Advertisements
Chapter 44 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   44 / 99

129K to 132K   out of 295.8K words

cikakken sunan gidan da zai nema da garin da suke.


Harka ta zamani da kwarewa Major ya bayar da cigiyarsu ta hanyar amfani da sojoji
ta bangaren Captain Onomza. Zasu koma Katsina su bayar da sati daya ko biyu idan
babu wata nasara da kansa zai je Nijar din nemansu. Ko a haka baya jin ya biya
Zayyan fansar ransa.


**********


Kwana biyar da komawarsu Awwab Katsina. Kullum zai kira Ummi ke dauka Radhiya ta
kirkiri wani abin da zai hanata karba. To ta karba tace me. Ta barshi da muguwar
kewa ya gaza yin abin kirkin da yayi niyya wato zagayen gidajen 'yan uwa. A rana
duk inda yayi biyu ko uku sai yace ya gaji. Sai dai fa duk dare suna tare da
Ghazalatu wanda hira da ita ke debe masa kewar Alheran kadan. Yana takaicin yadda
baya iya sake mata kamar da kuma hirar ma yana yi ne don kada ya wulakanta ta. Abin
yazo ya fara damunsa ga tunanin Radhiya da rashin jin muryarta. Mafita ya nemawa
kansa zuciyarsa kuma tayi na'am da shawarar.


Major yayi musu bayanin yadda ake ciki Ummi har kuka sai da tayi. Saboda abin
duniya Maikudi ya kasheta ita da 'ya'yanta da bakinsa ya rabasu da danginsu.


Su Malamijo kuwa sauki ya samu daga shi har amarensa. Yau gidan an tashi da kukan
Asabe tayi rantsuwar ko ana ha maza ha mata sai Malamijo ya saketa don bazata yarda
ya kasheta da ciwo ba. Fafur taki karbar girki ita takarda take jira shi kuma yace
bai gama cin sadakinsa da kudin da ya kashe na aurenta ba. Rigima taki ci taki
cinyewa duk jama'ar gida yanzu sun san lalurar da ta kwantar musu da uba.


Nene tana gogawa Radhiya maganin makeron da ta karbo wanda a cikin sati kan har ya
fara hadewa yayi baki ta hanata fita kallon rigimar da take son taje ta yi.
Kunkuninta ta gama da zumbure zumbure ta hakura.


"Ni kuwa tun zuwanku Radhiya kinje gidan Gwaggonki Salame?"


"Gaskiya kada kice inje Nene bazan iya zuwa ba"


"Akan wane dalili"


"Ita da ko Malamijo bata zo ta duba ba sai nice zani?"


"Wannan kuma tsakaninsu ne. Ina ruwanki ko ke kika haifa masa ita?"
Ranta dai bai son zuwa ta soma jan hanci Nene ta dungure mata kai "me tayi miki
kike gudunta rigimanatu"


Duk wani abu da zata iya tunawa da Salame ta taba yi musu ta rinka daukowa kawai
saboda neman dalili. Karshe tace "kuma harda aurewa Ummi baban Danmama. Ai da na
sani Ummina zai aura don ma dai bana so kawai kuma ana ta cewa an kusa biki fa sai
Ummi ta makance ita kuma Gwaggon ya aureta."


Tashi tayi jin rikon Nenen yayi sauki ta suri hijabinta ta tafi kallon kwal uwar
daka a tsakar gidan nasu. Nene ko bi ta kanta bata yi ba sai dogon nazarin da ta
samu kanta da yi. Tabbas anyi haka amma tun lokacin bata jin wani yayi tunani a kai
ma. Makantar Mairama farat daya tazo duk da an san tana ciwon ido. Bata mantawa ita
Mairama ta bawa firinjinta ta sayar wani lokaci suka je asibiti akace babu komai a
idon nata. Ko dai da hannun Salame tunda tafi kowa sanin abinda ya taba hadasu da
marigayi Zayyan. Saurin kawar da tunanin tayi. Duk bakin halin Salame ace harda
makanta kanwarta saboda namiji? Kasa nutsuwa tayi ta nemo yaro cikin yaran gidan ta
bashi wayarta ya kira maigidanta. Tayi masa bayanin zarginta ne tace ya kamata a
nemo kaikayi koma kan mashekiya.


