Advertisements
Chapter 7 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 99

18K to 21K   out of 295.8K words

alkhairi. Idan ta sake haihuwa ke zaki dawo
ko?"

Mairama ta tashi daga wurin da sauri saboda kunya. Nene tayi masa dakuwa tana
murmushi "kuji min dan kaniya, wato a gaban nawa kake rashin kunya ko Zayyanu"

"Fada nayi fa saboda kada ace wata daban ce za ta zo." Tare su ka yi dariya don ta
saba da barkwancin surikin nata.

Kofar dakin ta kalla ta tabbatar Mairama tana wurin kishiyarta sannan ta dan matso
fuskarta babu alamun wasa "Zayyanu nasan kana sane da son da Salame take yi maka"

Gabansa ne ya fadi ya dago kai yana kallonta da kallon kofa "Nene ki bar zancen
nan, yau ko Mairam zata fadi ta mutu bazan auri Salame ba. Matar da aure bai hanata
nunawa mijin kanwarta soyayya ba"

"Tun yaushe ta fara son ka?"

"Kafin muyi aure...don Allah bana son kowa yaji. Ni dai babu abinda ya taba hadani
da ita"

Hankalinta taji ya kwanta "nagode Zayyanu. Ka rike min amanar Mairama. Ga maraici
ga rashin dangin uwa har yau mun rasa a wace rugar ma suke zaune. Duk tsiyar
Malamijo yana ta kokarin nemansu domin ya faranta mata. Salame kuma ka barni da
'yar banza. Idan ta nemi tada muku hankali da kaina zan gyara mata zama don ba
gagararmu tayi ba"
Kafin azahar sun koma Sumaila inda ta sake kwana biyu suka bar garin bayan ihsani
mai tsoka da ya yiwa Malamijo da matan gidan. Mairama har mamakin ina ya sami kudi
haka takeyi saboda ita tasan duka duka albashin nasu babu wata tsokar kirki.

Sun baro Sumaila tana sa ran za su wuce Sakkwato sai gani tayi sun shiga cikin Kano
zuwa wata unguwa yana yiwa dreba kwatance. Gaban wani gida zubin zamani a wancan
lokacin mai kyau da tsari tun a waje aka ajiye su. Mukulli ya dauko da ga aljihunsa
ya bata yana dauke da Radhiya.

"Bude mana da sunan Allah"

Kallon tuhuma take masa yayi murmushi da ka yayi mata alamar ta bude. Ba musu ta
bude yana cewa ta shiga da Bismillah. Farfajiyar gidan tana da dan girma daidai
mota guda daya. Sai kuma ainihin ginin wanda flat ne gidan. Yana gaba tana biye
dashi zuciyarta da tarin tambayoyi har ciki.

Wani korido su ka fara bi a karshensa kofa take inda suka tarar da katon falo ga
kofofi a ciki. Daya bayan daya suke shiga yana mata bayanin. Kitchen, dakuna hudu,
store da kuma bandakuna ko ina da fenti amma babu kaya. Daki daya ne aka shimfide
da leda ga katifa sabuwa da filo biyu sai zanin gado a cikin ledarsa ko budewa
ba'ayi ba.

"Sojana ina ne nan?"

"Mairam ga gidan mijinki na halak yau kin shigo"

"Gidanka ne nan?"

Takowa yayi gabanta ya hadeta da Radhiya ya kankame.
"Gidanmu dai Mairam"

Zaunar da ita yayi ya mata bayanin kudin gadonsa da ya narkar a wannan gini domin
inganta rayuwar iyalinsa. Ya zabi zuwa Kano saboda gujewa fitina daga bangaren su
Jume. Dama yanzu matsanancin fushi suke yi dashi saboda an gama taron suna basu ga
komai ba. Da Jume da tado zance yace gida dai shima na mahaifinsa ne, idan basa son
ya rabesu a raba gado ko dakin mahaifiyarsa a bashi. Sunyi rigima ba kadan ba ya
fito musu gar da gar dinsa a soja mara daukar raini ko kadan. Suna ji suna gani
dole suka hakura da haram din da suka kwallafawa rai.

