Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
kaisu ga rasa rayukansu,
su bar iyalai babu gata. Ku tuna da marayu da zawarawan da sojoji suke bari, ku
tuna da su kansu sojojin domin damu dasu babu abinda za'a biyamu ya maye mana
gurbin kewar da muke kwana mu tashi da ita idan suna bakin aiki. Abu daya kawai
nake so shine kasarmu ta dena mantawa damu da sadaukarwar mazajenmu. Bakunan
al'umma su rinka yi musu addu'a a duk inda suke domin su sake samun kwarin gwiwar
yin aikinsu."
"Maman Dolapo mungode"
"Mune da godiya"
Ana dauke camerar daga kansu Radhiya taje ta rungume Maman Dolapo tana hawaye. Wai
a haka ma don matar ta sakaya wasu abubuwan ne.
Kafin su tafi envelop ta dauko a cikin jakarta. Sakon Ummi ne a ciki na dubu hamsin
ta mikawa Maman Dolapo da kuma katin da aka buga da wuri na walimar da suka shirya
ta dawowar Zayyan domin ta bawa matan wadanda suka zauna tare. Dubu dari dama Ummi
ta ware musu ita da Christie saboda idan ka cire su Mami bata da tamkarsu kuma a
zamansu na barrack din.
Washegari gidan wani soja mai konanniyar fuska suka je. Duka duka bai fi shekaru
talatin da biyu ba. Nasa labarin ma ya tabasu inda yace an tura shi aiki ne cikin
garuruwan da ake yawan rikici. Wataninsa bakwai ya dawo gida bayan wata biyar da
dawowar tasa matarsa ta haihu. To ba shiba kusan kowa ya tabbatar jariri ba nasa
ba. Mata da ta ga an ganota tace laifinsa ne baya bata kulawar da ta dace. Tun
aurensu sau nawa ya taba yin wata guda tare da ita. Yayi bakincikin abinda tayi
masa iyayensa suka raba auren ya sake tafiya aiki. A can kuma wuta ta kama a wani
ginin maaikata bayan rikici ya balle suka je kai dauki. Nan ya kone sosai da kyar
aka samu ya rayu amma rabin jikinsa da fuska sun kone. Aikin da yake ji dashi dole
ya hakura sannan shekara biyar kenan duk inda ya nema ya rasa saboda munin
halittarsa. Babu wanda yake tunawa da cewa mutum shida ya tseratar daga gobarar nan
kafin zuwan motar kwana-kwana. Lokuta da dama ji yake inama ya mutu ya huta da
kyamar da al'umma suke nuna masa.
A tsukin kwanaki goma su Radhiya sunyi yawo a garuruwan Nigeria lungu da sako suna
hira da sojoji ko iyalansu. Kuka kam ba'a cewa komai. Darakta Bigman ya ga wani
salon rayuwa da basu taba sanin akwai ba. A irin yawon sun hadu da matan da suka yi
sa'ar samun wani abu na kyautatawa daga daga dangi ko abokai ko kuma cikin abinda
ake bawa mazajensu daga wurin aikin. Sai dai da yawansu babu abinda yake daga musu
hankali kamar kewar mazansu na bakin aiki ko wadanda suka rasu. Abin da ban tausayi
matuka. Masu nakasar dole a dalilin rashin wata gaba da suka yi a bakin aiki su ma
tasu rayuwar yana cikin garari. Da dama cikinsu kuma sai su kasa rungumar wani
aikin saboda tsaro suka sani shi su ka fi iyawa. Tafiya ce irin wadda ake kira
mabudin ilimi suka yi.
Wuri na karshe da suka je shine garin Onitsha (Onicha) wurin Christie. A wata
makarantar kwana ta 'yan mata suka sameta inda take aiki a matsayin malamar
Geography. Christie tayi kukan sake ganin Radhiya sai da ta hadasu a waya da Ummi
kamar yadda ta hadasu da Maman Dolapo. Ta amsa tambayoyin da Radhiya tayi mata inda
take tambayarta yadda ta sami kanta a aikin koyarwa.
Sa'arta daya sai da ta hada NCE dinta sannan tayi aure. Bayan labarin mutuwar
mijinta ta koma gida ashe tana da ciki. Da Radhiya da camera man suka bita cikin
gidanta da tace su shigo. Kofar wani daki ta bude yarinya budurwa na kwance tana
bacci ga kafafunta a lankwashe.
"Rebecca sunanta. Kashinta bashi da kwari bata tafiya ga matsalar kwakwalwa. Saboda
ita ban sake aure ba ga rashin kudi da kyar na sami wannan aikin na koyarwa.
