Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
wannan abin burgewa ana ta murmushi da dariyar
farinciki.
Can gefen slideshow ake yi na hotunam da suka dauka rannan kowa yana bin baiti ana
nuna amaryarsa. Saboda basu taba zato da tsammani ba shiyasa mamakinsu da farinciki
yayi musu yawa.
Radhiya sai da taji kamar a wurin ta rungume Awwab ta kwana tana fada masa cewa shi
kadai ne farincikinta a rayuwa.
Sai da wakar ta kare a daidai imda suke rawa a tsugunne suna kada hannuwansu su ma
su Awwab hakan suka yi wuri kuwa ya kaure da tafi kamar zasu tsaga hall din. Gashi
duk yadda manyan nan suka so yin liki an saka wani abu kamar ribbon alamun babu
wucewa. Suna gamawa fita suka yi haske ya mamaye wurin MC yace za'a fara cin
abinci. Ana ta hayaniya da zancen yadda abu ya kayatar Fauziyya tazo ta ja amaren
zuwa dakin da zasu canja kaya. Lace suka saka coffee color da gold head da sauran
accessories aka gyara musu kwalliya. Ana tambayarsu yaya suka ji game da babban
surprise din su Awwab sai murmushi an rasa me cewa wani abu. To su ce me bayan
amgwayen sun gama musu komai.
A wurin shiga suka hadu dasu Awwab da Radhiya na gaba su Arifah na bayansu. Wannan
karon shadda suka saka golden babbar riga da hula. Sun shiga kafin su zauna aka
canja waka zuwa ta Nura M Inuwa wato 'Yar amanar da Radhiya ke matukar so. Wannan
karon kam iyayensu mata sai da suka fito Awwab da Yousuf basu bar komai na irin
takun Zango da ya hau wakar ba suna faman baza babbar riga. Liki akeyi kamar
ba'asan ciwon kudi ba Awwab ya makale matarsa a gefe ganin wurin babu masaka
tsinke.
Taron ya tashi sa misalin shadaya da rabi na dare anyi hotuna anci an sha rayuka
sun faranta. Ghazalatu kamar ta hadiyi tabarya haka bakinciki ya tsaya ya tokare
mata wuya. Tana ta bin Awwab da ido bata san ta ina ba sai jin Nura tayi a bayanta
ya rungumota a waje da suka fito ana tafiya gida. A fusace ta juyo tace masa bata
son wulakanci meye haka zai tabata.
"Dazun nan na mayar dake Ghazy" yace yana shafa keya.
Ashar ta dankaro masa saboda tsabar bacin rai. Tana hangen yadda zatayi ta sami
Awwab shine don rashin mutumci ya mayar da ita. Ko sauraronta baiyi ba ya jefata a
motar da yazo da ita yace mata yau zasu fara angwanci.
Wuri ya watse saura mutane kadan Awwab ya karbi mota a wurin drebansu wadda yada ya
kawo masa ya budewa Radhiya. Yau duk ya kashe mata baki da abubuwan mamaki. Babbar
rigar ya cire da hula ya dora mata akan cinya kamshin turarensa ya mamaye hancinta
ya shiga mazaunin dreba ya tada mota.
Shiru ta kasa magana sai murmushi ya kalleta yace "tunanin me kike yi Schatzi?"
Kafin ta bada amsa ya zame mata gwaggwaronta da ya zauna das a kanta ta ja mayafin
da ta ce a saka mata a jakar kayan ta rufe kanta.
"Ke nake sauraro?"
Ido ta runtse ta soma magana a hankali "Hammana bani da wani buri da ya wuce
faranta maka. Abinda kayi min tun farkon haduwarmu har zuwa yau bazan taba mantawa
ba. I love you with all i've got. Alheran is never complete without Awwab. Nagode,
nagode, nagode" ta daga hannunta mai zoben da ya saka mata ta sumbata.
Hannunta kawai ya kamo ya rike a haka ya kaisu gida suna kallon juna suyi murmushi.
Ita kuwa harda sunkuyar da kai.
Kusan kowa ya dawo ga motoci nan birjik a ciki ya samu wuri yayi parking.
Rigarsa da hular ya dauke daga cinyarta ya jefa baya inda ya cilla mata gwaggwaro
sannan ya juyo da jikinsa yana fuskantarta ya jinginar da kansa gefe.
"Baby" taji yace a hankali sai da tsigar jikinta ta tashi.
"Uhmm"
"Na gaji sosai"
"Ai dole ka gasa jiki ko ka kasa tashi gobe" ta fada gabanta na faduwa.
