Author : Batul Mamman Category : Complete Novels
manta wanki, shara da wanke-wanke.
Wahalar gidansu a yanzu har tafi ta da tsanani ko don zawarci suke oho. Hankalin
Mairama yana kan inganta rayuwar 'ya'yanta, na Salame yana kan me zata yi ta kere
Mairama ko ta hanata cigaba. 'Ya'yanta musamman Radhiya sun tsole mata ido. Abu
kadan ne zata yi ta kai mata hannu da duka amma Mairama bata taba tankawa ba.
Lokuta da dama wurin Yadikko suke zama ko Hajjo idan 'yan mutumcin suna kusa.
Wata rana ta gama zobonta da lamurje ta kukkulle a leda santana suna cikin wani
katon baho a nan bakin famfon tsakar gidan inda take aikinta ta tashi ta tafi jawo
ruwa a rijiya zata wanke wurin. Salame tana ta fakonta don dama ta gane yanayin
aikin nata. Idan ta gama kullewa sai ta janyo ruwa ta wanke wurin sannan ta dauka
ta kai firig dinta ta jera. Su kan wuni da wuta amma da wuya ta kwana.
Tafasasshen ruwan zafi Salame ta taho dashi a bokiti tayi daurin kirji kamar mai
niyar shiga wanka sai da tazo daidai bakin bahon da kayan Mairama suke ta sheka
musu ruwan nan. Ledojin dole suka yi laushi sunyi tsamo tsamo babu dadin tabawa.
Salati ta soma yi wai wucewa zata yi ta sirka ruwan wankanta don ta ga kamar famfon
wurin yana diga an kawo ruwa. Mairama ci gaba tayi da diban ruwanta sai da ta ciko
bokiti tana zuwa ta ajiye shi sannan ta cira hannu ta kwashe Salame da mari mai
gigitarwa don tana kallon yadda komai ya faru.
Ihu ta kurma gidan da suke neman abin gani kuwa aka fara fitowa bawa ido abinci.
"Ni kika mara Mairama?"
Rai a bace Mairama tace "ko zaki rama ne?"
"Kan bala'i, billahillazi baki mari banza ba sai na rama"
"Gaki ga kumatun Adda Salame. Na gaji da wannan abubuwan da kika tsira tun kafin
muyi aure har yanzu ana abu daya. Kece dukan min yara, yada min habaici da bakaken
maganganu duk akan me? Me na tsare miki?"
"Dole kice haka mana tunda kin rabani da wanda nake so"
Yadikko na jin haka ta kora yaran gabadaya tace su shiga dakinta. Hajjo ba kunya ta
bisu don jin ba'asi. Salame kasa karasa bayanin tayi don tasan ita ce da jin kunya.
Tabarmar kunya ta nade da hauka wai Mairama tana yi mata gani gani saboda ta fara
rike kudi.
Da daddare da Malamijo ya dawo Yadikko ta bashi shawarar ya raba musu daki mana.
"Babu wadda ta bani ko asi domin ginin gidan saboda haka idan zasu cinye kawunansu
ne ma su cinye bai dameni ba. Wadda taji haushi ta kawo miji tayi aure"
"Idan bazaka rabasu ba ka taimaka ka zame musu uba na kwarai ka kawo karshen wannan
rashin jituwa da yake tsakaninsu. Kafi kowa sanin cewa da ba haka suke ba"
Shu'umar dariya yayi kafin ya turo hularsa gaba ya bata amsa "ki kan bani mamaki
wani lokacin kamar baki san zafin zawarci ba. Kodayake baki taba danawa bane amma
cuta ce mai zaman kanta. Shiyasa kika ga suna harin junansu. Babu mai tayar min
hankali ni dai"
Babu yadda ta iya haka ta tashi ta bar dakin nasa tana kara godewa Allah da bai
bata haihuwa da Malamijo ba.
