Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
kamaka duk duniya bana jin kana da wanda zai fito da kai. Nima kaina
tsoronsa nake ji dan jakar uba, daurewa kawai nake ina masa barazana. Amma muje
zuwa sai na dawo dashi tafin hannuna. Uwarsa ma mai suna kamar na tsuntsaye bata
iya karawa dani ba”
**********
Sati uku da dawowarsu a tsukun lokacin iyayen Hadir sun zo daga Kano an daidaita
maganar aurensa da Zainab. Kullum ya dawo ya ishi Zayyan da labarin hirarsu ko
maganar biki. Ranar da ya bishi kuwa yadda ya kula suna son juna musamman Zainab da
duniya bata ganin kowa da gashi sai Hadir sai yaji muguwar kewar Mairama.
Ranar lahadi ya samu da babu training sosai ya fita yaje ya sanar da Mal Aminu da
mutum biyu cikin ‘yan uwan mahaifinsa game da auren da yake nema. Sunyi farinciki
da alkawarin bayan ya koma Kanon ya fadawa mahaifin yarinyar zasu je bayan sati
daya da zuwan nasa. Godiya yayi musu ya nemi matar Mal Aminu mai suna Gwaggo Ladi
matar da ta maye masa gurbin uwa wurin kulawa da bashi abinci da sauran abubuwa
lokacin da kowa ya gane gashin kuman da Jume take yi masa. Kudade ya bata da yake
so a fara siyayyar kayan aure ta yadda idan zasu tafi zasu je ne a shirye saboda
nisa.
[02/11 7:28 AM] My 2nd Mtn: F
Sai da ya nemi izinin fita na kwana biyar, da kyar kuwa bukatarsa ta biya saboda ba
kasafai ake son suna yin nesa da barikin ba. Ranar da zai tafi sai da ya bi ya
sallama da Captain Mustapha. Yanzu alakarsu tamkar wa da kani ga kuma yaransa sun
mayar da Zayyan uba na biyu. Shi Captain Mustapha asalinsa da Katsina ne daga shi
har matarsa don auren gida ma su ka yi.
Asubancin fita yayi ya shiga cikin gari gidajen dangin Mal Muhammadu. Daga can ya
wuce tasha sai Kano.
Yayi sa’a masu kilishi sun fito ya sayawa Malamijo. Shi dai a dan zamansu na farko
bai hango komai a tattare da shi ba sai barkwanci.
Kwanakin da suka gabata Salame ta dami Mairama wai me ya hana Zayyan dawowa saboda
Salisu ya matsa lamba kuma Malamijo ya riga ya bashi. Ganin akwai kudi yaron ya
kara shiga ransa. Salame so take ta tabbatar Zayyan bazai dawo ba sai ta amince
masa ko babu komai zata huta. A haka tana tsoron saurin amincewa ya dawo a bashi
Mairama ita kuma ta rasa. Akwai ranar da ta tambayi Mairaman ko ta fadawa Zayyan
yanayin gidansu.
“Kinsan boye-boyen babu amfani gara yasan wa zai aura kada Malamijo ya nuna masa
hali”
Bata rai Mairama tayi “yau da kanki Adda Salame kike cewa Malamijo zai nuna hali?
Ni dai soyayya bazata sa na kwashe sirrin gidanmu na kaiwa saurayi ba. Idan bai
aureni ba shikenan ya gama sanin komai nawa. Kuma ko yaya Malamijo yake ai babanmu
ne dole mu so a mutunta shi”
Waskewa Salame tayi amma a ranta tana ganin ta sami hanyar rabasu “irin wannan
sharhi ba wani abu nake nufi ba, abar maganr dai”
Yau kamar daga sama sai ga dan aike wai ana sallama da Mairama inji Zayyan.
Wanka take yi lokacin ta gama aikin fura Salame ce taji sakon. Jikinta har bari
yake tsabagen murna ta fada dakinsu da sauri. Kaya ta sauya da sauri ta shafa hoda
harda janbaki ta sako daya daga cikin kayan da Ta Madina ta dinka mata. Komai da
azama take kada Mairama ta fito ta sameta. Tazo fita ta koma ta cire mukullin sif
din kayansu bayan ta kwashe duk wani kayan sawa ta saka a ciki ta jefa a karkashin
sif din ta fita tana dariyar mugunta.
Bata yiwa kowa sallama ba don basa tsakar gidan ta fice zaure. Dama niyarta da an
tambayeta ina zuwa tace wurin Innarta zata je.