Hannunsa ya mika mata duk lokacin yana kallonta tana jin idanuwansa a jikinta ta
dukar da kai tana wasa da yatsunta da suka sha lalle. Sai da ta sake jin sabuwar
faduwar gaba ta mika masa hannun damanta.
Tayi zaton rikewa kawai zaiyi ashe hanya ya nema ya janyota gabadaya jikinsa tana
kan cinyarsa. Rungumeta yayi sosai yana sauke numfashi ta soma mutsu mutsun son
tashi.
"Kinga" yace yana jan wani dan compartment a gaban motar tayi arba da mukullai "na
gidanmu ne, ko dai ki nutsu ko na juya kan motar a biyoki da kayanki gobe"
Da sauri tace "Kai Hammana"
"I am serious baby na gaji sosai...mun kusa wata da aure da yanzu kin fara amai da
tashin zuciya...."
Salati ta soma yi kunya kamar ta nutse a wurin "ni dai babu ruwana"
"Da nawa ni kam please ki bani janbakin nan na goge miki ko kuma mu tafi gidan"
A tsorace tace "idan wani ya ganmu fa?"
"Baki ji nace janbaki zan goge ba...haka zamu fada musu ai" ya sake yi mata wani
irin riko.
"Wannan fa wayo ne"
"Ki bari nayi miki wayon mana" ya kyabe fuska shi a dole zaiyi mata shagwaba.
Dariyar da ta soma yi ya datse da bakinsa tun tana jin tsoro har ta biye masa suka
manta a cikin gidan Daada suke.
💕[11/2, 8:22 AM] 61💕🏽
Da kyar ta samu ya kyaleta ta fito daga motar ko ido ta kasa hadawa dashi. Shi
kuwa ko a jikinsa sai ma murmushi da yake ta yi yana rike da hannunta.
Kashe mata ido yayi yace "yau ba zaki kara shafa wani ba don kada a gane?"
Motar ta nuna masa "shiga ka tafi ni dai"
Dariya yayi mata sannan ya dora hannunsa akan kirji ya ce "Kora ta kike yi? You are
breaking my heart Schatzi, nayi zaton yau babu mai rabani dake"
"Ba korarka nake yi ba amma yanzu ina shiga ciki kunyar su Adda Zahra zanji. Sun
san fa mun taho tun dazu amma kawai sai su ga na dade ban shigo ba?"
"Kin ma bani tausayi, idan kika tare Alheran na rinka baki kunyar nan kenan. Yadda
nake so matata ta rinka kulawa dani haka nima zan rinka yi miki" ya janyota jikinsa
ya zagaye kwankwasonta da hannuwansa.
Kunya sosai take ji gasu a waje kuma a gidan da yake da mutane tasan ko yaushe wani
zai iya fitowa. Kukan shagwaba ta soma yi masa yace to ta shige ya rakata zuwa
falo. Sun kusa shiga ta fara cewa ya juya ya tafi ita bata son su Fauziyya su
ganshi.
Kai ya girgiza yana janyota ta hanyar dora hannunsa a kafadarta suna jerawa "indai
Zahra da Fauziyya ne ina tabbatar miki kowacce tana wurin mijinta yau babu mai
kwana a nan. Femi da Jawad suna wurin Zayyana da Rahima"
Baki Radhiya ta rike "a ina zasu kwana?"
Hancinta yaja a hankali ya juyo da ita gabansa ya rage tsayi tare da hada nasa
hancin da nata yana magana a hankali "su na inda muka baro yayyen naki kowacce
tasan abinda ya kamata. Wannan tsallen da muka sha sai da tausa..." kwantar da
murya yayi mai kashe mata jiki "Allah Sarki Awwab tasa matar kunyar mutane tasa ko
tunanin ciwon jikin da zai kwana yana y batayi ba. Dani da na biya sadaki da
Ibrahim da Emzee babu maraba"
Hannuwanta ta ware kawai ta shige jikinsa ta kankame shi. Yau dinnan ya gama mata
komai da performance dinsu. Hawaye take yi na tsabar son Awwab da kuma rashin son
bata masa rai "Hammana kada kayi fushi dani"
"Kin wuce haka a wurina baby. Bazanyi fushi ba amma sai an rama min."
Kai ta gyada da murmushinta "na yarda"
"Ranar da aka kawoki fa..." yace yana shafa fuskarta.
"Na amince" ta bashi amsa a dake.
"Baby kada fa ki chanja shawara ba kyaleki zanyi ba" yace da warning voice yana
dariya.
