Advertisements
Chapter 98 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   98 / 99

291K to 294K   out of 295.8K words

sa ta
yiwa yanka madaidaita ta tafasa da kayan kamshi su, citta, tafarnuwa, black pepper
da albasa. Ruwan naman bayan ta tafasa shinkafa ta wanke ta juye shi ta karasa
dafata da shi. Butter ta zuba a non-stick pan mai zurfi ta soya sausage da lawashi
wanda ta yanka kananu juye shinkafar a kai batare da ta saka curry ba ta soyata.
Naman shima soya shi tayi sannan ta hada attaruhu da albasa wadatacciya tayi
grating ta soyasu da maggi da

curry sannan ta hade da soyayyan naman. Sai kuma coleslaw da kunun aya. Gidan ya
sha turaren wuta ga girkin amarya da sanyin AC Ba ta je airport din ba ta zauna
kwalliya.


Motar na tsayawa a gurguje taje ya gaishe da iyayensa da su Baba Hadir ya tashi
Mama tana zolayarsa bai iya cewa komai ba sai dariya ya taho gida. Yana kama handle
din kofar kafin ya murda ta riga shi. Kallon kallo su ka tsaya yiwa juna shi ya
kara yi mata kyau da cika. Awwab na yi mata kallon fuskarta ta fada duk da kyaun da
tayi mai fizgarsa. Rungumeta yayi tun a bakin kofa ya saki jakarsa yana kissing
dinta cike da kewa. A hannu ya shige daki da ita sai da ta ga da gaske yake ta
dakatar dashi saboda jininta da bai dauke ba. Bai damu ba ya rungumeta kawai a
jikinsa yana fada mata yadda yayi kewarta.


"Tashi kayi wanka kaci abinci Hammana" ta ja hancinsa.


Wasa yake da gashinta ya dago ta su ka zauna "babu ko daya da zanyi sai kin fada
min abinda ake boye min baby. Me ya sameki 4 days ago?"


Babu hanyar guduwa ta sunkuyar da kai ta ce "Hammana miscarriage nayi"


Jikinsa a take ya soma rawa ya janyota ya kankame "Schatzi dama kina da ciki?"


Kuka ta saka a hankali "Ban tabbatar ba shine na siyo abin PT idan ka dawo mu duba"


Ya dago fuskarta yana kallo "was it painful?"


Ta gyada kai ya sake rungumeta yana bata hakuri da rashinsa a kusa lokaci irin
wannan. Sabuwar jinya aka koma yi kamar yau abin ya faru ya hanata yin komai. Iya
kwana ukun da suka yi kulawa yake bata sosai. Ranar juma'a da daddare su ka tashi
zuwa France inda ya cinye hutunsa ita kuma tana zuwa makatanta amma da ta dawo sai
yawo tare da su Arifa ko ita kadai da Awwab. Ranar da zai tafi kuka tayi da kyar
Tante ta shawo kanta.


**********


A hankali kwanaki ke tafiya cikin Ummi ya shiga watan haihuwa ga jarabawarsu ta
karshe da suke yi. Lokacin Fauziyya ta kusa arba'in din Sahla jaririyarta. Zahra
kuma cikinta yana wata biyar.
Cikin ikon Allah sai bayan kwana takwas da gamawa ta tashi da nakuda. Allah Ya
taimaketa yadda ta sha wahalar cikin sai haihuwar ta zo mata cikin sauki saboda ko
minti talatin basuyi ba da zuwa asibiti aka fito musu da sankacecen saurayi kamar
Radhiya tayi kakinsa har dimple din gefe dayan.


Farincikin Zayyan Tureta a wannan rana ba zai fadu ba. Mairama ta sha addu'a sosai
a wurinsa sai da tayi kuka. Ya kira Malamijo yace a yiwa shanu uku kudi a garkensa
a yanka ayiwa mabukata sadaka. Mami ce ta yi mata wanka saboda a ganinta duk girman
Mairama bata da wani cikakken experience game da haihuwa. Mama kuma ta sille jariri
aka yi masa hoto ana turawa yayyensa da ke nesa. Radhiya ji tayi kamar tayi
tsuntsuwa ta iso gida wurin baby da Ummi amma tana da sauran jarabawa daya sati mai
zuwa. Ita da Tante da Arifah mai tsohon ciki suke zuwa siyayyar kayan baby saboda
su Mammee sun ce ta hado kayan barka na gani da fada. Akwati biyar tayi manya manya
uku na baby biyu na maijego.


