Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
na bayanshi yana dariya a nan din ma sai sun gwada rashin mutumci irin wanda
yayi musu sanadin fadowa wannan gida.
Maza ukun da hira suna ganin abinda ake yi masa suka taso suna nade hannuwan riga
"idan kana da matsala a dakin nan ka nemi daya daga cikinmu amma ba'a taba 3810"
"Ku kiyaye Boss dina baya son raini fa"
Dayan da suka shigo tare yace musu yana zaro idanu.
"Alamu sun nuna kun shigo prison da zafin kai, sai dai ko zaku gwada hali kada ku
taba shiga harkar OUR ZAYYAN. Muna jurewa komai banda bacin ransa"
Basu daddara ba dayan ya daga hannu zai mari Lt Zayyan Muhammad Tureta mai lambar
prison 3810 wadannan maza uku suka far musu fada ya kaure a tsakaninsu. Yana nan
zaune inda yake har gandirobobi suka shigo rabasu.
🏽
[11/2, 6:51 AM] 🏽
: 32.💕
TUNA BAYA
"Daga hannuwanka ka dora a bayan kanka" akace daga bayansa da gurbataccen turanci.
Ruwa, iska hade da hayakin wutar da take ci sakamakon tashin bom din wurin yasa
ganinsa yayi rauni amma duk da haka ya fahimci ba mutum daya bane a wurin. A kalla
sun kai su takwas ko sama da haka kowannensu yana nuna shi da bindiga. Hankalinsa
ne yayi mummunan tashi da ya tuna cewa muddin aka harbe shi dole zai daga kafarsa
daga kan wannan land mine din. Yana dagawa kuwa banda wadannan mutanen harda Major
da Hadir a cikin wadanda zasu iya rasa rayukansu. Dole ne ya kara musu lokacin yin
nisa da wurin kafin mine din ya tashi.
"Kuyi hakuri ko me kuke bukata daga gareni zanyi muku amma kada ku harbe ni. Akwai
landmine a kasan kafata"
Dariya suka kwashe da ita tamkar basu fahimci nasa turancin ba. Bai hakura ba ya
cigaba da cewa su taimaki kansu suyi nesa dashi kada su mutu tare don bai san
karfin abinda ya taka ba.
"Get down" wani gabjeje yace masa fuskarsa babu digon imani a cikinta.
Zayyan ya sake cewa akwai bomb a kasan kafarsa. Mutumin a fusace ya matso gabansa
ya daga kasan bindigarsa wurin fadin ya maka masa a gefen fuska. Wani mahaukacin
zafi, radadi da zugi yaji a take turame biyu cikin hakoransa suka fita ya furzar
dasu tare da jini. Duk da haka kafarsa yake kokarin dannewa a kasan kada ya tayar
da bomb din 'yan uwansa basuyi nisa ba. Idanunsa suna kan hanyar da Hadir ya bi.
Mutumin ya bi wurin da kallo ya yiwa wani nuni da ka. Sai gashi a gaban idon Zayyan
mutumin ya cizge irin abin kasan mulmullalan bomb dinnan ya dage ya jefa shi hanyar
da suka bi din. Wannan shine bomb din da Major da Hadir suka ji wanda karfinsa yayi
sanadiyar fadawarsu kwazazzabon da firgici yasa Hadir bai kula dashi ba.
Mutum biyu suka zo suka damki Zayyan wanda ya saki ihu sosai sakamakon tashin bomb
din yana mai cike da tsoron ko ya shafe su. Zuciya ce ta debe shi ya tuna irin
ta'asar da suka yiwa gabadaya rundunar da suka taho wurin da niyyar taimako. Mutane
biyun ya sakalawa hannuwansa a wuyansu ya daga kafar da niyar dukansu su mutu tare
akan sai sun tafi ya mutu shi kadai. Ko babu komai ya sadaukar da rayuwarsa ya rage
mugun iri. Runtse ido yayi yana jiran yaji ya tashi sai dai maimakon kararsa sai
sautin dariyar muguntarsu yaji. Wani cikinsu ne ya taho daga shi sai dogon wando da
singeletin da ba lallai a gane ainihin kalarta saboda mugun datti yazo ya durkusa a
gabansa ya ciro abin da suka binne a wurare daban daban masu yawa domin danawa
mutane tarko. Duk wanda yayi tunanin landmine ne yaki dauke kafarsa ya zama nama a
wurinsu inda zasu fito daga mabuyarsu su kama shi su azabtar domin neman bayanai.
