Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
babu nisa fa" yace kawai ya taka ya riski Halifa. Awwab ya ja
motar tare da kamo hannun Radhiya ya rike gam. Ba magana suke yi ba sai dai kallon
da suke yiwa juna kawai mai cike da shauki. Rahima bata kula da abinda yake faruwa
a gaban ba saboda tashin hankalin da take ciki. Me ya sami Emzee kamar bai san ta
ba.
Suna zuwa gidan ta sauka daga motar ta shige ciki. Awwab ya dago hannu ya shafa
fuskar Radhiya ta lumshe idanu. Jinginar da ita ya yi kokarin yi yana cewa "bayanki
bazai sage ba kin zauna kinyi gaba Schatzi"
Da sauri ta dago jin zai hada bayanta da kujerar tare da yin kara cikin wani irin
sautin wahala "aashhh Chèri da zafi"
Gabadaya Awwab ya rude "mu gani" yace yana shirin kwanto da ita jikinsa ta matsa
da sauri tana rufe idanu.
"Silly girl" ya ja hancinta "ashe ciwon ba na gaske bane tunda bai hanaki jin kunya
ba"
Kyabe fuska tayi kamar me shirin kuka "Hammana ina kayan dubiya?"
"Bayan kin fada min kika yi sai a wurin Mami naji."
"To kuma sai ka taho hannu na dukan cinya"
Kai ya girgiza yana dariya "wata maganar idan kika yi sai ta tuna min wata yarinya
da na hadu da ita shekara uku da suka wuce a falon Mama mai kwalkwalin kai"
Shan kunu tayi tana kumbure kumbure "sai na fadawa Daada kana tsokanata"
Dariya yake mata ta cukule fuska "baki san yadda hoton kan yarinyar ya zauna min
bane a kaina"
"Kaga bana so"
"Idan baki so a bani janbaki na shanye ki gani idan zan sake tsokanarki" ya kare da
lumshe idanu yana budesu a kanta.
Kunya duk ta kamata shi kuwa kamar ya cusata a zuciyarsa kawai yake ji saboda yadda
komai nata yake burge shi. Hira suke yi a nutse yana ta tsokanarta daga baya ya
kare da bata shawarar a matsayinta na babba kada ta bari ko kadan su Rahima su ga
wani chanji daga garesu. A irin wannan lokacin ne mutum yake kwasar lada domin ya
rama sharri da alkhairi. Sosai take jindadin shawarar tasa kafin daga baya su
gangara kan shirin dinner din da za ta daki Abuja nan da kwanaki.
Halifa da Emzee basu dade ba suka isa gidan inda suka shiga dakin da iyayen nasu da
kakanni suke. Emzee yana kallon Umminsa ya hango Rahima a jikinta Ummin kamar tayi
kuka tana kallon fuskarta.
"Ni dai ko asibiti zan kaita ne a Kano wannan idon yayi kwanciyar jini" tace tana
juya fuskar Rahiman yadda su Innawuro zasu gani.
Kirjin Emzee yayi wata irin dokawa saboda yadda fuskar Rahimansa ta
koma...Rahimansu dai ya gyarawa kansa da sauri tare da saurin barin wurin. Yana
tafe fuskar tana masa yawo a ka cike da tashin hankali. Ba zato yaji ance "Karami"
Juyawa yayi yana kallon Salame tayi wani iri. Fuskar Rahima ya tuna yaji ransa ya
baci amma albarkacin Ummi sai ya gaisheta. Kasa boye mamakinta tayi saboda tasan
bata kyauta musu ba amma yaran suna da ladabi duk da fitinarsu da ake gani musamman
Radhiya.
"Uhmmm dama...nace...dama...uhmm"
"In tafi ne?"
"Cewa nayi ko za ka kira min su Radhiya da Halifa"
"Radhiya ko Rahima?"
"Radhiyan dai" kunyar ganin Rahima take ji sosai kuwa.
Wayarta ya kira sannan ya tafi kiran Halifa wanda tun a hanya yake bashi hakuri
yace kada ya damu magana ta gama wucewa.
Radhiya da Halifa sunje sun sameta sai ta rasa abin fada sai da Halifa yace zai
tafi ta iya hada kalmar hakuri ta baiwa Radhiya. Murmushi kawai tayi tace babu
komai saboda yadda bata sakewa a gabanta. Bayan tafiyarta ne ta dan sassauta murya
tace da Halifa
"Me kanwarka take cewa game dani?"
"Me zata ce kuwa Umma banda kuka"
Shiru tayi na rashin sanin abin yi kafin daga baya tace "wai fuskarta ta kumbura?"
