Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
sai da aka binciko wanda aka buga masa
KIA wato killed in action. Sai gashi suna bin komai da kyau aka gane gaskiyarsa
daga kwanakin wata da abubuwan suka gudana.
Babu wanda ya iya tafiya saboda su ma takaitaccen lokaci Mr President ya basu su
hada komai. Ga Excellency shima nasu ne tsohon soja ya roki alfarma shima. Lokaci
ne da siyasa ta gabato zabe saura wata uku. Dawowar Zayyan wata gagarumar sa'a ce
da dama da ta fadowa shugaban kasa mai ci a lokacin zaiyi amfani da ita wurin
karkafa kamfen dinsa. A matse yake da ya samu a fito da komai fili domin duniya ta
shaida irin kokarinsa da jajircewa. Su kansu sojojin yana son samun hadin kansu ne.
Da farko ranar da aka ce masa gwamnan Plateau na son magana dashi kamar bazai
amince da wuri ba saboda dan jam'iyyar hamayyarsu ne wanda suka tsayar da wani
jajirtaccen tsohon soja a matsayin dan takarar shugaban kasa. Sai da yaji me yake
faruwa shine fa ya sako kansa ayi dashi. Shine fa tun daga saukar jirgin da ya
dauko su zuwa yanzu ana ta daukar komai a video ne da hoto. Idan komai ya tafi
daidai a saki al'ummar Nigeria ta shaida.
Karfe uku na dare ranar talata shabiyu ga watan november 2015 aka kammala bincike
akan Lt Zayyan Muhammad Tureta. Babu wanda bai nuna gajiyawa ba sai shi kadai. Da
sun bukaci a wayi gari a haka da matukar wahala su ga gazawarsa. Ko da ba a filin
training bane, Zayyan ya horo matukar horuwa da hakuri da juriya a zaman gidan
yari. Wani Lt. Gen mai mukami daidai da Cheif of army staff ne ya fara tasowa zuwa
gaban kujerar da Zayyan yake zaune sai ya mike shima. Hannu ya mika masa yana
murmushi da alama shine yake shugabantar committee din.
"Welcome home Lieutenant"
Zayyan ya karbi hannun ya rike kafin kuma ya gyara tsayuwarsa. Sauran mutum hudun
da akayi tare dasu kowa yazo ya bashi hannu suka gama sannan shugabansu a zaman da
ya fisu nuna shekaru ya murmusa.
"Nasan akwai dan sauran kananun abubuwa da suka rage kamar cike-ciken takardu da
sake daukar biodata dinka. Da kuma daukar statement din Rtd Major Mustapha da Rtd
Lt Hadir. Amma duk da haka ina da tabbacin cewa a karshen komai da zamu iya gamawa
a cikin sati guda kaine zaka fito da nasara kamar yadda muke tsammani."
Kansa ya sunkuyar kawai, emotions kala kala suna kai kawo a zuciyarsa. Mutumin ya
sake kallonsa yace "kana da ra'ayin cigaba da bautawa kasarmu ko kafi son yin
retire? Wannan tambaya ce da ya kamata nayi maka idan an kare komai..." ya dakata
yana dariya "but I realy can't wait naji amsarka"
Zayyan ya kalli mutanen nan daya bayan daya. Dukkaninsu a shekaru sun girme masa
amma kayan jikinsu sune suka fi komai fito da cikarsu a matsayin zaratan sojoji
irin wadanda kasa take tinkaho dasu.
"With all due respect Sir, I remain a soldier"
Gyada kai suke yi in approval. Shugaban ya kallesu sannan ya dafa kafadar Zayyan
yace "Although unofficial amma bazan iya tafiya gida ba batare da na gabatar muku
da precious mutum kamar wannan ba. GENERALS, I GIVE YOU A HERO LIKE NO
OTHER...MAJOR GENERAL ZAYYAN MUHAMMAD TURETA"
Gaisawa suka sake yi dashi sannan shugaban ya sake cewa Zayyan "strictly
unofficial" wato yana nufin yayi shiru har sai sun gama. Doki ne kawai ya debe shi
da yadda Zayyan din ya burge shi.
Bude musu kofa akayi daga waje aka kaishi wani babban hall sanyin AC na ratsa ko
ina. Chibuzor yana ta gyangyadi, Awwab na kallon agogo. Shi kuwa Excellency kamar
ba dare ba amsa waya yake ta yi ta 'yan uwansa 'yan siyasa da suke akan kayar zabe
mai zuwa.
Basu sha wahalar shawo kan Zayyan akan ya hakura gobe zasu kaishi gida ba saboda
shima ya san yanzu dare yayi da yawa kada ya firgita iyalin nasa.
