Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
kansa yana dariya lokacin da Yousuf yace kuma idan ya
cigaba da jan rai zai ji ana biki a Nijar. Yasan so yake ya nuna masa ya gano wa
yake so, shi kuma sai yaji kunya kada ya nuna abinda zai iya sosa ran Yousuf din.
Da kyar suka yi sallar asuba jam'i su biyu don sai da aka idar Awwab ya iya farkawa
saboda gajiyar da suka tara.
***********
Yau da Radhiya akayi aikin breakfast ita da Ummi suna yi tana kara yi mata bayanin
project dinta. Abin ya kayatar da Ummi matuka tace me zai hana tayi magana da Daddy
sai a nema mata alfarmar samun adireshin wasu daga cikin matan da suka zauna tare a
Sakkwato wadanda mazansu suka rasu ta saka su a sashen shirin nata da ta kira da
(Hidden Heroes).
"Ummi kece ta farko a cikinsu sai dai bazan iya saka ki a ciki ba saboda kuka
zamuyi ta yi" tace da kwalla a idanunta.
Da murmushinta mai ciwo tace "Allah Ya jikan Daadaa dinku. Halinku kadan ne da
bambanci. Shi baya shagwaba irin wadda kika koyo wurin Nasara sai dai ya shagwaba
wasu"
Dan tsalle tayi tana son hirar babanta "Ummi yana shagwabani?"
"Kamar ba gobe" ta amsa mata tana tuno rayuwarsu ta da murmushi na kufce mata.
"Kema yana shagwabaki ko?" Ta tsare Ummin da idanu tana daga gira daya da wani dan
banzan murmushi.
"Kaniyarki, fita ki bani wuri" ta biyota da cokalin miya. Dariya ta saka ta gudu
daki.
"Na fa zata ta kintsu ashe nutsuwar ta karya ce" Ummi ta cewa kanta ita kadai tana
girgiza kai. Mai hali baya fasa halinsa.
Yau ma atampa ta saka amma riga da skirt. Ita kadai take juyi a gaban madubin bayan
ta gama kwalliya ta karkata nan ta karkata can tana turo baki.
"Fita mana kije kiyi a gabansa sai ya fada miki inda yake bukatar gyara idan akwai"
Ta madubin ta harari Fauziyya kamar idanu zasu fado ta zagaya karbar Jawad zata
shirya shi Fauziyyan tayi wanka sai ga Zahra kamar an korota ta shigo da sauri kana
ganinta farkawarta kenan.
"Jama'a na shiga dubu a gidan nan yau"
"Me ya faru Adda?"
Kasa fada tayi wai saboda Radhiya ba aure gareta ba.
"Babu komai dai"
"Ina fa babu komai dazu Mami ta aiko Zayyana da Femi wai tana ta zuba ido jiya da
daddare kije ki karbe shi taji shiru ko kinzo kin kwanta ne kin bar mata shi. Bai
dade da komawa bacci ba yana dakin Ummi"
"Duk dad dinshi ya ja min" tace kamar tayi kuka.
Fauziyya ta zauna a gefen gadon kusa da ita harda rage murya za'ayi gulma "kwana
kika yi a can tare dashi?"
Duka ta daka mata a cinya kafin tace "dawowa yayi fa duk cizon sauro yayi wani
iri...daga hada masa ruwan wanka bacci ya daukeni"
"Allah Sarki...kinsan bacci babu ta yadda baya zuwa. Ina fata dai kinyi ya isheki"
Fauziyya tace tana dariyar ta dago me ya sami yayartata.
Radhiya taji sun sakata a duhu ta kasa fahimtar me suke nufi ga son jin zancen na
cinta tace "don Allah kuyi min bayani dalla dalla"
"Ke da wannan bayanin sai a gidan Hamma" Fauziyya ta sake yin dariya. Bakinta ya
kara budewa ta zama mai tsokana sosai.
"Me? Aure zaiyi? To ni ina ruwana ai dai ba zuwa gidan zan rinka yi ba" tace tana
bata rai.
"Nasan ba fahimta zakiyi ba dama. Shirya Jawad ga kayansa nan zanyi wanka."
Hannu ta mika zata dauki yaron ya zille ya koma wurin mamansa ta kuwa harare shi
kamar sa'anta ta fice daga dakin tana mita.
"Yara ku cigaba da yi min kyuya sai na baku mamaki. 'Yan mata zan rinka haifa in
hanaku aurensu"
"Allah Ya tashemu zaki fara ko, ke da wa kuma?" Ummi tace ta fito da Femi ya farka
yana neman mamansa.
"Jawad mana Ummi. Wai ni suke yiwa kyuya shi da Femi."
