Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
sai ma goyon baya da su ka baiwa Mama aka
korasu yau su kwana a gidansu.
Ummi da Radhiya ne suka yi girki yayin da Zayyan yake sake jin daukakar da Emzee
yake samu a NDA tun shekararsa ta farko. Ya yaba kwarai da dan nasa yana jinjinawa
a ransa wannan wai magajinsa ne wanda bai barshi ta ko ina ba...suna da aiki.
A kasa Radhiya ta ajiye musu abincin Zayyan yace ta dauko babban plate yau a kwano
daya zasu ci ya ga girman lomar kowa. Da dariya aka soma ci sai gashi su hudun sun
buge da zubar hawaye lokacin da ya kallesu daya bayan daya yace "ko yanzu mutuwa ta
riskeni zan tafi ina mai farinciki da cika godiyata ga Allah."
Ummi ce ta fara hawaye sai Radhiya ta kama harda shessheka. Emzee ma duk dauriyarsa
sai da yayi "don Allah ni dai a dena kukan nan abincin da dadi amma zaku sa ya fita
daga raina"
Dundu Ummi ta kai masa "acicin kawai"
"Zancen gaskiya Ummi. Ba abin nayi fuska na gama ci sannan nayi nawa kukan ba na
rasa me tayani"
"Ashe haka kake Zayyan? Shiyasa Malamijo yace yana nemanka kaje da bindiga ko ta
katako ce"
"Nemana kuma Daada?"
Ummi ta amshe da fada musu sakonsa na dazu "sai ku shirya zamu tafi tare. Zamu
barku a can mu wuce Sakkwato daga can muje Nijar"
Radhiya ta rike baki "Ummi wai ni din da gaske yace ko dai kin fada ne kawai don
kada nace baya sona"
"Kaniyarki" ta kai mata duka Zayyan ya tare yana cewa babu mai taba masa uwa.
"Da gaske nake Daada, cewa fa yake yi idan yaji muryata gabansa faduwa yake yi" ta
turo baki da takaici.
"Gonarsa take zuwa tace wai dabba ta kasa tasa a yanka. Ka kuma sanshi da
dabbobinsa sarai" Ummi tace tana murmushi.
"Amma anya lafiya kuwa yake nemanmu?" Emzee yaji abin ya daure masa kai. Malamijo
fa ko waya baya kiran kowa sai dai a kira shi.
Kowa da tunaninsa amma sunfi kawowa da gaske akwai matsala. Ko ma dai meye jibi da
wurwuri zasu bar Abuja. Gara suyi su dawo da wuri Radhiya ta fara aikinta. Zayyan
yaji dadin wannan program da zata yi yace idan tana bukatar bayani game da halin da
sojojin suke riskar kawunansu a filin daga a shirye yake. Basu ankara ba suna
wannan hira sai gani suka yi daya da rabi na dare. Dole aka tashi ba don sun so ba
saboda hirar tayi musu dadi. Suna jindadin yadda iyayensu ke zolayar juna. Ummi
tace mijinta dan saurayi ne wanda ya tafi yanzu an kawo mata wanda ya fara furfura.
Zayyan yace "ko kiyi shiru ko na tona miki asiri su san cewa a wurin bin kwalaben
mutane a gidan biki kina shanye ragowar mirinda muka hadu"
"Bonono rufe kofa da barawo...ai ka gama tonawa"
Emzee da Radhiya dariya harda hawaye. A zahiri idan kewarsa ta ishi Mairama tana
bawa yaranta wannan labari amma yadda ya fada yana kwatanta yadda tayi da ya kamata
dole suyi dariya. It was a time well spent a tsakaninsu.
**********
"Ikon Allah jama'a dama Zayyan yana da dan uwa da suke mugun kama banda wadda na
gani a wurin Zayyan karami?" Alh Salisu yayi magana a lokacin da suke shiga gidan
Baba Hadir shi da yaransa ya kasa dauke ido daga kallon Zayyan din.
