Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
Zayyana da tun daren jiya aka yi
mata nata ta tashi da sauri tayi bakin kofa za ta karbi DK ta ga baya hannun Mama
ko Mami.
Baki ta tura tana leka waje "Mama ina DK?"
Mami ta daure fuska tace "Meye haka babu gaisuwa ni matsa ki ban wuri yana wurin
Ibrahim a mota"
Murmushi tayi kafin ta matsa tana gaishesu. Mama tace taje ta karbo shi kunya take
tana ganin idan ta fita kowa zai gane meye tsakaninsu. Ganin Hibbah ta taso zata
karbo shi yasa ta fita da sauri. Hibbah tayi dan murmushi suna hada ido da Rahima.
Fauziyya ta hararesu "gulmammu ko dai ku fasa mana kwan nan ko yau na danneku a
daki ayi muku balotelli ko ya kike gani babbar yaya" ta kalli Radhiya.
Dariyarsu kadai ta isa tona asiri amma Zahra tace "ku bari ta dawo mu sakata a daki
ta fada ko yau ayi taro tana gida"
Hibbah da Rahima dai sai dariya Fauziyya tace su din ma duk sai ta binciko nasu
tunda Radhiya ta kauce su ne next.
Wata irin tafiya Zayyana ta rinka yi kamar bazata isa wurin motar ba saboda irin
kallon da Ibrahim yake yi mata. Tana zuwa ya fito da DK a hannu yana murmushi.
"Kawo shi" tace tana mika hannu.
Kara makale shi yayi a jikinsa yana harararta "dama ba wurina kika zo ba?"
"Ni kanina nazo dauka"
Wani irin kallo ya bita dashi "Ya kina ganina amma ta wannan yaron kike yi. Tun
wuri ki sani bazan yarda da wasan kanin miji ba."
Kamar gaske ya hade rai ita kuwa dariya ma take yi "Ka jira a haifi kanin mijin
wannan dai twin dina ne ko ba ka ji sunansa ba...Zayyan da Zayyanatu" tayi masa
gwalo.
Bata fuska Ibrahim yayi ya tale baki yadda take yi ta cigaba da dariya. Muryar kuka
ya soma yi mata "idan ba kin janyo na rage masa matsayi ba tunda haka ne. Tun farko
ni me yasa ba'a saka min Zayyan din ba shi a saka masa Ibrahim?"
"Saboda shi Zayyan kanina ne, shi kuma Ya Khaleel...." juya idanu tayi bata karasa
ba ta kama hanya za ta gudu.
Ibrahim kamar wanda aka dora a gajimare yake yawo don dadi ya biyota ya mika mata
shi. Tana karbarsa ta kai hancinta jikin nasa tana gogawa tare da yi masa murmushi
"baby DK dinaaaa"
Jingina Ibrahim yayi da bango yana kallonta da jin sabuwar soyayya na dibansa "yaro
kaji dadinka ko yaushe ni kuma zan sami arzikin ayi min haka wa ya sani"
Kai ta dago ya kashe mata ido bata iya cewa komai ba saboda kunyar da ta ji ta
shige ciki ta barshi a tsaye yana ta murmushi.
Emzee ne ya shigo ta karamin gate da ledar mangaro masu kyau wanda ya sauka daga
motar ya tsallaka siyowa da suna hanya kafin su shiga kwanar gidan. Yana karasowa
motoci uku suka shigo manyan mata wayayyu suka rinka fitowa daga ciki. Mom Arifah
kadai suka gane suka gaisa da ita da sauran matan tace Emzee ya kaisu wurin
Mairama.
Yana gaba sauran duka suna bayansa da ita suka shigo. Su Radhiya suka gaishesu
sannan Zayyana ta hau sama ta fadawa su Ummi. Gayyar lallen ce ta tashi dama sun
saka wata leda a wurin basu bata ko ina ba suka tafi daki.
Dukkaninsu matan manya ne su takwas. Biyu matan gwamnoni, uku matan sanatoci,
karamar ministan ilimi sai matar ministan ilimin wai sun zo sake yiwa Mairama murna
ne zasu koma garuruwansa. Duka Mom Arifah ce ta gayyato su. Abubuwan ci da sha aka
kawo musu Salame tana daga daki take jin muryoyin manya don su Yadikko bayan gidan
suka tafi wurin aikin nama kafin isowar su Mama da Mami da zasu hadu ayi abinci da
Tante. Ko da wasa bata hangi kanta tana taya aikin komai ba a gidan banda kwanan
bakinciki da tayi jiya saboda yadda ganin Alh Salisu ya kara tada mata hankali shi
da matarsa. Fitowa tayi tana hura hanci Mairama kuwa tace musu ga yayarta tana
nunata.
