Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
yau kwana uku baki kiramu ba"
"Exams....gidan ma bana zama sosai fa. Yanzu dai ki dan zungure shi kadan yayi kuka
naji"
Duk abin Awwab sai da yayi murmushi suna hada ido da Zahra ya cigaba da tsakurar
abincin dake gabansa. Tana nan da halinta wato.
"Dan nawa zan zungura Radhiya? To ko dai balotellin kike so nayi miki? Ina da sabon
scisssors mai kaifi"
Dariya tayi da tasa tsigar jikin Awwab tashi saboda yadda yaji muryarta har tsakar
kansa. Dannewa yake kada Zahra ta sami damar tsokanar shi tace tayi galaba a kansa.
"To ni shikenan bazan ji muryarsa ba" ta fada cikin shagwaba.
Idanunta akan Awwab tana ganin wani annuri da yake bayyana gareshi a hankali tace
"zan ga ranar da zaki girma. Anyway yaushe zaki je Nigeria?"
"Saura na exams biyu amma Yousuf yace na jira mu tafi tare nan da kamar two weeks I
think. Zamu fara zuwa Agadez ne sannan mu taho"
"Yousuf dinnan yana ji dake" Zahra tace tana dage gira daya tare da kawar da kai
daga kallon Awwab da ya tattaro hankalinsa garesu batare da niyya ba.
"Kawai yana da kirki ne. Kiyi min addu'ar exams"
"Allah Ya bada sa'a, ni dai ki tabbata kinzo lokacin da zani"
Muryar namiji Awwab yaji yana kiranta da Alheran ya tashi a fusace ya bar falon.
Meyasa shi bazai kirata Radhiya ba kamar yadda kowa yake fada. Da takaicin wannan
abu ya kwana. Washegari jirgin dare suka bi zuwa Abuja. A hanya ya rasa yadda zaiyi
ya tambayi Mami waye Yousuf kada tace har yanzu ya damu da Radhiya. Shi ba damuwa
da ita yayi ba kawai dai curiosity ne.
Dreban Daddy da Ibrahim ne suka je daukarsu. Mummy ta kasa boye murnarta da suka
shiga estate din. Wai sune a gida irin wannan mai kyau kuma Major ya sami aiki.
Awwab ma yayi murna sosai ya kuma yaba da unguwar da iyayen nasa suke.
Nata gidan da sauran gyara na kayayyakin da zasu saka saboda bata nan. Abubuwa
kadan ta iya fadawa Daddy a dauko mata daga Katsina. Sauran kuwa sai tazo da kanta.
Daddy yana gidan Baba Hadir saboda Mama da Ummi sun hadu a gidan Mami suna girki.
Suna shiga Awwab yayi ido hudu da Ummin da yake yiwa wasan buya.
"Allah Ya kamaka Awwab babu alkawari...oh ni Mairama 'yan sa ido sai su zuba ruwa a
kasa su sha sunyi nasarar shiga tsakanina da dana"
Mama sai dariya "wai 'yan sa ido, kaga Awwab gara ka kamani don Ummi da Mami 'yan
hamayya club ne"
Shi dai kunya ma suke bashi ya gaishe su duka yana neman wurin zama Ibrahim ya nuna
masa dakin da aka tanadar masa don zaman hotel ya kare masa a garin tunda babu
fuskar zuwa gidan Mummy.
"Kunga yadda Awwab ya sake zama babban mutum kuwa? Ni dai gaskiya ayi masa aure
haka nan" cewar Mama
"To ya hau dokin zuciya yana ta fushi damu akan tafiyar Radhiya" Mama ta bata amsa.
"Shashanci kai, yana nan wallahi buzayen can zasu fara kawo mata hari. Wami hotonta
da ta turo min fa Allah nayi mamakinta sosai. Ki turo min shi Mami idan kun huta ya
kamata na karanta masa fari da baki"
Ummi tace "gidana zai fara zuwa akwai tamu dashi, duk abinsa sai yaje gidansu
Ghazalatu ya gaishe da iyayensa wannan karon"
Mami ta ce "ni dai a nuna min nawa dakin naje nayi wanka yunwa nake ji"
"Ummi inkiya akeyi mana mu fita fa...kinga ni nayi nan kafin ki fara jin gyaran
murya Daddy ya zo oyoyo"
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Zainab baki da dama wallahi. Amma zan fada masa
tunda sharrin naki harda shi"
"Rufa min asiri don Allah" sai da ta kusa kai bakin kofa ta juyo "yo ai dai gaskiya
na fada idan kin musa mu dawo mu tayaki wuni"
"Allah Ya shiryeki kina nan kina zance sai ya shigo" Ummi tace ta rigata fita.