Kalle kallen garin yake kamar ba cikin duniyar da ya sani ba har suka isa gidan
gwamnatin Plateau din. Maman Arifah tasan maigidan nata zai zo da baki amma bata
san ko su waye ba. Dawowa cikin dare da baki kuwa ba sabon abu bane ga 'yan siyasa
irinsa bare ma saboda harka da kamfen. Dakunan da za'a basu a gyare ga abinci sai
da Zayyan fa yaci alwashin wallahi shi da abinci sai na matarsa. Awwab out of
solidarity sai yaki ci shi ma. Chibuzor ne kawai yaci bacci ya kwashe shi. Awwab da
Zayyan kuwa sabuwar hira suka bude idanunsu sun soye. Hirar dai game da iyalinsa ne
shiyasa Awwab ya rinka kaucewa wasu abubuwan saboda yana gudun tayar masa da
hankali daga dawowarsa. Ai bazai so jin kalubalen da suka fuskanta su duka gidajen
uku ba kafin komai ya daidaita yanzu. Zayyan tuni ya fahimce shi. Dama can yana da
saurin karantar mutane shiyasa ya hakura aka mayar da hirar ta Alheran. Ai kuwa
baiyi danasani ba don ya sha dariya sosai.
Bayan sallar asuba Excellency ya kawo musu kayan sakawa da kansa. Duka kayansa ne
dai sun yiwa duka su ukun har Chibuzor yawa.
"Ko nasa a dinko maka kaya kafin muzo tafiya anjima?"
"Na fuskanci kamar da gayya kake son ja min lokaci. Wane irin dinki kuma ana zaune
kalau."
"Kasan Allah bazaka je wurin Maman Alheran a haka ba. Infact mai aski za'a dauko
yazo ya aske maka wannan kasumbar a gyara fuska sannan kayi wanka. Ko so kake su
rinka mafarkinka idan kaje a haka?"
"Baka tausayi na ne ko? To askin ma bazanyi ba" Zayyan ya koma ya zauna ya bata
rai.
Excellency yace idan ta kama ya danne shi zai danne shi ne ayi askin kuma a kulle
shi a bandaki yayi wanka.
Awwab yana kallonsu yana dariyar yadda suke wannan rigima. Rtd Col Nasiruddeen
tamkar babban wa yake ga Zayyan. Ya dauke shi kamar kaninsa da suka fito ciki daya.
Sarai ya fahimci yana kewar iyalinsa amma ko yaki ko yaso bazai barshi yaje garesu
a mummunar kama ba.
"Kai Awwab kalli babanka da kyau banda aski me ya kamata ayi masa" yace a
commanding voice.
Shima bai tsira ba sai da ya sami guzurin harara daga Daadaa. Ya daga kai yace "da
dai zamu samu a gyara harda farce"
"Kai Awwab haka zaka yi min?" Yace da muryar ban tausayi.
Excellency bai saurare shi ba ya kira PA dinsa ya fada masa abubuwan da yake bukata
saboda yana so yau Zayyan yayi sallar azahar a cikin iyalinsa. Harkar kudi sai da
kudi. Karfe goma na safiyar laraba an siyowa Zayyan kaya readymade shadda da
yaduka kala goma da takalma. Shima wai kawai don ya zabi wanda zai saka ne. An
dauko mutum biyu daga wani sanannen wurin aski na zama masu shegen tsada kamar idan
anyi askin baza'a kuma yi ba. Suna zuwa suka fara aiki. Mutum daya yana askin dayan
kuwa dakalalliyar kafa da faratan Zayyan ya tasarma da gyara. Bakinsa bude yana ta
al'ajabi wai ace zamani ya kai harda masu gyaran kaushi.
Ana wannan aikin Awwab ya samu ya kebe kansa ya kira Mama. Cikin rawar jiki ta
dauka a can kuryar dakinta duk da cewa ma babu kowa a bangaren nata sai Ibrahim da
Emzee suna nasu dakin.
"Awwab yaya" tace cikin tashin hankali. Jiya da kyar ta iya bacci tana ta juye juye
ga fargabar kada ta kira taji mummunan labari ko wani yaji.
"Mama na turo miki sako ta whatsapp. Ki duba zan sake kiranki" yace yana karamar
dariya.
Ita ta fara kashe wayar don sauri ta duba whatsapp dinta. Alamun Awwab ya turo mata
hoto ta gani. Hannu na rawa ta bude. Bata san lokacin da ta saki wayarta ta fadi a
kasa ba ganin hotonsa da mutumin da babu tantama aminin mijinta ne.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Zayyan...." dukawa tayi ta dauki wayar ta sake
kunnawa daidai da kiran Awwab ya shigo.
