Advertisements
Chapter 43 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   43 / 99

126K to 129K   out of 295.8K words

ya riga ya faru amma sai
tado zancen kike. To wa zaki burge cikinsu? 'Yan uwan matar nan suna da arzikin
kula da ita da yaranta, meye don nima naci daga arzikinsu. Ba wan ubansu nake ba?"


"Hakkinka ne da zaka ci?"


"Ho Jume, kin ma manta lokacin da ki ka matsawa Zayyanun da kanki akan ya baki
kudin gadonsa."


Sai da taji ba dadi da ta tuna irin abubuwan da ta rinka yi wa Zayyan a wancan
lokacin. Gashi ya tafi ya bar mata duniyar dan cikinta ya zame mata kadangaren
bakin tulu.


"Kinga ni tashi zanyi daga gidannan nan da sati guda zaki huta da ganina. Gobe zan
zo da masu aikin kwashe kaya" yana kaiwa nan yasa kai ya fita ya bar mahaifiyarsa
da kunar rai.


Majalisarsu yaje ya zauna gefen wani gida inda suke wuni suna buga karta, gulmar
duk mai wucewa da kallon 'yan mata. Hira suke gasu dai magidanta amma babu mutumci
a tare dasu sai kyakyata dariya suke abinsu. Da yake lungun motoci bazasu iya shiga
ba daga gefen titi suka yi parking sojoji suka rinka durowa daga motar harda masu
bindigogi kirar AK47. Hankulan jama'a tuni suka tashi ana tunanin yau ko lafiya
unguwar. Da karfinsu suke tafiya Baffa Habubakari da dansa Manu nadamar biyo wannan
zugar sojoji suke yi. Tsoro suke kada su manta cewa tare suke a kafta musu hancin
bindiga.


Su Maikudi sai gani suka yi mutane na shigewa gida da sauri ga sojoji suna tafe da
sassarfa. Wasu cikinsu zasu tashi ya ce su zauna.


"Meye abin tsoro a soja, kanina ma har ya rasu soja ne. Ko wane mai tsautsayin suka
biyo har cikin unguwa don jaraba wa ya sani"


Kamar ance ya kalli tsakiya ya hango wani mutum cikin shadda dinkin tazarce ya
karkace hula yana rike da sanda ruwan kasa daga samanta da yake a lankwashe kasan
kuma baki ne. Dogo ne kakkaura mai cikar haiba da zati.


"Banten uba" Maikudi yace da ya tabbatar wannan mutumin ne da suka zo neman Radhiya
da uwarta kwanakin baya. Jikinsa har mazari yake don tsoro garin sauri ya bar wurin
ya cambala kafa a cikin kwatar gabansa. Bai ko damu ba ya soma sauri. Captain
Onomza ya gane shi da sauri ya bada dokar a damko masa shi.


"Don't let him get away" yace da karfi.
Mutum daya ne yayi kukan kura ya kwaso Maikudi gabadayansa sai gashi kwance a gaban
Captain Onomza.


Hanjin cikin Maikudi ya buga wani uban sauti shi ba na yunwa ba shi ba na lalacewar
ciki ba. Kallonsu yake tsakanin Major Mustapha da Captain Onomza wanne ne zaifi dan
dama dama wurin sassauci. Yawun bakinsa duk ya kafe ya laso lebe ga gumi ya fara
jika shi. Muryarsa kamar an takewa muzuru jela da takalmin karfe yace da Major "me
yayi zafi ne haka ranka ya dade? Yarinyar nan da kaina zan kaika garin da suke. Ko
makon da ya gabata naje na fada musu kazo kana nemansu shine uwar tace babu inda
zasu je. To amma yanzu tunda anyi haka ina maka rantsuwa irin ta addinin Islama ko
a ka ne zan dauko Radhiya na kawo maka. Kai harda kanin nata Zayyanu."


