Advertisements
Chapter 94 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   94 / 99

279K to 282K   out of 295.8K words

you so much" duk da yasan ta dade da soma bacci ba zata ji ba.
Hannunsa na dama ya sarke da nata yana shafa kanta a zuciyarsa yana addu'ar Allah
Ya basu zaman lafiya da albarka a zaman aurensu kuma Ya basu hakuri da juna.
Soyayyar gudan jinin Tureta da ita ya girma yana rainon abarsa a zuci tun kafin su
sake haduwa. Idan da akwai abinda yafi love at first sight kuwa to shi ya fada head
over heels akanta. Ita ce duniyarsa, farincikinsa, cikar

💕* 63*💕
************************************
Kiran assalatu na farko ya farkar da Awwab ya tashi da sauri yayi wanka saboda kada
ya makara. A hankali yake komai saboda kada ya tasheta. Da ya gama ya sa dogon
wando jeans ya dora rigar sanyi akan shirt din ciki don tun dare garin yake a
lumshe ga iskar nan ta tsananin sanyin arewacin Nigeria da asuba. Zama yayi a gefen
gadon yana shafa fuskar Radhiya a cikin duhun dakin sai haske kadan da yake fitowa
daga toilet da ya bar fitila a kunne. Tashinta yayi yace asuba tayi. Sannu a
hankali ta dago kan ta daga pillon ta bude nannauyan idanunta da fitowar hawaye.


Yatsansa ya dora akan lebenta "Shhhh haba babyna kinyi bacci da kuka kin tashi
dashi bai kamata ba. Idan bazaki iya tashi ba ki jirani na dawo daga masallaci"


Hannunta na dama ta dunkule ta kai masa duka a kirjinsa tana kara narkewa cike da
shagwaba da hawaye "bana bukata tunda ba ka sona"


Awwab yayi murmushi tare da mikewa yana son tayar da ita sosai "zan baki amsa idan
na dawo"


Kunyarsa na tare da ita tayi saurin boye fuskarta cikin lallausan duvet din "Allah
Ya tsare"


"Amin Alheran"
Yasa kai ya fita sannan ta tashi tana cije lebe don ma ya fita da ya ga raki da
shagwaba mai lasisi. Duk abinta bata so ya dawo ya sameta a kwance saboda tana jin
kunyarsa kada yace zai taimaka mata ba yarda zata yi ba. Shawarwarin Mama Zainab da
Innawuro tsohuwar kakarta da tun farko ta fara gyara mata jiki da lalle tayi amfani
dasu wurin cire son jiki ta gasa kanta da ruwan zafi sosai. Tunda akwai sanyin gari
sai ta kara jindadin hakan. Bata bata lokaci sosai ba saboda gudun kada ya dawo ya
sameta ta shafa mai mai kamshi da body spray sannan ta mayar da t-shirt dinsa da ya
bata kafin su kwanta da dogon skirt dinta. Hijabinta ta dauko a falo tazo ta tayar
da sallah tana faman runtse ido.


Lokacin da Awwab ya fito a bakin gate ya hadu da Daddy. Kunya kamar ya nutse a
wurin ya ji kamar ya koma saboda wani nauyin mahaifin nasa da yake ji. Samun kansa
yayi da durkusawa har kasa yana tambayar Daddy din "an tashi lafiya? Yaya baki su
ka kwana?"


Sakin fuska yayi saboda ya fuskanci Awwab din a takure yake da kunya ya ce "Lafiya
kalau Captain yaya kwanan diyata?"


Kara masa kunyar yayi ya kasa amsawa sai kai da ya sunkuyar yana sosa keya. Daddy
yayi murmushin manya yana musu addu'ar zaman lafiya.


Da aka idar da sallah a masallacin ya so yayi saurin tafiya gida amma idon Daddy ya
zaunar dashi. Tsohon sojan ba wuya ya gano bakin zaren shiyasa yayi kokarin katse
wani makocinsu da yake neman jansa da hirar zaben da ya kusanto ya tashi su ka
dawo.


Gyangyadi Radhiya take yi akan abin sallah ta jingina bayanta da gadon ta ji ana
rufe kofa. Cikin sauri ta cire hijabin ta hada da abin sallar ta ninke ta koma
gadon ta rufa har ka. Sauran rufar ma a idon Awwab tayi saboda bude kofar dakin da
yayi da sallama. A zuci ta amsa masa a zuwan bacci take yi. Yana kallon yadda take
ta gyara kwanciya irin na masu baccin karya ya kyaleta sai da ya cire kayansa don
yasan ba dadin kwanciya dasu zaiji ba ya saka jallabiya.


