Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
mai daci.
"A BEG MAKE UNA HELP ME"(don Allah ku taimaka min) matar tace tana ciccije lebe ga
'yan fashin suna daka tsawar tayi musu shiru ko su harbe ta. Emzee na jin haka ya
duka a gaban matar nan daga shi sai hasken farin wata yayi abinda bai taba zato ko
tsammani ba. Ashe aikin soja ya wuce duk yadda ake tunaninsa. Yau shine da karbar
haihuwa abinda ko a tv bai taba yarda ya kalla ba. Yana gabanta tana nishi tana
fada masa ya duba ko kai ya fito.
Muryar mahaifinsa yaji ya dafa kafadarsa "Make me proud my son." Ya tashi yayi waje
batare da sauraron kiran da Emzee yake yi masa ba.
Tashi yayi zai bi babansa matar tayi wani nishi iya karfinta sai ga da yana neman
faduwa dole ya tare ya rike mata shi. Wuka ta dauko a gefen rigarta ta bashi ya
yanke cibiya tace masa tun da mutanen suka fara harbi ta boye wukar domin tsaron
kanta ashe zata yi musu amfani.
Karar harbi suke ji daga waje ya tashi da jinjirin nan a jikinsa ta bashi wani
mataccen dankwalinta ya zura yaron ya daure shi ta gabansa kamar wanda yayi daurin
karaya. Yana fita ya sami maza uku a kwance ashe Zayyan ya shammacesu ne ya karbe
bindigar daya. Harbi na hudu yaji ga hasken asubu ya fara ratsowa daidai da tahowar
Zayyan daga bayan wasu bishiyu. Murmushi Emzee yayi ya taho gareshi da sauri ya
mika hannu zai rungume shi kawai su ka ji sautin fitar bullet sai ga Emzee ya tafi
gabadayansa ya fada jikin Zayyan tare da jaririn.
Da hannu daya Zayyan ya riko shi suka kai kasa ya daidaici mutumin da yayi harbin
ya sakar masa bullet a tsakar ka kafin ya fara kiran sunan Emzee a gigici yana
kukan da ko fuskar Emzee din baya gani sosai.
"Muhammad kada kayi min haka ban dawo domin in ga mutuwarka ba...Muhammad kada kasa
na kasa fuskantar mahaifiyarku" kuka yake yana juya Emzee ga jaririn jikinsa ya na
neman a ina aka harbe shi. Ba karamin tsorata yayi ba da ya ji a gefen cikinsa ne
ya leka kangon matar ta tashi da dafa bango ya bata jaririnta sannan ya dawo ya
goya Emzee su ka fara gudu saboda yana tsoron ko akwai wasu 'yan fashin a kusa. Sai
da rana ta fito sosai wuraren karfe goma su ka bullo a bakin titi jikinsa jike da
jinin Emzee. Motocin sojoji ne birjik a wurin an baza search party sai fito da 'yan
fashi suke yi. Wani ne ya fara hango su da sauri ya soma ihun murna sauran su ka
taho aka hadasu su ukun aka zuba a mota zuwa airport saboda a zatonsa Emzee ya riga
ya cika. Ambulance ce tazo daukarsu daga airport din Abuja a guje aka tafi dasu
National hospital.
A daidai wannan lokacin kuma Allah Ya sauki Radhiya ta haifi 'yarta mace.
Theatre aka shiga da Emzee emergency cikin sa'a bullet din bai taba muhimman organs
ba aka cire. Zayyan yana tsaye a bakin kofar Daddy, Baba Hadir da Mairama suka iso.
A guje ta rungume shi tana kuka sosai yana bata hakuri akan suyi masa addu'a. Suna
kallo aka gangaro shi zuwa dakin hutu idanunsa a rufe.
Radhiya ko awa batayi da haihuwa ba tace a kaita wurin Emzee da Daada. Yanayin da
take ciki na tashin hankali Awwab ya daukota da Rahima da Mama aka bar babyn a
asibiti da Mami.
Jigum jigum ake zaune Radhiya ta fado dakin tana kuka a jikin Daada yace tayi
hakuri.
"Kai Adda ashe dai kina sona" su ka ji Emzee yace da gajiyayyar murya..
Ita da Ummi da Daada suka yi kansa Rahima tana gefe tana kuka.
Sannu sannu suke yi masa ya kalli Radhiya "Adda ina cikin?"
"Tana asibiti ta taho tarbar Baffanta da kanta" tace tana murmushi.
Sai lokacin Daada ya kula "Taho kinji Innata mun saka ku a tashi hankali" ya
rungumeta tare da Nasr da ya makale masa sai da ya ganshi ya dena wannan kukan.
