Advertisements
Chapter 62 Reading Ku Dube Mu by Batul Mamman BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ku Dube Mu by Batul Mamman

Author :  Batul Mamman Category :  Complete Novels

Chapter   62 / 99

183K to 186K   out of 295.8K words

murmushi tare da mika
masa yaron yace cikin alfahari "Ibrahim Hadir da Zayyan Hadir"


Zayyan ya juya ya kalli Hadir ya yi murmushi sannan ya bashi yaron. Wata 'yar
budurwa ya gani ta kusa da wadda yake kallo tun shigowarsu wato Radhiya ta turo ta
gaba ita kuma sai kunya take ji ya dan rage tsayi "kema in daukeki ne?"


'Yan uwanta ta kalla ta dan marairaice a kunyace "a'a nima ka fadi sunana"


Ibrahim ya girgiza kai, ashe bata dena shagwaba ba. Ji yadda take tale baki ita da
ta gama secondary.


"Kiyi hakuri ki fada min da kanki inyi miki babbar kyauta"
"Zayyanatu Mustapha" tace saboda taji Ibrahim ma ya fadi harda sunan babansu.


Baki bude Zayyan ya kalli Major da ya kafe shi da ido kamar idan ya rufe zai bude
ya neme shi ya rasa.


Emzee ne ya rage a gabansa. Yaron tunda suka shigo yake ta kallon wannan mutumi
yana tunanin a ina ya taba ganin fuska shigen wannan. Kallon kallo suke yi Zayyan
yana jin kamar yana kallon younger version dinsa ne. Ashe Radhiya ma ta soma
tunanin inda tasan fuskar ita da ta haddace kamanin mahaifinta a hoto.


Emzee ya bude baki kenan ta matso da sauri tana jin jikinta yana rawa. Tunda suka
shigo ya gama gane wacece dinsa shiyasa ma ya bar yi mata magana sai a karshe.


"Kamar na san ka wallahi" tace muryarta a kasa kamar mai rada.


Hannu yasa ya janyota gabansa sosai ta tsare shi da manyan idanunta "Alheran
Radhiya baki gane Daadaa ba?"


"Ya Allah" ta furta a gigice ta rungume shi tana kuka mai sauti. Bayanta kawai yake
shafawa yana kokarin mayar da nasa hawayen.


"Ehemm..ni sunana..." Emzee yayi gyaran murya shima yau dauriya ta kare sai hawaye
"Muhammad Zayyan Tureta"


Haba...koda yaji wannan yaro zuciyarsa ta bashi cewa jininsa ne. Sakin Radhiya yayi
hawayen da yake kokarin kada ya zubar a gaban 'ya'ya suka fito suka rungume juna
cikin farinciki suna kuka. Zayyan ya dago yana ta shafa fuskar Emzee wai wannan ma
nasa ne.


"Kafi jindadin ganinsa a kaina ko?" Yaji Radhiya tace a raunane tana kara karyar
masa da zuciya.


"A'a Alheran" yace yana sakin Emzee ya sake rungumeta.


"Kenan ni bakayi murnar ganina ba?" Shima Emzee yace yana jin haushin tayi masa
kauron jin dumin babansa ya koma wurinta.


Zayyan sai ya rikice yana soma cewa "ba haka bane" ya ga Alheran ta kafe shi da ido
shima Emzee ya tsaya yana jiran amsarsa.


Dariya suka ji daga bayansu. Falon da ake ta kuka ma'abota cikinsa sun koma dariyar
wannan haduwa ta uba da 'ya'yansa. Hadasu yayi kowanne a bari daya ya rungumesu
kamar za'a kwace masa su
**********


Kowa yana son jin yadda ta kasance dashi su duka suna zaune a falon. Emzee da
Radhiya kusan danne masa kafafu suka yi kowannensu yana so ya rabi jikinsa.


Dagawa yayi suka hada ido da Ummi da take ta kallonsa sai taji kunya sosai ta kama
ta. Major ne yayi gyaran murya yace a yiwa Annabi SAW salati. A tare suke yi da
karfi suka karanta Fatiha, Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasul sannan ya dade yana jan
su da addu'a duka domin godiya ga Allah SWT.


"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah...wannan rana ce da bazamu taba
mantawa da ita ba har mu bar duniya. Amma kafin mu zauna jin yadda al'amura suka
kasance Zayyan ka zauna kaci abinci ka huta. Ku kuma kowa ya tashi mu bashi wuri
ya huta"


Dukkaninsu suka fita Ummi ta tashi tayi kitchen tana godewa dabara irin ta Mama aka
bar Zayyan da 'ya'yansa an rasa wanda zai fara tashi cikinsu.


