Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
mata dama?"
"Alheran sunanta ma"
"Da gaske?"
"Yakushina fa kika yi" yace yana kallon yadda ta ware idano ta saman kofin
hannunsa.
Tasowa tayi ta dawo kujerar gefensa yadda zata gani sosai tana ta karkata kai hagu
da dama "Allah Hamma, ko dai don nace ban tunaka bane zaka dora min" ta rinka dage
girarta duka biyu a tare tana cewa "eyye, eyye?"
"Cute" ya furta a sanyaye ya rasa me yake damunsa tun da ta fito daga dakin. Wasu
abubuwa take yi da suke tado masa da memories din kuruciyarsu. Ta bude ido ta
lumshe, ta turo baki ta sha kunu ko murmushi.
"Da kina yarinya kin fiye rigima da fada...uhmm harda kuka. Gashi naga alama babu
wanda kika dena cikinsu."
"Tsokanata akayi ne, amma yanzu na dena fada"
Fauziyya da ta duka za ta zuba masa abincin a plate tace "A yaushe kika dena
fadan?"
"Babu ruwanki da hirarmu bar abincin ma zata zuba min idan na tashi ci. Tafi kawai
ki barmu kinsan ba wurinku nazo ba"
Dadi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha yace ba wurinsu yazo ba. Kai na rawa tana
jujjuya idanu tace mata " yehhh sai a tafi kinji me Hamma Awwab dina yace. Dama na
fada muku idan ya zo zai dena kula kowa sai ni, nima kuma in dena kula ku ehe"
"Shikenan ka bata damar cigaba da raina mu ni da Zahra"
Kallon tuhuma yayi mata "wai haka?"
"Fada kawai take yi don ta hadamu, kowa ya shaideni a gidan nan wurin girmama manya
ba daga nan ba" yanayin maganar kadai zai gane karya taje yi. Bata da innocent
face, kana ganinta kasan akwai jini a jika.
"Allah Ya shiryeki Radhiya" Fauziyya tace tana tafiya za ta je kaiwa Zahra tsirku.
Abincin ya nuna mata ta soma zuba masa "ba kya son na kula kowa?"
Ta dago kai "eh wallahi, ko na yau kawai kada kayi musu magana su gani duk kafi
sona. Ni kadai ce kanwarka banda su"
"Gobe zan koma Kt ba kya so nayi hira dasu Ibrahim?"
Dena zuba abincin tayi tana jin babu dadi a ranta "gobe kuma Hamma ko sabawa bamuyi
ba zaka koma?"
Wannan karon shi ya fara janye idanunsa daga gareta. Ya rasa gane me yasa suna
kallon juna sai yaji abu ya taba zuciyarsa. Ya dai alakanta hakan da dawo masa da
tunanin baya da take yi ne.
"Akwai wani sabon da ya rage msna bayan wanda muka yi in less than an hour?"
Wuya ta shiga sosawa irin na marasa gaskiya tana sunkuyar da kai da murmushi.
Dimple dinnan ya sake kallo ya miko hannu kamar zai saka yatsansa yadda ya saba yi
mata a baya ya tallabo habarta da ragowar yatsunsa sai kuma yayi saurin janyewa.
Alheran is not a child anymore ya yiwa kansa fada.
"Na yarda kayi hirar minti goma goma da kowa su Baba kuma awa daya, sauran kuma
duka nawa ne."
"Bazaki gaji dani ba?" Bai san me ya kaishi yin tambayar ba. Yayi saurin datse
bakinsa bayan ta fito.
Da ido daya ta karkace kai tana kallonsa "hmmm na gane wato ka gaji dani ko? Nasan
komai idan ana yi min irin haka saurin fahimta nake yi. Kora da hali kake min irin
na Ummi idan ta gani da hirata"
Hannu ya daga yana bata hakuri "ba haka nake nufi ba, yadda kike so haka za'ayi. A
lokacin kowa ma sai a cire minti daya da rabi in kara miki"
Murmushi ta saki tayi masa gwalo "na maka wayau"
Girgiza kai kawai yayi yana jin nishadi da farinciki suna ratsa shi.
**********
Malamijo ke zaune a tsakar dakinsa akan filo yana sharba gumi. Zafi ya ishe shi
daga shi sai dogon wando Hajjo da tayi karkon zama kamar Yadikko saboda bakinta
dake kwatarta a wurinsa tana masa firfita.
"Ya kamata kaje asibiti fa, ka kwana ka tashi da abu daya ba'a zauna a gida ba"
Daure fuska yayi ga azaba ta ishe shi da kyar yake magana "zaki biya min kudin
asibitin ne?"