"Baki iya yi musu yadda zasu sake dake bane. Harararsu fa take yi Ummi"
Faduwar gaba taji tun da ya fara magana. Tabbas taji wannan kamshin mai shiga ko
ina a jikinta yana tasiri amma duk a zatonta ya shigo ya fita ne. Ashe yana tsaye
ne a bayanta da kofin kunu a hannu. Diba yayi zai koma daki ta fito tana mita.
Tayi matukar kyau kayan sun kara fito da ita. Rashin sanin yana wurin karamin
mayafi ta yafa da ya dan zame baya yadda gaban gashinta da ta daure da ribbon ya
kwanta ya bayyana.
"Kuma gara ta koya tun wuri don ni dai babu mai kawo min ajiyar 'ya'ya" Ummi ta
fada tana kokarin barin wurin.
"Ummi kawo shi ki gani" ta zura hannu zata karbi Femi dan albarka sai ya yarda "kin
gani ko..."
Zahra ce ta bude kofar dakin a lokacin yana ganinta ya soma kuka yana mika hannu da
zillo. Radhiya taji kamar zai fadi ta mika mata shi. Tana karbarsa yayi shiru harda
dora kansa a kafada ta shiga shafa masa baya.
"Nima dai inzo in haifi nawa su rinka like min ina muku yanga"
Ummi kada kai tayi ta fita tana murmushi da taji me take cewa. Sai yanzu Mama tayi
mata wayar baby ya tashi don Ummi bata tashinsa yin wanka sai dai ta jira shi wai
duk cikin 'ya'yan nasu shi tafi so dole ayi masa yadda yake so ba takura.
"Waye ya fada miki yara masu likewa iyaye dadi ne dasu?"
"Ba gashi kuna gayunku ba ke da Maman Jawad"
"Allah Ya baki muna gefe ai musha kallo. Wa yaga Radhiya da baby" Zahra tace tana
komawa dakin domin bawa Femi abinci.
Satar kallon Awwab tayi da yake tsaye a bakin kofar dakin Emzee tun dazu ya tokare
kafarsa da bango ya jingina. Hanyar fita tayi ya dakatar da ita.
"Kinyi breakfast ne?"
"Bana jin yunwa" tace a takaice.
"Realy? Kwaikwayona kika soma yi kenan" yace yana matsowa inda take tsaye. Yadda
take ganin yayi matukar kyau haka shima yake ganinta.
"Kai ba gashi zaka sha kunu ba" ta dan tura baki tana lumshe idanu.
"Na Yousuf ne..nima bana jin yunwa" ya sami kansa da cewa.
Kawai don kada ya yarda shi take kwaikwayo har ya fassarata ta dauko kofi a cikin
wata drawer mai kyan tsari dake gefen dinning table ta zuba kunu.
Gefenta ya tsaya ya rage murya tana jin wani abu na kwasarta "ki dena yi mana
addu'ar yara masu kyuya don nima ina da son kulawa kada su rinka shiga lokacina"
Ta riga ta gama zuba kunun ta ajiye flask din da babu abinda zai hana ta sake shi
yadda ta saki teaspoon din hannunta jiki na rawa saboda mamakin kalamansa.
"Careful and please kisa babban mayafi" yace yana kashe mata ido sannan ya ajiye
mata kofin hannunsa ya dauki wanda ta zuba yayi gaba ya barta da bude baki.
Jiki a sake ta zauna zuciyarta da gangar jikinta suna neman karkata akalar
tunaninta daga basarwa da jan aji zuwa sake fadawa cikin soyayyar Hammanta da bata
taba fita a ranta ba. Ta dade da fahimtar manufar Yousuf a kanta amma sai tayi
kamar bata sani ba saboda bata jin akwai wanda zata iya sakawa a gurbin da Awwab
yake zaune cikin zuciyarta. Kwantar da kanta tayi akan table din tana bubbuga kafa
"wai ni nake wahalar dashi ko shi yake wahalar dani...ahhhhhhh sai na rama nima"
Ta fuskanci da gangan ma ya fadi maganar don yasan me zata yi mata. Shikenan a tafi
a haka zata sake dammara don so take taji ya fada da bakinsa yana sonta kafin ya
koma aiki. Kai so take ya sota fiye da yadda a baya yayi ikirari. Yaji ta a ransa
kamar yadda take jinsa a nata. Kwalla taji ta taru a idonta...soyayyar da take yiwa
Awwab kamar tafi karfin kirjinta take ji lokuta da dama. Amma shine ya iya shareta
duk tsahon lokacin nan kawai don tabi umarnin Ummi a abinda yake gyara ga zumuntar
danginsu. Don dai yayi sa'a tana son shi ne amma ba hakura zata yi ba idan ba sai
ta rama. Ta nanatawa kanta kafin ta dauki kunun da ya ajiye mata ta shanye duk da
ya huce sai dumi kawai.
