama da
Salame ne…”

Ko gaisuwar da suke masa bai iya amsawa ba ya koma ciki jikinsa na bari.

Wanke-wanke ya hango Mairama tana yi yayi kanta a fusace.

“Ashe ba banza ba dazu kike murmushi abinda baki saba ba, wato kunje Kano idon ku
ya bude shine kika kai karata wurin hakuma ko?”

Dago kai tayi da sauri Salame ma ta fito daga dakinsu don maganarsa ta hasko mata
su waye. Kenan batayi sa’ar rabasu ba.
Shi kuwa a harzuke yake matuka ya shiga nuna su da yatsa “nasan kece mai bakar
zuciya ke ki ka ingiza Salame ku ka kai karar, amma ku sani babu wanda zai kamani
akanku, biki ne na barku kunje kuma san nan nace za’a kawo muku ku ci me ya rage”

Kana ganinsa kasan a tsorace yake sauran matansa su ma duk sun tsure. Yadikko ce
tayi karfin halin riko hannun Mairama

“kin san ko su waye a wajen?”

Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta Yadikko ta kuma maimaita tambayar. Ganin ta
ki magana sai ta sake cewa “kodai surukai ne daga Kanon?”

A guje Mairama ta yi hanyar dakinsu cike da kunya. Yadikko ta fadada murmushinta
tana yiwa Malamijo da yayi saroro a wurin bayani. Sai gashi yana wani kasaitaccen
murmushi yana kada kai.

“O’oh kaga su Mairama Daso ‘yar Ma’aikin Allah. Ashe dai da farinjinin ta ban sani
ba. Baku ga sojojin ba fa gwanin ban sha’awa. Ganinsu kadai ya sani shauki na tono
lokacin da muka fara zuwa gwaji Jaji a can kasar Kaduna…”

Hajjo ta tuntsire da dariyar rainin wayo don tasan kawai sakin kwai zaiyi duk
labaransa bata taba ji yace yaje barikin sojoji ba.

Hankalinsa ya koma ga Salame yana tambayarta ko ita ma da bakonta. Ciwon da yake
cin ranta bai bari ita ta gwada kunyar ba kawai ta hade rai ta koma daki.

Mairama ya kwalawa kira ita ta bashi tabbacin akwai wanda yake son ‘yar uwar ta
ta. Sai ga Malamijo baki yaki rufowa “Ka ga Ummassalama abu yayi kyau. Allah dai
Yasa mai shaddar ne naki don bazaki iya da hakuma ba, wannan sai ‘yar kunama. Bari
dai na koma wajen bakin”

Su na tsaye ya barsu da kokonta sai gashi ya dawo da fara’arsa har babbar riga ya
doro akan kayan jikinsa.

Tabarma aka shimfida musu a zure shi kuma yana daga kan wata kujerar karfe ya baza
riga don ya cika ido. Gaishe shi suka sake yi Hadir yayi masa bayanin komai game da
zuwansu da bukatar idan ‘yan matan sun amince ayi komai da wuri musamman saboda su
basa samun damar fitowa daga barikin suyi dogowar tafiya batare da dalili ba.
Yawonsu baya wuce cikin gari kada a nemesu sunyi nisa.

“Ku kwantar da hankalinku Kano dai ba bakuwata bace sannan a can birnin Shehun ma
akwai wanda na sani don na taba zuwa garin. Kunsan wani mai kilishi a hanyar Dange
shuni? Yana nan wani dan firit haka yace min asalinsa ma mutumin Zaria ne. Kila zai
iya tuna ni don naji dadin kilishinsa na sayi da yawa lokacin…”

Duk sun dauka wata alaka zai ce tsakaninsu ko karin bayani sai suka ji zancen
yakare, Zayyan sarkin dariya tunda yace mai kilishi dan firit ya daga kai ya kalli
Malamijo sai kawai ya kunshe dariyarsa kada ya jawowa kansa. Sun ji dadi ya ce ya
basu yaran sai su fara shiri. Tashi yayi yace su jira zai turo su ko gaisawa suyi
tunda su Zayyan a ranar zasu koma Sakkwato.
Kusan a shirye Mairama take kira kawai take jira yayin da Salame ta nade akan
katifa wai zazzabi ke damunta. Mairama tayi mata sannu ta bi bayan kanwarta da ta
sanar da ita Malamijo yace taje wurin bakin.

