Advertisements
Chapter 57 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   57 / 99

168K to 171K   out of 295.8K words

mace yake magana. Gara ta bashi wuri idan
ma akwai wata I love you da zamanta a wurin ya hana a fada sai yaji dadin sakewa.
Tashi tayi da karfinta ai kuwa goyon nata taji gabadaya yayi sako-sako yana neman
kwancewa baby ya fado. Yadda gabanta ya fadi sauri tayi ta duka jikinta na rawa ta
tallafo Daadaa da hannuwanta ta baya. A hankali ta saki tana kokarin gyara gaban da
ya kwance duka yaron yayi motsi a gigice tace "Hamma"


Yana da kallonta amma a zatonsa goyon zata gyara. Kuma tsabar tsoro ta kasa daga
murya kada yaron ya tsorata ya fado.


"Hamma ka ajiye wayar mana" tace tana daga murya.


Sai lokacin ya cire wayar daga kunnensa "me kika ce?"


Kafafu biyu Daadaa yake dan shureta dasu alamun baya jindadin yanayin da yake.


Kuka ne ya taho mata kada ta saki dan mutane "Hamma please help" tace tana rike
gaban zanin sosai kuma taki dagowa.


Wayarsa ya ajiye da sauri akan kujerar da ta tashi ya zagayo yana dukawa ya ga me
ya sameta "meye?"


A rikice take bata san ya zasu kwashe da Ummi ba idan ya fado "goyon ya kwance"


"To ki gyara mana" yace yana mikewa ya gyara tsayuwarsa.


"Ban iya ba fa Hamma"


"Seriuosly?" Shima ya soma rikicewar ganin tana ta saka hannu daya a gaba daya a
baya.


"Zai fadi" ta sake cewa da yayi wani irin zillo yana canyara ihu ya gaji.
"Kwace zanin da sauri" yace yana saka hannu a bayan yaron ita kuma ta kwance gaban
"tashi a hankali"


Tana tashi yaron ya fada a hannunsa ya kankame shi a kirjinsa "are you okay?" ya
tambayeta yana kallon yadda tayi wuri wuri.


"Allah Ya soni da ya fado..."


"Da sai mu haifi wani" yace yana kallon dimple dinta.


Idanunta ta dauke daga kansa maganar tana dada shiga kwanyarta. Duk wasu matakan
nuna masa yanzu ba da bane ta nemesu ta rasa sai uwar kunyar da ya hadata da ita.
Ya san me yayi mata amma sai ya wayance irin yadda ta taba yi masa.


"Silly girl, me kike tunanin ina nufi?"


"Ba nufinka idan ka haifi naka nima na haifi nawa sai mu kawo mu hada mata ba?"


Kanta tsaye tayi maganar kafin ya gama gano lagonta ta tafi ta barshi da baby a
hannu.


**********


"Wurin wa kazo?"


"Waye shugabanku a nan barrack din?"


Dariya ya basu suna masa kallon wanda bai san me yake yi ba. Barrack ai ba wurin da
zaka zo kai tsaye bane idan baka san wanda kake nema ba.


Chibuzor ya rasa wa zaice musu. Sai da yayi sati a garinsu ana ta jajantawa
iyayensa abinda ya same shi sannan da kyar ya kwaci kansa ya taho Sakkwato saboda
cika alkawarin da ya daukarwa kansa da Zayyan. Bai san komai game da tsarin sojoji
ba kamar chanjin mukami shiyasa kawai yace "Lieutenant Hadir nake nema" yana fata
daidai ya fadi sunan.


Duk wani hargagi da zasu yi masa sunyi a ganinsu bai san me yake yi ba. Gashi dai a
haka yayo fes dashi. Kin tafiya yayi tun safe har yamma ana ta abu daya yana tsaye
a bakin gate. Wani ne cikinsu ya shiga ciki bangaren ofisoshinsu suna hira da wani
da yake zaune a bayan wata kanta yake bashi labarin wani msi naci a waje.