"Haba Marka ina amfani wata ta warke wata ta makance? Yanzu dai tunda kin fara
tunanin haka ki hadani da Mairama ko Radhiya din zan sanar dasu add'o'i da
Ayatusshifa a karanta mata ana tofawa a ruwa tasha ta wanke idon. Zamu tsananta
addu'a in Allah Ya yarda zamu sami makarin abin indai sihiri ne. Amma kada ki fada
mata kada ki tada rigima idan zargi ne kawai. Ki bari mu gwada mu ga ikon Allah"


Godiya tayi masa ta ajiye wayar zuciyarta tana karfafa mata zarginta akan Salame.

***********


Washegari kuwa Nene bata yi kasa a gwiwa ba ta nemi Ayuba. Duk cikin yaran gidan
shine ya tashi da ustazanci yana ma koyarwa a Islamiyya. Bayanin mijinta tayi masa
shima ya hada da nasa ilimin da kansa ya siyo ruwan roba c'est bon babba yayi mata
tofin nan yadda ya kamata. Ranar shi wuni tana sha tana shafe ido. Nene tace mata
su gwada ko za'a dace ne ta karba da murnarta.


Bayan kwana biyu Ummi ta fara jin jikinta yana canjawa tafi jindadinsa sosai gashi
ruwan tofin saura kadan. Radhiya ta nema saboda ta jiyo muryarta tana cewa Malamijo
yau kwadayi take ji yana rantsuwar kada ta bishi gonar da zai tafi a lokacin.


"Kin raina min uba ko" ta tambayeta bayan ta amsa kiran.


Sanye take da riga da skirt na atampa ta gama shirinta da hijab ruwan madara wanda
ya dace da kayan iya gwiwa za ta bishi gona tayi barna.


"Ummi balance dayet muke bukata"


"Allah Ya shirya min ke, zo ki dauki kudi ki siyo min ruwa irin wanda Ayuba yayi
tofi a ciki. Ki siyo guda uku sai a ajiye"
Murmushi tayi "Ummi kin fara gani ko dan dishi dishi?"


"Ke dai ki sakani a addu'a ido ya bude na ganku ke da kaninki"


"Amin Ummi, wayyo dadi"


"To wuce ki tafi banda yawo" sai ana jaddada mata kamar karamar yarinya.


Tsokanar Ummin tayi tace "Ina zani ko azahar ba'ayi ba inje basu gama abinci ba
balle na sa rai da balance dayet din"


Muryar Malamijo ta ji yana magana daga soro ta yi murmushin mugunta. Daga masa
hankali zatayi tayi ta binshi yana fada ta dage gonar zata je tunda a kafa yake
zuwa. Sai sun isa wurin shagon da zata je sannan zata rabu dashi.


Da dan gudunta ta taho kamshi da idanun da suka kafeta a gaban Malamijo suka kashe
bakin da jikin nata baki daya.


Wani murmushi Awwab yayi mata ta mayar masa idanunsu sarke da na juna. Malamijo bai
kula ba yana ganinta yace "Allah Ya taimakeni yau ga yayanku na Katsina yace sako
ya kawo muku ke da Mairama. Idan kika sake kika biyoni zai koma da kayansa sai in
ga karyar cin balanciye din"


Ficewa yayi ya barsu a tsaye. Wani irin kallo yake yi mata taji ta takura.


"Muje wurin Ummi din" tace bayan ta juya masa baya saboda wani nauyinsa da take ji.


