Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
ne nawa shi kam bama kwana uku bamu gaisa ba"
Ta sake kunna Radhiya bata sani ba. Wancan karon Ghazalatu yanzu kuma Arifa. Itama
haka zai zo yace ta hakura ya fara aurenta? Zaman sai taji ya isheta so take su
tafi kawai. Tana kallo suka tashi suka bi wata kofa Mom dinta na cewa dama an dade
ba a hadu ba yau tasan zasu sha hira ne.
Haushin kowa ta rinka ji harda su Fauziyya. Basu dade ba suka dawo ta fada masa ne
Excellency ya karbi nambar wayarsa a wurinta yace zai kira shi kada yaji waya
bazata ya dauka wani abu ne. Suna dawowa yace zasu tafi Mom ta hada kowa da gift
tana ta godiya.
A jikin motar da matan suke Arifah tace musu gobe idan suna da lokaci me zai hana
su je park. So take su saba da juna sosai. Zahra ta amince ko don mijinta mai zuwa
camping a filling station.
💕********43. 💕
"Nima haka nayi tunani. Zauna Awwab. Duka wani protocol da gon kamata nabi domin
sanin gaskiya nabi. Yanzu haka ina jiran kira daga Mr President ya bamu go ahead mu
nemi ganawa da gwamnatin kasar domin a sake shi"
"Kana nufin Babana Zayyan yana da rai duka tsahon shekarun nan a prison" hawaye ne
mai zafi ya zubo masa baiyi yunkurin dakatar dashi ba.
Dukkan bayanai Excellency da kansa yayi masa yaci kuka tamkar kankanin yaro. Zancen
da girma kuma da nauyi. Gashi yace yayi shiru har su dawo saboda yana tsoron sakawa
iyalinsa rai da abinda ba gaskiya ba.
"Ka samo min hotonsa, na matarsa dana 'ya'yansa. Idan da hali harda copy na
national identity card dinsu ko international passport domin mu tabbatar musu bashi
da alaka da Liberia"
Kamar anyi masa duka haka ya koma gida zuciyarsa tana ta bugu da karfi. Zahra bata
dakinsa a nan ya kwana sai dai ko digo bai iya runtsawa ba. Kwana yayi yana tunanin
ta yadda zai samo hotunan da ake bukata. Duk da yace kada kowa yaji dole ne ya nemi
mai taya shi. Jira yayi sai da su Yousuf da Tante suka tafi airport zasu wuce
Nijar, shi dai bai bisu ba su Radhiya ne suka tafi rakiya ya shiga bangaren Mama.
Baba Hadir yana falo sai ya wayance da ganin Daadaa ya tafi. Mintu talatin bai cika
ba ya kuma dawowa har yanzu yana falon ita ta tashi. Zama yayi kamar akan kaya yana
jiran Baba Hadir ya fita ko ya koma daki shiru. Mama tun da ta dawo take karantarsa
daga karshe tace wa mijinta ya basu wuri zasu gana da danta ta ga alama son aure
yake yi.
Baba Hadir ya girgiza hannuwa wai babu ruwansa ya tashi ya shiga ciki. Sai kuma ya
kasa cewa komai.
"Awwab ka fara bani tsoro. Akwai abinda ke damunka fa"
Siririn hawaye ta gani ya ziraro daga idonsa ta soma tafa hannuwa "Radhiya ta sake
cewa bata shirya auren bane?"
"Ni ai na shirya so bana bukatar amincewarta" yace yana kakalo murmushi.
"Good, me kake boye min?"
Yanayin da ya shiga da Excellency yake masa bayani har tafi shi. Zainab kuka take
rikewa Awwab yana bata baki da ta daure saboda kada a gane. Abubuwan da yake bukata
ya zayyane mata tace zata yi masa kokari zuwa dare. Daurewa kawai ta rinka yi kada
ayi saurin ganota musamman da Ibrahim da Emzee zasu dawo yau gidan zai kara cika.
