Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
ya janyo mata kin amincewa ba sai zugar mahaifiyarta wadda itama Hussaina ce ta
ingizata kan cewa su hada Ghazalatu da nata dan Nura. Hussaina gani take ta sami
dama da zata dandali arzikin gidan Gambo yadda ya kamata. A zahiri Gambo da Mami
sun fi ta rufin asiri. Sai dai bata sani ba Mami a nata gidan kafin Major ya sami
lafiya har ya fara aiki guminta ake ci. Ita kawai gani take suna da kudi ne suke
son hada nasu 'ya'yan ita ko oho. Mummy Gambo an hau dokin zuciya ba bata lokaci ta
amince bayan sun bar gidan Mami a jiya.
"Saboda ance ya auri wadda mahaifinsa ya nema masa?" Baban Fawaz ya tambayeta.
"Ni dai kawai bana so ne yanzu"
Alh Baba yace "babu wanda zan tilasta a cikinku na gama wannan yayin. Tunda ba kya
so Allah Ya kawo miki naki rabon. Kai kuma ku gama magana da waccan ina bukatar
amsa da wuri" yana kaiwa nan yace duka ya sallamesu su tashi su tafi. Ghazalatu
kuka kamar ana yankar naman jikinta amma tasan halin Mummynta da masifa. Idan ta
kuskura ta komawa Awwab sai taji babu dadi. Hussaina duniya shar ta kira Nura tace
ya fara yakin neman soyayyar Ghazalatu ita ta gama nata aikin.
Awwab bai jira kowa ba ya fita ya bar gidan. Jin kansa yake kamar an zare masa wata
kaya da ta tokare shi. Lallai zuciya bata da kashi. Bai tantance zafin so ba sai
akan Alheran. Kinsa da Ghazalatu tayi ko kadan baiyi masa ciwo ba don tunda Mummy
taje gidansu sau biyu tana cin mutumcin mahaifiyarsa yasan ko ya aureta wani kaso
mai girma na kimarta ya riga ya sauka daga idanunsa.
Sallar magariba ya tsaya yi kafin ya shiga gidan. Shigarsa tayi daidai da isowarsu
Mami a motar Daddy. Zahra ce ta tuku su Fauziyya na gaba su Mami na baya. Idan ka
ga Zahra fuskarta tamkar wadda aka baiwa kujerar Makka. Murmushi ne yaki tafiya
kamar an zana mata shi har tsokanarta Daddy yayi yace shima sai ta nemi amincewarsa
sannan zai kira Imam Abdulwahab mahaifin Raji.
Kunya taji ta ruga cikin gidan kai tsaye ta tafi dakin Mami. Ummi ta gani akan
sallaya ta fada jikinta tana ta dariya.
"Zahra me muka samu irin wannan murna haka"
"Ummi Alh Baba ya amince"
"Da me?" Mairama ta tambayeta tana tayata murna tun kafin taji.
Sallamar Mami yasa ta kasa cewa komai ta tashi ta koma nasu dakin da tsalle. Sai da
Mami ta idar da sallah ta fada mata yadda al'amura suka juya. Ummi bata ji dadin
fasawar da Ghazalatu tayi ba kuma ga dukkan alamu Mami da 'yan uwanta basu shirya
ba. Indai haka ne kuwa to babu makawa Radhiya ma bazata auri Awwab ba. Meye ribarsu
ayi auren da ya taba zumuncin iyaye.
Fauziyya da Zahra ma sallah suka shiga yi suka sami Radhiya ta dukunkune kanta ta
cure wuri guda tana baccin wahala. Tayi kuka ne har ya saka mata ciwon kai shine
bacci ya dauketa. Zayyana ta fito daga bandaki ta yayyenta kowacce da murmushi a
fuskarta. Zahra ta rungumeta tana dariya itama tana tayata ta tabbata abinda yasa
su kuka dazu ya wuce. Ihunsa ya tayar da Radhiya da kyar ta iya bude ido sun
kumbura tayi musu sannu da zuwa.
Fauziyya ta tuna cewa dazu maganganun su Mummy su ma daga dakin Awwab sun ji bare
kuma ita da suka bari a nasu dakin. Sai taji tausayinta ya kamata "kinyi sallah
kuwa ko sai nazo nayi miki balotelli?"
Murmushi tayi kanta kamar ya tsage ta daure "da almakashina a jaka"
Dariya suka yi su duka yanayin dakin yana chanjawa daga shiru shiru zuwa na 'yan
mata wadanda ke tsaka da jindadi. Da bin bango Radhiya ta je tayi alwala ciwon kai
yayi tsanani ga zazzabi. Bayan ta idar Zahra ta taba wuyanta ganin duka jikinta
yayi la'asar.
