Advertisements
Chapter 63 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   63 / 99

186K to 189K   out of 295.8K words

shima dole zumuncin nan ayi dashi
mai karfi. Kuma da yake shine babba don har Major ya girma a shekaru yace "na dauki
matsayin babban yaya mai fada a ji. Idan kuma aka ki ji to fa na iya displine"


Zayyan yana dariya yace "Ka tuna min da 'yan gidanmu Yaya Babba. Ina ta tunaninsu
wallahi. Ko yaya Maikudi don yafi kowa baudadden hali a gidan"


Dariyar da suke yi yaji dif ta dauke har ya soma zargin ko rasuwa akayi a gidan
nasu.


"Maikudi ya rasu ne? Ku fada min dama nasa rai da ba kowa zan samu a raye ba"


Major ya sake kallon Excellency "to Yaya Babba ai sai kayi masa bayani mu dai babu
ruwanmu ko Hadir"


Excellency ya dan dake "wato zamewa zaku yi? Kada ku manta ku kuka fara naku ma
harda duka. Ni me nayi Allah na tuba banda dan tsare shi kuma ba ya fito ba last
month"


"A fada yadda zan gane ni dai"


Major ne ya soma bashi labarin yadda ta kasance da Mairama bayan an tabbatar da
rasuwarsa a wancan lokaci. Maikudi ya handame abinda ya bar musu kuma don karfin
hali yayi ta musu kazafin mutuwa ya rabasu da masu taimaka musu.


Iyakar kulewa da bakinciki Zayyan ya kwasa ga tashin hankali da suka ce masa a
makance suka dawo suka sami matarsa. Ashar yake nema da zai turawa Maikudi sai dai
takaicinsa daya bai ma san wanda ake yayi ba yanzu.


"Kiyayyar da yake min har ta kai ya cutar min da iyali irin haka?" Yace a raunane.
"Kuma meye dalilinsa na yi maka karya kaima" yayiwa Baban Arifah tambayar.


"Barni da karamin dan iska, da yaci uban duka cewa yayi fa wai dan firit ya ganni
ya zata buzu ne."


Shi ya bada amsa da seriousness amma dariya suka saka ganin yadda yake kosasshen
dan siyasa. Ya kuwa hade rai saboda dariyar da suke yi masa.


Su Mami suna ta bawa Ummi baki a daki su kuma a falo sun cigaba da tattaunawa.


***********


Kiran sallar la'asar da aka soma daga masallacin wani gida a nan kusa da estate din
inda suke zuwa jam'i shine ya farkar da Awwab da yake baccin wahala a falon Mami.
Yunwa yake ji kamar yaci babu, idanunsa suka sauka akan plate din da Radhiya ta
rufe akan centre table bayan yayi bacci. Daukowa yayi ko kuskure baki bai iya tashi
yayi ba ya shiga ci da sauri. Ko rabi bai ci ba sai amai kamar zai fitar da kayan
cikinsa. Ibrahim da Emzee kakarinsa suka ji daga toilet din da yake cikin falon
suka fito. Emzee ya tafi zai taimaka masa shi kuma Ibrahim ya tafi gidan Mama dauko
mukullin motarta idan abin zuwa asibiti ne su tafi.


Yanayin yadda ya shiga falon da sauri shi ya tada hankalin Radhiya tana gyara
hijabin jikinta tayi alwala.


"Ibrahim ya?"


Shima gwanin rudewa ne yana ta bincike a falon yace "Hamma ke amai ban san me ya
same shi ba"


"Amai?" Radhiya tace a tsorace tana fita da sauri.


Da shigarta gidan Mami ta hadu da Emzee a falo yana gyara wurin amma bata ga Awwab
din ba.


"Adda fita ki koma gidan Mama" Emzee ya umarceta saboda baya so Awwab din ya leko
ta ga yadda ya jigata lokaci guda.


"Don Allah Emzee ka barni na gamshi minti daya kawai" kuka yazo mata.


"Kina so su Mami su zo su ganki a nan ne ace kin biyo saurayi?"


"A'a"


"To ki koma idan ya dawo falo da kaina zan kirawoki kinji" ya koma lallabata saboda
yadda ya kula ta shiga wani yanayi.


"To...toh...don Allah kada ka manta"

A sanyaye ta fita ta koma ta tada sallah.
Ibrahim kuma yaje bangaren Ummi lokacin su Daddy sun taso zasu je suyi sallah sai
Excellency ya wuce a bar Zayyan haka sai gobe kuma. Da ya fada musu halin da ya
baro Awwab mukullin mota ne bai gani ba zai kaishi asibiti Zayyan ya dakatar dashi.