A mutumce suke gaisawa da ita sai ta saki fuska ta samu ta zauna a kujerar da tafi
kusa da Mom Arifah tana ta wangale baki.
Hannun Ummi da Mom Arifah ta gani ta yaba "gaskiya ina son lallen nan Mairama yaya
zamuyi? A ina mai yi take? Yayi kyau sosai"
Dadi Ummu taji " 'yata ce tayi min sunanta Rahima"
Matar gwamnan Abia kasa hakuri tayi tana shafa hannun tare da kallon kafar gwanin
sha'awa "ni dai a kirawo ta idan tana kusa tayi min inje dashi gida yarana su
gani...nawa ake biyanta don basira irin wannan nasan da tsada"
Salame an dade ba'a shiga aji ba amma dai tana fahimta kan bai gama toshewa ba. Ji
tayi jikinta ya soma rawa taji kudi hankalinta a tashe 'yarta zata yiwa matar
gwamna lalle. Sauran ma kowa tace tana so saboda yadda zanen ya fito radau sannan
kalar tayi maroon sosai. Bude baki tayi za ta ce ko dari uku ne ma su kawo sai Ummi
ta riga ta.
"Ku da 'yarku ko nawa ne ma kuka bata sai dai muyi godiya"
Mugun kallo Salame ta watsa mata sai dai babu wanda a kula a zuci tace "shegiya
'yar bakin ciki"
"No, no please Ummin Alheran ki fada a biya don nima zanyi. Muna da yawa bare ace
alakoro ne" Mom Arifah tace suna dariya.
"Yanzu kuke magana" Salame ta sake cewa a ranta.
Ummi dama ko kadan bata da niyar manyan matan nan suci bulus. Ta dai fadi haka ne
don kada a ga kamar bata da kara. Amma wannan ai kofa ce da Rahima zata samu.
Aunawa tayi ta ga a garin Abuja suke inda komai kudi ne.
"N2000 take yin hannu da kafa"
Wata Dr. Lara 'yar lukuta da ita karamar ministan ilimi tace "kirawota ta fara yi
mana ko a gama da wuri tunda kuna da aiki a gabanku"
Matar gwamnan Abia kuwa jakarta ta balle ta dauko bandir din dubu daya ta mikawa
Ummi "take this hundred k sister Maryam for the eight of us."
Baki Ummi ta bude zata yi godiya Mama ta rigata a gayance don kada a rainasu "Thank
you Madam"
Hannun Salame har wani kaikayi yake yi burinta Mairama ta miko mata tunda duniya ta
shaida ita ta dau cikin Rahima ta haifeta ta shayar. Saboda haka tafi kowa hakki
akan dukiyar 'yarta.
Gilmawar Emzee Mami ta gani yana dauke da plate da ya bawa mai aikinsu ta yanka
masa mangwaron zasu sha shi da Ibrahim tace ya kirawo Rahima. Zuciyarsa har wani
dan tsallen murna tayi ya hau sama ya kwankwasa musu kofa. Radhiya ce ta amsa ya
dan daga murya don kofar a rufe take.
"Turo min Rahima ana kiranta"
Kululu haka cikin Rahima ya kada da taji muryar Emzee. Hannunta kasa rike ledar
lallen nata tayi sosai saura yatsa daya ta gama yiwa kanwarta Khadi ta tashi bayan
ta lallaba ta gama.
Hijabinta ta gyara ta bude kofar yana tsaye ya jingina da bango yana shan mangwaron
da fork. Mika mata yayi ta girgiza kai cike da kunya. Kofar fita daga falon ta nufa
yana tsaye har lokacin a inda ta ganshi da ta fito.
"Kawar soja"
Dakatawa tayi amma bata juyo ba har ya iso inda take ya tsaya a gefenta. A hankali
yace "abinda muka yi jiya bai yi kyau ba ko?"
Sai lokacin ta kalle shi da idanuwan da suke narke masa zuciya cikin sanyinta tace
"yayi kyau sosai"
"Amma kika kasa fada min?" Yace kamar yana fushi.
"Kayi hakuri Ya Emzee" ta kira shi yadda taji Zayyana na fada.
"Kowa fa ya fada ke kadai ce banji kince komai ba"
"Kayi hakuri yayi kyau"
"Sosai?" Yace excitedly
"Sosai sosai"
Murmushin fuskarsa ya dauke "kai duk da haka ban hakura ba. Yau idan an shirya za'a
tafi idan baki ganni ba a wurin kada ki shiga motar kowa I will come for you"
Idanunta ta zare tana kallonsa ya nuna mata kasa da ake jiranta suma jin Mama na
cewa ya fada mata ta taho da kayan lallenta.