"Radhiya baki da lafiya kika zauna shiru a daki. Bari na karbo miki magani"
Da saurinta ta fita taje dakin Mami tana tambayar panadol. Ummi sai da taji babu
dadi tasan halin Radhiya da saka abu a rai. Karshenta kuka ta rinka yi ya janyo
mata zazzabin da ciwon kai.
"Nemo min Awwab yazo ya kaita clinic dai. Ga gajiyar hanya kuma an taho ana tsaka
da biki duka babu wani hutu" Mami ta umarci Zahra tana bin bayanta zuwa dakin. Ummi
ko motsi bata yi ba tana addu'ar Allah Ya kawo sauki cikin lamarin saboda tsoro da
ya fara darsuwa a zuciyarta.
Hankalin Mami ba karamin tashi yayi ba da ta taba jikin Radhiya. Jiki yayi mugun
zafi fuskarta har wani ja take yi.
Awwab yana cikin shiryawa bayan yayi wanka Zahra taje ta fada masa sakon Mami. Ya
rigata fita daga dakin da sauri. Sallama ya tsaya yi a kofar nasu dakin amma da
kyar ya daure bai kutsa kai ya shiga ciki ba. Mami ta fito da Radhiya da ta tallafo
a jikinta.
"Me ya sameta haka Mami?" Awwab yace a raunane. Abinda zai kashe bakin Radhiya da
wannan kuzarin nata ba karami bane shima ya sani.
"Kuje mota bari na dauko mayafi. Zazzabi ne ina jin da ciwon kai"
A hankali ta rinka tafiya ganin Awwab ya sake tayar mata da hankali. Tana son shi
dole ta barshi idan ba tana son abinda Ummi take guje mata ya faru da ita ba. Wasu
hawaye ne suka zubo mata duk yadda taso daurewa ta kasa.
Sai da ya dan matso da kansa kusa da ita yana son rage mata damuwa ya tsokaneta
dacewa "come on Schatzi bana son shagwaba fa. Ke da zansa a yiwa allura kamar hudu
kuma kike min kuka"
Duk da ciwon haka ta harare shi yayi murmushi yana cewa "in dauke ki ne?"
A dole ta daga kafa tana jin kunyarsa. Da Mami suka je asibitin aka dubata likitan
yace banda zazzabi harda damuwa. Mami sai ta alakanta komai ga abinda ya faru a
gidan zuwan su Gambo. A take ta yanke shawarar sanar da Daddy yayiwa yaran magana
gobe idan sun amince wa juna ayi bikin kowa ya huta.
Da suka koma gida ta fita tana jiran Radhiya shiru Awwab ya hanata fitowa ta shige
ciki tana fadawa Ummi wai ta ga alama ciwon soyayya ne yake damunta. Ummi dai
dariyar yake tayi, neman abokin shawara take gashi Zainab bata nan.
A wajen Awwab ya tsare Radhiya da tambayoyin son jin damuwarta duk da shima yana
tunanin ko abin dazu ne "me kika sa a ranki har ya saka kiki fever?"
"Babu komai Hamma"
"Saboda zuwan Mummy ne dazu ko? Komai ya wuce kinji yanzu babu zancen Ghazalatu ma.
Ke kadai ce dani Schatzi kuma kin isheni don son da nake miki bana jin akwai wadda
zata sami rabinsa a wurina"
Kalaman sun mata dadi, da babu wannan matsalar da tafi kowa farinciki amma yanzu
bata da wani abin yi sama da murmushi ta fake da rashin lafiya. Shima da ya ga
shirun nata yayi yawa duk sai ya damu.
"I miss my Alheran, wannan mara lafiyar duk ta hanani ganinta. Kije ki kwanta and
please take care of yourself for Awwab"
"Hammana sai da safe" yaji tace da karamar murya tana tafiya sai bayanta kadai yake
iya gani.
Haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi zuciyarsa tana tabbatar masa da cewa akwai wani
babban al'amari a tattare da Alheran. Ko ma meye yayi niyar jira zuwa wayewar gari
taji karfin jikinta sai ta fada masa damuwarta.
Daddy kuwa a daren ya kira Imam Abdulwahab ya fada masa basu da masaniya akan cewa
akwai alaka tsakanin Raji da Zahra har aka yi mata miji. Imam yace basu yi sati da
sani ba shi da matarsa. Sai da suka ga shige da ficen asibitin nasa yayi yawa suka
matsa Munnirat kanwarsa ta sanar dasu. A lokacin hakuri kawai ya bashi tunda suna
da labarin aurenta ya kusa. Major yace to aure ya tashi saboda ta sanar bata son
angon nata. Yanzu haka ya kira ya sanar dashi ne cewa asabar mai zuwa ya kamata
daurin aurenta amma za'a basu dama idan sun amince ya turo Raji neman aurenta.
