Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
da ita abu guda ne ya janyo hakan. Nasiha da jan kunnen da ta yiwa Rahima ya
sake ninninka girmanta a idon Salame. Cikin hikima da sanin ya kamata take nuna
mata ta ajiye komai tayi karatu. Ga mamakin Salame har ji tayi tana cewa,
"Karami ba autan maza bane kada ki bari tun ba ku daidaita ba ya san cewa kina son
shi haka. Kuma kada ki sakawa zuciyarki lallai sai shi, rayuwa bata da tabbas, kiyi
kokarin inganta rayuwarki da ta iyayenki da kuruciyarki"
Kunya sosai Rahima ta ji. Sai yanzu da maganganun Ummi ta soma rarrabe abubuwa ba
kamar da ba da ta afkawa soyayya da ka babu wani ilimin sanin duniya. Ummi uwa ce
ta gari kuma mace da ta san girman zumunci. Ba don zumuncin ba Allah kadai Ya san
irin rayuwar da za tayi da 'ya'yanta. Mutane da dama sun taimaka mata albarkacin
zumunci ba ta da dalilin kin kwatanta alkhairi bayan itama anyi mata.
Da Zayyan ya dawo Salame har kasa ta durkusa ta gaishe shi ta kuma roki gafararsa
wannan karon da zuciya daya take yi saboda duk abinda zai kawo hawaye a idanun
Rahima gudunsa take. Kwananta biyu ta tattara ta koma da shatara ta arziki daga
wurin Mairama. Rayuwa bata da tabbas, yadda ka dauketa haka za ta zo maka.
Rayuwarsu ta cigaba da tafiya gidan Mami shiru da ga ita sai Zayyana su Fauziyya an
koma Katsina, Zahra kuma rana daya ma su ka tashi da su Awwab sun koma Germany.
Ibrahim yana Kano, Emzee a Kaduna kowa ya cigaba da harkokinsa.
***********
Zaune suke a cikin jirgi kamar Radhiya za ta shige kirjinsa ta dora kan ta a
kafadar Awwab, yatsun hannuwansu na sarke da juna yana yi mata rada a kunne tana
dariya.
Dago kai tayi tana tura baki "ka ga bana so"
"Ni ina so baby, ina jira ki kirani bayan na koma ki tabbatar min kawai"
Gabadaya zancen ma kunya yake bata so take a canja wani. Ta yaya zaiyi ta cewa wai
yana jin tana da ciki zai fara siyayyar haihuwa tun yanzu.
"Wane suna kike son mu saka kinsan tun yanzu zamu fara shawara"
"Kai Hamma wai me yasa kake min haka ne. Ni wallahi kunyarka nake ji"
Ido ya bude yana mata wani irin kallo "Really? Da gaske kunyata kike ji with all
the......"
"Shhhh" tayi saurin rufe masa baki da hannunta ya rinka cizon cikin hannun sai da
ta dauke tana kai masa duka.
"Ke ce da wani abu za ki hanani fadar gaskiya"
"Ni dai mu bar zancen nan ko na canja seat"
Alamun zip ya yiwa bakinsa ya koma ya narke mata jiki tana biye masa suna hirarsu
ta masoya. Kwanaki goman da su kayi a Greece sun kafa tarihi a rayuwarsu domin kuwa
sunyi su ne cikin kulawa da tsantsar kaunar juna. Kowa kokarin zarta dayan yake
wurin kyautatawa ga shakuwarsu ta kara karfi kusan komai tare suke yi. Wani lokacin
sai su cinye rabin dare suna hira kawai da bawa juna labarai. Yawo kuwa anyi kamar
kafafu zasu tsinke.
Shiru Radhiya ta ji Awwab ya dena magana ashe bacci ne ya kwashe shi. So da
tausayinsa take ji saboda idan sun sauka a Abuja yau jibi da yamma zai tafi. Sabon
da su ka yi da juna a kwanakin su tare yayi karfin da ba karamin ji zasuyi a
jikinsu ba idan sun rabu. Gashi zaiyi a kalla sati uku ko hudu kafin ya sami kansa.
Saboda tsarin aikin nasu mutum zaiyi aiki na wasu awanni ne masu yawa sannan ya
sami break wani ya karba. Haka suke yi shiyasa su kan dauki kwanaki ko watanni
batare da iyalansu ba. Kullum suna tare kamar cingam idan tayi nesa dashi bata san
yadda zasu ji ba. Hannunsa ta kara damkewa a hankali itama bacci yayi gaba da ita.