Kuka kawai ta fashe dashi "Awwab kuna ina?"
"Zamu taho daga gidan baban Arifah tare muke. A nan gida zamuyi azahar in sha
Allahu. Sai dai tun jiya yaki cin komai wai sai yazo gida zaici na Ummi"
Dariya tayi ga hawaye a idanunta "Zayyan kenan, yaushe Mairama zata iya girki idan
ta ganshi. Amma kada ka damu abincinta zai ci in sha Allah. Sai kun iso"
Mayafi ta yafa ta fita zuwa gidan Ummi. Baby Zayyan yana can a bayanta tun da tayi
masa wanka. Tayi mamakin fitowar Maman saboda sun hanata yin komai ita da Mami.
"Jikin ne Zainab?" Ta tambaya da kulawa.
Jiya tsabar damuwa kasa komai tayi sai tsananin fargaba. Da aka dameta da tambaya
tace zazzabi ne da ciwon kai suke damunta. Karshe dai Mami tace a dage taron sunan
da ya kamata suyi a jibi sai wani satin ta kara samun sauki. A ganinsu cikar da
gidan yake yi ne ya hanata hutawa. 'Yan uwa masu tahowa a yau kenan duka ta dakatar
dasu da kanta. Bata san me zai faru ba amma bata da wani kuzarin yi taron suna
wanda su Ummi ne suka takura sai anyi.
"Na ware sosai. Gajiya nayi na fito, kina da garin masara kiyi min tuwo? Miyar
kukar rannan kinsan ta min dadi sosai"
"Kinyi sa'a akwai saura kuwa."
Fauziyya na wurin tace bari ta yi Mama tayi saurin cewa akwai fruits a bangarenta
ko zasuyi fruitsalad kada su lalace. Radhiya taje ta kira suyi tare duk tayi laushi
saboda rashin wayar Awwab da shareta da ya rinka yi kwana biyu. Ta ma kudurta a
ranta ta dena basarwa idan ma dalilin haka ya janyo ya dena kulata.
Ummi bata kawo komai ba taje ta jika busasshen kifinta da ruwan zafi ta bara ta
wanke shi tas. Bata rabo da jajjage ba bata lokaci ta hada wake, naman sa da kifin
nan ta soma dafawa tare da daddawa da gishiri bayan ta kara albasa da kayan
kamshinta da Innawuro take hada mata garin tafarnuwa, citta, kaninfari da masoro.
Maggi sai miya ta dauko dahuwa. Girkin baifi na mutum uku zata yi ba yadda zai ishi
Mama har dumame. Tana yi suna taba hira Mama sai ta kalleta ta kawar da kai ta
share kwalla. Mairama komai nata da nutsuwa take yinsa gwanin sha'awa.
Sabon flask da ba'a taba budewa ba Mama tasa Radhiya da suke aikin fruitsalad ta
kawo mata ta zuba tuwon da ta kukkulle a leda.
"Yau kice da Baba Hadir za'a ci tuwon nan"
"Ko daya ki boye min a dakinki sai anjima zan zo naci" Mama tace tana mikewa.
"A daki kuma? A kawo miki mana"
"Ke dai ajiye min ko a nan ne kada a taba. Da zaki taimaka min da wannan shayin
naki mai kayan kamshi da kin gama min komai"
Ummi ta girgiza kai "anya baki kunso wani ba? Wannan abu kamar me yaron ciki"
"Rufan asiri ina fama da kaina. Zainabu tayi sanyi in fada miki. Idan ba gani nayi
ya fara takawa da kafarsa ba ko kallon babansu na dena yi"
Me Ummi zata yi kuwa banda dariyar mugunta. Allah Sarki Mama an ga haza. Dakinta
suka koma da hira da dabara Mama tasa ta kuma gyara shi duk da ma Radhiya ta gyara
da safe ta wanke toilet. Amma Mama tace wai ana sanyin nan da yakunno kai gadan
gadan ina ita ina bedsheet single. Ta fito da mai hade da duvet ta shimfida mana. A
take Ummi ta fara zargin wani abu amma duk iya tunaninta ta kasa. Wani mai masifar
kyau da laushi tsarabar da Radhiya tayi musu su uku zuwanta na karshe kafin wannan
ta shimfida.
Tana gamawa Daadaa wato baby Zayyan ya farka. Yana cinyar Mama dama da zata gyara
gadon. Shigewa tayi tana wanka zuciyarta na tunanin manufar Mama. Gabanta ne ya
fadi da tayi tunanin ko shammatarta akayi ne aka daura mata aure? Idan ba haka ba
meye na sa ta a gaba ta gyara daki. Hmmm zasu sha mamaki kuwa idan aka nemi turo
wani cikin rayuwar da bazata taba sake irinta ba tunda ta rasa Sojanta.