"Idan baki jirani ba zamu dena kawancen nan so please ki jira ko bana nan zan dawo"
Kallonsa tayi ta dauke kai ya dan sake matsowa ya rage murya "Rahima please do this
for me"
Bai jira amsarta ba ya sauka ita kuma ta koma ta dauko kayan lallen ta sauka
gabanta na wata irin faduwa tana jin kamar rayuwarta bazata taba dadi ba idan babu
shi a cikinta. Sai dai kuma tunanin yafi karfinta ta kowace fuska yana karyar mata
da gwiwa.
Jikinta ne yayi sanyi da Ummi ta nuna mata su wa za ta yiwa. Da wane hannun za ta
taba wadannan matan masu kwarjini haka. Da kyar ta iya cewa bari ta kwaba wani
saura kadan wancan.
Yawun bakinta har bushewa yayi tana tsoron kada taje tayi musu mistake. Ummi ta
lura da ita sai ta tashi tabi bayanta zuwa kitchen din da ta shiga da ledar kayan
lallen. Salame ma sai ta bisu da sauri kafin Mairama taje ta bata dubu biyar ta
murkushe sauran ta cinye ita kadai. A fusace take tazo shiga maganarsu ta dakatar
da ita.
"Ummi kingansu kuwa? Ni dai tsoro nake ji"
Ummi ta tayata dibo ruwa tana tsiyaya mata a robar da ta zuba lallen da kayan hadi
"na fiki tsorata in fada miki wai nice da matan gwamnoni a gidana"
Rahima tayi murmushi "kema da kanki?"
"Ahh tabdi to ni na taba ganinsu ne?"
Murmushi ta sake yi sai kuma damuwa ta bayyana "kada hannuna ya rinka rawa"
Kafadunta Ummi ta dafa "Rahima! So nake kasuwa ta bude miki ace matan manyan nan
kike yiwa kunshi kina jina. Ki ajiye tsoro ki tuna cewa neman halak kike yi zaki
taimaki Baffanki ko?"
"Eh"
"To ki nutsu yanzu haka dubu dari aka baki amma zan ajiye sai zaki koma gida na
baki"
"Dubu dari Ummi?" Rahima tace mamaki ya isheta ta rungume Ummin tana murna "in bawa
Baffana da ke da Umma sai mu raba sauran da kannena"
"Kut..." Salame tace tana yunkurin shiga kitchen din.
"Banda ni ki bawa Baffanki da Addata su sa miki albarka kinji Rahima. Allah Yasa
budi ne zai zo miki da hakan."
Kasa boye murnarta tayi ta kuma rungume Ummi "Ummi nagode...dama kece Ummana da
naji dadi"
Dammm zuciyar Salame ta buga taji wani irin abu ya tokare mata wuya. Ka haifi da ya
rinka fatan dama wata ta haifeshi...kenan fa Rahima bata sonta ko?
"Kada na sake jin magana makamanciyar wannan kina jina. Ko me Adda Salame za ta yi
miki kiyi hakuri domin duk duniya ba ka da masoyi sama da mahaifiyarka. Allah Yana
fushi da mai sabawa iyaye"
Hawaye ne ya ciko idanun Rahima ta fashe da wani irin kuka "Ummi bata sona"
Da sauri Mairama ta sake rungumeta ko damuwa da lallen da ta cambala mata a jikin
riga bata yi "tana sonki Rahima, nima kuma ina sonki. Baki san kece autar Ummi
ba...Karami da kike gani dan karo ne kece autar"
Murmushi Rahima tayi saboda Emzee da Ummi ta ambata.
"Ko ke fa...wanke fuskar muje mu caski naira"
Da gudu gudu Salame ta bar wurin kafin su fito ta nufi dakinsu. Abin da ya zame
mata sabo a rayuwarta tayi wato kuka akan yadda Rahima ta dauketa. Yanzu ashe
abinda take yi mata ya isa ya sanya Rahima jin inama ba ita ce mahaifiyarta ba?
Hawaye sosai take yi zuciyarta ta kuntata. Tabbas ta cutar da 'yarta saboda wani
dalili mara tushe wato rashin arzikin mahaifinta. Zama tayi a dakin tana ta tunane
tunanen abubuwan da ta rinka yiwa mata. Sai kuma shaidan ya tuna mata da kudin da
aka bada na kunshi. Kamar an tsikareta ta tashi tayi sama saboda bata ga Ummi a
falon ba. Gara ta samu ta daidaita da 'yarta yadda ko arzikin yazo tare zasu ci
abinsu.