Dawowa da baya Mama tayi tana nunawa Mami fridge "nayi miki ajiya fa ya kamata ki
fara dubawa ki sha..."
💕[11/2, 7:11 AM] 40.💕
"Alheran ZM Tureta
Gajeren faduwar gaba taji lokacin da daya daga cikin malamansu kuma supervisor
dinta ta leko da kanta ta kofar seminar hall din ta kira ta.
Duka daliban da suke aji daya tare su kadai suke zaune banda ita. Nasara tana zaune
a kusa da ita cikin kujerun da aka zube a korido din domin zama ko hutawa tana
karfafa mata gwiwa.
"Tante" Radhiya tace kamar tayi kuka.
"Ina nan ina jiranki kinji ko...jeki" Nasara tace da murmushi.
Kungiyar ma'aikatan jarida na kasar France ne suka rarraba kudade a fitattun
jami'o'insu suna neman zaratan dalibai. Gasa ce suka saka na neman zakaran gwajin
dafi inda aka baiwa daliban damar kowa ya kawo wata matsala da yake tunanin zaiyi
kyau a bude program a kanta imma ta gidan TV ko rediyo domin wayarwa al'umma kai da
kuma taimakawa ga wadanda abin ya shafa.
Dalibai uku ake son zaba a kowacce jami'a 'yan aji uku ko hudu za'a basu grant
(tallafi na kudi) suje suyi aikin da suka kawo na wata shida su dawo makarantar
dashi. Wandanda suka yi nasara kofa ce babba zata bude musu ta arzikin samar da
program da kila duniya duka sai tasan da zamansu. Radhiya ta kusa wata tana ta
bincike akan topic din da ya kamata tayi karshe ta tsaya akan abu guda bayan tayi
magana da Ummi da Baba Hadir. Su kadai suka sani sai Nasara. Jiya ko runtsawa ta
kasa yi ta gama hada slides na power point da zata yi presenting sannan ta dukufa
sallah da addu'a. Yousuf shine babban malaminta na addini bayan ta dawo kasar.
Bakin gwargwado tana da nata ilimin tun a gida don kafin su gama secondary ita da
Emzee sunyi sauka. To amma ilimi na sauran fannonin addini Yousuf yayi fice wurin
zaburar da ita a kansa shiyasa matsayi daban ta bashi. Tana girmama shi sosai idan
suna tare sai ka rantse wata muguwar nutsattsiya ce babu rigimar nan.
Sai da ta gama addu'ar Annabi Yunus da salatin Annabi SAW sannan ta kalli zoben
hannunta mai harafin A, aa hankali ta kaishi bakinta ta sumbata. Computer dinta ta
bude aka jona ta projector wakilan kamfanin Dupont Broadcast Corporation (DBC) da
malaman jami'ar da suke musu alkalanci suka fuskanceta.
Bakar abaya ta saka mai kyau da karancin ado irin wadda wuyata zagaye ne kawai bai
sauka kasa ba. Adon duwatsunta maroon ne shiyasa tayi nadi da maroon din mayafi
tana sanye da loafers suma maroon da suka zame mata yawancin takalman zuwa
makaranta. Hall din an kashe duka fitilu babu sauran haske sai wanda yake fita daga
makeken screen din projector din.
Bata ce musu komai ba sai wani gajeren video na sakan goma sha biyar da ta kunna
musu. Filin yaki ne baka jin komai sai tashin bomabomai da harbi gami da ihun
mutane da kukan yara. Wuri ne na firgici da tsoratarwa ga wanda bai san yaya
mutanen da suke da 'yan uwa a wuraren da rikici ke ballewa suke ji ba. A tsakiyar
wannan tashin hankali sojoji ne wani ya kwanta akan yara biyu ya toshe musu kunne
saboda karar bomb. Wani ya dauko wata mata mai tsohon ciki yana gudu da ita ga jini
ya wanke masa fuska alamun shima yaji rauni. Wani likita ne a cikin sojojin ya duka
gaban dan uwansa soja da hannunsa ya fita saboda tashin bomb. Kai jama'a mutane ne
a cikin tsanani basu san ina suka dosa ba. Duka mutanen da suke wurin tuni Radhiya
ta kwashe hankulansu da tunaninsu ya dawo ga abinda zata gabatar.
Hoton karshe ya tsaya ne akan wadannan sojoji kowa da abinda yake yi na ceton
al'ummar da babu lallai ma na kasarsa ne ta dora musu katon question mark (alamar
tambaya).