"Baku saka shi tsallen kwado ba?"
"Tausayi ya bani. Ya dage wai sako ya kawowa Lt Hadir. Ban taba jin sunan ba ma.
Amma an chaje shi babu komai a jikinsa"


Wani yazo wucewa suka tambaye shi ko ya taba jin mai wannan sunan. Wanda yake
bayansa ne ya amsa "an taba yi mana amma shi fa yayi retire saboda rashin lafiya
tun bayan dawowarsu daga Liberia an dade don tun ina non-commisioned officer"


Wanda ya kawo zancen ya mike "yayi zancen Liberia fa. Bari dai na koma naji"

💕[11/2, 7:11 AM] 42💕.

.Mamaki sosai yayi da aka sanar dashi bakon nasa yace da sakatariyarsa tayi sauri
ta shigo dashi duk da cewa ya gama shiri zai tafi gida ne lokacin tashi yayi. A
bakin kofa ya tsaya ya tarbe shi yana murmushi suka kama hannuwan juna suna
gaisawa. Kowannensu sanye yake da manyan kaya da babbar riga. Kana ganin bakon
kasan naira ta zauna da kyau. Daga hularsa har zuwa takalmi babu wani abu da
kudinsa yake kasa da dubu ashirin.


"Alh Salisu wai kaine nake gani ko dai mafarki nake yi?"


"Tuba nake Alh Musa ni din mai laifine a wurin mutane da yawa. Nine da kaina ba
sako ba na yakice ayyukan gabana nace sai nazo"


Alh Musa ya nuna masa wuri ya zauna sannan ya tashi ya kira sakatariyarsa ya soma
fada mata me zata hadow bakon ya dakatar dashi.


"Kada ka damu kanka a koshe nake."


Zama ya sake yi suka kuma gaisawa da tambayar juna bayan rabuwa.

"Yara suna dakunansu ko?"


"Wallahi kuwa"


"Naso zuwa daurin auren nan amma wallahi Musa zama a wuri daya na sati gagarata
yake yi"


"Ya fa kamata ka sassautawa kanka Alh Salisu. Mutum yana fafutukar neman kudin nan
fa kawai sai mutuwa ta riskeshi. Sai ya laluba ya ga babu wani abin arziki da ya
tara sai wahala. Shiyasa ka ga na makale wuri daya yanzu"


"Mtsww ni zan fada maka yawon nan baiyi ba ko kadan. Amaryata fa mai aiki ta kama
da dreban da na daukar mata a cikin gidana don bala'i"


"Subhanallahi garin yaya haka ta faru?"
"Kaima ka sani ai, cewa tayi bana zama bani da lokacinta. Inda na gode Allah bamu
haihu ba da ta saka ni wasiwasi"


"Ka chanja tsari Alh Salisu. Girma sai dada kamamu yake yi da kunya irin wannan na
fitowa daga gidajen aurenmu. Ai kamata yayi ace macen kwarai ko bata sonka ta san
kiyaye addini da darajar kanta"


Daya daga cikin wayoyin Alh Salisu ce tayi kara ya kasheta sannan yace "ka tuna
Halifa ai babban dana. To mahaifiyarsa wallahi ita ta cire min son mata gabadaya
shiyasa bana damuwa da zama dasu tunda nasan kudin ne ya kawosu sai na basu kawai.
Da bamu rabu ba ina mai tabbatar maka ko zanyi yawo ba kamar yadda nake yanzu ba.
Sannan mafi yawa tare zamuyi gani gata"


"Kace kun zuba soyayya" Alh Musa ya fada da dariya.