"Wait"


A nutse ya tako ya dawo gabanta ya tsaya. Jeans navy blue da layin fari da ya
dusashe daga tsakiya ta gaba da shirt mai maballai ruwan toka ya lankwashe dogon
hannunta zuwa rabin hannun. Fuskarsa a gyare sai hancinsa ya kara fitowa. Kanta ta
sunkuyar ta ma kasa kallonsa.


Da wannan muryar tasa mai kauri da tafiya da hankalinta yace "baki tambayeni me ya
dawo dani ba, ko dama kinji a jikinki zan zo?"


"Ba wurin Ummi kazo ba?"


"Basarwar ce?" yayi tambayar yana son sake hada ido da ita.


Hijabinta ta janyo gaban fuskarta zata rufe ya girgiza mata kai.
"Ahhh" yace yana mata alamar ta bude baki.


Kafada ta noke tare da murmushi.


"Please Alheran"


Sake nokewa tayi yace "dadin abin tare muke da My G tana mota"


"Ahhhhhh" tace da sauri har tana bashi dariya domin kuwa ya gama tabbatarwa ba shi
kadai bane ya fada wannan kogin da baya fatan fita.


Irin sweet din rannan ce dai wadda ya taho da ita daga Germany ya fito da ita daga
bakinsa ya kankance ido yana kallonta "See what you did. Kin cikani da surutu kinsa
na kusa shanyewa"


A bakinta ya saka mata kunya tasa ta rufe ido da tafin hannunta.


"Kinsan wani abu" ya bijiro da maganar don kawar da hankalinsa daga kallon bakinta
da take shan sweet din dimple dinta da yake matukar burgeshi yana ta sake shigewa
ciki.


Kai ta girgiza masa ya dawo gefenta ya tsaya "ta kare miki Alheran auren dreba ya
tabbata a gareki"


"Ni dai a'a"


"Are you sure? Ko da dreban mutumin da kike shan sweet din bakinsa ne?"


"Ya Allah" tace yadda yake yi idan yaga abin mamaki tana jin wani irin farinciki
mara misaltuwa.


"Na sani ai bazaki so kada ta kare miki ba in dai shine"


Kokarin saita kanta tayi ga murmushinta yaki bacewa "inji wa"


"Ba sai munje nan ba kawai ki amince kamar yadda na amince"


Cike da shagwaba tace "Ni dai wallahi...."


"Me? Ba haka bane?"
"Alawar ce ta kare" tace tare da yi masa gwalo ta soma tafiya da sauri.


"Zaki aureni?"


Ita ce tambayar da taji ya jefa mata a daidai lokacin da kafarta daya ta fita daga
soron. Tsayawa tayi a wurin ta kasa gaba ta kasa baya har ya karaso inda take ya
rabe ta gefenta ya wuce har cikin tsakar gidan da sallama yana kiran Ummi.

[11/2, 6:48 AM]🏽
]🏽 : 31B.💕

Ummi kamar daga sama ta tsinkayi muryar Awwab. Yadikko ce ta amsa masa suka gaisa
ta nuna masa dakin Hajjo.


"Shiga tana ciki"


Radhiya ta hango tsaye ta kasa yanke shawarar komawa taje aiken da akayi mata ko ta
bi bayansa.


"Ji min shirme Radhiya kina tsaye ashe kina kallonsa maimakon ki kaishi wurin
Mairaman. Dauko filas din wajenta in zuba masa kunun nan da zafinsa"


Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta shiga dakin. Yana zaune daga gaban
Mairama tana tambayarsa mutan gida da hanya.


"Mamaki nayi da naji muryarka fa. Amma dai kowa lafiya ko?"


"Ummi kada ki damu lafiya kalau."


Dagowa yayi yana kallon Radhiya tana neman flask din ruwan zafi. Yana gabanta amma
da yake hankalinta yayi nisa bata kula ba. Ummi ce tace "wai har kin dawo ne?"


