Advertisements
Chapter 85 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   85 / 99

252K to 255K   out of 295.8K words

taji Emzee ya kirata "me ya kaiki gidanta ba dazu kuka iso ba?"


"Rahima na biyo" ta amsa cikin kuka.


Kansa ne ya daure sosai "Rahima kuma?"


"Eh Emzee, don baka ga irin dukan da take yi mata ba"


"Me ya hadata da Rahima kuma? Ko wacce kike nufi na kasa fahimta" yace jikinsa a
sanyaye yana tsananta addu'a kada abinda yake zargin tana nufi ya tabbata.


"Rahima dai mana"


"Wadda nake gani tare da Zayyana?" Yace a tsorace.


"Eh" ta soma gajiya da tambayoyin ga serious maganar da ya kamata suyi.


Muryarsa taji kamar zaiyi kuka a raunane "Adda kina nufin Rahima 'yar Gwaggo Salame
ce?"


"Kanwar Halifa ba..."


Wayarsa ce ta subuce daga hannunsa batare da ya sani ba yaji kansa yayi mugun
sarawa. Hawaye sosai Muhammad Zayyan Tureta ya soma yi a garin yaya Rahima ta cuce
shi haka? Meyasa bata taba fada masa ba? Shiryawa suka yi ita da babarta ko kuwa
shima asirin aka yi masa tunda ta saba? Ko kuwa ta turota ne domin ta sake
bakantawa mahaifiyarsa saboda tsanar da tayi mata?


Duka wadannan tambayoyin basu rage daidai da cikin cokali na soyayyar da yake yiwa
Rahima ba sai dai wani irin zafi da yake ji a zuciyarsa domin ko sonta zai kashe
shi bazai taba auren irin Salame ba.

"Why Rahima???" Ya durkushe a kasa yana kuka kamar karamin yaro.

💕[11/2, 7:54 AM] 58💕

🏽: *KUYI HAKURI DA RASHIN YAWANSA BANA JINDADI NE YAU. NAGODE*




Idanun Salame sunyi zuru-zuru saboda asirinta da wadannan 'ya'yan na Mairama suka
sani. Daga nan kuma bata san yaya za ta kare ba. Radhiya kashe wayarta tayi bayan
ta gama magana da Emzee ta koma kallon Salame tana ta hawaye.


"Me Ummi tayi miki Gwaggo? Mata nawa ne suka taba son wani Allah bai kaddari
zamansu tare ba kuma suka hakura?" Matsowa ta rinka yi inda Salame ke tsaye gumi na
karyo mata. Wannan shi ake cewa kada Allah Ya kaimu ranar da za'a tsare mutum ana
masa tambaya akan laifukan da ya binne. Ya Allah Ka rabamu da hisabi irin wannan da
za'a tono komai da komai da muka taba aikatawa a rayuwarmu domin WALLAHI da matukar
wahala mu haye.


Kuka Radhiya take yi amma muryarta kowa naji a cikin gidan saboda karshe ranta ya
kai kuloluwar baci "Kinsan tsananin da yake tattare da makanta kuwa? A lokacin Ummi
ta rayu ba miji ga marayu sannan babu wadatar abincin da zata ci ta ciyar da
yaranta. Gwaggo kina kallo sai da ta sayar da duk wani abu da ta mallaka muka dena
karatu saboda neman magani." Kukanta ya kara tsanami ta matse kirjinta "sau
nawa....sau nawa ina rokon Ummi ta barni nayi bara ko talla saboda bama koshi da
abincin gidan Malamijo tana hanawa. Ba don Allah Ya dube mu su Innawuro sun zo ba
kina jin da watarana bazata amince ba ko don kada yunwa tayi mana lahani. Sai Allah
Ya sakawa Ummi Gwaggo" ta kare da fashewa da wani irin kuka. Rabonta da kuka sosai
irin haka tun ranar da Ummi tace kada ta amsa cewar tana son Awwab. Yau ga abinda
yafi rabuwa da Awwab kaji ko ka ga mutumin da baya kaunar mahaifiyarka kuma yake
neman ganin bayanta.