"Wace soyayya? Matar da ta aureni alhali tana son mijin kanwarta. Kaji fa kanwa da
suka hada uba kuma bata iya boye min. Kishi take da kanwar abin babu kyaun gani.
Shiyasa da na saketa bayan abin ya fito da mijin kanwar ya rasu ko shi Halifan bana
bari yaje wurinta sosai"


"Amma kuwa kayi kuskure Alh Salisu wa yake raba da da uwa banda abinka? Nima nayi
irin auren nan amma wallahi Zainab 'yar halak ce. Ka tuna kazo daurin aurenmu. Ita
dole aka raba auren mijin ya sami paralysis ga rashin magana amma ta kafe sai ta
zauna dashi. Kasan Allah ko zanyi rantsuwa bani da kaffara tunda na aureta Zainab
bata sake zuwa Kano ba sannan ko a bayan idona idan tayi waya da danta bata taba
cewa ina mahaifinsa. In karkare maka zance na saketa kuma mijin ya sami lafiya.
Aisha ma ta kirani wai ta haihu...kai kaji kudura ta Ubangiji"


Sosai Alh Salisu yaji dadin shawarwarin Alh Musa don gaskiya yasan bai kyauta ba.
Kasuwancinsa ya bunkasa sosai amma zumunci dai bashi da lokacinsa. Yana China
babansa ya rasu haka yana India babarsa ta rasu da kyar ya roki yayyensa aka
jinkirta jana'izarta. Kudi dai danginsa sun warke amma ganinsa yayi wuya.


"Nagode Alh Musa, zan gyara don ina komawa zansa a kai Halifa Sumaila wurin babarsa
da kakaninsa. Bai saba da kowa ba sai ni. Cikin gidan ma kannensa ba shirginsu yake
shiga ba ni kuma ban damu ba ganin duka mata ne"


"Matan idan babu kai ba shine gatansu ba?"


"Hakane, sai ka tuna min da abokaina na kuruciya da duka na watsar da kace mijin
matarka na da yana da paralysis. Akwai aminina soja ne a yaki ya kamu da wannan
lalura. Sau biyu naje duba shi shikenan kamar wani sallamamme na dena waiwayarsa.
Daga baya kunya da nauyin jinkirin yasa na kasa zuwa kuma"


"Tunda kana da rai ai babu wani jinkiri. Itama Zainab din mijinta fa a yaki ne tasa
lalurar sunansa Hadir"
Alh Salisu sai ya gyara zama da kyau "Hadir Murtala mutumin Kano?"


Da mamaki sosai a fuskarsa yace kwarai kuwa "shine aminin naka?"


"Shine Alh Musa wallahi shine. Ina zuwa Kano gidansa zani...ni kam kudi naga
sharrinsa tunda ya nesanta ni da makusanta na"


Alh Musa yayi matukar mamaki. Da Alh Salisu ya rike zumunci da Hadir bai kwashi
wadannan shekarun a kwance ba. Kudi ne dashi fa na ban mamaki don shi a haka bai
kama kafarsa ba. Duniya komai sai Allah Ya nufa amma sakacinmu ke janyo mana.
Adireshin gidansu na Abuja ya nema wurin 'yarsa ya bashi.


"Daga nan ni sai birnin tarayya inji mutanenmu."


Godiya mai tarin yawa ya yiwa Alh Musa sannan ya koma katon gidansa dake garin Port
Harcourt din. Halifa ya kira yace masa ya shirya gobe ya taho Abuja. Bautar kasa
zai fara dayake a turai yayi karatu ya gama da wuri. Sake tunani yayi na tuna cewa
yaron da kannensa ma babu shakuwa yace masa dashi da kannen nasa mata ne su hudu su
taho tare. Sai kuma ya kira matarsa uwar uku cikin yaran Farida, Husna da Meena.
Dayar mai bin Halifa a jerin haihuwa Hibbah tata maman ta dade da fita itama ya
fada mata tace yaran su shirya. Baiwar Allah har ranta taji dadi yau da kansa yana
wani garin yace a tura masa 'ya'yansa kuma wai kuma su da Halifa. Bata taba kin
yaron ba duk miskilancinsa da shiru shiru. Irin 'ya'yan baba dinnan ne sangartattu
amma ba wai ya lalace da dabi'un banza bane sai son jiki.