Dakinsu ta shiga cikin kayan Baba Hadir ta dukufa bincike. Bata yi mai yawa ba ta
samo hotunan Zayyan da khakinsa shi da Hadir. Da wayo da dabara tasa Radhiya ta
kawo mata passport dinta wai zata gani. Hadawa tayi da hotunan ta bawa Awwab cikin
wata leda wai sako ne. Yana karba yaje yayi photocopy na passport din ya dawo mata
dashi. Sauran hotunan ta waya ta tura masa duka yayi printing ya kaiwa Excellency.
A hanyarsa ta komawa gida ya kira shi ya sanar dashi shugaban kasa da kansa ya nemi
shugaban kasar Liberia zai bada umarnin a duba masa mai wannan suna a prison din.
Wannan dare ma bacci barawo da kyar ya dauki Awwab, Mama Zainab da Col.
Nasiruddeen. Dare ne mai tsayi a garesu wanda a safiyarsa ne zasu ji dahir. Ayi ba
ayi ba sai gabanin magariba wayar Excellency ta shigowa Awwab.
"Karfe tara na safe zamu tashi gobe, Zayyan has been found"
"Alhamdulillah" Awwab yace idanunsa na cika da kwalla. Baya jin komai don yayi kuka
saboda abin kukan ne ya same su.
A daren ya sanar da su Mami tafiyar gaggawa ta kama shi Lagos wai kamfanin jirgin
da yake aiki zasu gabatar da wani shiri. Ita kadai ce karyar da ya iya nema ya fada
musu. Rashin zamansa a gida yasa bashi da lokacin neman Radhiya abin har ya soma
damunta. Tun daren da akayi masa wayar sai yau yaje wurin Ummi saboda yana gudun ta
fahimci wani abu a tare dashi kamar yadda Mama tayi. Zancen tafiyar yayi mata tayi
masa fatan alkhairi. Yaso ganin Radhiya sai dai tayi bacci da wuri period pain ya
kwantar da ita. Da safe kafin ta tashi ya tafi sai labari taji wai ya tafi Lagos.
Fada ta soma yiwa kanta na saurin bada kai da taso yi bata san babban aikin da yasa
a gaba domin iyalansu gabadaya ba.
Da yaje airport yayi mamakin ganin official plane din shugaban kasa aka bayar
dungurungum domin dauko Lt Zayyan Tureta. Su tara ne duka a tawagar. Shi, gwamnan
Plateau, Deputy chief of army staff, Chibuzor da wasu sojoji guda biyar. Gani yake
kamar da shi yake tuka jirgin sai yafi haka gudu amma sannu sannu bata hana zuwa
sai gasu sun sauka a filin jirgin Monrovia babban birnin kasar.
Su ma sojoji suka turo domin daukarsu ana musu zancen tafiya hotel Excellency yace
ko ruwa bazai iya sha ba sai ya ga Zayyan tare dasu.
**********
Kararrawa aka buga lokacin cin abincin dare yayi 'yan prison din suka soma fitowa
daga dakunansu da aka bude. Kusan kullum cin abincin tamkar yaki ake yinsa kowa na
sauri ya sami abin arziki.
Tafiyar nan tasa da dogayen kafafunsa yake yi cikin nutsuwa ya isa layin ya tsaya
kenan wani kato yazo ya sha gabansa. Sai ya ja baya ya bashi wuri saboda gudun
rigima. Sati uku da kwanaki da tafiyar Chibuzor dan guntun hope din da yake dashi
gabadaya ya tafi. Fadawa kansa yake yi ya cigaba da hakuri da kaddarar rayuwarsa me
yiwuwa shi da iyalinsa sai a lahira. Shi da kasarsa kuma sunyi bankwana kenan.
Rikici ne ya kaure daga gaban inda ake rabon abincin garin dambe aka zubar da
kulolin abincin a kasa. Mutane kuwa suka dira akansa suna wawaso ga gandirobobi
suna ta kokarin raba su.
