Advertisements
Chapter 69 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   69 / 99

204K to 207K   out of 295.8K words

zargi ne kawai"


"Tunda kika fadawa Malamijo nasan ya wuce zargi." Yace a fusace.


"Kwantar da hankalinka Zayyanu. Ni dai na haifi Salame ina mai tabbatar maka babu
wani iskancin da zata zo dashi da ban ga wanda ya fishi ba. Zan bi diddgin maganar
da kaina. Kai dai ka rufa min asiri kada yayarka taji zancen nan mu duka mu shiga
uku. Ka fita hakuri da nutsuwa ka bari muyi komai cikin lumana" Malamijo ya sami
kansa da lallaba Emzee.


Ficewa kawai yayi daga dakin a hanya yaci karo da Halifa. Wani mummunan kallo ya
maka masa Nene tana biye dashi tace da Halifan allurar soja ce ta motsa saboda
Malamijo yayi masa fada. Da yake ba bakon zafi bane sai ya yarda harda tausayawa
Emzee din.


Dakin da suka kwana ya shiga ya rinka naushin bango ko zai ragewa kansa fushi. Da
ya bar maganar a cikinsa gara ace bai ji ba. Kai dama ace Radhiya ce taji ta
gwadawa Salame me ake nufi da uwa. Wai saboda wani can Alh Indararo shine ta
makanta musu uwa. Kuma karin abin haushi wai Daada dinsu take so.


"Wallahi sai dai ki mutu amma yafi karfinki"
"Kai da wa?" Yaji Ibrahim yace daga bayansa. Kasa amsawa yayi sai kwanciya da yayi
yana ta juya zancen. Abin ya dame shi matuka ya dena walwala ya matsawa Ibrahim
suka tafi Kano gidan kakaninsa. Halifa da Hibbah su ma zasu tafi amma kememe Emzee
yaki yarda su hada tafiyar saboda baya ko son ganin Halifa. Washegarin tafiyar tasu
yaje yace da Malamijo ya basu kudin mota. Dubu goma ya bashi duk da yasan kudin
yayi yawa amma gara ya tafi ko hankalinsa ya kwanta. Kullum da zulumin kada Radhiya
ta gane yake kwana. Ta shiga damuwa sosai akan yadda kanin nata ya koma sai matsawa
Malamijo take yi akan ya tambaye shi ko ta sanar da iyayensu.


**********


Kwanan su Zayyan uku a Sakkwato sai birnin Agadez a kasar Nijar. Da kwatance suka
isa unguwar inda gidan Alh Ghoumar da Alh Sidi suke makotaka da juna. Mammee suna
Niamey da mijinta tunda dan siyasa ne. Kowa yayi mamakin zuwan Mairama ita kadai
tace banda yaran ta tahi lokacin da ta kira kwaya domin a kwatanta musu hanya.
Tante Nasara sai da ta kira Radhiya da Emzee taji muryoyinsu ta tabbatar kowa
lafiya kafin isowarsu gidan.


Murnarsu kuwa bayan sun ga Zayyan bazata misaltu ba. Masu kuka na yi masu suma suna
yi. Dangin Innar Zayyan sun sake nuna bajintarsu da kwarewa wurin rikon zumunci da
murnar dawowarshi. Mammee tayi kuka tayi fadan me yasa basu sanar da ita ba sai da
suka iso gashi kowa ya rigata ganinsa. Kwanansu biyar 'yan uwa suna faman kokarin
kyautata masa da nuna masa cewa shi din dan dangi ne. Tamkar kada ya baro kasar sai
dai dole ya koma saboda litinin zaiyi reporting a headquarter ana nemansa.

[11/2, 7:24 AM]🏽
]🏽 : ***********50💕


Tsattsaye suke maza da mata a kofar dakin a aibitin likitoci suna ciki suna aikin
kokarin ceto rayuwar yarinyar da ke ciki.