Emzee yasan ya kamata su tashi amma Radhiya ita ta ga wurin kwana. Kallon babanta
kawai take yi tana cewa Daadaa yana amsawa da murmushi. Ta kira yafi sau goma bai
gajiya da amsawa.


"Emzee kuma wai nan ba mafarki nake yi ba ko?" Tace tana lumshe ido tana sake
budewa a kansa.


"Ko in mintsineki ne?"


"A gabana Zayyan?"


Wani dadi yaji ya kama shi mahaifinsa ga kira sunansa da sunan raba gardama
tsakaninsa da Addarsa. Kai wannan abu da me zai kwatanta shi. Muryar Umminsu suka
ji tana cewa "in fara kawo maka abinci ko tea?"


"Duk wanda kika kawo zanci Fillo. Saboda jiran abincinki rabona da saka wani abu a
bakina tun safiyar jiya"


Wai da irin dabarar nan Emzee sai ya yiwa yayarsa alama da ta tashi su ma su fita.
Shiru bata gane rangwada kan da yake yi ba sai da yace "Adda taso muje muma Daada
yaci abinci"


Hannunsa da ya riko nata ta ture "kai kyaleni ka tafi idan kana so. Ni ban gaji da
ganinsa ba." Matsowa ta sake yi jikin kafar Zayyan tana murmushi "Daada na chanja
kama daga yadda ka sanni ko?"


"Kin koma tamkar Innata"
"Bani labarinta"


Emzee sai ya shiga kada kai. Idan abin Addarsa ya motsa fa bata dogon tunani. Yanzu
ace daga dawowarsa zai fara bata labari. Ita kuma neman abinda zai zaunar da ita
wurinsa take yi kada ta tashi ta dawo ace ya koma inda ya fito.


"Kin yiwa Hamma Awwab godiya ne? Dashi aka je dauko Daada fa naji Mama tana fada"


An tuno mata da Hammanta sai ta tashi tana murmushi "Daada bari naje na dawo kafin
nan kaci abincin"


"Sai kun dawo Alheran"


Wani abin ta tuno zata taambayeshi Emzee ya turata waje ta karfi ya rufe kofar.


Ummi tana ajiye tray a gaban Mijinta taji gabanta ya fadi da aka rufe kofar ga
kunya kamar wata sabuwar amarya.

Dariya taji Zayyan yayi yana kallon kofar "ina kika samo min wadannan yaran Fillo?
Nan fa dabara yayi mata don su bamu wuri"


Sai da tayi murmushi yaji zuciyarsa tana kadawa da tasowar dadaddiyar soyayyarta
tace "sakamakon tureni da Tureta yayi ne" ya sake yin dariya.


Ta gama ajiye komai a gabansa zata fara zuba masa tea din domin ya gasa cikinsa ya
riko hannunta bai zaunar da ita ko ina ba sai cinyarsa. Kunya matsananciya ta kama
ta yayi mata wani irin riko da yaji tana neman tashi. Rungume tayi ya dora kansa a
tsakiyar kirjinta. A hankali taji hawayensa yana jika mata gaban riga. Tallabo shi
tayi ta sake rike shi itama nata hawayen yana sauka a kansa da ya cire hularsa.


Sunyi kusan minti biyar a haka sai ajiyar zuciya kawai da take yi. Da taji yana
neman dago kansa ne ta sassauta rikon "ga tea ka fara sha sai na zuba maka tuwo"


Bai bata damar tashi ba sai lebbanta da ya shiga zanawa da karamin yatsansa ya soma
magana a hankali "ban taba dena sonki ba Mairama, ban manta ki ba da kyautatawarki
gareni. Idan kunci yayi min yawa sai na cika zuciyata da ranar da na fara kamaki
kin saci mirinda"


Murmushi tayi mai hade da hawaye shi kuwa ya cigaba da abinda yake yi "a duk
lokacin da zan ganmu cikin wannan yanayin nasan mafarki ne wanda nake kwadayin
cikarsa idan mun hadu a aljannah. Ashe zan sake ganinki matata. Ashe da rabon na
sake samun kaina cikin farincikin zama miji a gareki..." hannu yasa yayo kasa da
kanta daidai fuskarsa "ban sani ba ko na manta ko zan iya tunawa"


"Me?" Ta tambayeshi gabanta yana lugude wai yau ita ce tare da Zayyan.
"Wannan" ya karasa fada da hade lebenshi da nata. Lumshe idanu kawai suka yi
kowannensu hawayen farincikin cikar buri yana saukowa daga idonsa suka sake rungume
juna tightly.