Yau ma bashi da abinci kenan zaiyi kwanan yunwa ya juya a nutse zai koma dakinsu.
Da rana wani tsoho ya barwa nasa saboda ya taho zai zauna irin shakiyan nan wani
yasa masa kafa yayi tuntube ya fadi. Yanzu kuma abincin duka an zubar. Ya kusa isa
dakinsu yaji da karfi ance.
"LIEUTENANT ZAYYAN MUHAMMAD TURETA"
Tunda ya shiga kurkukun nan sunansa 3810 sai ko mutanen da suka san sunansa kalilan
amma su dinma numbar tasa suke kira. Gabansa ne yayi mugun faduwa ya juyo da
sauri. Babban prison Warden dinne da kansa ya shigo wurin. Wannan salon tafiyar
tasa da shi kadai ya iya kayarsa yayi zuwa gaban mutumin. Ga mamakinsa sai ya ga ya
cire hularsa ya maketa a kasan hannu daya sannan ya gyara tsayuwa ya sara masa.
Habawa sai idanu suka tattaru a kansu shi ma sai yayi saluting mutumin yana jin
idonsa ya soma ruwa domin hasken da ya fara hangowa na rayuwar 'yanci
"This way Sir" Chief Warden yace masa ya bi bayansa. Sun fara tafiya ya juya ya
kalli prison din da jama'ar cikinsa sai ya tsaya at attention ya kame yayi saluting
dinsu. Da yawansu su ma sai suka yi masa wadanda suka taba jin cewa soja ne suna
taya shi murna.
Wani office aka kaishi Chief Warden ya bashi takarda ya saka hannu a kai sannan ya
kuma gyara tsayuwa.
"Kai jarumi ne da ban taba ji ko ganin kamarsa ba. Kasarka bata san kana raye ba
tsahon shekaru ashirin da biyu sai yau zaka koma gida. Ba kai nake tausayi ba sai
ire irenka da dama da suke da rai a hannun abokan gaba ko kurkuku irin wannan
batare da an sani ba. Goodbye Lieutenant"
Musabaha suka yi sannan ya kuma nuna masa kofa suka fito tare. Wani gate da bai
raba sanin akwai shi ba duk tsayin zamansa a wurin suka bi sai ga motoci biyar a
jere na Nigerian Embassy dake Liberia a baya kuma wasu uku ne na sojojin kasar.
Motar tsakiya aka nuna masa ya shiga yana jin kansa kamar a ire iren mafarkan da
yake yi na komawa gida. Cikinta ma sojoji ne da sai suka yi saluting dinsa suka
shiga aka tayar. Jiniya ce tun daga prison din har babban ofishin jakadancin
Nigeria dake Liberia.
Awwab ya kasa zaune ya kasa tsaye haka ma Excellency. Duka a waje suke daidai kofar
shiga tare da Ambasadan suna tsaye zugar motocin nan suka jeru a gabansu.
Kafin ya yunkura an bude masa kofa ya sako kafarsa waje sanye da takalmin roba da
ya mutu murus. Kayan jikinsa a kode suke sosai. Fatarsa kuwa bai san cewa ta shiga
wani yanayi ba sai da ya ga mutanen dake tsaye a wurin sun zuba masa ido.
"Uncle" yaji ance da muryar da ya sani. Chibuzor ne ya taho wurinsa da hawaye yabe
yabe a fuska. Zayyan ya rungume shi.
"My son I owe you my life"
"And I owe you mine" yaji wani ya fada daga bayansa.
Sannu a hankali ya juya yana kallon mutumin dan lukuti ga tumbi amma komai nasa
yana nuni da cewa ba karamin mutum bane. Ina yasan fuskar nan yake ta tunani.
"Baban Alheran kayi hakuri banzo da wuri ba"
Zuciyarsa ta nemi bugawa don bai manta mutumin da yake kiransa da wannan sunan ba.