Daga can gefe Hussaina ce take kuka wiwi jikinta duk jini tana sambatun kada
autarta ta mutu. Duk cikin yaranta kowa ya shaidi yadda take masifar son auta Hany.
Yarinya ce kyakkyawa mai mugun shiga rai. Bata da hayaniya ga kokari a makaranta.
Hussaina duk inda ake hirar yara tamkar sauran shidan babu su zancen bai wuce Hany
tayi kaza ko Hany tace kaza.


"Kiyi shiru mana Hussaina mu samu su fito aji halin da take ciki" Ummansu tayi mata
tsawa.


Alh Baba da akayi komai a kan idonsa ya biyo su asibitin shima hakuri yake bawa
Hussainar hankalinsa a mugun tashe. Saboda soyayya yarinya ta sanya reza ta tsinke
jijiyoyin hannunta wai gara ta mutu da a rabata da wanda take so. Wannan wane irin
zamani ne rikirkitacce haka.


Lokaci ya shude kafin likitan ya fito yace anyi nasarar tsayar da jinin amma fa
wanda ta zubar da yawa ana bukatar a kara mata ko leda daya ne zuwa biyu. Hannu na
rawa Hussaina ta kira Nura. Blood group dinsa daya da Hany tace maza maza yazo a
debi jininsa.
"Kawai ki nemi wani" taji ya bata amsa ga alama ma cikin maye yake don a datse
maganar ke fita.


"Nura ni kake fadawa haka? Kanwarka fa nace"


"Tare fa aka gwadamu kuma kema irin naki ne ki bata mana" ya kashe wayarsa ya fada
gado rigijib. Kwance a kasa Ghazalatu ce rike da cikinta bayan yayi mata mugun
duka. Da rarrafe ta soma tafiya domin ta bar dakin sai ta gano ashe jini ne yake
naso a duk inda ta bi ga azababben ciwon ciki ya murdeta. Lallabawa tayi zuwa
dakinta ta kira Mummy Gambo ta fashe mata da kuka.


"Sai da nace bazan dawo ba Mummy gashi nan zai kasheni"


Hannu ta kai ta tabo Daddy Haroun ta saka wayar a speaker hankalinta a tashe saboda
yadda take jin muryar Ghazalatun.


"Me ya sameki?"


"Mummy dukana yayi ga jini yana bin kafata kuma cikina...cikina..."


Kashe wayar tayi da sauri ta kira Hussaina wadda take kwance ana diban nata jinin.
A zatonta Nura ne shiyasa ta matsawa Ummansu ta bata wayar sai dai tana karawa a
kunne ta jiyo masifar Gambo hatta Umman tana ji.


"Hussaina ki rubuta ki ajiye sai nasa an daure Nura in ga uban me kuke takama
dashi. Yarinyata ba jaka bace da zai rinka dora mata hannu duk lokacin da ta raya
masa. Dama kuma na fadawa Alh Baba idan ya kuma dukanta ya daki aurensa"


Muryarta ta zama weak sosai tace "Gambo muna asibiti da Hany ki bari..."


"Bazan bar komai ba. Ki tura a dauko min yarinya a kaita asibiti tace jini yana bin
kafarta"


Yunkurin tashi tayi Umma tace ta kwanta ta fita ta sanar da Alh Baba wanda ya hana
a fadawa mijin Hussaina da Baban biyu komai sai yadda ta kaya. Dan tsohon sai ya
kara shiga firgici ba yadda ya iya haka ya kira Baban Biyu ya sanar dashi. Yana
gida a zatonsa Umma tana gidan Alh Baban ne ashe kuma suna asibiti. Kanin su Mami
ya nema Allah Yasa ya dawo gida dayake bashi da nisa daga gidan iyayen nasa yazo
suka fara tafiya gidan Nura. Bugun duniya Kawu Mas'ud yayi a dan karamin gate din
gidan ba'a bude ba. Ya shiga kiran Ghazalatu tana can bata san inda kanta yake ba
sai da Baban Biyu yace ya zai kira wasu cikin 'yan uwa su taru a balle kofar sai ga
Nura cikin maye ya bude gate din.


