Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
yi dafifin
kare shugabansu. Mutum uku ne suka fito daga motar wata shadda suka saka iri daya
ruwan zuma mai dan karen tsada. Dinkinsu da komai hatta hula da takalmi basu
bambanta ba. Suna fitowa aka fara daukarsu a hotuna tun kafin su karasa ciki. Uban
gayya ne Major General Zayyanun dan mutan Sakkwato yana ta murmushi kamar shine
angon. Har yau da yake shirin aurar da 'ya bai dena tafiya da hankulan mata ba.
Daga gabansa rike da wata sanda mai kyau domin samun balance din jiki Daddy Rtd
Major Mustapha ne mutumin Katsinan Dikko kunya gareku ba tsoro ba. Kamilin mutum
msi tafiyar da komai cikin tsari da haiba. A bangaren damansa kuwa aminin kwarai ne
wanda abotarsu ta zame musu 'yan uwantaka Rtd Lt Hadir gaisuwarsa daban take
jinjina ga dan mutan Kanon Dabo mai dutsen Dala da Gwauron dutse, Kano ko da me
kazo an fika. Hadir Murtala abokin da Zayyan Tureta wadanda sukayi zamani a
matsayin zaratan jaruman samari kyawawa. Su ukun nan tarihin rayuwarsu abin duba ne
domin kada duniya ta manta da soyayyarsu da sadaukarwa domin kasarsu domin
abotarsu. Taku suke maza 'yan uwansu na waigensu domin sun isa a dube su din. Cikin
masallacin suka shige ana ta gaisawa da 'yan uwa da abokan arziki.
Daga waje mintuna kadan bayan shigewarsu wata motar ta iso Awwab ya fito rike da
waya a hannunsa yana sanye da shadda fara kal wadda aka yiwa aiki da zare ruwan
toka msi duhu. Hula da takalminsa kalarsu daya da zaren sai agogo da links din
hannun rigar duka silver masu kyau. Saboda kurewar lokaci ranar da zai taho yayi
aski saisaye aka yi masa wani irin gyaran fuska da ya fito da gajeren kwata miliyon
dinsa. Matashi ne ajin farko mai tattare da nutsuwa da kamala. Kallo daya za ka yi
masa kasan cewa yau din ta dabance a wurinsa ranar aurensa da Alheran dinsa. A
gefensa angon jiya ne Yousuf bayansu kuma Emzee da Ibrahim sanye da wani ubansun
yadi da Mama ta dinka musu. Su dinma kamar iyayensu daga sama wato hula har takalmi
babu ta inda su ka bambanta komai. A tare dasu Halifa ne shima ya fito fiye da
zato.
A cikin masallacin kuwa wakilan ango da amarya aka nema Hadir da Zayyan su ka matso
gaban limanin suka zauna a kusa dashi. Yadda yake a tsarin musulunci haka aka
gabatar da komai inda Hadir waliyin amarya ya karbi sadakinta naira dubu dari daga
hannun Zayyan waliyin ango. Addu'a aka yi aka shafa Captain Muhammad Awwab Mustapha
ya zama mijin Alheran Radhiya Zayyan Tureta.
Hamdala ya rinka yi babu tsayawa a lokacin da yaji kammaluwar komai Schatzi dinsa
ta zama tasa halak malak. Hotuna ake ta yi da gaishe gaishe na 'yan uwa da abokan
iyayensu. Malamijo da tawagarsa kadai sun isa gayya. Gidansu Zayyan aka wuce ya
sakarwa 'yan uwansa da matansu Badaru ragamar girkin da za'a ciyar da mutane kafin
su tafi. Da farko Mairama yaso su zo su kwana a garin domin yin abincin ita kuma
tace dama ce ta nuna musu yana kaunarsu kuma ya yarda dasu. Ai kuwa basu bashi
kunya ba domin kowa yaci ya sha anyi abu cikin girma. Kuma sai da Baban Arifah ya
samu yazo shima duk da mutanen da ya baro a gida. Maikudi ne dai idan akwai namijin
mujiya to shi ne a wannan taron. Yana ta rakubewa a gefe Zayyan sai ya dauke kansa
kawai. Daga baya ya ga bai da amfani nunawa duniya akwai baraka tsakaninsu shiyasa
ya koma sako shi cikin al'amuran. Da yace Maikudi kuwa sai ka ganshi da mugun sauri
ya taho.
Ba su suka sami saukin kebewa daga mutane ba sai lokacin da ya idar da sallar
la'asar. Yana zaune da 'yar cikinsa ya ajiye babbar rigar da hula can gefe. Bayan
doguwar addu'a ya dauko wayarsa ya turawa Radhiya text din da yake ta son yi tun
bayan an daura auren.
