Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
sani ba ko shima yaji amma ita dai wani abu
ne ya zarga mata har kasan zuciyarta.
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: 15. Maikudi ne tsaye a ofishin da aka tura shi cikin
barikin su Zayyan akan maganar kudi ne dai.
"Jiya Babanku yazo akan zancen nan mun fada masa bamu da komai. Ya bada adireshinsa
duk lokacin da kudi yazo zamu nemeku" officer din ya bashi amsa bayan ya gama jero
tambayoyi.
Yana hargaginsa na rashin mutumci yace "Ashe cewa yayi shine babanmu don ya ci
kudin gado. To wallahi karya yake. Babu wata alaka ta jini tsakaninmu"
Wani sojan ne ya shigo yana tambayar wancan me yake faruwa cikin harshen turanci.
Sai da ya sara masa ya bashi amsa da gani ya fishi mukami.
Maikudi yana jin ana bayani duk da bai iya gane duka maganar amma ya dan fahimci me
akeyi ya katse wancan "You understant Zayyan Muhammad Tureta is die? Me.
Biggggggggg broza. Is me faza dinmu daya ai" ya nuna kansa yana murmushi yana so su
fahimci shine babban wan Zayyan.
Mutumin ya hade rai yace a kore shi kuma idan ya kuskura ya sake zuwa ba'a neme shi
ba a kulle shi saboda yana mudu hayaniya. Dayan yana soma fassara masa bai tsaya
jin karshen ba ya fice yana ta Allah Ya isa an kashe masa kani. A hanyarsa ta
komawa ne ya rinka tunanin dole fa akwai abinda Zayyan ya barwa matarsa. Idan ba
haka ba da me suke rayuwa duk tsahon lokacin nan? Yafi karfin ita da kwadayayyen
babanta suyi masa wayau akan hakkinsa.
Yana zuwa dakin da Malamijo yayi masauki ya shiga. A shirye suke suna jiran dawowar
Mairama.
"Dama nazo akan yaran nan ne Radhiya da Zayyan. Nace ko zaka yiwa Mairama magana
idan ta yaye shi zan zo na dawo dasu gabanmu saboda gatansu dai bai wuce wurin
dangin mahaifinsu. Idan kun tafi yanzu kai ma nauyi ne kawai zai kara hawa kanka.
Sannan bazan zuba ido bane tayi aure 'ya'yana su koma agolanci a gidan wani"
Malamijo an tabo inda yake masa kaikayi kuwa. Ina zai kai karin bakuna uku a
gidansa. Gara Mairama yana son abarsa, amma yaran nan da aka ha'ince shi yayi ta
yiwa babansu kallon kitse ashe rogo ne "indai wannan ne babu damuwa. Zanyi magana
da ita kuma dole ta amince don nima bazan so suyi rayuwar agolanci ba azo ana
wulakantasu"
Maikudi ya fita da wani mugun murmushi. Soro ya koma ya zauna jiranta. Ilai kuwa
babu jimawa sai gata tana ta sauri kada a gaji da jiranta. Dukawa ta danyi ta
gaishe shi ya yafito ta da hannu.
"Yaki zo Mairama. Magana nake son yi da ke"
Kanta a kasa ya fada mata yadda ya fadawa Malamijo. Ai tuni ta saka kuka iya
karfinta tana rokansa ya rufa mata asiri ita bata da niyar sake aure.
"Kinga da har mun gama magana da babanki"
Gabanta ne ya fadi. Ta san halin Malamijo kuma tas zai bada yaran nata.
"Don Allah kayi hakuri"
"Naji, amma bazaki bar garin nan ba sai kin fito da dukiyar kanina. Dole ne a raba
gadonsa saboda a sauke masa nauyi"
Hannunta yana rawa ta zaro envelop dinnan daga jakarta ya warce gabadaya. Sakar
masa tayi kafin ya hada da hannunta.
