Advertisements
Chapter 82 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   82 / 99

243K to 246K   out of 295.8K words

sha kunu


Ummi ma daure fuska tayi ta ja plate din "idan ba kya so sai na dauke"


Da sauri Salame ta janye yawunta ya gama tsinkewa "barshi dai....kada kiyi zaton
zanci da dadin rai ne don dai kawai ba kyau wulakanta abinci ne. Kuma ga bakinku
ana kallonmu kada na kunyata uwar gayya Mairama matar Zayyan mai kudi"
Ummi gimtse dariya kawai tayi tana ganin yadda idanun Salame suke walainiya akan
plate din. "Bari na baki wuri kici"


Wani iri Salame taji bata so ta tashi amma bazata nuna ba "haka kika iya dama naki
bola wasu can bare sun fimu matsayi."


"In zauna kenan kike nufi?" Ummi tace a ranta kuwa dariya ce fal take dannewa.


Baki fal da taliya da nama Salame tace "In kin so tunda ai ba sai kin nunawa duniya
bama shiri ba"


A zuci Ummi tace "da baki girmeni ba da nace baki da kunya ma...kina so kina kaiwa
kasuwa"


A can kujerun karshe daga bari daya Yousuf ne da Awwab suke hira duk yawanci akan
bikinsu ne da shirin da su ka tanadar masa. Dinner din da zasuyi basa bukatar
taimakon iyaye da kudinsu suke son yi gasu duka babu wanda ya waye da harkar biki a
Nigeria.


"Ka bari idan mun koma gida muyi maganar da Bilal tunda shi dan gari ne" inji
Yousuf


"To shikenan. Yanzu dai shawara nake nema. Ina tunanin sayen mota amma kuma Alheran
da zan barwa idan na tafi aiki itama ba zama zata yi ba."


"Kawai ka barshi sai ta gama ta dawo nan din kunyi settling sai ka saya idan ba
haka ba wa zaku barwa? Tunda akwai motocin nan a gida kawai ka bari"


Arifah su ka gani ta nufosu da plates biyu Yousuf yayi saurin tashi ya karbo suka
koma wani table din yana yiwa Awwab gwalo wai ga inda ake kula da miji. Arifah
kunya taji ta kai masa duka a hannu ya rike hannun yana kallonta kamar su bar wurin
nan ya samu damar nuna mata soyayya.


"Ehemm da mutum a nan dai...albarkacin kanwata bari na baku wuri"


Tashi yayi ya fara tafiya Radhiya ta kira shi kamar tasan ita zai nema. Tambayarsa
tayi ina yake ya fada mata sai gata da plate guda daya da robar maltina.


"I am starving Hammana"


"Me yasa kike zama da yunwa" yace yana gyara mata kujera ta zauna.


"To ba kaine nake ta nema ba muci" tace tare da turo baki.
Bakin yake kallo yana lumshe idanu "kici abincin ni kuma ki bani bakin cin abinci
yunwarsa nake ji"


Kunya Radhiya taji har ta rasa inda zata sa kanta. Awwab kuwa yadda take yi ga
dimple dinta yana ta shigewa ya burgeshi sai da yasa hannunsa a wurin.


"I love this...." kanta ta sunkuyar yasa hannu ya rike kunnuwansa "sorry baby ina
takura miki ko? Lets eat amma kinsan bazan ci na bakinki ba ko" ya kashe mata ido.


Bata fuska tayi "Ewwwww ka zama kazami dai"


"Kinga laifina an aura min ke"


Hannuwa ta nade a kirji tana cika tana batsewa yana mata dariya. Kawu Zakari ta
hango ai kuwa ta daga masa hannu tana dariya za ta rama.


"Kawu Zakari tun dazu nake ta nemanka"


Fuskar Awwab ba shiri ta sauya ya bata rai kamar wanda aka yiwa duka. Yau dai ya ga
wannan Kawu Zakarin. Dan kyakkyawan bafillatani ya karaso ya mikawa Awwab hannu.
Radhiya sai sakin murmushi take sai da ta ga Awwab ya koma abin tausayi ta dena
jansa da hira.


"Me yasa baka zo Antyn tamu ba ne?"


"Tayi nauyi bana so ta wahala"


Ba kunya Awwab ya saki fuska "ashe kayi aure"


"Eh muna da yaro daya ma ga na biyu a hanya" Kawu Zakari yayi murmushi.


"Kai Madallah wannan abu yayi kyau Allah Ya bar kowa da masoyinsa" Awwab yayi
maganar farinciki ya mamaye fuskarsa abin dariya.