Matsalar farko da na fara samu shine rashin mai kula min da tunda bani da kudin da
zan biya mai raino. Wurin aikin suka ce na dena zuwa da ita a bayana lokacin tana
da shekara goma na fara. Nasan wasu zasu daukeni mara imani amma bani da yadda
zanyi. A gida nake kulleta naje aiki na dawo in tarar tayi kashi da fitsari. Ko ta
mirgina inda zata iya jin ciwo daga baya na soma daureta idan zan fita shima da
kaina naga rashin dacewarsa. Shine fa nake takura mata na hanata baccin dare har ta
saba sai da safe tayi har naje na dawo. Albashina dashi muke cin abinci da sayan
magungunanta duk sati. Rayuwarta akwai tsada sosai shiyasa na kasa daukar mai aiki
har yanzu"
Dole mai imani ya zubar da hawaye idan ya ga rayuwar Christie da 'yarta. Itama dubu
hamsin Radhiya ta bata inji Ummi da katin gayyata.
An sha wahala amma ana fatan bukata ta biya. Tare suka koma Abuja harda Darakta
Bigman saboda zai duba video din gabadaya bayan an gama editing. Arifah da Radhiya
kamar kada su rabu ance sabo turken wawa. Gashi dai suna gari daya amma saba su
kwana daki daya suyi komai tare. Kafin ayi bacci kuwa kowacce zata raba lokaci da
masoyinta idan an kare su koma hirar samarin nasu suna dariya. Kwanaki bakwai ya
rage mutan Nijar su zo kawo gaisuwar Arifah. Yousuf kuwa jiransu yake yi su dawo
dama ya taho domin kara gina kansa a zuciyarta.
Kowacce ta shiga motar da mahaifinta ya turo daukarta. Cameraman da Bigman motar su
Arifah suka bi za'a saukesu a hanya sai jibi idan sun kammala aikin hadawa zasu je
gidan Major General Zayyan.
A guje Radhiya ta shiga gida ta kwakume Ummi tana murna. Itama Ummin tayi kewarta
sosai gidan kamar ba shi ba. Zayyan da taya bera bari kuwa dagata yayi yayi juyi da
ita ai kuwa yasha nishi. Ummi ta rinka dariya. Abinci taci sosai Zayyan yana ta
tausayinta wai ta fada tana gamawa tace bacci zata je tayi sai jibi da safe a
tasheta.
"Ana la'asar zaki ji bugu idan baki tashi ba" cewar Ummi
"A tasheni sallah amma banda cin abinci. Na gaji sosai Ummi"
Tana sauke hakarkatinta akan gadon sai bacci kamar an jibge kayan wanki. Da kyar
take tashi tayi sallah ta koma. Bayan isha ne Daada yace Ummi ko kunu ne ta dama
mata baya so ta kwana da yunwa.
"Sai kace wata jaririya..idan taji yunwa zata fito ne"
"Ni dai ki dama don Allah. Baki ga yadda tayi zuru zuru ba kin kuma san meye a
gabanta. Ni bazan kai 'yata gidan miji a bushe ba azo ana mata gori"
"Oh ni Mairama, waye zaiyi mata gorin?"
"Awwab mana. Yanzu tana murmurewa a gidansa zai ce kamar ba ita ya dauko a bushe
ba."
Tafa hannuwa ta shiga yi tana dariya "Wannan uban amarya mun ga ta kanmu."
Lallabata ya koma yi saboda da gaske yake dan wuya ya gani ta fara yi saboda rashin
hutu "taimaka kinji 'yar albarka Mairama baiwar Allah"
Ba yadda ta iya haka taje ta dama kunun gyada ta tafi dakin. Wata irin kwanciya
Radhiya tayi a wargaje tsabar ta tara gajiya a jikinta. Ummi kuwa ta sakar mata
duka a cinya ashe Zayyan ya gani "A'a Wallah ki bari fa. Daga cewa ki bata kunu sai
cin zali"
"Dubi yadda ta kwanta fa"
Murza idanu Radhiya take yi ta tashi tana tura baki "Ummi me nayi?" tace cikin
magagi.
Zayyan karasa shigowa yayi ya zauna a gefen gadon kusa da ita "tashi kisha kinji
Innata kada ki kwana da yunwa"
"Na koshi" tace da kyar idanunta na rufewa.
