Advertisements
Chapter 83 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   83 / 99

246K to 249K   out of 295.8K words

dauko masa wata. Ya kusa cinyewa suna ta masa
tsiyar dama da yunwar Ibrahim ya shigo. Kafin yayi parking Zayyan ya duku kansa
tsakanin Ummi da Emzee.


"Jama'a wai ni yaushe zaku koya min mota ne? Da kunya fa ace Zayyan Tureta bai iya
dan murza sitiyarin nan da kowa keyi ba"


Me kuwa zasu yi banda dariya shi kuwa ya cukule yana cewa a motar Emzee zai koya
yadda zaiji dadin bubbugeta kuma bazai ba da kudin gyara ba.


Ibrahim yana karasowa bayan ya gaishesu ya karbe fork din hannun Emzee wai zaici.
Emzee ya damke hannun ya hana shi.


"Yanzu ko loma daya bazan samu ba?"


A daidai kunnensa Emzee yace "Idan ka dawo Zayyana ta dafa maka"


Yana jin haka ya gane wace ta dafa ya tasa Emzee a gaba karshe a tsaye ya karasa ci
yana ta juya baya Daada da Ummi suna cewa da mai kwadayi da mai rowa. Cikin sauri
sauri su ka bar gidan Ibrahim ya ajiye shi ya dawo. A hanya ya turawa Rahima text
yana godiya da girkin da tayi masa da rokon kada ta bar gidan sai ya dawo.


A ranar ne kuma Aishatou kawar Tante ta iso za ta fara gyaran amarya Alheran
Radhiya. Tante Nasara tace mata ta tabbata ta fito mata da 'yarta ta yadda ko ita
kanta Radhiyan idan ta kalli mudubi sai tace bata gane kanta ba. Sai da Ummi taci
dariya tace to ayi mata wankan inji mana daga nan.


Ba bata lokaci suna gama baccin gajiyarsu da kwana biyu aka fara gyara ciki da
waje. Baki kuma kowa ya kama gabansa su Salame duka sun koma Sumaila na Nijar da
Sakkwato suma sun tafi.


**********
Wayar gaggawa Daddy ya samu daga Katsina da daddare Alh Baba yana son ganinsa tare
da iyalinsa. An tabbatar masa kowa yana lafiya sai shi Alhajin ne ma da yake ta
fama da ciwon suga.


Washegari kuwa ya hada kan iyalinsa su ka tafi. Dama kuma a ranar Bilal yaso tafiya
da Fauziyya idan an fara bikin sai ta dawo.


Awwab sallamarsa da Radhiya da ga nesa-nesa akayi. Tun ranar da akayi taron nan da
suna waya yace mata akwai sauran rawar da za ta yi masa. Wani mugun kida kamar zai
tsaga mata waya ya tura mata yace tun wuri ta koya suna sake haduwa zata yi masa.
Shikenan take gudunsa duk da yayi ta magiyar cewa wasa yake yi. Ana fara gyaran
jiki Aishatou tace shima mijin sai ana masa rowar ganinta domin a haka ne idan sun
hadu zai fi ganin kyaun da tayi. Haka yayi ta korafinsa da mita ya hakura tunda ya
fuskanci da gaske maigyaran jikin da Tante Nasara suke. Zamu hadu kawai yake cewa
Radhiya don sai ya fanshe wannan punishment din na babu gaira babu dalili an hana
shi ganin matarsa.


Mota uku su ka yi ranar da zasu tafi. Daddy da Mami a motarsa dreba na jansu. Sai
Awwab da ya dauko Zahra, Raji da Zayyana. Mota ta uku kuwa Fauziyya ce da Bilal ana
tuki ana shan soyayya wai kara'i take yi saboda laulayi ya sa ka ta a gaba kwana
biyu yanzu kuwa anyi lafiya.