Karfe uku suka firfito Daddy yace su biya har Asokoro gidan Plateau state
government house su gaishe da maman Arifah da take ta cigiyarsu. Taron matan
gwamnoni ta taho Arifah tayi mata rakiya.
Dakin Ummi taje shiryawa ta samu ta sanar da Tante gidan wa zasu je fa.
"Kada kice min tsoronsu kike ji saboda abinda ya taba hadaku"
"Ni bana son zuwa ne kawai" tace a sanyaye da gaske tana jin karayar zuciya.
"Ina sojan 'yata ta shiga ta bar min wannan mai tsoron? Sunyi zaton suna da abinda
zai kaiki kwadayi ne ina ga tun farko shiyasa suka kara rainaki."
"Duk fa akan Ghazalatun nan ne"
"Ai da baifi da ba amma Mairama tayi musu kawaici don a zauna lafiya. Ki saki
jikinki in kunje idan ba haka ba za'ayi aurenku ne kina kin shiga dangin miji?"
Shagwabar ce ta motsa tace "Ni nace zan aure shi ne Tante?"
"Baki ce ba shiyasa tunda na kula Yousuf dina na sonki zan fadawa Papa"
Tashi tayi da sauri zata gudu Nasara ta rinka dariya tace ta saka kayanta ta gani.
Tana taimaka mata ta shirya tana bata sirrikan sake janyo Awwab gareta "idan na
gaji da gulmar taku zaki wayi gari watarana kawai a kaiki gidansa an daura aure
kuna bacci"
"Kamar wata 'yar tsana"
"Yi sauri kafin Mairama ta shigo ta fara mana fada daga ni har ke"
Abaya ce ta gani a fada kalar lilac mai ado ruwan madara. Duwatsun jikinta kadan ne
ba irin mai daukar ido daga nesa ba an jera su sunyi zagaye zagaye daga wuya har
kasa a tsaye ta tsakiya. Gefen mayafin ma haka yake sai dai kafin tayi rolling sai
da daura wani karamin dankwali saboda wancan yana da santsi kada ya zame ga maikon
kanta. Kayan kwaliyar Laura Mercier take amfani dasu. Tayi light make up dinta tasa
janbaki nude bayan tayi lining lebenta da lip liner purple. Sai ya tashi ya bada
wata kala mai kyau. Wani killer smile ta saki tana kallon Tante tana gode mata a
ranta. Matar nan ba karamin kulawa da gyara take bata ba. 'Ya take yi da ita da
zuciya daya shiyasa itama ta bata matsayin da ya kamaceta na uwa.
Garin yayi lufluf sanyin bai fara hana sukuni ba. Takalminta heel ne shiyasa tana
tafiya taku daidai irin na matan da suka san kansu ta fito da karamar sling bag
wadda babu komai sai tarkacen su hoda da wayarta a hannu.
Tun daga kofar gidan Mami da suke jiranta saboda motocin a can aka ajiyesu Awwab
yake kallonta ya kasa dauke ido. Wani mahaukacin kishi ne ya taso ya rufe shi da ya
ga kamar duka hankula suna kanta ne. Itama shi take kallo tana murmushin da yake
kara susuta tunaninsa. Gaskiya motar da zai ja yake so ta shiga ta zauna a kusa
dashi. Da ka yayi mata alamar ta taho ai kuwa ta nufi motar. Sai da ta tsaya a gaba
kamar zata bude ta juya wurinsu Fauziyya.
"Adda wannan zaki tuka?"
"Wannan Hamma ne zai ja"
"Ohhh" ta juya ta koma jikin daya motar ta shiga baya ita da Zahra da Femi. Gaba
kuma Zayyana ce da Jawad sai Fauziyya da zata ja su.
"Rufe bakin mana loverboy" Raji yace da turanci suka tafa da Yousuf suna yiwa Awwab
dariya. Wai shi zata yiwa haka ta sa masa rai ta basar. Ba don gudun fadan Ummi ba
da babu inda zai je saboda bashi da kuzarin tukin ma. Wani kallo ya watsa musu suka
sake kwashewa da dariya sannan suka shiga motar yana gaba Fauziyya na binsa a baya.