Juya masa idanu ta shiga yi tana jijjiga kai "meye a cikin tausa da ba zan iya ba
Chèri? Allah Ya kaimu"
Karamin yatsansa ya dago ya hada da nata "pinky swear?" yace yadda yara suke yi.
"Sealed and stamped" ta kuma bashi amsa da kwarin gwiwa duk da har kasan zuciyarta
tasan kawai fada take yi. Tun yanzu ma kunyarsa take ji ga faduwar gaba idan su na
su kadai bare kuma ace daga ita sai shi a gida.
"Yanzu zan tafi da kwarina..." sake kissing dinta yayi ya rakata har cikin falon da
babu kowa sannan ya juya ya tafi yana mitar wannan kwanaki da ake ta cinye masa na
kasancewa da matarsa. Zancen zuci yake yi yana tuki "Allah Ya kaimu dai ki haifa
min baby girl. Idan ta girma ana daura aure zan bawa mijinta su tafi don ni dai kam
wannan tsarin bazan yarda a sake yiwa kowa ba".
**********
Yamutsa fuska Zayyan ya kula Mairama tana yi tun da suka dawo tayi wanka ta gama
shirin bacci ta kasa kwanciya. Kwalbar turaren hannunsa ya ajiye ya dawo kusa da
ita akan wata kujerar cushion mai laushi sosai guda daya da take dakin.
"Fillo yaya ne?"
"Warin panadol dakin nan yake yi kuma na duba ban ga inda magani ya zube ba"
"Panadol kuma? Bana jin komai sai kamshin turaren wutar da kika saka"
Hancinta ta matse ta hanyar sake yamutsa fuska "yanzu baka jin kamar panadol ya
rube?"
Zayyan bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba harda buga kafa "rubabban panadol
ne dai kin tabbata ba nine na tube din ba ko?"
"Eh tayani dubawa ba wasa nake ba" ta tashi tana kokarin dukawa ya dawo da ita kusa
dashi.
"Nace miki na tureki kinki yarda. Tunda kika kin taba jin panadol ya rube?"
Kunya taji tana murmushi "wurin dinner dinma fa haka ya rinka yi"
"Fillo wata nawa ne ki dena ja min rai" yace yana kallon saitin cikinta.
Wata irin kunya ta rufeta wai ita ke da ciki. Dazu da safe Mama ta kaita asibitin
an tabbatar mata wata biyu ne. Da yatsu tayi masa alama Zayyan harda hawaye "kinga
ikon Allah da yadda Yake gwada karfin mulkinSa ga wanda Yaso a lokacin da Yaso. Ina
sonki Mairama Allah Yayi miki albarka Yasa ki zama matata har aljanna"
"Amin Sojana...ba ka jiye min haihuwq ga 'ya a gidan miji"
"Itama ta haihu nan da wata tara nake fata. Arziki ne ni dai nagode"
"Nima ai nagode"
"To muje mu kwana kafin na fara jin rubewar panadol din nima" yaja hannunta suka
kwanta kamar kodayaushe aka bude sabon babin tsohowar soyayyar da kullum suke aikin
sabunta ta.
Da safe da yawa cikin bakin sun tafi musamman na Kano. Na Sakkwato kuwa sun jira su
koma tare the next day. Zahra da Fauziyya ko keyarsa babu sai a ranar tafiyar.
Awwab yazo yayiwa Radhiya sallama tare da saka mata kudi a jakarta ko za ta bukaci
wani abu saboda shi da su Mami Katsina zasu wuce. Ummi, Mama da Tante ne zasu
Sakkwaton.
Can ma gagarumin taro aka hadawa 'yar Zayyan don sunyi bajinta sosai 'yan uwansa.
Anyi komai an gama lafiya. A ranar 'yan daukar amarya suka zo da ga Katsina da
akwatunan lefensu guda takwas da kit. Awwab yayi kokari matuka abu kadan ne ba shi
ya saka ba.
Duk wannan bidiri da akeyi Ghazalatu suna can wani karamin hotel da Nura yana
angwancewa. Tayi kuka tayi bala'in ta koma rarrashi duk ya toshe kunmuwansa. Cewa
yayi sai ranar da za'a kai amarya Katsina zasu koma lokacin an gama share gidansu
domin can zasu wuce. Tana kuka ta kira Mummy Gambo wadda tace mata umarnin Alh Baba
ne tayi hakuri ta zauna gidan mijinta da kansa yayi alkawarin idan Nura ya sake
tabata zai dauki mummunan mataki a kansa. Ba sa son da kuruciyarta a fara kirga
mata aure. Ba haka taso ba amma dolenta ta hakura ko don gudun kada jiki yayi
tsami.