Mairama ta gama yiwa Karami shirin bacci ta goya shi tana jiran kanwarta ta kawo
Radhiya da take wasa a wurinsu Salame ta shigo ta dawo daga zance da dan gayun
saurayinta. Matashi ne ko auren fari baiyi ba. Baje ledar da ya bata ta tsire tayi
a gefen katifarta da burin cusawa Mairama haushi. Abin dariya yadda take ci tana
shuu da baki.
Tana ganin Radhiya ta sake bude ledar da kyau. Yarinya tace "Ummi nama"
Mairama ta dauko wata leda babba ta mikawa Na'ima kanwarta tace suje su raba sannan
ta dauko wata 'yar madaidaiciya ta bude ta janyo hannun Radhiya ta bata cinyar
gasasshiyar kaza. Sai yanzu take gode Allah da haka nan ta bawa Bature kudi ya siyo
kajin nan guda uku. Ta dauki daya ta basu biyu su raba.
Ai kuwa Salame ta shaka har wuya ta shiga fadin maganganu wai gara su suna kwance
ake basu. Wahalallu kuwa sai sunyi da karfin jikinsu kafin su dandani zakin nama.
Shiru ma magana ce. Mairama bata ce mata komai ba haushi ya kamata tsiren ya fice
mata a rai.
"Dazu nace kin rabani da masoyina baki tambayi ko waye ba bare ki bani hakuri"
"Indai Salisu ne nayi imanin bazai sakeki saboda ni ba. Allah kadai Yasan dalilin
mutuwar aurenki sai kuma ku kanku"
Kallon cikin ido ta yiwa kanwar tata "Mairama, na rigaki ganin Zayyan kuma na
rigaki fara...."
A harzuke Mairama ta tashi duk wani kulli na kanta yana kwancewa. Yanzun ta gama
gano duk abubuwan da Salame tayi mata sunfi kama da kishi. Duk da mijin nata baya
raye amma tana tsananin kishinsa itama.
"Ya isheni ba sai kin karasa ba, na fahimci da aurenki kike son nawa mijin. Idan
abinda Salisu ya gano ya sakeki kenan sai ince Allah Ya dada karawa."
Daga haka bata koma cewa komai ba sai da ta tabbatar Salame tayi bacci ta sha kuka
ta godewa Allah. Ta tabbatar Zayyan ya sani shiyasa shima baya son Salame saboda
kada yaci amanarta. Sabuwar kewarsa ke ratsa duk wani sassa na jikinta tana inama
yana nan tare da ita.
***********
Shekararsu biyu a gida Salame tayi aure. Kafin auren Mairama ta tuna cewa Salisu
abokin Hadir ne a lokacin ta kwantar da kai wurin sau uku tana tambayar Salame
kwatancen gidansu Salisu. Ita kuma ganin ta matsu tasan ko meye yana da mahimmanci
shiyasa taki fada. Gashi baya zuwa garin don idan za'a kawo mata Halifa aiko
drebansa yake likkafa ta kara ci gaba.
Bayan auren Salame ne Idris dan gidan Mal Kallamu abokin Malamijo ya sami aikin
koyarwa a makarantar firamare ta gwamnati ta cikin Sumaila. Da yake suna shiri da
Mairama kamar wasa ya gabatarwa Headmaster da ita akan ko 'yan aji daya ne ta samu
ta rinka koyarwa. Shine ya amince aka yi mata cuku cuku sai gashi ta sami aikin a
karkashin L.E.A. Kwalin karatun nata iyakarsa sakandire shiyasa bata wuce aji daya
ba a koyarwar. Ita dai ko yaya ne hakan yayi mata don albashinta yana mata rana ga
cinikin zobo da lamurje.
Haihuwar Salame daya aurenta ya sake mutuwa. Wannan karon lalaci da rainawa miji ya
janyo mijin ya saketa. Duk abinda zai kawo mata sai ta karba a wulakance tace ba
haka baban Halifa yake yi ba. Sai da ta kaishi makurar da yayi mata duka ya sakota.