Zagayawa yayi gefen gadon bangaren da fuskarta ke kallo ya durkusa. Da sauri da
sauri take fitar da numfashi saboda tsabar kaduwa ga hawayen tausayin kanta tana
yi. Hannun Awwab ta ji ya janye rufar da tayi ya bude fuskarta. Cikin gashinta da
ya bazu akan pillow din ya sarke yatsunsa yana jin yadda ta soma rawar jiki.


Idanunsa yake lumshewa yana budewa a kanta cike da kasala ya ce "Da kinyi soja yau
da nayi musu dariya saboda kin basu kunya karshe. Abu kadan sai kuka jikinki yayi
ta rawa."


Bakinta ta turo "to ba kaine ba..."


Ya karyar da kai idanunsa a kan bakinta "Saboda kin fini baki Schatzi, nima fa
kukan nan ya kamata nayi tunda jiya aka kawoni"


Dariyar da bata shiryawa bace ta kama ta. Yadda take dariyar ma baiki ya koma
gareta ba saboda tamkar wanda aka sakawa magnet haka yake jin kansa. Sai dai yana
tausayinta don yasan taji jiki...Allah Ya taimake shi an ware musu wuri ba a cikin
gidan aka basu daki ba da an tafka abin kunya yadda ta rinka kiraye kirayen mutane.


"Yaya jikin naki my amazing wife?"


Juyawa take son yi daya barin saboda kunyar tambayar da yayi mata ya rike mata
hannu yana girgiza kai.


"Ko zaki juya ki bari na fada miki abinda nayi niyya kafin kiyi bacci jiya" kasa
kunnuwa tayi saboda ko me Awwab zai fada mata abin so ne a gareta. Ba tun yau ba ya
kware wajen fada mata kalmomin da kan sa ta kwana tana murmushi ita kadai. Idonsa
sarke da juna suna aikawa juna sakonni da fahimtarsu sai su din ya soma magana da
muryar nan mai tsuma zuciyar Alheran Radhiya.


"Na karbi amanarki kuma na baki tawa. Matsayinki bana jin akwai wadda za ta taba
samu a zuciyata. A kanki nasan mecece soyayya kuma nasan amfanin shakuwa. Baby kin
faranta min rai sosai jiya duk da kin so cika min kunne da kuka...." murmushi tayi
ta kawar da kanta shi kuwa tafin hannuwanta ya bi ya sumbata. Kafin ya cigaba da
cewa,


"You have my love" ta dago kai kadan ta dube shi.

"You have my trust" ya matse hannunta yadda ba zata ji zafi ba.

"And you have my respect" ya duka tare da kissing goshinta.


Zai dago Radhiya ta zura duka hannuwanta ta rungumeshi a jikinta. Suna shakar
kamshin jikin juna a haka ya dawo kusa da ita ya kwanta karatun nasu ya tattara ya
koma na sababbin auren da suke matukar so da kaunar juna. Radhiya tayi dauriyar kin
yi masa kuka amma ta kasa daga karshe. Kuka ne da tasan ba na wahala bane kawai
harda wata irin soyayyar Awwab mara misaltuwa. Shi ma yana namiji yaya mamakin
ganin yana tayata hawaye a lokacin da sabuwar soyayyarta take huda kowane bari na
jikinsa tana sake samun mazauni. A take a wannan lokacin jikinsa yake fada masa
cewa da wahala matuka wata mace ta sake samun gurbi irin na Alheran....son ta a
jinin jikinsa yake. It has always been Radhiyan Hamma Awwab.


Bacci suka koma irin wanda da wuya in sun taba yin irinsa mai tattare da nutsuwa da
kwanciyar hankali. Basu san lokacin da Zayyana tazo wurin goma ba tayi ta doka
sallama da breakfast dinsu har ta gaji. Kofar net da aka zagaye karamar barandar da
ke gaban katuwar golden kofar gidansu mai kyau ta bude ta ajiye kwandon tunda a
rufe komai yake da wani kyalle mai kyau. Komawa tayi ta fadawa Mama ita fa taji
shiru.


Shadaya saura wayar Awwab ta soma ruri ya dauka da sauri zai kashe saboda kada
karar ta tasar masa Radhiya dake kwance akan faffadan kirjinsa. Sunan Mama ya gani
babu damar kashewa kenan yayi kokarin zame jikinsa Radhiya ta kara cukwikuye shi
tana zumburo baki. Murmushi ya saki ya kawar da gashinta daga kan fuskar yace "so
adorable".