"Radhiya ba sauki yau kin motsa mana Hamma. Jikina yana bani kamar da wuya ki koma
France babu aure fa kila ma da dan guzuri"
Zahra ce ta zunguro Fauziyya rainon Mama zata yi barin zance a gaban Zayyana. Jinsu
kawai take tana murmushi da kewar 'yan uwanta Ibrahim abokin fada da Emzee mai
lallabata. Da suna nan ko kallon wannan motar bazata yi ba. Radhiya tayi murmushi
kawai zuciyarta fes. Masu sayar da irin lemukan nan da ake saka kankara a leda ta
hango maltina yawunta ta tsinke. Da can bata iya sha har cewa suke giya ce. Zuwanta
na karshe ta dandana shikenan ya zama abin shanta har da guzuri da zata koma.
"Adda don Allah saya min maltina"
"Wacce a ciki? Nima fakiriya ce irinki babu chanji a hannuna" Zahra ta amsa mata.
Dan turo kanta tayi gaba "Adda Fauzinmu taimaka"
"Ni da kika ki shirya min yaro harda harara"
"Yanzu kullata ta kika yi a ranki kamar ba babba ba? An dai yi abin kunya"
Yadda tayi maganar yasa su duka dariya. Zahra tace "Wani idan ya kalleki a haka dai
zai ce irin high class babes dinnan ne. Sai an zauna dake a gane ashe 'yar soja ce
mai balotelli"
Rokon maltina ta cigaba duk junction amma Fauziyya taki saya.
"Ki roki Hamma idan mun tsaya"
"Roko zaki koya min?" Ta zaro idanu.
"Kayan masoyi ai naki ne...ke da kuke sharing spoon meye don ya saya miki maltina?"
Bata sake iya magana ba taji kunya ta koma ta zauna shiru har suka isa. Ita bata
taba zuwa gidan ba. Su kuma rabon su da zuwa tun bikin Ghazalatu farkon tafiyar
Awwab Ukraine. Su ne a gaba ita a karshe suka bi bayan mazan zuwa cikin gidan.
Zahra ke ta sallama shiru ba'a amsa ba. Mai aiki ce ta leko daga baya lokacin Awwab
ya fara jin haushin zuwan nasu tace su shigo Mummy tana sama za ta yi mata magana.
"Kice mata su Zayyana ne" Zahra tace su duka suka sami wuri suka zauna a falon da
mai aikin ta kaisu.
Muryar mace tana kuka suka ji wata tana daga murya "Mummy ba fa zan koma ya
kasheni ba"
Kafin Mummy Gambo tace wani abu mai aikin ta fada mata suna da baki.
"Su waye?"
"Wai su Zayyana"
A dan tsorace tace "ba dai falon kasan nan kika kawo min su ba ko"
"Mummy ke kika ce nan zan rinka kawo bakinki"
Ranta a bace kamar ta kai mata duka ta fasa tana huci. Karshenta sun ji hargagin
Ghazalatu. Tsaki tayi tace ta kai musu abin sha tana saukowa. Bayan fitarta ta koma
kallon Ghazalatu da ta rame tayi baki kamar ta dade tana cuta. Ga fuska a kumbure.
Ido daya yayi ja jini ya kwanta.
"Sami wuri ki kwanta zan kira Hussaina idan sun tafi ba aura masa ke akayi don ya
kasheki ba"
Cikin takun kasaita ta sauko ta ga falon nata a cike. Duk yadda taso daure fuska
kasawa tayi tana ganin Jawad da Femi suna ta kai kawo babu mai shekara biyu cikinsu
amma duka akwai girman jiki da lafiya. Iyayensu sun gaisheta harda Radhiya da bata
gane ba ta dan saki fuska tana yiwa su Jawad wasa.
"Yaya Mamin taku kowa lafiya ko?"
Zayyana ce ta amsa da "lafiya kalau"
"Madallah, ku masu gida ina cefane ko haka kuka zo min hannu na dukan aljihu?"
Dariya ce su Fauziyya ke yi ta yake kowa ta ciki na ciki yadda ta yiwa Maminsu
rashin mutumci musamman da bikin Ghazalatu.
"Awwab yaushe a gari? Yaya aiki?"
"Shekaranjiya muka zo da Zahra. Ga mijinta Raji"
A ladabce Raji ya sake gaisheta don Yarbawa akwai ladabi sosai. Kyakyawan mutum a
haka harda dan gemunsa na ustazai amma ita ce mai yadawa a dangi cewa Zahra ta rasa
miji an buge da auren bayerabe. Sai gashi a gidanta ido ba mudu ba yasan kima tasan
cewa babu tsiya a tare dashi. Kyakkyawar yarinyar da take ta wasa da Femi ta kalla
"wannan fa, bakuwa kuka yi?"
