Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
kulla shawarwari game da yadda bikin zai
kasance.
Washegari Awwab ya sauka a garin nasu cike da tsantsar farinciki ya rinka sallama a
kofar dakin Mami. Tana sane wai sai ta ja masa rai taki amsawa.
"Mami manaaaa"
Dariya tayi "shigo dai ba don halinka ba"
Da saurinsa ya bude kofar idanunsa suka sauka akan Umminsa Mairama maman Alheran.
Murmushi take ta yi masa daga inda take zaune wai wannan muryar Awwab ce. Shi kuwa
wani dumi yaji a idonsa da sauri ya karasa gabanta ya riko duka hannayenta biyu ya
dago kai yana kallon fuskarta.
"Ummi"
Da hannunta daya take bin fuskarsa tana shafawa "Awwab kaine ka zama babban mutum
haka"
Mami tana gefe tana murmushin jindadi Ghazalatu kuma ta coge a bakin kofa.
"Ummina kina lafiya? Kin rinka tunawa dani kuwa" yace yana matse hannuwanta cikin
nasa. Yau gashi da Umminsa abinda ya dade da cire rai saboda yadda shekaru suke ta
yawaita.
Hawaye ta soma yi "ban taba mantawa daku ba Awwab. Ina ma zan iya ganinka da kyau
in gani ko wannan tsayin kamar bulala ka dan cike shi da tsoka"
A razane ya kalli Mami sai ya ga tana hawaye. Hannunsa yasa yana yawo dashi a gaban
idanunta ya ga ko gezau. Awwab kasa mallakar kansa yayi ya kifa kansa a cinyarta
yana kuka.
"Kaji mutum kamar ba namiji ba, meye na kukan? Ai komai ya wuce da yardar Allah"
Hawaye yake da gaske yaji bazai iya zama ba ya tashi ya nufi inda yasan nan ne
dakinsa. Mami tace da Mairama ta dena damuwa zai hakura kamar kowa.
Ghazalatu ko shiga dakin bata yi ba ranta ya baci da kukan da wannan makauniyar ta
saka mata shi. A take taji wani haushin Mairama ya kamata. Dama akan wannan da
kallo daya zai sanar da mutum daga kauye take yake ta damuwa harda kuka.
"Ghazalatu shigo mana, kinga yayanki na kuka ko? Kada ki damu zanyi masa magana"
Ba yadda ta iya dole ta shiga tana nadamar tahowa don gidan har ya fice mata daga
rai. Akwatinta ta tura gefe sai da Mami tace "ga Ummin Awwab ki gaisheta mana"
"Sannu"
"Yauwa sannu 'yata. Yaya gajiyar hanya?"
Mugun kallon da Mami ta watsa mata ya sa ta chanja salon gaisuwar tace "ina wuni" a
dakile.
Ba jimawa Mairama ta shiga bandaki ai kuwa Mami rai a bace ta soma yiwa Ghazalatu
fada.
"Kar ki yarda na sake ganin irin haka kina jina? Wannan matar da kike gani ba
karamar daraja da kima gareta a wurinmu ba. Dangi kowa kokari yake ya tayamu
karramata. Bazan lamuncewa dabi'ar banza ba kinzo kina wani cin magan"
Abinka da makaho kunne ya kara fikewa. Mairama tana jinsu tayi murmushi kawai. To
dama yaushe zata yi tunanin kowa nasu zai sota. Ita ce fa wadda mahaifinta har yau
bai taba bin sawunta ba sai dai ita har sau uku taje kuma tana aika masa da 'yan
abinda ba'a rasawa.
"Kiyi hakuru gajiyar hanya ce" Ghazalatu tace da ta tuna Mami ce fa mahaifiyar
Awwab.
"A dai gyara"
**********
Fauziyya da Zahra suna kallo a falo Zainab tana duba takardun asibitoci uku da
likitann nan ya aiko mata. Ibrahim baya gidan yaje gaishe da kakaninsa Hadir kuwa
bacci yake a daki.
