Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
da ita yaja kofar ya rufe.
Mammee tayi dariya tare da goge 'yar kwalla "sannu da kokari Mairama nasan irin
halin Alheran. Haka yayata take kusan komai nata ta dauko. Zama da kishiya ne yasa
tayi sanyi amma ko shi Mal. Muhammadu ai yayi fama da kiriniya tun farkon haduwarsu
har auren."
Murmushi Ummi tayi tana sauraron labarin uwarmijinta da bata taba gani ba sai a
hoto.
Wani falo Emzee ya kai Radhiya ya girgiza kai "ni da kin sani ni na fara fitowa
yadda zan iya zaneki son rai. Sam baki kula da kunyar da Ummi take ji ba kike ta
takurata da tambaya"
"Ayya Emzee ban gani ba bari naje na bata hakuri" tace innocently.
"Kin ji ki kuma, shiru ya kamata kiyi ki rinka taimaka mata idan tana son wani abu"
Gyada kai tayi sai kuma ta hau murmushi "Amma kai baka yi murna bane? Ni fa na
matsu naji ranar haihuwar"
Hannunsa ya sakalo a kafadarta yana jinjina wautarta "Addata ta kaina ina tausayin
Hamma nasan ya gamu da shiririta"
"Kai dalla me ka sani, Hammana yana ji dani sosai don wallahi jiyama da dadd......"
A gigice Emzee ya fara neman kofar fita daga falon yana cewa "na shiga uku don
Allah kada ki fada"
Ya kai bakin kofa tace "kai wank...."
"Sai anjima" yace da sauri ya fita yana tunanin ko dai wanka za ta ce yayi mata
tunda tace yana ji da ita.
Tabe baki tayi da ya fita din tace "meye don na fada maka ya tayani wanke-wanke ba
abin farincikinka bane ace mijin yayarka yana sonta" wani tunani ne ya darsu a
zuciyarta bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba harda rike ciki "shege Emzee
ko dai yasan me akeyi ne...tabdi gara ya nemo mata mu kaishi."
Ta nufi part din 'yan matan gidan inda su Zahra suke ta kuma ganin Emzee da tiyo
yana wanke fuska ta zuci tace sumumu kasau wannan idan kayi aure matarka ta shiga
dubu da soyayya. Cikin 'yan uwata ta shige tare dasu Fauziyya ana mata tsiya bakin
ya kasa ramawa. Bayan isha Awwab ya kirata wai tazo su tafi ta rasa yadda zata yi.
Can sai ga Tante Nasara ta kirata suka fita har wajen gate sannan ta daga waya ta
kira Yousuf. Da faransanci tace masa,
"Ga kanwarka nan ka kaiwa mijinta kafin Zainab ta cinyeni"
Ya kwashe da dariya "Mam ina sonki wallah"
"Da na kyaleka ka boye matarka ko? Zamu hadu a gida ne sai ka gaya min wanda ya
baka shawarar satar amarya" ta ce tana dariya.
Tare suke da Awwab a kofar gidan Alh Ghoumar ko minti biyu ba'ayi ba suka iso. Baya
Awwab ya bude mata ta shiga ta gaishe da Yousuf tana tambayarsa Arifah yace wurinta
zasu je.
Wani katafaren hotel ne da yake cikin jerin manya a kasar baki daya suka shiga.
Hawa na bakwai Yousuf ya bude mata wani daki bayan ya kira Arifah yace tare suke
sannan suka juyo shi da Awwab zasu siyo musu abinci.
Radhiya da Arifah suka rungume junansu suna murna. Arifah ke fada mata yadda daga
Yousuf zai kaita gida ranar dinner suka kare a hotel.
Radhiya tayi ta dariya suka koma hirar sabuwar rayuwarsu. Arifah ta girmi Radhiya
sannan ta fita wayewa musamman ta wannan fanin. Shawarwari ta shiga bata yadda zata
ajiye kunya ta bawa mijinta kulawar da ta dace.
"Kinga ba mazauni bane idan ba kya kulawa dashi yanzun nan wata zata rabaki dashi"
"Dena fada Sis" tace da rawar murya bata fatan ganin wannan rana. Ko zaiyi mata
kishiya bata burin ace saboda gazawarta ne sai dai hali na rayuwa.
Goma da rabi suka dawo Yousuf ya shigo yace mijinta na jiranta a waje. Tana fitowa
ta fada jikinsa sai da yayi mamaki kuma ya nuna jindadinsa sosai ita kuwa sabon
karatun Arifah ta dauka.
"Miss me?" Yace yana mata jagora zuwa nasu dakin.
"So much Hammana"
"Love me?"