Gigitacciyar tsawar da Captain Onomza ya daka masa ita ta janyo mararsa ta saki
fitsari ya soma tsartuwa. Mutane har sun fara fitowa kallo tunda sun fuskanci an
kama wanda aka zo dominsa.


"Nine ka yiwa kerya yace min wife na Lt Zayyan yayi aure, baby ya mutu and you have
the girl with you. Ko ba anyi haka ba"


Idanun Maikudi kamar an kasa kwai a faranti sunyi tsilli tsilli yace "ni ban
fahimci me kake cewa bare na baka amsa"


Wawan mari ya dauke Maikudi dashi sai ji kake garam-garam masu leke suna komawa
inda suka fito ana rufe kofofi. Captain Onomza da ko cikin sojojin ma ana tsoronsa
saboda baya sassautawa mara gaskiya shine Maikudi zai kawowa wargi.


A take habo ya kama Maikudi. Major ya kawar da kansa su Baffa jiki ya hau tsuma. Da
sunsan abin zai hada da sojoji babu abinda zai fito dasu daga rugarsu.


"Ka fahimta wanna ko"


"Kuyi hakuri yallabai yanzu me kuke bukata?"


"Bundle him up"


Mutum biyu ne suka taho kan Maikudi aka cukwikuye shi guda ya saba shi a kafada
yayi gaba dashi.


Major da Captain Onomza suka sake gaisawa Captain din yace zai kira shi ya tabbatar
masa a daren yau kafin gari ya waye Maikudi zai fadi ina kudaden marayun suke.
Gidansu na Kano ma zai fadi me yayi dashi haka zalika idan yana da hannu a dauke
kafar da 'yan uwan Innar Zayyan suka yi shima duk zai fada da bakinsa. Da sassarfa
suka bar lungun sannan Major yace su shiga gidan.


Jume bata yi mamaki ba bayan ya gama mata bayanin me aka yiwa dan nata.
"Yanzu sai yaushe zaku sake shi?" Ta tambaya cike da jimami ga matarsa da yara suna
kuka don labari ya iso gidan tun kafin shigarsu ma.


"Sati daya zaiyi in sha Allah"


"Yanzu babu wani abu da zaku iya yi a fitar dashi?"


Wani murmushi Major yayi da ya tabbatar musu babu wani abu da zasu yi da zai sa ya
fito da Maikudi. Dole Jume taji babu dadi amma dan nata yana bukatar saiti ita
kanta ta sani. Su Major sun tafi akan idan da wani abu zai nemesu.


"Uhmm nace ko zaka nemi Mal.Aminu. Aminin Malam ne da suke zuwa Nijar din tare,
dashi akayi komai na auren Malam din da ita Innar Zayyanu"


Godiya Major yayi mata suka rabu zasu dawo washegari a raka su gidan Mal. Aminu.


Captain Onomza baiyi sanya ba wurin ganin Maikudi ya samu tarba irin wadda ta dace
da macuta irinsa. A wannan daren ya bambance aya da tsakuwa, ya gane waye soja da
hatsarin dake tattare da shiga hurumin sojoji ko da a bayan ransu ne. Mutane ne
masu hadin kai da tsayawa juna domin kare martabarsu koda a bayan idanunsu ne.
Abinda ya kara tunzura Captain Onomza shine takaicin ace dan uwa na jini ne da
wannan muguntar. Kuma ya rasa wa zai ha'inta sai iyalin Zayyan dinsu.