Sanarwar saukar jirgin cikin mintuna kalilan ne ya tashesu. Radhiya ta gyara
fuskarta ta gyarawa Awwab wuyan rigarsa da ya lankwashe su ka jira saukar jirgin.
Dreban Daddy ne yazo daukarsu tare da Zayyana da Rahima wadanda su ka kankame
Radhiya suna murna. Anje shiga mota Awwab ya ja Radhiya gefe.
"Schatzi ki rage tsallen nan kada ki taba lafiyar ajiyata" yayi maganar yana kallon
saitin cikinta.
Dariya ta yi "Na shiga dari Hammana idan ya zama gaske za ka barni na sakata na
wala kuwa?"
"Sosai ma, indai ba zai dami babyna ba"
Gidan Mami su ka wuce Radhiya ta sami kanta da matsananciyar jin kunyarta kuwa.
Mami ta taho da murnarta za ta rungumeta ta zube a kasa tana kwasar gaisuwa.
"Kaniyarki Radhiya, surukar ki na can Maitama" tayi nuni da kofar gidan tana nufin
Ummi "zo nan in gani idan ya kula min da ke yadda ya kamata"
"Mami ni zaki fara dubawa ko tana kula dani" Awwab yace yana zama a hannun kujera.
"Waye yake ta katon mutum kamar ka? Zayyana dauko musu mukullinsu aje a huta
abincinku ma yana can"
Duk wani nauyi ya kama Radhiya da kyar ta iya tashi bayan Mami ta matsa mata. Suna
fita su ka shiga gidan Mama Radhiya ta dauki DK yaron sai girma yake karawa ga
wayo. Da murna ta rungume Maman ita kuwa baki yaki rufuwa ganin 'ya'yan nata sunyi
shar da su gwanin ban sha'awa. Abincin da ta dafa musu ita ma su Rahima sun kai
musu nasu gidan.
Awwab ne ya bude kofar yana rike da hannunta "finally we are home...shiga da kafar
dama kuma kiyi addu'a"
Umarninsa ta bi su ka shiga tare. Numfashinta ne ya tsaya a bakinta saboda irin
dukiyar da mahaifinta ya narkar a falon kawai. Awwab ne ya ke janta sai da su ka
shiga kitchen, store da dakunan gidan guda uku wanda daya da yafi kusa da kofa falo
aka maidawa Awwab saboda baki maza.
Wanka da salloli su ka gabatar sannan aka ci abinci. Ranar kafin tara sun kwanta
jiki kamar anyi musu duka. Washegari ma kafin fa dora komai an kawo daga gidajen
biyu shiyasa ba ta dafa komai ba. Gidan Mami da Mama suka je su kai musu tsarabarsu
sannan su ka wuce gidan Ummi.
Daada baki yaki rufuwa ya ga Alheran dinsa ta kara kyau ta ciko.
"Awwab me kake bata ne?"
Kunya ta kama Awwab ya sunkuyar da kai. Ummi tana ta jansa da hira sai ya kasa
sakin jikinsa. Radhiya ta rinka masa dariya saboda itama sai da ya tsokaneta wai ta
gama hada shi da jambaki ta kasa kallon Mami. Ya san dariyar ta meye shiyasa ya
rinka harararta. Falon sama su ka koma ita da Ummi ta dame ta da tambayar wai don
Allah Yaushe za ta haihu.
"Wai ke ba kya jin kunya ne? Da girmanki kinyi aure mamanki za ta haihu kamata yayi
ko maganar kika ji ki gudu" cewar Ummi
Wata jaka mai kyau irin ta babies Radhiya ta daukowa tana cewa "Humm uhmm...da ga
wannan ma ki haifo wani ina so ni dai"
"Allah Ya tsareni ke dai kuje kuyi mun bar muku a haifa mu goya"
Abinka da sarauniyar shirme budar bakin Radhiya sai cewa tayi "Kinsan Hamma yanzu
kullum addu'a yake wai Allah yasa ina....." tunowa tayi da tabargazar da za ta
tafka ta tashi da gudu "na shiga ukuna Ummi baki ji ba ko"
Mairama dai dafe kai tayi sai da ta ji alamun ta sauka kasa tayi murmushi. Ance
hali zanin dutse gara ta dena damun kanta da yawan damuwa idan tayi wani shirmen.