Jiki na rawa ga tsoro amma Salame bata so ta nunawa Radhiya sai cewa tayi "idan kin
gama sharrin sai ki fita ki tafi in kuma zaki rama mata ne to na fara jin didif a
jikina sai na san cewa kin haifu"


Kallon da Radhiya tayi mata da jajayen idanunta kallo ne mai firgitarwa da nuna
kwarewa wurin fitina da sanin yadda zaka rama abu cikin ruwan sanyi.


"Ummi tayi mana tarbiya wadda ni ko Emzee bazamu taba watsa mata kasa a ido ba in
sha Allah. Gwaggo Salame ke ba sa'ar yi na bace domin kin girmi mahaifiyata
ma...amma.... zan hadaki da wanda yafi cancanta ya hukunta ki" tana kaiwa nan ta
daga waya ta soma kiran mahaifinta Zayyan Tureta.


Duk wannan abu da suke yi Alh Indararo da Maman Danmama suna kofar dakin sai dai su
basu kula da tsayuwarsu ba sannan shima yana so ya gama gane kan zancen kafin ya
afkawa Salame.


A can hostel dinsu kuma Emzee bayan ya gama nasa kukan shima babu wanda yake so da
burin saukewa nauyin zuciyarsa sai mahaifinsa. A take shima ya soma kiran wayar
Zayyan din.


**********


Yana zaune a dakin Jume kan tabarma yana cin abincin da ta dafa masa da kanta suna
hira. Abin mamakin da ya gani bai wuce sabon fenti ba ciki da wajen gidan ana ta
gyare gyare wanda yawanci jikokin gidan samari keyi.


"Wai ni wannan gyaran Jume waye zaiyi amarya ne?" Zayyan ya tambayeta yana dariya.


" 'Yan uwanka ne suke son yin gyara saboda bikin Alheran mana. Ita ce fa jikar
farko ta bangaren namiji a gidan nan ka ga kuwa mune da biki"


Dadi yaji sosai "Allah Ya saka da alkhairi Jume nagode"


Dan harararsa tayi "meye haka kamar wanda aka yiwa wani abu. Kai dai ka gama ci ga
'ya kayayyaki can da suka hadawa amarya."


"Harda wata wahala kuma?"


"Ashe ba 'yarsu bace indai abinda suka yi sunansa wahala"


Saurin bata hakuri yayi ya gama cin abincin sannan ya mika mata wata leda mai
kauri. Budewa yayi ya dauko kullin kudi guda uku kowanne dubu dari biyar biyar yace
gashi nan ta bawa yayunsa Badaru, Rayyan da Maikudi. Sannan ya dauko kananun kullin
su kuma dubu dari bibbiyu ne yace na matan ne su ma su uku. Wannan duk cikin kudin
da aka bashi ne wanda yake ganin idan bai nemi lada ya raya zumunci dasu ba yayi
asara kuma bai godewa Allah da ya dawo dashi gida lafiya ba.


Jume sai kwalla tasa zani ta goge "Zayyanu da wane bakin zanyi maka godiya kuma in
cigaba da rokon yafiya akan zaluncin da nayi maka?"


Baya son tana yi masa haka domin uwa ya dauketa "kisa min albarka kawai Jume abar
maganar. In Allah Ya yarda ke kuma hajjin wannan shekarar zamu je dake da Mairama"


"Ayya...ayya Zayyanu...Allah Ya jikan Innarka da Malam. Na cutar da baiwar Allahn
nan ashe nice da moriyar danta" tace tana kuka sosai. Cikin wanda ta ya fara bata
na dubu dari biyar din ta dauko ta mika masa kuma tana sane saboda ta gano Maikudi
ya taho dakin amma ya tsaya daga waje saboda ya hango Zayyan.