Kamshin turare wanda Salisu ya kawo mata zuwansa na karshe ya fara ji kafin ya
ganta. Ta gumbuda turaren sosai kuwa a ransa yaji dadi ba Mairamansa bace take
wannan aika-aikan. Fuska ya saki yana mata murmushi. Ta sunkuyar da kai tana ‘yar
dariya don jin kanta take kamar yau take sallah saboda ganin Zayyan.
“Babban bakonmu barka da sauka, yaya hanya?”
“Lafiya kalau Saude ya mutanen gida”
Wani abu taji ya soki zuciyarta, wato ku sunanta bai rike ba. Bata nuna damuwar a
fuska ba sai ma wani kasha murya da ta tsiri yi “Salame dai ko, baka ma rike sunana
ba saboda baka damu dani ba”
Banbarakwai yaji zancen nata “Afuwan kada ki fadawa Mairama tace ta fasa na yiwa
Addarta ko ince Addarmu laifi”
“Ba wani abu ai, ita ma bata soma fada ba yadda ta matsu tayi auren nan. Allah Ya
dube mu, masu gudunmu saboda Malamijo zasu sha kunya”
Zayyan mutum ne mai saurin dago ina mutum ya dosa idan suna magana, yanzu ma tuni
ya fahimci akwai abinda Salame take son fada masa tun hirar bata tsawaita ba.
“Ban gane masu gudunku saboda Malamijo ba, ba babanku bane?”
Hannu ta dora akan bakinta kamar gaske tana ware idanu “ba dai Mairama bata yi maka
bayani ba? Irin haka ai da wuri ake fada saboda toshe matsala don kada kaji a waje.
Idan na koma zan fada mata gara ta sanar da kai komai da wuri zai fi. Sai ka danyi
hakuri ta gama aikin furar sayarwa ne ta shiga wanka”
Wai shi za ta jawa rai, kawar da kai yayi abinsa yana kallon waje. Haka nan bata yi
masa ba tun haduwarsu ta farko a gidan Gwaggonta da akayi bikin yaranta. Sai tayi
ta wani kifi-kifi da idanu amma sau goma idan zai dago kai sai sun hada ido.
Yanzu da ta ji bashi da niyar tambaya sai ta sake salo. Jan hanci yaji tana yi
alamun tana kuka. Dawo da hankalinsa yayi gareta da sauri.
“Ya dai?”
Goge hawayen da ko digonsu babu tayi sannan ta dan tabe baki duk yana kallonta
“gara kawai na fada maka don abin zai yiwa Mairama nauyi”
Halin Malamijo kaf da yanayin zamantakewar gidansu ta kwashe masa. Hatta dangin
mahaifiyar Mairama sai da ta kwancewa zani. Jinjina kai kawai yake yi yana kara
tausayin Mairama sosai. Yanayin rayuwarta kusan daya da tashi wato dukkansu basa
jindadi a gidan iyayensu.
Salame sai ta dauki sauyin yanayinsa a matsayin tarkonta ne ya fara kamu ta dan
murmusa “nasan rashin dangin uwa lokacin aure a kusa da ciwo…..” ta dan ciji
labbanta “…uhmmm ni kaga dangin Innata suna garin nan kuma bikin da muka hadu ma
nasu ne, Mairama kara kawai aka yi mata”
Yanzu ya gama gane manufar wannan dogon sharhin. Kaurara murya yayi ya hade rai
“Salame!....”
Bai karasa maganar ba sai ga Mairama ta fito da sassarfa sanye da kayan da tayi
aikin furar ta makale a bayan kyaure.
“Adda” ta kira Salame tana kunyar fitowa.
Zayyan ne ya amsa yana mai jindadin ganinta “Mairam yau a nan zamuyi tadin?”
Kai ta sunkuyar ta sake yafito Salame sai kawai tayi gaba abinta ta fice don tasan
me take nema. Kusan minti goma tun bayan fitowarta take ta neman mukullin sif din
bata gani ba. Baki ta saki ganin ta fice bayan tasan kiranta take. Duk sai taji ta
muzanta saboda Zayyan ma ya gani kuma baiyi mamaki ba duk da bai san me take bukata
a wurinta ba.
“Nima in zo bayan kyauren ne?”
“A’a ina zuwa don Allah kaya zan sauya”
Hannu ya daga ya dakatar da ita “dawo abinki nima nan kayan jikina sun sha wahala
da kurar hanya amma na kasa hakuri ko masauki ban nema ba nayo nan”
Jikinta ta kalla musamman zanin taji babu dadi. Zayyan ya matsa mata akan ta fito
ba zai dade ba sai dare zai dawo. Busu-busu haka ta fito kayan jikinta masu saurin
nuna datti ne dama saboda haskensu.