"Lallai ma Malamijo, to don Allah zauna kada kaje ka gani idan zan damu. Ka bar
kudin kar ka tabasu idan ciwo ya karasa ka a raba mana gado. Nasan a lalace idan
ban saka dogon buri ba zan tashi da a kalla shanu uku manya."
Ido ya ware yana jin kamar ya shakota amma jikinsa babu kwari. Ta turo dankwali
gaba tana lissafi da yatsunta "kaga mafi girma a ciki in sa a danne a yanka min. In
soya, in gasa, inyi miya. Kai har tafasasshe sai naci. Sauran biyun kuma in sayar
nayi sababbin dinkuna kafin Allah Ya kawo bazawari"
"Mmmugguwa, saaai kin riga..rigani mutuwa"
"A hakan, karmai-kamai da kai kamar kazar mayu?"
"Akwai mayyyyyyar da ta wuccceki ne?" Yace yana cije lebe.
Yadikko ta dago labule ta shigo fuskarta da damuwa "Malamijo anya zaku cigaba da
zaman nan kuwa haka? Use da Asabe fa suma irin lalurarka ta same su. Asabe sai kuka
take da kyar na bata hakuri na fito"
Hajjo na jin haka ta tashi da sauri "Yadikko kice ciwon na ango ne da amarensa.
Wannan abu shi ake kira guzurin masoya. To ni nayi nan. Kayan lefen can da aka gama
gani zan je in killace kada ayi sibare inzo banci nanin ba nanin ta cinyeni ace don
ba ni na haifesu ba ina musu bakinciki na bari an kwashe musu kaya"
Fita tayi tana rangaji da dariyar mugunta. Malamijo da amarensa duka sun kasa
fitsari. Duka duka Asabe watanta uku a gidan ya cike gurbi da Use. Auren sati uku
an wayi gari sun kasa fitsari. Shi tun jiya ya fara gashi yace a matse yake amma ko
digo ya kasa yi.
Bata gama gyara kayan ba Yadikko ta shigo babu walwala a fuskarta saboda yadda ta
kula yana jin jiki.
"Hajjo me ya kamata ayi ne, rashin fitsarin nan fa ba karamin abu bane. Malamijo
sai zufa yaje yi yana numfarfashi"
"Sai kiyi ta damun kanki Yadikko. Akan me? Nan yayi auren nan fa ya soma mana
wulakancin da ya saba. Saboda alhaki kwikuyo ne da yace mu dena girki wai ya bamu
hutu kannenmu suyi ai ga sakamako nan ya samo. Banda kwadayi irin na namiji yaran
da basu fi yayi jikoki dasu ba wai sune kannenmu"
"To dai a bar tone-tone mu kira su Habu yazo ko da motar da yake haya ne a kaisu
asibiti. Zan tura a fadawa Salame ke kuma ki kira Innawuro ta fadawa Mairama itama
su zo babansu ba lafiya sannan ga karbar lefe ma da basu san anyi ba"
Ido Hajjo ta zaro "Ni shegiya inji dan daudu, da wane bakin zan fada musu
mahaifinsu ya kamu da tagomashin soyayya? Kyaleni naji da aike gidan waccan mara
mutumcin Salame. Amma Mairama ai akwai kunya taakaninmu, yarinyar mutumcinta yasa
yanzu kunyarta ma nake ji"
"Meye kuma tagomashin soyayya ni Yadikko?"
"Sunan da ya dace da ciwon nasu kenan ai"
Yadikko ma dariya ce ta kama ta. Sai yamma aka samu biyu cikin mazan gidan suka
dawo. Dama daga Mairama sai taron maza. Matan da suka taso kuma halin Malamijo ke
korar musu manema. To yanzu anyi sa'a mutum hudu cikinsu abin yazo tare. An aikawa
Salame dan aiken ko kallo bai isheta ba kamar ba kaninta ba. Mairama kuma Bature ne
ya kira lambar Baffa Habubakari ya fada masa. A daren ya nemi layin Major ya sanar
dashi cewa a fada mata.
**********
Hankalin Mairama ya tashi duk da bata san me ya sami Malamijo ba amma tunda aka
fada mata tana ganin ba karamin abu bane. Major ya tsara musu tafiya washegari
ganin duk ta tashi hankalinta. Dama motocin da yayi order biyu an riga an kawo su.
Daya domin bukatarsa dayar kuma saboda Mami da kuma kai Zayyana makaranta da suke
jiran a koma hutu ta fara SS1 sabon zangon karatu mai kamawa.