Addu'a ta rinka jerowa yana amsawa daga nan yace to fa ta shirya jiya da ya taho
cikin Kano siyayya yayi musu yana so ko sati suyi a gidan kafin ya koma aiki.

Kitchen ta leka ya siyo karamin risho, tukwane biyu da yan kayan bukata. Wani sabon
shafin amarci su ka bude a gidan ga diyarsu a gefe tana samun kulawa. Wasa-wasa
kwanansu goma sha biyu sannan su ka fara shirin komawa Birnin Shehu. Duk yadda taso
kuwa yaki kaita gidan Salame don baya kaunar duk wani dalili da zai sa su hadu.

**********

Watansu biyu da komawa Zainab ta haihu. Sai dai ita a gidan iyayenta ta zauna su
Mairama da Mami ke zuwa kullum har akayi suna. Jariri yaci sunan kanin baban Hadir
da ya rasu gabanin haihuwarsa Ibrahim.

Rayuwar wadannan bayin Allah haka ta cigaba da tafiya cikin so, yarda da aminci. A
kowane mataki su na kokari wurin ganin sun tsayawa juna cikin dadi ko akasinsa. Da
Salame ta haihu ya barta taje ta kwana hudu a Kano inda ta rinka fuskantar Gadara
da wulakanci daga wurin yayarta ta. Da yake ta fara sabawa da wannan bakon hali sai
ta daure zuciyarta don kada ayi batacciya.
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: ....ALLAH NA NASA 11.

"Ummin Awwab me yake damunki ne kwanakin nan sai wata rama kike yi kamar wadda za'a
yiwa kishiya"

Dago kai Mairama tayi jiki a sanyaye "Mami ni kaina na rasa gane dalilin wannan
rama. Kuma ke shaida ce ina cin abinci sosai"

"Kinbi kin dashe kinyi fayau. Jiya ina ji baban Radhiya yana fadawa Hadir wai kinki
bari ku je asibiti. Baki ga yadda ya damu ba fa"

Mairama tayi shiru ita kanta ramar da take yi tana damunta. Dadinta ma dai Radhiya
kullum kara habbaka take. Suna wannan hirar Fauziyya ta shigo da Radhiya tana nishi
anyi daukan rungumarni mu fadi.

Kafin su shigo kukan Radhiyan ne ya isar da zuwansu. Mairama ta girgiza kai tana
takaicin wannan kukan banza na Radhiya. Tana jaririya babu ruwanta amma yanzu
rigima da kuka ga fada duk ta iya. Idan ta raina girman mutum ya dauketa sai
yakushi tana doke doke duka wataninta tara a lokacin. Zayyan dariya yake yace 'yar
Soja bata daukar raini. Wasu lokutan kuma sunanta na gaskiya yake kira idan yana
jin nishadi. Har ta gane indai taji Alheran tasan babanta ne.

A cinyar Mairama ta ajiyeta ta kalli uwar tasa dariya. Zainab tace "kunji min mara
kunya ko? Mu da take gani kullum yanzu dariyar ma sai mun roka. Dadinta dai har
Awwab bata yiwa"

Homework yake yi a gefe yana jin tsokanar da ake masa ya taso ya kinkimeta yana
cewa "Ummi wallahi tayi nauyi da yawa ki dena bata abinci"

Me zasu yi banda dariya kuwa. " to sarkin wauta, an taba hana mutum abinci saboda
kiba ne?" Cewar Mami

Shi dai bai ga aibun maganarsa ba ya dauketa gashi siriri sai tsayi da yake faman
yi ya tafi dakinsu Zahra. Kayan wasa ya baje mata yana cewa sai tace Ummi da Daddy.
Gajiya tayi da wasan ta soma rigima sai ya dauketa. Duk da haka kukan take masa ya
sabata yana haki "gaskiya kin fiye kuka Alheran dinnan"