Wani masallaci su ka tsaya sallah irin na matafiya kafin su shiga Kaduna Zayyana ta
tsaya sakawa Jawad takalminsa su Daddy Haroun su ka shigo wurin. Mummy Gambo,
Ghazalatu da kanwarta suna shiga masallacin su ka ga su Mami suna sallah. Su din ma
sallar suka yi an idar sai yiwa juna kallon kallo saboda abinda ake cewa ta ciki na
ciki. Ko kadan sun kasa sakewa da juna ayi hira yadda aka saba. Ba su Mamin ba, ba
kuma ga yaran nasu ba. Nama da lemuka Awwab ya siyo ya kira Zayyana tazo ta karbar
musu. Ghazalatu na can gefe da kanwarta Fauziyya ta fara yunkurin jawosu jiki.


"Kuzo muci abinci"


"Mun koshi" Ghazalatu tace a kunyace saboda nauyinsu da take ji idan ta tuna duk
abinda ya faru saboda ita ne.


Basu sake cewa komai ba amma cin abincin baya yi musu dadi saboda ga 'yan uwansu a
gefe. Su kuma saboda sunce sun koshi babu damar zuwa su sayi wani.


Mummy Gambo sai ta rasa yadda za ta yiwa Mami magana saboda kunyar kowa yanzu yasan
bayan sun gama yi mata tijara ga yadda auren ya kare. Mami kuwa sai ta yi kamar
bata lura da yadda ta takura ba ita da yaran tana cin abincinta hankali a kwance. A
zuci tausayin Gambo take ji sai dai dole ne ta nuna mata kuskurenta. Can da abin ya
ishi Mummy Gambo gashi Daddy Haroun ya tsaya suna magana da Daddy wadda duka akan
yanayin sabanin iyalansu ne ta dan matso kadan kusa da Mami.


"Ina ta zuba ido ko zaki gayyacemu taron da kuka yi na dawowar uhmmm baban yarinyar
nan amaryar Awwab sai muka ji shiru"


"Banyi zaton zaki so zuwa bane" Mami tace kai tsaye.
Mummy Gambo dama neman kofar magana kawai take yi amma ba ta zargin yayarta don ba
ta gayyacesu ba "Mami...hmmm...Mami kiyi hakuri akan duka abubuwan da suka faru"


Zahra na jin haka ba ta jira Mami tayi magana ba yace duka su tashi su bar wurin
don ta san maganar ta manya ce. Ghazalatu har ta soma hawaye. Mami ta kalli
kanwarta tana tuna irin batancin da suka yi mata har gida.


"Ki bar maganar nan mu karasa Katsina nan ba muhallinta bane"


"Naji amma kice kin hakura don Allah" Mummy Gambo ta fada a raunane tana kara
tsanar abubuwan da tayi.


"Na yafe amma a bar zancen haka."


Gaba Mami tayi da sauri don kada ta soma hawaye a wurin suka tafi kowa ya shiga
mota. A jere suke tafiya har Katsina gidan Alh Baba. Anyi abinci sosai na tarbar
bakin gidajen guda biyu. Sai da su ka yi sallar la'asar aka ci abinci sannan Alh
Baba ya kira kannensa, Ummansu Mami sai kuma Mami, Hussaina da Gambo kowacce da
mijinta da kuma 'ya'yan da abin ya shafa wato Awwab, Ghazalatu da Nura. Ba tare da
bata lokaci ba Alh Baba ya soma magana.