Emzee da Ibrahim su ma makaranta ta sarke musu wuya ana ta jarabawa. Su Fauziyya ke
rokon alfarmar kada ayi suna babu su Ummi ta ce babu taron da zata yi. Mama da Mami
su ka ce sai anyi. A zahiri Ummi bata son yi saboda rashin Radhiya da Emzee amma
kunya ba zata bari ta fada ba. Ita dai burinta ace 'ya'yan da suka sha gwagwarmaya
tare dasu za'ayi komai.a lokacin da Allah SWT Ya dube su. Shima uban gayyar mijin
nata kasa fada masa tayi sai da hillata ya ganota.


"Su Fillo wasa wasa kina da son 'ya'ya fa" yace yana dora jaririn a kafadarsa.


Tayi dariya "Duk abuna na kai dan mutan Tureta ne?"


"Ko kusa a bayana kike saboda haka ki rinka komawa gefe idan suna kusa ba ta ke
nake yi ba"


"Naji amma ka bani jaririna don kasan shi dai bana jin kunyarsa kamar sauran"


Zama yayi kusa da ita ya ce "na rasa sunan da zan saka masa Fillo. Ga Major, Hadir
da Baban Arifah cikinsu waye baiyi min halacci ba? Kinga ko da Hadir yake mai
lalura nayi imanin da yana da hali kamarsu Mairama zai iya sadaukar da komai nasa
domin iyalina."


"Na sani Sojana ko dai na haifo wasu ne a cike sunayen" ta ce tana dariya.


Ranar kwana hudu kenan da haihuwa nauyin 'yan uwan nasa rabin jiki yana damunsa ya
rasa wa zaiyiwa takwara a cikinsu.


Washegari da aka kawo Mami tare da Daddy da Baba Hadir su ka zo. Daddy ya mika
hannu ya karbi kyakyawan jaririn daga hannun Zayyan ya mikawa Hadir.


"Ni na yiwa Alheran yau kuma kaine da danka ka zaba masa suna don na rasa me yake
damun abokinka sai wasa yake mana da hankali"
Murmushi Baba Hadir yayi ya duka ya yiwa yaron addu'a sannan ya dago kai yace
"Allah Ya raya mana NASURULLAH"


Daddy yayi murmushi ya karbi yaron ya sumbace shi kumatun hagu da dama "hakika
Allah mai kyauta da kari cikin nasarar da Ya bamu ne muka wayi gari mu ka ga wannan
rana ace Zayyan ya dawo garemu har Allah Ya azurta shi da sake samun karuwa."


Kwalla ce ta taru a gefen idon Zayyan ya sa hannu yana kade ta Daddy yace "me nake
gani haka? Are you still a Lady?"


Baba Hadir da Zayyan sai dariya yana cewa "wallahi namiji ne ranka ya dade"


Excellency Nasiruddeen Aliyu wanda ya sake samun kujerar gwamnan Plateau a daren
ranar ya sauka a Abuja ganin wannan dan baiwa da za'a iya cewa alkawarin Allah Ya
cika domin haihuwarsa baiwa ce. Sunansa da na Nasrullah daya ne duka daga nasara
sai dai bambanci kadan shiyasa yace shi aka karrama aka yiwa takwara saboda haka
gagarumar kyauta yayi masa wadda ta tsorata iyayensa sai dai yace babu abinda zai
yiwa jinin Zayyan ya fadi domin ko me ya zama a rayuwa sanadiyar zubar jini da
hawayen Tureta ne.


Kamar lokacin DK dan gidan Zayyan don babu abinda ya kware a fada irin Daada shima
Nasrullah an dage taron sunansa sai yayyensa sun dawo nan da sati biyu ake sa ran
kowa yana gida banda Zahra.


Tante ta tafi Nijar da kwana biyu Radhiya ta koma gidan Yousuf jiran Awwab yazo
zasu tafi Abuja. Kafin.ya iso yayi booking hotel online daga airport ya gudu da
matarsa sai washegari su ka hadu dasu Arifah a wurin convocation din Radhiyan.
Kyaututtukan da ta samu ba kadan ba musamman saboda shirin Military Voice. An yaba
mata sosai basu bar makarantar ba sai da a gaban shugaban makarantar tasu da Awwab
ma'aikatan Aljazeera su ka kawo contract na shekara hudu wanda su ka bata tayi
Military Voice Africa (MVA). Da amincewarta kuma anyi alkawarin acknowledging dinta
a matsayin wadda ta samar da shirin suka nemi izinin yin Military Voice Asia da
Europe. Kudin da zasu biyata ba na wasa bane bukatarsu duka kasashen Africa guda 53
taje ta gana da sojojinsu da matansu su kuma zasu ware lokaci domin sanya shirin
sau daya a sati. Yadda za'a rinka dauka da gabatarwa duk yana cikin contract din.
Awwab baiyi gaban kansa ba ya kira Daddy da Daada suka bashi goyon baya sannan ya
yarda ta amince aka saka sunansa a matsayin wakilinta.