Dadinta daya yadda Awwab yake sonta a hakan ta. Allah Ya kara musu zaman lafiya da
fahimtar juna tace a zuci. Jakar ta dauka baka ce 'yar madaidaiciya mai kyau ta
farke ledar da aka nadeta. Gefe ga aljihu hudu biyu a gaba da baya sai kuma wurin
zura feeder da karamin flask. Da dan nauyinta ta bude sai da taji kwalla. Kaya ne a
jere an ninke suna wani irin kamshi a sama da 'yar takarda ta rubuta (welcome to
the world baby Tureta).
Overall ce fara da farar hula na auduga masu bala'ain laushi. Sai vest da pant mai
zebra stripes. Da wasu unisex kayan babies guda uku, tawul din wanka, shawl yellow
shima mai laushi amma ba na sakar kulu ba. Sai feeder, siririn flask da kayan wanka
harda baby perfume.
Ummi ta rinka murmushi tana yiwa Radhiyanta da Emzee addu'a. Shima kullum idan ya
kira sai yace Ummi jikinki babu matsala ko? Ba zai fito kai tsaye yace ciki bane
wai shi kunya. Idan tace lafiya sai yace Allah Ya kaimu lafiya. Tana nan Daada ya
sameta ta nuna masa.
"To ai tunda ta saya in sha Allah da ita zamu je haihuwar"
"Da kai za'a?"
"In sha Allah" ya bata amsa.
Tare su ka sauko yiwa Awwab sallama sun ce sun yafe masa zuwa gobe. Mami tayi musu
tayin abinci da su ka koma amma Awwab ya rufe ido yace na Radhiya zai ci.
Murmushi tayi "kinyi girkin ne Radhiya?"
Kai a kasa tace "banyi ba Mami"
"To kaji sai ku dauka a nan a daren nan za ka takurawa 'yata"
"Haba Mami gobe fa zan tafi banci abincinta ba kuma" ya turo baki.
Yayi sa'a Mama na gidan ta tare masa kafin Mamin ta tsige shi tace su tafi gida.
Sai da su ja fita tace "Mami 'yan hana ruwa gudu"
"Yanzu laifin me nayi?"
"Shi girkin da mace za ta yiwa miji akwai sirrin dankon soyayya. Kyalesu taje ko
karfe nawa ne ta dafa masa tunda yana so."
Kitchen Radhiya ta shiga Awwab ya tafi yin wanka. Aikin nata ya dauki kusan awa
guda da rabi har ya gama shiri ya shigo tace ya fita kada kamshin girki ya kama
masa kaya.
"Tayaki zanyi"
"Nagode Hammana just wait for me a falo"
Kallo ya zauna yi amma zaman duk ya isheshi saboda yau baya son abinda zai nesanta
shi da ita. Tunanin yadda zaiyi managing rayuwarsa idan ya tafi ya addabe shi sai
gata ta fito tara da arba'in da wani tray mai murfi silver. Murfin zurfi gareshi da
fadi marikinsa a mulmule.
Kan dinning table ta ajiye ta koma ta dauko banana and coconut shake da ta hada tun
kafin ta fara komai yayi sanyi sosai.
"Hammana na gama" tace tana fiddo plates.
"Inzo inyi miki wanka sai mu ci?" Yace yana murmushi.
"Na yafe please ka zo kaci kafin nayi wanka"
Hannunsa ta kama ta ja masa kujera ya zauna sannan ta ce ya ci ta shige dakin.
Murfin ya bude saboda kamshin da ya cika masa hanci. Kaza ta gasa tayi golden brown
irin gashin larabawa ta zagayeta da hadin salad wanda ta kawata da kayan lambu
daban daban ga chips a gefe daya. Rufewa yayi bazai iya ci ba bata nan.
Wankan yau na daban ne komai has to be extra special yadda Hammanta zaiyi ta
tunaninta idan ya koma. Mimi skirt ta saka da wata top mai hannu three quarter ta
bata lokaci tayi kwalliya ta gyara gashinta sannan ta fito tana kwas kwas da wani
heel shoe dinta.
A tsakiyar falon Awwab ya tarota ta bata rai ganin bai ci ba. Kunnuwansa ya kama da
hannu.
"So nayi ka fara cin abincin sai nayi presenting maka sabuwar member ta Awwab crew"
ta kashe masa ido.
"Fully employed with all benefits baby...mu ci abincin nan kafin hankalina ya
barshi gabadaya"
Daga cin abinci aka kwana ana sallama da kyar ya samu tayi bacci saboda kuka. Kuma
da kukan ta tashi ta kasa sakin rai karshe yace ba zata bishi airport ba tunda haka
ne. Sai da ta ga da gaske yake idan bata yi shiru ba bazai yarda ta bishi ba ta
goge hawayen amma kana ganinta kasan kukan take yi a boye.