"Maman Biyu gani da 'ya'yanki da kowa a wurin nan kamar yadda nayi miki alkawari
zanyi kokarin yi musu sulhu." Kallonsu yayi daya bayan daya "Hassana, Hussaina da
ke Gambo mun taba zama daku shekara uku da suka wuce akan auren Muhammad da
Ghazalatu. A wancan lokacin nawa idon ne ya fara rufewa da son ganin kamar yadda da
yawa cikin 'ya'yanmu su ka auri juna su ma jikokin suyi haka. A zatona zumunci zan
karawa karfi ashe ruguza shi nake yi. Kuma sai akayi rashin sa'a zumuncin na
'ya'yan mutum daya na bata. Maman Biyu kiyi hakuri"


Mami da kannenta kowa sai sharar kwalla yake yi saboda ganin Ummansu tana kuka.
Tayi bakin kokarinta ta shiryasu abu ya faskara shiyasa ta kawowa Alh Baba kukanta
kuma bata ji nauyin fada masa gaskiya ba kai tsaye ta dora masa laifin bata
zumuncin 'ya'yanta.


Alh Baba ya koma ga su Awwab "Muhammad da kai zan fara. Kai da kanwarka kun hada
kai bisa rashin sanin mahaifinka har ya nema maka wani auren. Tabbas ka fini
gaskiya a lokacin da ka nemi hada mata biyu domin fitar da mahaifinka kunya."


A hankali Awwab ya daga kai ya kalli Alhajin ya mayar da kansa kasa yana saurarensa
lokacin da ya koma kan Nura yayi masa kaca-kaca akan irin tozarcin da ya yiwa
Ghazalatu.


"Wannan abu duk mun sanya son kai a ciki karshe bamu ji dadi ba. Gambo kin biyewa
'yarki tace bata son kishiya...."


Awwab na jin zancen ya koma kan iyaye ya kalli Nura da yake tsananin jin haushi da
Ghazalatu wadda tamkar a zare allura babu wata soyayya da ta rage masa a zuciya
game da ita sai ta 'yan uwantaka da tausayin halin da ta fada a gidan miji.


"Ku tashi mu fita"


"Ban gama ba dreban sama ku koma ku zauna" cewar Alh Baba.


"Alhaji zamu dawo tunda na ga maganar yanzu ba tamu bace" karamar tsawa ya dakawa
Nura dama ya girme shi "kai tashi mana"


Da sauri ya mike su ka fita su ukun. Alh Baba da sauran kakanin sun yabawa Mami
wurin tarbiyantar da 'ya'yanta gashi har yasan su tashi saboda iyayensu za'ayiwa
fada.


Fada, nasiha da jan kunne sosai Alh Baba ya yiwa su Mami musamman Hussaina da ya
dorawa alhakin ingiza wutar rikici tsakanin Mami da Gambo.


"Abinda akayi ta rigimar dominsa gashi sai da ya faru..." Baba Karami yake cewa
dasu "munje mun karbawa Muhammad auren yarinyar nan Radhiya. Ku kuma da kuke ta
tada jijiyar wuya gashi gayyar ta watse. Kunyiwa yaranku auren huce haushi sun kare
da hadaku fada da juna"


Hussaina tafi kowa jin kunya ga ishrar da take gani a wurin Hany har yanzu bata da
lafiya dangin saurayin kuma sunki amincewa.


"Nasan hakkinku ne yake bibiyata Hassana da Gambo ku yafe min don Allah"


Ummansu ma kukan take yi a dole su ka rinka cewa sun yafewa juna. Iyayensu albarka
suka saka musu sannan aka sake kiran su Awwab. Baban Biyu yace yana bukatar
daidaituwar zumuncinsu ko me zaije ya dawo tsakanin iyaye daga yau bai yarda su
juyawa juna baya ba. Sun tashi zukata wasai. Daddy ne yayi saura da iyayensa yake
fada musu irin alkhairin da Zayyan yayi masa da duk wanda ya rabe shi.