Radhiya ce ta fito yau babu hijabi tana dan murmushi fuskarta tasha kwalliua harda
janbaki. Fauziyya da Zahra suka shiga gyara dankwalayensu. Zayyana daga shiga deban
abinci a kitchen ta kasa fitowa tunda taji muryar Radhiya tana cewa.
"Ha mutum ya fito yasha iskar Allah."
Tana zama su Zahra suka mike, Zainab ta kwashe da dariya. Radhiya ta zama horror
tunda tace zata yi musu balotelli. Jiya a gabanta Ibrahim ya nuna musu hoton Mario
Balotelli wani dan ball baki na kasar Italy wanda yake kwashe kansa hagu da dama ya
bar tsoro guda a tsakiya tun daga gaba har keya.
A karkace ta kallesu "tashi kuma zaku yi daga zamana?"
"Ni bacci nake ji" cewar Fauziyya
"Fitsari zanyi ni kuma" Zahra tace tana matsawa gefe.
"To sai kun dawo, gumi ne ya dameni yau na saka lasi" kawai sai ta tuge dankwalinta
rantal ya bayyana.
Wata irin dariya suka kwashe da ita har Zayyana dake kofar kitchen. Zainab na dago
kai ta mayar dashi kan takardu kafin ta soma dariya itama. Radhiya ta bata rai
"ayi dariya da kyau naje soja na dawo. Kuma na dena daura dankwali iska zan rinka
sha"
"Ki rufa mana asiri don Allah ki rufe" Zahra tace idonta harda hawayen ganin wannan
gashi na Radhiya tsilli tsilli.
"Allah bazan rufe ba iska nazo sha."
Kyalesu tayi suka sha dariyarsu tana cewa su kiyaye kada tayi sanadin da zaa kai
amare da kwalkwal. Daga nan hira ta kaure don daga Zahran har Fauziyya basu da
girman kai duk da ba sa'arsu bace. Suna cikin hira ta soma gyangyadi Zainab tace ta
koma daki ta soma musu irin na masu magagi wai ba bacci take ba. Kafin la'asar ta
bingire akan doguwar kujera abinta. Ana kiran sallah duka suka watse sai Zayyana.
Ta wayar Fauziyya Awwab ya kira yace yana kofar gida don dreban Harun ne ya kawo
shi. Zayyana da ta amsa wayar taje ta bude masa gate tana murnar ganinsa.
Suna shigowa falo idanunsa suka gane masa Radhiya. Kanta yake iya gani sai rabin
jikinta ta rufa dankwalinta daga kasa kuma fuskarta jikin kujera take kallo. Ya dai
tabbatar kayan mata ne a jikin mai wannan kan a sanyaye ya karasa shigowa Zainab
tana turo Hadir ya kallesu da tausayawa. Da guda daya tilo da suka haifa ashe dan
daudu ne jiya da Mami da Ummi suna bashi labarin komai yana kwalla basu hada masa
da wannan ba.
[02/11 7:30 AM] My 2nd Mtn: 24. Zainab baki yaki rufuwa "Awwab, Masha Allah sannu
da zuwa...zauna, zauna kasha hanya"
Shi dai murmushi yake yi amma hankalinsa gabadaya yana wurin wannan kan dake kwance
akan kujera. Allah ne Ya taimaka Zainab ta kula da me yake kallo tayi saurin dora
yatsanta a baki wai yayi shiru. Dankwalin da Radhiya ta rufe kafa dashi shi ta
dauka a hankali ta mayar mata dashi kanta. Sai lokacin ya iya dauke ido daga kanta
ya mayar garesu. Gaban Hadir yaje ya durkusa ya rike masa hannu yana jin kwalla ta
taho masa.