"Wane dan...."
Naushi yaji ya sauka a bakinsa da hanci zaiyi magana hasken fitilu ya nuna masa
fuskar kakansa da kuma kanin babarsa wanda ya sauke masa naushin kafin ya bangaje
shi ya shiga ciki. Kofa biyu ya bude yana leke ya sami dakin da Ghazalatu take
kwance a kasa. Da sauri ya ciccibota don ma wahala ta sake zugeta bata da nauyi ya
fito ya sakata a bayan mota. Nura yana tsaye ya yi ribas suka bar wurin bai iya
motsi ba.


Asibitin da aka kwantar da Hany suka kaita tunda nan Alh Baba yace su samesu. Ana
zuwa Ghazalatu tayi bari na 'yan biyu. Umma kuka ta zauna tana yi sosai kamar yadda
Hussaina duniya tayi mata zafi.


"Kinji dadi Hussaina, ga ribar shiga tsakanin Gambo da Hassana kin gani zahiri ko.
Itama Gambon da shegiyar kafiya da kin jin magana zata zo ta ga nata sakamakon na
dora son zuciya akan komai."


"Umma kada kice haka" Hussaina tace a raunane.


"Matsa min ni na wuce"


Umma ta fita tana share hawaye. A wajen inda motar Kawu Mas'ud take ta sami Alh
Baba da Baban Biyu. Ranta yana kuna yau ta manta da surukuta da girman Alh Baba ta
soma magana.


"Kun tuna lokacin da Awwab da iyayensa suke rokon a barshi ya auri Ghazalatu da
daya yarinyar abokin Mustapha ko? Ku ka kekashe kasa kuka nuna naku, naku ne dan
kowa bai isa ba. To yau gashi Hannatu tana son yaron da iyayensa sun rantse sai dai
ya auri 'yar uwarsa kuma su danginsu basu zama da kishiya"


"Fatima!" Baban Biyu ya daga murya da niyar yi mata fada.


Kukanta ne ya tsananta tace "Ko me zaka ce sai dai ka jira na gama fadin nawa.
Saboda wannan akidar ta auren dangi da ba farilla ba kun raba min kan 'ya'yana.
Dukansu yanzu daga masu goyon bayan Hassana sai 'yan bayan Gambo. Hussaina kam dama
ita ta sayawa kanta koma me ya sami nata yaran saboda kofar da kuka bude musu tun
farko. Ni dai baku yi min adalci ba wallahi". Bayan motar ta bude ta shige "kaini
gida Mas'ud" ta umarci dan nata.


Alh Baba da Baban Biyu aka rasa me cewa komai. Yanzu yake bawa kaninsa labarin
abinda ya kaisu da zuwa asibiti. Hussaina ta damu da halin da Hany ta shiga saboda
dangin saurayin nata sunki yarda ayi auren shine ta tsefe ido ta tafi gidan Alh
Baba tana rokon ya sanya baki tunda kakan yaron abokinsa ne. Fadan da ya soma yi
mata ne akan soyayyar ya sake jagula komai ta fita ta yanka hannunta. A take
Hussaina ta kira mahaifiyarta tana kuka shine ta taho gidan suka wuce asibitin
tare.


"Yanzu ita Hussaina ba kwari gareta ba ga jinyar mutum biyu. Na rasa yadda zanyi da
rigimar nan. Nura bashi da hankali dole muyi wani abu"
"Ko baka ce ba wannan wajibi ne. Tunda Fatima ta ajiye kawaicin tayi magana kasan
an kure hakurinta."


Umma na zuwa gida ta kira Mami ta fada mata abinda ke faruwa tana kuka. Hankalin
Mami a tashe ta sanar da Daddy. Suna haka Daddy Haroun ya kira shi wai Gambo babu
lafiya jininta ya hau suna asibiti.