"For as long as I live" tace tana kashe masa ido.
Bude dakin yayi dama ya ajiye musu kayansu ya rungumeta "ki rinka sassauta min
babyna wannan sabon salon naki zai hanani abin arziki"
Zama yayi ta dare cinyarsa abinta tana magana cikin jan rai "wane abin arziki da za
kayi?"
"Uhmm wai da yau dai na bar amarya ta huta gajiya...to amma"
Tana ganin abin zaiyi gaba ta tashi tana raba idanu "kayi hakuri Hammana ji nayi
ance wai haka yana kara kauna"
Guje-guje suke a dakin taki bari ya kamata yana cewa "kaunar zan nuna miki ai wadda
ta karu"
"Chèri bani da lafiya fa"
"Harda karyar ciwo kike yi?"
Ta girgiza kai tana shagwabe masa "a'a lafiyata kalau ni dai kayi hakuri"
"Na hakura janbaki kawai zaki bani..."
Daga inda take ta taho gareshi da saurinta ta hade bakinsu "ba kayi bayani bane tun
dazu kasa ina wani tunanin"
"Tunanin naki ma zai tabbata kema kin sani"
**********
Washegari tun shabiyu suke tsakanin gidajen kawunan nasu ita da Arifah wadda aka
kawo officially. Sai yamma aka yi wasan hawan rakuma a wani babban fili inda amare
da angwaye kai harma su Ummi da Daada suka yi shigar gargajiya ta 'yan kabilar
tamasheq. Yousuf da Awwab sun sha rawani buzaye sak.
Radhiya da Arifah kuma nasu kayan harda sarkoki, abin hannu, na gashi da na hanci
duk an makala musu sunyi kyau sosai. Kowacce amarya angonta ya taimaka mata ta hau
rakumi su na rike da akalarsa an rufe rabin fuskar amaren suka zagaya wurin dasu
ana ta daukar hoto.
Salame tayi kallo ta ga abin mamaki a zuri'ar dangin mijin Mairaman da ta
wulakanta. Kannen Halifa da matar Alh Salisu sun zo kai kace sun fita matsayi a
wurin saboda yadda ta zubar da mutumcinta a baya.
Ana tafawa amare da angwaye ance suyi tsere akan rakuman Emzee ya kalli Addarsa da
mijinta ya zauna a bayanta ya rike linzamin rakumin da suke kai ya kalli Rahima da
take kallonsu itama abin yana burgeta ya ce
"nima in zo in samarwa kaina buzuwa ko ma hau rakumi da bikinmu"
A can gefe take zaune mutane duk anyi gaba kallon tsere shine ya biyota don kawai
ya bata haushi.
Wani matashi kyakkyawan gaske cikin jikokin Alh Sidi ta nuna masa duk da zafin
kalamanta tana murmushi "Ya Emzee to ko muma a hada namu bikin ne? Ka ga Aman yace
muna komawa zai zo wurin Ummi"
Hadari ma yafi fuskar Emzee kyan gani ya ce "yazo yayi mata me?"
"Maganar aure ce don yace ba da wasa yake ba" ta yi masa wani dan banzan murmushi
da ya daure masa zuciya.
"Saboda an rasa mazajen aure a Nigeria daga zuwanki kwana daya a nan za ki ce kunyi
maganar aure da wani" ya ce yana huci.
Kwafa tayi a zuci tana jindadin ko ma fushin me yake da ita bai dena sonta ba "Abin
ne yazo mana a bazata"
"To bari kiji in fada miki indai Aman ne yana yana shaye-shaye ah to sai ki nemi
wani"
Hannuwanta ta rungume tana kallon saitin Aman din "sai inyi masa addu'a Ya Emzee
yanzu ba'a gudun mutum don hali taimaka masa ake ya chanja"
Bai san ya soma fada ba yace "inji uban wa? So kike ya rinka dukanki a gida? Ke wai
da wane yare ma kuka magana bayan bai iya hausa ba"
Rahima ta dake tayi murmushin da ya sake kawata fuskarta "ko babu yare mun fahimci
juna...Ya Allah Ka bani...."
Kishi tuni ya rufe masa idanu yace "Shut up, wallahi kika ce Ya baki Aman sai na
tattakaki a wurin nan"
Ranta ya soma suya saboda bacin rai "Sai na fada din...Allah Ka "
Hannu ya daga zai mareta Mairama cikin bacin rai duk da bata san me ya hadasu ba
amma ihunsa da daga hannunsa gareta ya matukar bata haushi.
"Muhammad kana hauka ne?" Ta daka masa tsawa.