(Ina hukuncin matar da bata daukar wayar mijinta? Ki fada mata Awwab ya zama na
Alheran kuma ta shirya karbar punishment dinta na share shi).
Hira suke yi da Fauziyya da Zahra rabi suna tsokanarta rabi kuma shawarwari ne suke
bata tunda yanzu itama girma yazo. Ita dai jiki yayi sanyi kamar ba ita ba. Wani
abin tayi dariya wani kuwa sai dai taji kunya idan sun fada amma ta kasa magana.
Duk da ba bikin bane ya taso amma gidan ya rude don ma anyi sa'ar kawowa Ummi masu
aiki biyu 'yar dattijuwa da kuma mai sauran kuruciya.
Sakon Awwab ta karanta suka ga murmushin nata ya koma na daban.
Fauziyya ta dago wuya zata leka wayar "Ango ya miko gausuwa kenan...mu gani me
yace"
Janyota Zahra tayi "ina ruwanki, idan kin matsu kiji me yace nemi naki mijin tunda
suna tare kema yayi miki text din. Radhiya tashi ki koma daki kiyi magana da
mijinki kinji"
Kasa mikewa tayi Fauziyya ta cigaba da zolayarta sai da Zahra tayi da gaske don ta
kula jikin kanwar tasu mai sabon mukamin matar yaya yayi mugun sanyi. Tana tafiya
Fauziyya ta tallabe kanta da hannu biyu.
"Jikin ta kanwa yayi la'asar fa Sis. Duk surutunta kinga fa bakin ya mutu. Allah
sarki irin matsoratan amaren nan za'ayi"
"Tausayinta kike ji ko tsokana?"
"Tausayin dai...hmmm kazo kayi ciki ka rasa inda za ka tsoma ranka kaji dadi"
Tuntsirewa da dariya Zahra tayi ta gano Fauziyya laulayi ne yasa ta a gaba shine za
ta saka mutane itama.
Bayan Radhiya ta koma dakin babu kowa. Gefen da tayi sallah ta kalla ta tuna
nasihar da Mama tayi mata a wurin bayan ta umarceta da tayi nafila ta godewa Allah
bayan an daura auren. Wata irin soyayyar Awwab take ji tana kara shigarta sosai ta
lumshe idanu ta kwanta sannan ta kira shi.
Sautin numfashinsa ne ya sanar da ita ya dauka amma yaki yi mata magana shima nata
hawa da saukar numfashin kadai yake sauraro wanda ya kara masa gudun bugawar
zuciyarsa.
Ita ta fara kartse shirun nasu ta hanyar gaishe shi da tattausar murya "Hammana ina
wuni"
Da kyar ya iya hada kuzarin amsawa yana jin kamar yau ya fara son ta "Matsoraciya
yaya kike?"
"Tsoron me nake yi?"
"Daga kinji nace zaki karbi punishment shine kika dawo daga strike din yi min
magana mana"
Kamar yana gabanta ta tura baki "to ba kaine ba"
Katseta yayi don yasan fushin har yanzu na menene "Ko ba ni zan aureki ba kinsan
bazan yi missing aurenki ba bare kuma Alheran din ta Awwab ce"
Kunya taji sosai yayi murmushi ganin yau ita ce babu baki "wai ni tun yanzu ina
bakin naki ya koma ne? Anya zamu shirya da wannan amaryar kuwa wata bebeya nan da
ita"
Ibrahim ne yayi masa alama da hannu motocin da zasu kwashesu sun iso. Ba yadda ya
iya sallama yayi mata yace tayi musu addu'a gasu nan fitowa zasu taho. Kafin su iso
anyi abinci sosai jiran isowarsu kawai akeyi. Kowa yaci ya koshi kuwa sai son barka
aure ya yi albarka sai fatan zaman lafiya ga sababbin ma'auratan.
A gajiye su ka dawo ana sallar isha kowa sai bacci. Angwayen biyu, Raji da Bilal
suna gidan Mami. Ibrahim da Emzee kuwa gidan Mama. Daya ga wata ta matso babu
lokacin zama babban taron da ake ta jira ne Allah Ya kawo shi. A haka ma da ba su
ne suka shirya ba basu da zama balle kuma na washegarin da yake nasu.
