Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
Major ya ga Ibrahim ya dauko a boot yaji zuciyarsa ta karye Zainab tazo
zata taimaka su dora shi yace bari yasa hannu. Hadir ba kiba gareshi ba shiyasa ma
suke jin saukin daga shi din.
Sai da ya zauna Major ya dube shi da tausayawa "kai kuma taka lalurar kenan Hadir?"
"Baba baya magana"
Zainab ta share hawaye ta bude musu kofar gidan. Mami da Major mamaki ya kara kama
su da jin wai baya magana kuma.
Sai da suka zazzauna yaran suka sake gaishe su Zainab ta rike baki "yanzu Zahra da
Fauziyya ne haka? Ikon Allah, Inna Awwab din Mairama. Ita kuma wannan 'yan matan
kamar a tafi a barmin ita wace"
"Zayyanatu sunana" ta amsa da kanta.
Mami tana murmushi tace "Daddy yaso yiwa Zayyan takwara sai tazo a namiji"
"Allah sarki Mairamu da Zayyan ban san yaya suke ba"
Hadir sai runtse idanu yayi Mami da Major na kallonsa da ita. Mami ta daure tace
"ashe baki san Allah Ya karbi ran Zayyan tun a Liberia wurin ceton rayukan
mazajenmu ba"
A gigice tace "ME??? Baban Radhiya ya rasu? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Kuka suke yi sosai mazan na hawaye harda Major duk dakiya irin tasa. Zainab ta
tsahirta tace su Zahra da taga suna tayasu kukan su shiga dakinta bari ta aika a
siyo abinci don bata yi girki ba.
"Turasu kitchen kawai su dafo mana"
"Ayi haka ko ware gajiya basuyi ba. Naga alamun daga nesa kuke"
"Babu komai ku shige kitchen ku duka kowa tasa hannu"
"Ibrahim jeka sai ka nuna musu. Su dafa mana abin da suke so, ko motsi bana son yi
daga wurin nan"
Sun san dai wai wayo ake son yi musu. Suna yin hanyar kitchen din Ibrahim ya dawo
da baya ya labe sai ga Zayyana ita ma ta dawo kusa dashi tana kara kunnenta a jikin
kofa.
"Meye haka" ya dan sha kunu.
A shagwabe tace "Your mummy and daddy are making mine to cry"
Wane kallon sama da kasa yayi mata "sannu baturiya ai ni ya kamata nace haka"
Kunnuwansu Zahra ta rike su biyun Fauziyya kuma tace "ku rufe mana baki dalla can
muji me ake cewa sosai"
Duka su hudun suka sami wurin tsayawa suna jiyo labaran ban tausayi daga iyayensu.
Yadda su Mami ke kuka a falon haka suma suke yi.
Sun tausayawa juna sosai kowa da irin tasa kaddarar. Damuwarsu sai kuma ta karkata
kan Mairama da Radhiya.
Sun share kusan awa suna jajantawa juna sannan Mami ta dan bude murya "yaya ne
shiru babu ku babu abinci"
Zahra ce ta fara fitowa taje ta fada jikinta tana kuka.
"Kuji min yaran nan, labe kuka yi kenan?"
Zayyana ta gyada kai tana sababbin hawaye. Zainab tayi dariya "to yau kunji rayuwar
iyayenku ko"
Ibrahim ba kunya ya koma gefen Zainab kamar zai shige mata ciki yana kara son
mahaifiyarsa.
"Anya wannan zaiyi soja kuwa?" Inji Major
"A'a wallahi ni malamin makaranta zan zama." yace da dukkan gaskiyarsa.