**********


Matafiya suna ta shiri an gama wanka da cin abinci. Ummi da Mami ake jira basu gama
hirar da suka dauko ba bayan wayar da suka gama da Mama Zainab. Zuwansu asibiti
jiya likitan da suke gani ya gama bincike akan likitocin da ake kira neurosurgeons
inda cikin sa'a ya sami wani kwararre da zai je Kuwait sati biyu masu zuwa. Likitan
dan asalin kasar Philippines kusan yawo yake kasa kasa yana duba patients. Matsalar
dai bata wuce samun shiga gurbin appointment dinsa ba karamin abu bane. Yini guda
suna ta cuku cuku aka cusa Hadir a matsayin patient na karshe da zai gani a wani
babban asibiti a Kuwait. Ba komai yaja hankalinsa ya karbe shi ba sai dadewar da
Hadir yayi da lalurar da kuma jin cewa soja ne da ya sami rauni a filin daga.
Tsananin rabo da addua suka sami alfarmar nan. Kudi dai Zainab zata kashe ba na
wasa ba abu ya tasarwa miliyan tara. Zuciyarta ta karye hankalinta ya tashi. Idan
ta bayar da wannan kudaden hakika zata tagayyara jarinta. Allah Ya taimaketa akwai
kayan da tayi order daga China dake kan ruwa da basu sauka ba. Sune zasu riketa
idan tayi sa'ar kasuwa.


Mami ta kwantar mata da hankali za ta sanar da Major domin nauyin ba nata bane ita
kadai. Ummi bata bata lokaci ba itama wurin neman Innawuro a waya. Shanu biyar
cikin abinda iyayen nata suka bata bayan ta koma hannunsu manya manya ta roki
alfarmar a saka a kasuwa a ga nawa zasu samu. Dama ajiyarsu take saboda karatun
'ya'yanta da auren Radhiya idan ya taso.


"Abinda za'ayi Mami ku tafi da Karami domin su hadu da Ibrahim su taimaka mata.
Bikin namu na kwana daya ne ana kai amaren washegari zamu tafi Kanon mu jira har su
tashi"
"Baiwar Allah wallahi ina tausayin Zainab. Hadir ya godewa Allah bana jin zai taba
haduwa da matar da zata kaunace shi rabi rabin yadda Zainab take yi"


Murmushi Mairama tayi ta bata labarin da Zayyan ya bata tun yana raye na ainihin
waye saurayin Zainab din. Sun sha dariya su biyun yadda abotar su ta kasance.


Kowa ya shirya sun fara fitowa amma babu Radhiya har Mami sai da tayi cigiya.


"Tana kwance inda tayi sallar asuba tana bacci"


"Bacci kuma?" Mairama tace tana mamaki don Radhiya ba mai baccin safe bace musamman
ma dai na yau da su Mami zasu koma.


"Taso ta Fauziyya tazo kuyi sallama"


Mami tayi saurin hanata "A'a wallahi ku dauko kayanku mu tafi. Nasan bai wuce
gajiya ba"


Kusan kwana tayi tana kukan hotunan wayar Awwab. Duk da ya goge takaici take don me
yasa ya tsaya har mace ta saka masa abinci a baki. Wannan ma salon ya jawo musu
zagi ne ace yayanta bashi da kamun kai. Ko mutum nawa ne suka gani? Mata nawa ya
bawa ko suka bashi abinci a baki? Alawar da ya bata ma sai da ta tuna ko sun taba
yin haka da wata kafin ita. Wannan yafi tsaya mata a rai taci kuka ta godewa Allah
shine fa bacci yayi awon gaba da ita da asuba.


Ghazalatu dama jira take kowa ya fita daga dakin ta zauna kamar tana gyara daurin
dankwali. Zahra na fita ta fiddo wayarta taje ta zame hijabin Radhiya da babu
dankwali ta kasansa a hankali wani bangare na kan ta ya bayyana tayi saurin
daukarta a hoto tana kunshe dariyarta. Awwab zata nunawa kawai don ta rage karfin
alakarsu duk ta yadda ya samu.


Awwab da yasan yadda ya rabu da kanwar tasa ya shigo tsakar gidan ya kai sau biyar
ko zai ga gilmawarta. Da yaji ance bacci take yi hankalinsa tashi yayi fiye da
zatonsa. Ta yaya zai tafi bai sake ganinta ba sai nan da sati biyu. Walwalar
fuskarsa gabadaya ta bace yana jin kansa sukuku suka fito. Rakiya harda Malamijo
shima yana cigiyar jikarsa mai fitina akace tana bacci.