To yanzu ma an sake dawowa gidan jiya. Dan da ta sake haifa shima babansa ya kaiwa
yarsa. Ta dawo gida an sake komawa zaman zawarci ga rashin abinyi. Bakincikinta ya
karu da yadda Mairama da yaranta suke rayuwa ta rufin asiri. Duka suna karatu a
inda take koyarwa.
Ta soma saka gilashi ne a lokacin da ta fara fama da matsanancin kaikayin ido da
gani dishi-dishi. Ta sha wahalar idon sosai ta kuma kashe kudi.
**********
Sun dawo gida da Emzee ya shiga dakunan duka matan gidan su hudu don tuni Malamijo
ya sake cike gurbi. Yadikko tana nan a matsayin uwargida Hajjo kuma ta biyu sai
amare Hanne da Binta.
A gajiye take ta kwanta tana murna anyi hutu. Sallama taji anayi ana kwala mata
kira ta tashi a zabure Salame tana kwalliya zata je wurin mamanta.
"Uwar yarinyar nan Alhihi take ko me kace Danmama?"
Danmama ya zumburo baki "Alheran amma Radhiya naji ana cewa. Ita ce ta mareni kuma
Anti batayi komai ba saboda 'yarta ce"
"Allah gamu gareka" Mairama tace a ranta kafin ta fita tsakar gidan zuwa wurin
matar.
"Hajiya kiyi hakuri rigima ce irin ta yara kuma tun a wurin an hukunta su"
Rai a bace tana nuna bayan Danmama ta ce "a hukuncin ne aka yi masa bulala biyar
ita kuma biyu saboda son kai. Dama wane adalci kuke yi idan kuna koyarwa a
makarantun da 'ya'yanku suke. Daga yau sai yau ki jawa 'yarki kunne. Idan ta sake
taba min yaro bazan yarda ba"
Hakuri Mairama ta bata duk kunya ta isheta. Radhiya ba dai dauko magana ba. Idan
anyi magana tace ita 'yar soja ce. Yadda take alfahari da aikin babanta sai ka
rantse ta tashi tare dashi. Ko ina ta tsaya ma yanzu bata sani ba. Bari dai ta dawo
yau mai rabasu sai Allah.
Ashe gidan Mal Kallamu ta bi Uncle Idris. Can taci abincinta a bangaren amaryar
Idris din sannan ta fito suka hadu da Malamijo a kofar shiga. Harararta yayi kamar
ya kwadeta jiya taje gonarsa ta sami wani sabon maikaci da yayi ta nuna masa wata
tinkiya wai Malamijo ne ya aiko ta fada masa a yanka ya dau kai da kafa. Ana cikin
fida yazo ya gani jikinsa na tsuma yayo kanta tace gani tayi ta kasa. Kunnenta ya
damko tana ihu
" 'Yar kundun uba ta ina kika ga ta kasa din?"
Ba yadda ya iya a dole jiya gidansa aka ci dafge kowa ya warwasa. Dakinsa ta bishi
yana gwawiyar kashi tace "Malamijo ashe kaima kana son naman dai. Allah Yasa in ga
wata ta kuma kasawa" da mafici ya biyota har yana tuntube.
Ita ce a gaba ta hango Umminta da Danmama da mamansa. A guje tayi niyar komawa
Malamijo ya riko wuyan rigarta ya kaita gabansu.