"Daren jiya na gansu shine nace dama yanzu zan fito dasu ayi abinda ya kamata"
Kankance idanu yayi yana kallonta bayan ya zaro takardun gidan da kuma damin kudi
da aka nannade da kyauro "ashe ke mutuniyar banza ce ban sani ba? Wato da guduwa
zakiyi da komai saboda tsabar mugunta da bakin hali kamar na tsohonki"
Ta shiga girgiza kai tana hawaye "a'a wallahi"
Wasikarta ta hango ta fadi ta mika hannu ya taketa da sauri da kafa "meye a ciki?"
Hankalinta yayi matukar tashi "wallahi Allah wasika ce ya bar min. Ba takardar
komai bace"
Sai ta ga yayi murmushi saboda ya fuskanci yadda ta rude "soyayya manya" yatsansa
ya kada mata "kalli nan, zan cire takardun gidan saboda dama ina binsa bashi da bai
biya ba. Ina jin gidan ma bazai isa ya biyani ba amma dai su kadai zan dauka. Muje
ciki idan munafukan dattijan nan sun zo ki basu kudin a rabawa wanda aka ga damar
bawa. Ni kuma nayi miki alkawarin babu wanda ya isa ya rabaki da 'ya'yanki kuma
zaki koma Kano da wasikar masoyinki"
Mairama kallon mugunta irin ta Maikudi ta tsaya yi ta rasa shawarar yankewa. A
zatonta zaa raba gado a barwa yaranta gidan sai su zauna a ciki. Ita kuma a cikin
kudin ta nemi abinyi domin kula dasu. Wani hawaye ke bin kuncinta tana jin zafinsu
har zuciyarta "hakan yayi maka?"
Ya dage gira "yayi...ki sani idan kina tunanin juya magana ko Jume tayi kadan tasa
na bar miki yaran nan balle kuma wancan tsohon Mal. Aminu. Mahaifinki kuma a yadda
na fahimta ko sadakarki na nema zai iya hada min"
Share idanunta tayi tabi bayansa. Kowa yayi zaton kukan tafiya ne take yi da
mutuwar mijinta. Su Mal.Aminu sun zo ta dauko kudi ta mika masa. A take aka kira
wani malami ya kasafta da aukinsu kuwa aka bata nata aka ware na yaran yace batun
bashi fa Mairama tace ya tabbatar mata babu msi binsa komai kafin ya tafi. Maikudi
ko tari baiyi ba ganin babu mai gadon nashi sai su kadai. Jume har dadi taji yayi
hankali.
Nasiha da ban hakuri aka sake yiwa juna sannan Mal.Aminu ya roki alfarmar kada ta
tafi ta yanke zumunci dasu albarkarcin 'ya'ya "mu kuma nan babban kalubale ne a
garemu mu da gwamnati. Mu dubi marayun yaran nan da mahaifiyarsu kafin mu ga me
Allah Ya tsara musu. Haka ma gwamnatin ta dubi rayuwar sojojin da take takama da
sadaukarwarsu. A dubi masu ran wanda suke a bakin aiki, a dubi masu rauni da nakasa
sannan a dubi iyalan mamatan domin a gaskiya akwai nakasu mai girma a rayuwar
iyalan bayin Allahn nan"
Sun fara fitowa mata ana ta kuka Maikudi ya samu ya tarar da Malamijo shi kadai
iska tana ta kada yalolon yadin jikinsa yana manne masa ramar tana kara nunawa.
Takardun gidan ya nuna masa yana murmushin samun nasara.
"Naga ka kawo idanu ka dora akan dukiyar da baka da alaka da taruwarta shine nace
bari dai na nuna maka waye Maikudi."
Ware ido Malamijo yayi ya karewa takardun kallo "na meye?"