Shi gabadaya ya kosa da tsayuwar ma "bari na kirawo miki ita ki gani"
"Dawo Halifa" tace tana yafito shi da hannu bai tsaya ba sai da yaje kofar dakin da
suke.
"Rahima kizo inji Umma"
Duk wanda yake wurin ya ga firgicin da ya bayyana a fuskarta ta kankame Mairama
sosai har ta soma kwalla.
"Tashi kije Rahima" Nene ta umarceta.
Tamkar wadda kwai ya fashewa haka ta mike tana kallon Ummi ko zata ce mata ta zauna
sai ta ga tayi mata alamar taje. A tsorace take sosai ta fito ta bi bayan Halifa.
Tana zuwa daga nesa ta zube a kasa ta gaisheta. Salame ta amsa yau babu wannan hura
hancin.
"Dama jiranki nake yi mu tafi"
A kidime tace "ina?"
Murmushi Salame tayi wai nan ita gyara za ta yi "muje gidana kiyi min kunshi saboda
Kamun gobe. Amma ki fara dauko kayan da zaki saka goben sai mu shiryo daga can"
Abinka da rashin sabo Rahima sai jin abin tayi bambarakwai ta kasa cewa komai sai
faduwar gaba. Halifa take kallo tana neman agaji.
"Umma ita za ta yiwa Radhiya kunshi fa ko?"
"Eh da su Anti Laila" ta ce cikin sauri.
Salame ta fuskanci akwai tsoronta a tattare da Rahima to amma so take ta gyara ya
kamata su bata dama.
"Nima ina nan din zan jira ki sai ku fara da wuri saboda yau nice da girki." Ta
murmusa hakoran nan masu gansa kuka suka bayyana "yau sai ki tayani muyi girkin
tare"
Qut...Rahima ta hadiyi yawu Halifa ya kalleta ya danne dariya saboda yasan karshen
takura da tashin hankali tana cikinsa. Salame ta bar wurin batare da Rahiman ta
amsa ba can kasan zuciyarta tana jin wani iri game da yadda idon yarinyar ya koma.
Yarfe hannuwa Rahima ta shiga yi tana kallon Halifa "yaya zanyi?"
Tausayinta yaji a ransa yana murnar shi namiji ne don gaskiya bai hango yadda zai
iya kwana da ita ba da shine Rahima. Babu wata sakewa ko shakuwar uwa da 'ya kawai
sai ku kwanta kusa da juna.
Kiranta taji Radhiya tayi bayan tafiyar su Emzee suna wurin Ummi tace a kira wata
mai lallen Rahima babu wanda zata yiwa saboda idonta. Radhiya dama a yatsu kawai
zata yi saboda dai kada ace amarya ba kunshi. Gidan ya soma kaurewa da hayaniya
Ummi ta fadawa Rahima ta tafi gidansu ta hado duk wani abu mai mahimmanci musamman
takardun makaranta da ita zasu koma gabadaya.
"Ummi gabadaya kika ce?" Ta kasa boye farincikinta. Tana son Mairama tsakani da
Allah saboda a dangin mahaifiya babu inda ta ga soyayya da kulawa kamar a wurinta.
Bayan la'asar kuwa ta sulale ta fice a soro ta hadu da Salame "yauwa dama ke nake
jira muje" ta nuna mata kofa.
A tsorace tace mata kaya zata debo a gida. Salame ko a jikinta tace idan ta dauko
ta taho gidanta gobe sai suyi sammakon fitowa.
Yau Rahima an shiga tsaka mai wuya. Yanzu idan ta rufeta da duka tana cikin bacci
fa.
"Naji ance jibi zaku wuce ne kinga zai kyautu mu kwana muna hira tunda zamu jima
bamu hadu ba"
Jiki a sanyaye tace to tayi hanyar gidansu. Baffanta da Iya basu ji dadin ganin
yadda idonta yayi ba ta hada 'yan kayanta masu kyau ta fada masa inda zata kwana.
Nan yayi tsalle ya dire yace ba dashi ba babu inda zata je. Iya ce tace ya kyaleta
tunda babu mai rabata da mahaifiyata. Ba don taso ba haka taje gidan. Kanenta na
binta da ido shekeke Salame ta daka musu tsawa tace bazasu gaishe da yayarsu ba.
Rahima da yaran a tare suka firgice Salame ina ma ta kula sai fada take wai basu
da tarbiyya basu san girman na gaba dasu ba. Murhu ta hada ta dawo ta kirata wai ta
tayata tankade. Tare suka yi girkin tana ta dararewa saboda kada jikinta ya gaya
mata.