Zayyan yana ganin haka yayi kukan kura ya kwace jikinsa daga wadancan biyun ya fada
kan wancan. Abinda yaje dauka yayi sa'ar samu wato bindigar da take aljihun
wandonsa ta baya. Baiyi wata wata ba ya saita kansa ya sakar masa harsashi.
Wadancan suna daga inda suke suna kokarin harbe shi da bindiga yayin da ogan nasu
yayi wani irin ihu saboda kaninsa ne Zayyan ya kashe ya sake saita mutane biyun da
suka fi kusa dashi suma ya harbesu yana daga durkushe. A take wurin ya hade sai
sautin harbi kake ji amma karfin ruwa ya bawa Zayyan damar kubcewa. Ya sadakar dama
yau mutuwarsa tazo amma bai hakura da harbin ba sai da ya sake kara mutum biyu
sannan aka same shi a hannun da yake harbin dashi. Dole ya saki bindigar kafin ya
farga wannan ogan nasu ya kafta masa bindiga a tsakar kansa ya fadi a wurin
sumamme.
Wani irin abu yake ji kamar ruwa yana zuba a fuskarsa amma kuma a shake yake. Yayi
ta yunkurin bude idanu amma ya kasa sai wani irin abu kamar an like idanun suna ta
radadi. Duk wani tunaninsa ya tsaya cak kwakwalwar ta cushe. Sai bayan wani lokaci
yana cikin wannan yanayi na shakewa da ruwa ya soma turjiya ya gane kafafunsa daure
suke a jikin wani abu sannan hannuwansa ma an daure su ta baya. Hannun da aka harba
dama tamkar ba a jikinsa yake ba saboda kumburi da ciwo. A kokarinsa na mikewa
tsaye ne ya gane cewa akan kujera yake a zaune. An daure kafafunsa da jikin kujerar
hagu da dama. Hannuwansa kuma suna daure ne ta baya harde da juna. A takaice ma
tsumma ne aka dora akan fuskarsa ana kwarara masa ruwa wani ya rike kan ta bayansa.
Sai da suka tabbatar ya azabtu iyakar azabtuwa aka cire tsumman. Tari ya rinka yi a
wahale ruwa na fita ta baki ta hanci. Idanunsa sun juye ya kasa tantance a ina yake
ga rashin wadatar haske a dakin.
Hargagin mutane yaji aka bude kofar hasken rana kwal ta mamaye dakin. Wasu mutane
ne suka shigo kai tsaye wurinsa suka nufa. Bayan sunyi magana da yare ne suka koma
turanci aka tambaye shi mutum nawa ne a sansaninsu da sauran. Sojoji nawa ne
Nigeria ta turo domin kwantar da tarzoma kuma a ina da ina suka kafa sansani. Idan
ma zai iya magana bazai fada musu ba saboda duka jikinsa hatta bakinsa da hakora
suka cire jiya da suka dauko shi ciwo suke yi. Dukansa suka fara yi saboda yaki yin
magana sai yaji muryar wani shima a wahale yake yace suyi hakuri ya sami lafiya sai
ya basu amsar da suke nema.
Marinsa wani yayi suka ce yayi musu shiru. Sai da suka sake yiwa Zayyan ligi-ligi
sannan suka yasar dashi a kasa suka tafi. Mutanen wasu tsageru ne cikin 'yan tada
kayar baya da gwambatin kasar ke nema ruwa a jallo. Su kuma suna son dakile
taimakon da kasarsu take samu na jajirtattun sojoji musamman daga kasarmu mai
albarka Nigeria. Shiyasa suke yi musu dabaru suna kashesu suna kama na kamawa domin
neman bayanai. Har yanzu dai babu nasara domin sojojin sun dauki amanar kasarsu
jini da tsoka. Idan suka kasa samun abinda suke so sai su kashe mutum.
Bayan fitarsu dayan mutumin da yake dakin ya janyo shi da kyar zuwa wani dan lungu.
Tsohuwar katifa ce a wurin da 'yan tarkacen asibiti. Kwantar da Zayyan yayi akan
katifar ya farke hannun rigarsa da ya kumbura. Ga dukkan alamu bullet din da ya
same shi yana ciki ga uban kumburi fitar dashi zaiyi wahala. Shi kanshi mutumin
wahala ta zuge shi duk ya rame.
Wata siririyar wuka ya dauko ya kunna lighter da take ajiye a gefe ya rinka saka
tsinin wukar a cikin wutar na dan lokaci ya dauki zafi sannan ya mika masa wani
tsohon yagwalgwalallen filo ko riga babu.