Radhiya tana dariya harda hawaye don yanayin relief din da ta gani akan fuskar
Awwab kamar wanda aka yiwa bushara.


Kawu Zakari yayi murmushi "mijinki yana da barwanci Radhiya. Ana kirana bari na
baku wuri"


Sai da ya tafi Awwab ya kalleta "to dai kinji yana da aure matarsa tana shirin
haihuwa ta biyu"
"Dadin abin nima ina da auren nan and God knows I love my husband"


Wani irin kallo yayi mata sai kuma kunyar abinda yayi ta kama shi ya cire hularsa
ya rufe fuska tana jin muryarsa sai ka rantse kuka zaiyi "did I just make a fool of
myself a gaban crush dinki Alheran?"


"Eh mana" itama ta yi kamar kukan zata yi.


Hular ya cire ya ajiye a gefe yana murmushi "laifinki ne Schatzi yanzu duk inda na
ganshi sai na tuna da wai likita kike so"


"Hamma Awwab" ta kira shi bata so ko kadan ya rinka tunanin akwai wani kafinsa ko
bayansa don babu.


Hannuwanta ya kamo ya rike "na'am"


"Kai na fara so kuma kai kadai zan so har abada in sha Allah" tace da wani irin
yanayi.


Zuciyar Awwab ta sake yi mata wani babban masaukin "Alheran ki sassautawa zuciyata
kada sonki yayi mata illa"


Bata sake magana ba ta nuna masa abincin. Spoon biyu ta sako amma yaki yarda sai
dai suci da daya duk da tana kunya ga iyayensu ko ina amma haka ya tilasta mata
suka ci babu magana sai kallo mai cike da ma'anoni.


DJ ya soma nasa aikin ana sako wakoki wuri ya kaure sai rawa wurin masu jini a
jika. Ana soma wakar Nura M Inuwa ta amarya 'yar amana jikin Radhiya ya fara mazari
tana hango 'yan mata musamman na Nijar 'yan uwansu ga Zahra can da Raji ana ta
nishadi ta mike tsaye.


"Ina zuwa?" Awwab yace jikinsa na bashi rawa zata yi.


Wurin rawar ta kalla da ka tayi masa alama.


Maltina ya cigaba da sha hankali kwance "zauna Schatzi please"


"Hamma manaa" ta langabe kai.


"Allah bazaki je kiyi rawa a wurin nan ba"


Idanu ta zaro "harda rantsuwa?"
"Kinga ya dace?"


Juyawa tayi ta hango Yousuf yana cewa Arifah wai zaiyi rawa tazo tayi masa video.


Kuka take shirin yi tace "Ka gani fa kowa yana yi"


"Mu ba kowa bane. Sunana Awwab sunki Alheran...don't tell me you expect me to seat
here and watch you dance a gaban mutane"


"To...to..." kasa karasawa tayi sai dai ya sani ran ta ya baci. Dauke kai yayi ta
gama kunkunin ta yana tunanin ma harda hawaye amma yaki bari ta tashi saboda indai
akan tayi rawa gaban mutane ne ya yarda tayi ta fushin ya rarrasheta daga baya.


Tana ji tana gani wakar ta kare aka sako wata Awwab ya tashi dama magrib ta gabato
"ki jirani a nan zanje na shigo da mota ciki na kiraki mu tafi"


Shan kunu ta sake yi harda kawar da kai gefe ya sunkuyo da kansa wurin kunnenta
"you still look sweet" ya yafi. Murmushi tayi duk da ba wai ta hakura bane.


To filin rawa ma Zayyana na hada ido da Ibrahim yana zaune da robar ruwa a hannunsa
ya sha kunu yana mata nuni da ta fita da hannu. Kafada ta noke ya kuma hade girar
sama da kasa dole ta fita tazo wucewa ta gefensa ta murguda masa baki.


"Naji dai, rawa ce ban yarda ba" taji yace yana murmushi.


Rahima dama bata shiga ba don bata iya ba tayi zamanta sai jakunkunan su Hibbah da
Zayyana da su ka bar mata. Karamar wayarta kirar samsung sabuwa mai torchlight ce a
hannunta tana game din snake jikinta ya bata kallonta ake yi ta baya. Juyawa tayi a
hankali ta ga Emzee yana murmushi.


Kujera yaja a kusa da ita ya juyata ya ware dogayen kafafunsa ya zauna ta yadda
gabansa ne ke fuskantar bayan kujerar ya dora hannuwa a samanta kansa akan
hannuwan.


"Kinsan saurin da na rinka yi kuwa da naje raka abokai na?"


"Meya faru?"