Halifa yaro ne sa'an su Ibrahim sai dai ya fisu duka girman jiki. Ga tsaho kuma da
'yar kibarsa daidai misali ta hutu da jindadi. Bashi da matsalar komai a rayuwa sai
mahaifiyarsa Salame. Duk kudin babansa yafi ganewa ya saya masa abubuwan bukata ya
bashi kadan kawai don kada ya kai mata. Ita kuma da zarar ta ganshi tamkar ta ga
nama ta rinka bani bani kenan. Ga matsalar muguwar kazantar gidanta ko yawu baya
iya hadiya idan yaje. Kannensa na gidan idan suka yanyame shi ya rinka yamutsa
fuska kenan. Daya kanwar tasa wadda Salame ta auri babanta farkon mutuwar aurenta
bai fi sau biyu ya taba ganinta ba. Itama nata baban sai a hankali babu kudi amma
dai bata da roko, sunanta Rahima. A haka itama bata huta da bani banin Salame ba
idan taje gidanta idan tace babu ta hadasu ita da mahaifin nata da danginsa ta
zagesu su tas. Yarinyar da iyakarta secondary don ma tana sana'ar kunshi da abin
sai ya fi haka mun.


Washegari Alh Salisu da 'ya'yansa suka sauka a gidansa na Abuja yace su huta ana
magariba zasu je gidan abokinsa.


**********


A can Jos Excellency bai huta ba Chibuzor bai huta ba. Bincike da tambayoyi yasa
ake ta yi masa sai yau ya gama samun duk wata shaida da zata tabbatar masa cewa
Chibuzor ba dan aiken 'yan hamayya bane sannan ba wata damfara bace ta kawo shi.
Hankalinsa in yayi miliyan to a tashe yake da yasa shi a gaba yana bashi labarin
rayuwarsu a kurkuku. Abu dai sai da ya kai Gwamna da zubar hawaye. Duk wani aiki da
yake gabansa yasa an dakatar dashi domin ya samu yayi aikin Zayyan kawai. A ka'ida
Major Mustapha da Hadir ya kamata ya nema amma sai ya tuna cewa yadda suka yi zaton
Zayyan ya rasu haka shima yayi wannan tunanin. Abinda yaga yafi dacewa shine yaje
ya kawo Zayyan Nigeria ya dangana shi da iyalinsa. Shawarar tayi masa, shi kadai
bayan sunyi waya da matarsa akan zuwan su Awwab gidan ya sake shawarar gara ya tafi
dashi ayi komai a gabansa har zuwa dauko shi.


Da wannan shirin suka kwana gobe zasu tafi Abuja shi da Chibuzor hedikwatar sojoji
dake unguwar Garki. Mukaminsa na Gwamna kuma tsohon soja yasa tun a daren da yayi
waya ya nemi ganawa da Chief of Army Staff Lieutenant General Enejo Adaji mutumin
Kogi aka saka masa appointment din karfe biyu da rabi na rana.


Dukkan wata kulawa da ta dace da bako mai mahimmanci ita ake yiwa Chibuzor. Emma
tayi murna sosai da ya fada mata yadda komai ya kasance. Da safe suna tashi da wuri
aka dangana su da filin jirgi. Convoy din Excellency dama a Abuja suka kwana.
Arifah da Mamanta sai ganinsa suka yi da bako kuma ko minti talatin basuyi a gidan
ba suka wuce Nigerian Army Headquarters.


Bayan 'yan gaishe gaishe irin na manyan mutane Rtd Col. Nasiruddeen ya gabatarwa da
Lt.Gen Enejo da Chibuzor da bayanin da yazo dashi.


