Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
Rabonta da kuka tun farkon zuwan su Mami rugarsu da ana
bada labarin abinda kawunsu Maikudi yayi.
Kuka tayi harda shessheka Awwab bai hanata ba har ta gama don kanta ya bata tissue
irin ya ledar nan karama ta goge idanunta.
"Feeling better?"
Ta gyada kai tana kallon kwanukan gabanta.
"Good, yanzu ki fada min tsakani da Allah me ya same ki? Nine ko?"
Rasa me za ta ce masa tayi ta kare da cewa "ba kaine kake murna zaka tafi ba"
"Ke kuma ba kya so na tafi?"
Kada fa ya fassarata ta soma tunani "dena fada kada budurwarka taji. Duk baka
tambayeni labarin komai nawa ba zaka koma kila bazan kuma ganinka ba sai an dade.
Shine naji raina ya baci"
"Sai nake ji kamar dai maganata ta dazu ce ta baki haushi. Amma nima bana son
tafiyar ko sabawa bamu gama yi ba ko" yayi yar dariya.
"Eh, ko askina ban fada maka me yasa akayi min ba"
Sai da yayi dariya sosai yace "an gaya miki ni bana tsoron kiyi min balotellin ne?
Ina sane naki tambaya kada na janyowa kaina"
"Ashe kai matsoraci ne" ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ta gama kuka ba.
Sweet ya dauko daga aljihunsa irin mai mint dinnan ya bare ya jefa a baki yana
dariyar matsoracin da ta kira shi.
"Dazu ka raba abin leda baka bani ba yanzu ma a gabana ka shanye alawar? Kuma nice
karama ni ya kamata ka bawa"
"Sorry gashi in kina so" ya cirota daga bakinsa dama niyyarsa kenan.
Wata zuciyar tana kwabarta wata tana ingizata har ta mika hannu tayi saurin janyewa
"wayo zaka yi min, na tuna me kace dazu"
"Ke dai kina kyankyamin abin bakina kawai"
"Haba dai..." bata rufe bakin ba ya saka mata sauran da ya rage har hannunsa yana
taba lebenta. Saurin tashi tsaye yayi ita kuwa ta rasa me zata yi ma.
"Ki rage min kinga kadan na sha"
Lumshe ido tayi tana tsotsar alawar yana kallon yadda bakinta yake motsawa yana jin
kamar ya taya shi. Girgiza kai yayi da sauri. Lafiyata kalau kuwa ya tambayi kansa.
"Ahhhh" Radhiya tace ta bude bakin ta mike tsaye yadda zai gano cikin bakin nata
sosai. Ta shanye alawar saura yar kadan.
"Cewa nayi ki rage min fa"
"Nima bata isheni ba. Babu kari?"
"Zan gamu dake ne, muje ciki su fito bana jin zamu iya wucewa a yau sai dai mu
kwana a Kano" tafiya ciki ya soma yi.
"Hamma gashi" ya juyo ta miko masa yar karamar sweet din ya karba yana kallon cikin
kwayar idonunta ya saka a bakinsa. Bata sani ba ko shima yaji amma ita dai wani abu
ne ya zarga mata har kasan zuciyarta.
[11/2, 6:42 AM🏽
M🏽 : 28. 💕
Basu dade da fita ba Daddy ya kira Mami yana tambayarta hanya da mai jiki, su ma
shigarsu Sakkwato kenan. Ya bukaci gaisawa da Malamijo wanda hakan ba karamin dadi
yayi masa ba. Da Mami ta sake karba ne yake bata shawarar me zai hana su kwana
washegari su kama hanya da wuri. Banda dare da ya tabbatar sai sunyi a hanya yana
ganin ko babu komai itama Mairama sun mutunta ta. Zata ji dadi su kwana yadda itama
taje nasu gidajen ta kwana. Mami dama harda tsoron dora musu nauyi da take yi yace
duka babu komai kwana daya dai ta sanar da Ummin Awwab yasan zata yi farinciki.
"Ummi yanzu Daddy yake cewa gara mu kwana saboda dare"
Murmushi Mairama tayi da ya nuna jindadinta kamar yadda Major yayi hasashe. Baza a
rasa dakunan da za'a sauke su ba. Abinci kuwa bata da matsala tunda da 'yan
kudadenta. Zata bayar ne a siyo abinda zata fita kunyarsu.