"Kawai waka na jiyo nace Allah Yasa kada Rahiman Muhammad tayi rawa if not tear gas
zan saki a wurin nan bayan na kai su Daada gida"


"Meye tear gas kuma?"
Yadda tayi tambayar kadai yasa shi shagala da kallonta kafin ya yi mata bayani.
Kanta a kasa take dariya da yace shi fa kishi gareshi "samarinki nawa ki kawo
numbers dinsu yanzu duk na kirasu na fada musu anyi miki miji"


"Goma ne ba yawa kasan ba wani farin jini gareni ba" Rahima tayi dariya saboda
kafin ta kai karshe ya kusa tuntsirewa daga kan kujera.


Gyara zamansa yayi yace yana bata fuska "Kasheni ki huta"


Shiru yaji tayi ya kira sunanta bata amsa ba. Tashi yayi ya dawo gabanta ya tsuguna
yana leken fuskarta. Hawaye ya gani suna gudu akan fuskar da yake matukar so yaji
hankalinsa ya tashi. Ya san iyakarsa ba don haka ba da ya rungumeta ya rarrasheta.


"Rahiman Muhammad?"


"Uhmm" tace da muryar kuka.


"Na bata miki rai ne?"


Gyada kai tayi "eh"


Zuciyarsa yaji tayi masa nauyi "Ya Salaam me nayi miki?"


"Cewa kayi fa na kasheka" ta fashe da kuka sosai.


"Oh my God...am sorry kinji wasa nake yi"


Soyayyar da suke yiwa juna ba ta wasa bace. Kowa na damuwa da damuwar dan uwansa.
Hankalinsa ya tashi da kukanta ita kuma bata kaunar wani abu ya gifta tsakaninsu
musamman mutuwa a yanzu da take jin ta samu farinciki irin wanda bata taba tunanin
akwai ba.


Irin matar da yake mafarkin samu mai shagwaba ya gani a tattare da Rahima saboda
yadda take yi da fuska da muryarta "To ka dena cewa in kasheka"


"Na dena...ban karawa"


Wayar hannunta ya karba ya saka numbarsa yayi dialling layinsa yana cewa "in chanja
miki waya?"


"A'a wannan ma sabuwa ce. Sai mun gama WAEC za'a bani wata" tace da murmushi tana
tuna abinda Ummi tace mata ranar da ta bata wannan din.
"Ajinki nawa? No shekarunki nawa kada ace ina koyawa yarinya soyayya fa" Emzee yace
yana dariya.


"Ajina hudu a primary kuma shekarata 13"


Kallonta yayi yasa yatsansa a baki ya ciza "da gaske? 13 amma kika iya kallon
soyayya? Wannan idan kika 20 na zama sorry"


Rahima sai dariya take irin wadda bai taba gani tayi ba hankalinta a kwance "kuma
babana yace kada na kula kowa sai nayi 25"


"Ba damuwa nima ba kulaki zanyi ba aurenki kawai zanyi sai ki karasa primary din a
gidana" ya amsa mata don ya fuskanci tsokanarsa kuma take yi.


Kalmar aure da ya sako ita ta kashe mata baki. Ya samu ta fada masa ainihin
shekarunta wato sha shida da ajinta a makaranta. A take yayi mata alkawarin yana
yin POP zai fadawa Daada a nema masa aurenta.


Ko da wasa Rahima bata kawo cewa Emzee bai san ko ita wacece ba. Dadin hira ya saka
shi mantawa da yi mata wannan tambayar tunda ta tabbatar masa da cewa tana nan a
gidan sai bayan bikin Radhiya.


**********


Wayar ta kalla tana ringing tasan Awwab ne ta kuma tura baki kamar yana wurin
sannan ta dauka "fito mu tafi" kawai yace.


Tafiyar kurame suka yi zuwa gidan ashe an fara komawa saboda iyayensu maza sun ce a
gida za'ayi magriba babu wanda za'a bari a wurin taron. Yasan Yousuf da Arifah zasu
tafi yau ma zaiyi rakiya shiyasa bai neme shi ba. Suna zuwa gida sai nishadinsa
yake fushinta kamar baya damunsa ya fito ya zagaya ya bude mata itama ta fito.
Hannunta ya kama kai tsaye ya wuce falon da su ka je jiya da ita.


Wayarsa ya dauko ya bude wakar yar amana ta youtube sannan ya kama mayafinta ya
cire ya ajiye akan kujera.


"Kinsan wahalar da nasha kafin na sami wakar nan a youtube kuwa? Ni bana gane me
suke cewa da kyar naji ance 'yar amana shine na nemo miki" idanunsa ya dora a kanta
yana ganin yadda tayi kyau sosai kamar wata 'yar tsana "baby ga 'yar amana ki tashi
muyi rawa"


Shan kunun ne ya kare ta soma dariya da Awwab yayi playing wakar.