Dadin abin ma kuma domin tallata shirin Radhiya Baban Arifah ya samu yace a saka
wani bangare nashi a wurin taron tunda shugaban kasa zai je. Ita kuma sai ta
gaggauta sanar da Supervisor dinta domin ta nema mata izini. Kwana biyu a tsakani
matar ta fada mata cewa su uku an wakiltasu zuwa su gani sannan su tayata murnar
dawowar mahaifinta. Ranar kwanan murna tayi sai gashi ana gobe taron sun iso. Duk
wannan lokacin angon nata yayi wuyar gani suyi nan suyi can saboda ganin sun
kammala komai bisa tsari yadda suke so.
Malamijo da kansa ya hada mutum biyar cikin masu zuwa taron daga gidansa a yara sai
kuma Yadikko da Hajjo. Shatar mota yayi musu ana shirin tafiya sai ga Salame niki
niki da kaya ita da yaranta wai itama zata je. Ba wani abu bane ya tunzurota kuwa
sai labarin da ta samu na cewa Rahima ashe ta bi Mairama. Zuwa zata yi har gidan
taci mutumcin yarinyar tunda tana son nunawa makiyanta cewa bata isa ba. Abu na
biyu kuma so take taje ta ganewa idanunta wace irin rayuwa Mairama da Zayyan suke
yi da akaje daurin auren 'yarsu a Sakkwato aka dawo ana zuzuta taron da angon da
Radhiya ta dace da shi. Malamijo bai hanata zuwa ba amma da karamar 'yarta kadai ya
yarda taje sauran ya turasu cikin gidansa.
Tunda aka shigo garin Abuja bakin Salame yaki rufuwa tana ta kalle kalle. A tasha
dreban ya tsaya aka tura wani dreban daga gidan yaje ya taho dasu. Nan fa cikin
Salame ya duri ruwa ganin sojoji da bindiga tun daga bakin gate din wani irin katon
gida mai kyau. Jikinta yayi sanyi kalau ba ta fatan ace wannan ne gidan Mairama.
Bata gama tunanin ba kuwa aka wangale gate din gidan. Wani bacin rai taji ya tuko
ta da fa yanzu gidan nan nata ne ba don bakincikin da Mairama tayi mata ba. Suna
shiga Ummi da kanta ta fito tarbarsu da murnarta tare da Rahima wadda tun safe da
tace mata Malamijo yace da Salame za'a taho jikinta yayi sanyi. Ummi tana kula da
duk motsin yarinyar kuzarinta ya ragu sai kayi mata magana bata ji ba saboda
zulumi.
Ashe kuwa ba a banza ba don suna saukowa daga mota da ta tafi da murnarta saboda
tana son Umman nata taje ta durkusa har kasa tana gaisheta. Kusan hambareta Salame
tayi kafin ta dangwara mata yarinyar da ta kai shekara uku tana wani irin wari.
"Ki wuce da ita ki gyara mata jiki tayi kashi sannan ki bata abinci "
Jiki na rawa Rahima ta karbi yarinyar da kafarta da komai amma dole ta dauketa ta
wuce Ummi ta shiga ciki. Itama Ummin ba ta niyar koyawa Rahima rashin kunya dole ta
bi umarnin mahaifiyarta. Sakin fuska tayi tana musu maraba. Salame tana ta wani
basarwa ita bata ga abin burgewa ba har suka shiga ciki. Tun daga katon falon zaka
san gida ne na wanda ya isa duniya take damawa dashi. Dakunan da zasu zauna ta nuna
musu da kanta su Radhiya suka zo gaishesu ita da Zayyana da Hibbah wadda tayiwa
gidansu kaura duk da cewa Maman tasu tana gari. Duj inda 'yan mata suka hadu sunfi
jindadin kasancewa tare musamman idan tasu tazo daya.
Rahima wanka ta shiga yiwa kanwarta Khadi yarinyar tana ta yi mata rashin kunya
"Ki dena tabani"
"Kin kona ni"
"Sai na fadawa Umma"
"Ni ki bani sabulun da kaina dan wanke"
Radhiya tuni ta hasala ta fada bandakin tace Rahima ta fita ta karbo mata kaya.
Wani irin kallo ta yiwa Khadi yarinya ta bare baki za tayi kuka ta daure fuska
"kina yi min kuka zan cillaki ta taga kowa ya huta mara kunyar kawai"
Yadda bata ga alamun wasa a fuskar Radhiya ba sai ta hadiya kukan dama na samun
wuri ne tayi mata wanka kamar tayi amai ace yarinya kamar wannan tana kashi a wando
ga wani kai a daddage babu gyara anyi kitson roba da yawa sun warware. Zuge sauran
tayi ta zuba mata shampoo akan ta soma kukan sai ta fadawa Umma saboda bata yarda a
taba mata kai ko Salamen sai tayi ta lallabata tunda tana ji da ita. Radhiya bata
sake bi ta kan rarrashi ba sai da ta wanke kan nan tayi mata wankan.