**********

Gidan Mami suka tafi saboda Emzee ya hango shigar bakon da suka zo da su Awwab din
Mama yasan manyan nasu can suka je. Ilai kuwa sun taru can dinne Excellency ya
gabatar musu da Chibuzor wanda ya fada musu sanadin haduwarsu da Zayyan. Wannan ake
kira al'ajabi su Major sun koka sun murmusa sun dara duk a lokaci guda. Yayin da
matansu suke dakin Mama su ma suna nasu mamakin.


A gidan Mami suma a falo aka baje hirar murna ta kaure sun saka Awwab a gaba sai ya
fada musu yaya akayi.


"I am exhausted ku bari ayi komai a tsanake"


Sallamar Radhiya yaji ya dago idanunsa da suka soma ja saboda muguwar gajiya da
yunwa. Jin kansa yake kamar yana yawo a iska babu kuzari ko kadan.


Emzee ne a gaba ko da ya shigo kai tsaye yaje ya rungume shi.

"Allah Ya baka abinda kake so duniya da lahira Hamma. Thank you"


"Kada kayi min kuka dai bani da karfin rarrashinka" Awwab ya zolaye shi.


Yana sake kallon Radhiya sai ga nata hawayen kamar famfo ya tashi da sauri. Wani
irin sonsa take ji ta kuma rasa da wace kalma zatayi amfani domin ya gane girman
farincikin da ya saka ta a ciki. Kofa ya nuna mata dama ko zama batayi ba ta fita
yana take mata baya suna jin shakiyancin Ibrahim da Raji wai love is in the air.


Wurin tsayuwa yake nema inda zasu samu su kadaice babu yayi gajeren tsaki. Da sunyi
aure fa shikenan duk inda yaso zai kaita. Yanzu anbi an cika ko ina an hana mutane
sakewa. Ta kula da yadda yake ta kalle kalle tayi murmushi.


"Hammana"


Dama ya lafiyar kura. Ya gaji tilis wannan kira da tayi masa yasa zuciya da gangar
jikinsa duka amsawa.


"Nagod..."


"Shhhhh kada ma ki fara. Idan kina da wani abin cewa dai ki fada"


Idanunta fal kwalla tace "ni me zan ce Hamma"
"Ni ina da abin fada Alheran." Da wata irin siga mai shiga rai yake kara hargitsa
ta da muryarsa "I am not a soldier kuma bani da zuciyar da zan taba zama. Kuma ni
ba likita bane, bana jurar ganin jini....But I love you so much kin hana min
nutsuwa tun daga ranar da na fara ganinki"


Kifta ido kawai tayi hawayenta ya sauko "nima haka Hammana"


Ya ce "wayo ko?" Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi "ina fata kin shirya aurena
yanzu?"


Ba shiri ta rufe fuskarta da gefen mayafi tana neman komawa gidan Mami.


Marairaicewa yayi sosai ya koma kalar tausayi ya shagwabe mata yadda take yi ita ma
"Come ooon na gaji fa. I need a wife, a friend....uhummm.... I need you."


Murmushi take yi sosai ta kasa dagowa ta kalle shi ma. Ya duka saitin fuskarta yana
neman hada ido da ita tana kaucewa "kin gani ba, ba don kin mayar dani gwauron dole
ba da yanzu I have Alheran to hug when I am happy or sad. My Schatzi to kiss when
love is in the air right?"


Gabadaya ta rikice masa ta ma kasa gudun ta barshi shi kadai yake ta zuba hirarsa.

"Kinsan me? I am so tired ga yunwa. Mu koma ciki?"


Tausayinsa taji kana ganinsa kasan a gajiye yake sosai kuwa.


"Muje na zuba maka"


"Baki bani amsa ba fa. Na dage ina ta debo zance duk don na burgeki"


Ya bata dariya ta gama kayarta sannan tace "I am all yours Hammana kai nake jira
tuntuni"


Amsar tayi masa dadi suka shiga falon tare. Babu kowa su Zahra sun shige dakin Mami
su Ibrahim suna dakin Awwab. Zama yayi akan doguwar kujera ta wuce kitchen zuba
masa abinci. Akan tray ta hado komai ta dawo sai dai me...Awwab ya mike abinsa wani
nannauyan bacci yayi awon gaba dashi abin tausayi. Kallonsa tayi tana jin
soyayyarsa tana dada zama sabuwa a zuciyarta.


***********

A kasa Mairama ta zauna Zayyan yana jingine da kujera ta saka plate din abincin a
tsakaninsu sannan ta tashi.
"Ina zaki?"