"Wai da gaske nemo min kayi Chèri?"
"Anything to see your smile Schatzi" ya janyota jikinsa yana shafa gefen fuskarta.


Tsigar jikinta ke tashi ta soma rawar jiki ya rungumeta tsam a jikinsa.


"Calm down ba yau zan baki tsoron ba ai. Rawa zamuyi kuma bazan bari ki fita a
falon nan ba sai kinyi"


Sai yanzu take jin kunya sosai "Hammana na tuba kayi hakuri"


"Baby I want to see you dance...ba wai don na hanaki ba dazu wannan bazan taba
yarda dashi ba amma between us harda kafi rawa zamu rinka yi a gidanmu"


"To ai dai nan ba gidanmu bane kayi hakuri" tace ido wiki wiki tana nadamar yi masa
gardama don ya hanata rawa.


"Tunda ance sai anyi biki zaki tare kowa sai ya rufe ido kawai a barni duk inda
kike muna tare"


"Naji amma na fasa banda rawa...kunyarka nake ji"


Fuskar tausayi yayi "Inje gida inyi kuka?"


"A'a"


Kashe wakar yayi ya kunna wata ta cikin wayarsa da yake yawan kunnawa idan yana
tunaninta lokacin da suka yi fada mai suna You and I. Kidanta cikin taushi yake
tashi babu hayaniya ko kadan sai kalmomi masu tasiri a zuciya. Takalmanta ya fara
cire mata matsu tsini shima ya cire nasa sai safa. Wani irin riko Awwab yayi mata
ya duko da kansa ya hade goshinsu. Hannuwansa na kugunta nata a kafadarsa sun
zagaye wuyansa a hankali yace "hau kan kafafuna"


Runtse idanunta tayi ta dora kafa daya a hankali tana jira taji ko zaice tayi nauyi
ko ta cire sai taji yace "dora dayar"


A tsaye take amma akan kafafun mijinta sannu a hankali yake bin kalaman wakar yana
fada a saitin kunnenta yayin da yake tafiya a nutse suna takun rawa amma shi yake
yin duka motsin. A haka suka kwashe kusan minti hudu bai nuna gajiya ba yana rike
da ita suna musayar numfashi har wakar ta kare.


"Duk lokacin da kike son yin rawa baby zan tayaki, a gaban wasu ne kawai ban yarda
ba saboda ina kishinki. Da sonki na girma a zuciyata kina tunanin akwai ranar da
zanso bata miki rai da gangan?"


Girgiza kai tayi a hankali kalamansa na shigarta sosai kawai ta rungumeshi tana
masa kukan da ake kira na kissa batare da tasan ma'anarsa ba. Idan an barta bata
san dalilin hawayen nata ba idan ka cire tsantsar soyayyar Captain Muhammad Awwab
Mustapha.


Habarta ya dago suna kallon juna ta kasa tsayar da hawayenta.


"Kukan na meye?"


"I. Love. You Chèri"


Kamar jira yake ta fada ya soma kissing dinta sosai. Karatu suka ji alaman an kusa
kiran sallah ya dawo dasu duniyar da suke ya shafi gefen fuskarta "Da nasan hanaki
rawa ne zai sa naji da kanki kin fada min wadannan kalmomin da na dade da cewa ban
yarda da rawa ba"


Duka ta kaiwa kirjinsa ya saketa ta dauki takalminta ta saka sannan ta bude jakarta
ta fito da janbaki za ta kara sakawa.


"Ana kiran sallah za ki sake kwalliya?"


Kunya taji tayi saurin mayarwa sai da ya matsa mata tace "Jiya Adda Fauzy cewa tayi
wai an shanye min janbaki"


"Mata. Mata sai a barku...an fada min kuna zuwa ma ganin tafiyar amare washegarin
da aka kaisu ko" yace yana tsareta da ido.


Ba karamin rikicewa tayi ba kuwa don babu karya ko ita sun gama JS3 da akayi bikin
wata 'yar ajinsu kawayensu suka ce wai azo aje gulma. Da ita aka je din amma babu
abinda chanjin tafiyar kawar tasu ya sa mata a rai sai tunanin ko duka mijin yayi
mata. A lokacin ta yiwa kanta alkawarin idan tayi aure miji ya kawo mata wargi sai
dai su daku don ba kyalewa zata yi yaci zalinta ba. Murmushi ne ya subuce mata da
ta tuna lokacin da sharrin kuruciya.