"Put it in your mouth"
"Wwwwhat?" Ya fada idanunsa akan filon da babu kyaun gani. Bai rufe bakinsa ba
mutumin nan ya tura masa filon lokaci guda kuma ya danna wukar cikin hannunsa
saitin inda yake iya ganin alamun bullet din ya shiga. A maimakon kara Zayyan cizo
ya kaiwa filon har hakoransa suka kusa hadewa ta ciki don azaba. Juyi biyu mutumin
yayi da wukar sai ga bullet ya fado kasa.
Zayyan yayi gumi ba kadan ba idanunsa sunyi jazur sai jijiyoyin kansa da suka mike.
Kwanciya yayi mutumin yana masa sannu. Babu bakin amsa sai kai yake gyadawa. Daga
wannan lokacin bai kara sanin me ya faru ba sai farkawa yayi yana jin kamar ana
dukan wani ga dare. A take ya wartsake ganin mutumin da ya taimaka masa ne ake yiwa
dukan kawo wuka. Mantawa yayi da ciwon jikinsa ya tashi a fusace yayi kansu. Ransa
ya kara baci ne da ya fahimci dalilin taimakonsa da mutumin yayi ne ake masa haka.
Dukan ya koma su biyo ake yiwa amma Zayyan bai hakura ya janye jikinsa ba. Sai da
suka gaji don kansu suka fita aka barsu a kasa kowanne jiki yayi laushi.
"Allah Ya isanmu tunda kunfi karfinmu....ashhh bakina" hannu ya dora daga gefen
kumatunsa bangaren da hakoran suka zuba. Wahalalliyar dariya wancan mutumin yayi
daga inda yake. Zayyan ya dinke fuska don ya jigata sosai yace "baka daku bane kake
dariya, ni yanzu suka sake dawowa suman karya zanyi"
Dagowa mutumin yayi da kyar Zayyan sai ya koma turanci "are you okay?"
Dariya mutumin ya sake yi sai abin ya dan bashi tsoro ya ja jikinshi kadan ba dai
mai matsalar kwakwalwa bane ko.
"Duk wannan dukan da muka sha ka sani dariyar dole" kallon mamaki Zayyan yayi masa
yana jingina bayansa da bango ya dora da cewa "ina kallonka nayi tunanin kaima
bahaushe ne"
"Kaima dan Nigeria ne?"
"Soja kamarka" yace da muryarsa da take a kausashe kamar wanda ya tashi daga bacci
ko aka shake masa wuya.
Zama Zayyan ya gyara yana kallon mutumin sosai. Wannan zai girmewa Major Mustapha
sai dai rashin khaki a jikinsa yasa a haka bazai iya gane mukaminsa ba.
"Lt Zayyan Muhammad Tureta, Giginya Army Barrack Sokoto"
"Colonel Nasiruddeen Aliyu, Bukavu Army Barrack Kano"
Soja ya ga ubangidansa, da ciwon hannun nasa haka Zayyan ya yunkura ya mike yana
dafa bango ya dan kame jikinsa yayi masa salute.
Kai Col. Nasiruddeen ya kada yana dariya "baka daku bane shiyasa kake iya tashi, ni
yanzu suka dawo cewa zanyi mace ne ni da kayan maza"
Ga wahala ga ciwo Zayyan sai da ya bushe da dariya. Sun dan zauna shiru kafin Col.
Nasiruddeen ya soma bashi labarin dalilin zuwansa wurin.
Col. Nasiruddeen Aliyu mutumin karamar hukumar Wase ne ta jihar Plateau. Likita ne
na sojoji wanda yake kwararren consultant a asibitin sojoji na Bukavu barrack a
Kano inda yake base dinsa. Rabon wannan wahalar da kansa ya nemi a sanya sunansa
cikin masu tahowa Liberia saboda burinsa na taimakawa sojojinsu. Sai aka shi turo a
matsayin Cheif Medical Officer tare da wasu mutum uku su ma duka sojojin ne kuma
likitoci. A lissafinsa yayi a kalla wata biyar tare da mutanen nan. Watarana sun
sami rahoton rigima tsakanin sojojin kasar da abokan rikicin nasu inda mutane da
yawa suka jikkata ana bukatar likitoci domin taimakon gaggawa. Shi da sauran da
suke sansani guda inda yake a matsayin wurin kula da masu rauni suka dunguma da
kayan kula da marasa lafiya da magunguna. Rabin tafiyar suka yi kamar yadda aka
shammaci su Zayyan su ma haka aka yi musu. Bayan musayar harsashi an kashe mutum
biyu cikinsu sauran kuma aka kadasu aka tafi dasu. Akan idanunsa saboda sun san
shine babba a cikinsu aka rinka kashe na kasa dashi don sunki bada bayanan da ake
bukata. Akwai takardu a jikinsa na bayanin sojoji masu tahowa, ranar isowarsu da ma
adadin makamai, abinci da magunguna da zasu taho dashi. Tsoron kada a cutar dasu ya
sanya ya fakaice su ya dunkule takardar ya cusa a bakinsa ya hadiya farat daya.