Da kyar Emzee ke magana ya yafito Baba Hadir ya ce "Baba don Allah ka aura min
Rahima kafin na mutu."
Kofar fita daga dakin Rahima ta nufa da sauri Daddy ya tsayar da ita "ko sannu baki
tsaya kinyi masa ba zaki gudu"
"Ba dole ba daga tashinsa zai matsawa 'yata" cewar Ummi tana harararsa.
"Daddy kasa baki wallahi ni aure nake so"
Daada yace "Anya yaron nan ba anasiziya bace bata sake shi ba?"
Emzee yayi dariya a ransa ya kuma kafe Rahima da ido "idan bata amince ba ni dai ku
aurar dani kada in sake zuwa wuri irin wannan ban dawo ba"
Rahima na jin haka ta zaro ido Radhiya ta rike hannunta "ta amince don Allah ka
dena yi mana sumbatu"
Dariya aka saka baki daya sannan su ka fita domin barinsa ya huta ita kuma Radhiya
ta koma wurin babynta.
Bayan kwana hudu Emzee yaji sauki sosai an nemo 'yan uwan matar da ya karbi
haihuwarta. 'Yan jarida har dakinsa matar tana yi musu godiya shi da mahaifinsa
tace yaya sunansu.
A tare su ka ce "ZAYYAN"
Ta ce "duka ku biyun?"
Su ka gyada kai.
Jaririnta ta mikawa Daada ta cewa "ina fata wannan Zayyan din ma ya zama soja
jajirtacce kamarku wanda zai iya sadaukar da rayuwarsa domin kasarsa. Nagode"
Emzee ma sai da ya karbi yaron ya rungume shi saboda akwai wani bond kasancewar shi
ya karbi zuwansa duniya. Bayan sun tafi ne Emzee yake fadawa su Daddy wayon da
Daada yayi masa akayi ta dariya. A gefe guda soyayyarsa da aka sakawa comma (,) shi
da Rahima ta sake daukar wani sabon salo mai shiga rai.
Awwab da Radhiya suna tare da 'yarsu ya lalace wurin basu kulawa da soyayya. Ranar
suna wanda aka yi gagarumin taro yarinya taci suna Zainab suna kiranta (Boubou).
Mama bata taba zaton wannan karamci ba ai kuwa tayi rawar gani sosai.
Boubou na ta wata takwas aka sake taruwa domin bikin da aka dade ba'ayi irinsa ba
na Barr Ibrahim Hadir da Zayyana Mustapha wanda aka dauro aurensu a Katsina sai
kuma Lt. Muhammad Zayyan Tureta da Rahima Idris Sumaila wanda aka dauro a Sumaila.
Salame sai da tayi kuka ranar.
Gida flat sama da kasa Daada ya kama musu babu nisa da su Radhiya saboda yace
amaren da angwayen akwai danyen kai duka da kuruciya.
Babu wanda ya rakasu gidajensu Emzee ya shiga nasa da yake kasa ya wuce daki kai
tsaye inda Rahima ke zauna akan gado an rufe mata fuska da mayafi. Yana shigowa
gadon ya hau ya tura kansa karkashin mayafin ya kwanta akan cinyarta. Kunya ta
kamata ta soma ture shi.
"Ya Emzee ka tashi don Allah"
Sake gyara kwanciya ma yayi "saibkin gyara min suna zan tashi"
"Me kake so nace?"
Kamshin da take fitarwa da tsananin kyaun da tayi yasa shi lumshe ido yana budesu a
hankali.
"Kin fini sani"
"Muhammadun Rahima ka tashi" tace tana murmushi gashi yaki bari ta budesu daga
lullubin.
"Rahiman Muhammadu ina sonki wallahi"
Murmushi tayi tana cewa ya tashi tunda ta fada yace to. Dago kai yayi kamar zai
tashi sai ji tayi ya birkitota gabadaya kansa ya rungumeta ya shiga kissing dinta.
Da kyar ya tuna ya kamata suyi nafila ya dagota suka yi alwala da sallah. A baki ya
rinka bata nama ita kadai take ci yana bin jikinta yana kissing dole ta hakura don
ba iya ci zata yi ba. A daren ta tabbata Rahiman Muhammadu matar Muhammadun Rahima
masoya daga Allah.
BAYAN SHEKARA BIYAR
Gidan Daada a hargitse yake da 'ya'ya da jikoki ana ta shirin zuwa Award Night da
gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar kasashe da dama na Africa suka shiryawa
Alheran Radhiya saboda services dinta to the military.
Captain Muhammad Awwab da gis one and only Scharzi Alheran 'ya'yansu uku Boubou mai
shekara biyar, Haidar takwaran tsoho mai ran karfe Malamijo mai uku da rabi sai
Fatima (Islam) mai biyu ga karamin ciki. Zahra bayan Femi ta kara da Hassana da
Hussaina (Taye da Kehinde) ana kiransu da duk wanda mutum yaso kira, sai Mu'az.