Daga bayanta Salame ce ita kuma rashin ganin sanyin idaniyarta Rahima Idris Sumaila
ne ya kawota wurin. Da sauri ta je ta kama hannun Rahiman wanda idonta ko gezau sai
tarin ajiyar zuciya da take saukewa.
Ummi ta damki hannun Emzee saboda bata taba ganinsa haka ba dayake filin a gefen
gidan Alh Ghoumar ne tattaki kadan suka shiga gidan. Dakin uwargidansa ta wuce
dashi suna zuwa ta rufe kofar ta juyo a fusace.
"Karami baka taba yi min abinda ya sosa min rai kwatankwacin na yau ba saboda haka
kafin nayi maka hukunci ka bude baki ka fada min me ya hadaka da Rahima har kake
tunanin idan ka mareta zamu wanye lafiya"
Salame lokacin tana rike da hannun Rahima ta kama hannun kofar za ta bude Rahima ta
hanata tana girgiza kai. Itama ta gaji so take ta san me tayi masa. Wannan wahalar
soyayya har ina kullum yana azabtar mata da zuciya.
Ga mamakin Ummi sai kawai Emzee ya saka mata kuka ya dora kansa a kafadarta. Rahima
na jin sautin kukansa itama ta fara nata yayin da jikin Salame yayi sanyi.
Sai da yayi mai isarsa yana cije lebe yace "Ummi I love her so much, wallahi Ummi
Rahima nake son aure kamar zanyi hauka saboda son da nake mata"
Salame ta yiwa Rahima kallon tambaya wanda ita kuma taji furucinsa a bazata duba da
yadda yake kyararta yanzu. Dariyar Ummin suka ji.
Fuskarta tana nuni da zallar farinciki ta dora hannu akan fuskarsa "Allah sarki
Zayyan Turetana ya girma, to waye ya fada maka ana dukan mace idan ana sonta? Ko
tace bata son karamin sojan Mairama ne?"
Takaici ya kama shi "Ummi yaya kike dariya this is not funny at all. Rahima fa nake
nufi. Rahiman Gwaggo Salame wadda ta makantaki tsahon shekara goma"
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Rahima da Salame suka fada a tare jikinsu na
rawa. Salame bata son Rahima taji zancen nan da wuri sannan a yau a yanzu taji wata
katuwar nadama ta lullubeta a gaban 'yar cikinta.
Emzee ya soma ruwan hawaye "Ummi ni bansan 'yar Gwaggo Salame bace da bazan fara
sonta ba, bakiji zuciyata ba Ummi ki rinka yi min addu'a Allah Ya yaye min. Ta yaya
zan so 'yar wadda bata son mahaifiyata kullum burinta kiyi kuka"
Mairama ma sai ta fashe da kuka Emzee ya rungume mahaifiyarsa yana jin dacin zuciya
da rashin adalcinta na son Rahima.
Hawaye na kwaranya a idanun Mairama tana share masa nasa ta ce "Karami idan kana
son kanwarka nayi maka izini ka manta da komai ka nemi soyayyarta"
"A'a" ya shiga girgiza kai.
Kuka take sosai tace "Lallai ashe baka da wayo ban sani ba. Abinda Adda Salame tayi
min ALKHAIRI NE babba a gareni. Yau da banyi wannan makantar ba maimakon murna
Karami zan shiga rudani mara misaltuwa ne akan dawowar mahaifinku. Ko kasan cewa ko
banyi auren soyayya ba dole zan nemi mijin aure saboda inganta rayuwarka da ta
yayarka? Da yanzu ina da 'ya'ya da wani mutumin ba Zayyan Tureta ba fa Karami. Kana
tsammanin duk wanda na aura ga zuri'a tsakaninmu zan iya barinshi kai tsaye saboda
naku mahaifin ne? Kasan girman dake tattare da aure irin wannan kuwa. Ga mijin da
nake so ya dawo amma wani yayi mana shamaki. Kila Allah Ya jarabceni da son sa fiye
da babanku"
Ta sake fashewa da kuka " nayi imani da yanzu mahaifinku yana cikin kuncin rayuwa
duk da tarin arzikin da ya samu. Ciki ne dani Karami da ta ina kake tunanin Umminka
zata sami wani rabon ta rabu da wani mijin da yara ta dawowa tsohon mijinta...ka
duba girman wannan alkhairi da Allah Ya bamu ka gode Masa domin ni wannan kadai ya
isheni dalilin da na yafewa Addata"
Bai taba tunani makamancin wannan ba amma duk abinda ta fada masa gaskiya ne.