Suna ta dariya Zainab ta dauko kudi ta bashi "kayi sauri ka siyo mana abinci tunda
labe ya hana ku girki"
Kwanan Radhiya biyu da yiwa gidan Ardo yaji tunda aka yi mata aski. Yaran dangi
sa'aninta duk Emzee ya fesa musu sai ta wuni suna zuwa gidan tsokanarta. Na yau
yafi bata haushi harda cire mata dankwali gashi Zakari dan gidan Baffa Habubakari
da take hasashen yana son ta yana gidan. 'Yar yayarsa ce ta cire mata kullin
maganin da take yi a kanta yanzu kunya ta isheta. Zakari sai ya rufe yarinyar da
fada ya fita.
Zaune take a daki tana kwafa don idan ta kamata sai jikinta ya fada mata, dazu ma
albarkacin kawunta taci kada abin kunyar yayi yawa. Muryar Baffa Gide taji yana
fada yana sanar da matarsa ya rasa taurin kan da yake damun Mairama. Maza sun fi
biyar masu neman aurenta amma kowa yazo sai tace wai ita makauniya ce. Yayi iya
kokarinsa ya samu makaho dan wani attajiri a cikin Giade mai mata biyu shine yaje
ya sanar da ita ta watsa masa kasa a ido.
"Na fuskanci yarinyar nan dama can fakewa take da makanta amma bata son yin aure"
"To banda abinka Malam ku kyaleta mana."
"Sai ta rayu babu aure? Yaran nan suna nasu auren fa zata soma jin shiru da
kadaici. Ni gata nake son yi mata amma taki gani. Fitowa nayi na barta tana ta
kuka"
Hijabinta ta figo bayan ta gama jin bayanin Baffa Gide tace zata tafi gida.
"Dena hararata ba kinji nace na barta tana kuka ba ni ban taba miki uwa ba"
Iyalle matarsa ta soma dariya don fuskar Radhiya a hade take.
" 'Yar soja a gaida gida"
Tana zuwa gidan ko dakin Innawuro bata je ba ta tafi wurin Umminta. Hotuna ne a
hannunta tana shafawa tana kuka. Babu mai sanin yanayin da zuciyarta take ciki sai
wadda ta tsinci kanta a irin yanayin. Zayyan ya tafi ya barta kuma babu wani
kwakkwaran bayani da zata kama taji salama a ranta game da mutuwarsa. Ko ranar da
ya rasu bata sani ba sai kiyasin lokaci da aka bata. Saurin daga pillow tayi zata
boye su da taji motsin mutum.
Radhiya ta rigata ta hanyar karba tana kallon iyayenta a ranar bikinsu.
"Ummi"
Share hawayen take da sauri kafin ta fara tsareta da tambayoyi.
"Meye, ba yaji kika yi mana ba mai kwal kwabo"
Radhiya tayi dariya duk da ta tsani askin. Tana son farantawa mahaifiyarta.
"Kaina yanzu fa yafi dadin wanka. Insa sabulu harda soso in dirje shi. Idan na
shirya na mulke abina da man kwakwar da Yadikko ta bani wancan zuwan da mukayi
Sumaila"
"Da kike ishi mutane da kuka harda yaji"
"Ba'a kyauta min bane...da kinga kan nan bazaki so ace nawa bane"
A hankali sai ga Mairama tana dariyar shiriritar Radhiya.
**********
Bayan kwana biyu da zuwan su Major Kano suka shirya harda su Zainab sai birnin
Shehu. Da yake Zainab 'yar gari ce dadewa bata sa ta manta hanyar gidan ba. Sun so
bata saboda gyare gyaren da aka samu kadan. Sojan da ake turowa kudi ya riga ya bar
garin ma ta banki yake turawa MaiKudi kudin.
Alhamdulillah gida ya cika da yara ko ta ina. Ibrahim yana tura Hadir gefensa Major
ne yana fada masa dawowar Awwab nan da kwana goma.
Matan ne suka fara shiga aka amsa musu. Sun gaisa Mami ta tambayi Jume wata yarinya
ta nuna musu dakinta.
"Fada mata abokan aikin marigayi ne da iyalansu suka zo"
Yarinya ta ruga sai gasu sun fito tare Jume tana musu marhabin da lale. Tabarmi uku
aka shimfida musu suka zauna aka gaisa.