A kasa kuma Rahima dakin da suke taje a gaban Salame ta durkusa tace a bata kayan
Khadi.
"Kin wanke wadancan ko kuwa ni zaki kawowa na wanke?"
"Yanzu zan wanke Umma"
Hajjo tuni ta fara zuwa wuya a kufule tace "Salame idan kinsan zuwa kikayi ki
tsangwami yarinyar nan ina mai tabbatar miki yanzu zan kira Malamijo a mayar dake
gida. Shashancin banza da hofi kai. Rahima ga jakarta can bude ki dauka"
Ummi tana wurin ita abin na Salame yanzu tausayi ne take bata saboda ta hana kanta
sakewa ta hana wasu. Rahima da ta duba kayan ashe na babbar Salame ta dauko garin
haushin an hanata zuwa da dukkansu. Rigunan sunyi girma haka dai ta dauki wata riga
zata saka mata ga pants din duk na babbar. A kanta Salame ta huce haushin rashin
dauko kayan daidai tana ta yi mata fada saboda bata san yadda zata yi ba.
Ummi ta kada kai "Rahima anjima bayan magariba kizo na aikeki dasu Zayyana"
"To Ummi" tace a sanyaye ta fita.
Tana cikin hawa benen Emzee na saukowa a gurguje yake tafiya suka kusa karo tayi
saurin matsawa gefe. Idanun nan nata ne suka sauka a kan fuskarsa wadda a take
murmushi ya maye gurbin bacin ran da ya sauko dashi saboda ganin Salame da yayi a
cikin tawagar 'yan Sumaila.
"Kawar Soja daga ina?"
"Ni dai ba kawarka bace"
Murmushi yayi ya nade hannuwansa a kirgi ya tsare hanyar wucewarta "nima ba
kawancen kawai nake so ba harda...."
Da sauri ta dago gabanta na faduwa "harda me?"
Kansa ya dukar daidai fuskarta "harda idanun Rahima...zan samu?"
Rikicewa tayi ta samu ya dan matsa ta kwasa a guje yana ta cewa tayi a hankali kada
ta fadi. Sai da ya ga ta bace masa ya dan rankwashi kansa "Muhammad Zayyan kalau
kake kuwa?" Ya tambayi kansa don ya rasa yadda akayi idan ya ganta daga bugun
zuciya sai kasa controlling kansa da bakinsa da yake yi. Kai ya girgiza ya sauka ya
dauki mota ya fita.
Bayan magariba kuwa Ummi ta bawa Zayyana dubu ashirin da biyar tunda ita ce babba
tace dreba na jiransu su siyowa Khadi kayan sawa kuma kada su manta da takalmi,
pants da brush. Sahad ya kaisu suka kwaso kayan da ya dace. Rahima tana da wata
dubu daya cikin kudin da Ummi ta basu rannan suka siyo kayan kwalliya ta sayawa
Khadi packet din ribbons na dari shida za ta yi mata kitso sai ta saka mata. Gida
suka wuce da murnarta bayan sun nunawa Ummi tasa musu albarka ta wuce ta kaiwa
Salame. Ba karamin dadi Salame taji ba don bata da komai sai dari uku amma dayake
ta saka hassada da kyashi a zuci sai ta kyabe baki.
"Ki fada mata ina komawa gida zan turo mata kudinta don nafi karfin cin arzikinta
yanzu ma don na manto jakar ne kuma a ciki kudina yake"
Tashi Rahima tayi zata fita Salamen ta kuma kiranta "ina kuma zaki je? dawo nan ki
kwanta kusa dani"
To ai ko numfashin kirki bazata iya ba bare bacci a gabanta a tsorace take sosai
Yadikko ta kama hannunta ta kaita bakin kofa ta ce ta wuce wurin yayarta Radhiya ta
rufo kofar. Tana dawowa tasa hannu ta dauke Salame da wani gigitaccen mari. A
kidime ta dago kai ga kannenta don ma Khadi tayi bacci. Hajjo tace tayi mata
daidai.
Rai a bace sosai Yadikko ta nunata da yatsa "ba ni na haifeki ba Salame amma ina
tsammanin rikon da nayi miki ya bani matsayin uwar da ta isa dake. Nayi miki
rantsuwa daga yau har mu tafi idan kika sake yin wani abu domin cusgunawa Mairama
ko Rahima sau naci mutumcinki la'ada waje. Mutuminyar banza wadda bakinciki ya yiwa
tsatsa a zuci."