"Wannan ka rike kayanka Zayyanu don wallahi ko kwabo bazan baiwa Maikudi ba."
Da sauri Zayyan yake dubanta "haba Jume me yayi zafi haka?"


"Komai ma. Zayyanu komai da komai yayi zafi daga lokacin da Maikudi ya danne
dukiyar marayu sannan saboda bakin hali da tsantsar mugunta ya aika da sakon
mutuwarsu har Nijar ya dakile masu tallafa musu"


Maikudi yana daga waje yaji kamar ya rafka ihu. Shigowa yayi ya rakube a gefe ya
durkusa amma ya kasa cewa Jume da kanin nasa komai. Ita kuwa kallon banza take masa
saboda irin abubuwan da yayi da irin yadda itama ya rainata.


"Saboda kaji ana zancen kudi shine ka taho ko? Ka gani..." tace tana dorawa Zayyan
kudinsa "to na bashi kayansa ban kuma lamunce ya baka ba ko da a bayan idona ba.
Yau ba don dawowar abokansa ba ina da yakinin haka za ka yi ta gina kanka da
dukiyarsu batare da nadama ba"


Zayyan kama bakinsa yayi tunda ita da danta sunfi kusa. Ba don zumunci domin Allah
ake yinsa ba ko inuwar Maikudi bazai sake kallo ba. Mutumin da baiji tausayin matar
da akace mijinta ya rasu ba ga danyen jego. Mutumin da yayi amfani da emotional
sentiment din Mairama yasa ta hakura da takardun gidan mijinta akan wasikar da ya
bar mata kafin ya tafi. Zumunci akwai dadi akwai wahala sai mutum ya daure ya kai
zuciyarsa nesa.


Wayarsa yaji tana vibrating ya dauko sai lokacin ya kula da missed call din Radhiya
da na Emzee. Tashi yayi ya saka kudinsa a aljihu yace da Jume yana zuwa. Wurin
dakin Innarsa yaje ya tsaya zai kirasu Maikudi ya biyo shi da sauri. Dukar da kai
yayi saboda mugun kwarjinin da Zayyan yayi masa.


"Yaya akayi?" Zayyan yace da dakakkiyar murya.


Kamar wanda aka tsuma a cikin ruwa don kunya Maikudi ya dago kai yana hada hannuwa
"Zayyan ka duba girman zumunci..."


"Wannan ka biyo kenan Maikudi..." ya zura hannu ya dauko kudin ya mika masa "gashi
na riga nayi niyya dama"


Ja baya Maikudi yayi "ba kudinka nake so ba Zayyan. Nasan akwai kunya in kalli
idanunka ko na iyalinka in roki gafara amma ku taimaka don Allah. Kawu Aminu yace
dama akwai ranar da zanji kunya gashi ko shekara baiyi a kasa ba lokacin yazo"


Zayyan yaji wayarsa ta sake vibrating kallo daya ya yiwa Maikudi yace " 'ya'yana
suna bukata ta zamuyi magana anjima"


Bai jira cewarsa ba ya daga wayar gabansa ya fadi saboda jin muryar Radhiya tana
kuka.
"Daada" tace lokaci guda tana kara sautin kukanta.


Faduwar gaba yaji sosai da sauri ya rinka watsa mata tambayoyi "Alheran menene? Ina
Umminku? Me ya faru?"


Salame na jin ta ce Daada hankalinta ya sake tashi don Zayyan ne mutum na karshe da
zata so yasan wannan abu. Jikinta ya hau bari musamman da idanunta su ka sauka akan
Alhaji Indararo da Maman Danmama. Radhiya ko a jikinta sai ma kara kwantar da murya
da tayi.


"Ummi tana gidan Malamijo"


"Ke kuma kina ina?"


"Gidan Gwaggo Salame" ta fada tare da kara sautin kukan kamar lokacin ma dukanta
ake yi.


Cikin fada yace "Can nace kije ko nan mijinki ya tura ki?"