Cikin wata hadaddiyar laffaya Mama ta shirya Radhiya aka fara shirin tafiya Katsina
da matar Awwab. Ummi dai ba binsu zata yi ba daga nan Zayyan zai zo su wuce Nijar.
Har yanzu bata bari kowa ya gane tana da ciki. Dauriya take sosai shiyasa Mama tayi
ta kawo mata abin da zai sassauta mata tashin zuciya a boye. An fito tafiya da
amarya idanunta a bushe saboda har yanzu ita fa bata ganin an kaita kenan tunda
tasan zasu je Nijar sannan a koma Abuja. Abinda ta sakawa ranta kawai wani bikin
zasu je a Katsina. An fito tafiya bakwai da mintuna Jume da Gwaggo Ladi sunyi mata
nasiha zasu tafi da iyayenta mata yayyen Zayyan da matan su Badaru ga wasu cikin
cousins dinta sai su Yadikko masu komawa Sumaila yayin da Hajjo da wasu yau din
zasu tafi Katsina.
Takalmin Radhiya me madauri ne ta durkusa tana daurawa wata tsohuwa tayi zaton kuka
take yi tace " 'yar nan sai hakuri ki dena kuka haka kowace mace haka aka yi mata
kema da sannu zaki saba"
Dagowa Radhiya tayi innocently tace "Iya ba kuka nake ba takalmina nake daurawa"
(wadda ta tsargu da ita nake.....)
Ummi na gefensu tsabar kunyar da taji bata san lokacin da ta durma mata wani uban
dundu ba sai da ta kuma durkusawa cikin fada tace "kuka kike mana, ba na hanaki
karya ba shine zaki kalli idanun Iya kice mata ba kuka kike ba"
Iya wadda ta kasance 'yar uwar Mal. Muhammadu ta kalli idanun Radhiya sosai "ai
kuwa kamar ba kukan take ba Mairama"
"Kuka nake mana Iya baki gani bane kawai...ni ku rikeni na fasa tafiya" Radhiya ta
soma yi musu hargowa ana rikota tana komawa ta rungume Ummi. Tsabar takaici ta rasa
me zata yiwa yarinyar nan ta huce. Wannan runguma a bainan nasi salon ace basu da
kunya.
Fada Ummi ta soma yi mata matar Rayyanu tace "haba Mairama ki rike yarinyar nan
taji dumin uwa mana sai ki hauta da fada kamar baki san ciwon rabuwa da gida ba"
Mama ta gimtse dariya tace "kinsan wani idan abu yayi masa yawa kukan ma kasawa
yake...tun da muka tashi asuba take sharar kwalla"
Ummi kamar ta hadiyi zuciya da Jume ta fito ga mutane suna ta cewa wai sun basu
tausayi wannan uwa da 'ya akwai shakuwa sosai a tsakaninsu. Duk yadda take jin
kunyar 'yar fari kuma a gidan surukai Sakkwatawan nan babu ruwansu suke cewa ta
shiga daki ta kwantarwa da 'yarta hankali.
Suna shiga Ummi ta juyo a fusace Radhiya ta kwashe da dariya sannan ta nutsu tace
"Ummi Allah Ya kara miki lafiya wallahi bani da kamarki duk duniya"
Hawaye ne ya saukowa Ummi ba shiri ta kai mata rankwashi ta goce. Da kanta ta
rungumo Radhiyan tana murmushi zuciyarta na sake cika da farinciki "Allah Yayi miki
albarka Ya baku zaman lafiya. Banda kiriniya kinga dai aure ba abin wasa bane kuma
kin girma"
Tana makale a jikin mahaifiyarta take amsa mata. Gudun kada a leko ta tasata a gaba
suka fito aka sakata a mota. Canter guda aka cika shake sosai da kayan gara gari
guda kamar masu shirin bude kanti.
Gidan Alh Baba aka kaita inda duka kakanin da matayensu suke zaune suna jiransu.
Yau dai wanda baisan Alheran Radhiyan Awwab ba ya ganewa idanunsa. Wasu ma sai
tausayin Awwab din ya kamasu yadda Alh Baba ya hana wannan auren da farko.
Zukekiyar bafillatana mai jinin buzaye irin wannan har ita ake yiwa yanga. Motocin
da suka kawota dama akwai na sojojin da suka biyosu domin kariya kowa yasan ta wuce
ajin raini ita da danginta. Yarinya an kawota da gararta abin kwatance sai son
barka.