Mami ta leka daki wurin Fauziyya, ita kadai ta rage a gidan ta fada mata zasu fita
zuwa asibiti.


Daren ranar basuyi kwanan kwanciyar hankali ba. Mummy Gambo ta tayar da hankalinta
saboda bata san halin da Ghazalatu take ciki ba. Can kuma Hussaina da daya daga
cikin 'ya'yan Alh Baba mata ne zasu kwana da Hany da Ghazalatu.


Garin Allah na wayewa sai haramar tafiya Katsina. Mami bazata bisu ba saboda
Fauziyya dake fama da laulayi ga yaro sannan mijinta baya gari. Daddy ne yayi musu
kara suka tafi tare. Al'amura dai basuyi dadi ba haduwar Hussaina da Gambo tamkar
ba ciki daya suka fito ba. Sai da Umma tayi kuka sannan kowacce ta shiga
hankalinta. 'Ya'yan dai da suke yi dominsu sune yau suka hadasu fada. Umma kuwa
tace hakkin Hassana ne ya kamasu. Shekara uku sun dauki gaba ta babu gaira babu
dalili akan abinda idan kowa ya ajiye son zuciya zasu daidaita shi cikin lumana.


Gabadayansu sun fahimci kuskuren abinda suka yiwa Mami akan auren Awwab tunda
kowacce ta gani a kwaryarta. Ita Hussaina yanzu 'yarta ce a matsayin Radhiya na da
kuma dangin mijin masu bala'in kudi ne saboda haka ana yi musu kallon masu kwadayi.
Mummy Gambo da take ganin 'yarta tafi karfin zama da kishiya ta kare a gidan
mashayi mai duka. Banda bari sai tayi jinyar jikinta da ya doku. Daddy Haroun ma
dai cewa yayi a raba auren saboda ko waya Nura baiyi ba bare yazo dubiya.


Bayan dogon zama da mayar da maganganu Alh Baba yace da mijin Hussaina ya umarci
dansa da sauwakewa Ghazalatu kafin sauran zumuncin iyayensu ya karasa lalacewa. Sai
dai Nura ya kafe bazai saketa ba. Hakuri yayi ta badawa akan cewa yana sonta kuma
bazai kuma shan kayan maye ba. Mummy Gambo ta tafi da ita Abuja suna jira idan ya
gama haukan a cewarsu zai kawo takardar.


***********

Rugar Barkindo da Gaya wurin Nene da su Ummi ke da niyar zuwa sai waya suka yi musu
suna bada hakuri da zarar ya gama da wurin aiki zasu zo. Innawuro tace babu komai
dama yanzu ai zama bai ganshi ba. Radhiya suka tsaya dauka kawai Emzee da Ibrahim
aka ce su biyo motar haya saboda motar tayi musu kadan. Kafin su tafi Malamijo yace
da Ummi idan ta sami sarari ta dawo zasu yi taro na 'yan uwa. Abin yayi mata dadi
kuwa sosai yadda baban nata ya sauya.

Hajjo ce dai take wahalar dashi yanzu taki yarda ta koma sai yawon ban hakuri yake
yi. Gidan kajinsa ko ashirin ba'a samu ba duka sun mace da cutar murar tsuntsaye.
Ayuba ne ya kwantar masa da hankali akan cewa yaci sa'a ba shi kanshi aka dauke ba
saboda kin fitar da hakkin Allah na zakka. Duk lokacin da yayi masa magana a
shekarun baya Malamijo sai yasa a kamo kaji uku ko biyu yace ayi miya zakka ce ya
fitar.
***********