💕 [11/2, 8:04 AM 60💕
: Tare suka yi girkin amma Rahima ce karfin aikin. Yaran gidan sai binta suke da
kallo ita dai kanta na kasa har suka kammala. Baffanta ne ya kira Ummi ya sanar da
ita inda zata kwana kada suji shiru. Addu'a ta rinka yi Allah Yasa kada wani abu
mara dadi ya biyo baya.
Lura Salame tayi da yadda Rahima take tsakurar abincinta. Tuwon masara ne da miyar
karkashi sai tashin daddawa take yi ga sukunbiya an saka saboda ita. A cikin kwanon
silva ta zubawa Rahima ta kwarara miyar a kai.
Sai da ta gama lashe hannunta ta bi irin abin miyar nan da ya kan makale a tsakanin
hakora da harshe tana sakato shi sai ji kake tana tsk-tskk da baki ta kora da ruwan
rijiya sannan ta tabe baki.
"Abincin namu bai kai na 'Yan Abuja dadi bane naga kina ta yafita kamar bakya so?"
Kafin ta kai karshen maganarta Rahima ta zunduma wata katuwar loma wadda ta kasa
hadiyewa saboda bata kaunar karkashi ko kadan. Da gudu taje bakin rariya ta zubar
ta dawo tana jiran Salame ta soma fada sai taji tayi mata magana babu wannan fadan.
"Ba kya cin tuwo ne?"
"Miyar...miyar ce dama...dama karkashi ne....bana sha"
"Yo maimakon ki fada nayi miki hadin mai da yaji sai ki cuci kanki? In kin fada min
ai ba dukanki zanyi ba" tace da ita amma idan kaji yadda muryarta ke fita sai ka
dan tsorata. Takaicin yadda yarinyar ke zabura duk motsinta ne yake damunta. Kwanon
ta dauka ta mikawa sauran yaranta da gudu suka far masa dama sun cinye nasu ita
kuma taje kitchen ta dibar mata wani cikin sauran da zasuyi dumame dashi da safe.
Mai kwantirola ta yaryada mata da gishiri ta dauko yaji da rabin maggi a dakinta ta
saka sannan ta bata. Ko kadan wannan hadi bai yiwa Rahima dadi ba saboda man danye
ne sai karni ke tashi amma kyautatawar da mahaifiyarta ta gwada mata karon farko
tun wayonta yasata yin kwalla ta janyo farantin ta cinye shi duka.
Basu wani jima da gamawa ba Alh Indararo ya dawo gida Salame ta kai masa nasa
abincin. Kayan jikinta tun na jiya ne babu zancen wanka a ajandarta duk kuwa da
cewa da murhu tayi girki ga kauri ga datti. Tunda ta shiga banda harara da habaici
babu abinda yake mata ya gama cin abincin yace ta fita kada ta sake zuwa turakarsa
da sunan kwana sai idan da kansa ya nemeta. Abu na biyu kuma ya bata lokaci kankani
ta san yadda zata yi su daidaita da Mairama a basu ko da mutum biyu ne cikin yaran
shi ma a rage masa nauyi.
Kallon raini ta bishi dashi "wannan shi ake kira karfin hali barawo da sallama."
Hannu ya kawo da sauri zai sauke mata ta fita ba shiri yana ta fada kuma wai kashin
tsiya gareta kada ya kuma ganin kafarta a dakin. Dama waye ya aiketa bayan jiya ya
mata dukan nan jiki yayi tsami. Dakinta ta koma aka yiwa yara shimfida Khadi tana
gado tace da Rahima.
"Kwaba lallen kizo ki yayyaba min dashi zan kwana saboda ya kamu sosai"
"Kada ya cabe ko ba mai ado kike so ba?"
"Ado kai 'yan nan. Kada ki damu zan iya kwana dashi."
Duk yadda idonta yake damunta bata nuna ba ta kwaba lallen nan ta zauna. Wayarta ta
soka a gaban dankwalinta bayan ta kunna torchlight saboda rashin wuta sannan ta
kamo kafar. Dandakuwa sunan wani abu. Ga datti da wani maiko maiko ga yalwataccen
kaushi yabi ko ina a cikin kafar babu inda babu. Kamar ta ce mata ko zata wanke
kafar amma babu fuska sai uwar hamma da Salamen take yi. Ba yadda ta iya haka tasa
kasan zaninta ta goge kafar sosai sannan ta baje basira ta soma zane. Goma ta wuce
ta gama Salame tace mata ta kwanta a daya gefen ya zamana Khadi na tsakiyarsu. Da
kyar ta iya bacci saboda rashin sakewa da sabo. Asubar fari kuwa ta mike ciwon ido
yayi sallama ya kara nauyi tana ruwa. Alwala ta dauro ta zo ta tashi Salame ta
kwashe mata lallen ta goge hannuwan da kafafu sannan itama tayi alwalar. Tun a
lokacin tana iya ganin yadda lallen nata ya fito radau yayi kyau musamman
hannuwanta. A sannu sannu gurbin da ta danne Rahima a zuciyarta ya fara neman nuna
kansa ga duniya. Sai take jin wani takaici da haushin kanta na kin sakarwa
yarinyarta tun farko.