"Yarona ya bawa kanshi wahala yaki cin komai tun jiya"


"Awwab din da bashi da juriyar yunwa?" Cewar Major.


"Ku bashi abu mai zafi ya sha sai yayi kamar rabin awa sai yaci abinci. Amma banda
ci da sauri ko da yawa sosai. Nima da naci na shekara ashirin da biyu gashi da kyar
nake tafiya"


Murmushi Ibrahim yayi yana jin Zayyan ya burge shi. Gidan ya koma lokacin su Zahra
suna can ya fada musu a hada masa tea. Ita ta hada masa lipton kawai da yaji kayan
kamshi da sugar daidai aka kai masa. Wanka kawai yayi da sallah ya sha ya sake
kwantawa kansa na juyawa. Bai ga ta ina zai taba iya zama soja ba. Su da suke zama
a bakin tituna domin tsaro ga mutane ko su yanki daji ko wuraren tarzoma ayi ta
fafatawa babu ci babu sha na tsayin awanni.


Radhiya na idar da sallah Ibrahim ya fada mata me Daada yace game da Awwab din.


Ya zauna a kan kujera yana cewa "amma fa da gani yana jin jiki...cikinsa a dame
sosai abin tausayi. Gaskiya yana bukatar kulawa. Naga kin fimu damuwa ko har an
daidaita ne ban sani ba"


"Allah Ya kaimu yaji sauki sai ka maimaita masa" Emzee yace daga bayansa "Adda ki
dafa masa wani abincin mana tunda na gidan ya saka shi amai"


Da sauri ta bar wurin ta koma kitchen din Ummi. Sai da ta tafi Emzee yace da
Ibrahim "kana da problem fa, ka ga yadda ka karasa tayar mata da hankali da abinda
kake cewa"


Shi bai hango me yayi ba da gaske yace "daga fada mata gaskiya? Kai baka ga alamun
yana jin jikin ba?"


"Kai baka iya sakaya zance bane"


"Kamar wani mace ayi ta luguiguita magana saboda wahalar da kai"


"Anya Ibrahim zaka iya soyayya kuwa? Irin janyo hankalin yarinya da dadadan kalamai
duk zero kake" Emzee yace da mamaki don Ibrahim kai tsaye yake abu yasha a jikin
Mama.


"Magana mai dadi ta wuce ina sonki kina sona mu hade kai kawai a daura aure a wuce
wurin? Kakale kakalen soyayya yasa na kasa samun wadda zata burgeni fa"
"Baka hadu da shagwababbiya bane sunfi tsayawa a rai"


"Allah Ya tsareni a rinka tale baki ana karya wuya kamar mara lafiya. Malamin jinya
ne ni?"


Emzee yana dariya Zayyana ta banko kofar daki ta fito ashe tana jinsu. Tsaki taja
da karfi yadda duka zasu ji ta wuce a fusace. Maganar Ibrahim ta sani sarai da ita
yake ba wani ba. Duk da tana shiri da su duka kuma bata da abokan hira idan suna
gidan sai su amma fa tafi jituwa da Emzee. A da bata ganewa idan Ibrahim ya fadi
magana akan yanayinta amma yanzu an kile anje bodin an hadu da 'yan mata. Ba wannan
Zayyan bace mai komai Daddy, ita ma yanzu ta san me take yi.


"Ka ga ka taba min kanwa."


"Da nayi me? Ai banyi komai ba sai na sami wannan bakin na dalle inji wa take yiwa
tsaki ni da kai"


Emzee ya mike yana daga hannuwa "my friend da kai fa take. Ba dama tayi magana ka
rinka cewa ana tale baki. Mutane irinka gidansu babu wani armashi komai a rinka yi
kamar yaki. Irin dan tattalin nan da rarrashi ni ban ga alamun zaka iya ba"


Ibrahim kallon tausayi yayi masa don shi soyayya bacin lokaci ya dauketa musamman
da ya dukufa karatun nan baji ba gani.


"Chege Emzee anya kai a NDA dinnan soja kaje zama ko kuwa dai idan kayi graduating
buzu zamu shimfida maka a kofar gida ka koma mai bada lakanin mallaka da inganta
kauna"


Cakumo shi Emzee yayi ya matse a tsakanin hannu da cikinsa yana cewa Allah Ya kawo
shi neman shawara ya ga yadda zai rama.