"Na gidan Zayyan ne wanda yanzu ya zama nawa. Kana iya kaini kotu don a kwatarwa
'yarka da jikoki hakkinsu amma ka sani kana yin hakan zan rabata da yaran nan ni
kuma. Ta fada min akan ta baka dukiyarta gara kowa ya rasa don baka ragawa kowa
akan kudi"
Kallon Mairama yayi zuciyarsa tana tafarfasa. Wato Zayyan yana da gida shine ta
dauka ta bawa wan mijinta tana tunanin zata dawo masa gida ta jabe ya ciyar dasu.
Lallai Mairama bata gama saninsa bane shiyasa har taje tana tona masa asiri. Har
shi zata ha'inta yana mahaifinta. Kwafa yayi yana jiran su kebe don bashi da
bukatar magana a gaban mutanen da ya kula bakinsu duka daya.
Maikudi kuwa dariya yayi bayan ya tafi. Alamun Malamijo da ya gani ne yasa shi
wannan magana sai gashi tazo daidai da halin nasa. Mairama da Zayyan ma ta kasa
tonawa mahaifinta asiri a gabansa me zai kaita fada a gaban Maikudi?
Radhiya ta dauka Hajjo ta goya Zayyan suka tafi tashar da zasu sami motar Kano. Sai
da suka dau hanya don Salisu ya biya su kadai ne a ciki Mairama tana hawayenta Nene
Marka na bata baki kawai Malamijo ya soma fada akan bayar da takardun gida da tayi.
Kai, ita kam da me zata ji ne a rayuwarta. Tana kuka tayi musu bayanin yadda abin
ya kasance.
"Ko dai mu koma ne a karbo takardun? Duk tsiyarsa baifi karfin hukuma ba fa
Mairama" Salisu yace nasa ran a bace.
Tsorata tayi "don Allah ku kyale shi. Yaran nan zai karbe, babansu ma baiji dadin
zama dashi ba"
Nene tace "Duk da haka Mairama mu zamu tsaya miki. Gidan a ina yake?"
"A Kano ne"
Salisu ya tabo dreban "Malam don Allah kayi hakuri ko zamu koma"
"Babu inda zamu je. Idan kuma sai kun koma to ni a ajiyeni a nan."
Nene Marka tace "haba Malamijo meye hakan?"
Rufe idanu yayi yana ta fada don sosai yaji haushin maganar Maikudi da rasa gidan
da yayi. Ace 'yarsa da yafi so da tausayi a cikin 'ya'yansa ita ce tayi masa haka.
"Ina nan kan baka na bazan koma ba sannan kuma ki shirya tunda dangin miji sunfi
uba ni bazan dauki nauyin kowa ba. Gida dai gaki gashi kuje a baku daki. Sai yanzu
na raina waye Zayyanun ma. Har me yayi miki wanda ni ban miki dubunsa ba. Ji gidan
da ya ajiyeki...."
Ta daure matuka amma bata jin zata taba jurewa wani ko da kuwa Malamijo ne ya zagi
Zayyan. Ko bata aure shi ba yanzu ta san daraja da kimar soja....wallahi yafi
karfin raini.
"Yayi min komai Malamijo" tace cikin kuka tana rungume Nene iya karfinta har
Radhiya sai da ta tsorata "ko a kango muka zauna dashi har abada bani da tamkarsa.
Wayyo ni ashe haka mutuwa take da daci da tona asiri? Lokacin da nayi maraicin uwa
bansan ciwon rashi ba saboda bamu saba ba. Allah Ka jikan Zayyan ko Ka dauki raina
nima na huta"
Zubar hawayenta ya taba Malamijo bare da ya ga ta rike kirjinta da yake mata mugun
zafi. Dreban yace wa su juya ta dago rinannun jajayen idanunta.
"Allah Ya kaimu masu gidan su girma zasu karbi abinsu da izinin Allah. Amma a yanzu
tunda yace yaji ya gani zai ci haram bazan shiga tsakaninsu ba"
Duk rashin halin Hajjo sai da tayi kukan tausayin Mairama. A haka suka tafi Kano
Salisu yana ta mamakin halin Malamijo. Ashe Salame gado tayi na munin hali ba taka
haye ba.