"Banda ceto rayuwarmu da yayi kudin da gwamnatin tarayya ta bashi a matsayin diyyar
wahalar da yasha wallahi yake ta bin mutane da alheri. Nasan ana cewa ka haifi
mutum baka haifi halinshi ba amma ina kyautata zato akan cewa Radhiya a cikin namu
dangin alkhairi ce. Ban taba kin Awwab da Ghazalatu ba. Duk abinda nayi nayi shi ne
domin kulawa da bayan wanda ya sadaukar da rayuwarsa dominmu. Nasan gabadaya
rigimar nan ta samo asali ne akan auren da na nema masa saboda haka ina mai rokonku
da ku yafe min"


Kowa yace ya yafe duk da ba laifi yayi ba. Hasali ma yayi abin yabawa ne sosai
saboda bai kasance mai manta alkhairi ba.


A hankali hira ta barke a tsakanin 'yan uwan inda su Zahra sosai suke jin zafin
Nura da abinda ya yiwa Ghazalatu. Ana haka ta hango Awwab a kan kujera can gefe a
cikin falon yayi nesa dasu. Murmushi tayi ta karasa inda yake wata sabuwar wutar
sonsa tana ruri a zuciyarta. Chatting yake da Radhiya yana ta murmushi ta zo ta
zauna a kujerar gefensa.


"Ango kasha kamshi" tace tana rausayar da kai da murmushi.


Hankalinsa na kan wayar yana yiwa Radhiya reply yace "Kamshi sai mata"


Murya ta karyar alamun kuka take shirin yi "kaji irin zaman da muka yi da Nura ko?"


Wayar yasa a aljihu ya maida hankali gareta "naji Ghazalatu sai dai ince kiyi
hakuri komai mukaddari ne."


Gwauron numfashi ta sauke tana tararrabin abinda za ta fada. Hannu ta ga ya mayar
zai dauko wayar tayi saurin cewa "Yanzu shikenan tsakaninmu Ya Awwab?"


Karo na biyu ya kuma mayar da wayar "ban fahimceki ba"


Sunkuyar da kai tayi kafin ta bashi amsa "nasan cewa ban kyauta ba amma kayi hakuri
idan da hali zan jiraka"


Ya fara gane me take son cewa sai dai baya son zumuncin da ake kokarin fardadowa
dashi ya kuma sake sumewa a dalilinsa "Ghazalatu mun riga mun wuce wannan matakin.
I am happily married matata ko tarewa bata yi ba so please kada ma mu komawa abinda
ya wuce"


Hawaye ne ya zubo mata "yanzu baka tausayin halin da na shiga? Ban taba cireka daga
zuciyata ba kuma a shirye nake na zauna da kai ko a ta biyun ne"


Ransa yaji ya soma baci amma baya son janyo hankalin kowa garesu "Allah zai baki
wanda ya fini amma bani da niyar mata biyu yanzu"


Wani irin murmushi tayi "wato nice baka so wancan lokacin shiyasa har ka iya
amincewa wata kuma ka fada da bakinka kana sonta ba wai don Daddy Mustapha ya nema
maka aurenta ba"


"Wai ni Ghazalatu Nura ya sakeki ne kike min wannan zancen?"


Da murnarta ta amsa "ya hakura yayi min saki daya"


"Idan dai ba lissafina ya baci ba ina tunanin har yanzu kina cikin kwanakin iddah
ko"


"Nasan da wannan amma bazai hana na fada maka abinda yake raina ba"
Neman abinda zai fada mata yake yi wayar Radhiya ta shigo. Yana dauka ta soma kukan
shagwaba wai baiyi mata reply ba. Dama hirar tafiya honeymoon suke yi ya bata zabin
kasashe uku yace ta zabi daya shine ta tura masa inda take so bai duba ba.

Hakuri ya soma bata Ghazalatu sai ta daga murya tana cewa wai yace gata zasu gaisa.
Gudun kada ta zargi wani abu tunda ta riga taji muryar mace a wurin yace mata ga
Ghazalatu zasu gaisa.


Mika mata wayar yayi ta koma kan kujera ta zauna tana magana a gayance kamar bata
so "amaryarmu ko ince uwargida sarautar mata yaya shirye shiryen biki?"