Wani kiran ne ya sake shigowa still dai Mama ce ya danyi gyaran murya kafin yayi
mata sallama sannan ya gaisheta.


"Awwab kayi hakuri surukanka zasu wuce ne mutanen Sakkwato da Sumaila shine suke
son yiwa Radhiya sallama. Sai na ga ya dace ka fara shigowa kayi musu bangajiya"


"Mama ni kadai zan shigo?" Ya ce kamar zaiyi kuka don tsakaninsa da Allah kunya
yake ji ya shiga gidan.


"Ka nemi 'yan uwanka su Bilal kuyi sauri. Ina kanwar taka ina fata ta tashi ta
shirya ba jimawa zasu shigo"


Shirun da yayi da guntuwar in'ina ya fahimtar da Hajiya Mama komai. Murmushi tayi
mai sauti Awwab ya rasa me zaiyi sai ya ga Radhiyan ma ta farka kawai shiru tayi
tana kunyar tashi.


"Bani ita Awwab" yaji Mama tace.


Dora mata wayar yayi a kunne kafin ta soma magana Mama tace "saurareni da kyau
Radhiya kin tuna me nace jiya ko?"


"Uhmm" tace a hankali.


"Tau, ki shiga ruwan zafi sosai kinga gobe akwai tafiya gabanmu idan ba so kike ayi
ta zancenki ba ki gyara kanki. Zan shigo anjima idan bakiyi ba zan gane kuma kinsan
sauran"


Rufe kanta tayi ta mikawa Awwab wayarsa. Tana ji ya tashi ya shiga toilet bai dade
ba ya fito ya yaye rufar da tayi sai da tayi masa ihun ganinsa da tawul kadai gashi
ya cire mata abinda ta rufe kanta.


"Muje muyi wanka" kawai yace ya sunkuceta yana cewa ashe buhun sumunti ce bai sani
ba. Duk wani zille zille da taso yi bai barta ta fita ba a haka akayi wankan. Bayan
sun gama ya hada mata ruwa mai zafi a robar da ta zauna dazu wadda saboda hakan
Mama ta saka musu ita.


"Kin sanni da kunne ina jin me Mama take fada" ya kashe mata ido ya fita ya barta
da tulin kunya.


Lokacin da ta fito ya gama saka kaya sai wannan kamshin nasa na musamman take ji.
Shadda ce ya saka mara nauyi ga hularsa a gefe.


"Ba don ina tsoron kaina ba kuma dai ana jirana da na tsaya shiryaki da kaina baby"
yace lokacin da ya ajiye brush din da ya taje saisayayyen kansa.


"Na yafe fita ka tafi"
Kan gado ya fada sai lokacin ta kula ya chanja komai amma kunya ta hana tambayarsa
ina ya ajiye wadanda ya cire.


"Kunyar fita nake yi kada a gane" ya tashi yana tafiya a gefenta "tayani dubawa
tafiyata bata chanza ba ko"


Bubbuga kafa ta soma yi "Hammana bana so"


"Ba fa dake nake ba, nima bana so a gane ne kinsan manyan nan..."


Daga murya tayi cike da shagwaba ta ce "HAMMAAAA"


Yana kyakyata dariya ya fita. Kwandon abincin ya gani ya dauko ya dora a kan centre
table sannan daga inda yake ya fada mata ta tabbatar ta ci kafin ya dawo.


Shiryawa tayi cikin wani hadadden lace tayi daurin da ya bayyana gashinta da tayi
packing ta sako shi tsakiyar daurin sannan ta gaban ma ta ja dankwalin ya danyi
baya. Fuskarta tasha kwalliya tayi kyau sosai. Sauri tayi ta gama saka awarwaron da
ta dauko kalar kayan sannan ta fito falo ta dan karkade kura duk da babu. Turaren
wuta ta saka a ko ina kamshi kuwa ya soma tashi kana tahowa bangaren za ka ji.


Fridge ta bude babu komai na kayan abinci sai ruwa da lemo kala kala. Da yake ana
sanyi tunda suka zo Katsinan sau daya aka dauke wuta shima bata dade ba aka dawo da
ita. Abincin da aka kawo ta bude, doya ce da aka soya da kwai a flask daya sai
bread da farfesun kaza ya ji kayan kamshi. Ga kayan tea da ruwan zafi a flask.
Kitchen ta kai ta ajiye don bata jin za ta iya cin komai duk yunwar da take fama da
ita kuwa sai Hammanta ya dawo.