Da suka je yiwa su Mami da Mama sallama gabadaya tausayinta su ka rinka ji saboda
fuskarta tayi ja alamun tayi kuka ta gode Allah. Ita da shi suna bayan mota sai
dreba su ka tafi yana aikin rarrashi da kwantar mata da hankali. Da su ka dawo
gidanta ta shige ta rushe da kuka ko abinci ta kasa ci a haka tayi bacci Zayyana
tana dayan dakin za ta rinka tayata kwana.
Sai bayan kwana biyu ta saki ranta Awwab yana shan rigima da koke koke a waya dai.
Shima dauriya yake yi tare da karfafa mata gwiwa. Kwanansa takwas da tafiya Daddy
ya gama yi mata shirin tafiya Nijar ta karasa aikinta. Katsina suka tafi tare da
Mami aka bar Zayyana da Rahima gidan Ummi. Kwanansu biyu ya hadata da 'yar kanwarsa
matashiya da su ke kusan sa'anni Na'ima saboda kada tayi tafiya daga ita sai dreba
da daracta Bigman da cameraman.
A can Nijar da connection din kakanni da iyaye aka samu aka hadata da wadanda ya
dace cikin sauki tayi aikin sati biyu ta gama hada komai. Lokacin sati hudu ya rage
mata ta koma France amma Awwab yace ko zai kara lokaci lallai ta jira shi yazo ya
maidata.
*********************************
********************************
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
A Katsina su ka sauka Mami da Daddy su na nan amma bangarensu take zama saboda
nauyinsu da take ji ga rashin 'yan hira. Gidan Fauziyya take wuni ko ita tazo.
Cikinta ya fito ga Jawad ya kara wayo.
Sun zaga gidajen 'yan uwa saboda jan magana na Fauziyya ta kaita gidan Ghazalatu.
Nura yana gida su ka zo ya rinka makalewa a jikin matarsa ba ta da damar motsi yana
biye da ita. Duk haushi ya isheta wannan aure babu ranar rabuwa ta sake samun wani
cikin. Ta kwantar da hankalinta amma rashin kunyarsa tana damunta. Duk wayewarta ta
baya Nura kwararren dan duniya ne amma dai ya canja hali tunda yanzu da gaske son
matarsa yake yi. Kadaran kadahan ta karbesu aka rabu lafiya.
Emzee yana nan yana takurawa Rahima da text idan ta ga dama tayi masa takaitacciyar
amsa guda daya tace lafiya. Wannan abu yana damunsa amma ya san shi da fita daga
makarantar nan da kyar idan ba sai ya gama ba. Jan ajin nata wani burge shi yake yi
ma amma yaki yarda ya kirata a waya.
Cikin Ummi ma ya fito tana fama da karatu ga laulayi yaki sauki indai tana gida a
kwance take. Yanzu an cigaba ta bangaren Salame tana yawan kiranta su gaisa.
Kwana hudu kafin dawowar Awwab saura kuma sati Radhiya ta koma makaranta Mama ta sa
a gyara mata 'ya. Gyaran jiki na musamman aka yi mata tana ta saka lalle a kasan
gashinta saboda sanin da tayi yana son hakan. Tun dare take jin cikinta a daure da
safe ma daurewa kawai tayi tana girki Zayyana tana shara yau bata da lecture. Suna
cikin yin breakfast ta ji ciwon cikin ya karu da kyar ta iya tashi tsaye ta ce
"Zayyana kirawo min Mami cikina..."
Sai da ta taimaka mata ta kwanta akan doguwar kujera sannan ta fita da hanzari. Ko
sallama bata yi ba ta fada gidan Daddy na tambayarta me ya sameta tace Adda Radhiya
ke ciwon ciki. Cikin sauri Mami ta fito tana tunanin ko ciki ne da ita.
Nishi take a wahale Mami ta taimaka mata ta tashi "Zayyana dauko mata hijab ko
mayafi mu tafi asibiti"
An gama saka mata hijabin jiri na kwasarta ta daga kafa Mami na rike da ita jini ya
biyo kafafunta. Basu kula ba sai da ta daga daya kafar tare da zubewa a jikin Mami
saboda wani matsanancin ciwo da bata taba jin irinsa ba da ya dirar mata lokaci
guda da fitar gudan jini. Tana jin Mamin a rikice tana cewa Zayyana ta fadawa Mama
da Daddy daga nan ciwo yaci karfinta jikinta ya saki.