Kamar taji me yace kuwa ta kai masa duka a fuska harda yakushi. Zafin da yaji a
gefen idonsa na hagu yasa shi sakinta tim a kasa ta fasa wata gigitacciyar kara.
Zainab da Mami ke rige rigen shiga dakin ya dafe gefen idonsa da yake jini ko ta
kanta bai bi ba a kasan. Zainab tayi saurin daukarta yayin da Mami babu tambayar
ba'asi ta dauke Awwab da mari.

"Me kayi mata take wannan kukan?"

Shima kukan yake sosai Mairama ta taho ta rike shi murya na rawa ya nuna mata wurin
"yakushi na tayi fa"

"Sai kayi mata me?" Mami ta kuma tahowa kamar za ta doke shi.

Da karamar murya ya amsa "Faduwa tayi daga hannuna"

Takaici ne ya kamata kuma wai Mairama tana kare masa. "Bari Daddynku ya dawo sai na
fada masa" ta koma ga Mairama rai a bace "ke kuma kin karbi yarinyar nan kin
rarrasheta ko kuwa"

Mairama tace to yau abin harda ita. Karbarta tayi ba shiri an tabo Mami yau ta
fara shayar da ita amai ya taso mata da gudu tayi bandaki. Abu kamar wasa sai gata
ko tashi da kafafunta ta kasa. Mazajen nasu ba ma sa cikin barrack din an turasu
wani training cikin jeji sai sunyi kwanaki. Dalilin ma da suke tarewa gidan Mamin
kenan.

Abu na taron mata tare su ukun da yaransu suka tafi asibiti. Ciki aka gano a jikin
Mairama har wata uku. Kuka ta saka ganin Radhiya duka duka nawa take. Kuma ga
kunyar ace yarinya bata shekara ba ta sake ciki. Su Zainab kuwa sai murna. Mami
tace mata ya kamata kafin su Zayyan su dawo ta yaye Radhiya saboda cikin yana
wahalar da ita ga tsotso. Da yake akwai kawaici a daren ta tafi ta barwa Mami ita
sai kayanta da ta turo Awwab dasu.

Yadda Mami ke bawa Radhiya kulawa ya kara tabbatar musu da cewa zaman mutumci da
amana ba sai da jini ba. Da ita da yaranta duk sun tare a jikin Radhiya an bar
Mairama da uban laulayi sai Zainab dake sintirin zuwa wurinta.

A kwana na biyar su Zayyan su ka dawo. Sun sha wahala sosai sai dai kuma aiki ne na
sabo. Da murnarsa ya shigo yana kiran 'yar soja Mairama tace masa tana gidan Major
ta tafi yaye.

"Yaye Mairam? Ko shekara bata yi ba"

Hannunsa ta kama suka zauna ta dora kanta a kafadarsa "Sojana bani da lafiya ne"

Ya dago kan ta "na sani kuma asibiti zan kaiki, amma meyasa baki bari na dawo ba
sai yaye?"

Baki ta tura masa "to ba..."

"Me?"

"Ciki" tace tana rufe fuska da tafukan hannayenta

Sungumarta Zayyan yayi yana murna "Mairam kice Tureta ya tureki a karo na biyu"

Salati ta hau yi tana mai jin kunyarsa shi kuwa ko a jikinsa. Dama ta samu sai
sabon amarci don ma laulayin yana hana sakewa. Sai da Radhiya ta cika kwana goma
sannan Mami ta dawo da ita da kaya da tarkacen wasa.

******

Bayan wata guda da yaye Radhiya wata litinin Mairama tana gyaran wake za ta yi
alala da rana Zayyan ya shigo ba lokacin dawowarsa ba. Hannunta ta dauraye ta fito
wurinsa.