Sunyi sallah Rahima ta gaisheta ta amsa tare da cewa ta bude idon da ta rufe mana.
Ai kuwa tana ganin yadda ya kuma hadewa gabanta ya fadi. Hakuri ne tun jiya ta kasa
bawa Rahima sai yanzu take sake ganin rashin hankalinta. Ruwan kunu taje ta dora da
ya tafasa ta debi wani a bokiti tazo ta gasa mata wurin. Babu wani sauki da taji
amma abubuwan kyautatawar da Ummanta ke yi mata kadai sun isheta farinciki.
Kafin ta dawo daga dama kunun Rahima ta soma janyo kayayyakin da suke soke a lungu
da sakon dakin babu wadatar isa ga zarni da wari duk ya hada. Gari guda ta hada
wanki sannan ta soma shara Salame ta shigo. Tunda take dan cikinta bai taba yi mata
shara ba. Na gabanta banda cin tsiya da fitsara basu san komai ba. Halifa namiji
ne, macen da zata yi kuma ta dauki karan tsana ta dora mata. Bata ce mata komai ba
Rahima ta aikatu sai wuraren shabiyu ta gama gyara dakin. Wankin kuwa Salame tace
zata yi da kanta.
"Lokaci na kurewa shirya ki tafi gidan Malamijo zan taho anjima ki bar min wankin"
Wanka taje yi bandakin babu kanta sai kawai ta shafa ruwa a fuska da kafa ta fito
sauran ta wanke musu bandakin. Da sauri ta shirya suka yi sallama ta fito. Sai
yanzu ta saki ajiyar zuciya ta sami nutsuwa saboda duk a tsorace take.
Da zuwanta gidan tayi sa'ar samun bandakin da babu kowa ta nemi ruwan zafi tayi
wanka. Ido suntum ta shiga daki wurin Ummi hankalinta ya sake tashi. Abinci ta sa
ta ci suka tafi asibiti a cikin garin. Sai bayan azahar suka dawo anyi mata allurai
tasha magani ta kwanta bacci.
Biki yayi biki gida ya cika da dangi abin farinciki harda wasu cikin mutanen
Sakkwato banda na rugar Barkindo zuga guda. Anci an sha babu kwandalar Mairama ko
ta mijinta. Malamijo ne yayi kusan komai sai kuma kannen Mairama su ma wasu katan
din lemo, akwai wadda tayi zobo da ginger aka kulla a leda, cincin da meatpie kowa
dai ya nuna da gaske sun gaji da zaman doya da manja zumuncin suke muradi ayi.
Amarya Radhiya sanye take da leshi mai dan karen kyau ja da adon duwatsu anyi mata
dinkin buba ta daura zamin a kai. Kafarta babu lalle sai yatsu kawai haka ma hannu
amma tasha ado ba kadan ba. Sarkar beads aka yi mata shirin ya kayatar matuka tana
tsakiyar fili ita da Mama da 'yan uwa ana kidan kwarya. Rawa take tana juyi karaf
idanunta suka gano mata shigowar Gwaggonta Salame tana tafiya tana dafa bango
saboda takalminta. To da yake Allah baiyi ta mutum mai riko ba indai anyi abu ya
wuce to fa ya wuce kenan a wurinta sai dai dan abinda ba'a rasa ba. Shiyasa take
kaifi daya babu munafurci ayi komai a wuce wurin. Tana takun rawar a girgiza 'yan
mata da masu kidan suke yi taje ta riko kafadun Salame ta kawota tsakiyar fili. Ba
laifi tayi kyau atampa ce a jikinta ta sako wani takalmi da bai tsufa ba tun na
lefe saboda bata sakawa sosai yayi mata tudu. Yau kuwa dole a dama da ita kowa
yasan cewa bata karewa Salame ba.
Bata gama gyara tsayuwa ba Radhiya ta rinka juyi da ita ana girgiza jiki ana rawa.