Cikin turancinta da sautin muryarta zai baiwa mai sauraro damar gane cewa
faransanci ya zaunu a bakinta tace.
"Who are they?"
Alkalai basu san me zata gabatar ba amma sun fara gyada kai in approval.
Murmushi tayi da ya kawata fuskarta ta dora da cewa "My name is Alheran and this.
Is. The Military Voice"
Hotunan screen din sai suka sauya inda zaka ga wani sojan rungume tsakanin
iyayensa, wani da 'ya'yansa, wani amaryarsa, wani matarsa da tsohon ciki wani kanne
da yayyensa suna dariya, suna murmushi ko suna hawaye.
"Tun farkon lokaci yana daga abinda yake daga darajar kasashe yawan rundunar sojoji
ko mayakansu. Sai dai mukan manta da cewa wadannan sojoji 'ya'ya ne, maza, iyaye
kuma 'yan uwa ga wasu. Suna tafiya filin daga a lokutan da iyalansu suke tsananin
bukatarsu. Sauran mutane suna zuwa wurin aiki su koma gida soja idan ya fita filin
daga shi da jindadi sai ranar da yayi sa'ar komawa ga iyalansa lami lafiya. Cikinsu
ko kunsan mutum nawa ne suka tafi iyalansu suna kuka suma suna na zuci amma basu
dawo ba?"
Hotunan suka karkata ga iyalan sojoji suna kuka, wani wurin kuma gawarwarkin sojoji
ne, wasu kuwa sojojin ne da nakasar rasa wasu bangarori na jikinsu.
"Kama daga KIA (killed in action), MIA (missing in action), dawowa gida da nakasa
ta gabobi ko lalurar da take shafar kwakwalwa wadannan sojoji suna wahala matuka a
duniya. Amma duk wanda ya dawo da wata tawaya ta jikinsa sai ya zama mutum mara
amfani ga al'ummarsa. Babu abinda suka sani ko suka iya sai tsaro amma tunda basu
da lafiyar yinsa shikenan amfaninsu ya kare. A haka rayuwar sojoji nawa muka manta
saboda babu abinda zamu mora a tare dasu. Idan sun mutu iyalansu kadai ke da asara.
Wasu sai dai su koma garuruwansu babu abokai, wasu matansu sun kasa zama dasu,
yaransu kila sun girma sai dai su kare rayuwarsu cikin kadaici da jin kawunansu
tamkar basu da wani sauran amfani"
Hotunan da suke ta tafiya akan screen din masu ban tausayi ne da taba zukata. Wani
ka ganshi a gidan giya, wani fuska da jiki bab u gyara, wani ya zama manomi a
kyauye, wani yana nan banda tuna lokutansa a filin yaki ko azabar da yasha a hannun
abokan gaba babu abinda yake yi. Wasu ma karamin hauka suke dawowa dashi duka a
dalilin bautawa kasarsu.
"Da wannan nake rokon ku bani dama in zaga in fito da rayuwar sojojin nan duniya ta
sansu ta kuma san cewa ko yaya suka dawo duk abinda ya samesu ya faru ne a
kokarinsu na kare dukiya da rayukan al'umma. Ina so sojoji da iyalan da suka bari
duniya ta kasa dubansu su sani cewa har yau har gobe suna daga cikin mutane mafiya
girman daraja a bainar al'umma saboda sadaukarwasu garemu. Nagode"
Fitilun hall din aka kunna gabadaya mutanen wurin suka mike tsaye ana tafawa
Radhiya. Cikin matan kuwa harda masu zubar da hawaye saboda tausayi daga hotuna da
video din da ta nuna musu. Sallamarta akayi akace ta jira tare da sauran da suka
gabatar da nasu. Sai bayan kusan awa guda an gama sauraron kowa aka kirasu domin
jin sakamako.
Tante Nasara tana nan a korido din ta kasa zaune ta kasa tsaye motsi kadan sai ta
kira Ummi tace wallahi ta saka mata 'ya a addu'a. Ummi sai dai tayi dariya tace ai
tana yi.
"Tanteeeee" taji muryar Radhiya kafin ta farga daga ina ne taji ta rungumeta tana
murna.
"Nayi ta daya Tante, zanyi Military Voice a Nigeria da Nijar"
Nasara ta rungume Radhiya tana ta murna. Ita take tuka su zuwa gida yayin da
Radhiya take ta waya da mutanen gida. Ummi, Mama da Baba, Daddy da Mami, Mammee
dasu Alh Sidi. Ibrahim da Emzee babu wanda bata kira ba tana sanar dasu cewa su
fara shiri tana nan tahowa Nigeria nan da sati daya.