Allah Sarki ji yayi bazai iya bari ba yana tausayin 'yar tasa. Da tare dashi suka
girma Allah kadai Yasan irin yadda zai shagwaba kayarsa. Gyara zama yayi ya dora
kanta a kafadarsa idanunta a rufe "rinka bude bakinki kinji Alheran sai Ummi ta
baki"
Baki Ummi ta wangale ta ma rasa me zata ce masa. Wannan sangarta har ina. Shi kuwa
kiss ya hura mata wai ta rufe bakin ko ya matso. Daure fuska tayi tana nuna masa
Radhiya dake zaune kanta a kafadarsa ido a rufe.
"To ki bata ko yanzu..."
"Naji, naji. Ke bude baki ko na kwara miki kowa ya huta"
Da rarrashi Zayyan ya samu take bude bakin Ummi na bata yana shafa mata baya har ta
shanye. Ta bude na karshen Ummi tace "ai sai ki rufe bakin ya kare"
Zamewa ta soma yi zata kwanta Zayyan yace ta dan yi hakuri ko yaya cikinta ya
sassauta. A daddafe tayi minti biyar sannan ya gyara mata kwanciya ya kashe fitilar
dakin sannan ya rufe kofa yana dariya shi kadai.
"Kalau kuwa Sojana"
"Lafiya kalau...yau dai mafarkina ya tabbata. Kin tuna na taba ce miki ina son
komai na Alheran ayi dani. Ko wanka kike kyuyar yi mata ni zanyi saboda bana son
missing komai na rayuwarta tun kafin cikin Zayyan. Na rasa abubuwa da dama amma
kafin ta koma hannun Awwab sai dai ku rufe ido"
"Sojana ba fa babyn da ka tafi ka bari bace. Kaima duk ka wani tsufa shine zaku yi
mana kara'i"
"Ba don kada abin nawa yayi yawa ba har goyata sai nayi"
"To ni a goyani mana" suka ji Emzee yace yana hawowa saman saboda bai ga kowa kasa
ba.
"Karasa min shi zaka yi?" Ummi tace suka sa dariya.
"Yau daya dai nima inyi shagwaba irinta Adda" Emzee ya zagaya bayan babansa ya sako
hannuwansa suka zagaye wuyan baban.
"Anya Zayyan ba zamu jira idan matarka ta haihu nayi goyon ba..na jika ne kamar
buhun siminti" Zayyan yace yana riko hannuwan nasa da suke wurin wuyansa.
Ummi ta yi gaba kuwa "Ah to ku bari na tafi don kada ma na dorar"
Emzee zai sake shi kenan ashe Zayyan shammatarsa yayi sai ji yayi ya raba kafafunsa
da kasa ya zagaye falon dashi. Kunya sosai ta kama Emzee sai gashi zai gudu daga
falon Zayyan ya janyoshi ya rungume.
"Allah Yayi muku albarka"
"Amin Daada" ya amsa da 'yar kwallarsa. Kasa yayi da gudu Zayyan ya kife akan
kujera.
"Fillo yau fa sai kinyi min tausa"
"Kai da kake jin goyo nima bari nazo na hau"
Wani kallo yayi mata kasa-kasa ta tashi tayi gaba da sauri. Har yanzu tana jin
kunyar mijin nata da baya rabo da tsokana kamar ba babba ba.
***********
Kwana biyun nan Radhiya bata komai sai bacci. Ita bata san ma ashe basa samun hutu
ba sai da ta dawo gida. A rana ta biyu sai ga Yousuf ya iso. Yayi wani fes dashi
aka fara tsokanarsa ya kusa zama ango saboda yadda Babban Arifah ya matsu da tayi
aure bai ga dalilin jira ba. To shima baban Yousuf din ya matsu nasa tilon dan yayi
aure shiyasa tun a waya su ka gama daidaitawa da Excellency. Abu ne na manya kuma
kowa yana ji da nasa.
Da yamma Emzee ya kaishi gidansu Arifah yace to ya nemi mai dawo dashi don yasan
yau din ta dabance a wurinsu. Shi kuwa gobe zai koma Kaduna makaranta yana da
abubuwan yi. Yana komawa gida an kawo copy na farko na aikin su Radhiya. Sakawa
akayi a falon Daada, Ummi, Bigman da Camera man da uwar gayya. Taken National
Anthem aka fara kafin nuna mutane a garuruwa daban daban na kasar da muryar Radhiya
tana bada takaitaccen uwa ma bada mama Nigeria uwar 'ya'ya da yawa.