"Radhiyan Hamma Awwab ce" Fauziyya tace kai tsaye lokacin da Ghazalatu take
saukowa. Ita da Mummyn suka zuba mata idanu sai ta basar duk da ta sake takura ta
koma gaishe da Mummyn.
Ghazalatu kamar ta juya ta koma don bakinciki. Radhiya dai da ta sani 'yar kauye
mai askakken kai ce a haka kamar wata balarabiya. Murmushin da Radhiyan tayi tana
kallon Awwab shi ya gaskakata mata ita saboda wannan dimple din nata. Mayar mata da
martani yayi har yaso ya manta a ina suke.
Kishi fal a cikin Ghazalatu ta kalli Awwab yadda ya sake zama babba ga cika ido.
Sai zaman ya koma na kurame tunda akace Daddy Haroun baya nan. Mummy tana hango
wautarsu Ghazalatu tana jin takaicin rabasu da Mummyn tayi. Nura dukanta yake kamar
jaka idan Mummy tayi magana sai Hussaina tace Ghazalatun ce bata da tarbiya. Kudi
ne suka so tatsa Mummy taki saki shiyasa suka dorawa 'yarta karan tsana. Drinks aka
kawo harda maltina amma Radhiya ta kasa sha musamma da Ghazalatu ta rinka jan Awwab
da hirar aiki da course da taji yaje Ukraine.
"Muna jiran tsarabarmu"
Tausayi take bashi yana son tambayar me ya sami idonta yana tunanin kada ya bata
kunya sai yace "zan kawo miki kafin ki koma KT. Bari mu wuce muna sauri ne"
"Da wuri haka Awwab ina zaku je, zaku dawo ku gaisa da Daddy ko"
Fauziyya ce ta sake cafewa "gidan abokin baban Radhiya"
Ghazalatu tace "a nan din? Nufina a Abujan nan? Cikin Nyanya hala"
Cin fuska Awwab ya hade rai Zayyana ma da abin ya bata haushi tace "gidan gwamnan
Plateau a Asokoro"
Mummy sai ta hangame baki tsabar mamaki. Kai gidan gwamna ai da mutane kila dai
maigadi ko irin gardiner dinnan.
"Hamma kafin ya fara kira yace ya jimu shiru. Kasan halinsa da yaji Radhiya tazo
Nigeria ya rinka damuwa kenan"
Sakato Ghazalatu tayi tana kallon su "ba a Nigeria take ba?" Tace da mamaki Radhiya
kunya ta kamata yadda su Zahra suke jindadin abinda suke yi musu.
"Kakanta ya kaita France ai can take karatunta"
Awwab kasa jurewa dramar matan yayi yace su fito haka. Harabar gidan Mummy ta
rakosu tana takaicin me ya rabata da yayarta mai sonta da zuciya daya da yaranta.
Ta dawo daga rakiyar Hussaina amma kunya harda ta Ummansu ta kasa fadawa kowa halin
da ake ciki.
Suna mota Fauziyya tace "dalla muna ta wasa ki maimakon ki turance su ko kiyi
french ke da Yousuf tunda ba kowa ke jinsa ba ki tada hankalin 'yan bakinciki"
"Naga alama kin fini rigima yanzu Adda"
"Hmmm ai dole bakina ya bude in fada miki 'yan mata sun saka min miji a gaba da
waya. Shi kuma ya fiye shiru shirun wai wulakanci babu kyau. Tuni na mike kafin ya
dauko min qaya"
"Su Fauziyya an iya kishi"
"Allah Yasa my in law ya kyallo wata idan kunje garinsu"
"Ba amin ba"
Radhiya da Zayyana suka rinka dariya yadda yayyen nasu ke fadan sakuwa da sakuwa.
An san da zuwansu gidan Excellency suna isa aka bude musu gate. Cikin girmamawa aka
kaisu falon matar gidan. Bata da ji da kai kamar mijinta ta rinka jansu da hira
tana fada musu me yiwuwa fa sai sun dawo cikin sati saboda jibi Excellency zai
taho.
"Munyi waya nake ce masa zaku zo yace gobe yana son ganinka da wuri Awwab wai akwai
important issue da zakuyi discussing"
"Ko maganar Arifah ce" da yake ta nuna sha'awar zuwa Ukraine masters yace sai ya
tambayi Awwab yanayin kasar.
Radhiya sai ta zaci ko maganar hadin aure ce kishinta ya motsa. Suna haka Radhiyan
ta shigo tabi matan nan kowacce ta rungume tana murnar ganinsu.
"Ashe duka kunzo babu gayyata. Mom kinga ni nake son zumunci dasu basa nemana.
Captain