Awwab kuwa da gaske sai da Bilal yayi da gaske su ka shiga falon Mami inda iyaye da
kakanni ke zaune. Ana ta tsokanarsa sai su Bilal ke ramawa shi kam baki ya mutu
Schatzi kadai yake tunani. Da su ka gama fita suka yi zuwa wurin Radhiya an gama
saka kayayyakinsu a motocin da zasu bi.


Duk kunya ta isheta gashi babu su Rahima an barta ita kadai da manya kowa da abinda
ya ke kara mata na nasiha. Kafin su fita Awwab ya dawo ya shiga daki sai gashi da
envelop guda biyu. Daya ya bawa Hajjo dayan kuma ya baiwa Gwaggonta Mubaraka kowa
su raba da abokan tafiyarsu. Shi kadai ya rakasu ta biyosu zuwa bakin kofar net din
suna cewa ta koma ba sai ta fito ba.


Tunda Awwab ya shigo suka ci abinci tare suke makale da juna sallah kadai ke fitar
dashi. Shagwaba kala kala yana gani tana kuma burge shi sai nan nan yake da ita
kamar kwai. A haka ma baya samun yadda yake so sosai saboda kunyarsa da tayi mata
yawa. Abincin rana ma kawo musu akayi daga ciki wannan karon Rahima ce ta kawo
Awwab ya karba. Su Zahra da Fauziyya suka kafa naci kamar bala'i sai sun je wurin
Radhiya.
Mama tace "gulmammu wace acikinku bata ga wannan daren ba eyye. Zaku je ganin kwaf
ku gani ko ta sauya tafiya ko..."


Mami sai da tayi dariya don ba karamar kunya suka ji ba har Fauziyyan kuwa. Zahra
kamar ta kifa don sauri ta fice daga falon kafin a karasa barota. Mama kuwa sun
kunnata bata iya yin shiru ba ta cigaba da sababi.


Kafin magariba ragowar tawagar Malamijo sun iso gidan saboda tafiya Nijar da safe.
Salame ce akan gaba ko zama bata yi ba wai sai ta ga dakin amarya. Sakin baki tayi
tana kallon kayan kudi sai da Mama taje da kanta ta yo waje da ita wai da bandaki
zata shiga ta rage mara tayi alwala ko tunanin cewa bandakin daya ne kuma a cikin
dakin baccinsu bata yi ba.


Sai da suka shiga ciki ne ta ga Halifa tare da Emzee da Ibrahim. Duka su ukun sun
gaisheta babu yabo babu fallasa sai dai yanayin fuskar Emzee ya tsaya mata a rai
fiye da zato da tsammaninta. Ganin Rahima ne ya mantar da ita komai abin mamaki ga
ita kanta Rahiman Salame wani mugun tattali take yi mata kamar ta maidata ciki.
Tunda Malamijo ya kirata yayi mata tas akan mutuwar idon Rahima tasha kuka kamar ba
gobe.


Ba komai ya tsaya mata a kahon zuciya ba irin yawaitar lokutan da Rahima ke
durkusawa a gabanta tana rokon idan laifi tayi mata ta taimaka ta yafe mata.
Yarinyar bata da matsala kuma bata santa ba. Burinta daya a duniya ta ga
mahaifiyarta ta sakar mata fuska ta kaunaceta kamar kowa. Ita da ta iya zuwa wurin
boka ta makanta Mairama da asiri yau an wayi gari 'yar cikinta ta gamu da lalurar
da indai wani abu ya sake samun dayan idon mai lafiya to ta makance kenan fa. Tana
ganin abubuwa amma ba ta iya rarrabesu. Ranar duk wani guntun rashin mutumci ma
nemansa tayi ta rasa. Fatanta bai wuce ta kyautatawa Rahima ba ko ta yafe mata
cikin sauki. Ga Halifa fuskarsa kullum a hade idan ya ganta musamman bayan matsalar
idon kanwarsa. Baccin kirki kasawa tayi da ta duba hagu da dama sai kaji tana ina
Rahimata?


A bangaren su Ummi ranar su ma suka wuce Nijar da Daada. Duk wani boyonta kallo
daya Mammee tayi mata ta ja ta uwar daki tana murmushi.


"Mairama ciki gareki ko?" Tace da hausarta mara fita sosai.


Ummi taji kunya sai sunkuyar da kai kasa take. Mammee kuwa tsabar murna ta fito
tana shelantawa. Ummi ta rufe kanta a daki ta kasa fita saboda yadda 'yan uwa suke
ta murnar wannan rantsatssen rabo. Zayyan yayi ta dariya yace maganinta kenan tunda
ta damu a boye gashi anyi mata mai gabadaya. Cikin 'yan uwansa mata harda mai
tambayarta wata nawa ne saboda a fara shiri. Ta ga gata muraran don ko cikin fari
ne a jikinta karshen abinda zasuyi mata kenan.