Tare suka sauka a tasha ya ja Mairama gefe ya fito da kudi masu tsoka ya damka mata
sannan suka nemi motar Sumaila shi kuma ya shiga hayis zuwa gidansa. Dama ya riga
ya gama shawararsa tun a hanya shiyasa yana ganin yadda Salame ta fito muzumuzu ita
a dole tana cikin alhinin mutuwar masoyi ko sannu bata yi masa ba ya dakatar da ita
zata tashi ta bar falon saboda ta ganshi.
"Salame ki hada kayanki ki tafi gida na sakeki saki daya"
Kiris...sauran kiris irin mai riss dinnan zawo ya tsinke mata. Tunda take bata taba
jin fargaba da tsoro kamar wannan lokacin ba. Ya saketa ta tafi ina? Sumaila? Allah
Ya kiyaye. A iya zurfin tunaninta Salisu yana mata son da zai iya hadiye kowane abu
tazo dashi. Shiyasa take yadda taga dama iyaka yayi fada anjima ya dawo yana
bibiyarta. To ko dai kunnenta baiji da kyau bane.
"Ni ka saka?"
"Halifa da muka haifa da ana komawa baya Salame bazan so hada jini dake da
mahaifinki ba. 'Yar cikinsa tana cikin magagin rashin miji amma dukiya yake nema
duk arzikinsa. Wallahi bazan iya ba. Kije Allah Ya baki daidai dake."
Kande ya kwalawa kira tazo ya cire naira goma yace ta wuce ta kaiwa mamansa Halifa
yana tafe. Dayake daga can gidansu aka kawota ta riga tasan gidan.
Salame tana kame ta kasa motsawa ya wuceta ya shiga daki. Sai da abin ya sami wurin
zama a kwanyarta ta shiga ta fara masa ihun masifa.
"Wato akan Mairama ka sakeni saboda Malamijo ya bata mata rai. Bazaka burgeni ba
sai naga ta tare a gidan nan ranar asabar"
"Ki fita sawunki a likkafa kafin na tashi" yace daga kwance
Tafa hannuwa tayi " nima na huta da auren kaddara zama da mijin da baka so"
Duk inda zata cusa masa haushi ta rinka nema ko a jikinsa tunda ya rabu da kwallon
mangwaro ya huta da kuda.
Gidansu ta koma ko ta kan Halifa bata bi ba. Awa uku tsakanin saukar su Malamijo da
dawowarta gidan.
Yadikko ta tareta ganinta da akwati niki niki "ke kuma daga ina?"
"Sakoni yayi" ta fada cikin yanayin ko in kula.
Ashar Malamijo ya lailayo ya saki yana kara tunzura da yadda take magana ko a
jikinta "wai nufinku duk kun dawo min gida kenan?"
"Ya son ranka? Ca nake mata biyu ka saki a dan tsukin lokaci guda, ai gara ka dana"
Hajjo ta fada masa sannan ta saki labulen dakinta.
"To Al-Qur'an daga ke har Mairaman kowa taji da kanta bazan iya ba. Yara masu bakin
hali kun fita a talauce kun dawo a tsiyace"
Dakinsu na da ta shige abinta ta barshi tsaye. Nan taci karo da Mairama da kyawawan
'ya'yanta. Kamar ta shareta sai ta fasa tace mata ya hakuri.
"Mungode Allah"
"Allah Ya jikan shi"
"Amin"
Daga haka babu wadda ta sake kula 'yar uwarta har suka yi shirin kwanciya. Ganin
Mairama da yaranta ya tuna mata da Halifa sai taji wani iri gashi bata yaye shi ba
dama.
Kyandir Mairama ta kunna a gefen katifar da suke kwance ta kwanto wasikar Zayyan ta
soma karantawa.