Bayerabe yasan darajar alkhairi kuma yana mutunta duk wanda ya karrama shi. Imam
Abdulwahab ya rinka kwararowa Major da iyalinsa addu'a kuma ya tabbatar masa in sha
Allah ranar asabar Zahra zata yi aure kamar yadda aka tsara tun farko. Da kansa
yaje dakin Raji da yake kwance yana jinyar zuciyarsa yayi masa kyakkyawan albishir.
A take ya wartsake sai gashi har asuba suna waya da Zahra wadda itama ta ware baka
ce ita ce take ta koke koke a kwanakin da suka gabata ba.
SABUWAR RAYUWAR
"To Alhamdulillah al'amura sun daidaita Alh Baba ya amince da auren Awwab da
Radhiya sannan duk da ba haka muka so ba Ghazalatu tace ta fasa. Allah Ya sani
Ummin Awwab ban so kuka san wannan matsalar ba ko kadan a madadin Gambo muna masu
baki hakuri akan cin zarafin da tayi muku jiya"
Ummi ta shiga girgiza kai "bamu hakurin tamkar kuna nuna akwai bambanci tsakaninmu
ne Daddy. Wallahi har raina banji haushi ba saboda haka magana ta wuce"
Mami tayi murmushin jindadi sannan Daddy ya kalli Awwab da duk motsin Radhiya akan
idonsa yake yana kokarin hada ido da ita amma taki dago kai. Gyaran murya yayi
Awwab din yayi saurin juyar da kansa daya gefen yana murmushi.
"Awwab ga kanwarka nan na baka amana ko bayan raina ban yarda ka rabu da ita ba.
Idan ta bata maka ko tayi ba daidai ba ka hukuntata amma ban yarda diyar Zayyan
tayi kuka saboda rashin adalcin gidan aure ba"
Farincikin da Awwab yake ji a wannan lokacin bazai misaltu ba. Dan taki kalilan ya
rage masa da mallakar abar kaunarsa. Yana sake dawowa ko sati daya ne hutun yake so
a daura aurensu.
"In sha Allahu bazan baku kunya ba"
"Radhiya baki ce komai ba" Daddy yace yana kallonta yana murmushi.
"Ai ka kashe bakin nata Daddy yau daya dai ga kunya ga sauran zazzabi 'yata bata da
ta cewa" inji Mami.
Hawayen zuci Radhiya take yi na samu da rashi da ya sameta a lokaci guda. A hankali
sautin kukanta ya fito fili. Yadda Awwab ya gigice sai ya baka tausayi ana ta
tambayarta ko jikin ne ta kasa magana. Ummi jikinta yayi sanyi amma ta san har ga
Allah hakan da tayi shine daidai. Tafi kowa sanin ciwon da ta kunsa saboda juya
mata baya da Salame tayi da rashin kyakkyawar alaka mai tattare da shakuwa da tayi
karanci a nasu gidan. Banda ma yanzu da abubuwa suke dan chanjawa amma a da kam
gidansu nafsi nafsi kawai akeyi kuma bata cire kanta a ciki ba saboda haka a ka
sabar musu.
"Radhiya ko bakya son auren ne?" Daddy yace bayan ya karar da duka tambayoyin da
yake jin zaiyi mata.
A razane Awwab ya kalle shi yace "Daddy?"
Ga mamakin su duka ukun Radhiya ta gyada kai. Daddy kansa sai da ya girgiza ba
Awwab da ya daga murya yace "karya take yi Daddy"
Daddy yace "Awwab ka nutsu ko ka fita"
Zama ya koma yayi amma babu nutsuwa bare kwanciyar hankali. Ita wadda akeyi dominta
kuka kawai take yi idanunta sunyi luhu luhu dama shi ta kwana tana yi.
"Muna sauraronki Radhiya"
"Daddy karatu nake son yi"
"Banda abinki Radhiya waye yace miki aure na hana karatu?" Mami ta tambayeta tana
dan sakin rai a zatonta wautar ce ta motsa.
"Ba nace miki zan samar miki admission a Abuja ba?" Awwab ya ce muryarsa tana rawa
yana kokarin danne bacin ransa.
"Daddy ni dai don Allah bana son auren nan gabadaya"
"Alheran!!!" Awwab ya daka mata tsawa ta kuwa sake tsorata ta fashe da wani kukan.