Jibi zai tafi Sakkwato kaninsa zaiyi masa rakiya su kuma yace washegari su tafi sai
su tsaya a Kano su dauki yaran.
"Amma ina ganin motar zata yi muku kadan. Bus din da aka kai Awwab Kano kuma yace
gobe zasu dawo. Dreban ya kamata ya huta haka shiyasa ba zan ce ya kwashe su ba"
"Awwab ya tuka ba sai ya bimu a baya ba" Mami tace su kuma dan gidan Hussainarta
Abdallah ne zai tuka su.
"Bana son tukin Awwab a babbar hanya gudun nan nasa kamar yana iska".
Mairama ta fara musu godiya sannan tace "da kun barshi Daddy a hakan ma nagode
sosai wallahi. Ba sai an sake wata wahalar daukarsu ba. Shima Awwab din yana
bukatar hutu"
Mami ce mai kwantar mata da hankali tace "haba Ummin Awwab ki bar wannan godiyar mu
dake duka daya ne. Babu matsala in sha Allah"
Babban abinda zai kai Major wanda zasu hadu da Baffa Gide a Sakkwaton shine
binciken dangin Zayyan na Nijar. Idan da gaske rashin idonsa a duniya yasa suka
zare hannunsu daga kan iyalinsa ko kuma su ma karya Maikudi ya shara musu duk zai
jiyo. Shi kanshi sojan da yake tura kudin zai baro bakin aikinsa ya taho don ransa
ya baci fiye da ba Major akan rainin hankalin da Maikudi yayi masa. Idonsa idon
Maikudi kawai yake jira.
**********
Tun dare anyiwa Zainab waya game da zuwa Sumaila duba Malamijo. Ita bazata sami
zuwa ba saboda Hadir gashi asibiti zasu koma. Tunda ba kwana zasuyi ba Mairama da
su Radhiya ne kadai zasu kwana sai ta yiwa Ibrahim izinin fita duk da shine karfin
taimaka mata akan babansa sai Emzee da yake taya shi sosai.
"Yaya zakiyi da Baba" ya fara cewa da tace yaje.
"Gara na fara sabawa, daga kai har Karami WEAC dinku ake jira a nema muku
admission. In kana makaranta zanyi ta jiranka ne?"
Godiya yayi mata don yana son bin 'yan uwansa amma baya son kwana saboda kada aikin
yayi mata yawa.
Dakin da aka sauki dreban gidansu Ghazalatu yaje ya tarar da Awwab ya karbi
mukullin motar. Kudin mota da Zainab ta bayar a kai masa da zai koma Katsina yaje
kai masa. Iyalan gidan su ma duka sati mai zuwa zasu taho Katsinan saboda bikin da
yake na gida duka a garesu.
Shi kadai ya koma ciki Awwab ya zauna akan dan ginin da ya zagaye flowers din da
aka shuka daga jikin bangon gidan. Waya yake son yi da Ghazalatu yau tun da ya taho
tana fushi basu sake magana ba.
Da sauri ta dauka da ya kira sai kuma tayi shiru don ta nuna masa fushinta na kin
kiranta da wuri.
"My G fushin ne ya tashi?" Nishadi yake ji sosai yadda suka rinka hira da Alheran
kamar basu rabu ba. Kusan komai na rayuwarta da zata iya tunawa ta fada masa sai
yake ga kamar a gabansa ta tashi.
"Idan nayi magana kace na fiye kishi ko korafi. Tun yaushe ka isa amma ko text ban
samu ba talkless of waya."
Sai yaji babu dadi don ya sani bai kyauta mata ba. Hakuri ya bata don bashi da
girman kai ko kadan. Yayi mata laifi dole ya kwantar da kai ya rarrasheta. Kusan
wayar minti talatin suka yi sai da yaji ana masa warning na karewar credit.
"Zan kiraki gobe in sha Allah, zamu je duba baban Ummi a garinsu. Dawowarmu sai
wurin jibi kenan dasu Mami"
"Mami ba tana gida ba?"
"Zasu taho da Ummina gobe sai mu wuce tare"
"Yayana kace mata zani please. Da saasafe sai na koma gidan mu taho tare"
Yaji dadi sosai saboda shima ya soma kewarta. Suna gama wayar yace ta kira Mami din
credit dinsa ya kare. Ta kirata ta wayance da cewa wurinsu Zahra take son zuwa.
Mami tace to ta zauna su zasu biyo su dauketa.
Falon ya koma ya same su kowa na cin abincin dare banda Radhiya da tasa plate a
gaba tana kallonsu.