"Sojana ya dai yau ka dawo da wuri"

Mikewa yayi akan doguwar kujera yana riko hannunta ta zauna a wurin da ya matsa
mata.

"Me kike dafa mana ne?"

"Alala zanyi"

Hanci ya dage "Uhmm kayan bata ciki"

Hancin nasa ta riko tana dariya "nasan ba ka ci, banyi tsammanin dawowarka yanzu ba
ne. Sai na canja abincin, waken...."

Kofar falon da taji ana bugawa da karfi kuma kamar muryar Zainab yasa bata gama
fadin me tayi niyar fada ba. Da sauri ta bude kofar tayi baya a tsorace ganin
Zainab tana rusa kuka kamar ranta zai fita ga Hadir a bayanta dauke da Ibrahim.

Hanya ta basu su ka wuce cikin falon Zayyan ya hada ido da Hadir yayi murmushin
dole jikinsa a sanyaye yace "ka fada mata ne?"

Zainab kuka take har lokacin Mairama ta rude sai tambayarta take me ya faru. Hadir
take kallo tana jiran bayani daga baya tace "ko dai aure za ka kara?"

"Wallahi dama auren ne Ummin Awwab da ya fiye min da wannan tashin hankalin"

Kanta ya sake shiga duhu "ba dai saki bane ko?"

"Liberia zai tafi"

Dif Mairama tayi sakon yana sauka a kwakwalwarta. Liberian da babu wanda yake cikin
barikin da bai san tashin hankalin da suke ciki ba. Nigeria ta shiga cikin lamarin
tana basu gudunmawar sojoji domin a kwantar da tarzoma. Dibansu akeyi lokaci lokaci
ana turawa. Rawa taji jikinta yana yi ta kasa tsayuwa da kyau sai da Zayyan ya
riketa ya zaunar da ita a kusa dashi.

Cikin tsantsar tashin hankali tace "da kai za'ayi tafiyar?"

Abinda ya dawo dashi gida da wuri kenan ya kasa fada mata. Kai ya gyada kawai ta
kalli yadda Zainab ke kuka itama ta soma hawaye. Duk wata kalmar rarrashi da ban
baki abokan sun lalubo domin kwantarwa matansu da hankali. Zainab ta fi gigicewa
itama tana son Hadir fiye da zato da tsammani. Da kyar ya samu ta tashi su ka koma
gidansu aka bar Zayyan da Mairama.

Ranar bata iya yin girkin ba jikinta yayi mugun sanyi. Abincin Radhiya ma sai shi
yake bata. Ita kwanciya tayi a daki kawai tana zubar da hawaye. Bai ce mata komai
ba sai cikin dare ya kwantar da ita a jikinsa yana rarrashi

"Mairam nayi zaton zaki bani goyon baya sosai har naje na dawo mu koma Kano"

"Yaushe zaku dawo?" Ta tambaye shi murya a dashe.

Tsokanarta ya fara yi don ta sake "tafiyar wata uku ce fa, zan dawo kafin ki haihu
in Allah Ya yarda"

Sake shigewa jikinsa tayi yana jin cikinta da ya fara tasawa ya dora hannu a kai
"Ashe haka ki ke so na ban sani ba?"

Shiru tayi ya cigaba da maganarsa shi kadai "a iya zamana dake Mairam bani da wani
abu da zan fada akanki sai alkhairi. Duk abubuwan da na rasa a baya zuwanki ya
wanke min kuncinsu. Shiyasa nake matukar son ki. Wannan tafiya da ina da yadda
zanyi ko dai na tafi daku ko kuma na hakura ne. Ina rokonki da ki karfafa min gwiwa
naji dadin bautawa kasata."

Wani irin abu take ji yana mata yawo a jikinta. Idan a da tana tunanin tana son
mijinta to a yau sonsa yana neman ranta ne. Gani take kamar bazata iya jurar
rashinsa a tare da ita ko da na kwana daya bane. Ashe baka sanin mahimmancin abun
da ka ke dashi sai yayi nisa da kai. Bata san lokacin da bacci ya dauketa ba sai
ajiyar zuciya da take ta saukewa.