Sai yanzu yaso ganin kama. Bakinsa yana rawa yace "Baban Arifah? Col.
Nasiruddeen?"
Rungume shi yayi suka fashe da kuka a tare mutane na kallonsu wasu suna yi.
Ga Awwab kuwa babu inda baya rawa a jikinsa. A yau ya yarda soja daban namiji
daban. Duk yadda yake son ya dake kwanansa nawa yana kuka saboda jin cewa Babansa
Zayyan yana nan amma babu tabbas sai ido ya gani. Shekarun da yawa amma tabbas
shine wannan mutumin da ya ga duniya kuma duniya ta ganshi.
Muryarsa tana rawa yace "kaine Tureta?" Yadda ya taba yi masa farkon haduwarsu.
Zayyan ya dago kansa daga kafadar Excellency yayi masa murmushi "nine yaro. Ka
sanni ne?"
Tsigar jikin Awwab har tashi tayi a lokacin da ya kamo hannuwan Zayyan duka biyun
"sunana Muhammad Awwab Mustapha...ka tuna ni?" Ya kare tambayar da kuka.
Wasu sababbin hawayen suka sauko daga idanun Zayyan jikinsa shima yana rawa ya
sanya hannuwansa biyu a gefen kumatun Awwab da suke tsayi kusan daya.
"Awwab din Mairamata?"
Awwab ya gyada kai nasa hawayen suna gudu kamar famfo baya tunanin yin komai domin
tsayar dasu.
"Major da Hadir fa?"
"Suna cikin koshin lafiya"
"Mairama?"
"Na barota lafiya"
"Alheran dinka?"
"Tana jiran Daadaa yazo ya aura mata Awwab" yace yana murmushi mai hade da kuka.
Zayyan ma sai ya fadada murmushinsa.
"Cikin jikin Umminka?"
"Alive and well sai munje gida zaka ga ko mene"
"Awwab?"
"Daadaa"
"Nayi kewarku, nayi kuka, nayi hakuri nayi hauka duka a rashin sanin makomar
rayuwata. Ku kaini gida...ku kaini wurin iyalina"
Kankameshi Awwab yayi suna kuka sosai abin tausayi da tsinka zuciya.
**********
💕[11/2, 7:11 AM] 44.💕
*SAKAMAKON ALKHAIRI...ALKHAIRI NE*
Awwani hudu bayan dauko shi Awwab da Excellency suka saka Zayyan a tsakiyarsu suna
zaune a cikin jirgi domin komawa Nigeria. Sai da aka hadu so da takardun neman
afuwa kuma mataimakin shugaban kasa yace zasu zo Nigeria officially bada hakuri.
Sun kama hanya cikinsu babu wanda zai iya bacci a wannan kasar idan basu ga kafafun
Zayyan sun sauka a kasar haihuwarsa ba. Babu wanda ya damu da wata tafiyar dare ko
nisa. A lokacin da suke hawa jirgin Zayyan ji yake kamar ana zare masa wata kaya
mai tsini daga cikin zuciyarsa.
"Baban Alheran" Excellency ya kira shi ganin idanunsa sun kasa daina zubar hawaye.
Kukansa kuwa kara raunana Awwab yake yi suke ta yi tare. Kallonsa yayi suka hada
ido yaji mugun tausayinsa ya mamaye masa zuciya.
Har yanzu kyakkyawan mutum ne da ya wadatu da arzikin kyakkyawar zuciya, amma
yasha wahalar rayuwa fiye da zato da tsammani. Ciwon da yake tattare da rabuwa yafi
karfi a gareshi domin shi yasan ya baro iyalinsa da rai ya azabtu da begen sake
ganinsu sabanin su da suka dangana saboda tunanin ya rasu. Akwai lokutan da yake
jin kamar zai zauce saboda kewarsu. Wani zubin kuma hakuri yake sakawa ransa, wasu
lokutan kuma yayi kuka har sai yaji kamar bashi da sauran hawaye.