"Ban je ba, Yadikko ce tace na dauko flas za ta zubawa Hamma kunu"


"Yi maza ki kai mata kije ki siyo min in samu yayi tofin kafin ya fita"


Ita Awwab ya tsare da ido yana tambayar Ummi "aikenta kika yi?"


Bayani Ummin tayi masa yaji dadi yana fatan Allah Yasa a dace. Da ido ya kalli
Radhiya yana nuna mata ta zauna ta girgiza kai.


"Bari naje na siyo Ummi ina zuwa"


"Daga zuwanka, barta ba nisa bane da wurin"
Tashi yayi ya sake cewa shi zaije. Ummi tace to ya bari ko ruwa yasha kafin ya
fita. So yake kawai ya tashi ya samu kebewa da Radhiya don ba da niyar kwana yazo
ba. Gabadaya ya shagala da kallonta. Takwanshe kafafu yayi ya tallabe kansa da
hannuwansa da ya dora akan cinyoyinsa ya zuba mata ido. Hanata sakat yayi ta kasa
dago kai saboda tsoron idanunsa take yi yadda suke matukar tasiri a kanta.


Wayar Ummi da ta soma ringing ce ta sa ya dena kallon nata na dan lokaci ta tashi
da sauri ta fita. Shi ya mikawa Ummin wayar ganin sunan Mami shima ya tashi ya gudu
yana dariya bayan ya amsa mata kiran ya saka mata a kunne.


"Dana kika biyo da kiran nan ko? Yanzu ya iso bai yi rabin awa a gidan nan ba"


Sai da Mami tayi dariya tace "nifa ina jin mu saka ranmu a inuwa kawai yaran nan
sun gama mana komai sai dai ma su jira mu"


Labarin yadda suka kwashe dashi bayan ya dawo daga sallar asuba tare da Major ta
bata suka rinka dariya. Yana shiga gidan yayi sa'a tana falo shine yake fada mata
zaije Sumaila. Da ta tambayeshi ko lafiya shine yace wai Alheran bata da waya kuma
ya san cewa irin haka ne yake sa 'yan mata su ji babu dadi sa'anninsu suna da abu
su basu da shi.


"Akwai waya a hannun Ummin taku ai"

Ita ce amsar da ta bashi.


Sosa keya yayi yace "So nayi na bata a matsayin gift na gama secondary school"


"Ina ta Karami da Ibrahim? Duka tare suka gama"


"Ibrahim yana da waya. Emzee kuma zan saya masa. Tunda ita ce babba shiyasa zan
fara bata"


"Ba sai kaje Sumailan ba, nan da 'yan kwanaki zaka gansu sun zo biki"


Fuskarsa tamkar zaiyi kuka yadda ta dage tana neman kure shi. Tsokanarsa ta cigaba
da yi daga karshe dai yace mata wai kewar Ummi ke damunsa.


"Kewar Umminka kuwa duk gidan nan banga mai cike maka gurbinta ba. Sai ince a dawo
lafiya ko"


Amsar tayi yadda yake so amma kuma ta makale masa a rai. Ko dai Mami ta gane wani
abu ne? Kai da wuya shi yasan baya yin yadda kowa zai san yana yiwa Alheran
zazzafar soyayyar da take nukurkusar zuciyarsa.


Daya motar ya dauko Mami tana korafin ranar zai takura mata yace tayi hakuri bazai
kwana ba. Jinsa kawai tayi sai kace Katsina zuwa Sumailan tafiyar awa daya ce. To
gashi dai a gidan Malamijo tare da Alheran Radhiya.


Yana fitowa har ta kusa kure layin nasu ya bi bayanta da sauri. Sai da ta dan
tsorata da taji muryarsa da ya kira sunanta. Ta juyo a nutse yayi mata nuni da
gidan da hannunsa.