Stapler din da take jiki wadda aka mannesu tare ita ce a lokacin hadiyar yana ji
tana kartar masa wuya har ta wuce. Bai fahimci mugun rauni tayi masa ba sai da aka
zo yi masa tambaya yana bude baki sai jini ya rinka zubowa ga uban radadi daga
cikin wuyan nasa. Ya sha wahala sosai karshe muryarsa ta koma haka bayan wani
lokaci. Babu ko mutum daya saura cikin abokan tafiyarsa duka an azabtar dasu an
kashe. Shi kuma sun mayar dashi likitansu. Abubuwan da ya gani da idanunsa mutanen
suna yiwa bayin Allah ba kadan bane, jiran amfaninsa ya kare kawai yake yi shima su
kashe shi.
Zayyan ya tausaya masa shima ya fada masa yadda ya fado hannunsu. Ranar hirar da
suka yi kenan kafin wahala ta sa suyi baccin dole.
Wurin da suke ba cikin daji bane hasali ma a cikin gari ne mutanen suka samu wani
tsohon gini da rigima ta kori masu shi suke dabdalarsu a ciki. Tsaron da suke masa
yasa har yanzu ba'a gano suna zuwa wurin ba. Sanyin asuba ne ya farkar da Zayyan ya
tashi ya ga Col Nasiruddeen shima ya farka. Gefe yaja jikinsa ya bubbugi kasa ya
dawo.
"Rabona da sallah tun la'asar ta ranar da muka fito"
"A haka zaka yi sallar babu alwala ko tsarki?"
"Akwai ruwa ne a kusa?" Zayyan ya tambayeshi yana leka lungunan gidan.
"A'a sai dan wanda suke kawo min tare da abinci. Idan yana da yawa dashi nake yin
alwalar nayi sallolin da suka samu"
Murmushi Zayyan yayi masa "shiyasa Allah Ya hore mana taimama domin saukakawa a
inda ruwa yayi karanci."
Col. Nasiruddeen bai nuna girman kai ba ya bari Zayyan ya koya masa. A zaune duka
suka yi sallah jiki ya kara tsami. Zayyan ya dade yana yi saboda yasan wanda suke
kansa da yawa. Addu'a yake ta yi Allah Ya tseratar dasu, Yasa su Hadir sun tsira
kuma Ya maida shi ga iyalinsa.
Sai da rana tayi sosai aka miko musu plate da wani abu da Zayyan bai gane shinkafa
ce, gero ko wake ba. Gashi nan dai a cure wuri guda. Col. Nasiruddeen yunwa ta
galabaitar dashi ya rinka turawa kawai. Shima Zayyan sai ya ga bashi da zabin da ya
wuce ya taya shi ci. Ba dadi ba dadadawa amma haka ake basu wannan abincin suna ci.
Sabo ne ya rinka shiga tsakanin wadannan bayin Allah da suke rayuwa a inda iyalansu
da kowa nasu yake tunanin sun mutu. Kullum dare bayan 'yan tawayen nan sawunsu ya
dauke daga dakin hirarsu sai ta karkata ga iyalansu. Dukkansu har jiran dare suke
domin su saukewa juna nauyin zukatansu. Matsananciyar kewar iyalansu tana damunsu
tana ci musu zukata. Yau ma bayan wata daya da kama Zayyan suna hira Col.
Nasiruddeen yake cewa.
"Idan Allah Ya fitar dani daga wurin nan ina komawa abu na farko da zan fara yi
shine yin ritaya. Zayyan na bar aikin soja har abada wallahi"
"Ka dena fadin haka Sir. Ni ka ga a duniya ban taba gani ko sha'awar wani aikin ba
bayan shi."