Banka kai tayi cikin dakin kai tsaye ta sameta tana nade gift da wrapping paper.
Kallon banzan da ta saba tayi mata sannan ta rike kugu ta mika mata hannu.
"Bani kudin"
Sai da Ummi ta bawa iska ajiyarta na cikakken minti daya ta karasa abinda take yi
kafin ta dago kai "kin bani ajiyar kudi ne Adda?"
"Kada ki raina min hankali Mairama ina kokarin muyi komai cikin lumana tunda gidan
da mutane. Kudin da aka bawa 'yata ta cikina Rahima na kunshi dubu dari nake magana
a kai"
Ummi ko ci kanki bata ce mata ba ta tashi ta dauko kudin a cikin wani kit ta mika
mata.
"Wato da har kinyi musu mazauni a cikin kayanki saboda bakar mugunta"
"Adda Salame..."
"Sunana kenan. Idan kinso kice Salamen kai tsaye ba damuwa zanyi ba"
"Kudi kika zo karba kuma na baki saboda haka ki fice min daga daki kafin ranmu yafi
haka baci" Ummi tace a haka ma kokarin danne zuciyarta take yi sosai akan halin
yayarta da yadda take yiwa Rahima.
"Oho dai, da fa bamu san asali bane sai ayi mana burga. Kunje kuna ta kwantar da
kai a gaban mutane saboda ace kuna da kudi"
Kashingida Ummi tayi akan gado ta nuna mata kofa "sauka kije ga irinsu can kema ki
kwantar da kan ko za'a dace"
Gani tayi da gaske bazata biye mata ga bakar magana ta yaba mata sai ta sauka kawai
tana kunkuni. Rahima na ganinta da envelop din kudin taji wani irin kunci a
zuciyarta don tayi imani da wuya ko kwandala ta bata a ciki wanda zata bawa
Baffanta da Iya. Hawaye ke neman subuce mata taji sallamar Emzee.
Matan wurin ke ta yabon abinda su ka yi jiya ana cewa iyayensu sunji dadi shi da
yayarsa kowa da baiwarsa. Duk zancen da akeyi Rahima yake kallo da take duke tana
yiwa wata lalle a kafarta. Kin kallonsa tayi saboda a haka ma da kyar take yi
jikinta ke rawa. Yadda take motsa hannuwanta yayi ta kallo har ta gama yiwa matar
ta soma na wata sannan ya tafi.
**********
Karfe uku da rabi Awwab, Raji, Yousuf da Bilal suka fito daga gidan Mami kowa sanye
da fararen kaya masu ado da koren zare da hula koriya. Saidai kowa dinkinsa daban
ne amma shigar kenan kore da fari.
Awwab nasa kayan wani lallausan yadi ne fari kal mai kyau anyi masa riga iya gwiwa
sai hannu dogo ya saka links masu wani stone green. Aljihun gaban rigar rabin yadin
da aka yi shi fari ne daya rabin kuma green sai yayi kamar triangle. Maballan rigar
har wuya su ma duka green dinne sai wani siririn ado na green din zare daga gefe
saya. Hular kansa da tasha kari hadin zare green da fari ce dai. Kafarsa farin
takalmi cover shoe sai silver agogon dior. Kamshi yake fitarwa mai dadi shi kadai
yake murmushi yana tsaye a gefen mota ya zura hannu daya a aljihun wandonsa yana
danna waya.
Text ya turawa amaryarsa cewa zasu dauko Arifah su biya su dauketa sannan su wuce.
(Ni kunyar ganinka nake yi) ta rubuta masa.
(Ni kuwa kwana nayi mafarkinki...can't wait to see you baby)
Hoton fuskar kunya ta tura masa na whatsapp shine yake murmushi.
"Mintuna kadan ya rage ka ganta kake wannan murmushin kai kadai" Bilal yace yana
bude gaban motarsa.
"Bazaka gane bane dan uwa....I love her to the moon and back" yayi maganar yana
lumshe idanu.
"Yau da bani da Fauziyya da ka saka ni neman aure amma yanzu sai dai nayi maka
dariya don duk abinka sai ka jira anyi biki zamu bari ka dauketa"
"Kayi hankali kada ku ja mu bar abin fada har jikoki"
"Me kenan?" Yousuf yace yana bude motar da zasu tafi shi da Awwab.
"Bari dai nayi shiru wadannan mazajen kannena ne kada su raina ni"
Sai da suka gama barkwancin Raji da Bilal suka shiga mota daya Awwab da Yousuf guda
daya.