"Ki jirani a wurin zaman nan ina zuwa"


Wani salihanci ne ya saukar mata a yau din, babu musu ta koma ta zauna akan tudun
nan tana jiransa. Hamma Awwab ne ya tambayeta ko zata aure shi. Tunanin maganar
kawai sai da ya sanya zuciyarta kadawa tsigar jikinta ta tashi. Kankame jikinta
tayi tana jin yadda farinciki ke mamayarta.


Magana take yiwa kanta ita kadai tana murmushi "lallai ta kare min, dreba kuma nake
so"


Shagon babu nisa bata dade ba Awwab ya shigo da katan din ruwan roba mai manyan
robobi. Za ta tashi yace ta bari ya kaiwa Ummi ya dawo.


Gabanta ke dukan uku-uku wannan karon da ya kuma dawowa. Zaman me zasuyi take
tambayar zuciyarta. Zance!


Bai dauke idonsa daga kallonta ba har sai da ya zo gabanta ya durkusa a tsugunne.
Kallon kofofi biyun da za'a iya shigowa wurin a same su take yi ta shiga gidan da
ta fita tana addu'ar kada Allah Ya kawo kowa.


"Amsar tambayata nake jira"


Rufe fuskarta tayi da hannu sai murmushi da yake manne akan kyakkyawar fuskarta.


Ba burinsa bane ta chanja daga Alheran din da ya sani don kawai matsayinta a
wurinsa ya chanja.


"Na takuraki ko?"


"A'a"


Tsoro ne ya dan darsu a zuciyarsa da sauri yace "Baki amince ba ne?"


"A'a"


"To menene?"
Kofofin ya ga tana bi da kallo kafin tace "Hamma ni kunya nake ji kada wani ya
shigo"


"Sai ki bani amsar da nake jira in tashi. Nima bakiji kafafuna ba sun fara sagewa"
ya kare maganar yana marairaice mata.


Tsokanarsa ta fara yi kawai don ta ja nasa rai "kasan sojoji an sanmu da dauriya ya
kamata kaima ka gwada jarumta ko na rabin awa ne"


Idan ta kara minti daya yana jin kila zama zaiyi kawai a wurin ya lankwashe kansa
gefe "habaaa mana"


"Na amince" din da yake jira ta fada kamar mai rada ta rufe kanta tsaf baya ganin
komai a fuskarta.


Tashi yayi ya zauna a gefenta a kan tudun "wahhhsh, da kin kara jan lokaci sai dai
ki daukeni idan mun tashi"


"Kai" ta waro ido tana dariya. Ta ina za ta dauke shi.


"Seriously, sai ya tuna min da punishment din primary dinmu a Sokoto. Frog jump
haka kawai don a wahalar da mutane mu kasa tafiya"


Da yake taji mugunta ta sami abinda take so sai dariya "yanzu harda zaman babur
akeyi yafi frog jump wahala"


"Bana fatan sanin yaya yake tunda ya saka ki wannan dariyar nasan ba abin kirki
bane"


Gyara zama yayi sosai ya kira sunanta domin yana son suyi magana ta nutsuwa da
fahimtar juna "abinda zan fada miki ina so kiyi masa kyakkyawar fahimta kinji" ya
kafa mata ido.


"To Hamma"


Nannauyan numfashi ya sauke saboda mahimmancin maganar da yadda ta rinka cin ransa
har ya kasa zama dole ya biyota ayita ta kare.