"Jama'a ina kuka shige duk shekarun nan ba'a jin duriyarku?"
Kunya ta kamasu duk da kowa dai da nasa uzurin. Sun dan yiwa Jume bayanin da zata
iya fahimta Major yana dariya yace "ina Alheran ne?"
"Wai, 'Yar soja ai tana rugar Barkindo, da yake dai akwai bikin yayarta 'yar wajen
Mubaraka nasan suna tafe in Allah Ya so"
Kallon juna suka shiga yi sai Mami ta gyara tambayar "aka ce mana bayan Mairama
tayi aure ita ta dawo nan wurinku"
Itama nema suke su juya mata kai ta kwalawa Matar Badaru kira "kinji wai 'Yar soja
suke cigiya ni duk ban fahimci zancen ba, nasan Badaru yana ciki turo min shi ya
musu bayani."
Tsayawa tayi suka gaisa sannan taje ta dawo tare da maigidanta. Shima ya gaisa dasu
a mutumce Major yayi masa bayanin yadda suka yi da sojan da yake turo musu kudi
akan cewa Mairama tana gidan miji, Radhiya kuma tana nan.
Badaru ya rike baki abin da daure kai "Yallabai gaskiya ka binciki mutumin da yayi
maka karairayin nan tun wuri"
"Ban fahimceka ba"
Mami da Zainab har sun fara damuwa ganin yadda iyalan gidan su ka canja fuska su
ma.
Badaru ya gyara zama ya soma yi musu bayani "zancen da nake muku Mairama tayi
akalla shekara shida ko ma fi da makancewa, Radhiya da Zayyan kuma suna tare da ita
a can wurin dangin babarta. Sai dai mutumci irin nata wallahi har ila yau tana turo
mana yaran idan sun sami hutu"
Kuka wiwi Zainab da Mami suke yi. Zuwa yanzu sai dai su ce sun ga jiya sun ga yau a
auren soja. Makanta, yanzu ace Mairama ta makance babu ido.
A sanyaye Major yace "ban tari numfashinka ba, wane Zayyan kake magana a kai?"
Jume tace "Zayyanu karami kanin Radhiya"
Mami ta zaro idanu "aka ce mana ta haihu jariri babu rai"
A fusace Jume tace "wai uban waye ne da wadannan karairayin? Yarinya tana fama da
lalura da rashin miji anbi an dabaibayeta da karya. Rashin waiwayarta da kuka yi
yafi komai damunta, bata da masaniyar inda kowa yake cikinku gashi dangin ita
mahaifiyar Zayyanu suma shiru rabonmu dasu tun sunan 'Yar soja"
Zuciyar Major tuni ta kawo wuya ya daga waya zai kira dan sakon nasa sai ga Maikudi
ikon Allah. Su Maikudi an karo wulakanci yana shiga yana fita duk wata yana jin
'yan chanjinsa a aljihu. Saboda son zuciya ma sai ya dena 'yar fafutukar da yake
tunda dai albashin nan yana shigowa babu fashi.
"Yauwa Maikudi gara da Allah Ya dawo da kai da yanzu."
Idanunsa akan bakin ya kula akwai maiko a tare dasu "hee...hee baki muka yi a gidan
ne. Sannunku da zuwa."
Matarsa ya shiga kwalawa kira "ya naga babu ko 'yar mantina dinnan a gabansu?