Akan doguwar kujera ya zauna ya kwantar da kansa baya. Alamun idanu yaji a kansa ya
dago. Ai kuwa duka shi suke kallo har Radhiya
"What?" Yace yana kallon kansa.
Fauziyya ta nuna masa plate din gaban Radhiya. Taliya ce fara da sauce din ganyen
alayyahu da ugu sai balangu mai dan karen dadi da Ibrahim da Emzee suka siyo. Dama
yanzu sune 'yan zuwa aike.
"Me ya sami abincin Alheran?"
Kunya taji ta kasa fada masa bayan cika bakin da ta gama. Zayyana kuwa tace "kowa
shaida ne Adda Radhiya zaki min gyaran akwatina tunda kin kasa"
"Dama akwai abinda zaki kasa?" Yayi tambayar yana kallonta.
Ta dai yi saranda inji bature kaudin nata bai kai nan ba ashe ta gama cika baki.
Tana ganinsa taji ko da wasa bazata iya fada masa zaman me take yi ba.
"Emzee me ya kama bakin yayarka ne ta kasa magana?"
"Babu ruwana ni dai" ya cigaba da cin abincinsa yana murmushi.
"Ni bari na fada maka Hamma" Ibrahim yace yana kallo Radhiya ta daure fuska
"Zayyana tace kafi sonta shine Radhiya tace don bata nan ne dama. To shine Zayyana
tace mata ita fa ko me take so kana yi mata. Idan kana gida hatta abinci tare kuke
ci. Shine Radhiya tace wai wannan na gaban nata kaine kace ta zuba muku tare kafin
ka shigo. Betting su ka yi"
Zamowa yayi daga kan kujerar yana janyo plate din gabansa bayan ya tankwashe
kafafunsa.
"Babu ruwana da wasanninku, Alheran matso mu ci yunwa nake ji"
Bude baki su kayi cike da mamaki harda ita Radhiyan.
Kifta mata ido Awwab yayi a kunyace ta matso ya dauki fork a kan tray din da aka
kawo kwanukan abincin.
"Muyi kama-kama irin na yara?" Yayi magana yana kallon idanunta. Tsabar kunya tashi
tayi zata gudu.
"Ba fa ki isa ba, wannan abincin na mutum biyu ne so just sit mu cinye"
"Kaci ka rage min Hamma Awwab" tace tana kallon su Zahra tana neman taimako.
"Tare zamu ci kada a barki da gyaran akwati"
"Babu komai zan iya"
Hade rai yayi "ina wasa dake ne?"
Ba shiri ta zauna tana bashi hakuri sai kuma ta waiga tana kallon kowa an zuba musu
ido "don Allah ka bari su gama duka su tafi kunyarsu nake ji"
"Kin tabbata zaki zauna muci idan sun tafi?"
"Eh mana"
"Kamar gaske"
Bude baki tayi za ta sake magana kawai ya tura mata fork din da ya ciko da abinci
tun dazu. Ibrahim ya dora hannu ya rufewa Emzee idanun da ya zaro sun ga abinda
basu saba ba. Zahra ma sai ta rufe nata ta sakalo hannuwanta akan idanun Fauziyya
da Zayyana suna faman dariya.
Radhiya kasa motsi tayi sai idanu da take ta kiftawa ba kakkautawa. Awwab yayi
murmushi duk da yayi ne kawai saboda kannensa amma abin ya tsaya masa a rai dakewa
kawai yayi ya dauko kofin da aka cika da juice ya miko saitin bakinta.
"Sorry na cika miki baki, hadiye ki sha wannan"
A guje Radhiya ta bar falon kafin ta kasa numfashi. Yau ta gamu da gamonta. Ita
bata taba kunyar wani mahaluki ba kamar yadda taji Awwab ya gama da ita ba yau.
[02/11 7:31 AM] My 2nd Mtn: 27. Shadaya da rabi mutanen Katsina suka iso. Radhiya
sai murna ta ga Umminta ta kara kyau. Mairama hadaddiyar mace ce da rayuwa ta yiwa
cikas. Kwanakin da tayi a Katsina da kulawar Mami yasa jikinta ya kara kyau kamar
ba ita ba.
Zahra da Fauziyya na ganin Ghazalatu suka sa ihun murna don basu san da ita za'a zo
ba. Mami tace bata san lokacin da zasu girma ba irin wannan tsalle da suke yi. Ita
Ghazalatu hankalinta yana kan Radhiya dake zaune a gefen Umminta ana mata tsiyar
Ummin na tureta bata ma san tana yi ba. Gaisawa suka yi aka dan taba hira Mami tace
gara su zo su dau hanya saboda a ranar suke son dawowa.