**********


Da daddare bayan sun gama dinner Radhiya tana wanke kayan da suka yi amfani dashi
bata ji shigowar Awwab ba sai hannuwansa da suka bullo ta gefe da gefen cikinta ya
riko plate din da take daurayewa suna yi tare. Jikinta tuni ya fara rawa saboda
hatta soso sai ya sarke yatsunsu sun wanke abu tare dashi.
Kiss taji a wuyanta ta kusa sakin glass cup din da suka gama daurayewa ya ce
"hankali baby"


"Ai kaine"


"Ni sarkin laifi me kuma nayi"


Tsuke bakinta tayi ya cigaba da abinda yake yi yana birkita mata lissafi. A daddafe
aka gama ta rufe ido kawai ta kwanto da kanta kan kirjinsa sosai na dan lokaci sai
kuma ta juyo suna kallon juna "Chèri muje na hada maka kayan tafiya gobe"


"Kin hada naki ne?"


"Suna cikin akwatin da Zayyana ta kawo min dazu da ta kawo abincin dare"


Dakin su ka koma ya dauko wani akwati mai taya hudu daga kasa irin wanda duk
nauyinsa mai ja baya ji saboda a tsaye yake rectangular. Na biyun karshen ya dauko
ya nuna mata kayan da zaiyi amfani dasu ta fito dasu za ta zuba sai gani tayi ya
zazzage nata kayan akan gado.


"Hammana ya ka juye kayan ko basu shiryu bane?"


A akwatin da take zuba nasa ya shiga jerawa "babu amfanin mu tafi da bags daban
daban ne"


"Idan ba masaukinmu daya ba fa?"


Janyota yayi suka fada kan gadon yana zagaye fuskarta "nasa Yousuf ya kama mana
hotel na kwana biyun da zamuyi"


Ai sai ta kasa hadiyar yawu don fargaba "duk kowa yana nan sai mu tafi hotel?"


"Yes...ta kare min Schatzi kema kin sani" ya cigaba da zana fuskarta da yatsansa
"idan da nayi hakuri yanzu bazan iya ba...KEMA.KIN.SANI" ya fadesu dalla dalla
kafin ya shiga nuna mata soyayyar da ko rabi rabin abinda ke ransa bai sauke mata
ba.


Kayan da basu karasa hadawa ba kenan su da akwati daya da himilin kayansu dake zube
a gefe suka kwana a kan gadon. Tun asuba da suka yi wanka ta karasa hada musu kayan
ta gyara dakin ta wanke toilet. Basu bar komai a waje ba bedsheet din ma cirewa
tayi ta dinke ta turasu cikin ledar da yake ciki da kyar saboda gudun kura.


Motoci harda wanda babu budget dasu mutane sun bi su Nijar ganin kwai da kwarkwata.
Kamar kullum karamcin mutanen yana bawa Radhiya mamaki. Kudi ne dasu iyaye da
kakanni amma akwai tarbiya da tsagwaron hadin kai a zuri'ar Alh Ghousman Agali.
Gidan Alh Sidi Radhiya ta shiga saboda ance Umminta tana nan ta fada dakin da aka
nuna mata da murnarta nan ta sami Emzee suna rigima da Mammee tana tura masa nonon
rakumi ya damtse bakinsa yaki karba. Kan Ummi ta fada da murnarta Mammee ta sakarwa
Emzee robar nonon ta tashi tana fada.


"Alheran yaushe zaki girma ne ni Aghaisha"


Turo baki tayi tana nanikar Ummin "me kuma nayi miki daga shigowata?"


"Dagata kada ki kassara min jika, maimakon ki tayamu tattalinta sai ki tsaya
shirme?"


Ina kasa ta bude Mairama ta binne kanta. Emzee ya dago fuskarsa da nono ya watso
masa ya kalleta sai wani nauyi ya bakunce shi ya dukar da kai. Radhiya kuwa ihun
murna ta saki bilhakki ta sake rumgume Ummin tana murna.


"Wayyo ni, wayyo Umminmu Allah Yasa mace zaki haifa me kama dani" tace tana dariya.


Emzee ya kalli yadda take yi ya kalli Umminsu da kunyar da ta lullubeta sai ya
tashi kawai yaja hannunta "Hamma Awwab yana kiranki muje na rakaki"


Zame hannunta tayi "kai Emzee yaushe kuka hadu?" Ta juya zata kuma zama "Ummi wane
watttttt" keyyyy haka Emzee yayi waje

94 / 99