Asibitin da suke zuwa na Sami Wadata su ka je jinin yaki tsayawa har lokacin aka
shigar da ita emergency. Sai bayan minti talatin aka gangarota zuwa wani dakin
likitan yace saidai suyi hakuri bari tayi kuma saboda yadda take zubar da jini sai
da suka yi mata wankin ciki. Mami harda hawayenta saboda tausayi Radhiya tayi fayau
da ita. Mama ce ta sanar da Ummi itama hankalinta ya tashi ta fadawa Daada shi kam
nasa yafi na kowa ma. A asibitin su ka wuni har ta tashi daga bacci.
"Mami cikina zafi" tace tana runtse idanu.
"Sannu kinji Radhiya zai dena in sha Allahu. Bari na hada miki tea ki sha"
So take ta tambayesu me ya sameta amma ganin iyayenta maza sai taji jikinta yayi
sanyi a hankali take share kwalla duk da bata san me ya faru ba. Ta riko hannun
Zayyana ta ce "me ya sameni ne?"
Zayyana sai ta fashe da kuka Mama ta fara fadan za ta daga mata hankali. A tausashe
ta dafa kafadar Radhiyan ta soma magana.
"Radhiya bari kika yi"
Gabanta ne ya fadi ta tuna cewa kwanaki sun shude da tayi missing period dinta
tunda Awwab ya tafi shine ta siyo PT strip take ajiyarsa sai ya dawo su duba tare.
Ashe ma ba mai zama bane. Iyakar daurewa ko don kada ta bawa Umminta kunya ta
tattaro tayi da abin ya ci tura kukan ya matsota sai ta juya musu baya. Kowa na
ganin yadda jikinta yake rawa alamun tana kuka Mami tace su fita a barta ta ji
saukin zuciyarta saboda cikin fari akwai shiga rai. Kukanta tayi mai isarta bayan
sun fita. Ta saka rai da cikin sosai saboda yadda Awwab bashi da aiki sai kwadaita
mata haihuwa da irin son da yake yi ya ga 'ya'yansu.
A waje Daddy yace yaji shiru Awwab bai kira ba ga matarsa a kwance. Daada yace kada
su fada masa tunda dai zai dawo nan kusa. Kuma bai kamata a tayar masa da hankali
ba duba da yanayin aikinsa rayukan jama'a a wuyansa.
Shadayan daren Nigeria Awwab yayi landing jirgi a Canada. Kamar kullum yana isa
masaukinsu ya kira Daddy da Mami sannan Radhiya. Yayi ta waya shiru ta na shiga
ba'a dauka an manta ta a gidan. Mami ce za ta kwana da ita kuma ta riga ta yi bacci
sai ya nemi Zayyana taki dauka saboda bata san me za ta ce masa ba. Lokaci ya duba
ya san dare yayi amma Radhiya ta rike schedule dinsa sosai na satin ta san lokacin
tashin jirginsa da sauka wani zubin kafin ya kira ta neme shi. Komai dare a Nigeria
sai ta jira shi duk fadan da zaiyi ba ta ji.
Washegari da asuba yayi ta kira shiru ya kuma kiran Zayyana tace masa bacci take
yi. Ya dai ji ne bai yarda ba . Mami ya kira da gari ya waye ya kusa tashi yace
mata ya kasa samun Radhiya jikinsa na bashi babu lafiya kuma Zayyana na yi masa
wasa da hankali. Hakuri ta bashi tace da kanta za ta kaiwa Radhiyan wayarta ce ta
fadi. Shiru lokacin boarding yayi ya sake tashi back to Germany cike da damuwar da
ake guje masa. Sai daren ranar aka kai mata wayar yana sauka ya kuma kira. Fada
yayi niyar yi mata saboda ko faduwa wayarta tayi ya bar mata kudi da za ta iya
sayen wata sannan ga wayoyinsu Mami. Amma yana jin weak voice dinta ya ajiye
makaman yakin. Karyar mura tayi masa ya bi ta da toh ba don ya yarda ba.
Da yamma ranar aka sallameta Mami ta hanata komawa nata gidan tana kulawa da ita
sosai. Karamin wankan jego ta yi mata ta rinka gasa mata jiki ga abinci mai gina
jiki ita da Mama su yi Ummi da Rahima sai dai su zo dubiya.
Ranar da Awwab zai dawo taji karfin jikinta sosai tayi masa abinci. Naman