Sai da ya tabbatar tayi bacci ya tashi ya dauro alwala. Yasan yaudarar kansa zaiyi
idan yace zaiyi bacci a wannan daren. Nan da kwana biyar zasu bar kasar, zai bar
iyalinsa wanda basu dogara da kowa ba sai Allah sai kuma shi da nauyinsu yake
wuyansa. Yayi nafila raka'a goma tare da witri sannan ya zauna yana jero addu'o'i.
Motsin Radhiya yaji yayi saurin fita da ita daga dakin don kada ta tashi Mairam
yaje ya hada mata tea a feeder ta shanye. Yana jiran ta koma bacci yarinya ido ya
soye ta fara kiriniya. Bata tafiya sai rarrafe da mikewa. Biye mata yayi suna
wasan. Sai gabanin asuba ta bingire a jikinsa tayi bacci. Kan ta ya rinka shafawa
baiyi zato ba sai hawaye ya ziraro masa ya goge da sauri yana baiwa zuciyarsa
hakurin cewa wata uku a wurin Allah kamar kiftawar ido zasu zo su wuce.

**********

Gidan Hadir ma basuyi bacci ba don Zainab kwana tayi kuka. Mami da sauki tunda ba
zuwan Major na farko wurin rikici ko yaki kenan ba. Sai dai itanma kukan tayi don
ba'a sabo da rabuwa.

Washegari harabar gidajen nasu kaf babu wata hayaniyar kirki. Sojoji ashirin ne
zasu tafi a cikin magidantan da suke wurin. Kowa yana gida tare da iyalinsa.

Bayan la'asar Zayyan ya dauki Mairam su ka je gidansu da gidan kawunansa da Mal
Aminu ya fada musu zaiyi tafiya. Kowa yayi masa addua da fatan alkhairi ban da Jume
da bata dena jin zafin rashin basu kudi ba. Duk da haka ya yi musu kyauta ita da su
Maikudi tunda sunyi aure. Matan ma a ranar sai da ya kai musu ziyara.

Sukuku su Mairam su ka koma babu walwala a tare dasu ita da Zainab. Mami ce tayi
musu fada akan idan sun cigaba da haka a wane yanayi suke so mazajensu su tafi. Sun
ji maganarta don kowacce sai da tayi kokarin gyarawa. Mairam dambun nama ta yiwa
Zayyan gari guda sai da ya dibarwa Hadir da Major. Ta kuma saki jiki tana bashi
kulawa fiye da yadda ta saba.

Sauran kwana biyu su tafi tana goge masa khakinsa Radhiya ta fito daga daki da
kafafunta a hankali saboda rashin kwarin tafiyar. Murna ta kama Zayyan ya sunkuceta
yana sumbatar kumatunta.

" 'Yar soja ta girma, yau yawo zamu je tunda anyi kafa"

Kamar taji me yace ta rinka bangala dariya. Ajiyeta yayi zai chanja kaya su fita
tasa masa kuka "Daaadaa" yaji tace tana dago masa hannuwa.

A nutse ya juyo ya tabbatar shi take kira. Har yanzu hannuwanta take miko masa
"Daaadaa". Ya kalli Mairam ita ma mamakin yarinyar ya kamata. Awwab bashi da aiki
sai koya mata Ummi da Daddy wai dole sai tayi magana. Yau gashi ta kira mahaifinta
dadi yasa yaji idonsa na alamun zafin kwalla. Daukanta yayi ya shiga dakin su ka
bar Mairam tana guga tana diga masa hawaye a kayansa.