Gaban Daddy ya koma ya durkusa "don Allah kada ka saurareta wallahi karya take yi
Daddy. Ka aura min ita ko ranar asabar ne tare dasu Zahra please Daddy"
Ummi ma dai kukan take yi tana tausayawa yaran har ta fara jin ko dai tayi kuskure
ko matakin da ta dauka yayi tsanani da yawa.
"Ba kya son auren ko Radhiya?"
"Eh Daddy"
"To tashi ki tafi wurin 'yan uwanki na kashe maganar zan nemeki daga baya"
Baki Awwab ya saki yana karyata abinda kunnuwansa suka ji daga gareta da kuma
Daddy. Jiki a mace ta tashi zata fita yasha gabanta.
Da fada ya fara cewa "Ni zaki yiwa haka Alheran? Ba sai da na nemi izininki ba
kafin nazo na fadi cewa zan hadaki da Ghazalatu ba? Kuma yanzu ta fasa bazan hadaki
da wata ba I promise" ya kare da kwantar da murya.
Daddy sai da yayi masa tsawa ya fita a fusace jikinsa yana rawa. Dakinsa ya tafi
yana shiga sai ga hawaye. Ransa yaji ya kuma baci ya rasa me zaiyiwa kuka tun
girmansa sai mace. Macen ma Alheran da ya bawa dukkan soyayyarsa a cikin abinda
baifi wata daya ba amma tasa kafa ta ture saboda dalilin da bashi da muradin sani.
Itama tana fita dakinsu Zahra ta nufa tana nata kukan kamar ranta zai fita. Bata
hangowa kanta sauran farinciki tunda ta rasa Awwab.
Shiru falon yayi Ummi na goge hawaye Mami ta rasa me zata ce ma. Tashi Ummi tayi
zata fita taji muryar Daddy a sojansa.
"Mairama dawo ki zauna ki fada min dalilinki na raba yaran nan"
Gabanta ne ya fadi Mami ta bita da kallon mamaki. Soja ba abin rainawa bane.
Yanayinta kadai ya sa shi saurin fahimtar tana da hannu a abinda Radhiya tayi. Zama
tayi ta nuna musu babban kuskuren da yake tattare da batawa da 'yan uwansu saboda
yara.
"Yau da Allah Ya dauki raina bayan rasuwar babansu Karami ina mai tabbatar muku
dawowar nan da kuka yi zaku sami yaran nan cikin mafi munin yanayi ne saboda babu
wanda zai tsaya min ya kula dasu a gidanmu yadda ya dace. Gidan nawa mahaifin babu
shakuwa babu sabo tsakaninmu sama da mutum ashirin. Wadda muke tamkar 'yan biyu da
ita komai namu tare tazo ta juya min baya a dalilin son da ta yiwa Zayyan tun yana
raye. Tun kafin muyi aure ta dauki gaba dani har yau bata sake zani ba. Ba yau da
muke tare da 'ya'yanmu bace abin ji, gaba da bata da kadan Daddy ita ce abin
dubawa. Mami don Allah ki sasanta da 'yan uwanki kafin kiyi tunanin auren nan. Kada
ki manta a dalilinsa rigimar ta faro na tabbata ana yinsa sai abin yafi haka"
Sai yanzu Mami ta soma hawaye itama ta san cewa gaskiya Ummi ta fada. Duk da haka
Daddy yace "da sai kiyi mana bayani ba sai kin raba su ba. Ummi yau kinsa Awwab da
Radhiya kuka anya bazamu hukuntaki ba?" Ya kare da murmushin dattako.
"Nasan idan da ta amince babu abinda zai hanaka daura musu aure. Radhiya dai 'yarka
ce wani ma zaka iya bata bare Awwab. Alfarma daya nake nema ayi sulhu a daidaita
zumuncin da yake neman lalacewa. Idan haka ta faru ko gobe ne wallahi ayi musu
aure"
Tana kaiwa nan ta tashi ta bar falon. Mami tana kuka tacewa Daddy hakika Mairama
tayi zurfin tunani bata so kanta ba ta hakura da farincikin 'yarta dominsu. Sun
yabawa Zayyan a baya yau suna yabawa matar Zayyan saboda a karo na biyu wannan
iyali sun sadaukar da nasu jindadin don su kyautata musu.
BAYAN SHEKARA DAYA
Matashiya ce kyakkyawa sanye da riga mai dogon hannu baka mai kanun fulawoyi jajaye
wadda ta tsaya mata a rabin cinya da skirt mai fadi shima baki tayi rolling da
mayafi ja. Takalmanta loafers ne bakake da bakar jaka mai fadi wadda ta saka
computer da tarkacen litattafai. Siririn agogon hannunta ta kalla tasan cewa kowane
lokaci daga yanzu Yousuf zai iya kiranta su tafi gida.