"Mairama ki jawa 'yarki kunne idan ba haka ba wannan karon idan kunje hutun
Sakkwato ki barta a can. Yarinya ce kamar aljana. Dubi kaninki nasa salihancin har
haushi yake bani. Ke kadai kina mace kin tattaro duk halayen kiriniyar kin dorawa
kanki"
Kallon da ta ga Mairama na yi mata tasan yau jiki zai fada shiyasa tana tura baki
da magana ciki-ciki tace "to ba shine yake wakar wai Malamijo tsolon rake ba, rama
maka fa nayi"
Jikin Malamijo da na uwar Danmama sai yayi sanyi. Danmama yayi wiki-wiki da idanu
hakan ya tabbatar ba karya take ba. Babarsa kuwa ta talle masa keya tana cewa ya
bashi hakuri. Yara kuwa sai dariya suke a hankali Malamijo yaji kunya ya shige
daki. Kunnen Radhiya Mairama ta kama tace ta wuce daki.
Da yamma ranar sai ga Alh Ado Indararo da kansa yazo bayan matarsa ta fada masa
abinda Danmama yayi. Sun saba ciniki da Malamijo baya son kasuwar ta watse don yana
dukan hancin Malamijo akan dabbobinsa sosai batare da shi ya sani ba.
Ya bashi hakuri ya nemi Mairama itama ta fito da babban mayafi ta gaishe shi.
Kallon farko Alh Indararo ya fada kogin kauna baya ji baya gani. Tana komawa ciki
baiyi kasa a gwiwa ba ya fadawa Malamijo bukatarsa. Zani ce ta tadda muje mu. Shima
kwadayin kudin Alhajin yake yace ya bar masa wuka da nama.
A daren ya sanar da ita tayi tsalle ta dire tace bata da sauran aure a duniya. Sun
fara rigimarsu bayan kwana biyu ta tattara ta tafi Sakkwato kamar yadda ta saba duk
hutu suna zuwa suyi sati daya ko kwana goma.
Duk gidajen 'yan uwan Zayyan na jini da makusanta irin su Mal Aminu sai taje. Kuma
bata fasa zuwa barikinsu ba ko zata sami labarin Zainab da Mami. Gidan iyayen
Zainab yanzu wasu ne a ciki. Ta matsu tasan halin da suke ciki amma babu dama. Haka
kuma har yau babu wanda ya kirasu akan wani kudi na ihsani ga jaruman da suka rasu.
Suna hira da matar Maikudi da Jume Maikudin ya shigo yana hade rai. Shi yafi kowa
sanin babban dalilinsa na kin zuwansu garin amma bazai iya fadawa kowa ba. Yaran
dama baya sakar musu fuska. Sai dai suna da kyakkyawar mu'amala da 'yan uwansu wato
jikokin gidan. Satinsu daya suka juya Jume kamar a bar mata su. Babbar damuwarta
shine rashin kowa daga bangaren Innar Zayyan wanda Jume tace har yau itama tana
zuba idanu ne.
Maikudi bai sami sukuni ba sai da suka bar garin. Sirrika biyu yake boyewa Mairama
saboda mugunta da kuma son kai irin na dan Adam.
Na farko dai wata shida da rasuwar Zayyan kawunsa Sidi yazo bisa shawarar 'yan uwa.
Ashe ya tura musu wasika da zai tafi ta tasha. Sidi yazo gari Jume da matan gidan
sun tafi Tureta biki. Maikudi kawai ya samu su Badaru basa gida. Lokacin yana tsaka
da jin haushin rashin mutumcin Malamijo kuma yasan idan mutanen nan suka san da
zamansu ba karamin alheri zasu rinka musu ba. Wanda zai koma jikin Malamijo a
karshe. Saboda haka ya matso hawaye ya sanar dashi mutuwar Zayyan da kuma hatsarin
da su Mairama suka yi ita da 'yarta suka rasu gabadaya. Wannan shine dalilin da
yasa aka dena ji daga garesu.
Abu na biyu kuma shine aike duk karshen wata daga kasar Germany wanda Retired Major
Mustapha bai taba dena yi ba tun bayan samun lafiyarsa da aiki a can din kusan
shekaru hudu. Kudi ne yake turowa ta hanyar wani soja da yake karkashinsa a da kuma
ya yarda dashi. Wannan mutumi duk wata Maikudi yasan ranar da yake zuwa har
barikinsu ya karbi kudin da suke mazaunin kudin makarantar Radhiya da kuma tallafi
ga Mairama. Soke abinsa yake ga gidan Kano ya saka 'yan haya. A takaice dai yana ta
gina kansa don ya sayi fili a cikin Sakkwato yana ta makara gini da kudin marayu.