"Nasan ka gama jin duk wani labari a wurinsu Mami kuma ka gama kukanka. Kayi hakuri
ka saki zuciyarka muyi murnar sake haduwa" Zainab tace tana kallon yadda Awwab din
ya koma ingarman matashi.
Motsi Radhiya ta soma yi dankwalin yana neman faduwa aka yi sa'a ya zauna. Ita dai
Zainab a tsorace take kada ta tashi a hagu su rasa inda zasuyi da ita.
"Ina Ibrahim da Zayyan karami?" Yayi tambayar har ransa yana fatan Allah Yasa ba
wannan na kwancen da ya kasa tantance waye ba za'a kira da daya daga cikinsu.
"Sun fita cikin gari amma nasan suna hanya"
Iska ya furzar yana fadada murmushinsa "da gaske? Huhhh Alhamdulillah"
Zainab sai tayi tunanin yana murna ne don tace suna hanya. Sake kallon Radhiya yayi
shi dai hankalinsa gaskiya bai kwanta da ita ba. Kamar ta san tunanin da yake a
kanta kuwa tayi mika ta tashi zaune. Dankwalin ya zamo daidai lokacin da ta sauke
idanu akan fuskarshi. Shi ma ita din yake kallo daga sama har kasa don ya tabbatar
da jinsinta sai dai fuskarta ta tsaya masa har ya kasa magana. Kai a lailaye ga
fuskarta harda janbaki. A hankali idanunsa suka fara saukowa daga fuskar a kokarin
kure mata kallo sai ya tsaya cak a wuyanta ya kasa karasawa yana jin wani yanayi da
bai saba ba a jikinsa. A hankali ya furtawa kansa "mace ce".
Tsuke baki Radhiya tayi tana jin ba don Innawuro ce tayi mata askin nan ba wallahi
da abinda zata fara yi idan ta koma rugar Barkindo shine ta sauke mata nata gashin.
Waye wannan da ya cika mata ido ta kasa sakin baki a gabansa ya gane mata sirrinta.
Motsa bakin ta sake yi ko ihu ne ta kwarma musu amma ta kasa. Kumatunta na dama da
yake lotsawa idan tayi yunkurin magana shine ya sake daukar hankalin Awwab ya kuma
kallonta da kyau.
"Kaddai? Nooo it can't be." Ya nanatawa kansa da sauri. Girgiza kai yayi shi kadai
gamo da Radhiya yana nema tafiya da nutsuwa da tunaninsa.
Su Fauziyya da suka taho yi masa barka da zuwa kowacce tayi shiru kamar ta hadiyi
kota suna jiran su ga me Radhiya za tayi. Dankwali dai gashi nan amma rabin kai a
bude yake. Hannunta ta dora a ka taji iya ina ne a bude. Tana ji ta janyo dankwalin
a hankali ta tashi bata ce komai ba ta bar falon.
Karar kofa suka ji da karfi wadda ta gwara saboda bacin rai. Zainab ta girgiza kai
su Zayyana jiki yayi lakwas. Awwab yana lura da yadda suka sauya su duka ya daure
yace "Alheran?" Da sigar tambaya yana tsananta addu'a kada ace wannan ce da ta
tashi yanzu.
Kamar jiransa suke suka bushe da dariya gabadayansu. Alheran din da yaci burin gani
har ya kasa zaman Katsina ce. Babu wanda ya tsammaci zuwansa Kano a yau ana tunanin
zai zauna ya huta amma doki ya hana. Ghazalatu har fushi tayi ya bata hakuri da
alkawarin zai dawo washegari. Kin zama tayi a gidan yayi mata shiru da yawa ta tafi
gidan Alh Baba wurin kakarta.
"Ita ce ta shige ciki yanzu" Zainab ta bashi amsa da dan murmushinta.
Da ba don da kanta ta amsa masa ba zai ce ko wani salon tsokana ne kuma suke yi
masa don ansan yadda ya damu da ita kuma ya matsu ya sake haduwa da ita.