_(Na rubuta wannan takardar tun ranar da sunana ya fito a cikin masu tafiya
Liberia. Sai nake ganin kamar jiya muka yi aure har zan tafi na barki. Mairam ban
sani ba ko zan dawo ko shikenan tafiyar. Don Allah alfarma daya nake roko kada
bakinki ya taba gajiyawa da sanyani a addu'a. Idan kewa ta isheki kinyi kukan
rashina ki sani cewa nima ko a ina nake idan na tunoki sai na zubar da hawaye. Ina
sonki Fillo Allah Ya sani amma ina son ki saka a ranki mijinki yayi alkawarin
bautawa kasarsa ne. Zanfi kowa son son ace ina tare da iyalina kamar kowane
magidanci. Sai gashi aikina yayi min tsakani da hakan. Lokaci zuwa lokaci zan rinka
tafiyar da babu lallai na dawo. Duk da haka ina alfahari da aikina kema ki tayani
kinji. Idan kin haihu kafin na dawo ki zabawa abinda muka samu suna. Ki kular min
da 'Yar Soja Alheran innar Daadaa. Sauran kalaman da suka rage a kirjina sai na
dawo gareki zaki ji su. Idan ban dawo ba na baki amanar kanki da ta 'ya'yana. Allah
Yayi muku albarka. Lt Zayyan Muhammad Tureta)_
TAKWAS
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: 16.***********
"Ke Radhiya, zo kije kantin sauki ki siyo min yis"
Shanyar kayansu da ta wanke take yi nata da na Emzee da Mairama. Kallon Binta tayi
tace "ki aiki Emzee ko wani don Allah kinga ni bana fita saboda Ummi"
"Inda na aike kin har wani nisa ne dashi da zaki fara yi min felekenki na tsiya. Ko
kuwa nace kije ki zauna ne?"
Zumburo baki tayi "Ummi wanka zata yi idan na gama shanya. Zaki kai mata ruwan ki
ajiye mata soso da komai a kusa da ita inji miki aiken?"
Mairama tana daki ta jiyo su ta rinka shafa bango har ta fito.
"Ke!" Tace da tsawa
Radhiya ta juyo tana jira taji Mairama ta umarceta da zuwa kantin ta fada mata kai
tsaye ba zuwa zata yi ba. Tunda mahaifiyarta ta makance ta kara hankali da bambance
su waye masu kaunarsu da gaskiya. Malamijo ya gina gidansa da turbar nafsi nafsi
kowa ta kansa yake yi. Babu wani jinkai na azo a gani saboda rashin wadata su da
abubuwan da ya dace. Idan ka cire Yadikko babu wadda take leka Mairama balle ace
mata yaya jiki. Dukkansu take kallo tana jin kanta daidai dasu. A duniya bata da
sama da Umminta sai Emzee. Shi kuma haushinsa take ji saboda rashin magana.
Gabadayansa bashi da walwala sosai yaron saboda tsangwama musamman daga Salame
kafin ta bar gidan.
"Ki karba kije ki siyo mata ko ma meye idan kin dawo sai nayi wankan"
Radhiya yarinya 'yar kimanin shekara goma sha daya wadda ta gado zuciya ta
mahaifiyarta, barkwanci da jarumtar mahaifinta da kuma jinkai da tausayi nasu su
biyu ta kekashe idanu "Ummi ni bazani ba idan na tafi ma zubar da kudin zanyi a
kwata ko na sayi danmalelen gidan Fadi. Haka kawai yau babu makaranta kowa yana nan
taki aikensu sai ni saboda bata damu dake ba" ta kare maganar muryarta da alamun
zata yi kuka.
Mairama ta daga hannu daga inda take tsaye kamar za ta dake ta "kizo ki karba kafin
ranki ya baci"
Juya keya tayi ta mika hannu ta baya tana jira Binta ta ajiye mata kudin harda wani
kada jiki. Emzee ne yazo ya karbe "ni zanje me za'a siyo miki?"