Salame tayi wuri wuri ta jigata 'yan uwa aka basu fili ba abin ta gudu ba ace bata
son zumunci tafi kowa laifi. Wata kanwarsu ce ta leka dakin da Mairama take zaune
da Rahima mai bacci tace mata ta leko tasha kallo. Daga bakin kofa ta hango rawar
da suke tika harda su Hajjo amma Salame jikinta yafi na kiwa girgiza saboda Radhiya
ta matsanta mata. Me Mairama zata yi kuwa banda dariyar yadda suke yi. Daidai
lokacin Salame ta dago kai suka hada ido Mairama ta daure fuska kamar ba ita ke
dariya ba ta shige dakin.
Kwafa Salame tayi cike da takaici a zuci take ta babatu "jimin rashin mutumci fa,
tana kallo 'yarta za ta ballani maimakon ta tsawatar shine ta koma daki, yanzu kayi
magana a hadaka da sojoji saboda rashin gata"
Wani kanin Mairama ne mai hoton yazo aka fara sannan fa Salame ta samu damar
sabulewa. Malamijo ma yazo ansha hutuna yana rike da 'yan biyunsa. Kyautar saniya
da sa ya yiwa Radhiya babbar jika yace amma a barsu a gonarsa ya cigaba da kiwata
mata. Abu yayi kyau zukata sun haskaka da farinciki.
Bayan isha ne Salame ta gama shirin tafiya ta shiga neman Rahima. Haka kawai take
son su tafi tare jiya taji dadi har ranta ko da bata iya nunawa ba. Tana daki wurin
Mairama tana faman lallabata taci abinci. Gobe da sassafe zasu tafi saboda a kaita
asibiti. Yanayin idon ya soma bata tsoro.
Daga jikin kofa Salame ta coge taki yiwa Mama da Ummi magana sai Rahiman ce tace
mata "Umma inzo mu tafi ne?"
Keyar Mairama kawai take gani amma jikinta ya bata gara ta hakura kafin wani abu ya
biyo baya. Duk da haka ta ga yana da kyau ta tunawa kanwarta wace tayi ciki da
goyon Rahima.
"A'a yi zamanki Rahimata, gobe zan shigo da wuri kafin ku wuce mu karasa hirarmu ta
dazu. Kayanki kuma zan bayar a kawo miki yanzun nan"
Dariya ce ta ciwo Ummi wai Rahimata...to dama waye yace ba tata bace? Ita kadai ta
nesanta kanta da yarinyar kuma zata fi kowa farinciki idan taja ta a jiki ta sami
soyayyar uwa kamar kowa. Sake maimaita kalmar tayi sai dariya tana ta kokarin
dannewa amma yadda Salamen tayi magana dole mutum ya dara. Mama na ganin haka ta
tace Rahima ta kawo ruwa kwarewa tayi.
Tana fita ta kalli Salame da ke tsaye har yanzu "dan bubbuga mata bayan mana Adda
Salame kina tsaye tana tari"
Idanu ta zaro kamar zasu fado tace "wa? Ni....shegiya inji dan daudu. Rufa min
asiri ina tabata yanzu zaki ji dirin motocin sojoji ana kiran Salame"
Kan kace kwabo ta fice abinta ko da Rahima ta dawo bata nan. Washegari sammako suka
yi saboda yadda Ummi ta matsu suje asibiti kullum idon kara kumburi yake yi. Ta
yiwa Malamijo zancen masu zuwa biki yace kada ta damu zai turo wasu Abujan wasu
kuma su bisu Sakkwato har zuwa kai amarya Katsina sannan wasu daban suje Nijar.
Hakan yayi mata kuwa sosai.
A ranar Mami itama da nata gayyar suka wuce Abuja. Abinda ya bata mamaki bai wuce
biyosu da Fauziyya da Bilal suka yi ba. A take ta nunawa Fauziyya bata son yawo ta
bari har sai ana gobe Bilal yace shine yake son su tafi saboda akwai abinda zasu yi
da Raji da angwayen. Bata matsa son jin ko meye ba suka kama hanya.
**********
A Abuja azahar ta riskesu saboda sammakon da suka yi. Dan kwana biyun da babu
Mairama Daada yaji jiki saboda har yau gani yake ko daya bisa dari na fanshe rashin
matarsa baiyi ba. Yana falonsa na kasa suka iso Radhiya ta makalkale shi yana
dariya. Ita kuma ta lura hakan na masa dadi sai yaji kamar bai rasa komai ba na
rayuwar 'ya'yansa shiyasa take yi. Rahima na gefe tana murmushi ta gaisheshi ya
sakar mata fuska