***********


Sai da Radhiya tayi kusan minti biyar tana tunani kafin ta yanke shawarar me zata
dafawa Awwab me sauki da zai ji dadinsa. Fridge ta bude ta fito da mince meat ta
juye a karamar non-stick pot sannan ta hada albasa, tumatir uku da attaruhu biyu
kanana tayi blending tare da tafarnuwa karama. Juyesu tayi a wani pan ta saki wuta
nan da nan ruwan ya kafe. Sai ta dora mince meat din shima batare da ta saka ruwa
ba na jikinsa ya bushe ya soma sauya kala sai ta zuba soyayyan mai a kai. Ta yanka
albasa babba ta juye a ciki tare da wancan kayan miya ta zuba gishiri da kayan
kamshi ta barsu suna suyowa a hankali. Sai da ta ga sauce din nata ya fara haduwa
ta kara maggi da curry sannan ta dafa couscous wanda ta sakawa butter da dan
gishiri a ruwan dahuwar. Ruwa ne kadan ake sakawa ayi komai cikin sauri kada ya
cabe ko yayi tuwo. Yayi kyau sosai a ido ta kwashe ta zuba a karamin flask. Sauce
din shi kuma ta zuba a wani bowl ta hada masa komai da plate da cokali ta bawa
Zayyana dake zaune tana kunkunin maganar Ibrahim ta kaiwa Awwab.
Fauziyya ta rinka mita saboda abincin dan kadan Radhiya tayi gashi ransu ya mugun
biyawa. Da yake hankalinta yana wurin Hammanta ko a jikinta sai cewa tayi idan suna
so su jira Hamma ya warke tayi musu.


"Ke wallahi lallaba dangin miji akeyi a zamanin nan" Fauziyya tace tana maka mata
harara don sosai tasa rai zata ci.


"Nima dangin mijin ce sai hakuri Adda babu yadda zakiyi dani"


"Don Allah ki taimaka min mana Radhiya idan banci ba bana jin bacci zai iya daukana
yau" ta koma kwantar da kai.


Zahra ta bita da kallon tuhuma "anya Fauziyya kalau kike kuwa? Jiya ma fa kinyi
mana daga an soya kwai da mince meat kika cinye fiye da rabin wanda aka ajiye a
dinning. To ko dan mince meat kika dauko"


"Kada kiyi min fata har yau ina tuna kalar kukan da nayi ina nakuda. A bar zancen
na yafe"


Radhiya ta sami na tsokana daga baya ta tausaya mata ta kawo sauran sauce din amma
babu cous cous duka ta juye masa ta bata.


Zayyana ce ta zuba masa a plate ta mika masa.

"Gashi inji Adda Radhiya"


Karba yayi tun kafin ya fara ci cikinsa yana dada rarakewa da yunwa. Yanzu kam a
hankali ya rinka ci sai abincin yayi masa dadi sosai. Yana gamawa ya kira wayarta
kuwa.


"Hammana ya jikin?" Yaji muryarta ta shige shi a nutse 'yan salihancin na kusa.


"Better. Nag...."


"Hey! Ka manta babu godiya ne" tayi saurin dakatar dashi.


A kasalance yace "To me zance na nuna miki naji dadi?"


"Babu komai ni dai kawai ka warke"


"Love you Schatzi"


"Me too Hammana" ta kashe wayar da sauri kamar yana gabanta. Kalmar nauyi take yi
mata bata jin zata iya fada.
Daga masallaci Excellency ya wuce Chibuzor yana mota tare da wani dreba su ka yi ta
masa godiya. Su Major ma suka ce to yanzu dai zasu bar Zayyan ya huta ya wuce ciki.


"Ango" yaji Baba Hadir yace da sigar tsokana a kokarinsa na magana.


"Malam ka bude baki kayi tsokanar da gaske naji. Ba kyaleka zanyi ba sai naji ina
fada kana fada"


"Kaga wuce wurin matarka. Idan kaso ma magrib da isha kayi naka jam'in da ita"
Major yace yana nuna masa kofa. Shi da Baba Hadir kowa ya tafi nasa gidan.


Shima sai ya tafi yana murmushi. Daga falo ya soma jin wani irin kamshi mai shiga
rai da bai taba sani ko jin makamancinsa ba. Turaren wuta ne dan gaske irin wanda
su Mammee suke aiko mata dashi ta saka a ko ina. Kofar da ya ga ta shiga lokacin da
take kuka ya bude. Nan ya sameta akan abin sallah tana addu'a ya zauna a kasa
gefenta ta kammala sannan ya tashi tsaye.


"Yanzu me zanyi?"