Kukansu suka yi sosai sannan yace "duk da haka Ummina bazan iya ba. Ki yi min
addu'a zan sami wata in kawo miki"
Salame da Rahima sunji komai haka Radhiya wadda fitsari ya koro tun tsayuwar su
Rahima a wurin take bayansu tana jin komai. Ganinta kawai suka yi ta wucesu ya bude
kofar dakin ta shige tsakanin Ummi da Karami suna hawaye.
Rahima kuwa da sauri ta matsa yadda babu mai hangosu daga cikin dakin ta shiga na
kusa dashi da bata san ko na waye ba tana fitar da numfashi da kyar ta rike
kirjinta tana dannawa. Salame ta gigice ta dafata "Rahimata yaya? Me ya sameki"
A matukar raunane ta kalli Salamen idonta babu hawaye ta ce "Umma, don Allah nima
ki soni kamar yadda Ummi ke son su Adda Radhiya. Wallahi Umma idan kika soni
ko...uhmm nayi miki alkawarin zan zama 'ya tagari a wurinki ko banyi kudi ba zanyi
miki biyayya."
Magana take kamar zautacciya saboda tsananin tashin hankali ace mahaifiyarta,
hasken rayuwarta, inuwar jindadinta ta aikata mummunan abu irin wannan.
Salame sai hawayen mai cikea nadama sosai taji Rahiman ta kama hannunta "Umma nima
kiyi min addu'a don wallahi ina son Ya Emzee...kinji kirjina Umma yana min zafi
saboda na rabu da shi. Bazan iya zama da shi ba har abada saboda zaiyi ta kallonmu
da laifin da muka yiwa Ummi"
Kukan Salame ya dadu ta rungume Rahima sosai a jikinta "ba ke kika yi laifin ba
nice nayi kuma zan je na nemi yafiyarta."
"Duk abinda kika yi nima na dauka Umma. Shi baya gudun Ummi sai ni zan
gujeki....Allah Ya kiyaye"
Salame ta dago kan Rahima ta ce "kiyi kuka Rahimata kiji sanyi a ranki. Idan
Mairama tace sai na kwanta na bata hakuri sannan zata yarda Karami ya aureki
zanyi...Rahimata kiyi hakuri kullum kuka nake sakaki akan son zuciyata"
Mikewa Rahima tayi harda karfin halin murmushi "ba kuka nake ba Umma kizo muje ana
tsere mu cigaba da kallo"
Kafin Salame ta ankara Rahima ta fita daga dakin ta durkushe a wurin ita kuwa tana
kuka mai tsananin taba zuciya...waye ya aiketa kuma me ya rudeta ta rinka lalata
rayuwarta da ta iyalinta da hannunta.
********
💕64💕
***************************
Kasa zama Salame tayi ta tashi bin bayan Rahima sai ganin Mairama tayi tana dube
dube. Ita take nema saboda Radhiya ta fada mata cewa sun ji komai. Daurewa tayi ta
saki fuska ta nunawa Salamen kofar dakin tana so ta shiga su yi magana. Ita yanzu
neman sulhu take yi saboda yadda damuwar Rahima ta zame mata kamar an ajiye mata
dutsen dala a zuciya.
Su na shiga kuwa ta juyo tana hada hannuwa ga idanunta sunyi ja sosai ta ce
"Mairama nayi miki ba daidai ba nima na sani. Ba ke kadai ba duk wanda ya rabeni na
cutar dashi na cuci kaina kuma, amma ki yiwa Allah da ManzonSa kada Rahimata ta
biya bashin da ba ita taci ba"
Mairama tana iya ganin gaskiyar maganganun Salame. Idan ma ba ta tuba bane don
girman laifinta kallo daya za ka yi mata kasan cewa she is desperate, ta kai
kololuwar bukatuwa da neman agaji a wurin wadda ta dade tana farautar farincikinta.
"Adda Salame nan ba muhallin wannan maganae bane ki bari mu koma gida" ta ce mata
tare da mikewa za ta fita.
Da sauri Salame ta tashi ita ma "babu damuwa Abujan zan biki wallahi"
Murmushi Mairama tayi ganin cikin lokaci kalilan Salame ta sauya. Za ta bude kofa
kenan ta ga hannunta ta riko nata hannun da dan saurinta.
"Tsaya dai mu yita da wajewa Mairama kinga a nan wurin...." ta fita ta tsaya daga
kofar dakin inda suka tsaya dazu da Rahima "naji komai lokacin da kike fadawa
Karami cewa kin yafe min. Kinga an rufe wannan shaftar kada sai mun tafi kice ba
haka ba, ni kuma nasan naji da kunnuwana"
Guntun tsaki Mairama tayi da dariya, mai hali baya fasa halinsa "tun kafin ki ce
komai na riga na yafe miki Adda"
Wani abu taji ya sauka daga makoshinta ta saki murmushi korayen hakoran nan su ka
bayyana. A take zuciyar Mairama ta soma tashi ta danyu baya.