Hankali a tashe Chief din na army staff ya soma buge bugen waya aka hau bincike a
bangaren aiki da na'ura mai kwakwalwa akan waye Chibuzor Kalu, asalinsa da
sana'arsa domin a tabbatar da ingancin zancensa. Yaga tasku ranar duk da babu duka
amma fa an kaishi dakin bincike ace wannan ace wancan duk don su ji ko zai chanja
magana idan bashi da gaskiya. A bangare guda kuma an binciko files din sojojin da
aka tura Liberia daga Giginya Army Barrack na Sokoto a shekarar 1993. Zancen
gabadaya an saka shi a jerin CLASSIFIED INFORMATION ba kowa ya sani ba sai mutane
kalilan. Sunci karfin bincikensu washegari zasu nemi sa hannun shugaban kasa domin
ya bada izinin ganawa da gwamnatin kasar Liberia. Excellency dai yayi ta rokon a
gaggauta komai don a matse yake da yaga an fiddo Zayyan Tureta daga kasar nan.


*********

Alh Musa ne ya kira Ibrahim ya fada masa bakin da zasu yi yace ya sanar da
mahaifinsa. Gobe zasu taho shi da Emzee. Ya gama jarabawa da kwana biyu kenan ya
tsaya jiran Emzee su taho. Bayan ya fada masa shine ya kira Mama ya fada mata.
Mamaki kwarai kuwa ya kamata ta sanar da Baba Hadir. Shi din ma mamakin yake.
Yaushe rabonsa da Salisu, har ya manta. Rubutawa Mama yayi cewa ta fadawa Ummi
tunda a iya saninsa akwai haihuwa tsakanin yayarta Salame da Salisu.


Itama tayi mamaki sosai nan fa suka hau shirin tarbar baki tunda ance shi da
yaransa ne. Mama da Ummi suka yi ta mamakin wai yau Salisun da ko ita Ummi da ya
taba auren yayarta rabonta dashi tun gaisuwar Zayyan. Halifa kuwa zata iya kirga
sau nawa yaje gidan Malamijo tun tana makauniyarta.


Sun shirya komai a gidan Mama suka tafi yin sallah. Awwab, Yousuf da Raji basu wuni
a gida ba ya kaisu ganin gari suma sai magaribar suka dawo.


Motocin biyu su Alh Salisu suka yi shi da 'ya'yansa. Daddy yaje gidan Daddy Haroun
sada zumunci da magana akan halin da Ghazalatu take ciki a gidan Nura da ya fada
masa. Shawara yake nema akan yadda zasu fadawa Alh Baba kada rigimar ta wuce yadda
take yanzu don Gambo da Hussaina harda zage zage tsakaninsu. Rufa rufa suke yi
kowacce bata son fitar da maganar kada aji ayi musu dariya.


A kofar gida Baba Hadir ya taresu suka karasa ciki shi da yaran. Zayyana ta tafi
bangaren Mami da Hibbah wata uwar surutu da karadi irinta. Yanzu take SS3 saboda
haka hirar ta 'yan mata ce masu tashen girma. Kanenta su Husna suna can suna fadan
daukar Femi da Jawad suna ta musu wasa. Dukkansu son yara garesu kamar su daukesu
suke ji. A falon gidan Mama su Zahra sun gaishe da Alh Salisu suka koma bangaren
Ummi a falo suka dasa tasu hirar.


Baby Zayyan Ummi ta mikawa Alh Salisu yace "Mairama ko ina da bakin wanke kaina a
wurinki da Hadir? Duk wani rikicin gadonku bani mantawa anyi dani haka lalurar
Hadir amma neman kudi ya hanani yin abinda ya kamata. Tabbas ba karamar kunyarku
nake ji ba ko ban taba auren Salame ba a matsayinki na matar Zayyan baici ace na
yanke zumunta daku ba"


"Komai ya riga ya wuce sai dai mu fuskanci gaba. Kurakuranmu sai muyi kokarin mun
gyara saboda kada yara su tashi basu san juna ba"


Halifa ya kalla da yake zaune ya karbi babyn yana masa wasa "Halifa wadannan duka
iyayenka ne saboda haka a rike zumunci"


"In sha Allahu"


"Ina Ibrahim ne da Zayyan?" Alh Salisu ya tambaya.