"Nine dai Salisu ba kama bace"
Gabansa yaji yayi wata irin faduwa ya shiga kallonsu yana jira wani yace wasa suke
yi amma shiru kake ji. Radhiya ce tayi dabarar kiran su Halifa da kannensa su ka
bita wurin Ummi.
Zayyan tasowa yayi ya kama hannun Alh Salisu wanda jikinsa ya fara rawa sai kuma ya
soma hawaye "kai din ne don Allah? Hadir Zayyan nake gani. La ilaha
illallahu....Zayyan dai nake gani."
"Nine Salisu Allah Ya dawo dani"
Mamaki da al'ajabi ne ya kama shi sosai da aka yi masa bayanin dawowar Zayyan.
Wannan al'amari da daure kai yake.
"Gashi a hanya muke ina da taro gobe da sassafe na 'yan kasuwa. Don Allah ku tsaya
a gidana idan kun shigo goben." Ita ce abinda ya fada musu karshe lokacin da suka
gama hira ya tashi.
Aka tura kiran yaran sai ga Halifa tare da Emzee yace a tafi a barshi zasu taho
gobe in sha Allahu shima yana son zuwa Sumailan. Alh Salisu yace babu matsala a
turo 'yan matan. Kusan minti goma suna jiransu suka taho da Zayyana za'a rokawa
Hibbah itama ta kwana.
Yayi dariya "Kuna tsareni da ido na isa na hana ne"
Kananan ma sai suka hau rigima saboda kaunarsu dasu Jawad da Femi.
"A'a kuma kada abin yayi yawa. Ku wuce muje su ma zasu taho gobe"
"Ka kyalesu mana nan da can duka gida ne. Dama su Alheran zamu ajiye a Sumaila mu
Kanon zamu kwana sai a kawo su gida"
Alh Salisu yaji dadi da Zayyan bai nuna fushinsa ba da ya fada masa laifinsa na
rashin kula masa da iyali. Dreban motar yaran ya roka arzikin ya koma can gidan
nasa ya kwana gobe sai yazo su tafi shi kuma ya shiga mota suka tafi.
Ga alamu Halifa ya damu kwarai da Radhiya komai ya kira ta ko ya sakota a ciki.
Yanzu ma hira suke yi take tambayarsa yaushe rabonsa da zuwa wurin Malamijo yace ya
dade sosai.
"Gaskiya kazo muje ka ganshi. Kila ma har Gwaggo Salame ba ka zuwa gidanta ko?" Ta
dan dage gira.
"Bazan miki karya ba ita ma bana zuwa yadda ya dace da ya ziyarci mahaifiyarsa.
Gidan nata ne ko hadiyar yawu bana iyawa ga yaran nan nata ko sunayensu ban rike ba
sai azabar roko"
Dan bata rai tayi "ba cikinku daya ba Halifa, ko zaka so ace wani bare suke roko?
Wai kuwa ina dayar nan bana rike sunanta"
"Rahima? Tana can nasu gidan" yace da rashin damuwa.
"Ni kuwa da zaka gyara zumuncinku da ka burgeni. Dube ku duk bamu saba da juna ba
haka su Ummi ma. Ita da Gwaggo Salame ban san yaushe suka hadu karshe ba"
"Ke Ummanmu ko gidan Malamijo bata zuwa in fada miki."
Yanayin zumuncin nasu baiyi mata dadi ba. Shi kuma da yake babba a nasu gidan sai
taji ya kamata ta bashi shawarar gyara tsakaninsa da kannensa. Ko ba komai yana
cikin rufin asiri zai kyautu ya rinka dan taimaka musu. Sunyi nisa suna tattaunawa
Awwab ya shigo yaci karo dasu suna dariya hira tayi dadi. Tuni fuskarsa ta chanja
ya koma ya kira wayarta. Tana dauka fito kawai yace ta tashi.