Su Awwab gidan Excellency suka wuce ko shiga basu yi ga Yousuf ya kira Arifah. A
shirye take ta fito daidau gate inda suka yi parking. Shaddarta fara ce itama sai
paint work green da stones daga wuya har kasa amma ba'a cika adon ba. Ashoke aka yi
mata dauri dashi mai hawa-hawa tayi matukar kyau fuska tasha make up. Ga mayafinta
green ta yafa a wuyanta. Yousuf gabadaya ya rikice ya fita ya bude mata kofar baya
tana zama Awwab ya fito ya karbe key din motar.
"Ina hauka ne zan bari ka tuka ni idanunka suna bayan mota? Shiga kawai muje kada
kayiwa matata asara"
Arifah dai kunya take ji murmushi kawai tayi tana gaisheshi. Yousuf dama jira yake
yana shiga ya rungumota yana mata rada a kunne wai jiya basu gama taya juna murna
ba. Da hannu ta rinka nuna masa saitin Awwab dake tuki.
"Wannan yafi kowa fitina ki kyale shi kawai"
Shiru yayi bai ce komai ba albarkacin Arifah da yake ganin mutumcinta sosai. Suna
zuwa gidan an shimfida katuwar darduma wadda su Daada suka yi jam'in sallar
la'asar. Su biyu suka tada tasu Arifah ta shige ciki.
Yau ma Mairama da kanta ta shirya Zayyan kamar kullum ya saka shadda army green
dinkin tazarce. Dayake tsayi gareshi ba karamin kyau yayi ba. Sai da ta tabbatar
ya gama fitowa ta rinka masa wankan turare sannan ta dauko nata kayan. Itama farar
shadda ce riga da zani amma dinkin Nijar anyi mata aikin green din zare ga
mayafinta to-match. Ankon kenan dama su fito a 'yan Nigeria sak banda masu taro
wato Major General Zayyan, Muhammad Zayyan (Emzee), Zayyanatu Mustapha da Zayyan
Hadir. Nasu kayan iri daya ne army green shadda.
Suna fitowa daga dakin Radhiya ta fito da ashokenta a hannu tayi wata kwana da
ribas ta dawo kawai sai ta daga tsalle ta dane Daada.
"Anya banyi garajen aurar dake ba, Fillo yarinyar nan bata girma ba fa"
Ummi sai dariya "kunfi kusa soja da 'yarsa."
"Ni dai ku tsaya nayi muku hoto" tace tana gyara musu tsayuwa "wayyo ni Daada da
Ummina sunyi kyau"
Dariya ta basu ta matsa baya zata dauka da wayarta Zayyan ya rungumo Mairama a
jikinsa. Ita kunya Radhiya kuma ta kanne ido daya wai a zuwan bata gani ba. Sunyi
bala'in kyau ta rinka daukarsu Zayyan yana biye mata suna yi a tsaye ko a zaune.
Muryar Arifah da ta jiyo ne ta bar wurin da sauri taje ta karasa shiri.
Hudu da ashirin kowa ya sauko sai fararen kaya kake gani da koren mayafi ko hula.
Zayyana gown dinta aikin da farin zare aka hada shiyasa ta saka farin mayafi bayan
anyi mata daurin yayi wanda dukkansu matan shi suka yi mai hawa-hawa da dankwalin
kayan.
Mutane ke ta fitowa babu wanda ya lura Rahima bata fito ba. Ita kadai take kokonto
idan Emzee yaki dawowa ta kade. To amma babbar matsalarta yanzu bai wuce bayanta da
yake ciwo saboda dukawa ba don yau ta aikatu.
Irin kayan Arifah sak hatta takalmi da jaka Radhiya ta saka rigar tasu mai high
neck. Basu saka sarka ba sai wasu doyayen dankunne green and white masu tsada da
daukar ido.
Ta kware da tafiya da heel bata jin wahalarsa ko kadan tana taku daidai ta iso
gaban motar. Zagayawa yayi ya bude mata daya gefen gaban yana tsaye zata shiga wani
ni'imtaccen kamshi na shigarsa ta ko ina ya rike mata hannu. Kallonsa tayi sau daya
ta dauke kanta.
"You look sweet baby"
"Ka fini yin kyau Hammana" tace tana murmushi.
Hannu kawai yasa ya janyota ta fito ya sake matso da ita jikinsa sosai yayi musu
selfie.
"Akwai bil adama a bayan mota" cewar Yousuf bayan ya sami chance din kaiwa Arifah
kiss a kan hancinta tana rufe idanu.
Dariya Awwab yayi