"Ku tsaya kuci abinci an gama tun dazu"
Mami tace "muci abinci muji bacci kenan, ni kin sanni da na koshi sai na fara neman
wurin kwanciya"
"Shiyasa nake jin alamun kinyi ukun yadda na sanki ashe" Mairama tace tana
murmushi.
Yaran dariya suke yi Zainab tace lokaci ne ai, shekarunsu na soma ja zasu fara
ajiye kiba ko da ta girma ce.
"Mama banda ni a kibar, mu sojoji ina muka ga lokacin yin kiba muna faman guje-guje
a daji"
Sai da kowa ya dara Fauziyya ta tabo Ghazalatu "kinga kanwar Hamma ko, Radhiya ake
ce mata. Yini daya kika yi da ita sai cikinki ya kusa ciwo don dariya"
"Na ganta". Gabadaya ranta babu dadi tun da ta ga wacece Alheran din da Awwab yake
ta rawar kafa a kai. Tayi zaton wata 'yar yarinya zata gani da bata fi Zayyana ko
kasa da haka ba. Dama jiya saboda wannan budurwar mai idanu a tsatstsaye ya taho
Kano ya barta.
Shigowar Awwab da Abdallah wanda ya kawo su Mami dan Hussainarta daga waje kenan
daidai lokacin da Mamin take ce mata.
"Idan ke soja ce bakiyi kibar ba mijinki da ba soja ba zaiyi ne"
Tsuke baki tayi tana kada yatsa "No, no, no, no , no Mami. Ni likita zan aura fa.
Kinsan shima aikinsu babu zama bazaiyi kibar ba"
"Mara kunya" Mairama tace tana daka mata duka a baya. Su Ibrahim an sami abinda ake
so suna ta dariya. Zainab ta maimaita musu abinda Radhiyan tace dazu wai ta raina
kowa idan ba soja da likita ba.
"Mama mu dasu aikin ceton rai muke yi shiyasa kowa bai kai mu ba"
Mairama sarkin kunya sai ta soma tsoron kada Radhiyan ta fadi wani abin da yafi
wannan. Ta tuna ranar da tace mata tana abu kamar ba bafillatana ba. Ita kuwa ta ce
dama ba ita bace, su Sakkwatawa ne.
"Ku barni da ita kwanannan zanyi mata miji a aurar da ita mu huta" inji Zainab.
Tun shigowarsu Awwab yake kallon yadda take ta zuba surutu. Dauke kansa yayi ya
kalli Ghazalatu ya sakar mata murmushi ta maida masa.
Ibrahim ne yace "Mama ki samo mata malamin makaranta kawai"
"Tabdi, yo ni malamin makaranta ba sai dai na zane shi da dorinarsa ba. Tsorona zai
rinka ji"
Fauziyya da ta saka musu ido ita da Awwab tun jiya kuma take fatan hakan tace "ina
jin zaki fi dacewa da dreban jirgin sama"
Mami da Zainab har Mairama sai su ka yi murmushi. Ko dai Fauziyyan ta ga wata alama
ne take hasashen abinda suke shiryawa. Awwab da yake shan ruwa cire kofin yayi yana
son jin amsarta. Abinka da 'Yar soja ta hade rai "ke kadai ce bakya sona Adda
Fauziyya. Me zanyi da dreba sai kace ta kare min?"
Kowa yayi shiru yana kallon Awwab da ya zuba mata idanu harda Ghazalatu da misalin
na Fauziyya ya kona mata rai. Bata san suna yi ba bare ta gyara zancen.
Zahra ce ta tace "mun ganku a rana ke da Hamma Awwab tunda shima dreban jirgin ne"
Ba arziki Radhiya ta tashi yana tsaye ya harde hannuwansa a kirji. Tayi zaton zaiyi
fushi sai ta ga shi ya fara dariya kafin sauran "wato mu sai ta karewa mace za ta
auremu ko"
"Wayo Adda Fauziyya tayi min ba haka nake nufi ba. Maimakon tace pilot yadda zan
fahimta"
"Sannu Queen Elizabeth wato sai anyi turanci zaki fahimta" Ibrahim yace.
"Ka kiyayeni Surbajo" A dolensa yayi shiru da yaji abin zai dawo kansa.
Tsokanarta suka cigaba da yi tana karewa kanta. Awwab yana kallon Ghazalatu yace da
Radhiya "ki shirya zata kare miki kwanannan kuwa don sai kin auri pilot. Kafin nan
kuma ki zamarwa matata 'yar aiki"
Mama da Zainab suka kalli juna suna gyada kai da murmushi.