Daga nan fa aka shiga shirin sosai. Komai yayi tamkar kana kallon film da aka bata
lokaci wurin kawata shi. Abin ya kayatar da Zayyan matuka. Mai camera dai
Excellency ya sallame shi amma duk da haka Zayyan yayi ihsani sosai. Bigman kuwa
cewa yayi rabin kudin zai karba saboda shi kiransa kawai da akayi ya bude masa ido
da abubuwan da bai taba tunaninsu ba bare ya damu. Hasali ma dai bai dauki soja da
wata daraja ba da ta wuce idan ya gansu suna checking a hanyoyi ya zagesu sama da
kasa ya wuce abinsa. Alfarmar da yake roko shine idan wannan shiri zai cigaba don
Allah yana son zama daraktansa kada su nemi wani. Inda baiyi musu ba sai a fada
masa ya gyara shima yanzu yake wayewa da aikin. Su Ummi sunji dadi nan take Radhiya
ta turawa Supervisor dinta sannan ta kara da doguwar wasika game da zato da suka yi
mahaifinta soja ya rasu da dawowarsa. Cikin minti talatin matar ta kirata a waya ta
tayata murna kuma ta yaba matuka da aikin na awa guda da aka yi a Nigeria. Sunyi
mamakin saurinta tunda wata biyar aka bata. Basu san dan Nigeria da dagewa bane.
***********
Bayan kwana biyu Radhiya tana ta rubutu ta saka computer a gaba tana hada report
akan project dinta a daki. Sanye take da dogon wando da rigar sanyi tayi parking
gashinta a tsakiya ba a nutse ba wani ya zazzaro ta gefe da bayan. Ummi ce ta shigo
da plate din fruits da ta yanka ta mika mata.
Fuskarta a sake take tace "Gashi 'yar gatan Daada kun maidani 'yar aiki ko" sai dai
har ranta Alheran tana burgeta. Waye zaice yarinyar za ta nutsu haka har ta bawa
karatu mahimmanci.
"Ummina yi hakuri so nake na gama ne kafin jibin da zamu tafi Sumaila"
"Wasa nake yi miki. Nima ina so inga kina kokari ai." Leka aikin tayi ta dan
karanta wasu layuka ta koma ta zauna akan gado "kin kusa gamawa ne?"
"Inzo?" Ta tambaya don tasan kila akwai abinda Ummin take son cewa.
Kujerar gaban working table din ta juya zuwa bangaren Ummi tana fuskantarta.
Murmushi Mairama tayi kafin ta soma magana a nutse "Alheran maganar aurenki da
Awwab ce ta taso"
Gabanta taji ya buga da ta tuna wancan karon yadda abubuwa suka kasance. Umminta ta
kula sai ta kwantar mata da hankali.
"Wancan karon na rabaku ne domin samar da maslaha. Yanzu kuwa sai inda karfina ya
kare babu mai rabaki da Awwab sai Allah"
Kunya ta kama Radhiya saboda Ummi bata saba yi mata magana haka ba. Dauke kai tayi
kamar bata kula da 'yar ta ta ba ta cigaba da magana.
"Nasara ta fada min cewa idan iyaye maza sun zo jibi akan maganar Arifah da Yousuf
zasu roki alfarmar ayi auren karshen watan nan saboda basa son a ja lokaci kuma a
ganinsu sauki nw tunda zasu zo taron baban naku dama. To shima maigidan nata ya
fadawa Daada shine Daddy dinku ya yanke shawarar idan anyi finalizing maganar a
haka to za'a daura auren Arifah ranar asabar ke kuma lahadi domin kawo sauki. Zai
kama 27th da 28th December. Biki sai bayan sati biyu lokacin kinga an gama taron
karrama Daada sannan munyi namu"
Ai jikin Radhiya sai yayi sanyi da ta gama lissafi a kanta kwanakin basu fi sha
wani abu ba. Nutsuwarta ta nema ta rasa duk ta wani firgice.
Hawaye ta soma "Shikenan ni daga dawowar Daada sai aure"
"Ki godewa Allah da yanzu haka za'a aurar dake mahaifinki yana kasa"
Kuka ta fashe dashi sosai Ummi tace ko tayi shiru ko ta kira Awwab tace masa ya
nemi wata ita ta fasa. Da saurinta ta dago kai sai taji kunya.
"Ki kwantar da hankalinki na yarda da Awwab kuma kema kin sani zuri'ar su Mami
sunfi karfin komai wurinmu. Sannan ki zama cikin shiri daga Sumaila wurin Innawuro
zaki zauna sai ana kwana uku daurin aure tace gyara zata yi miki. Mun riga munje da
Daada da kina can aiki"
Tashi Radhiya tayi ta dare gadonta da tsalle "ni ko gadon ban mora ba Ummi zaku
koreni"
"Sai ki zauna morar gado sarkin shirme"
Bayan kwana biyu suka tafi Sumaila ita da Ummi taron da Malamijo ya shirya. Emzee
ya riga ya koma makaranta bazai fito ba sai gab da taron da za'ayi. Washegarin
zuwansu sauran 'ya'yansa kowa ya gama zuwa. Su Habu da Bature sun ajiye iyali shima
Ayuba saura watanni kadan bikinsa.