Sai da tazo bakin kofar da zata sa da ta da zauren da suke, kunya ta hanata shiga.
Da Hadir ya hangota, ya fara zolayarta cewa ko sune bata son gani bari su basu
wuri. Kai a kasa ta rufe fuska ta shiga ta gaishesu. Salisu yana cigiyar gimbiya
Salame ta sanar masa bata da lafiya. Yanayin fuskarsa ya nuna baiji dadi ba.

“Ki dai taimaka min naga alama so take ta saka min ciwon zuciya”

Zayyan da Hadir ne suke kwantar masa da hankali har suka fita don a bar Zayyan suyi
magana da Mairama.
“Mairam tafiya ba sallama ko?”

Kanta a kasa ta amsa “kayi hakuri”

“Nayi tunda zuwan nawa ya haifar da da mai ido gashi an bani ke”

Wata matsananciyar kunya ce ta shigeta ta sake dukar da kai. Shima yasan a hanya
suke shiyasa bai ja ta sosai ba yace zaiyi kokarin dawowa kafin magabantansa su zo.
Yau a hanya suke suna sauri. Wata leda ya mika mata, yayi yayi, taki karba sai ya
tashi ya barta a wurin. Iyakarta bakin kofa tayi musu sallama da kyakkyawar addu’ar
tafiya.
[02/11 7:28 AM] My 2nd Mtn: E
*TUN RAN GINI…*


Tana shiga daki ta sami Salame a tsaye sai safa da marwa take saboda zulumi. Yanzu
shikenan abinda take so sai ta hakura dashi saboda Mairama. Gaskiya bazata iya ba
domin son da take masa ba kadan bane. Kuma ma dai ai ita ce ya kamata yaso tunda
danginta ne, Mairama kara kawai akayi mata. Ta nisa a cikin tunani taji Mairama
tana mata magana.

“Adda jikin ne dai? Ko na sanar da Yadikko a fadawa Malamijo?”

Hade rai tayi ta koma ta zauna akan tabarma “ke yanzu banda rashin kamun kai me ya
kaiki dadewa wurin saurayi daga zuwansa na farko? Mutumin da ba wani saninsa ki ka
yi ba don iya zubar da aji.”

Kwarai Mairama tayi mamakin kalaman Salame don a iya sani da kuma shaidar da za’ayi
mata a gidan tafi kowa saukin kai da dadin mu’amala. To amma meye ya kawo wannan
zantuka haka? Kasa daurewa Mairama tayi ta koma bakin katifarsu ta zauna ita ma.

“Adda Salame wai me nayi miki ne haka don Allah? Kwana biyu kenan sai kiyi ta
harara ta kina fada min maganganu”
“Ji rainin wayo ki min kwace kizo kina min dadin baki” tace a ranta amma a zahiri
sai ta daure tayi mumushi “gani nayi daga yin saurayi kin haukace a kansa ko
tunanin idan kin bar gidan nan da wa zan zauna ba kya yi?”

Jikinta sai yayi sanyi ta sake matsowa kusa da Salamen “kai Adda me ya kaiki wannan
tunanin? Shine kike ta fushi…ohh ni wallahi duk kin tayar min da hankali na damu.
Kema ga Salisu ba sai mu bar gidan tare ba.”

Turo baki Salame tayi “dena min zancensa wallahi baiyi min ba, ke dai kinyi sa’ar
Zayyan kawai kina murna”

Rarrashinta Mairama ta soma yi a zatonta da gaske tunanin rabuwarsu a gaba ke
damunta. Sauran kannensu mata babu sa’anninsu, maza biyar ne su ke binsu. Koda
Salisu ta shiga yi tare da bata sakon gaisuwarsa ta yi tsaki da gaske dai bata son
zancensa.

“To na bar zancen nasa Allah Ya kawo wanda ya fishi alkhairi. Shima yace na
gaisheki da jiki kuwa”

“Shi wa?” Salame ta fada cikin gatsali wanda Mairama duk ta sawa ranta duk a cikin
rashin son su rabu ne.

Tambayar kunya ta bata ta soma inda-inda ba ta san da me za ta kira shi ba. Sunansa
dai da wahala ta iya fada a yadda take matukar jin nauyinsa.

Zungurinta Salame tayi da kafa tana mata wani irin kallo mai tattare da kishin da
ake kokarin sakayawa.
“Zayyan kike nufi?”

Kai ta gyada ga mamakinta sai ta ga fuskar Salame ta washe sosai tana murmushi
“ashe bai manta ni ba. Me yace? Ina nufin da yaya ya baki sakon? Ki gaishe da
Salame yace ko me?”