Watanta tara tana daukar kos na koyon turanci da faransanci sannan aka samar mata
gurbi a University of Grenoble dake kasar Faransa inda ta fara karatu sati uku da
suka wuce a fanin aikin jarida wato mass communication.
Kamar yadda tayi hasashe wayar Yousuf ce ta shigo mata ta taso tana tafiya kai baka
taba cewa Radhiyan rugar Barkindo bace. Ta koma hadaddiyar budurwa mai ji da gayu
da wata irin nutsuwa kamar ba ita ba.
Kamar kullum sai da ya bude mata ta zauna sannan ya shiga ya tayar da motar. Gaishe
shi kawai tayi ta soma waya da Umminta wadda take karatun jarabawa saboda tuni
itama ta koma karatu ta sami gurbi a jami'ar Bayero ta Kano tana karanta Adult
Education. Mairama Ali Gidado ta zama babbar mace da maza suke kawowa hari ta
kowane fanni suna neman aurenta. Da yawa basa yarda ma tana da yara biyu matasa da
suke karatu a jami'a.
"Ina Tante din taki ko kina makaranta ne?"
"Ina hanyar komawa dai Ummi"
"Kice ina gaisheta. Gobe zamu je NDA na fada miki za'ayi taro kuma Karami yana
cikin masu yin match pass"
Turo baki tayi cikin shagwabar da Tante dinta take kara ingizata take yi yanzu tana
biye mata tace "ni yanzu bazan gani ba kenan? To ku daukar min video kinji Ummina"
Dariya Ummi tayi ta rasa yaushe Radhiyanta zata girma "zan dauka in sha Allahu 'Yar
soja rigima"
Dariya tayi mara sauti Yousuf ya kalleta yana jin lokaci yayi da zai sanar da
mamansa ya mugun kamuwa da son 'yarta. Sun cigaba da hirarsu da suka gama ta kira
Ibrahim tana tambayarsa progress din jikin Baba Hadir.
"Akwai babban albishir sai na koma gida zamuyi skype. Ke dai bari kawai na tsakura
miki, ya fara tafiya babu sanda"
Wata dariya da tayi sai da Yousuf ya manta me yake yi na dan lokaci. Tana zuwa gida
da sauri ta shiga ta haye sama dakin 'yar Mammee wadda ta kasance kanwa kenan ga
mahaifinta Zayyan mai suna Nasara ta fada jikinta tana murna.
"Tante Babana Hadir ya soma tafiya babu sanda"
"Da gaske Alheran" tace tana tayata murna.
"Oui Tante" (eh anti) tace tana rungumeta.
"To maza kije kici abinci kizo"
Radhiya na fita Nasara tana kallonta zuciyarta fes.
Bayan fasa aurenta da Awwab wanda yayi sanadiyar da ya bar gidan ana dawowa daga
daurin auren kannensa ya koma Abuja kwana uku kafin hutunsa ya kare. Yayi fushi
sosai da Radhiya wanda har Daddy yayi masa bayanin dalilin yin hakan bai dena jin
zafin abin ba. To bayan komawarsu ne aka turo daukarsu daga Nijar inda suna zuwa
Nasara diya ga Mammee tazo hutu da mijinta da dansa Yousuf wanda mahaifiyarsa ta
rasu ta shiga rokon arzikin a bata ita. Bata taba haihuwa ba gashi tana da son
yara. Ita tana yi mijinta na tayata aka kai maganar gaban Ummi ita kuma tayi
kawaicin hadasu da Daddy. Ba tare da bata lokaci ba ya amince ko babu komai yana sa
ran zata samu kyakkyawan sauyi a rayuwa. Zamanta tare dasu ba'a cewa komai sai son
barka. Nasara tamkar ta goya Radhiya don so. Babu ta inda ta rageta ta fanin gyara
shiyasa tun a yanzu tayi fice ta wuce raini nesa ba kusa ba. Kakaninsu ba a barsu a
baya ba wurin yi musu aike ita da Emzee duk karshen wata.
Emzee ma sun so rike shi a Nijar amma fafur yaki shi soja yake son yi abinda bai
taba fadawa kowa ba. Cikin dan kankanin lokaci Daddy da taimakon Captain Onomza
suka samar masa admission. Ibrahim kuma ya sami Law a Buk itama Ummi ta sake WAEC
shekara na zagayowa ta koma makaranta. Gidan Zayyan na Kano Alh Sidi yayi mata
gyara na gani na fada ta koma tare da kanwarta daya da kaninta