"Kiji tsoron Allah Radhiya me nayi miki kike kara kuka haka" Salame tayi maganar
tana komawa kalar tausayi sosai.


Shi kuwa Zayyan kukan 'yarsa har kokon ransa yake jinsa. Lallabata ya koma yi don
yaji me ya faru "Alheran dena kukan ko waye ya taba min ke ba kyalewa zanyi ba"


Ba kunya ta sakarwa Salame murmushi sannan tasa speaker ta kure volume din wayar
"Daada dukana tayi da wayar rediyo fatar bayana ta cire..."


"Laaaaahhhh kuji min yarinya...ba Rahima nazo duka ba kika tare? Ni ina ruwana da
'ya'yan gidanku me zai kaini dukanku...." idanunta har sun fara tara kwalla saboda
wani sauyin numfashi da take iya jiyowa na Zayyan ransa ya soma baci.


"Wai don na gane ashe tana sonka kuma ita ta makanta Ummi don ta auri Alha...."


Salame kasa hakuri tayi tasa hannu ta toshe bakin Radhiya saboda yadda Zayyan yace
"ME???" da karfi.


Alh Indararo yana jin haka shi kuma ya wawurota ji kake tas-tas ya tsittsinka mata
mari. Zayyan da ya zata tasa 'yar ake duka a kidime ya kashe wayar ya kira Mairama.


Baiwar Allah bata san me ake yi ba tana tare dasu Innawuro ana hira ta dauka.
Abinda bata taba ji ba wato Zayyan ya daga mata murya taji a yau. Zai iya hakuri da
komai banda taba masa 'ya'ya ba kuma wai don bashi da kara ba sai don yasan wacece
Salame a da lokacin da bata ji kunyar kai masa kokon barar soyayya ba alhali yana
neman kanwarta. Abu na biyu kuwa bai wuce shekarun da ya kwasa cike da tsananin
kewar iyalinsa. Yanzu da ya sami dama ta biyu ba zaiyi wasa da ita yana ji yana
gani 'ya'yansa suna zubar da hawaye ba. Bashi da uwa ba uba sai mata sai su. Baya
fata amma ya sani ana chanja mata amma jininsa bazai iya taba chanja shi ba.


"Kije gidan yayarki Salame ki dauko min Alheran sannan gobe zanzo na dauketa mu
koma gida"


Tashi tayi ta matsa daga cikin mutane hankali a tashe "Sojana ban fahimceka ba"


"Nima ban fahimta ba Fillo.."yace cike da damuwa "Alheran ta kirani yanzu wai
Salame tana dukanta da wayar rediyo...."


Ko karshen zancen bata tsaya ji ba ta koma ciki da sauri danunta sun kada sunyi ja.
Nanatawa take yi yau ko ita ko Salame...ta gaji da wannan halayya da take nuna
mata. Rahima ma a yanzu ba bari zata yi ta tabata ba bare kuma Radhiyanta. Wani
dauke kai da take yi akanta ba shine yake nufin bata son abarta ba. Bata hada son
'ya'yanta da komai sai dai sanin rayuwa da kyaun hali yasa bata sangartasu da
soyayya ba.


"Mairama ina zaki haka lokaci guda kin fita hayyacinki" cewar Yadikko tana tasowa
ta riketa.


"Gidan Salame zani Yadikko. Kuzo muje kuyi shaida ayi min tsakani da ita domin na
rantse zan nuna mata duk abinda nake yi ba wai rashin sanin ciwon kai bane. Idan
zumunci dani ne bata so a yau ni da kaina zansa wuka na datse shi uban kowa ma ya
huta"


Mama cire DK tayi da take shayarwa ta mikawa Laila ta dafa Mairama "kiyi hakuri ki
fadi me tayi miki"


Kowa ya ga Mairama yasan tana cikin bacin rai dama ga ta da zuciya. Hakurinta da
yawan kau da kai shine yake sawa a ga kamar bata da fushi.