Kanta ta sunkuyar tana kallon kasa ta gaisheshi ya amsa fuskarsa a sake. Lura yayi
a takure take sai ya mika mata ledar kilishin Malamijo yace ta shiga gida sai
anjima zai dawo.
Yana tafiya a hanya amma zuciyarsa ta fada kogin tunanin kalaman Salame da kuma
yanayin da ya ga Mairama. Yana da yakinin Salame ko dai tana son sa ko kuma kawai
bata son cigaban kanwarta ne. Ko ma meye zaiyi kokarin sanin wacece Mairama Ali
kafin ya koma bakin aikinsa.
A cikin gidan kuma Mairama sake komawa tayi neman mukulli har ta hada gumi amma ta
rasa ina ya fada.
Da ta gaji da nema ga rashin sanin ina Salame ta tafi sai kawai ta cire kayan
jikinta taje ta wankesu. Dije ce ta kasa hakuri tace mata me take yi da daurin
kirji ta fada mata bata ga mukulli bane.
“Kin tambayi Salame?”
“Ta fita”
“Taje gidan uban wa?” suka ji Malamijo ya daga murya yana fada.
Tsoro taji da tasan zai shigo gidan a lokacin bazata fada ba.
Tsawa ya sake yi mata “baki da baki ne?”
Da ya ga bata da niyyar amsawa saboda rashin sani da kuma kokarin rufa mata asiri
sai ya mayar da akalar tambayar ga Dije.
Hannuwa ta yarfe “ina dakina ina zan sani, dama tunda yaron nan mai kudi ya fara
zuwa daga birni naga take takenta so take tafi karfin kowa”
“Babu mai fin karfina a gidan nan, idan ta dawo a turo min ita inji da izinin wa ta
fita”
Zai shiga dakinsa Mairama tayi saurin dauko masa kilishin “Malamijo gashi yace na
baka”
Ledar ya karba da sauri yana lekawa. Ganin kilishi yayi gari guda ya soma dariya
“soja yazo kenan Mairama”
Kanta ta kawar gefe tana murmushi ya bantaro mai dan girma kamar tafin hannunsa ya
mika mata
“gashi kema ki taba, ko ya baki?”
Sai da ta karba din tace masa nasa ne kawai. Dije tuni yawu ya tsinke tayi kasake
tana jiran ya bata amma sai ta ga bashi da niyya.
“Bani nawa mana zan fara aikin tuwo ne”
Harararta yayi yana kanne ido “iyayen kwadayi ungo kafin a tara min taragutsan nan
su fara min kallon nama”
Wani dan guntu ya bata ta jefa a baki a kan idon Hajjo. Fitowa tayi itama tana bata
rai “ko a bani ko na gayyato jama’ar gidan nan”
Bashi da zabi haka ya dangwara mata a tafin hannunta. Jefashi tayi duka a baki
sannan ta daga murya tace kowa ya fito Malamijo yana rabon kilishi.
Ai kan kace kwabo sun soma taruwa mutum kadan ne basa nan. Malamijo kamar ya
hadiyi zuciya haka ya rinka yafita musu yana badawa ba da zuciya daya ba.
Ana tsaka da kiran magariba Salame ta shigo gidan. Can wurin Ta Madina da taje
bacin rai kawai ta karo don sosai take fushi da ita har yanzu saboda abinda tayi
mata a Kano. Sallama tayi a dakin Mairama ta amsata ciki-ciki. Tsaki ta doka ta
ajiye gyalenta ta fita yin alwala. Bayan tayi sallah ne Mairama ta tambayeta ko ta
ga mukullin sif din.
“Ajiya kika ban ko me?”
Zuciya ta soma cin Mairama saboda ta tabbatar dazu da gangan Salame ta fita duk da
tasan kiranta take yi. Wai ma me ya kaita wurin Zayyan din.
“Shikenan”
“Shikenan me?”
Maimakon amsar fatar baki sai gani tayi Mairama tasa iyakar karfinta tana jijjiga
kofofin sif din tana neman ballesu. Da saurinta ta mike don ta dakatar da ita.
“Meye hakan?”
“Dame yayi miki kama? Balleta zanyi tunda mukullin ya bata in nemi kayan sawa”
“Saboda saurayinki zai zo?”
Salame tace da kaushin murya.
“Adda Salame idan wani abu nayi miki ki fito fili ki fada min amma ba ki zauna
kullum kina jin haushina kina min tsaki ba. Kin sani wallahi ba don ke Addata bace
….”