Zuciyar Radhiya har ta fara tafasa da kishi musamman saboda yanayin yadda Ghazalatu
ke fitar da harufa daki daki tana wani yauki.


"Lafiya kalau" ta daure tace.


"To ga amanar Yayana nan dai ki kula mana dashi sosai...idan kina bukatar
shawarwari game da hanyoyin sace zuciyarsa ki karbi numberta a wurinsa." Wata
shu'umar dariya tayi "kinsan na karance shi kamar tafin hannuna"


"Abinda ba'a sani ba ake karantawa, ni da Hammana kuwa warin takalmi ne komai namu
iri daya....how do I put it?" Radhiya tace muryarta na fita cikin nutsuwa. Dariya
tayi a hankali saboda samo kalmar da ta dace ta fada "Alheran is the female version
of Awwab...amma duk da haka nagode da tayin da kika yi min"


Awwab tsabar mamakin abinda Ghazalatu tace kasa yi mata magana yayi sai jinjina kai
yake da halin mata. Kallonsa tayi ta saki murmushi duk da ranta in yayi dubu ya
baci da amaar Radhiya amma ai ba'a fara komai ba ma "Ga angon namu.....Yayana
sauran maganar tamu fa?"


Fizgar wayarsa yayi ransa a hade ta sake maimaita tambayar da dan karfi yace zasu
karasa daga baya. Da sauri ya saka wayar a kunne yana cewa hello Radhiya ta katse
kiran. Yasan za'a rina sai dai yana sake kira yaji ta kashe wayar gabadaya.


***********


Ko sati ba'ayi ba da taji Mami tana fadawa su Ummi matsalar gidan Ghazalatu da
mutuwar auren shine daga zuwansa Katsina yau zasu tada tsohuwar soyayya. Allah Ya
bada sa'a tace a zuci ranta yana kuna tayi jifa da wayar ta kifa kai tana kuka.


Kamar wasa ta kwashe yafi awa guda tana zubar da hawaye. A haka Rahima tazo ta
sameta sai dai bata ga fuskar ba tayi zaton bacci kawai take yi. Awwab tun yana
daukar abin wasa har ya fuskanci fushin nata na gaske ne. Bai san sau nawa yana
gwada wayarta ba amma duk kira a kashe. Gashi layi daya gareta bare ya nemi wani. A
ranar su biyun da kyar suka yi bacci saboda tunani. Asubar fari yana dawowa daga
masallaci ya sake gwadawa nan ma shiru har bayan azahar. Bashi da kwanciyar hankali
lokacin kana kallonsa za ka gane akwai abinda ke damunsa. Mami tana ta yi masa
magana akan cewa su Umma da sauran matan kakanin sun ce lallai idan an dauko
Radhiya daga Sakkwato nan Katsina za'a kawota ayi budar kai kafin su wuce Nijar.


Sama-sama yake jin muryar Zahra tana cewa gaskiya tana tausayin Radhiyan saboda
zasu sha yawo. Wayarsa a hannu yana yi mata text bai amsa ba Mami ta kira shi da
dan karfi "wai meye yake damunka ne ana magana ka kasa amsawa? Ka ji abinda nake
fada ma kuwa?"


Saurin kallonta yayi "Mami naji, gajiya ce dai kowa sai yayi a tanadi maganin ciwon
jiki kawai"


Murmushi tayi tana cigaba da fadawa Zahra ta rubuta abubuwan bukata na walimar da
za suyi ranar budar kan "tunda wahalar saboda ku ne ai kai ya dace ka siyo mana
maganin"


Murmushi kawai yayi ya tashi kamar jira suke Mami da Zahra su ka tambayi juna me
yake damunsa ne.