Wannan ai halin karanta ne. Waye nan a cikin yaran azo a nemo musu abin sha mai
sanyi"
Ran Jume ya fara baci tace "to dan ayi jikan na'isa, mu duk bamu iya ba sai kai. Ni
zo ka jiye min baki ke neman Radhiya wai an fada musu a gidan nan take"
A take kuzarinsa ya fara raguwa "ki fada musu inda take su je mana"
"Mutanen nan fa abokan Marigayi ne, shi wannan yace ya dauki lokaci yana aiko da
kudi kuma ance a gidannan ake karba" Badaru ya kara masa haske
Abinka da munafuki gumi ya soma yi kamar an kwara masa ruwa "indai don Allah suke
yi sai abar tone tone su sake mata kyautar tunda sun dawo. Ni bari na shiga ciki na
gaji"
Wani irin kallo Major da Hadir ke yi masa. Ashe Jume ma tasha jinin jizkinta. Ai
kuwa bazata barshi ba indai haka ne. Kankace ido tayi ta kaurara murya
"Maikudi kada kace min kana da masaniya akan maganar da mutanen nan suke yi"
Ja da baya ya soma yi a tsorace "Ni kuma? Daga shigowata? Uhmm nayi nan akwai mai
son ganina a waje" kafin su farga ya fice da sauri.
Yau da ace Hadir na da lafiya Maikudi sai ya yabawa aya zakinta. Major ma tashi ne
dai baiyi ba amma ko ciki daya suka fito da Zayyan sai ya nuna masa yayi kuskure.
"Ku tashi mu tafi" yace dasu gabadaya.
Jume tana kuka matan gida da Badaru suna salati suke basu hakuri.
Babu alamun wasa a fuskarsa yace "Ku bani nambar waya da zamu nemi kwatancen inda
Ummin Awwab take. Shi kuma wancan kafin na turo masu kama shi a fada masa nasan iya
abinda na turo saboda haka ina bukatar kudin nan...da gaggawa"
Ransa yayi matukar baci ne yaki amincewa da masaukin da Jume tace ayi musu a gidan.
Giginya hotel suka yi masauki washegari sai ga Badaru da sassafe ya kira yace zaiyi
musu rakiya har Rugar Barkindo.
**********
Saboda yanayin matsanancin zafi da ake fama dashi yau gidan har Ardo suna zazzaune
a karkashin katuwar darbejiyar da ta yiwa tsakar gidan inuwa suna taba hira.
Yammaci ne na asabar Radhiya tasan cewa Zakari zai zo kawo wani sabon maganin ciwon
ido da aka rubutawa Mairama a asibitin Bauchi inda yake aikin lab wato dakin gwaji.
Gyaran nono ta gama wanda ta cire man shanu sannan ta je tayi wanka.
Shiryawa tayi cikin riga da skirt ta saka hijabinta iya gwiwa don zuciyarta tana
raya mata yau kawun nata zai fada mata abinda idanunta suke ganin yana
boyewa...soyayyarta.
Har kofar gidan Ardo aka rako su Major suka firfito kowa da nasa tunanin. A yayin
da rayuwa tayi ta garasu ita Mairama kauye ta fado. Kauyen ma ruga da abubuwan
cigaba suka yi mata karanci fiye da ko ina.
Fitowarsu ke da wuya sai ga Emzee nan da wani abokinsa sun dawo daga kiwon shanun
Ardo. Sanda ce a wuyansa amma shirt da dogon wando ya saka suna ta hirarsu ta
samari.
Ba Major da Hadir ba, hatta Mami da Zainab sai da gabansu ya fadi da ganinsa.
Wannan banda haske babu ta inda zaka ce ya baro mahaifinsa.
Kawunsa ya hango ya yi saurin barin abokinsa ya taho "Kawu Badaru yaushe ka iso"
"Tare da bakin Umminku nake. Yi maza ka shiga kayi mana iso"
Gaishe su yayi cikin gurbatacciyar hausarsu ta tsantsar fulani ya shiga ya fada
musu. Mairama ta auna ta auno ta kasa gane su waye zasu zo nemanta tare da Badaru.
Radhiya da ta tabbatar zuwan bakin zai hanata sakewa da Zakari ta shiga tura baki.
Innawuro tace tayi shimfida sannan aka ce su shigo.
Zainab da Mairama kowacce wai dakewa take yi kada suyi abin kunya a gaban 'ya'yansu
amma da sauri suka shiga gidan.