A bakin mota ta ganshi ya jingina bayansa ya harde kafafunsa da hannuwa a kirgi.
"Sannu da hira" yace fuska babu fara'a.
"Hira kuma?"
"Ba ita kike yi ba na taso ki"
Duka girarta biyu ta rinka dagewa tana wani juya masa ido da dariya "Chèri kishi
kake yi? Oh my, my , my sai naji na koma wata sarauniya"
Sakin baki yayi ya kalleta kafin ya girgiza kai "mutum ma baza'a barshi ya nuna
bacin ransa ba"
Kashe masa ido tayi tace "no chance baby" Wani irin kallo ya bita dashi ta tsure
"kasan Allah subutar baki ne ba baby zan ce ba"
"Ah kawai kice kin girma. Daga fara saka min sunaye nan gaba ni din zaki dauke"
Kamar tayi masa kuka ta sake cewa fitowa yayi kawai.
"Saboda shine a ranki ko? Kinji me Daada yace dai ki fara hada kayanki"
Dagewa tayi bisa subutar baki ne shi kuma yayo ta zolayarta sai gashi sun koma
hirarsu mai dadi.
"Please ni dai bana son yadda yaron nan yake shige miki. Nasan dan uwanki ne bazan
rabaku amma ni dai a kula kinji ko. Ina kishinki sosai Schatzi"
"In sha Allah Cheri amma nima fa kada kaje kana yiwa 'yan matan jirgin nan masu dan
skirt dariya wallahi. If not za ka ganni a mafarki muna fada"
"Naji...kuma banda zuwa rugar Barkindo ki rinka zuwa hira wurin Dr Zakari. Nasanki
da likitoci ba sauki"
Dariya ya bata sosai. Ita sai yanzu ta gane ashe lab attendant ne ba likita ba "ka
doke kowa fa ni sai dreba ko ba abin hawa"
Sunyi ta hira kamar kada su rabu don washegari karfe bakwai zai bar gida. Da safe
da wuri ta tashi don suyi sallama duk da wayar da suka dade suna yi cikin dare don
ma ya dage sai ta kwanta. Bayan tafiyarsa ba jimawa su Zahra su ma suka dauki hanya
ita da Raji sai kuma tawagar su Ummi. Gidan sai yayiwa su Mami shiru don ma
Fauziyya tana nan amma Ibrahim da Zayyana duk sun bisu. Shi Ibrahim zasu yi kwanaki
kadan da Emzee a Sumaila su dawo Kano gidan nasa kakannin.
***********
Tun dare Malamijo yake ya da habaici a cikin gidansa wanda Hajiyayye bata fahimta
ba.
"Gobe iwar haka watan tatse rashin mutumcin wasu zai tsaya."
Hajiyayye tana sakace hakori zazzaro masa idanu "me kenan kake nufi"
"Zancen zuci ne ya fito fili. Ko an hana magana ne ban sani ba?"
"Kayi abarka. A dai kula ne kada yawan surutun ya tasar min yara kasan halinsu.
Yanzu duk naman da suka ci sai kaji suna neman kari"
Dauriya kawai yake a kai gobe amma yana cikin tashin hankalin rashin sanin ina
shanunsa. Yau tun asuba yake gonar. Tsagerin yaron nata da yaje daukan wasu sai ya
kasa saboda ganin idonsa da wasu bakin fuskoki dole ya tafi.
"Allah Ya hada fuskokinku da sarkin mayu dai amaryata" Malamijo yace harda hade
hannuwa irin na mai addu"a.
Cikin Hajiyayye kuwa ya cure wuri guda a take kamar zata yi zawo "wannan wane irin
mugun fata ne Malamijo?"
"Ban gane mugun fata ba. Yanzu kamar ni kinsan dadin da zanji duk ranar da na hadu
da Mai Martaba Sarkin Kano Dan Lamido kuwa?"