Cikin sigar rainin wayo wadda za ta nuna Salame har kullum Salame ce sai ana mata
uzuri ta ce "sai naji kuna zancen ciki kuma? Ina ke ina sake haihuwa an fara girma
ga 'ya'ya suna tafiya gidan miji"
Idan ta biye mata ba fa shiryawa zasuyi ba sai ma dai a karawa rigimar fetur. Amma
ko yaya sai ta dan rama za ta ji dadi.
"Soyayyar kenan Adda, ba dare ba rana kullum miji yana dokinka. Indau kuma batun
auren Radhiya ne kada wannan ya dameki ni nan harda matar Karami sai mun kara
haihuwa" tana fada a zuciyarta tana cewa (Allah Kada ka nuna min wannan bakar rana)
Ta sake tabawa Salame inda yake mata kaikayi ta ce "zaki sha aiki kuwa don indai
Rahimata ni ta biyo za ki kwatsa 'ya'ya kamar dabino. Za dai kiyi masa maganar ko?
Ba yabon kai ba ni ban taba ganin 'ya mai ladabi da biyayyarta ba. Nake fada miki
halin Sahabbai ta gado"
Ran ta yana baci da maganganun farkon gashi na karshen suna bata dariya shiyasa
kawai ta fita tana murmushi da rokawa 'yar uwarta shiriya.
**********
Emzee dakin da suka yi masauki ya tafi ya kwanta yana ta juyi ya rasa shawarar da
ya kamata ya dauka cikin dimbin shawarwarin da zuciyarsa take bashi akan Rahima.
Bari dai su koma gida yayi magana da Daada. A haka gani yake soyayya bata yi masa
adalci ba ta kaishi inda baya son zuwa kuma babu alamun za ta fiddo shi nan kusa.
Radhiya kuwa da ta fito janyeta akayi za'a cigaba da hotuna jikinta duk babu kwari.
Awwab ya kula da yadda tayi zuru-zuru kwalliyar ta goge saboda cabewar da tayi da
hawaye sai ta goge kawai shiyasa ganinta haka ya shiga damuwa saboda bata da
walwala. Samu yayi ya faki ido saboda yamma da tayi hankalin iyaye yayi nesa dasu
ya fitar da ita daga wurin. Rawaninsa ya cire ya nemar musu taxi ko Yousuf bai nema
ba suka koma hotel dinsu.
A hanya bai ce mata komai ba sai da suka shiga dakinsu ya rage mata kayan jikinta
da danginsu sarkoki da sauran kayan adon ya zaunar da ita a gefen gado sannan ya
zauna a kasa a gabanta ya dora kafafunta akan cinyarsa yana matsawa a hankali.
"Me ya sameki Alheran?"
Dama kiris take jira kawai ta fashe masa da kuka. Hankalinsa a tashe ya tashi ya
zauna a gefenta ya rungumeta tayi kukan ta gaji. Sai da ya lura numfashinta ya soma
dawowa daidai ya sake tambayarta.
Da kyar ta iya fada masa abinda ya riga yaji daga wurin Daada lokacin da suka je
Sumaila bayan Salame ta daketa. Sai dai yayi matukar kaduwa game da dalilin
makantar Ummi da kuma karshen bayanin Radhiyan wanda shine musabbabin kukanta a
yanzu.
"Hammana ka tuna lokacin da aka ce na hakura da kai saboda kada na bata zumunci?"
Ya gyada kai yana tuna lokaci mai daci da ya shude a rayuwarsa. Ya azabtu da rashin
cikar burinsa ya kuma ji haushin amincewarta a lokacin taki goya masa baya.
Siririyar muryarta da ta dashe saboda kuka ce ta katse shi yaji ta ce,
"It was so painful Chèri sai lokacin ma na fara sonka sosai. Yanzu yaya Emzee zai
ji? Yana son Rahima ashe kuma yana gudunta saboda Ummi. Emzeee yana da sa abu a rai
nasan da wahala yau ya iya bacci"
Awwab sakin baki yayi yana kallon ikon Allah. Radhiya ta cigaba da fadin halin da
kaninta zai shiga cike da tausayawa.
Hade bakin nasa yayi ya ce "yanzu duk wannan hawayen na Emzee ne ba ma Ummi ba?"
Tsakaninta da Allah tace "Ummi ai ta yafe nasu ya wuce. Emzee nake maka magana
yanzu. He is so hurt yana ganin