Dadi taji ganin sauyi a tare da yayarta ta kuwa biye mata tana fada mata yadda yace
da zai bada sakon gaisuwar. Har dare ranar Salame motsi kadan sai ta tuna wai
Zayyan yace a gaisheta, sai taji wani dadi yana ratsata.

**********

Matafiya sun sauka a cikin garin Sakkwato lafiya. Ba wata gajiya su ka yi ba don
sun dade da fara sabawa da wahala suna jure mata sosai. Gidansu Zayyan su ka wuce
zai dauki kayansa da ya bari sai su koma barrack dinsu.

Gidan yanzu dama daga Jume sai Maikudi, Rayyan da Badaru wadanda sune Zayyan yake
bi dukkansu babu mai aure. Matan kuwa Fiddausi, Mubaraka da Hafsatu duk suna
dakunansu. Kwasar tuwo Jume take yi Badaru yana zaune akan turmi da ya kifa sai
Maikudi kwance a kofar daki yana faman firfita su ka ji sallamar Zayyan din.

Babu wanda ya amsa masa cikinsu sai harara da suke binsa da ita. Dakinsa ya wuce
kai tsaye ya dauko jakar kayansa a ransa yana bakincikin halayyar ‘yan uwan nasa.
Ba haka ya bar jakar ba alamu sun nuna an bude an yamutsa masa kaya wurin neman
abin da yake zaton kudi ne, sai dai ko kwandala bai bari a ciki ba. Ratayo abarsa
ya yi ya fito ya kulle dakin.

“Sai Allah Ya sake dawo damu ni zan wuce” yace daga tsaye yana dan rissinawa Jume.

Maikudi ya tashi zumbur yana kallonsa, ita ma Jume ta juyo da kujerar da take zaune
a kai yadda za ta fuskance shi da kyau.
“Zayyanu ni zaka wulakanta a gidan nan? In baka umarni saboda ba uwarka bace sai
kasa kafa ka take. Kwana nawa ina sawa a dubo ko gidan Aminun ka makale babu kai
babu labari sai yau. Shine har kake da bakin cewa zaka wuce.”

Baya son ya kai ga yi mata abinda zai zo yana nadama nan gaba ga darajarta na
matsayin wadda ta rike shi kuma matar babansa, da idan ya fada mata wata maganar ko
hanyar da ya bi bazata so ta sake bi ba.

“Jume Kano naje biki ba maganarki naki ji ba”

Maikudi ya dawo kusa dashi ya miko hannu kamar wanda ya bawa ajiya “ina kudin da
tace ka karbo a wurin wancan tsohon munafukin?”

“Yanzu aminin Baba kake kira munafuki?”

“Kaga kafin ka fara dogon surutu bani kudin ka wuce bana son rigima da al’murun
nan” Jume ta fada tana kara tamke fuska.

Dago idanu yayi ya zube mata a kanta sai gashi jikinta ya yi lakwas. Rayyan da
Badaru ma kowa ya sha jinin jikinsa. Maikudi ne kawai hankalinsa bai kai wurin ba.

“Jume!”

“Eyye” ta amsa a dan tosrace.

“Kudi dai gadona ne ni kadai kamar yadda a gabana aka bawa kowa nasa...”

“Kai, rashin kunya za ka yi mata a gabanmu?” inji Maikudi.

“Idan na fahinceka Zayyanu kudin ne ba za ka bani ba saboda ban isa in nemi abu a
wurinka in samu ba?”

Tausayi ta bashi yadda ta hakikance akan rashin gaskiyarta bata ko tunani sai son
bukatarta ta biya. Hannu ya zura cikin aljihun wandonsa ya zaro naira dari ‘yan
ashirin guda biyar ya mika mata.

“Ga wannan ku kara cefane” yace cike da nutsuwa, bai kuma jira cewarta ba ya fice
waje inda Hadir yake jiransa.

Yana fita Maikudi ya warce kudin a hannunta yana jaddada mata tasan yadda zata yi
ta karbo musu ragowar idan ba haka ba shine zaiyi ajalin Zayyanu sai ya ga ta inda
zaiyi amfani da kudin.

“Banza shashasha to sai ka dawo, kafin kayi ajalin nasa shi zaiyi naka. Har mamaki
kake bani yadda kake manta zuciyar Zayyanu da kuma kasancewara soja. Yanzu idan
yasa aka

3 / 99