Da hannu ya nuna hanyar da ta bi ya marairaice fuska "wannan din?"
Basu dena dariyar ba kuwa Zainab tace "yau idan kuka shiga hannunta ko kafata
bazaku gani ba"
Rige rigen bashi labarin Radhiya suka shiga yi kowa tana fadin nata. Awwab bai san
lokacin da ya saki murmushi ba wato bata chanja ba kenan daga sanin da yayi mata.
Shiru kusan minti ashirin bata dawo ba abinda bata saba ba. Hadir yana ta kallon
kofa Zainab ta fahimce shi tace su dubo mata ita.
"Mama gaskiya ki tura Zayyana ita ce karama"
"Wani sabon abu ne kuka koya a aikeku ku tsaya zaben mai zuwa?" Awwab yace yana dan
bata rai.
"Radhiyan ce ai Hamma"
"Come on tashi ki karawo min ita Zayyana"
Tana zumbura baki ta shiga kofar hanyar dakunan. Tun kafin ta karasa take jin
shesshekar kuka. Da dan gudu tayi sauri ta bude kofar dakin. Radhiya ta gani kwance
akan abin sallah tana kuka fuskarta har tayi ja.
"Uhmm Adda Radhiya kizo inji Hamma Awwab"
Zumbur ta tashi zaune Zayyana ta dan ja baya kadan ta share kamar bata gani ba,
cikin yanayin damuwa tace "shi wannan na falon shine Hamma Awwab din?"
"Eh"
"Kunci amanata! babu wanda yace min zai zo kuma aka ki tashina daga falo da zai
shigo" Radhiya tace tana sake fashewa da kuka. Yanzu da wane ido zata kalli mutumin
da taci burin haduwa dashi saboda irin labaran da ake bata. Ance mata sun shaku da
tana karama kuma yana sonta sosai. Ashe ma ya zama dan gayu irin haka kamar likita
amma aka bari ya ga askinta.
Zayyana komawa tayi tana jin tausayin Radhiya. Ko ita ce da kwalkwal bazata so ace
kowa ya gani ba.
"Ina take?"
"Kuka take yi Mama"
Da 'yar damuwa a fuskarta tace "Yanzu dai Awwab duk kaine ka janyo wannan rigima da
ka ga kanta, yau ban san yadda zamuyi ba"
"Ni kuma me nayi daga zuwana" Su Zahra ya tsare da idanuwa "me yasa baku tasheta ta
rufe kan ba?"
Kusa dashi Zayyana ta zauna "haka tace wai munci amanarta da bamu tasheta ba ma"
Samun kansa yayi da rashin jindadi, ba haka ya tsara haduwarsu ba. Garin yaya ma
aka yi mata aski irin haka don Allah? Sallamar Ibrahim da Zayyan ita ta katse
tunaninsa. Zaratan samari ne dake ganiyar tashinsu.
"Kunga Hammana" suka ji Zayyana ta fada tana murmushi ta nuna shi.
"Naki ko namu?" Ibrahim yace yana mika masa hannu.
"Da gani kaine Ibrahim, sau biyu Zayyana tana kawo min kararka. Baka san ba'a
tsokanar autar Daddy ba?" Awwab yace cikin sakin fuska.
"To kace ta dena shagwaba ko muma mu fara ko Emzee, mu dinma duka autoci ne"
Kalmar tasa ta karshe ta sanyasu dariya. Awwab ya kalli Emzee yaron is very calm
sai murmushi da yake yi kawai. Ji yayi ya burge shi, a fuska ya tuna masa da
babansa Zayyan sosai amma wannan Zayyan din da gani ba mai hayaniya bane. Hannu ya
mika masa suka gaisa Emzee yana dari-dari ba kamar Ibrahim mai saurin sakewa da
sabo ba.
"Dama kai nake jira taimaka ka fito min da yayarka wadannan duk matsorata ne" ya
nuna su Fauziyya.