"I love you Alheran Radhiya, I miss you a duk lokacin da kika bacewa ganina. Da zan
iya da na dora hannunki kinji yadda kike hana zuciyata samun nutsuwa saboda
tunaninki"


Tamkar ana zubawa jikinta ruwan dumi haka take jin saukar kalamansa suna kwantar da
duk wani abu da yake yawo a ranta sai shi kadai da tunaninsa.
"A cikin kwanakin nan da na kara saninki na fahimci kina da kishi" gefensa ta dan
kalla kamar zata yi magana sai ta fasa. Tabbas tana kishinsa, kishi ba na wasa ba
kuwa "gashi ni kuma na hadawa kaina zafi ina zaman zamana. Ban san inda zan kai
mata biyu ba amma Alheran bazan iya rabuwa da Ghazalatu ba don ina sonki"


Sake kallonsa tayi sai ya ga kwalla ta soma taruwa a idonta. Har cikin zuciyarsa
yake jin komai na kanwar tasa. A zahiri zai iya boyewa amma a zuciyarsa yasan
soyayyar gaskiyarsa tana hannun Alheran "kada kiyi kuka please. Ban zo gareki ba
sai da nayi ta tunanin what will be the best for the three of us. Look at me!"


Umarnin yayi mata tsauri a yanzu da ya gama da zuciyarta amma bata iya ketarewa ba
ta dago idanunta hawayen zuna zubowa batare da sauti ba. Da zai iya da ya rungumeta
sai dai ko da suka tashi nesa da gida Mami na aiki sauran tarbiyarsu ta koma ga
mahaifinsu baiyi musu da wasa ba. Bai bar yaransa dabi'un nasara sunyi galaba a
kansu ba ta hanyar yawan kulawa, tsawatarwa, ja a jiki da kaiwa Allah kuka.


"I love you! I love you!! I love you!!!....kafin komai ki bar wannan ya zauna a
zuciyarki. Kin tuna ranar da nace idan kin sha abin bakina zan tambayeki wani abu?"


Jikinta a sanyaye ta gyada kai "kiyi hakuri amma alfarma zan rokeki da wannan
damar. ALHERAN DON ALLAH KI YARJE MIN NA FARA AUREN GHAZALATU."


Jin maganar tashi tayi tamkar saukar aradu a tsakar kanta. Tsiwa take son tayi masa
ko tayi bore ko dai tayi wani abin domin nuna masa cewa bata yarda ba, zuciyarta ma
bazata barta ba sai ta kasa sakamakon raunin da take iya karanta a idanunsa da suka
soma chanja launi.


"Mummyn Ghazalatu sister din Mami ce iyayensu daya. Daddy dinsu kuma cousin din
Mami ne kuma cousin din Daddy. Iyayensu maza duka ukun brothers ne. Shekararmu biyu
tare da ita sai yanzu muka yanke shawarar fada a gida bayan bikin su Zahra. Kina
ganin na kyauta idan nace mata na fasa saboda ke?"


Roko ne yake yi duk da bai furta yadda zata gane a magana ba amma ta gane a
yanayinsa. Duk kishinta tana da hankali kuma tasan daidai. Indai zata zama
mallakinsa itama wallahi zata iya hakura ya fara aurenta. Da dai ace da ita ya fara
haduwa da labari ya sha bambam amma tunda ita ce tazo daga baya hakuri ya zame mata
dole.


"A'a" tace a nutse don ta bashi kwarin gwiwa.


Farinciki ne ya bayyana a fuskarsa ma'abociyar yawan murmushi "Don Allah kin yarda
zaki jirani ko na shekara daya ne na fara aurenta sannan na aureki?"


Runtse idanunta tayi wasu zafafan hawaye na gudu ta gyada kai don babu bakin
amsawa.
Ajiyar zuciya ya saki yana hamdala. Daga Ghazalatu har Alheran yasan babu wata
saliha a cikinsu. Ko yasha giyar wake bazai ajiyesu a gida daya ba ma. Rigima ce
gagaruma ya hadawa kansa amma baya jin akwai yadda zaiyi ya sabule ko daya a
cikinsu. Dukkansu akwai babban al'amari tsakanin iyayensu da nasa kuma babu wadda
aka tura masa. Da kansa ya nemi soyayyarsu saboda haka dolensa ya tattaro duk wani
karfin hali na maza ya dorawa kansa idan yana son

44 / 99