**********
Mairama ta koma ta tarar da babbar kura. Malamijo ya karbi sadakinta daga hannun
Alh Indararo an saka biki wata uku kafin ya gama yi mata gyaran gida. Ta shiga
matsanancin tashin hankali har Nene Marka tazo amma kowa cewa yake tayi auren ko
zata sami hutu itama.
Tayi kukan, tayi haukan duk a banza bata da mai tsaya mata. A bangare daya kuma
duniyar Salame ta juye. Mutum kamar Alh Indararo ace yana son mace kakarta ta yanke
saka. Shine wannan karon ma irin abinda take muradi ya tafi ga Mairama. Rantsuwa
tayi cewa hakan bazata sake sabuwa ba.
Gidan Malaminta da suka saba kashewa kudi domin a dawo mata da Salisu taje. Bayan
dogon bugun kasa yace ta saka ranta a inuwa akwai rabo yana iya gani tsakaninta da
Alh Indararo amma sai an kawar da Mairama.
"Malam rufa min asiri kanwata ce fa. Ni dai bazan iya kasheta ba"
Gemunsa na munafurci da suke cutar jama'a dashi ya ja yana murmushi "waye yace sai
kin kasheta. Idan kina so nakasa kawai zamu dora mata wadda zata saka ya fasa."
Kwana biyu tana tunani kafin ta hasko me take son ayiwa Mairama. Magani ya bata ta
wuce gida ta saka a inda ya umarceta.
Kwana uku a tsakani kuwa wata safiyar lahadi Mairama ta tashi bata gani sai dususu
komai yayi hazo. Cikin maganin digawarta na ido Salame ta zuba mata maganin. Cikin
wata guda idanun Mairama sai suna. Duk abinda ya rage mata ya kare a neman maganin
ciwon idon amma asibiti basa ganin komai.
Kuka ashe bai kare mata ba. Bata gane kowa sai duhun inuwa. Tashi guda Radhiya ta
koma idanunta madogararta. Alh Indararo ya canja sheka bazai iya auran musaka ba
Salame har ta tare abinta.
Karatun yaran ya tsaya yau da gobe Malamijo ya gaji da dan mikawar da yake yi. A
bisa dole ta hakura da karatun Radhiya da Emzee. Tana kuka kan kuka amma mahaifinta
bazai iya kulawa da ita ba bare 'ya'ya, iyakarsa dasu shine za'a dafa abincin gidan
dasu. Radhiya ta fara hankali tasan cewa mahaifiyarta tana bukatarta shiyasa bata
fita idan ba aike ba. Emzee kuwa dama daddawar daka ne shiyasa bata hadu da
matsalar ace suna yawace-yawace ba. Rayuwar Mairama matar soja ta cika da
wahalhalun da suka sa take bukatar a dube ta.
***********
Maza ne uku a karkashin bishiyar darbejiya wadda ta yiwa wurin yalwatacciyar inuwa.
Daya yana zaune akan kujera sauran biyun kuma suna gabansa ne kana gani kasan mai
mulki ne da wadanda yake mulka.
Gyaran murya na kan kujerar yayi suka dawo da hankula gareshi "Mal Gide"
"Ranka ya dade" wanda yafi manyanta cikinsu ya amsa.
"Habubakari"
"Allah Yaja zamaninka" na biyun ya amsa.
Dan murmushi yayi domin kuwa su biyun yayun matarsa ne Innawuro.
"Mal Gide kaine babba saboda haka ta kanka zan fara. Ba tare da jan zance ba magana
ce akan sakacinku da zumunci saboda wani abu can da ya faru shekarun baya"
Mal Gide ya hadiyi yawu yana kallon Habubakari shima kuma yayan nasa yake kallo.