Rai a bace tace "to meye hadin sarkin Kano da sarkin mayu?"
"Meye ne naga kin soma gumi? Namu sarkin shine sarkin Kano. Ke kuma naku Sarkin
mayu. Yadda nake son ganin namu kuma nake kaunarki shine ne nake miki fatan haduwa
da naku kema"
"To ba amin ba...kaga ni kudi nake so kamar dubu dari karshen wata yaran nan namu
kowanne ana yi masa yanka shi kadai saboda rage karfin maitar"
Allah Yaso shi ba don abinda yaji da kunnuwansa ba da yanzu hankalinsa in yayi dubu
ya tashi akan neman kudin. Amma yanzu sai cewa yayi tayi hakuri zai tanadar mata
zuwa dare gobe.
Saboda samun wuri harda yi masa tsaki tace "to a hanzarta"
"To ranki ya dade"
Matsawa tayi akan katifar tana nuna masa wuri "taho mu kwanta ni bacci nake ji"
Hadiyar yawu yayi saboda sai yanzu da yake sansano tsira ya kara tabbatar da
kazantarta da muguwar rama. Wa ya aike shi kwanciya kusa da ita karshe kasusuwan
jikinta suje suyi masa sartse ko su soke shi.
Karfe takwas na safe ya soma kiran Ummi wai yana fata yaran sun taho tace masa tare
zasu zo da ita harda Halifan Salame.
"In kin barni na ma manta da sunansa tunda uwarsa bata san mutumcina ba. Wannan
yaro ina tsammani kamaninsa ma sun bace min. Kinga sai kun taho dai. A hanzarta do
Allah"
Ta gama tabbatarwa lallai babu lafiya gidan nasu. Sun kimtsa kowa ya fito suka yi
sallama dasu Mami da Mama.
Emzee da akace ya sako kayan makaranta sai ya sami irin shirt dinnan da ake yi da
zane zanen khakin sojoji ya saka akan bakin wando. Radhiya kuma atampa ta saka da
mayafi tayi kyau sosai. Umminta kuma wani lace ne dan ubansu mai tsada da kyau ta
saka green da orange ta dora orange din mayafi da farin gilashinta tayi kyau sosai
Zayyan ji yayi kamar a dage tafiyar ko na awa guda ne ya samu ya yaba mata yadda ya
dace. Dadinsa ma mota guda Daddy ya bashi da dreba daga shi sai ita. Motar gidansu
Halifa kuma mai wuri uku ce yaran suka duru a ciki.
Abinka da tafiyar sammako da kuma rashin tsaye tsaye a hanya karfe hudu suna cikin
garin Sumaila. Shekarun baya ne suka rinka dawowa Zayyan. Zuwansa garin nan na
karshe lokacin da Mairama tazo yawon arba'in din Alheran ne. Yanzu gashi Alheran
dinsa aure yake shirin yi mata. Bacci ko na minti biyar bai iya yu ba sai kalle
kallen chanjin da aka samu. Kafin su karasa gidan Malamijo motar da su Radhiya suke
ciki ta tsaya daga bakin wata kwana. Halifa ne ya sauka ya taho wurin motar su Ummi
ya leka ta taga.
"Gwaggo Mairama nace bari naje wurin Umma na fada mata kunzo tazo ku gaisa kafin ku
wuce Kanon"
Zayyan bai manta da wace Salame a baya ba kuma har yanzu ba wai yana dokin ganinta
bane. Ya kula Halifa yaro ne mai nutsuwa daga jiya da suka kwana gashi uwa uba da
ga Alh Salisu. Jiyan da Mairama taso sanar dashi cewa sun rabu da baban Halifa
saboda kada yayi masa maganarta sharewa kawai yayi.
"Ta san da zuwan naka ne?" Ummi ta tambayeshi.
"Bata da waya amma nasan zata zo ko don ta tayamu murnar dawowar Daada" ya kare da
murmushi.