***********
Sai kai kawo Ummi da Mami suke yi a hanyar dakin theatre din da aka shiga da Mama.
Ciki ya wuce kwanakin da ake sa ran haihuwarsa harda sati takwas yana cikin wata na
goma sha daya yayi mugun girma. An so inducing dinta da wuri taki saboda tsoro ga
dadewa bata haihu ba. Daga baya da kyar Baba Hadir ya lallabata sai da Ummansa da
Mamanta suka sa baki ma. Shine aka yi inducing din nata kwana biyu tana fama da
matsananciyar nakuda amma haihuwa shiru. Yammacin rana ta biyu ne aka yanke
shawarar yi mata CS.
Baba Hadir yana mota hankalinsa ya tashi matuka. Shiyasa ya bar inda su Mami suke
kada su ga shima namijin yayi rauni. Zainab dinsa bazai taba iya hada soyayyarta da
ta kowa ba. Tayi masa abinda har ya mutu bazai taba iya biyanta ba. Inama cikin zai
dawo jikinsa da ya hutar da ita. Text din Ibrahim ne ya shigo wanda tun safe yake
yinsu ya kasa amsa masa. Sauran kwanakin tana daurewa ta dauki wayarsa su gaisa.
Sauransa jarabawa biyu ya gama level 2. Ummi ta riga shi gamawa dama ba department
dinsu daya ba amma tare suke tafiya a karatun. Kwana biyu taje tayi a Sumaila ta
wuto Abuja saboda sanin halin da Mama ke ciki haihuwa ko yau ko gobe. Yau da ciwo
yaci karfinta har aka shiga cs din Ibrahim bai sami kowa ya daga wayarsa ba shiyasa
gabadaya ya kasa sukuni.
Baba Hadir yana kokonton amsar da zai turawa dan nasa Major ya kira shi ba wai don
ya amsa masa da baki ba, ya dai san zaiji me yace.
"Hadir ka bar mata a ciki suna ta nemanka an fito da Zainab. Mun sami namiji"
Kabbara Baba Hadir ya shiga yi a zuci yana ta kokarin ya iya fitar da sauti da
bakinsa ma. Waye zai karyata Kadaitar Allah a matsayin Ubangijin talikai? Shi Hadir
da ya shafe shekaru yana kwance sai yadda akayi dashi. Fitsarinsa da kashinsa tun
dansa Ibrahim yana da karancin shekaru yake wannan dawainiya shine a karo na biyu
ya sake haihuwa da Zainab. A take ya turawa Ibrahim kyakkyawan reply sannan ya fita
daga motar ya koma ciki.
Dakin da aka tura Zainab din aka nuna masa. Ummi na rumgume da baby din an nado shi
da shudin shawl mai laushi sai raba idanu yake yi. Mami kuwa ta saka shi a gaba wai
yasan yana son kallon duniya me ya zauna yiwa kanwarta a ciki.
Sai da ya dan kwankwasa sannan ya tura kofar ya shiga. Zainab baki ya mutu tana
kwance allurar anasiziya bata gama sakinta ba. Sai dai da yake ta ido biyu ce tana
jin me suke yi tana murmushin wahala. A kusa da ita ya zauna a gefen gadon Ummi ta
dora masa jajirinsa a hannuwansa da ya bude.
"Zz..Zayyyyan" Baba Hadir yace da dukkan dagewar da zai iya yana rungumar yaron a
jikinsa.
Idanun Ummi tuni sun ciko da kwalla har ta fara zuba Mami ta riko hannunta suka
fita domin a basu wuri.
"Hadir magana kayi?" Mama tace tana kallon fuskarsa.
Murmushi yayi mata yana shafa kanta da hannu daya ya kuma cewa "Zayyan"
"Alhamdulillah...don Allah ka rinka kokarin magana kaji. Ina son jin muryarka Baban
Ibrahim da Zayyan"
Kai ya gyada yana ta murmushi idanunsa na yawo tsakanin baby Zayyan da Zainab. Tun
ranar da aka tabbatar mata da cewa namiji ne ta sani ko bai fada ba sunan yaronta
Zayyan. Ko yana da rai tasan su biyun masu musayar sunayensu ga 'ya'yansu ne bare
kuma daya baya nan ya bar musu wawakeken gibi a zukatansu.