Ardo Barkindo ya dan duku da kansa kadan daga kan kujerar "wannan zumuncin da kuka
banzatar ina mai tabbatar muku sai Allah Ya tambayeku akansa. Kune kuka ci bashi
kamar yadda naji a bisa dole. Dole tasa kuka biya bashin da kanwarku sai gashi daga
karshe ya sakota ya bukaci kudinsa ko. 'Yar uwarku ta sadaukar da farincikinta
saboda ku amma shekaru sun tasanmu talatin marainiyar da ta bari baku san cinta ba
baku san shanta ba"
Habubakar wanda abin shima ya dame shi amma tsoron Gide ya hana shi furtawa ya
sharce kwalla "Ardo zamu gyara, wallahi nima abin ya dameni. Ali bashi da kirki ko
kadan. Allah ma yasa tana da rai yarinyar nan"
"Yarinya da ranta amma tana cikin mawuyacin hali. Yanzu da na kiraku dama sanar
daku zanyi cewa zan daukota ko dan kwanciyar hankalin Innawuro"
Nan ya sanar dasu komai game da Mairama kamar yadda yaji daga bakin mijin Nene
Marka bayan ya soma binciken nemota.
Mal Gide sai hawaye. Bakar zuciya tasa ya umarci 'yan uwansa da babu su babu
zuri'ar Malamijo, ciki kuwa harda 'ya daya tilo ga kanwarsa Mairo wadda ya yiwa
auren dole da Malamijo.
"Da kaina zanje in daukota da yaran su zauna a gidana Zan gyara wannan abu duka
laifina ne"
Ardo Barkindo ya kada kai yana murmushi "haba dai Gide ai bazamu yi haka da kai ba.
Yarinya a wurin babarta zata zauna. Duk na gama wahalar neman sannan kace zaka
daukota ka kwashe ladan"
Murmushi ya maida masa "duk yadda kace ranka ya dade, kamar yaushe zamu tafi?"
"Jibi in sha Allahu. Ina so ku tattaro kan 'ya'yanku har na gidan aure da suke
rugar nan da kewaye maza da mata. So nake muje mu cika musu ido mu wanke gorin
dangin uwa da na tabbatar ansha yi mata."
Sun tashi da fara'a kowa yana jin kamar an sauke masa nauyi daga zuciya. Ardo
Barkindo ya nisa yana tunanin ya boye musu makantar Mairama saboda yasan duka
hankulansu zasu tashi. Idan sun je zasu ganewa idanunsu. Ko matarsa ya kasa fadawa
ita da ta uzzura masa akan neman 'yar yayarta da take bi.
Mal Gide kuwa har ya isa gida yana tunanin da yardar Allah zasu kula da ita bakin
iyawarsu su daidaita tsohuwar baraka. Tunawa yayi da umarnin Ardo ya tura guda
cikin 'ya'yansa da yaje ya fara sanar da yayyensa cewa suna da zuwa Kano jibi daga
rugarsu wadda take cikin karamar hukumar Giade a jihar Bauchin Yakubu.
[02/11 7:29 AM] My 2nd Mtn: 18. WAIWAYE....
Zainab tayi kuka har ta gode Allah. Hadir dinta ne kwance baya iya motsa kowace
gaba a jikinsa sannan baya iya magana. Idanunsa kadai ke aiki idan anyi magana kuma
yana ji amma babu damar amsawa. Tun iyaye na rarrashinta har suka kyaleta ta koka
ko zata ji sa'ida.
Zuwansu Kano kenan aka kaisu tsohon dakinsa inda yake zaman jinya. A hankali ya
bude idanunsa ya saukesu a kanta. Murmushi yayi wanda ya hado da zubar hawayensa.
Sunanta yake kira amma babu mai jin sautin saboda baya iya