"Wannan murmushi Ummi to me yasa baki fada min kina so mu kwana ba? Duk daya muke
fa"
"Nasan kinyi haka ne don kada ki dora min nauyi. Amma zanfi so ku kwana ko daya ne
a gidan da bani da tamkarsa"
Yadikko da Hajjo ta sanarwa Malamijo na ji yasa aka taso kannenta ya bada umarnin a
gyara dakuna biyu daya domin mazan dayan kuma na 'yan mata. Ita Hajjo tunda ita ke
da girki 'yarta zata gyarawa Mairama da Mami nata dakin. Baki masu alheri irin
wannan karramasu ya zama wajibi a wurin Malamijo ko don ya kara samun wani ihsanin
kafin su tafi.
"Karami jeka ka fadawa yayanku ya nutsu yaci abincin tunda babu tafiyar"
**********
Kallon kallo suke yi daga bayan Awwab da ya juyawa kofa suka ji ana gyaran murya.
Ba kowa bane illa Emzee wanda ya gama ganin musayar sweet. Shi ba abin ya juya ko
yace bai gani ba. Murmushi ne ya subuce masa da suka hada ido da Awwab.
"Dama Mami tace na fada maka yanzu Daddy ya kira yace ku hakura da bin hanya yamma
tayi"
"Bari naje na sameta, ko Kano muka koma mun rage wani abin"
Tafiya yayi Radhiya ta tsaya dauko kwanukan da tabarma. Emzee ya karbi tray din
tana nade tabarmar yace "Allah Sarki bawan Allah"
"Wa?"
"Dr Kawu Zakari mana"
Gabadaya daburcewa tayi "me...me..ya same shi?"
Dariyar da bai fiye yi ba ya yi mata ganin duk ta rude irin na marasa gaskiya "babu
komai na tuna irin son da kike yi masa ne a raina nace dan gata. Idan ku ka yi aure
alawa zaki rinka bashi"
Borin kunya ya kamata ta fara fadan da babu gaira babu dalili. Dariya ta sake bawa
Emzee ya sakalo hannunsa a wuyanta "kinga dai bance komai ba, idan kika tona kanki
ba ruwana"
Baki ta bude tana harararsa, wai me yake nufi ne.
Aljihunsa ya rinka lalubawa ya zazzagesu yana cewa "rufe bakin mai alawar ya shiga
ciki ni kuma ko kuli babu a jikina"
"Kwana biyu jikinka bai karbi sako ba shiyasa kake damuna" tace tana daga hannu za
ta kai masa duka ya gudu tana jiyo dariyarsa.
Har yanzu babu wanda ya tashi daga tsakar gidan. Awwab ta nemo da ido ya dan
durkusa a gaban Mami yana rokonta ko Kano ne su tafi. Mairama tana jinsa tace wato
bazai iya kwanan kauye ba.
"Ba haka bane Ummi, bana so ki bawa kanki wahala ne kawai"
"Wace wahala ga kannenka ko ta ina, yanzu Karami zai gyara muku dakin da zaku
kwana. Yau kowa zai dana kauyenmu"
"Ko don kada kice ina gudun kauye dole na kwana."
Matsawa yayi gefen Malamijo da yake ta bawa Zayyana da Ibrahim labaran kiriniyar
Radhiya. Awwab yaso su tafi da gaske. Ya rasa gane kansa da zuciyarsa akan kanwar
tasa. Zuciyarsa ta gaza nutsuwa balle ya fahimci me yake damunsa. Har yanzu
dandanon sweet din da ta bashi yake ji a bakinsa na daban da lokacin da ya fara
sha. Shi kadai yake murmushi yana satar kallonta tana wurin wanke-wanke tana magana
da karamar Antinta cikin amaren da za'ayi bikinsu su hudu. Hajjo ta yiwa Mami da
'yan matan tayin ganin lefen kannen Mairama. A lokacin Mairama tace tunda bikin
haka yake kurkusa gaskiya ta fasa komawa Rugar Barkindo. Zata jira ayi bikin a gama
nan da kwanaki sha biyu sai su wuce Katsina kuma. Idan an gama biki kaf su tattara
su tafi. Tasan Innawuro da matan Baffaninta ma zasu zo idan an aika musu. Dakin
Hajjo suka tafi su duka kafin a gama gyara inda zasu kwana. Radhiya ta biyo bayansu
zata shiga kenan Malamijo ya kwalawa Emzee da ya zage abinsa yana shara kira yana
hura hanci shi mai arziki.