**********
Shabiyu da rabi kowa yayi wanka mata na gidan Ummi maza na bangaren Mama wurin Raji
suna ta hira. Mama ta koma wurin Ummi ta sallami duka yaran nan zuwa gidanta tace
baki zasu yi zata kira su su gaishe su. Ya rage daga ita sai Mami da Ummi. Zahra ce
karshen fitan tana tafiya Mami tace
"Wallahi Zainab mun gaji da wannan nuku nukun naki. Yanzu Daddy yace wai
Excellency ma ya kirasu su dawo gida, suna hanya shi da Baba Hadir. Kin saka mu a
duhu"
Kwalla ta share duk yadda taso daurewa "kuyi hakuri nan da mintuna kadan ne komai
zai fito"
**********
Zayyan kallon kansa yayi yana karawa. Babu abinda ya kai tsafta da gyara dadi. Shi
da mayar da jikinsa da yin kyau sosai sai an kwana biyu amma ko a haka sai dai ace
Alhamdulillahi. Fuskarsa ta fito an gyare shi sosai. Wanka kuwa kamar bazai fito ba
saboda jindadin ruwan da yayi da yadda yake cire dattin jikinsa. Lallausan yadi
irin na masu hannu da shuni fari kal Awwab ya zaba masa a cikin kayan da aka siyo
da bakar hula. Yau ya ga me ake kira turare designer da ko sunansa bai taba ji ba a
da. Komai na shiryawa hatta links din hannu Awwab ne ya saka masa. Shima yayi wanka
amma kayansa ya mayar suka fito duka aka dunguma motocin da suke jiransu. Yau mota
biyu akayi saboda gwamna baya son a gane shine.
Tafiyar minti shabiyar suka shigo cikin estate din bangaren gidajen guda uku da
suke gefe da gefe da juna.
Ana tsayawa Zayyan ya damki hannun Awwab.
"Tabani in tabbatar nine" yace muryarsa tana rawa da iyakar gaskiyarsa.
Awwab sai ya kara karfin rikon dake tsakanin hannuwansu. Gabansu duka faduwa yake
Zayyan ya runtse ido ya kuma budewa a hankali yake cewa "Ya Allah kasa ba mafarki
nake yi ba. Idan kuma mafarki ne Allah kasa na mutu a cikinsa"
Hannunsa Awwab ya sake rikewa suka fara takawa sannu a hankali bangaren Mairama Ali
Gidado uwar Alheran da Muhammad Zayyan.
"Ba mafarki kake yi ba Daadaa. Ka tsaya a nan minti daya in fara shiga" yace
lokacin da suka taka matattakala biyun da ake hawa kafin ya shiga gidan.
Da sallama ya shiga ya sami iyayen nasa duka a zazzaune sun saka Mama a gaba harda
Major ana son jin bayaninta. Tana ganin Awwab ta mike sa sauri.
"Yauwa Awwab kun iso? Ina yake?"
Sai suka kara daurewa kowa kai da Awwab yace yana bakin kofa zai shigo dashi.
Komawa yayi da baya ya bude kofar ya riko hannuwan Zayyan suna tsaye da Excellency
ya iso wurin.
Awwab ne ya daga labule yayin da muryar Zayyan ta karade falon a lokacin da yake
cewa "Assalamu alaikum"
[11/2, 7:11 AM]🏽
]🏽 : 45💕
Gabadayansa ya bayyana a gabansu kafin muryar ta gama shiga kunnuwansu.
"Daddy, Baba...." Awwab ya soma cewa sai dai tuni Zayyan yayi gaba haka ma Daddy
din da Baba sun taso daga wurin zamansu sun tare shi a tsakiyar falon.
"Zzzzayyyannn kaine?" Baba Hadir yace da karfinsa.
Manyan maza magidanta duniya ta sanyasu kuka tamkar yara. A wannan lokacin Hadir ne
tsaye a gaban Zayyan dinsa. Hannuwansa yasa yana shafa shi kafin su kankame juna.
Major da ya tabbata ba mafarki ne ba ya ware hannuwansa ya rungume su su duka biyun
a tare yana nasa hawayen. Excellency ma nasa yake yi a gefe yana jinjina karfin
soyayyar wadannan mutane.