"Kun taba jikinta kuwa lafiya take babu zazzabi? 'Yar sojan ce zata yi bacci har
goma na safe indai ba kwaya ta soma sha ba". Dariya ya basu sosai.


"Mami ko dai bata da lafiyar? Hancinta na gani yayi swelling da saman idonta" inji
Zayyana.


Ummi tace "ko ma meye ku bari su tafi a taso ta don yanzu tana zuwa sai ta bata
musu lokaci"
Ba dai kukan ta sake yi ba Awwab ya tambayi zuciyarsa. Tamkar kada su tafi haka ya
rinka ji. Ghazalatu motarsu ta koma Zahra ta shiga wadda su Mami suka zo don kada a
barta ita daya.


Kusan awa daya da tafiyarsu bayan Radhiya ya soma damunta saboda kwanciyar kasa ta
bude ido tana mika. Dakin shiru babu kowa ta tashi da sauri babu jakunkunansu sun
gyare dakin da katifar. Nauyin bacci gareta shiyasa bata ji motsinsu ba. Gabanta na
dukan uku-uku ta garzaya dakin Hajjo wurin Ummi.


"Ummi sun tafi ne?" Tace cikin tashin hankali.


"Ina hankalinki ne, babu sallama babu gaisuwa"


Fita tayi ta dawo cikin sauri ta gyara kuskurenta sannan ta maimaita tambayar da ta
riga tasan amsarta tunda bata ga Mami ba kuma babu kayanta.


"Sun tafi kina can kina bacci. Ko baki da lafiya ne?"


Hawaye ne ya taho mata tayi kokarin boyewa "shine basu tashe ni ba?"


"Kiji dadin isarsu da surutu ba. Sun wuce da Karami zai zauna a Kano..."


Alamun kukan Radhiyan taji ta dakata tare da mika hannu inda take jin sautin tun
yana tashi a hankali har yayi karfi. Wani irin kunci da bacin rai take ji hade da
gagarumar kewar Hamma Awwab. Me yasa bai ce a tasheta ba sunyi sallama. Me yasa
daga zuwansa zuciyarta take shiga mabambantan yanayi daga tsananin farinciki sai
bacin rai irin na jiya da ta ganshi da mata. Yau kuma don bai damu da ita ba yayi
tafiyarsa.


"Ke menene?"


"Ummi ba komai" ta amsa muryarta na sake karyewa. Ta dauki kanta jarumar mace mai
dauriya amma lokaci kalilin ta zubar da hawaye fiye da tunaninta. Ita kanta bata
san me ya sameta ba sai an mata karin bayani.


Tun Ummin ta na rarrashi har ta koma fada amma taki cewa komai sai kuka. Daga
karshe karamar wayar da Mami ta bar mata ta dauko. Ba kudin sayen bane dama ta rasa
sai dai karancin wadanda zata kira. Emzee da Radhiya kuwa taki saya musu ne duk da
tasan ana yayinta sosai tana jiran su gama sakandire.


"Ungo ki kira Mami da sauran 'yan uwanki ku gaisa kiyi musu sallama kinji 'Yar
sojan Daaadaa"


Ba wuya anci galaba a kanta. Bare kuma rarrashi daga Umminta sai tayi dan murmushi.
"Kyalesu ni na fasa tunda basa son tawa sallamar" ta basar a zuwan taba damu ba.


"Ke dai ki karba kafin ki zo da kanki na hana"


Sautin dariyar Radhiyan taji ta girgiza kai. Wannan yarinya sai addu'a. Radhiya na
kira da taji ta shiga sai kuma kunya ta kamata ta mannawa Umminta wayar a kunne.
Dauka Mami tayi tana fada mata inda suke yanzu.