"Zayyanu yaka zo, bar wannan aikin zan sa a karasa. Ka raka wannan samarin gonata
su gani"
Da baya da baya Radhiya ta dawo "ai wallahi tunda naji muma sai munje. Bari naje na
kira su Adda Zahra"
"Ban gayyaceki ba fitinanniya, idan sai kinje ne na fasa kowa ya shiga daki ya
kwanta dama kun kwaso gajiya"
"Ni din? Ashe yau rabon kosashiyar saniya za ta kasa ne"
"Buhun ubaki mai idanu a tsakar ka, Qur'anin Allah kika yi min barna a gona sai an
biyani" yunkurin tashi yake don ya riga yasan hali. Muddin tace zata yi to da
wahala idan basu dawo gida da nama ba. Shi yadda yake tsoronta ma yana tsammanin da
kanta zata iya yiwa shanunsa rauni kawai don a yanka.
Awwab da Ibrahim sai dariya suke yadda ta dage sai taje Malamijo ma ya dage.
"Malamijo da dai ka kyaleta tunda kasan ko ka hana sai taje" Emzee yace da sigar
laluma.
Malamijo ya tamke fuska yana kallon Awwab "yaro ga amana, idan kuka je ko kaza ce
ta sami matsala sai kun biyani."
"An gama Malamijo" Awwab yace yana murmushi. Tsohon burge shi yake kamar yadda
Zayyan Tureta yaji farkon haduwarsu.
"Ni nafi zargin ita wannan ce ya kamata ta fito a namijin shi kuma salihin nan ya
fito a mace sai aka sami mushkila. Yasin duk mai auren 'Yar soja sai yayi shiri da
gaske"
Murmushin Emzee ya fadada ya saci kallon Awwab da duk motsin Radhiya sai ya kalleta
a ransa fata kawai yake ya ga ranar da za'a ce sunyi aure.
"Kirawo su idan basu gaji ba" Malamijo yace yana binta da harara. Fatansa Allah
Yasa suje su dawo lafiya kada yaji labarin da zuciyarsa bazata iya dauka ba.
Da murnarta taje ta fada musu zasu je gonar Malamijo ganin dabbabinsa. Ghazalatu
tana kashingide akan gadon Hajjo tace ita babu inda zata je. Gabadaya ranta ya gama
baci da kwanan garin nan. Kana ganin gidan duk girmansa kasan gidan talakawa ne sai
wani so ake a burge su. Tana ji lokacin da Yadikko ta tunawa Malamijo kajin da ya
bayar ya hadiyi yawu don yayi zaton kajinsa sun sha kafin a sake shawarar kwana. Ba
don yaso ba yace a dauka ayi miyar tuwon dare dasu.
Zayyana da Fauziyya tuni suka tashi aka gyara fuska suna murna zasu je. Zahra ma
tace bazata iya zuwa ba kan ta ya soma ciwo. Ita dama bata da juriyar tafiyar mota
daga amai sai ciwon kai.
Zasu fita Mairama ta dakatar da Radhiya "don Allah kada kije ki yiwa Malamijo barna
kinji ko, kuma ana magariba ku dawo"
Dariyar shakiyanci tayi tana kissima me zata yi don babu yadda za'ayi taje ta fito
sikau basu ci nama ba. Jama'ar gidan dashi kansa mara lafiyan da amarensa da ta
gani kowa yana bukatar protein.
"Haka fa ya cewa Hamma wai ga amanata kada na taba komai. Ni yanzu Ummi da girmana
me zanje in taba a gonar nan?"
Da yake Mami ta san waye Malamijo yanzu tun bayan labarin gidan da Mairama ta basu
ga kuma sanin da ta yiwa 'yar tata sai ta rinka dariya ita ma. Ghazalatu na jin
Radhiya tace Hamma ta diro daga kan gadon tana cewa ita ma zata bisu.
Radhiya ta tabe baki bata manta me tayi mata ba dazu "ba yanzu kika ce bazaki ba?"
"Iska nake son sha" tace fuska ba annuri. Indai Awwab zaije kuma Radhiya ma zata
dole ne ta bisu. Bata son wannan likewar da take yi masa daga gani irin abin nan ne
na 'yan kauye an ga dan birni ana so a cusa kai ko Allah zaisa yace yana so.
Emzee yace gonar a bayan gari take da 'yar tafiya shiyasa Awwab yace gara su je a
mota tunda yamma tayi. Da sauri sauri Ghazalatu ta riga kowa fitowa. Awwab na bude
mazaunin dreba lock din ko ina ya bude ta kama kofar gaban mota ta bude ta shige
kamar wadda take tsere da wani. Burinta ta riga Radhiya shiga. Awwab na zaunawa ta
kalle shi tana murmushi ya daure ya mayar mata. Ji yayi yafi son Alheran dinsa ta
zauna ko da irin zaman dazu ne ta juya masa baya.