Duk abinda suke yi Mairama tana zaune kamar an dasata ta kasa motsi. Tana iya jiyo
kukan Mami da Mama sama sama ita kuwa ta kasa. Wai shin ta cigaba da zama ne a
wurin tana kallon Sojanta ko kuwa ta tashi itama taje ta rungume shi ko sau daya ne
kafin ta farka daga wannan daddadan mafarki. Tunda take mafarkin Zayyan bata taba
irin wannan da zata gansu a wuri daya duka tare ba. Ina ma Radhiya da Emzee zasu
shigo suma su karasa cike mata mafarkin.
Tayi nisa a wannan tunani bata san Zayyan ya iso gabanta ya duka ba. Hannuwanta da
ya rike masu laushi wani irin shock yaji na soyayya, tausayi da girmamawa a gareta
da ta dauki shekaru ashirin da biyu tana dakon soyayyarsa bata yi aure ba. Runtse
idanu tayi tana ayyana da gaske ne haka Zayyan zai dawo mata duk ya rame? Ashe kuwa
zata dauki lokaci wurin ganin ta ciyar dashi duk abinda zai taimaka ya sake gina
masa jiki.
Rikon da yayiwa hannunta da kakkarfan hannunsa sai kuma yatsansa da yasa yana kore
mata hawayen dake gudana a fuskarta batare da ta sani ba shine ya sanyata dawo
cikin hayyacinta daga tunanin da tayi zurfi tana yi. Tsigar jikinta ke tashi a
lokacin da Zayyan ya mikar da ita tsaye ya dora hannuwansa akan kafadunta yana
tayata kukan.
"Wai kuka zamuyi ta yi ne? Bazaki yiwa mijinki barka da dawowa ba?" Yayi maganar
kamar baya so saboda shaukin dake dibarsa.
Wani hawayen ta matse ta hanyar runtse idanunta sannan ta budesu ta kalle shi da
kyau wani abu yana sauka a kahon zuciyarta. A hankali ta daga hannunta daya ta
shafa kumatunsa da wahala ta ramar.
"Ashe ba mafarki nake yi ba" tace lokaci guda ta sulale a jikinsa ta fadi
sumammiya.
"Fillo" ya kira sunanta hankalinsa a tashe. Mama ta daure tace ya kwantar da
hankalinsa abin ne yayi mata yawa. Ita kuma Mami ta samo ruwa a kitchen.
Ana shafa mata ta bude idanu suka sauka acikin na Zayyan.
"Da gaske ba mafarki nake yi ba?" Hawaye na gudana a idanunta take yi masa wannan
tambaya.
"Nima tsoro nake kada a tasheni daga bacci"
"Ina ka tafi ka barni?" Tace tana fashewa da wani irin kuka.
"Wurin da ko makiyina bana fatan yaje. Kiyi hakuri Fillo na aureki na barki
cikin..."
Kai ta shiga kadawa tana daga zaune akan kujerar da aka kwantar da ita da ta suma
"kada kace komai sai godiyar Allah"
Sun bawa kowa na wurin tausayi. Major ya katse maganar tasu saboda kada aji kunya
gasu a wurin ga Awwab da yake ta aikin share kwalla ya zama a koke.
Zayyan ya dago ya sake kallonsu yana fitar da murmushin mai karawa fuskarsa annuri.
Ya tambayi Awwab "ina kannenka?"
Da sauri ya nemi nambar Zahra tana dauka yace su zo su duka falon Ummi anyi bako.
Duka suka taho harda Raji. Baby Zayyan yana kafadar yayansa Ibrahim wanda Allah Ya
sanyawa kaunarsa daga haduwarsu jiya.
Daya bayan daya suka shigo falon. Kowa na zaune banda Awwab da yake daga gefen kofa
sai kuma wani dogon mutum da suna fara shigowa ya tashi yana murmushi.
Awwab yace da kannen nasa da dan karfi "introduce yourselves"
Radhiya ta juyo suka hada ido ta kawar da kai ita tana fushi kuma a ranta bata da
niyar fadin nata sunan.
Fauziyya ce ta farko ta matso gabansa zata gaishe shi ya mika hannu ya karbi Jawad
"Fauziyya?"
Tayi mamaki har ya nuna a idanunta. Shi kuwa ya tuna ta ne kasancewar duka 'ya'yan
Major ita kadai ya sani fara sauran duka wankan tawarda suke.
Yaronta ya bata saboda ganin wani da yayi a hannun ta kusa da ita ya karbe shi
shima "Zahra?"
Duk da bata sanshi ba taji dadi ko waye wannan mutumin mai kwarjini itama ya santa.
Wani jaririn ya kuma gani a hannun wani matashi da babu tantama kamanni sun nuna
dan Zainab da Hadir ne. Kafin ya ambaci sunansa Ibrahim yana