Mama ce ta masa bayanin suna makaranta amma zasu taho gobe. Sai Radhiya da ya gani
cikin matan da suka shigo dazu.


Awwab dasu Yousuf da suka dawo sun shiga bayan sun gaisa dashi Mama tace ya nunawa
Halifa bangaren Ummi ya gaishe da Nasara tunda can zasu koma cin abinci.


Fadan su Farida akan daukar yara har waje Radhiya tana alkalanci. Jeans ne baki a
jikinta da top sai da dora hijab mai hannu da ya wuce gwiwarta kadan. Suna shigowa
ta koma tana sulhun daga zaune.


Halifa ya kalleta ya kara duka akan idon Awwab yana mamakin yadda ta zama. Da
kuruciya basa shiri saboda Salame ta koya masa kinsu haka itama bata son shi tunda
dan Gwaggo Salame ne wadda bata son Umminta.


"Radhiya bazaki gaisheni ba" yace bayan ya zauna.


Murmushi tayi tace "Ka rainani Halifa ko don kana ganin ka zama basamude"


Yadda take magana ya sashi dariya "ance Emzee yana NDA ko, ke kuma me kike yi
yanzu? By the way you look great and ...beautiful"
Turnuku, ya kai Awwab wuya Yousuf ya koma kallon Awwab din yana dariyar mugunta.


"Thanks" tace da murmushinta.


Bai da son hayaniya amma yaji yana son tsawaita hira da 'yar uwar tasa da ya jima
basu hadu ba.


"Da gaske fa da a waje muka hadu bazan ganeki ba. Nafi gane wannan terror din
abokiyar fadana...tsoronki fa nake ji da"


Fauziyya sai ta tattara 'yan matan da yaransu suka koma daki saboda kada Awwab ya
fashe musu a wurin. Da Halifa zai ga irin kallon da yake masa kila da yayi shiru.
Radhiya ta gani sarai ko zama ya kasa yi amma ta biye masa.


"Ta da dinma tana nan sai dai idan ba'a tabota ba"


"Halifa mu bazaka yi hirar damu bane sai 'yar uwarka?" Yousuf yace domin ya kawo
karshen hirar. A fusace Awwab ya juya ya fita. Kalmar great and beautiful ta tsaya
masa. Jikin mota yaje ya tsaya sai ya sami kansa da kiran layinta.


Su uku suka rage a falon saboda Zahra tana can dakin Awwab da mijinta tunda ya leko
suka fice. Yanzu hirar da Yousuf ake yinta yawanci akan makarantar da ya gama a
Dubai da kuma wadda take yi yanzu.


Allah Yasa wayar na gefenta ta ga kiran ta dauka.

"Fito" kawai yace mata ya kashe.


Tashi tayi tsam ta saka wasu flat shoes dinta masu kyau ta fito wajen ta hango shi
zaune cikin mota. Kallo daya tayi masa tasan ransa ne a bace sai taji babu dadi
kuma.


"Hamma" tace a dan tsorace.


"Get in" ya umarceta. Bata ce komai ba ta shiga gaban ya daga waya ya kira Ummi
yace mata Alheran zata raka shi siyan magani ba jimawa zasu yi ba.


"Hamma baka da lafiya ne?" Idonsa akan titi yaki kulata.


"Ko mu koma gida a taho da namiji ka ga idan lalurar tayi tsanani sai an daukeka ni
ba karfi gareni ba Allah."


Bai san lokacin da ya soma dariya ba tun yana yi a hankali har ta fito.
"Yanzu fushin ma bazaki bari nayi ba?"


"Fushin me?" Tace kamar bata

57 / 99