“Sai ki dakeni ko ba haka ba”
Wata fuzga ta kaiwa kofar sai gata ta bude ta dauko kayan da zata saka bata sake
kula Salame ba. Gefe ita ma ta koma tana ta hucin kishi ganin yadda Mairama ta zage
tana kwalliya saboda Zayyan.
“Aikin banza ki gama adon yace ya fasa tunda yanzu yasan daga wane irin gida ki ka
fito.”
A tsorace ta waiwayo “fada masa kika yi?”
Salame sai ta tsame kafarta tayi waje. Tana zaune tana jira a raba tuwon gidan na
al’ada a bata nata Mairama ta fito bayan an fada mata dawowar Zayyan. Da tazo
wucewa tana jin uban tsakin da Salame taja har sai da Dije ta soma sababi ko da ita
take.
Hira suka yi cikin nutsuwa rabi duk shi yake maganar saboda kunya irin ta Fulani.
Tana son tambayarsa game da abubuwan da take zargin Salame ta fada masa amma ta
gaza. Kamar ya sani kuwa da kansa ya shiga bata labarin asalinsa da rayuwarsa ta
baya zuwa yanzu. Tausayinsa taji har idanunta su ka ciko da kwalla.
“Bana so yanayin rayuwar gidanku ya sanya ki fara tunanin zan gujeki ko hakan zai
shafi zamantakewarmu. Gidajen da muka fito daban, sannan gidan da zamu samarwa
kanmu da ‘ya’yan da nake burin ki haifa min shima daban.”
Tamkar kasa ta zage ta hadiyeta taji saboda kunyar kalaminsa na karshe. Da dabara
ya samu ya rinka kwantar mata da hankali da kwadaita mata irin tanadin da yake mata
idan ta zama mallakinsa. Ba shi ya bar gidan ba sai tara da rabi na dare. Washegari
ya sake zuwa kuma a ranar ne ya sanar da Malamijo zuwan kawunnansa idan ya koma.
“Abin da nake so da kai shine ka fada musu su taho da sadakinsu ayi komai a kare.
Yaran nan sun zaunu babu dalilin ayi ta jan lokaci. Budurwa kamar Mairama ta bawa
shekaru shatakwas baya harda watanni ina kallonta tana kallona. Ga yayarta ita ma
zan fadawa yaron nan Salisu sai ayi a lokaci guda”
Dadi maganar ta Malamijo tayi masa yayi na’am da ita. Ana gobe zai koma yana jiran
fitowar Mairama sai ga Salame da ta shiga tashin hankali sakamakon gabatowar
aurenta da Salisun da bata so. Hanyar waje tayi a daidai inda yake zaune ta jefa
masa takarda ta fita. Ba nisa tayi ba tana layin bayan gidansu tana jiran ya
karanta wasikar yazo ya sameta.
Layuka kadan ya karanta inda take sanar dashi son da take masa da kuma jiransa da
take a bayan layi idan ya amince yazo ya sameta. Mairama ce tayi sallama sai kawai
ya yayyaga takardar ya dunkuleta a hannunsa.
Sun jima suna hira yana fada mata haduwarsu ta gaba ta zama tasa tana dariya a
hankali Salame ta dawo kamar kububuwa. Ta kwashi awa guda da doriya tana jiransa
bai zo ba. Yanzu da ta shigo takardar hannunsa ya watsa a iska ko kallonta baiyi
ba. Zuciyarta kamar za ta fashe saboda bakinciki ta wuce ciki.
Bahaushe ma yasan babu wanda ya isa ya sauya kudurar Ubangiji ga bayinSa shiyasa mu
kan ce wai tun ran gini….Bayan duka wasu shirye shirye da hassada daga bangaren
‘yan bakinciki irin su Jume da ‘ya’yanta da kuma Salame mai son maso wani, da
azahar din wata asabar aka daura auren Zayyan Muhammad Tureta da Mairama Ali
Gidado. Sai kuma Salisu Lawan da Ummusalma Ali Gidado. Kowacce cikinsu angonta yayi
bajinta gwargwadon aljihunsa ya yi mata kayan lefe. Ko ba’a fada ba kayan Salame
sun kere na Mairamu duk da Zayyan din ma baiyi kasa a gwiwa ba, amma a haka Salame
ta dauko ido ta sakawa kayan Mairama a ganinta da ita su ka fi dacewa.
[02/11 7:28 AM] My 2nd Mtn: H
**********
“Kasan Allah Malamijo idan naje Sakkwato haka zikau Allah shi tsinan”
Fuskarsa a murtuke kamar zai kai mata duka ya tashi daga kwanciyar da yayi “ wai ni
dake waye ya haifi yarinyar nan ne eyyee?”