"Babansu Karami ya kirani yanzu wai Salame tana dukan wannan yarinya da wayar
rediyo"


"Me kika ce?" Malamijo yace da sauri yana nufosu. Hayaniya yake ji har soro shine
ya fito.


Cikin kankanin lokaci Malamijo, Nene Marka, Yadikko da Hajjo su ka hadu da Mairama
zasu tafi gidan Salame kowa ya kasa gane me yake faruwa. Mairama ta kira Radhiya
amma tana dauka kuka kawai ta rinka yi bata ce komai ba. Zasu fita ta ga Mama
Zainab a tsaye bata da niyar binsu.


"Yanzun nan in fada miki ana dukan 'yarki amma ki tsaya a nan Zainab" cewar
Mairama.
Gani tayi abin ya shafi danginsu bai dace ta tura kai ba "Kuje ku dawo Ummin Awwab"


Fushin nata kan Mama ya nemi komawa tana ta kumburi tace "kada kije din...kuma sai
na fadawa Mami" fuuuu tayi gaba tana sababin da babu wanda ya santa dashi.


Nene Marka tace "maza Zainabu dauko mayafinki wannan 'yar uwar taki bata iya fushi
ba ko kadan"


Duk da babu nisa motar Mairama suka shiga sabo mutane dreba ya ja su.


**********


Bayan marin da Alh Indararo ya rinka saukewa Salame zuciyarsa a sama har yana haki
ya nuna ta yatsa "naji komai kuma nasan komai. Sai yau na fahimci yaya akayi na
aureki Salame"


Radhiya gefe ta koma abinta bayanta na zugi tana jiran isowar su Ummi saboda Daada
yace ta jira gasu nan zuwa.


Kuka yaki zuwar wa Salame sai kumatunta duka biyun da ta rike zugi da radadi na
shigarta.


Cigaba yayi da fadansa sa'arsu daya babu yara a gidan kamar anyi shara. Dama na
Salame ne masu zama su ma yau Radhiya tayi musu jan ido babu ko daya.


"Lallai biri yayi kama da mutum. Salame ko ina shan giya me zai kaini aurenki bayan
tun kina gidan Idris na sanki. Sau nawa nake bawa matana labarin yadda yake zuwa
wurina neman bashi saboda ya auri hatsabibiyar mata mai bani-bani wadda ta raina
shi. Kinsan talaka ne amma kike amfani da son da yake miki kika tatike shi. Ranar
da zaki haifi Rahima ma idan baki sani ba ni na bashi aron mota aka kaiki asibiti.
Sannan ragon suna da kika matsanta masa shima bashi ya nema a wurina sai da ya
shekara uku ya iya hada min kudin ragon."


"Alhaji me ya kawo wannan tone-tonen? Kada kace ka yarda da zancen yarinyar..."


Mugun kallon da ya jefa mata yasa ta koma tayi lakwas "Salame kyan dan maciji
asirinki ya tonu" ya nuna Maman Danmama "ga uwargidana nan ki tambayeta ko da
Mairama ta makance nan nazo na fada musu matar da zan aura ta sami matsalar ido
kuma tana da marayu. Idan ta tare duk wadda ta cutar da ita a bakin aurenta. Amma
duk wannan abu lokaci guda naji zan iya rabuwa da kowa a kanki Salame. To
albishirinki aikin boka yayi ci da kyau domin ke da gidan nan sai dai kiyi min
takaba ko a fitar da gawarki. Kinzo kenan 'yar kundun uba"


Wayar da ta gama dukan su Rahima da ita ya dauko daga kan kujera ya daga kawai ya
shiga lafta mata. Saukar farko Salame ta zabura za tayi rawar 'yan bori. Ashe ba
dadi ta sa matar da ya saki karshe sai da yayi mata dukan kawo wuka kawai saboda ta
dakar mata 'ya. Dukan da yake mata ya soma firgita Radhiya da uwargidansa duk
haushinta da suke ji Radhiya sai ta sami kanta da janyo Salame bayanta yayin da
Maman Danmama ta rike hannun Alhajin yana ta kumfar baka yana masifa kamar ya ari
baki.