"Baban Alheran kayi hakuri shine abinda zanyi ta fada maka har muje gida. Ni dasu
Hadir da Mustapha duka zaton mutuwa muka yi maka"
"Ka dena bani hakuri domin Allah Ya riga Ya warware min ciwon da yake raina. Ku
bani labarin me ya faru daku da matata"
"Bazaka jira mu koma ka nutsu ka huta ba?"
"Labarin ne kadai zai sa na cigaba da dauriya har mu sauka. Idan ban manta ba ana
cewa aski idan yazo gaban goshi..." yayi murmushi.
A takaice Excellency ya labarta masa dalilin tunaninsu na cewa ya rasu, ya kare da
cewa "sauran bayani zaka ji idan mun isa gida ka huta yanzu"
Ruwa da abinci aka kawo musu amma shine ya fara daga hannu domin dakatar da air
hostess din daga ajiye masa.
"Daadaa kaci wani abu mana. Kafin mu taho ma ko ruwa baka sha ba duk wannan lokacin
da aka bata" Awwab yace yana rokonsa.
Murmushi yayi sai ka rantse Emzee ne a wurin yace "babu abinda zan sake ci ko sha
sai naje gida in sha Allahu Mairama ta bani."
Yana so ya tambayi Awwab ko tayi wani auren amma baya tunanin zuciyarsa zata iya
daukan nauyi irin wannan komai kankantarsa a yanayin da yake ciki shiyasa ya ja
bakinsa yayi shiru suka cigaba da tafiya kowa yana murmushin farinciki da jindadi.
A awa uku mintuna kalilan ne babu a tafiyar suka iso Nnamdi Azikiwe International
Airport na birnin tarayya Abuja. Jirgin yana sauka Zayyan sai ya soma jin kamar
mafarki yake yi. Anya shi din da ya yi bacci ya farka a kuntataccen dakin kurkuku
dazu da safe wanda suke sharing shi da mutane shida kowa akan katifa mara kyaun
gani a wata kasar da ko sunanta baya son ji shine yake sauka a kasa mai dimbin
daraja kamar Nigeria? Ana bude kofa ya hango hasken lantarki na ciki da harabar
filin jirgin saboda dare sai yaji wasu zafafan hawayen da suka fi na dazu.
Excellency ya nuna masa kofa da murmushi a fuskarsa "ka fara fita".
Sannu a hankali yake takowa ga wasu sojoji kowa da bindiga a hannu suna jiran
saukowarsa. Sojijin da suke da alaka ne da binciken dawowar dan uwansu bayan
shekaru masu yawa a prison. Babu abinda yake kallo sai kwaltar dake shimfide a
makeken filin da jiragen suke sauka da tashi. Kafarsa na taka kasa ya sake fashewa
da kuka.
Wani soja ya daga murya yace "Atteeeeention!"
Sauran suka jeru a layi guda kowanne ya gyara daga bindigarsa sai kuma suka sauke
suka sarawa jarumin jarumai mazan fama Lt. Zayyan Tureta domin duk da sai an sake
ji daga bakinsa amma basu sami wani dalili na karyata komai nasa ba a bisa
bincikensu. Ayya, sake karyar da zuciyarsa suka yi ya daure ya kame shima cikin
kayansa na kurkuku ya sara musu sannan kawai ya fadi ya kai goshinsa kasa domin
nuna tsantsar godiya ga Sarkin Sarauta wanda MulkinSa shine cikakken Mulki Allah
Azza wa Jallah. Sujjada yayi ya rinka kwararo kirari ga Ubangijin sammai da kassai
yana hamdala da ganin wannan rana. Shi shaida ne akan kansa cewa ba don Allah Ya so
shi ba da tuni ya sami tabin kwakwalwa a prison dinnan saboda yawan tunani.