Zahra ce ta shigar da ita falon kanta a rufe ba ta iya dago kai ba amma jikinta ya
bata Awwab yana ciki saboda wani fitinannen kamshin turaren da yake amfani dashi
yanzu. A gefen kakarsu Maman Biyu aka zaunar da ita Alh Baba yace "dawo kusa da
mijinki jikata"
A sanyaye ta tashi Zahra ta ja ta kusa dashi ta zauna a darare ita kuma ta fita.
Nasiha tsofaffin nan suka rinka yi musu baka jin komai sai sheshshekar kukan
Radhiya da gaske fadan yana shigarta. Da yake ta baza laffayar a kasan inda ta
zauna ta karkashi Awwab ya zura hannu ya kamo nata sai da ta zabura amma yaki saki
yana matsawa a hankali. Kukan nata ne ya tsagaita Baba Karami yace a wuce da ita
gida su samu su huta.
Uwargidan Alh Baba ce ta fito da ita aka damkata hannun iyaye mata suka wuce gidan
Daddy. Dangi ne ko ta ina ga su Hajjo ma sun iso. Ana neman uwar amarya Mama ta
fito ta rike hannun Radhiya har dakin Mami suna tare da 'yan uwanta ana hira kamar
wani abu bai hadasu ba.
Bayan gaishe gaishe da tambayar hanya Mama ta kama hannuwan Radhiya dake zaune a
kasa har yanzu bata bar kuka ba jikinta yayi sanyi ta dora a tafin hannun Mami na
dama sannan ta kawo na hagun ta dora a kai ya zama na Radhiya ke tsakiya.
Muryarta babu alamun wasa tace "Mami ga amanar 'yata...."
Mami ta harareta "meye haka Zainab, Radhiya 'yata ce kada kiyi min haka"
Girgiza kai Mama tayi harda 'yar kwallarta "Mami ki barni nima na aurar da 'ya
yadda kowa yake yi. Alheran dai a tafukan hannunki ta fado duniya kece kika karbi
haihuwarta. Ko da aure ko babu ke uwa ce ga tsatson Mairama da Zayyan. A madadin
babansu Hadir ina mai baki amanarta. Kinsan halinta babu wani abu sabo a wurinki.
Idan tayi kuskure kinfi kowa sanin ta yadda zaki tsawatar ki sakata a hanya. Na
baki amana ne ba don bazaki iya ba sai don taji da kunnenta cewa yanzu da da ba
daya bane. Da can 'yarki ce yanzu kuwa jininki ta koma. Ke kuma Radhiya daga yau
kin girma saboda haka duk abinda na fada miki a gida ki fara aiki dashi domin ibada
kika zo yi"
Zantukan Mama Zainab ya taba Radhiya da Mami suka rungume juna suna kuka. Yadda
suka yi ya taba matan dake dakin sosai suna kara girmama wannan kyakkyawan zumunci
na mutanen nan.
Mami da kanta ta kama kai Radhiya dakin da Fauziyya suke tana fita kuwa suka fara
zolayarta sai dai babu bakin ramawa an kashe mata jiki gabadaya. Bayan sunyi sallar
la'asar anci abinci Mama ta hada 'yan uwanta da wasu kannen Mairama suka fito suka
zaga kofar baya bangaren Awwab da yake jikin gidan amma kofarsa daga barin hagu ake
shiga. Da can dan karamin falo ne da daki sai toilet. Amma ana gab da daura auren
Daddy ya fadada masa wurin aka kara girman falon sannan akayi kitchen. Sun saba
kowa a garinsu yake zuwa sallah. To haka yake son ta kasance ga tilon dan nasa. Sai
kuma ya ga gidan nasu babu yara Zayyana kanta ba dadewa za'a aurar da ita ya zama
daga shi sai Mami. Shine yayi wannan gyaran yada idan anzo Awwab ba sai ya nemi
wurin ajiye iyali ba ko kuma su rinka rabe rabe a cikin gidan. Lokacin da ya fadawa
Baba Hadir yayi wannan gyaran alfarma Hadir din ya roke shi akan cewa kada ya bari
Zayyan ya sani haka kuma matansu sun boyewa Mairama. Komai da ya kamata a saka a
cikin gidan nan Baba Hadir da Mama Zainab ne suka yiwa 'yar tasu. Daki daya ne aka
saka mata wani makeken royal bed mai kyau. Ba'a cika dakin da tarkace ba bayan
kayan gadon sai wani irin show glass na gani da fada wanda yasha turarukan wuta na
asalin da humra da wasu irin turaruka masu maiko.