Mairama tana zaune akan tabarma ga sandarta a gefe ta yafa mayafi kalar kayanta.
Daga bayanta kuwa babu tantama Alheran Radhiya ce wadda ganin 'yan gayu suna
shigowa yasa ta manta da batun Zakari ta shiga washe baki.
Mairama tana ji Innawuro tana yi musu barka da zuwa amma yaran kadai ke amsawa.
Manyan kuwa Mairama suke kallo da take ta murmushi a hankali a zatonta babu mai ji
tace "Ke su waye ne sai kamshi nake ji"
Mami a gabanta ta zauna tana kuka ta kama hannunta da makanta bata hanata ayyuka
irinsu yin fura ba da nata lallausan hannun. Zainab kuwa a gefenta ta zauna ta
rungumo Mairama a jikinta. Rasa gane me yake faruwa ita da kowa na gidan suka yi.
Radhiya da ta kurawa Major da Hadir idanu ta saki ihu kamar an tsunguleta.
"Yasin Ummi na ganesu na hoton nan ne"
Mami tasa hannu ta shafa fuskar Mairama tace "Ummin Awwab"
Duk da bata gani sai da idanunta suka kara girma gabanta ya tsananta faduwa, baki
na rawa tace "Mami??? Ke duba hotunan akwai wannan a ciki?" Ta fada tana kankame
hannun Mami kamar zata kuma tafiya.
"Ai shikenan tunda baki ce a duba dani ba" Zainab tayi maganar da wasa cikin kukan
da yaci karfinta.
Mairama fashewa kawai tayi da kuka su ukun suka rungume juna suna hawaye sauran
jama'ar wurin suna tayasu mazansu da matansu.
[02/11 7:30 AM] My 2nd Mtn: 20.Mairama ta ga gata da ya amsa sunan gata a Rugar
Barkindo. 'Yan uwa ke tururuwar ganinta har ana fadan gidan wa zata zauna. Ardo
yayi tsalle ya dire yace matarsa ce zata dauka ai ita ce mace. Dole sauran suka
amince aka barwa Innawuro.
Idan manya ko dattijai cikin danginsu sunzo sai ayi ta kallonta ana cewa kaza dinta
irin na Mairo ne. Murmushi kawai take yi don ko hoton mahaifiyarta bata taba gani
ba. Sun tausaya mata da jin labarin rasuwar mijinta ga makanta.
Radhiya da Emzee sai gasu cikin 'yan uwa sa'anninsu ana ta nishadi. Abinci da nama
anci an ture. Kafin sati ya zagayo jikinsu ya fara nuna kwanciyar hankali da koshi.
Mairama kullum cikin godiya take ga Allah da Ya dawo mata da dangin mahaifiyarta.
Ba jimawa sabo ya kullu sosai a tsakaninsu baki daya. So da tausayawa suke nuna
mata da 'ya 'yanta. Ardo ke cewa su duka marayu ne ababen dubawa.
Bata cuci kanta ba ta roki alfarmar su Radhiya su koma makaranta. Tare aka nema
musu JSS 1 ita da Emzee da ya gama aji biyar. Ita a makarantar kwana ta gwamnatin
jaha ta mata shi kuma jeka ka dawo ta maza. Ranar da dan gidan Baffa Habubakari ya
kawo takardun tubure musu Radhiya tayi da kuka wai bata so.
"Karatun kike yiwa haka Radhiya?" Innawuro tace tana kokarin bata baki.
"Dama saboda bama cin abinci mu koshi ne fa Ummi ta kaini makaranta inyi kudi"
Mairama kunya ta isheta tasa hannu tana nemanta "haka muka yi dake? Kuji min
yarinya"
"Da naga ko nama bama ci irin na gidan Baba Kallamu shine nayi zaton haka ne" ta
mayar mata da amsa tana shure-shure.
"Idan bata yi ba ai ba'a kirata jikar Ali ba" Innawuro tace tana dariya.