Duk abinda Ghazalatu tayi na saurin zama a gaban Radhiya ta gani. To dama ita dinma
yanzu bata ra'ayin gaban. Bata son zama kusa da Awwab din saboda yadda yake sawa
tajita kamar ba ita ba.
Kusa da Zayyana ta zauna a tsakiya tana ta zuba surutu. Awwab ya kasa hakuri ya
gyara madubin motar yadda zai rinka ganinta da kyau. Yana saita madubin suna hada
ido da Emzee. Hade girar sama da kasa yayi da Emzee ya dago masa hannu yana
murmushin tsokana. Kansa ya janye gefe Awwab ya hango Radhiya tana nunawa Zayyana
makarantar da tayi primary.
"Ranar hutun da muka gama primary 5 muka yi dambe da Danmama a wurin bishiyar can,
ko me yake yi yanzu oho"
"Damben fada kika yi dashi?" Zayyana tace da mamaki.
"Ke baki ji wulakancin da yayi min bane. Malamijo suke zagi ni kuwa na nuna musu
matsayinsu."
"Zan so sake ganin Danmama, yanzu sai dai muyi gaisuwar mutumci idan an hadu"
Wani azababben kishi ne ya turnuke Awwab "duk yawan 'yan uwanki basu ishe ki ba sai
kin hada da abokin fadanki? Wai shin ke namiji ce ne ma kike fada da maza?"
Ita me tace da zai rinka yi mata fada daga labari. Kallonta yayi ta madubin ta
murtuke fuska "kuma idan na zama soja ....."
"Stop dreaming babu inda zaki. Idan bazaki yi karatu irin na kowa ba sai ki hakura"
A duniya ita tana da burin da ya wuce zama soja ne? Duk mai son hanata bai nemi
zaman lafiya ba. Ko da kuwa Hamma Awwab din da take ji dashi ne. A take ta bata rai
"ai dai Daddy yace zai nema min"
"To zamu gani" yace yana shiga kwanar da Emzee ya nuna masa.
Fauziyya tace "Hamma ka barta tayi kawai mu sami soja mace. Ni har hangota nake yi.
Kasan Radhiya bata daukar raini kowa zai shiga hankalinsa"
"Idan kin haifi taki 'yar sai ki turata amma wannan dai na gama magana"
"Kai Hamma kada fa mu ganku a rana wannan kanwar taka bata iya fada ba. Sai ku
kwana kuna yi"
Bai ce komai ba yayi parking a gefen gonar. Tun daga inda suke suna iya hango shanu
da tumaki. Malamijo fa akwai kudi arziki ne kawai babu don bashi da zuciyar fitar
da kudinsa a mora. Kowa ya fita saura Ghazalatu da Awwab a motar. Gani yayi bata da
niyar fita ya koma ya zauna yana tambayarta me taki fita.
"Yayana kaki zama muyi hira, nayi maka wani abu ne?" Ta marairaice masa.
Tausayinta yaji domin daga baro Abuja zuwa Katsina, Kano da Sumaila duka tayi
dominsa ne.
"Kiyi hakuri, kinga ban samu na zauna bane"
"Amma ka sami lokacin hira da kanwarka ko?" Tace cikin yanayin da ke nuna tsantsar
kishi.
"Me yasa Alheran ta tsaya miki a rai ne?"
"Shakuwar taku tayi yawa Yayana, bana son abin ya koma wanda bazai mana dadi ba a
gaba"
"Idan zakiyi min adalci Ghazalatu kin sani cewa duk wanda yasanni da su Mami to
dole ya taba jin zancen Daddyn Alheran, Umminta da ita kanta ko da sau daya ne.
Family dinsu suna da matukar daraja a idanun iyayena" tunawa yayi da zancen rasuwar
Zayyan da Daddy yayi masa a daren da zai taho Kano da nanata masa ko bayan ransa ya
taya shi rikon amanar iyalinsa. A daren sai da ya zubar da hawaye. Yayi zaton idan
ya ga Radhiya kawai shakuwarsu ta baya zai tuna kila ya ga ma ta sauya daga sanin
da yayi mata. Sai ya zamana abin ba haka yake ba. Ganin kwana daya Alheran nema
take ta shige kowane bangare na jikinsa.
"Tunanin me kake yi ne?"
"Fito muje ba dadewa zamuyi ba" yace yana fita.
Dole tabi bayansa a ran ta tana jin dole ne ma suna komawa ya sanar da nasa iyayen
idan ma kudin aure ko saka rana za'ayi duka ayi da wuri kafin abin yazo yafi
karfinta.