"Ka kwanta ko baka yi bacci ba nasan jikinka yana bukatar kwanciyar"


Da yake yamma ce sanyin da aka fara ya karu sosai shiyasa ta kashe AC sai fanka
kawai. Kayan jikinsa ta kalla tasan bazai ji dadin kwanciya dasu ba. Kamar yasan me
take tunani ya cire rigar ya ajiye akan kujera daya dake dakin. Da farko kunya taji
sai dai tana ganin yadda ya koma bata san lokacin da wani irin kuka yazo mata ba.


"Sojana kaine haka?" Ta bi wuyansa da kirji tana shafawa. Ya masifar ramewa fiye da
yadda take tsammani dazu da yake cikin riga.


Rigar yayi saurin dauka "bari na rufe kasusuwan nan kada su firgita min mata" sai
ya ga ta kama rigar ta mayar ta ajiye ta rungume shi tana jin wani iri a zuciyarta.
Wace irin rayuwa Zayyan yayi ne. Ta sani har abada idan ba samun kanta tayi a irin
wannan yanayin ba to bata isa ta fahimci ainihin radadin da yake ji a ransa yake ta
kokarin dannewa da fara'ar dole ba. Sojoji nawa ne a irin rayuwar sun rabu da
iyalansu babu ranar sake haduwa. Nawa ne matan suka sake aure suka sake sabuwar
rayuwa ashe mazan nasu suna da rai. Yanzu da tayi aure fa? Da Allah Ya jarabceta da
son waninsa fa kuma ya dawo full of hope na ganin iyalinsa. Shikenan duk wannan
farincikin sai ya koma ciki ya dawo matarsa ta zama ta wani kila ma da zuri'a a
tsakani. Wayyo bayin Allah. Allah Sarki sojojin kasata.


Kuka mai tsanani ta sake fashewa dashi yana shafa mata baya ta dago kanta a hankali
"yanzu da nayi aure fa Zayyan? Da shikenan ni da kai..."


Bai barta ta karasa maganar ba domin kuwa shima wannan tunani yana damunsa kuma Ya
san wata kyauta ce kawai daga Allah da yanzu labari ya sha bamban. A take ya soma
nuna mata wata irin zazzafar kauna mai tsayawa a rai, ruhi da gangar jiki. Soyayya
bata tsufa sai dai ma'abotanta su tsufa. A wannan rana abinda suka kwana suna
tunawa junansu kenan.


**********


WATAN DA YA GABATA



Malamijo ne ya coge a jikin bango yana ta kamshin turare dan d'uri. Sanye yake da
manyan kaya babbar rigar nan kamar a nade shi dukkansa a ciki. Ga jar dara wasu
bangarorin sun dan cinye ta koke. To amma dai ita ce ta fi dama dama cikin hulunan
nasa. Kafarsa kuwa cover shoe ne na maza mai dan tudu ta kasa da tsukakken baki ya
coko gaba.


Wata mata ce ta fito ta kofar gidan da yake tsaye a gefe taci kwalliya foundation
tayi kuka. Kallo daya kacal zaka gane irin matan nan ne da ake kira da masu kirar
coca cola. Murmushi ta saki da ta ganshi shima ya maida mata jikinsa har rawa yake
ya ga mace irin wadda yake so. Amintaccen yaronsa Talle da yake taya shi nemo 'yan
mata ne ya tallata masa 'yar makotansu sakin wawa kyakkyawar mace son kowa kin
wanda ya rasa.


Sai gashi kwalliya ta biya kudin sabulu. Matar tayi ta ko ina ga ta gwanar
kwarkwasa bata sha wahalar tafiya da imanin Malamijo ba. Da zai tafi kyautar dubu
biyar yayi mata a ziyara ta farko. Yana zuwa gida dakinsa ya fada hankali a tashe.
Ga mace har mace fa ya samo amma babu guri a gidansa, mata hudu ne a gidan. To
yanzu wa zai sallama?


Yadikko dai yana da yakinin duk ranar da ya sallameta 'ya'yansa kaf sai sun masa
rashin mutumci irin wanda bai taba tunani ba. Banda Mairama da ta dage yanzu wurin
ganin ta hada kan kannen nata babu wata shakuwa a tsakaninsu. Akwai nutsatsu akwai
fitinannu duka ya tara amma tarayyarsu daya shine girmama Yadikko da Hajjo da itama
tayi nisan kwana a gidan. Atine tsohon ciki gareta, Na'e kuma ko wata uku bata cika
ba. Idan ya saketa yanzu ya cuci kansa tunda bai gama more kudin da ya kashe mata
na aure ba. Ranar Malamijo kasa baccin kirki yayi tunani ya addabe shi.