Suna kallo ya gangara daga baya sai ka rantse wani babban Alhaji ne. Girman jikinsa
da irin shaddodi da yadikan da yake sakawa suke kara masa cika ido.
Malamijo yau ko kofar gida bai leke ba yana jiraj zuwan bakinsa. Abinci biyu akeyi
yanzu a gidan nasa. Nasu Yadikko daban na amarya da iyalinta daban. Kunya tasa bai
iya fadawa Yadikko zuwan bakin da bai ma san suna da yawa ba kuma. Ita ranta ya
dade Hajiyayye kuma babu dalilin da zaisa ya fada mata. Dirin mota yaji yana
kashingide a tsakar gida daga shi sai dogon wando da 'yar shara duk sanyin nan ba
ji yake sosai ba ya tashi da sauri kai baka ce tsoho bane mai shekarunsa sam baya
jin jikinsa. Silifas dinsa ya saka yana washe bakin nan Hajiyayye ta fito daga
kitchen da katuwar cooler shakare da farar shinkafa 'yar gomnati ta dafawa 'ya'ya
zasu zo su ci banza.
"Ina kuma zaka je kake wannan saurin? Ga abinci ka jira in dan tsakura maka ladan
ganin ido ko"
Bai ma jira masu tare masan sun shigo ba ya dora hannuwa a kugu ya daure fuska "a
cikin gidan nawa kike zancen tsakura min abinci? Ashe baki da mutumci ban sani ba.
To ki jira in dawo ciki zaki ga yadda zanyi dake mutuniyar banza"
Ta tsorata sosai amma sai ta dake kada tayi saurin nunawa "ni Hajiyayye kake yiwa
wannan magana? Ko magagin baccin da ka soma ne bai sakeka ba?"
Kallon banza yayi mata harda su juya idanu yau take sallah fa a wurinsa ya fita a
gaggauce. Kiris ya rage ya saki fitsari da ya ga 'ya'yan Hajiyayye ne ashe a akori
kura manyan mazan su uku katti dasu tamkar ba daga cikinta suka fito ba. Dirowa
suka yi daga bayan motar suka cewa dreban yaje gidan gonar ya jirasu. Zasu ci
abinci ne su zo a dauko shanu ko hudu ne idan motar zata dauka. Idanun Malamijo sai
suka kawo ruwa ya fara kokawa da kwalla. Samarin suka sauko kai cikin gidan suna
muzurai su a dole mayu 'ya'yan mayya. Tsabar wulakanci basu duba tsufansa ba suka
ringa bangazar kafadarsa suka shige cikin gidan. Jiki a sanyaye ya juya zai koma
sai ga wasu galla gallan motoci guda biyu sun doso gidan.
Ihu ne kawai baiyi ba don tsananin murna ya koma daga soron ya tsaya yana jiransu.
Jin kansa yake daidai da kowane maye da yake cikin gidansa.
Emzee da Ibrahim ne suka fara shigowa ya tarbesu cikin nishadi. Sai 'yan mata
Hibbah da Zayyana sannan Radhiya ta biyo bayansu.
"Malamijo nawa" tace tana murmushin da ta saba idan zata yi masa tsiya.
"Yanzu ace kin zo kasar 'Yar soja bazan ganki ba sai nayi cigiya? Ina Mairaman
take? Duniya Mairama duk tafi sona kaf 'ya'yan babu mai girmama maganar Malamijo
kamar ta." Yayi maganar batare da korafin Radhiya kada tayi masa wani abu ba daidai
ba a cikin gidan.
"Uhmm Malamijo tare fa muke da..." Emzee ya soma fada masa saboda yana tunanin gara
ya sani kada abin yazo masa a bazata.
Hannu ya yarfe gefe yana kallon Mairama da wani mutum yasha yadi na maza mai
masifar kyau da tsada cikin wanda Baban Arifah yasa aka dinka masa.