Kwana biyu su ka kara sai gida Nigeria da kwalinta na degree wanda ta fito da
sakamako mai kyau. Iyaye da 'yan uwa an tayata murna. Da gudu ta shiga gida sai da
ta dauki Nasrullah hankalinta ya kwanta. Kasa ta sauko dashi wurin Awwab ya
rungumeta da babyn yana cewa Allah Ya nuna masa ranar da za ta haifa musu nasu.


**********


Shirye shiryen zuwa P.O.P din Emzee suke yi Daada yace Ummi babu inda zata saboda
Nasrullah baiyi kwari ba. Sai da ta ajiye kunya ta dangana da hadashi da Daddy ya
barta taje.
As expected Second Lieutenant Muhammad Zayyan Tureta ya fita da sakamako mafi kyau
a wannan shekarar saboda kokari da kwazonsa musamman akan abinda ya shafi training
dinsu. Ya sami lambar yabo kala kala iyayensa basu da abin cewa sai godiya ga
Allah. A wannan rana Malamijo sai da yazo halartar taron sai dai ganin sojoji a
kowace kusurwa rike da bindiga ya kada masa hanji. Tare su ka dunguma zuwa Abuja
yau dai gashi a muhallin Mairama Daso. Yana rungume da karamin jikansa yana mai
mika godiya ga Allah da Ya tsawaita kwanakinsa ya ga haduwar kan 'ya'yansa. Gida
MashaAllah ya cika da 'yan uwa daga rugar Barkindo, Sakkwato, Nijar da Sumaila.


Sunan da ba'ayi ba aka hade da murnar kammala karatun Radhiya, Emzee, uwar gayya
Mairama da bakon duniya Nasrullah. Major General Zayyan Tureta sai da yayi kukan
farinciki a daki kafin ya sauko faefajiyar gidan inda ake taron. Yau shine Allah Ya
yiwa arzikin ganin wannan rana wadda da sai dai ayi babu shi. Kyauttuka kam an sha
su.


Ibrahim kamar ya lashe Zayyana don so shi kuwa Emzee da Rahima tsakaninsu sai satar
kallon juna. Ta gama makaranta abinta tana jiran a fara karatu a school of nursing
da ta sami gurbi. Emzee ya mamayeta yadda Awwab yace duk motsinta yana wurin amma
babu yiwa juna magana. Ita ta sakawa ranta ta hakura dashi ne duk da tasan cewa
yaudar zuciyarta take yi. Kullum sai ta jira text dinsa wanda babu kalmar soyayya
sai nuna tarin kulawa.


Sai dare su Radhiya suka koma gida Awwab ya jikata da salon soyayyarsa. Washegari
ya damka mata mukullin hadaddiyar motar da ya saya mata a matsayin graduation gift.


*********

SALLAMAR BANKWANA


Wata hudu bayan gama karatun Radhiya suka je gidan Daada da Awwab gaishesu. Emzee
ya tafi wani training a Warri yanzu mukaminsa ya koma Lieutenant. A falo su ka yada
zango tana yiwa Nasrullah uban 'yan kyuya wasa ya hade rai abinsa yana neman Ummi
da idanu ta ce,


"Indai nice za ka zo ka sameni ne har gida kuma ba bari zanyi ka shigo ba"


"Ba dole ya rinka gudunki ba kina zare masa idanu" cewar Awwab ya karbe shi.


Kusa da Daada ta koma suna hira a hankali ta soma hade fuska tana sansana jikin
kujera da su labule tana dagawa.


"Lafiya dai kike min dage dage?" Cewar Ummi.


Sake baza hanci tayi da kyau tace "Ummi warin magani ko dai maganin Nasr ne ya zube
a wani wuri?"


Daada na jin haka ya ajiye jaridar hannunsa yana kallonta "maganin kamar panadol
yake Alheran?"


Ta tafa hannu "eh wallahi Daada ka canka..."


Ummi ya kalla ya soma dariya yana cewa "kina ji kamar ma ya rube ne?"


Awwab ne ya bashi amsa "jiya sai da tasa na na juya gado da shirin falo gabadaya
muna neman maganin da ya rube. Kuma ni bana jin komai wallahi ita kadai take ji"


Dariya sosai Daada yake yi Ummi ta bar wurin da sauri don kunya tana ji yana cewa
"wannan warin bazaka taba jinsa ba Awwab. Ke kuma sai hakuri yanzu kika fara ji
amma ku je asibiti kiyi musu complain. Ina jin likita kika hadiya"


Ta zaro ido "likita kuma Daada?"