"Tsakanin ke da Maman yara bansan wanda ya koyawa yarinyar nan shagwaba ba. Ba
karamin abu kesa aji kukanta ba. Yanzu kuwa kukan gaske take min wai bakuyi sallama
ba"


"Allah sarki Radhiyata, bata wayar mu gaisa"


Karba tayi ta gaisheta kamar ba ita ke kukan ba ta kuma gaisa da Zahra "ina su Adda
Fauziyya?"


"Suna daya motar da Hamma ke ja. Yanzu zan fada mata ta kira ki"


Katse wayar tayi ta kira Fauziyyan ta fada mata. Ita kuma tana jiran Zahran ta turo
mata nambar take fada musu wai Radhiya tayi kuka da bata gansu ba.


Motar sai ta koma hirarta da kewarta da suke yi. Ghazalatu haushi ya kamata kamar
wadanda aka yiwa asiri kowa ya bude baki sunanta yake kira. Awwab tuki kawai yake
yi kamar ruwa ya cinye shi. Matsananciyar damuwa ya shiga na son sanin dalilin
kukan da kewarta da take ratsa shi ta ko ina. Yana ji suna hira da ita wannan ya
karba ya bawa wannan amma bata yi cigiyarsa ba, shima bai nema ba tunda yana tuki
ne.


Daurewa kawai tayi bata neme shi ba duk a cikin fushin idan kowa baice a tasheta ba
shi ya kamata yace. Ummin tana jin yadda muryarta ta sauya cikin jindadi ta gama
wayar ta tashi ta tafi yin wanka.


Sun isa Kano shabiyun rana. Mama tayi musu abinci tace su ci kafin su wuce. Aka
zubawa Awwab ya kalli plate din yaji gabadaya yunwarsa ta tafi. Cin abincinsa da
Alheran a soron gidan Malamijo yake muradin maimaitawa. Kasa daurewa yayi ya fita
ya bar Abdallah da su Ibrahim suna cin abinci. Mami da Mama kuma suna can suna
tattauna yadda al'amarin aikin Hadir zai kasance. Cikin motar ya koma ya zauna a
baya sannan ya kira Fauziyya yace ta turo masa nambar da zai kira su Ummi. Dariyar
shakiyanci ta rinka yi masa ya fara fadan da bata sanshi dashi ba tayi saurin katse
kiran ta tura masa.


Bugu biyu Ummi ta shafa wurin daukan kira ta kara a kunnenta. Muryar Awwab taji ta
tambaye shi yaya hanya. Sun taba hira kadan kamar ta fuskanci me yake jira ta
kwalawa Radhiya kira.
Bata tambayi ko waye ba ta karba "hello"


Shiru yayi yana jindadin amon sautin daddadar muryarta. Ita kuwa ta gaji da hello
hello din tace "Ummi anki magana fa"


"Ko ta katse, duba zaki ga nambar Awwab ce ki sake kira. Mami tace ta saka nambar
kowa"


Tashi tayi da gudu ta bar dakin, Ummi sai shiru taji ta koma inda suka kwana tana
jin wani nauyi a ranta. A hankali tace "Hamma"

[11/2, 6:48 AM] : 31.💕
🏽

"Kukan ne har yanzu baki dena ba?" Yace a hankali yana jin farinciki na shigarsa
saboda jin muryarta.


"Ni ba kuka nake ba"


"Shine daga tashinki kika soma damun mutane da waya ina jin ko wanka bakiyi ba"


"Ba kune ba sai kuka tafi bakuyi min sallama ba"


Siririyar dariya taji yayi "Silly girl. Cewa zakiyi nine na tafi banyi miki sallama
ba ko ba haka kike son fada ba zaki basar?"


"Inji wa? Ni da munyi fada da kai"


"Ke abu baya wucewa a wurinki ne? Kuma ba na goge ba. Wai ma in tambayeki fushin na
meye?"