Binta ta warce kudin "bazaka je ba din, wannan fitsararriyar nake so inga uban da
ya tsaya mata a cikin gidan nan. Har ni kike juyawa keya saboda baki da kunya"
Mairama daurewa kawai take yi saboda rashin ido. Itama ta sani an tsangwami
'ya'yanta an hanasu rawar gaban hantsi saboda an ga tana zaune. Amaren Malamijo
Hanne da Binta sunfi kowa kaudi da takura musu. Kuncin zuciyarta ne ya taso ta tuna
mijinta. Da yana raye waye duk gidan nan ya isa ya taka su? Yadda kowane uba ke
kaunar 'ya'yan shima tasan zai so nasa kuma ya kyautata musu rayuwa.
"Karami janyo min hannun yayarka"
Da kanta ta karaso gaban Mairama ta kama hannunta don ta nuna mata ta iso. Hannunta
ta shimfide mata a gadon baya, dukan ya shigeta amma ta dake. Mairama kanta ciwo
take ji yana addabar zuciyarta "in ce kije aiken ki ce bazaki ba saboda ban isa ba?
Ko saboda bani da ido sai yadda..."
Zubewa tayi a kasa tasa kuka "Ummi kiyi hakuri don Allah zanje."
Kudin ta karba daga hannun Emzee tana cewa ya mayar da Ummi daki kafin ta dawo. Rai
a bace taje ta siyo yeast din naira hamsin maimakon na ashirin da aka aiketa. Da ta
dawo daga bakin kofa ta tsaya ta zura hannu
"Gashi"
"Shigo ki bani" Binta tace da gadara tana fadawa yayarta "kinga fa irin jarabar da
muke fama da ita. Uwa makauniya 'ya'ya marasa da'a"
"Mu ba jaraba bane" Radhiya ta maida mata da tsiwa.
Bintu bata bata lokaci ba ta kai mata lafiyayyen mari.
"Uwarki makauniyar nan ma bata isa ba wallahi"
Tana kuka baki bai mutu ba "ba dai uwata ba"
Ran Binta ya kara baci "sai ta wa?"
"Wanda ya tsargu dashi nake" Radhiya ta amsa kai tsaye. Kafin Binta ta ankara ta
fice daga dakin. Da sauri ta kamo Radhiya a tsakar gidan tana shirin shiga dakinsu.
Mairama tana jinsu ta yi salati ta sake tashi "me kika sake yi kuma?"
Binta ke dukan Radhiya da zagi amma a hakan cewa take ba dai tata uwar ba. Hajjo ta
taho kwatar Radhiya Binta ta sake tunzura ta daga hannu zata sake kai mata duka ga
Mairama har ta soma hawaye suka ji sallama.
Amsa sallamar bakuwar suka yi Binta bata kula ba ta kuma daga hannu taji matar da
ta shigo tace tayi hakuri kada ta sake dukanta yara sai da rarrashi.
Idanu a soye don itama Binta ba kunyar gareta ba tace "yau ko uban da ya haifi
uwarta ne wallahi bai isa ya hanani dukanta ba"
Malamijo wanda motocin da ya gani a kofar gidansa suka saka shi tasowa daga
majalisar da yake ko kallon mutanen wajen baiyi ba tunda ya ga daya ta shiga
gidansa. Ya shigo kenan ya ji me Binta tace ya kuwa murtuke fuska.
"Ahhh lallai yarinya kwananki a gidana ne ya kare shiyasa kike zagina. To shiga ki
kwaso tsiyarki kizo ki wuce na sakeki saki biyu"
Innawuro ta kalli Ali tana jin wani bacin rai. Wato duk tsayin shekarun nan yana
nan da bakin halinsa na sakin mata. Ta sani wadda