Numfarfashi Salame take saukewa su ka ji sallama daga waje wadda mai yinta ko ba'a
fada ba yana cikin bacin rai ne da fushi. Ba'a dena sallamar ba cikin daga murya
tare da dukan kofar gidan a fusace.


Alh Indararo shima cikin bacin rai ya fita yaci karo da Idris rungume da 'yarsa
Rahima idonta daya ya kumbura ga shatin waya yayi bororo a rabin fuskarta har wurin
idon da samansa.


Mutum mai hakuri ba sawa ba fitarwa irin Baffan Rahima yau shima an kure shi karshe
ko gaisawa basuyi ba ya soma fada "Billahillazi huwar Rahmanu Alhaji ka gargadi
matarka idan ba haka ba zan tube rigar mutumci in shiga har cikin gidan nan inci
mutumcinta. Dubi wannan diban albarka da ta yiwa Rahima. Yau yarinyar nan ko zaman
kishi suka yi da uwarta a yanzu da babu aure a tsakaninmu bata cancanci wannan abu
ba bare kuma 'yar cikinta."


Saukowa Alh Indararo yayi saboda yadda yarinyar ta bashi tausayi "dakata muyi
magana Baban Rahima"


"Wace irin dakatawa zanyi? Kullum da fargaba da komai ni ko Iya muke matsanta mata
tazo gidannan saboda uwa uwace komai lalacewarta. Babu ranar da Rahima bazata dawo
min gida da hawaye ba amma yau ka duba ka gani don Allah. Dubi yadda fuskarta ta
koma daga zuwanta"


Motar su Mairama ce ta tsaya suka firfito gabadayansu. Kafin su karaso Rahima ta
kwasa a guje ta rungumeta tana kuka mai ban tausayi. Hajjo ce ta fara ganin fuskar
ta dago kanta da sauri. Mairama ma ta gani a tsorace tace "meye wannan Rahima?"


"Umma ce ta dakeni"


Mairama cije lebenta kawai tayi ta damki hannun Rahima ko Alh Indararo da Baffan
Rahiman bata tsaya yiwa kwakkwaran kallo ba ta shige cikin gidan tana cewa "SALAME
kina ina?".



************************************


Cikin Salame kullewa yayi da ta ji muryar Mairama. Yau ko ba'a fada ba ta sani cewa
kashinta ya bushe ta kure kanwarta ta. Radhiya kuwa da sauri ta iso bakin kofar
dakin idanu sunyi ja sun kankance.


Ummi na ganinta a haka taji hankalinta ya sake tashi yau 'yar kunyar ma babu ta
janyota jikinta za ta dubata ta saki siririyar kara saboda bayanta da aka taba.
Ai kuwa da sauri Ummi ta zaro idanu ta juya Radhiyan ta dage rigarta. Ga farar fata
ga gyaran da take sha jiki yayi mugun laushi shiyasa wayar tayi mata wani dogon
layi da yake tsartuwar jini daga tsakiya. Ruwan bala'i da masifa yau sun tarar wa
Mairama ta kama hannun Radhiya ta hada da ba Rahima.


"Kama kanwarki kuje Lucas yana mota ya kaiku MHC"


Mama kallo daya ta yi a kofar dakin ta hango Salame kamar kaya jibge a kasa tayi
saurin jan hannun Rahima saboda duk lalacewa baza su so ta ga mahaifiyarta a wannan
halin ba. Da taimakonta suka kama Rahiman saboda ta fi Radhiya jin jiki suka fice.
Itama bata son ayi a gabanta gara yau dai suyita ta kare a gaban mahaifinsu.


Dama jiran fitarsu Ummi take yi tausayin Rahima ya dakatar da ita. Dakin ta banka
kai ciki a fusace Salame ta mike da kyar.


Cike da bacin rai da masifa Ummi

85 / 99