"Kin fitowa tayi?" Ibrahim yace da mamaki "kullum fa zancenta idan ka dawo zata
dena kula kowa a gidannan"
" 'Yan cin amana sun saka mana ido ya muka iya yau sunci amanarmu" Awwab yace yana
aron kalmar da Zayyana tace tayi amfani da ita.
Ibrahim yace "Mama me suka yi mata?"
Zayyana ce ta bashi labari kafin Zainab ta soma magana.
"Anci amana gaskiya, bari na koma cikin gari na kwana don ga dukkan alamu yau
mutanen gidan nan zasu kwana da balotelli"
Emzee ya daki kafadar Ibrahim suna dariya kafin ya nufi dakin. Tana nan zaune hanci
ya kumbura, idanu sun kankance sunyi ja saboda kukan da tasha. An cuceta da aka
aske mata kai. Da an bar mata na zaman falon da ta roka ko babu komai zai rufa mata
asiri yau.
"Adda kizo inji Hamma Awwab"
"Ni fa gida zan tafi"
Daure fuska ta ga yayi "ke babu dama ranki ya baci sai kice zaki je gida? Idan Ummi
taji abinda kike yi a gidannan zata ji dadi ne? Kowa na tsoron bata miki rai kina
jin dadi kamar abin kirki"
Mamakinsa ta soma yi. Emzee din da babu ruwansa ko me tace ta zauna shine yake mata
fada. Jan hanci tayi "to ba kaina suka bari ya gani ba"
"Ance iska kika je sha, kina da wannan kan da kike boyewa ki rasa wurin shan iska
sai falo. Yanzu da Kawu Zakari ne ya zo fa?"
"Bakinka ya sari danyen kashi, wannan ai mugun fata ne." tace tana harararsa ta
tuna wanda ya dan gani a gidan Baffa Gide.
"Tunda Allah Ya rufa miki asiri ba shi din bane ba sai kawai ki basar ba irin a
zuwan baki ma san me ya faru ba. Da nine ke fa wallahi da magagin baccin karya zan
bar falon"
Sauran hawayen ta goge da bayan hannunta tana dariya harda kyakyatawa "shege Emzee
ka iya bada shawara Yasin"
"Shine zaki zageni to" ya harareta yadda take masa.
Dan ture shi tayi bayan ta daure kanta da dankwali ta saka hijab "wasa ne dalla"
ita ce a gaba yana bayanta. Sai da suka zo bakin kofar ta kasa fita tana jin kunya.
Emzee na zuwa ya turata ta soma turjewa amma da ta ga kowa ita yake kallo sai ta
dake yadda yace mata ta basar.
Duk da kumburin fuskarta bai hana Awwab sake gano kamannin wannan Alheran din mai
askakken kai da 'yar karamar kanwarsa mai rigima ba. Ta girma amma tana nan da dan
jikinta don tafi karfin a kirata ramammiya sannan baza'a ce ta shiga sahun lukutaye
kai tsaye ba. Radhiya a dire take ta ciko ta ko ina. Da kadan ta dara Zayyana a
tsayi ita da ake yiwa kallon doguwa saboda tsayin kafa.
Yayin da Awwab ke kokarin hada ido da ita, ita kuma su Zahra ta kalla tana ta
kokarin kada ta kalle shi. Tunda Emzee yace ta basar to fa basarwar zata yi.
"Shine baku tasheni nayi sallah da wuri ba Adda Zahra"
"Naga baccin naki yayi dadi ne"
Sai ta maida hankalinta ga Ibrahim "ka fadawa Umma ina gaisheta?"
"Tace kafin ku koma kije kiyi mata kwana biyu"
"Mama gobe zaki sa ya rakani?"
"Sai dai jibi Radhiya. Gobe asibiti zan kaiki ko har kin manta?" Asibiti za ta
kaita saboda makeron da yaki barin gashinta yayi abin kirki.