Tun dare aka fara soye soyen nama da kayan miya kai kace biki ne za'ayi washegari.
Yara da manya abin ya zame musu sabo amma kowa murna yake yi. Shadaya na safe
washegari kowa da kowa ya hallara a katuwar tsakar gidan da aka saka mata rumfa da
tabarmi. Kujera daya ce a tsakiya Malamijo ya hakimce abinsa bayan an bude taro da
addu'a yace kowa ya tashi ya gabatar da kansa masu 'ya'ya kana gama fadin naka
yaranka su fadi nasu.
Salame ce ta fara tashi tana ta hura hanci tasha leshi mai kyau amma fa ita daban
shima daban. Yadda ta matsawa Halifa lamba cewa tayi idan ya bari aka ganta a
wulakance to kansa ya wulakanta. Cikin shagunan mahaifinsa yaje ya siyo mata mai
kyau kuwa bai tsaya kanta ba ya siyowa duka yaranta sannan ya bawa Hibbah na Rahima
yace ta kai dinki amma kada ya kai girmanta. Har kofar gida ya kai mata sai taji
dadin zuwan nasa fiye da kayan. Ciki ta kaishi wurin kakarta ta kasa boye
farincikinta tana ta cewa ga yayanta na Kano. Babanta ya saya mata mayafi mai kyau
daidai aljihunsa da ya dace da kayan sai gata tayi wani irin kyau kakarta tayi ta
wasa ta kafin ta fito. Da ta iso gidan a cike daya daga cikin kannenta ta gani ta
tambayesu ina Ummansu yarinyar a tsiwace tace mata ta duba mana ko ta bata ajiya
ne. Ajiyar zuciya tayi ta rinka dubawa ta ganota a can gefe taki sakarwa 'yan
uwanta jiki. Yawan mutane yasa ta zauna a kusa da wata mai kama da larabawa sai
wani irin kamshi take yi tayi kyau cikin jar atampa super.
Radhiya ta dukufa yiwa Awwab text bata kula da ita ba sai ta taji Salame tana fadin
sunanta ta ajiye wayar a cinyarta ta koma saurarenta.
"Sunana Salame kamar yadda kuka sani kuma mijina Alhaji ne don ya sauke farali tun
kafin wasu su fara rike naira"
Rahima cusa kanta tayi a cinyarta saboda kunya Halifa yaji kamar yayi tsuntsu ya
bar wurin.
"Babban dana ma da babansa duka alhazawan ne yayi karatu a kasar Misira ne ko ...."
neman Halifa ta rinka yi da ido ya dukar da kai.
"Zauna haka Salame bari yaran suyi da kansu za'afi gane juna" Hajjo ta dakatar da
ita. Malamijo ya samu ta dawo bayan ta gama fushin yanzu sannu a hankali yake
binta.
"Halifa sunana a Kano muke da zama"
Salame tayi caraf ta amshe "waye zai ganeka a haka? Ka fada musu sunan babanka Alh
Salisun kwari wanda kowa yake gani a talabijin"
Duk da ita ta haifeshi ko kadan baiji dadi ba dama ga kadaicin rashin zuwan Emzee
saboda makaranta. Yana zama Rahima ta mike a kunyace. Ita bata san mutanen gidan
sosai ba Radhiya kuwa ta bita da kallo.
"Sunana Rahima Usman" ta kara da sunan mahaifinta a zatonta haka ya kamata tayi
tunda taji an yiwa Halifa fada.
"Kin manta baki ce musu me buga iska a titin...."
"SALAME!!!" Malamijo yayi mata wata irin tsawa da shi kanshi baya jin ya taba daga
murya irin haka. Wata irin dabi'a ya karance ta da ita yanzun nan. 'Ya'yan da ta
haifa da masu kudi sune mutane Rahima kuma bata da amfani. Da girmanta ta janyo wa
kanta zubewar mutumci a gaban kannenta da 'ya'ya.
Ummi sai tayi saurin mikewa domin katse shirun da ya ratsa wurin ana ta kallon
Salame.
"Sunana Mairama daga Adda Salame sai ni"
Harda masu ihun murna cikin kannen saboda tuni ta fara janyosu a jiki tun bayan
yadda