Ranar ashirin da daya ga watan Mayu na 1993 ne Giginya Barrack dake cikin garin
Sakkwato ta kwashi sojojinta za'a kaisu Lagos washegari su tashi zuwa Liberia ta
ruwa.
Daren ranar ya kasance dare na soyayya, jaddada alkawura da kuma sabunta matsayi a
zukatan su Zayyan da iyalansu. Daga shi har Mairam babu wanda ya runtsa kuma hakan
take a wurin Hadir da Zainab da Major kansa da Mami.

Komai Mairam ce ta yiwa Zayyan hatta abinci a baki take bashi. Tayi ta daurewa kada
tayi kuka zuciyarta ta kasa daukan wannan lamari. Ko kadan baya son nuna mata
damuwar da yake ciki shiyasa ya fake da yiwa Radhiya wasa.

Jiniya mai sanar da su fito ce tayi kara sai da cikin Mairama ya murda kawai ta
fashe da kuka iya karfinta.

"Zayyan"

Tashi yayi ya rungumeta tsam a jikinsa "ashe kin iya fadin suna na"
"Ka ajiye aikin nan mu koma Nijar ko kiwo ka rinka yi"

Fuskarta ya zagaye a tsakiyar tafukan hannunsa.

"I love you Maryam Ali Gidado. Ki rike wannan a zuciyarki har na dawo. Nayi miki
ajiya a kan mudubi idan na tafi ki duba"

Hade bakinsu yayi tamkar ranar su ka fara haduwa yana jin karar jiniyar a karo na
biyu ya saketa ya dauki Radhiya.

"Ki tayani kula da Umminki da baby kinji mamana."

"Daaadaa" tace tana washe hakoranta biyu dimple dinta ya lotsa ciki sosai.
Ita ma ya sumbaci kuncinta hagu da dama kafin Mairam ta farga ya fice daga
gidan.....ALLAH NA NASA

"Ummin Awwab me yake damunki ne kwanakin nan sai wata rama kike yi kamar wadda za'a
yiwa kishiya"

Dago kai Mairama tayi jiki a sanyaye "Mami ni kaina na rasa gane dalilin wannan
rama. Kuma ke shaida ce ina cin abinci sosai"

"Kinbi kin dashe kinyi fayau. Jiya ina ji baban Radhiya yana fadawa Hadir wai kinki
bari ku je asibiti. Baki ga yadda ya damu ba fa"

Mairama tayi shiru ita kanta ramar da take yi tana damunta. Dadinta ma dai Radhiya
kullum kara habbaka take. Suna wannan hirar Fauziyya ta shigo da Radhiya tana nishi
anyi daukan rungumarni mu fadi.

Kafin su shigo kukan Radhiyan ne ya isar da zuwansu. Mairama ta girgiza kai tana
takaicin wannan kukan banza na Radhiya. Tana jaririya babu ruwanta amma yanzu
rigima da kuka ga fada duk ta iya. Idan ta raina girman mutum ya dauketa sai
yakushi tana doke doke duka wataninta tara a lokacin. Zayyan dariya yake yace 'yar
Soja bata daukar raini. Wasu lokutan kuma sunanta na gaskiya yake kira idan yana
jin nishadi. Har ta gane indai taji Alheran tasan babanta ne.

A cinyar Mairama ta ajiyeta ta kalli uwar tasa dariya. Zainab tace "kunji min mara
kunya ko? Mu da take gani kullum yanzu dariyar ma sai mun roka. Dadinta dai har
Awwab bata yiwa"

Homework yake yi a gefe yana jin tsokanar da ake masa ya taso ya kinkimeta yana
cewa "Ummi wallahi tayi nauyi da yawa ki dena bata abinci"

Me zasu yi banda dariya kuwa. " to sarkin wauta, an taba hana mutum abinci saboda
kiba ne?" Cewar Mami

Shi dai bai ga aibun maganarsa ba ya dauketa gashi siriri sai tsayi da yake faman
yi ya tafi dakinsu Zahra. Kayan wasa ya baje mata yana cewa sai tace Ummi da Daddy.
Gajiya tayi da wasan ta

7 / 99