Hannuwansa duka ya dora a ka "Na shiga uku kin taba zuwa kenan nima za'a zo mana"


Da sauri ta rinka cewa bata je ba yana cewa sai ta fada masa gaskiya. Nan aka fara
kiran sallah ya fita kamar ya tafi da ita. Ciki ta wuce ana ta layin alwala a waje
mazan ma suna nasu.


Gidan sai bayan isha ya dan daidaita inda Daada da su Daddy da iyalansu suka zauna
a falonsa suna hira. Mama ce tace ita dai sai ta bude gift din DK daga bangaren da
matan suke zaune yaran nasu suka soma murna suna jira a bude. Mami ce ta farke abin
suka ga takardu ne a ninke. Ta bude ta karanta tana wani irin murmushi ta mikawa
Mama. Ita kam hawaye ne ya zubo mata na farinciki Baba Hadir na kallonsu yace
"Zainab?" Da alamar tambaya yaji me ya faru.


Ibrahim ta bawa takardun yaje ya mika masa falon yayi shiru sai da ya karanta ya
kalli Zayyan.


"Yayi. Yawa" ya daure yace shima muryarsa na nuni da taba masa zuciya da abin yayi.


"Babu ruwanka da kyautar uba da da kuyi mana addu'a Allah Yasa yaci gajiyarsa."


Amin kowa yace ana mamakin Zayyan ya mallakawa Zayyan Hadir gidansa na Kano. Wannan
ya biyo bayan dogon nazarinsu shi da Ummi sun san cewa duka sunfi Hadir karfi yanzu
kuma Daddy yana da gidan kansa a Katsina.


Mama ta karbi na Zayyana ta bude a take su ka bude baki da mamaki.


"Zayyan meye haka ne?" Daddy yace yana kallon dankareren saitin gwal din da ya
mallakawa Zayyana. Dankunne, sarka hade da zube da manyan abin hannu guda biyu iri
daya biyu iri daya na kudi har dubu dari biyar.


"Kada ku shiga tsakanina da 'ya'yana ba ku na bawa ba"


Mami ta share kwalla tana jinjinawa zumunci irin na Zayyan da matarsa mai goya masa
baya.


Gift na karshe na Emzee mukullin mota ne sabuwa fil. Zayyan yace "waccan sai ta
zama ta Ibrahim shi kadai. Allah Yayi muku albarka 'ya'yana"


Saidai ayi ta cewa amin domin babu sauran godiya a tsakanin wadannan iyalin. Kaya
Zayyan ya chanja zuwa farare irin na Daddy da Baba Hadir ga matansu kayansu iri
daya suka zauna akan 3 sitter mazan a tsaye kowa a bayan matarsa aka dauki hoton
tarihi na iyali uku masoyan juna.

[11/2, 7:46 AM]🏽
]🏽 : 57. 💕

Washegari kafin a kira assalatu Emzee ya gama shirinsa. Ana kiran sallah yayi tare
da Daada a nan wurin masu gadi sannan yace zai tafi.


"Ba ka ci komai ba Zayyan, Umminka bazata ji dadi ba"


Agogonsa ya kalla "Daada so nake kafin 9 ina cikin NDA in sha Allah"


Addu'a da fatan alkhairi Zayyan ya yiwa dansa suna jiran karasowar Ibrahim ya
kaishi tasha saboda ba a gidan ya kwana ba. Kan wasu kujeru masu kyau daga gefen
kofa suka zauna suna hira irin ta uba da da gwanin ban sha'awa. Ummi ce ta fito
sanye da hijabi akan doguwar rigar baccinta da ta daura zani ta ciki da tray yana
ta turiri ta taho inda suke.


"Inata saurin kada ka tafi ba ka ci komai ba. Ungo kuma ban yarda ka rage ba"
Indomie ce guda biyu da daffafen kwai biyu sai kofin orange juice mai sanyi. Tasan
halinsa baya shan abu mai zafi da safe sai dare.


"Wayyo Ummi kinsan bana iya cin abinci da sassafe" yace yana kallon Daada yana
neman agaji.


Daure fuska tayi "baka isa ba kuwa, ina fitowa kitchen na hadu da Rahima a falo ina
jin ma ruwa ta fito sha idonta alamun bacci bai isheta ba amma ta karbi girkin tayi
kuma kace na mayar"


Karba yayi da sauri bai gama jin me take cewa ba ya soma ci yana murmushi.
Rankwashi ta sakar masa tana zaune akan kujerar da Zayyan ya tashi ya koma bayanta
ya tsaya. Kuma ya hana Emzee tashi ya

82 / 99