Ummi na jinsu ta dawo da sauri saboda ba karamin aikin Zayyan bane sakin baki a
gaban suruki shiyasa tace yazo wayarsa na ringing. Ita kadai ta dawo daga baya suka
yi sallama Awwab ya wuce asibiti da ita duk da tana cewa babu inda yake maga ciwo
sai warin maganin. Gwajin ciki suka yi mata tana dashi har na sati tara.


Murna a wurin Awwab ba sai an fada ba. Auren nasu shekara guda da watanni kadan ga
Arifah tana nan da Nasrin dinta wadda sunan Tante taci aka juya mata shi.


Tare suke kula da cikin yana ta girma har yayi wata bakwai. Laulayi gareta kamar
Ummi shiyasa idan zai koma aiki sai dai Zayyana ta dawo gidan ko Rahima.


Ranar wata asabar tafiya ta kama Daada zuwa Asaba aiki shi da wasu a karkashin
jagorancinsa. Convoy din motoci biyar suka yi ciki Emzee da yake ta fushin kasa
samun kan Rahima yace zai raka shi. Basu taba tafiya daga shi sai dan nasa ba
saboda haka wannan ta basu damar yin hira sosai irin ta uba da da. Zayyan yasan
komai game da lamarin Rahima ya rinka bashi shawarar yadda zaiyi ya shawo kanta su
daidaita.


Sun wuce wani kauye da kadan su ka kula motoci da yawa suna dawowa a guje wasu ma
da ribas suke tafiya. Nan da nan yaransa su ka fara kiransa suna tambayarsa ko su
ma su juya.


"Are you crazy?" Ya dakawa mai tambayar tsawa "civilians su gudu muma mu gudu to
waye zai kai taimako idan ana bukararsa"


Kai tsaye ya bada umarnanin kada a tsaya. Kowa yana sanye da kayan sojoji tunda
official tafiya ce banda Emzee dan rakiya. Suna karasowa motoci suka gani guda
shida da 'yan fashi su ka kama sun kashe titin ta daya bangaren babu mai karasowa
ga harbi suna yi kamar hauka sun kashe drebobi uku masu kokarin guduwa. Ganin
motocin sojoji ga su suna dirowa da shirinsu yasa ogansu kiran wadansu ashe mugun
yawa garesu.
Tashin hankali ne muraran mutanen da suka biyo hanyar suka tsinci kawunansu a ciki.
Baka jin komai sai tashin harsashi da kukan mutane. Abin ya wuce zatonsu dan
karamin kauyen da yake gefen wurin shima sun yiwa mutanensa mummunar barna saboda
rashin basu mafaka.


Jikin Emzee a take ya fara rawa yau gashi a filin daga na gaske. Major General
Zayyan tuni ya fito daga mota a sukwane babu wani tsoro ko fargaba yana bada
umarnin duk wanda su ka kama zaiyi gardama su harbe shi a inda zai raunata shi
sannan su tabbatar anyi saving mutanen wurin.


Bindiga kirar AK47 ya dauko ya damki hannun Emzee ya bashi cikin rawar hannu ya
saketa a kasa ga sautin harbi da kukan mata daga wannan kauye ya yawaita.


Dauko bindigar Zayyan yayi ya ratayata a hannunsa kamar yadda ya rataya wadda zaiyi
amfani da ita ya rike fuskar Emzee a tafukan hannunsa.


"MUHAMMAD" ya kira shi da murya ta umarni babu wasa ko rangwame saboda dan cikinsa
ne "this is why you became a soldier Lieutenant. You live and die for your country.
Wancan kukan da akeyi da firgici aikinka ne ka tsayar dashi ka tseratar da mutanen
nan"


Jiki na rawa ya gyada kai yana jin kunnuwansa na neman toshewa saboda bala'i.


Bindigar Zayyan ya sake mika masa yana jin wani karfin gwiwa su ka fara hawa dan
tudun da zai karasa dasu kauyen Zayyan yana ta bada umarnin a kwashe tseratar da
mutanen da aka kamawa motoci su bar wurin. Saboda wutar da aka bude 'yan fashin da
yawansu sun buya ne a bayan gidaje suna harbin kan mai uwa da wabi.