Abin farinciki da murna ashe kiran da aka yiwa Zayyan kira ne na alkhairi. An
tabbatar masa da sabon mukaminsa na Major General sannan kuma gwamnatin tarayya
tare da hadin gwiwar Nigerian Army su ka yi masa kyaututtuka na bajinta. Da farko
dai an bashi dankareren gida a unguwar Maitama nan cikin Abuja da masu gadi kananan
sojoji. Gida na gani na fada ginin zamani wanda bai taba tsammanin akwai irinsa ba
bare ace zai mallake shi. Sai kuma motoci guda uku banda daya da take mazaunin
official car tare da drebansa. Basu tsaya a nan ba aka hada masa da cheque wanda
ganinsa ya sanya shi fitar da hawaye a matsayin compensation. Ina zai kai wannan
kudin yake ta tunani. Ranar shi da iyalinsa sun ga soyayya daga wurin 'yan uwa da
abokan arziki. Daddy da Baba Hadir sunfi kowa murna babu kyashi babu hassada.
Zayyan ya cancanci fiye da wannan ma. Taron karramawa kamar yadda aka yi masa
bayani tun farko za'a yishi ne daya ga watan junairun sabuwar shekara abinda bai
kai watanni biyu ba. Shi kuma nasa taron da kudurin da yake dashi na wannan ranar
sai washegari biyu ga wata.


A cikin satin su Ummi suka yi parking din dan abinda ba'a rasa ba domin sabon gidan
babu abinda babu cikin manyan kayan bukata na gida. Abinda baiyi musu ba ko babu
sai su canja. Ranar Juma'a suka tashi Ummi tayi kuka tamkar bazata sake ganin Mami
da Mama ba. Suna yi tana yi mazansu na bada hakuri.


"Meye abin kuka bayan ko minti ashirin bana jin zakuyi a hanya kafin ku ga juna"
cewar Daddy.


Mami tace "Mun saba fa tafiyar kafa ce kullum muna tare"


"To ai sai kuyi hakuri kowa ta koyi zaman kula da mijinta ku dena yawo"


Ummi da Mama kunya ta kamasu saboda shi ba mai yawan surutu bane. A haka dai suka
tare Baba Hadir ya baiwa Zayyan shawarar cewa ana iya yiwa Ummi tranafer ta karasa
karatunta a Nile ko Baze University da suke a nan tunda babu amfanin ace tana
karatu a Kano shi yana Abuja.


"Ko zaka kara aure ne?" Ya tsokane shi.


"Yi hakuri kada taji yau ta hanani tuwon dare"


"Kafin a koma hutu sai mu nemi bayanin yadda ake yin transfer din"


Littafin da ya rubuta masa Zayyan ya kalla ya dan bata rai "wai da gaske haka zamu
rinka hira Hadir bazaka kokarta kana magana ba?"


"Wwwahhalla" Baba Hadir ya bashi amsa.


"Duk da haka ka daure don Allah. Idan ba bude baki kayi muna zantawa ba gani zan
rinka yi kamar ban hadu da Hadir ba har yau"
Alkawari yayi masa cewa zai cigaba da kokari. Cikin motocin da aka bawa Zayyan
wadda tafi kyan ya bawa Ummi aka hadata da dreba. Daya kuma ya bawa Ibrahim
mukullin "kai da dan uwanka. Nasan ba gari daya kuke karatu ba saboda haka tana nan
sai kunzo hutu babu mai tafiya da mota makaranta"


A hakan ma sun gode matuka iyayensu suka tayasu murna. Da yake gidan bene ne babba
akwai dakuna shiyasa guda biyu da suke kusa da juna a kasa aka bawa Ibrahim din
daya Emzee daya. Radhiya tana murnar zata gyara daya a sama Ummi tace kada ma ta
batawa kanta lokaci aurar da ita zasuyi daki na Zayyana ne.


Mama ta bata rai "ya haka ne kun kwashe yaran duka?"


"Wadda taji haushi ta sake haihuwa" Ummi tace tana satar kallon Mami.