Sumbatar wannan kasar da muka raina, muke zubar da jini, zina, sata da manya manyan
laifuka akai yayi saboda shi uwa ya dauketa wadda idan 'ya'yanta sun lalace ba ita
bace ta lalace sai dai a kawo mata gyara. A yayin da daruruwan mutane suke fatan
budewar kofar da zasu bar Nigeria idan suka tafi ko ta halin kaka bazasu dawo ba
mutane irin Zayyan da dama zasu iya fansar da rayuwarsu domin suyi yini guda da
iyalansu a cikin wannan kasa. Tabbas Nigeria bata lalace ba sai dai a cikin
'ya'yanta akwai bara gurbi. Ya Allah Kayi mana maganinsu Ka shiryemu baki daya.
Baso wani bata lokaci a airport din ba motocin mai girma gwamna dana sojoji zuga
guda suka rankaya zuwa ga babbar headquarter dinsu. Dare ya riga yayi ana neman
goman dare amma ga mamakin Awwab sai yake ganin baban nasu da kuzari babu alamun
gajiya ko yunwa. Shi da yayi shekara ashirin da biyu yana jiran wannan rana ba
karamin abu bane zai sarar masa da gwiwa bayan isowarta.
Excellency ne yake masa bayani da cewa zai amsa tambayoyi ne domin keeping record
da binciken da ba'a rasa ba kamar yadda aka yiwa Chibuzor. Idan yana so zaiyi
magana a barshi ya wuce wurin iyalinsa gobe ya dawo.
Wani irin kallon anya kana tausayina ya yiwa Excellency din yana komawa Zayyan
dinsa na da "idan akace maka zan fito gobe sai ka yarda?"
Dariya yayi "ina zan yarda kuwa Baban Alheran....to muje in sha Allah ba dadewa
zamuyi ba"
"Suna Sumaila ne ko ta zauna a Sakkwato?"
"Duka muna nan Abuja Daadaa, ka shiga ku gama mu tafi gida" Awwab yace yana dauko
wayarsa daga aljihu.
"Mu gani Awwab" Zayyan ya mika hannu zai ga abin mamaki. Juya wayar ya rinka yi
yana shafawa "Allah mai Iko, a prison dinmu na kan hango su a hannun wasu maaikatan
sai aka ce wai cellular ce. Ni dai nayi mamaki sosai ace 'yar wannan abar ita ce
waya yanzu. Kuma kamar nawa take?"
Maimakon amsa kuka ya sake sake Awwab. Duniya ta cigaba sosai amma Zayyan bai sani
ba saboda a prison da yake na masu manyan laifuka ne sosai wadanda gwamnati bata
musu sassauci. Musamman ake kai firsunonin yaki da 'yan tawaye wadanda suka kawo
asarar rayuwa da dama da dukiya a kasar.
"Yi hakuri na dena magana tunda kuka nake saka ka" suka rungume juna sannan Awwab
yace ya tsaya tare da Excellency da Chibuzor Zayyan a tsakiya ya mikawa wani soja
wayarsa ya daukesu a hoto fuskar kowa cikinsu a sake. Ai da ya nunawa Zayyan sai ga
dariya yana kada kai "kara mana daya dai na sake gani"
Awwab ya yi dariya a ransa yana ayyana irin abinda Alheran zata aikata ne idan abu
ya burgeta. Wata matsananciyar kewarta ta soki zuciyarsa ya fara matsuwa da su tafi
gida haka. Hoton Chibuzor ya daukesu su biyu dashi da Zayyan sun sakala hannuwa a
kafadun juna sannan aka shige dashi wani daki da manyan sojoji aka rufe kofa.
Tambayoyi ne dai kamar bazasu kare ba daga manya manyansu da aka hada comittee na
bincike akansa. Komai nasu anayi ne bisa tsari daki daki. Da ya gama bayani a dauko
wani. Suna yi suna duba takardun da aka basu daga can Liberia da kuma information
da suke dashi akansa saboda har file dinsa