"Ko ma waye su zo ku hadu ku ci uban 'yan iskan gidan nan"
"Su wa kenan?" Radhiya tace da doki sai dai Malamijo baya ma jinta ko kadan.
Mutuwar tsaye yayi hannunsa a kahon zuci yana farfar da idanu bakinsa ya kasa hada
kalmar Zayyan da yake son ambata.
Zayyan na karasowa da murmushinsa ya mika hannu ya riko hannun daman Malamijo. Ai
hannuwansu na haduwa Malamijo yayi sharaf a sume ya fado masa a jiki.
Dama sun sani dole ya tsorata. Emzee ya rugu zai daga shi Zayyan yace ya wuce su
gyara inda zai kwantar dashi ya ciccibe shi shi kadai tamkar ya dauki yaro karami.
To abu ne babu body babu alamar body. Dama ya lafiyar kura...tuntuni babu jikin
Hajiyayye mayya tazo ta karasa gawar da ba tata ba.
Tsakar gidan babu kowa sai gayyar su Hajiyayye rashin wadatar dakin yasa ta dawo
dasu nan duk da ma dai akwai sanyi garin. Banda cooler din shinkafa a gefe ga ta
miyar da ta wadatu da nama na tinkiyar da suka dauko jiya ga salad da su tumatir
yau din bushasha za'ayi saboda jiya sun tarki sa'a. Shanun da suka dauka suna ajiye
a gidan Talle ranar kasuwar dabbobi zasu kai a kwashi naira.
Da sauri Emzee ya shigo sabuwar tabarmar da ta shimfida yaran nata sun soma zama ya
murtuke fuska duk da bai sansu ba "kai ku tashi"
"Yaro kai kuma daga ina?" Babban cikin nasu ya tambaya yana masa kallon raini. Ido
kawai Emzee ya watsa masa yaja baya da sauri. Tsabar training sai budewa kwanjinsa
yake yi musamman daga kirji, hannuwa suna murdewa irin na kakkarfan namiji. Rigar
jikinsa ma kusan ta kama shi ita ta karasa tona asirin yanayin jikin nasa. Wanda ya
rage akan tabarmar mai bin babban ya kalla yayi masa alamar ya tashi.
"In naki fa?"
Emzee bai sake tunani ba ya ja tabarmar ya kifar dashi a wurin ya koma gefen dakin
Malamijo ya shimfide masa ita sannan ya shiga ya dauko masa filo. Radhiya dakin
Yadikko tayi da sauri ta same shi a rufe da karamin kwado sai ta je na Hajjo. Nan
ta tarar da komai ba yadda ta sani ba sai karajin Hajiyayye daga bayanta.
"Ke daga ina kuke ne kike leka min daki?"
Da mamaki tace "dakinki? Ina Hajjon kuma?"
Daidai nan Zayyan ya shigo da Malamijo a hannu ya kwantar dashi a inda Emzee ya
nuna masa Ummi tana take masa baya hankali a tashe.
"Ku su waye ne?" Hajiyayye ta matso inda suke ta kalli Malamijo ta watsar.
Cikin salama Ummi tace mata "ni 'yarsa ce wadannan kuma yarana ne da babansu"
Tsaki taja duk da suturun jikinsu sunyi mata kwarjini amma bata so raini ya shiga
tsakaninta dasu. Yadda uban yake tsoronta to kowa ma fa yaji tsoro kada a kawo mata
wargi ba dauka zata yi ba.
"Me ya same Malamijon?" Tace a dakile wanda tuni ran kowa ya sosu.
"Tsorata yayi ya suma" Ummi ta bata amsa.
"uhmmm" ta tabe baki "bana son hayaniya kamar yadda shi uban naku ya sani a kiyaye"
Hayaniyar da take yi ce tasa mutanen cikin gidan suka fara lekowa ganin da wa take
yi. Na'e ce kawai da wasu