Sai da suka gama hawa tare da wasu sojojin Zayyan ya rike hannun Emzee idanunsa
suka dan kada na dakika kadan "ka taimaka min na maidawa Mairama danta cikin
aminci...Allah Ya tsare min kai"


Bai jira komai ba ya kusa kai tsakanin katangar wani gida da na kusa dashi inda ya
fi jin harbin ya soma sakarwa 'yan fashin nan harsashi. Emzee tuni ya nemi tsoro ya
rasa sai aikin neman lada ya bautawa kasarsa. Harbi suke yi ba kakkautawa sai da
suka tabbatar sun kora 'yan fashin suka soma dauko mutanen da suka jikkata a wurin
suna dawo dasu bakin titi bayan kiran waya domin a kawo musu agaji.


Duk sunyi futu futu dasu a tunaninsu sun gama Emzee ya jiyo kukan mace daga wani
gida. Kutsa kai yayi ya hadu da mata mai tsohon ciki a durkushe tana murkususu.
Fita yayi da sauri ya kira Zayyan dake rike da wani tsoho. Wani sojan ne ya karasa
da tsohon shi kuma ya bi bayan Emzee. Suna shiga gidan aka rufe kofa 'yan fashin
nan su hudu su ka sakawa matar bindiga sannan aka umarci Zayyan ya fadawa yaransa
kowa ya bar wurin saboda tsaron rayukansu suka yi garkuwa da su.


Tsananin tashin hankali sun shige shi domin matar gidan tana cikin mawuyacin hali.
Zayyan bashi da zabi saboda rayuwar matar da dansa ya bada wannan umarni. Yaransa
sun so yin gardama sai yayi musu bayani cikin lauya zance wanda su kadai sojoji ke
ganewa akan cewa zasu iya hauro katangar gidan amma su bada lokaci.


Cikin wadanda suka sami tserewa nan da nan labari ya bazu cewa 'yan fashi sun tare
hanyar Asaba sunyi garkuwa da wasu sojoji. Yadda labari ke gudu a social media
kafin a farga Ibrahim da ke Kano ya sami labarin. Hankalinsa a tashe saboda dazun
nan suke chatting da Emzee sai ya ji shi shiru. Baba Hadir ya kira ya tambaya yace
baiji labari ba. Shi da Daddy su ka shiga neman layukan Zayyan da Emzee shiru.
Headquarter su ka je neman ba'asi amma aka so boye musu. Sau kuma ga 'yan jaridu da
gidajen tv zancen kenan dai akeyi. Daddy da Baba Hadir basu bar wurin ba har dare
sai da Baban Arifah ya zo sannan aka saki rahoto cewa lallai an sami distress call
daga hanyar Asaba sojoji na neman taimako an kama shugabansu Major Gen. Tureta da
dansa.


Kan kace meye wannan zance ya zaha lumgu da sakon Nigeria ga masu mu'amala da
social media ko sauraron labarai. Fadin tashin hankalin da Mairama ta shiga ma
bazai yiwu ba. Tayi kuka har hawaye ya kafe a idanunta. Ga da ga miji ko shekara
biyu baiyi da dawowa gareta ba. Duk wannan tashin hankalin kuma ga Radhiya can a
labour room da ga jin zancen nakudar dole ta kama ta. Ga Nasr yana wani irin kuka
na fitar hankali Mairama ta rasa inda zata tsoma ranta. Tana goye dashi suna
asibiti tare da su Mami saboda an hanata zama ita kadai tana fama da tunani.


A can kauyen da sojojin su ka haura gidan cikin dare basu ga kowa ba. Ashe karbe
abin maganar Zayyan suka yi aka fasa sannan su ka tafi dasu cikin dajin wai bazasu
barsu ba sai sun tabbatar cewa sun tsira. Ana wannan tafiya ga mai ciki ciwo yaci
karfinta a wahale tace haihuwa ce suna tsare a wani kango.


"Ku taimaka min" tace cikin tsananin azaba.


"Daada taimaka mata ni zan rinka lekawa in shammacesu mu gudu" Emzee yace ko kallon
matar baya son yi saboda tsoro.


Duk da rashin wadatar haske Zayyan harararsa yayi "kai ya kamata ka taimaka mata
saboda idonka yafi nawa gani girma ya kamani"


"Laahhh Daada tun ina yaro aka ce na gado ciwon idon Ummi" yace yana matsawa baya.


Zayyan bai ga abinda zai sa shi ganin haihuwa ba don gara a cigaba da fafatawa a
wurinsa.


Dakewa yayi yace "Lieutenant this is a command ka taimaka mata. Ba don chanjin
zamani ba nasan cewa haihuwa a lokacinmu da naku da bambamci da ni zanyi komai" ya
hadiyi yawu

98 / 99