Bayan kwana biyu Atine ta sauka aka sami 'yan biyu mata. Da murna Hajjo ta tare shi
da wannan zance ya hade rai.


"Don bala'i tun ana daidai din kuma yanzu abin ya koma bibbiyu? Wai ni bazaku barni
na sha iska bane? Mata kowa tazo bata da aiki sai haihuwa. Mtswww"


Hajjo tasan halin mijin nasu sarai kuma dayake da ita aka je asibitin ta ga irin
wahalar da Atinen ta sha sosai.


"Idan ka gama tsakin sai ka kawo kudin da za'a siyo abubuwan karin jini ayi mata
girki mai kyau. Kuma dai wannan karon a daure a bamu na yin kauri. Yarinyar nan
taji jiki"
Abin da bai taka kara ya karya ba dama neman rigimar yake ido rufe da daya daga
cikin matansa don sosai Hajiyayye ta gama tafiya da imaninsa da wani salon soyayya
da take gwada masa. Ji yake kamar bai taba aure ba.


Ya karkace kai ya kankance idanu "Rashin kunya zaki yi min Hajjo? To sai ki kwata
tunda da uban mutum muka tara ki yiwa kishiya girkin bikin jiki"


Ranta ya sosu da zagin da yayi mata "Nagode madallah sai dai ka sani uban nawa da
bai ajiye ko dan marakin sa ba duniya bata yi masa shaidar auri saki ba."


"Wuyan wata yayi kauri. To sai ki tattara ki koma gidan wanda baya auri saki. Ali
mai auri saki kema yayi miki saki daya"


Da farko kunnenta har nema yayi ya toshe saboda abu ne da ta sakankance bazai taba
faruwa ba. Shiyasa ma ta saki jiki ma ta saki jiki kuma ta dauki salon Yadikko na
ganin sun rungumi duka yaran da babu uwayensu musamman masu kananun shekaru. Barta
da fada da rashin barin ta kwana amma duka matan Malamijo bai taba auren wadda take
sonsa soyayya ta gaske ba zaman hakuri ba irin na Yadikko kamarta ba. Kuntata musu
da yake yi yasa da wahala soyayyar ta fito ana kokarin ci a koshi.


"Me kace Malamijo?" Ta fada a razane.


Shima kuma sai jikinsa ya dan so rissina "nace a tattara a tafi na sauwake miki.
Idan akwai nama a gidan tsoho sai kije kuyi ta ci"


Duk wani abu da take tunanin fada masa domin ragewa kanta bakinciki sai ta ga yayi
kadan. Zuciyarta tana zafi ta shige dakinta. Mayafi kawai ta dauka ta fita daga
gidan batare da ta leka dakin Na'e ba tunda Yadikko ma tana asibiti wurin maijego.


Kafin ta karasa bakin titi sai kuka ya kufce matan. Da kyar take ganin gabanta haka
ta tafi gidan iyayenta a cikin gari.


Malamijo kuwa tunda ta fita yaji duk ya shiga damuwa sai dai wayar Hajiyayye a
lokacin ta mantar dashi komai sai gashi a washegari ya tura wakilai gidansu. Abin
mamaki basu bar gidan ba sai da suka bada sadaki don iyayenta sun ce basu ga
dalilin jan lokaci ba.


Yadikko tayi kukan wannan wulakanci da ya yiwa Hajjo taje ta fadawa abokinsa da
suka yi hannun riga wato Mal Kallamu. Ko kadan baiji dadi ba amma yasan Malamijo
baya jin shawara. Duk da haka yaje gidan basu kwashe da dadi ba kuwa. Abin takaici
cikin 'yan matan nam hudu da yayiwa aure lokacin da idanun Ummi suka bude biyu an
sakosu. Sauran kuwa zaman wulakanci da kaskanci suke a nasu gidajen. Sun auri mazan
da basu san darajarsu ba ko kadan. Kina magana kuma a goranta miki cewa babanki ma
yafi haka.


Daga nan dai Malamijo ya shiga gyaran gida amarya zata tare. Yadikko hakurinta ya
kare ta kudurta a ranta cewa Atine na yin arba'in zata bar gidan. Yarinya ce karama
marainiya. Babu wata mace tsayayyiya da ta gani daga danginta da zasu bata kulawa
ita da 'yan biyun nata. Ana sauran kwana biyar ne

63 / 99