Awwab sai binta yake da ido tana ta jan mutane da hira banda shi kamar ma baya
wurin. Sai da Zainab tace "wai baki ga Awwab bane?"
Radhiya ta wani bude baki da idanu irin mamakin nan "laahhhh Mama yaushe yazo?
Hamma, oyoyo"
Emzee tashi yayi ya sulale daga falon saboda tsabar kunya. Radhiya halinta sai ita.
Yace ta basar kamar ba'ayi ba shine zata nuna bata ganshi ba gabadaya. Ji yayi
kamar ya saka kuka da ma bai bata wannan shawarar ba.
"Baki ma ganni ba sai yanzu?" Yace yana kallon fuskarta. Dimple dinnan da yake saka
yatsansa a ciki idan tana dariya yake kallo yana tuna masa rayuwar da.
Dakewa tayi abinta "ina na ganka na fito ina ta hira da 'yan uwa, yaya hanya? Ka ga
Ummi?"
"Baki ganni ba da kika tashi daga bacci dazun nan?"
Radhiya an koyi basarwa da gaske ta wani langabe kai "yaushe? Ka dade da zuwa ne?"
Wai raina masa wayo zata yi ne? Kowa kallonsu yake yi ana dariya kasa-kasa. Hadir
kansa murmushinsa ya kusa zama dariya da ya gane so take ta nuna bata ganshi ba.
Awwab da bai fahimta ba dama shima anyi masa tambarin wauta idan abin dan farin
nasa ya tashi yace "dazu fa kin farka har muka hada ido."
Tsuke baki ta soma yi. Ya kamata idan ta basar sau daya kawai a wuce wurin amma sai
neman jan zance yake yi.
"Ni din? Bacci fa nayi a kan kujerar nan sai farkawa nayi na ganni a daki su Adda
Zahra sun rikeni sun kaini saboda nauyin baccina, ban san lokacin da ka shigo ba"
Zahra ta soma kifta masa ido akan ya bar zancen haka shi kuma ya dage sai ya ga
abinda ya turewa buzu nadi.
"Lokacin da abin kanki ya zame haka " ya kwatanta da dan jan dankwalin Fauziyya "
har na ga kan...."
Ihu ta saka ta tashi da sauri tana jin kamar taje ta toshe masa baki kada ya karasa
fadin ya ga kanta. Kamar zata yi kuka take kallonsa "idan nace ban ganka ba sai
kawai ka yarda haka ake yi ko Em..." shiru tayi ta shiga waige da ta ga baya wurin
"ina Emzee?" Tayi tambayar tana kallon Ibrahim da dariya tasa ko magana ya kasa.
"Ya fice"
"Ku ga min shegen yaro, shi yace idan na basar kamar ba'ayi ba komai zai wuce."
Gabadaya falon ya sake kaurewa da dariya. Zainab ta tashi ta kama kujerar Hadir
"bari naje na bawa babanku magani, Fauziyya ku kawowa Awwab abinci ko ruwa bai sha
ba tunda ya shigo kun saka min 'ya a gaba"
Gani tayi ya dace su baiwa yaran wuri don ba ta biye musu ana tunzura Radhiya ba.
So take Awwab ya so kanwar tasa da wuri, gara su fara sabawa da juna. Taimakawa
Hadir tayi ya kwanta ta dauko takardun asibitin ta koma kusa dashi tana yi masa
bayanin kowanne don neman shawararsa. Da ido da yanayin chanjin fuska take fahimtar
abubuwa da dama da yake nufi idan tayi masa tambaya.
Sakale tayi tana kallon Awwab yana murmushi "ban san haka kike so ba, to koma ki
sake fitowa. I promise zan tayaki basarwa"
Ita ma sai da abin ya bata dariya ta koma ta zauna tana jiran fitowar Emzee ko ma
ina yaje ya buya. Dama idan ba ganganci ba me zaisa ta karbi shawararsa.