"Hannu zan wanke" ta amsa tana sunkuyar da kai saboda tunanin abinda yayi mata
mintuna kadan da suka wuce. Tasowa yayi shima yace zai wanke nasa hannun.


"Yi zamanka ina zuwa"


Bata dade ba ta dawo yayi zaton ruwa zata kawo masa a roba na wanke hannu sai gani
yayi ta zauna ta debo tuwon ta kawo bakinsa.


Yau kam bashi da karfin zuciya ko kadan. Yau daya dai a Zayyan mijin Mairama yake
wanda ya kwashi dimbin shekaru yana muradin sake ganinta ko da daga nesa ne. Hannun
nata ya kama ya karasa dashi bakinsa.


"Ashe haka tuwo yake da dadi muka rinka cewa bama so da muna yara" taji yace ta
soma dariya ya fara bin yatsunta daya bayan daya yana sudewa.


Fillo sarkin kunya sai ta kasa kara diban wani ta bashi. Ya sanya hannu ya dago
kanta idanunta a rufe "alfarma nake nema Fillo"


"Babu alfarma a tsakaninmu kaima ka sani"


"Yau daya don Allah ki tattaro duka kunyar nan ko Alheran ce ki bawa ajiya. Mairama
kadai nake bukata in nuna mata yadda shekaru ashirin da biyu suka galabaitar da
Sojanta"

💕[11/2, 7:11 AM] 46💕
🏽
A haka ta gama bashi abincin yaci mai yawa. Yaushe rabonsa da tuwo ko abinci mai
dadi? Miya tasha nama da bushasshen kifi yaci son ransa duk loma yana binta da
addu'a da kalmomi masu nuni da kewarta da yayi.


Harararsa tayi cikin wasa "kasan dai ba'a son magana ana cin abinci ko"


"Gani nake yi idan nayi shiru kamar zaki bace na dena ganinki" ya bata amsa kai
tsaye yana kallon idanunta da suka cicciko da kwalla.


Hannunsa ta kama ta rike gam da hannun hagunta ta cigaba da bashi da daman.

"Babu inda zani Sojana"


Murmushi suka yiwa juna basuyi aune ba ya cinye leda daya madaidaiciya harda karin
rabi na tuwon. Nama ma ba kadan ta bashi ba sai da yaji cikinsa yayi masa nauyi don
kansa yace ya isa yana dariya.


"Kada na kasa tashi daga wurin nan fa Fillo. Ina zaune kina ta zuba abinci a tumbin
da yunwa ta cinye shi."


"Inda kake horon yunwa suke yi maka? Dubi yadda ka rame sosai ko da dai ba kiba
gareka ba amma yanzu ana ganinka za'a gane rama ce ba siranta ba" tayi maganar
yayin da ta soma hade kan kwanukan zata kai kitchen.


Da wata irin murya mai sanyi Zayyan yace "Mairama...ki kira min su Major muyi
magana kafin na saka hakarkarina a makwanci."


"Ka huta don Allah"


"Yadda kuke matse da son jin me ya sameni nima haka na damu da son jin yadda kuka
rayu ke da 'ya'yana da aminai na. Kirjina yana son amayar muku da nauyin da yayi ta
dako ko zanji sauki"


Wani irin tausayinsa take ji tana gama kai kwanukan ta wanko hannunta ta dawo ta
kira Mami ta sanar da ita.


Su Major so suka yi ya huta ko zuwa gobe ne amma yasan shi dai bazai iya hakurin
nan baiji me ya sameta ba.


Har wannan lokaci Baban Arifah yana gidan tare suka dawo falon Zayyan yace a kira
masa duka yaran domin su ma sun cancanci sanin ina mahaifinsu ya shiga tsahon
lokacin nan. Falon yayi tsit Awwab ne kawai babu. Radhiya dama tana dawowa ta sake
komawa gabansa yana daga kan kujera tana kasa. Zayyan ya dube su daya bayan daya ya
jinjina kai domin yasan wannan labari yanzu ya fara bada shi har sai duk wanda ya
kamata ya sani ya sani. Sojansa ya koma rikakken namiji ma'abocin cikar zati kafin
ya fara magana.


"Kwanaki kadan bayan rabuwarmu da Baban Arifah zuwa wuraren karfe daya da rabi na
jiya sunana 3810 mazaunin gidan yari da ake yiwa zargin dan tawaye a Liberia"


Major da Baba Hadir sun ji kadan daga labarin daga wurin Baban Arifah amma sauran
matan musamman Ummi da Alheran sun dimauce matuka.