Fauziyya bayan Jawad da Sahla ta kara da Mustapha (Ansar) da Iman. Arifah biyu
gareta Nasrin da Nasir. Zayyana tayi biyu itama Zayyan (Junior) da Hassana (Mami),
iyayen garke Rahima da Emzee suna da Hadir (Little), Idris (Abba), Ibrahim
(Khaleel) sai Kauthar don haihuwa take duk shekara maigida kuma ya hana planning.
So da kauna yake gwada mata kamar ya hadiyeta.
Anyi taro lafiya an gama lafiya kowa ya koma gida cikin kewar juna.
Tun dare Radhiya ta gama hadawa Boubou da Haidar kaya zasu tafi Katsina dasu Mami
gidan zai huta na kwana biyu daga kiriniyarsu Awwab ya gama shirin sabon amarci.
Gidan Daada su ka fara zuwa da yaran inda su Mami zasu zo daukarsu.
Shigowar motarsu ke da wuya DK da yake wasa akan keke ya arta a guje ya shige cikin
gida yana kwalawa Daada kira.
"Menene DK?" Ya leko falon daga sama.
"Su Boubou ne Daada" yace kamar zaiyi kuka.
"Taho mu rufe kofa" ya dauke shi suka shige dakinsa ya kulle kofa Mairama tana musu
dariyar wannan abu.
Boubou na shigowa ta fara bude daki daki da bindigar wasanta a hannu tana kiran
"Uncle DK".
Yadda take matsanta masa da fitina idan yaji tazo baya iya zama. Nasr kuwa boss ne
mai zaman kansa ba ta zuwa inda yake dama sai yaso wasa. Idan ka ga ya sake Ibrahim
da Zayyana ne a gidan anzo da Mami.
Gajiya Boubou tayi da nemansu ta fada jikin Ummi "Umminaaaa"
"Boubou naaaa" Ummi tace tana jan hannunta zuwa dakin Daada, Radhiya da Awwab suna
dariya don sun san sai anyi drama. Ai kuwa muryar Daada su ka ji yana cewa "Zainab
ba fa zaki rinka zuwa kina takura kin yaro ba" sannan suka sauko su duka su Mami
sun iso ga Baba Hadir da Mama.
"Ummiiii" ta tabe baki tana kukan abinda Daada yace.
"Rabu dasu idan kin zama soja babu ruwanki da kowa" cewar Mama
Ta saki murmushi dimple dinta biyu suka lotsa. Fakar idonsu tayi ta dane bayan DK
tana kai masa harbi hannu da kafa "zo muje muyi training Uncle DK kada a kaimu
makarantar soja su koromu"
Awwab ya tashi zai rabasu Baba Hadir ya hana sai zama da suka yi suna kallonsu ana
dariya manya na fassara lamarin.
Yana daga kwance ta danne shi yace "ni bazanyi soja ba don Allah ki dagani"
Idanunta ta ware a kansa tana sukuwa a bayansa har ta soma tara masa gajiya "to
waye zai kareka idan ana fa'a"
Hantsilota yayi yana nishi "ba gaki ba idan kin zama sojan sai ki kareni"
Tayi wani murmushin bada fadi ita ga soja sai kuma ta janyo kwalar rigarsa yana
shirin guduwa "idan zan kareka ni me zaka rinka bani to?"
"Boubou wuyana" ya ce ta sake shi da kyar "zan rinka siyo abinci ina kawo miki
yadda Daada yake kawowa Ummi Baba kuma yake kaiwa Mama"
"Ahh irin na Abbana da Mamma kenan fa...to na yarda amma wallahi ka goyani" ta haye
bayan nasa Nasr ya janyota ta fado,
Dama shima tara shi take yi ai kuwa ta juya ta ce "Haidar taron dangi"
Barin kayan wasan yayi suka hadu shi da Boubou suka danne Nasr. Baba Hadir na ganin
haka ya tashi ya raba fadan ya hadasu da sweet suka tafi yana jin DK yana Boubou ki
kyaleni sai ta ce idan ta zama soja ta fasa kareshi.
Awwab da Radhiya basu bi ta kan sauran yaran ba dama nan suka yi niyar barinsu suka
wuce gida yana cewa yau zai kwana goge mata janbaki.
Falon ya rage Zayyan da Mairama, Mustapha da Hassana sai Hadir da Zainab su ka
zauna hira suna tunowa juna wasu lokuta da suka gabata da yadda rayuwa ta sauya
musu. A kowane yanayi sai dai bawa yace ALHAMDULILLAH.