Yadikko ta galla masa harara “kaine ubanta wanda na sani da ana sakewa wallahi bana
jin ko tsinken ashanar gidan nan zai so a alakanta shi da kai. Me kake yiwa yaran
bayan haihuwarsu? Nan haka muka kaita gidan miji abin kunya babu wani kayan arziki
wai kuma ‘yarka ce, kai da garin nan kowa ya shaida arziki gareka”
“Sa ido, sa ido…kowa zaiyi ya bari tunda ba da uban mutum muke kiwon ba”
“Ba sai ka zageni ba, gaskiya ce dai dole na fada maka. Mairama baka fitar da ita
kunya da biki ba dole kayi bajinta ita ta fara kawo maka jika a gidan nan. Ka kuma
hada da gara tunda ba’ayi musu komai ba da bikin. Salame ba don mahaifiyarta tana
kusa ba itama da haka za ta tare ba garar”
Malamijo ya mike yana kada hannuwa yana kumfar baka saboda an bukaci kudi “garo ba
gara ba, idan sai na bada kudi kunyi mata gara zaku je don Allah kuyi zamanku na
yafe. Yo dangin uwarta ma suka bace bat a doron kasa basa waiwayarta tunda ta rasu
balle ku”
“Laifin waye to idan bana ka ba? Kowace mace ka gani kana so saboda zalama. Kuma ba
dole su bace ba. Kayi auren biyan bashi tana haihuwa kace ka saketa kuma sai sun
biya rabin kudin. Tsoro yasa sun gudu bakinciki kuma ya kashe yarinya karama ta bar
marainiya”
Yadikko kin hakura tayi sai da kyar da sudin goshi Malamijo ya bata dubu uku da
kuma tinkiya guda daya “gashi nan a tafi a kaiwa ‘yar kunama kafin na fara ganinki
cikin bacci na. Ke dai da mayya ce da tuni na dade a tukunya”
Warce kudin tayi a hannunsa “fadi ka kara, aradu da ina maita da tuni an dade da
raba gadon ka”
Hanjin cikin Malamijo ne ya kada da gaske furucinta ya bashi tsoro. Ko dai mayyar
ce ne? shiyasa kullum baya gaba sai dai baya kamar kudin guzuri.
**********
Kwance take akan doguwar kujera a falonta lokaci lokaci ta dago kai ta tsartar da
miyau a duk inda ta ga dama tana faman yatsina fuska. Salisu ne ya shigo da langa
cike da gurasa da tsire irin wanda take so.
“Salame tashi kici abincin”
Kallonsa tayi ta watsar tana kokarin zubar da wani yawun ya taho da sauri ya mika
mata kurtun da ya ciko da kasa “zuba a nan kinji don Allah Salame na” yace da
rarrashi.
Kamar bazata zuba ba sai kuma ta tofa ya mayar ya ajiye jiki na rawa ya miko mata
langar ta amshe ta soma ci don yunwa take ji dama. Ta dauko yanka na biyu ya saki
fuska yana dariya “yau da albishir na dawo, me zaki bani tukwici?”
“Rike kayanka indai sai na bada wani abu zaka fada”
Baiyi fushi ba don ya saba da halinta. Bata boye masa kiyayya har yanzu da take
dauke da ciki na wata biyu. Tsiyarta take tsulawa a gidan tana cin karenta babu
babbaka kawai don tasan Salisu yana masifar son ta.
“Mairama ta sauka yau kwana hudu an sami mace”
Naman da take shirin hadiya ne ya makale mata a makoshi ta soma tari. Ruwa ya bata
ko kalla bata yi ba bare ta karba.
“Me kace?”
“Mairama….”
“Dakata malam, wannan har wani labarin fada ne?”
Mamaki ya kama shi “ke, Mairama kanwarki nake nufi”
Zuciyarta ce take tafasa da bakin kishi. Yanzu Mairama har ciki Zayyan yayi mata ta
haihu. Saboda shi tafi wata uku Salisu bai sami kanta ba sai da ya hada da fin
karfi. Rigima sosai suka kwasa kamar auren bariki tana ta yi masa Allah Ya isa.
Ganin babu sarki sai Allah daga baya ta hakura ba don tana son sa din ba sai don
kawai ba ta hango mafita daga kaddararren aurensa ba. Da ciki ya bullo kamar ta
zare don bata kaunar komai tsakaninsu lokacin da za ta kasha auren ta nemi hanyar
shiga gidan Zayyan. Indai soyayya