"Cigaba da yi min fata kizo ku haihu rana daya da Radhiya muga tsiya"


Ai gaban Ummi sai da ya fadi tana ta cewa ba amin ba Mama da Mami suna dariya wai
sun ga honeymoon din kamar bazai kare bane sai ta sauka. Kunya sosai taji kuwa ta
ja bakinta ta tsuke.


Duk wani shiri da ya kamata ayi domin fara aikin da ya dawo da Radhiya Baban Arifah
ne kan gaba. Abinda take shirin yi ya kayatar dashi matuka inda ya dauko mata hayar
kwararren cameraman aka hadata dashi. Arifah kuma ta zabi zuwa a matsayin wadda
zata yi co-ordinating komai saboda ya tafi bisa tsari tamkar shirin film ba kara
zube ba. Da connection din Excellency ya samu aka nemo masa wasu cikin makotansu
Zayyan wadanda mazansu suka rasu a Liberia dasu zata fara.


Yau litinin suka gama shiri zasu tafi Kwara state can karamar hukuma Moro. Suna
airport kafin jirgin ya sauka Radhiya ta matsa gefe suna hira da Awwab. Rigima take
yi masa tun jiya wai ya dawo.


"Schatzi saura kadan fa na gama. Ko baccin kirki bana yi saboda saurin da nake yi
na dawo wurinki."


"Ya za ka dena bacci sosai salon kaje kayi mistake a kara maka kwanaki ko"


"Ya Allah, yanzu yaya kike so ayi?"


"Ka rinka bacci, cin abinci akan lokaci da tunanin ina nan ina kuka saboda ba ka
nan"


Tamkar yasa hannu ya daukota ta cikin wayar haka yake ji "Do you miss me that
much?"
"Every second Hammana" ta amsa masa da murmushi.


"Ki kula min da kanki okay, banda kula likitoci kuma."


Dariya tayi mai sauti yana jinta har ransa "yanzu ko asibiti idan ba dole ba ai
bazani ba saboda ta kare min"


Shima dariyar ta bashi. Yana so yaji tace ta kare mata dinnan cikin shagwaba "I
love you Alheran"


Kalmar da har yau take yi mata wuyar maida masa a kunnensa kenan. Nauyi take ji
sosai sai dai ta kare da me too. Tun yana korafi har ya hakura.


"Chèri ka turo min hotonka amma yanzu zaka dauka please kafin mu tashi"


"Ba yadda na iya dake" yace sannan ya katse kiran. Shi ba ma'abocin daukar kansa a
hoto bane sai dole yanzu ma abokin aikinsa ya bawa ya dauke shi ya tura mata. Bayan
kamar minti biyar ta turo masa wani. Daukar kanta tayi tayi kyau sosai dimple
dinnan ya fito ta hada da nasa a photo college wani frame mai kyau. Akan hotonsa ta
rubuta Alheran Schatzi a nata kuma Awwab Chèri. Sun tafi zasuyi boarding ta sake
kiransa.


"Ka saka shi wallpaper dinka. Idan ka dawo zan duba. Yanzu zamu shiga kayi mana
addu'a. Yaya Arifah tana gaisheka"


"Whoa, ki dan tsaya mana in amsa kowanne kafi ki cigaba"


"To ai yanzu zamu tashi"


"Allah Ya tsare Yasa kiyi ki gama a sa'a kuma Ya sa mana albarka a ciki. Ki gaishe
da Arifah"


"Amin" tayi ta cewa har aka bada umarnin a kashe waya tana masa hira sannan ta
kashe.


Arifah ta kalleta tana murmushi "ba fa zaki rigani aure ba duk wannan lovey dovey
din naku sai na riga"


"Nima zan fi so babban yayan nawa kada yazo bikina yana gwauro"


Dariya suka yi tare kafin su dora hirar Yousuf da Awwab. Magana dai tsakaninsa da
Arifah ta kankama don yace ta fada a gida zai zo wurinta amma da

69 / 99