Yawo su Radhiya ke yi sosai ga masu kiwon dabbobin suna ta bin bayansu ana musu
karin bayani. Wurin wata saniya suka je ana tatsar nono. Mutumin da yake tare dasu
yace ta haihu ne wani sa ya tunkuye dan makarakin bai shura ba.
"Ina son yin tatsar nima" Zayyana tace da Radhiya wadda lokaci lokaci sai ta waiga
baya ta gani ko su Awwab sun fito. Haushi ne ma ya kamata saboda yace bazata yi
soja ba a gaban mutane ta yi gaba cikin takaici tana jin zuciyarta tana nauyi.
"Muje na koya miki" Emzee yace da Zayyana bayan ya gama karantar yayarsa.
Irin hular kaba da suke sawa su kare rana mai fadin kasa Radhiya ta gani wani
cikinsu ya cire ta dauka ta kwama a kanta ta sami kasan bishiya ta zauna akan wani
dutse tana kallon su Fauziyya harda Ibrahim kowa tatsar nono yake yi. Idan wannan
ya gwada sai ya matsa wani yayi.
Awwab da Ghazalatu ta gani suna tahowa taji wani abu na taso mata daga kirji har
wuya. Rufe idanu tayi ta ja hular ta dora akan fuskarta. Duk abinda take yi Awwab
na kallonta har ya karaso inda take. So take ta bude fuskar saboda wani sihirtaccen
hamami da yake tashi a ciki amma bata san ta ina Awwab ko Gayanatunsa zasu bullo
mata ba. Babu wanda take son gani cikinsu. Wari ne ya isheta ba arziki ta cire
hular tayi jifa da ita sai a cinyar Awwab da zamansa kenan.
"Wai Allah, wannan shi ake kira gumama inji takari. Wannan uban wari....."
Kasa karasawa tayi tana kallonsa da hular a cinyarsa tsabar mugunta ta rinka
dariya. Shi da budurwarsa suka janyo mata saka hular ai.
"Kina da matsala, kin gama bata rai kin zo kina dariya" yace yana kara rungume
hular
"Na ga ka kama hula ka rungume ne kamar ta ka"
Miko mata yayi ta goce da sauri kada ta sake tabawa "nagode, ungo abinki tunda taki
ce"
"Warin maza take wallahi" ta kwashe da dariya da ta ga ya tashi da sauri hular ta
fadi kasa.
Yamutsa fuska yayi yana kallon yadda take jindadi hankali kwance "wannan wace irin
kalma ce haka ko dadin ji babu?"
Idanunta da ya yarda suna dauke masa hankali ta watsa masa "wace kalmar? au wai
warin maza. Kada kace min baka ji ba. Dauko ka sansana"
Dukawa tayi zata dauko yasa kafa yayi ball da hular yana kada kai yana kai
hannuwansa wurin hancinsa ya kawar da kansa da sauri "dirty girl wannan kika dora a
fuskarki"
"Rashin sani, nasan yanzu fuskata wari take yi ko"
"Ban sani ba" yace yana yin gaba. Daya daga cikin mutanen ya tambaya ina zai sami
ruwa yace sai dai a rijiyar da suke debowa dabbobin. Ina wani bambanci da hular da
ruwan da ya tabbatar shima bashi da tsafta. Emzee ya kira ya fada masa ruwa yake so
da sabulu.
Kallon rashin fahimta yayi masa "wanka zaka yi a nan?"
Awwab ji yayi kamar ya hada shi da Radhiya ya musu duka. Ghazalatu da sauran duka
kallonsa suke yi.
"Abu na taba zan wanke hannuna shikenan!"
Kamar yadda ya zata su uku suka tafi siyo ruwan da Ibrahim da Zayyana. Awwab ya
koma wurin da Radhiya take zaune Ghazalatu za ta bishi Fauziyya ta sako mata zancen
bikin da shirye shiryen da zasu yi. Tayi haka ne don tafi son yayansu da Radhiya su
fara soyayya taji dadi fesawa Mami. Bata san su ma burinsu ba kenan ga kuma rashin
sanin tsakaninsa da Ghazalatu.
Kin yi mata magana yayi ita kuwa ta ga lagonsa ta biyo shi ta zauna a kusa dashi a
kan katuwar jijiyar bishiyar da ta fito.
"Ko ba komai na rama"
"A'a kin dai yi kazanta kinji dadi. Me nayi miki ma da zaki rama?"
Tura baki tayi cikin shagwabar da ta koyi yi masa "Cewa kayi fa bazanyi soja ba"
Sai da ya fuskanceta sosai yace "haka kawai kamar courses