Kasa hakuri yayi ya kira Ummi saboda ba karamin kewar Radhiya yake yi ba ga damuwa
tunda yasan fushi take yi dashi. Lokutan da ya sami damar kasancewa da ita kadai
idan ya tuna sai yaji kamar ya budi ido ya ganshi tare da ita. Sun gaisa da Ummi
lafiya kalau yadda su ka saba ya rasa da yadda zai nemi Radhiya. Ita da kanta ta
fuskanci me yake damunsa.


"Awwab kaima ka kira kanwarka baka samu ko?"


Da sauri yace "eh"


Murmushi tayi "Jiya Karami sai da ya kirani na hadasu, dazu ma ya sake cewa na bata
su gaisa wai ya kirata shiru kuma bata kira shi ba. Ban san me yake damunta ba sai
aikin kwanciya...."


Rahima ta bawa wayar ta kai mata. Har ta mika hannu tana tambayarta ko Emzee ne
Rahima tace ba shi bane. Tunda taji haka tasan ko waye sai cewa tayi ta mayarwa da
Ummi wayarta yanzu za ta kunna tata ta kira shi. Awwab yana jin duk abinda tace
kamar yayi ihu saboda yadda ya matsu ta amsa masa taki.


Fitar Rahiman ke da wuya ta sake fashewa da wani kukan ko abinci ta kasa ci sai
tunanin yana can suna soyayya da Ghazalatu.


Zuwa dare jikinta yayi mugun zafi da ciwon kai saboda ita dama ba mutum bace mai sa
abu a rai. Wannan karon da tayi shiru sai yake neman yi mata illa. Ummi ta gaji da
wannan zaman daki da tsura da ga jiya zuwa yau take tambayar Aishatou mai gyaran
jiki ko ta ga wani chanji game da ita.


"Shiru shirun da take yi ne ke damuna dai Ummin Radhiya. Kuma kamar kuka tayi ma
shiyasa jiya da yau aikin namu bamu dade ba. Ina jin fargabar aure ce ta fara taba
ta. Kinsan fa ance aure yakin mata"
Ummi ta soma dariya "yakin matan zamaninmu ko, yanzu budurwa ko ita ce ta hudu
banda rawar kai me su ka sani"


Hira suke abinsu akan bambancin matan da da na yanzu Mami ta kira suke zancen
walimar da dole yanzu sai tayi a Katsina. Ummi ma tace dalilin da yasa ta kira dazu
kenan Malamijo yace kafin su fara bikinsu a kawo masa jikarsa suyi nasu taron tunda
ya kula wannan bikin ba na zama bane yawo za'ayi ta yi.


"Yaran nan zasu wahala musamman Radhiya da take mace ko dai mu matso da bikin kada
mu cure komai cikin sati guda muzo ana 'ya kwance uwa kwance" inji Mami.


"Ke da 'yarki ne zaku kwanta ni kam garau zaku ganni don ko suyar albasa bazan
tayaku dashi ba" Ummi ta bata amsa da dariya.


"Kyale wannan 'yar rabona da ita tun jiya"


Sai yanzu Ummi ta fara damuwa "Mami bari na dubo yarinyar nan. Jiya da yau a daki
ta wuni muna cewa ko fargabar aure ne amma dai bari na duba" tace tana hawa sama
zuwa dakin Radhiya.


Bata ajiye wayar ba ta shiga ta same kwance a kasa ta rike kai da hannu biyu. Da
sauri ta durkusa a gabanta tana dora hannu a kan goshinta da yayi zafi ga idanu a
kumbure anci kuka an gode Allah.


"Ke me ya sameki?" Ummi tace a tsorace tana ajiye wayar a gefe. Tayar da ita tayi
ta koma kan gado.


"Kaina zai tsage Ummi" tace a wahale.


Mami na jinsu hankalinta ya tashi ta soma kwalawa Awwab kira ta ma manta suna
Katsina ne Radhiya na Abuja. Tare da Daddy su ka shigo daga waje ta fada musu me
taji Radhiya na fada. Sosai hankalin Awwab yayi matukar

83 / 99