Daburcewa tayi ta rasa me zata ce masa har ya sake maimaita tambayar "uhmm to ai
zaka janyo mana ace yayanmu ne kai kuma kaje ana baka abu a baki"


"Ba ma ki da kunya, kema fa na baki har sau biyu"


"To ai ni kanwarka ce" tayi maganar da wasiwasin iya matsayin da take so daga
gareshi kenan ko kuwa.


"Tunda dai bakya so na dena. Da Ghazalatu kadai zamu rinka yi"


Kit ta kashe wayar zuciyarta na tafarfasa. Ai sai yaje su karata ita dama meye ya
dame ta dasu.
Kallon wayar hannunsa yayi yana tambayar kansa meye tsakaninsa sa Alheran. Ta wuce
kanwa shi kansa ya sani amincewa ta rage. Lokaci yayi da zai dena yaudarar kansa
don bazai iya ba. Bashi da karfin zuciyar jurewa. Kallo daya yayi mata ranar da ya
fara ganinta a gidan Mama aka kwance duk wani notin jikinsa. Sake kiranta yayi
wayar na hannunta dama tana nadamar kashewar da tayi kada yaki sake kira.


"Ke da na hana tashi idan muna magana shine kike katse min waya."


Baki a kumbure tana fushi tace "kayi hakuri"


"Bakin naki zan like tunda baya son yi min magana bashi da amfani"


"Ashe rabon wani ma zai nemi nasa ya rasa ne" tace tana dariya da tayi tunanin
abinda ta taba son yiwa Gwaggonta Salame wata rana da taji ta zagi Umminta. Wurin
Hanne taje lokacin tana auren Malamijo da niyar karbar super glue ta saka mata a
kunu tayi rashin sa'a ya kare.


Jin kansa yake cikin nishadi yace "Ki gwada ki gani idan Ghazalatu bata zane min ke
ba"


" 'Yar soja ce fa Hamma ko ka manta ne"


"Na dai ce bazaki yi sojan nan ba kuma kin yarda"


Bata sanin tana shagwaba sai maganarta ta fito kamar yanzu da tace "to gaskiya ka
dena cewa bakina bashi da amfani"


Fuskarta kawai yake haskowa tana magana. A kasalance yace "fada min amfaninsa guda
daya sai na kyale shi"


"Shan sweet in rage maka" tace da sauri ta dora hannu akan labbanta ta rufe bakin
tana jin matsananciyar kunyar kalamanta. A karo na biyu ta sake katse kiran tare da
kashe wayar. Kan katifar ta hau tana shure-shuren kafafu kamar zata yi kuka tana
mai kunyar maganar da tayi da yanayin da tayita cikin wata irin siga mai tsayawa a
rai.


Wani irin dumi yake ji yana ratsa shi tun daga tsakiyar kansa har kafa. Ya runtse
idanunsa yana hangota cikin zuciyarsa. Abin takaici bashi da hotonta ko daya a
wayarsa. Bazai iya sati biyu bai ganta ba shiyasa ya fara neman abinda zai fake
dashi ya koma Sumaila cikin kwanaki kadan.


**********


Mal Aminu yayi bakinciki mara misaltuwa da jin yadda Maikudi ya yi da dukiyar
marayu bayan Captain Onomza ya fadawa Major.
Gidan Zayyan na Kano yana nan tsahon shekaru ya zuba 'yan haya a cikinsa. Kudin da
ya rinka aikowa da kudin hayar dasu ya tamfatsa katon gida mai bene a nan Sakkwaton
a cikin wata sabuwar unguwa da yanzu ta fara cika. Bai kuma yi jayayya ba saboda
dukan da yaci ya fada musu cewa yan uwan Zayyan na Nijar sun dauka iyalinsa duka
sun rasu kamar yadda ya fada musu. Mal Aminu jikin girma bazai iya doguwar tafiya
ba amma ya baiwa Major

43 / 99