Kafin gari ya waye duk wanda ya kamata yaji haihuwar nan yaji. Iyayen Mama da na
Baba murna ba'a cewa komai. Har waya suka yi suna yiwa juna barka. Soyayyar nan
daga Allah ce. Dubi shekarun da tayi a gidan Alh Musa sau daya tayi bari sai gashi
daga samun lafiyar Hadir anyi ciki har an haife. Wannan shine dan soyayya inji
Mami.
Radhiya kamar ta jawo tafiyarta da ta rage kwanaki uku. Wani babban mall ta shiga
ta jidowa kanin nata kaya na ga na fada ta kara akan tsarabar da ta gama hadawa.
Duk zuwa gida sai tayi wannan tsarabar saboda bata ga me zata yi da kudaden da suke
jibge a account dinta ba. Mijin Nasara yayi daga Nijar kakaninta kamar masu gasa da
juna wurin yi musu aike ita da Emzee. Ga uwa uba His Excellency ya mayar dasu kamar
masu daukar albashi.
Kwananta Mama biyu a asibitin aka sallamota. Ummi ita ce uwar da tsakaninsa da Mama
shayarwa ce sai kuma dare idan zata koma gidanta. Mami kuma duk wata bukatar
maijego tana wuyanta. Baba Hadir gani yake sunfi kowa sa'ar zumunta a duniya. Babu
ta inda jini ya hadasu amma dangantakarsu kullum kara karfi take yi.
Fauziyya ta matsawa Bilal da zaiyi tafiya Lagos wani aiki ya kaita Abuja ita da
Jawad dinta da ya fara yawo ko ina. Zahra ma Radhiya tana sayen ticket ta fara yi
mata famfo har yau bata taba ganin Femi a zahiri ba. Ba don yaso ba Raji yace zai
kawota amma da sharadin idan ya kasa hakuri zata ganshi kuma dole su tafi. Shima
yana son zuwa gaishe da yan uwan iyayensa ne a Osun state shine zasu fara zuwa
kafin.ya dawo da ita Abuja.
Gidajen uku sun fara shiri duk da an dage suna ma sai sunyi sati biyu maijego ta
kara samun sauki.
Yau da wuri Ummi taje ta yiwa baby wanka ta dawo gida. Dakuna uku ne a gidan daya
nata sai na Emzee da Radhiya idan sun zo hutu. Rigima irin ta Radhiya wai dambun
shinkafa take so taci shiyasa Ummi ta koma gida ta dora. Idan ba haka ba tunda da
Nasara zasu zo tasan sai sun hanata sakat da mita. Hadi na musamman ta yiwa dambun
nan da kayan lambu da hanta gida ya kaure da kamshi. A wadace tayi shi kuwa saboda
dawowar Radhiyan rana dayane da Zahra. Dama shirya abinsu suka yi wai sun dade basu
hadu ba ana kewar juna. Mami ta aiko mata da farfesun kayan ciki cikin flask wanda
ta hada dasu da zata yiwa Mama saboda a nan duka zasu ci abinci bangaren Ummin.
Fauziyya tuwo tayi musu Zayyana 'yan mata kuma salad da drinks ta hada aka jere
komai a gidan Ummi. Su Zahra da azahar zasu sauka Radhiya kuma sai biyar na yamma.
Major jiran zuwanta kawai yake yi saboda murnar nasarar da ta samu na project
dinta. Ita da Zayyana da ta gama secondary bana ya tanadar musu wani babban
surprise.
Duka suna wannan abu Mama ta kira Awwab kwanaki biyu da suka wuce ta tambayeshi
yaushe zai dawo ne yace sai nan da sati uku. Yanzu haka ya koma Germany babbar
hedikwatar kamfanin nasu akwai abubuwan da zai karasa ya taho gida.
"Babu yadda za'ayi ka dawo ranar Juma'a?"
"Mama so nayi na gama komai yadda idan na dawo sai na cike wata biyuna kafin na
koma aiki" ya bata amsa.
"Ni dai idan da hali ka taho ina son ka taho iyayenka na bukatarka. Ka kusa shekara
fa rabonka da gida duka ka barmu da kewa."
"To Mama zanyi kokarin tahowa tare da Zahra tace min jibi zata taho. Idan na kwana
biyu sai na koma na karasa aikin"
"Allah Ya shi albarka Awwabun Ummi"
"Amin amma naki ne yanzu. Ummi ta dade da yayeni ai. Kada ma kice musu zanzo ita da
da Mami ba murna zasu yi ba."
Mama sai murna ta dana tarko zata sha kallo. Ta san idan Radhiya ta iso baifi sati
biyu zuwa uku zata yi ba zata fara aikin da ya dawo da ita. Shi kuma