"Da kuruciyarka ni kuwa girma ya soma zuwar min. Sa'annina da kannena suna kwance
comfortably da iyalansa a wannan lokacin ina zaune a inda Allah kadai ya sani cikin
wari da kazantar najasata. Babu wanka babu abinci mai kyau sannan duk abinda zamuyi
sai dai mu yi shi a inda muke kuma mu kwana a ciki"
"Saboda abinda Allah Ya zaba maka kenan. Ya halicci mutane bayan kariyar da yake
bamu da IkonSa kuma ya sanya mu garkuwa a garesu masu taimaka musu. I believe we
soldiers are not made...we are born to protect (na yarda mu sojoji ba yinmu ake yi
ba....haihuwar mu ake yi domin bada kariya)"
"We are special, nima na yarda...." Col. Nasiruddeen ya amsa da murmushi a fuskarsa
"amma bazan cigaba da sacrificing rayuwata ga mutanen da basu san nayi musu ba. Ni
da wannan aikin sai dai idan mutuwa nayi a wurin nan"
Dariya ya bawa Zayyan yadda ya hade rai da gaske ya gama da aikin soja "wannan
magana fa kamar a kunnen Arifah. Nasan zata so ka cigaba da aiki muna biye daku"
Kafada ya noke kamar yaro "ko me zata yi sai dai tayi kuwa. Idan na mutu bakin aiki
wa take dashi da zai kula min da ita? Burina kawai na koma gida na cigaba da bata
kulawa. Shekara da shekaru ina neman haihuwa amma don ganganci ban tashi barin gida
ba sai da na sami 'yar. Idan na mutu fa duka duka shekara hudu muka yi tare. Kila
ma ta manta dani gabadaya"
Sai kuma ya bawa Zayyan tausayi. Col ya fada masa yadda ya kwashe shekaru shabiyar
da aure tun da kuruciyarsa babu haihuwa sai akan Arifah. Yana son tilon 'yarsa
kamar rai. Ranar da zai taho Liberia da kansa ya kaita makaranta nursery da take ta
rinka kuka sai ta bishi. Zuciyarsa ta karye, ya baro mamanta tana nata kukan a gida
itama tana yi kuma daga nan Lagos zasu wuce. Da kyar ya rarrasheta aka karbeta daga
cikinsa tana ihu ya bar harabar makarantar.
Ranar da yaji labarin iyalin Zayyan ya tausaya masa matuka. Cewa yayi kada Zayyan
ya kuma kiransa da wani abu da zai alakanta shi da soja sunana Baban Arifah shi
kuma yana kiransa Baban Alheran.
Kwana uku a tsakani Zayyan ya soma tunanin hanyar guduwa. Sai da Col. Nasiruddeen
yayi ta bashi shawarar kada ya fita ya fishi dadewa kuma shima ya gwada babu sa'a
amma yaki hakura. Ta yaya zai hakura bayan kullum sai anzo an bashi wahala domin ya
bada bayani shi kuma yaki. Sai ma zancen kashesu da aka fara wai zasu bar wurin an
kusa gano su. Shiyasa yaga ya dace dole su nemi hanyar tsira.
Lallabawa yayi yana neman hanyar fita ya hango tawagar 'yan tawayen sun shigo
wurin a guje. Masu gadin nasu da wasu kowa hankalinsa ya tashi. Cikin ikon Allah ya
hango mutum biyu da kayan sojojin kasar amma umarni suke badawa a tabbatar babu
wanda ya tsira a cikinsu. Su duka masu laifi.
"Shot on sight" (a harbe duk wanda aka gani) yaji ana bada umarni daga waje.
A guje ya koma ciki ya gano wani bari na katangar da ya dade yana tunanin haurawa
sai kuma ya fasa ya shige inda suke ya tada Col. Nasiruddeen da yake bacci.
"Baban Arifah we need to run"
"Baban Alheran nace..."
Harbi suke ji da ihun maza da alamun guje guje. A gaggauce shima ya mike suka nufi
wannan katanga. Zayyan ya haura saman ya miko hannu domin taimakawa Col.
Nasiruddeen amma ya kasa saboda bashi da tsaho sosai. Ga tsira yana gani amma ya
gaza. Idanunsa hawaye fal suna jin harbin yana kusanto inda suke yayi saluting
Zayyan.
"It was nice meeting you Lieutenant. Take care"
Zukatansu sun karya su duka. Zayyan sai tuno Major Mustapha da dan uwansa Hadir
yake yi. Soja shi kadai yasan ciwon soja. Durowa yayi kasa kafarsa tayi kara duk da
haka ya kama Col. Nasiruddeen da mamaki mai tsanani ya kama shi na karamcin wannan
yaro. A kafadarsa ya dora shi ya mike tsaye.
"Baban Arifah haura"
Col. Nasiruddeen ya mika hannu ya haye katangar bai sauka daya barin ba ya gano
sojojin kasar da 'yan tawayen sun taho wurin gadan gadan. Su ma 'yan tawayen
katangar suka zo haurawa. A gigice yace "yi sauri Zayyan"
Zayyan ya mika hannu ya hau katangar bai haura da kafafunsa ba bullet ya shiga
kafadarsa. Col Nasiruddeen ya