"Shiyasa taki gaba taki baya babu wani cigaba a rayuwarki" Hajjo ta kara da nata.
Sunyi mata tatas don sai da tayi hawaye Yadikko ta kyaleta tana jin zafin wannan
mummunar halayya ta Salame yarinyar da a da can tafi kowa shiru shiru a gidansu
ashe macijin sari ka noke ce.
Da rana Ummi ta bawa Yadikko katinsu na shiga wurin taron haka ma ta baiwa Tante
wanda zata bawa nasu mutanen. To dayake dama da yawansu sun zo ne akan ainihin na
gidan ba wannan ba da gwamnati ko muce sojoji suka shirya ba sai ba'a sami rikici
ba. Katin ba yawa garesu ba kuma dai bazasu so suje su bawa kansu kunya ba. An gama
hada masu tafiya su Mami suna gidan Emzee tun safe da yasa kafa ya fita basu sake
ganinsa ba.
Kafin sallar magariba sai ga Arifah da Mom dinta da gudu suka rungume juma ita da
kanwarta Radhiya. Matar Alh Salisu itama ta iso aka fara shirin fita domin karfe
takwas za'a fara taron.
Sai da Ummi ta shirya mijinta bayan kyakkyawar kulawar da ya samu tamkar kada ya
tashi saboda yadda yake jin matar tasa a rai. Sababbin kayansa da suka dace da
mukaminsa ta taimaka masa ya saka ta saka masa sabuwar farar safa da bakin
takalminsa tafiyayye cover shoe. Ya sake gyara fuska sai wani annuri yake fitarwa.
Sai da ta kammala dashi sannan ta fita itama ta shirya don tare zasu tafi.
Lace ne ta saka army green da digon gold a jiki. Mai kwalliya Mama ta dauko amma
aka ce tayi mata matured kwalliya ba mai cika fuska ba kamar karamar yarinya. Tayi
kyau matuka ta fito a Mairama Fillon Zayyan babu wata makusa sai hassadar makiya.
Mayafinta gold ne sai takalmi heel da wata karamar dinner pause itama gold ga farin
gilashinta ya sake fito da kyakkyawar fuskarta, hannuwa da kafafu sun sha jan lalle
mai kyau da tasa 'yarta Rahima tayi mata. Matan manya ne suka fito ita da Mami,
Mama, Tante, Mom din Arifah da Matar Alh Salisu.
Fita suka yi kowacce ta shiga motar mijinta abin gwanin ban sha'awa sojoji na mara
musu baya. Mutum biyu aka kara daga Nijar sai kuma Mubaraka yayar Zayyan da matar
Badaru. Yadikko kuma ta bawa Salame, Ayuba da Bature kati don Laila ita dama tuni
Ummi ta bata nata tana tare dasu Radhiya ana ta shiri.
Kowa ya gama nasa shirin suka fito Radhiya ta saka wata abaya mai masifar kyau da
daukar ido ja da bakaken stones. Covershoe mai madauri ta saka baki sai purse da ta
saka wayarta da hoda. Duka dama abayar suka zabi sakawa sai dai kowa tata daban.
Ummi ta fito da 'yarya Rahima don itama ta saya mata wata baka mai duwatsu pink.
Idan kaga matan sai ka juya ka kara babu wadda bata yi kyau ba. Jawad da Femi a
gida aka barsu saboda taron babu yara suka fito aka shiga motocin da suke jiransu.
Mazan ma ba'a barsu a baya ba sun hade duka cikin suits kamshi na dukan kamshi su
ma suna gamawa sai Nicon Hilton inda za'ayi taron a wani babban dakin taro da yake
cikin hotel din.
Decoration din wurin komai green ne da white an kawata shi fiye da zato ga
ma'aikata a tsaye suna jira a shigo su nunawa kowa seat dinsa saboda akwai number a
jiki. Awwab da Yousuf a matse suke da ganin amarensu abin takaici number din seat
dinsu ya nesanta su da juna. Radhiya wata faduwar gaba taji da suka hada ido yana
zaune kusa da Yousuf rike da waya a hannu. Ya hade cikin three piece armani suit
khaki color da coffee coloured necktie ga brown din cover shoe. Daga inda yake a
zaune ya daga wayarsa ya dauketa a hoto ta sadda kanta kasa a kunyace su Zahra suna
mata dariya.
Bayan an zazzauna kamar