Radhiya ta turo baki "Malamijo muke kiransa mu dai"
"Ina yaga malanta sai bakar rowa da mammakon tsiya"
"La la lahhhh baban Ummi ne fa"
Ardo yana jinsu yana rubutu a jikin allo yace "da kyau 'yar albarka ki kare masa
kinji ko. Duk tsiyar naka ai naka ne Innawuro"
Dariya rigimar Radhiyan ke bata tace "kasan ni ba bakuwar zafi bace Allah Ya baki
hakuri. Nima kizo na baki labarin 'yar uwata Mairo. Ga kyau ga kirki kamar wata dan
daren goma sha hudu"
Idanu Radhiya ta bude sosai da mamaki "wata dai irin na sama Innawuro?"
"Akwai wata a kasa ne?" Mairama ta fada tana jin kamar ta mangareta.
"Tabdi, Ummi kenan Innar taki a mulmule take kamar wata. Ga Malamijo kamar tsolon
rake. Mu dai Allah Ya taimakemu ke daidai kike."
Mairama ta fusata ta fara wawurarta "Karami dauko min yayarka ko ka janyo min ita.
Yau tambotsan nata harda iyayena kuma"
A guje ta tashi "Ardo don Allah ba Innawuro ce ta fada ba."
Innawuro ta dauko muciya "bari na mulmule ki kema sai aji dadin kiranki jikarta"
Hanyar waje tayi tana gudu wai ita gidan Malamijo zata koma.
Mairama ta daure fuska "da ya fi miki mu ma mu huta. Kuma karatu ki ma fara shiri
sai kinyi"
Dawowa tayi da baya tana murza yatsan kafarta a cikin kasa tana tura baki "to don
Allah ki kaini soja irin na babana indai kina so nayi karatu"
Gaban Mairama ne ya fadi ba shiri sai ga hawaye. Innawuro da ta dauki abin wasa
tana biyewa Radhiya ta shiga bata hakuri tasan bazai wuce mijinta ta tuna ba.
Radhiya ma sai ta soma kuka tana cewa tayi hakuri zata yi karatun ko wanne ne.
**********
Alheran Radhiya Zayyan Tureta irin fitinanun daliban nan ne marasa tsoro ga kin ji.
Duk inda akace 'yan aji daya sunyi laifi to in sha Allahu Radhiya tana cikinsu. Kan
kace kwabo tayi kaurin suna tsakanin dalibai da malamai. Kirikiri tace sunanta 'Yar
soja haka babanta yake kiranta daga Mairama ta bata labari. Shikenan makaranta suka
santa da wannan sunan. Anyi sa'a tana dan taba karatun babu laifi.
Wata rana suna layin dibar ruwa suna ta hayaniya irin ta 'yan makaranta ta dage
tana ta zuba.
"Allah Ya kaimu siniya wallahi zan warwasa a makarantar nan. Duk wasu jiniya a
lokacin sun shiga talatin a hannuna"
Kawarta Ruqayya tace "ke 'Yar soja so kike yadda muke tsinewa su senior Jummai kema
a tsine miki?"
"Ke baki gane ba. Lokacin kannen su senior Jummai mai tafiyar agwagwa ne a
makarantar. Ramuwa zan zauna yi"
Wata tace "ai kuwa nima zan so, rannan fa kwai tace nayi mata a karkashin gadonta"
Radhiya ta daka tsalle "inama nice wallahi, na samu na sassaka mata kashi mai
waaaaaari"
Dariya suke duniya sweet kampo sai ga senior Jummai ta taho da tafiyar catwalk
dinta da su Radhiya suke yiwa lakabi da tafiyar agwagwa. Ta gama jinsu tsaf suna
bayan ginin da famfon yake.
Idonta ya kyallo mata ita sai kawai ta canja hirar amma saboda tsoro muryarta har
rawa take yi.
"Allah Yasa senior Jummai tace in zama daughter dinta a makarantar nan. Daga ranar
wanki da