Daga lokacin da ya rabu dasu Hadir kawo ga haduwa da rabuwarsa da Baban Arifah da
zamansa a wannan prison din ya sanar dasu mahimman abubuwan da suka same shi.
Wahalhalun zaman kurkuku da tsananin begen komowa gida garesu. Kuka duka matan suke
yi wurjanjan. Ummi saboda tsananin kaduwa tsigar jikinta har tashi take yi ta kasa
zaman falon ta tashi tayi ciki sai sautin rufe kofar daki aka ji.


Murmushi yayi yana kallon kofar da ta bi "banda abin Fillo komai ba ya wuce ba"


Jikkuna sunyi sanyi. Girma, kima da darajar wannan bawan Allah ta ninku a cikin
idanun duk wanda yake zaune a wurin. Ga su Daddy dadin ciwon abun duka su ukun fa a
garin ceton rayuwarsu ne ya fadawa wannan kaddara mai radadi da sosa zuciya.
Idanuwa sunyi kuka ba babba ba yaro shiyasa Mami ta cewa yaran dukkansu su tashi
tunda sauran labarin ba bakonsu bane. A sanyaye suka fice zuwa gidan Mama ita kuma
da Maman suka shiga wurin Ummi. Dama kuma tun zuwan su Zayyan din bayan anyi zaman
gabatar da juna sallah suka yi shine Daddy ya jagoranci addu'a da suka yi. Emzee da
Ibrahim gidan Mami suka wuce su.


Da kyar bayan fitarsu Major yace "Zayyan ka ga rayuwa ni bani da wani bakin magana
ko baka hakuri. Nauyi da girmanka nake kara gani ina jin inama ban biyo motar da
taje camp dinku ba ranar. Da bazan biku wurin ba kai kuma babu dalilin da zai sa ka
koma daukoni har wannan abu ya faru. Nine silar komai Zayyan ka yafeni" ya kare
muryarsa tana rawa sosai.


Idanun Zayyan sai suka kada suka yi jazur "ashe ni din ba kaninka bane kamar yadda
nayi zato. Matsayin da muka baka ni da Hadir ba shi ka bamu ba"


Sai ga hawaye ya saukowa Major da sauri yace "a'a Zayyan ba haka bane. I feel so
guilty"


"Saboda kaninka yayi rayuwar da ko da babu kai ita Allah Ya zaba masa? Hadir kace
wani abu mana ka barni inata babatu ni daya"


Wani mashahurin shiru yaji ya ratsa falon ya kalli Hadir ya kallesu duka a dan
tsorace yace "kada kuce min wannan mutum-mutumi ne ba Hadir dan uwana ba"


Hadir din ne ya fara dariya kafin sauran su biye masa da kyar ya iya cewa
"Zayyyyyan ko" yana kada masa yatsa. Abokin nasa bai chanja hali ba. Suna cikin
damuwa sai da ya saka su dariyar dole.


Tashi yayi yaje yana dan dukan kafadar Hadir din a hankali "tun zuwana banjin kayi
min magana ba dole na tambaya."


Baban Arifah Excellency yace "ka zauna Mustapha zaiyi maka duka bayanin da ya dace"


Haka ya koma ya zauna yana sauraron Major wanda ya fara da labarin tasa rayuwar
sannan ya gangaro dawowarsu Nigeria da sake haduwa da Hadir. Jikin Zayyan wata
tsuma yake yi da tashin hankali da yaji rayuwar da suka yi. Wane irin ciwo ne PTSD
yake ayyanawa a ransa da ya nemi haukata Major mutum mai dauriya da karfin zuciya?
Yanzu Hadir dinsa ne yayi shekaru baya iya motsa komai nasa kuma baya magana...kai
rayuwa shine mutane suke kwallafa rai da neman haram bayan idan Allah Yaso sai Ya
dauke maka komai Ya barka da ranka. Hadir mutuwar zaune fa yayi kuma aka raba shi
da nasa iyalin alhalin yana cikinsu. Sai yaji yafi tausayin aminin nasa akan tasa
rayuwar.


Bayan ya gama jin komai ya kalle shi

" To gaskiya shawarar da zan baka shine ko ka bude baki ka fara magana ko kuma kaf
tarihin 'yan matanka wadanda zan iya tunawa da wanda ban tuna ba in dora nawa zan
kaiwa Zainab mu koma gefe ni da Fillo musha kallo" Zayyan yace a yayin da yake ta
kore kwalla da yatsansa. Dariya Baba Hadir yayi ya taso suka sake rungume juna.
Excellency yaji suna kara burge shi "ina zaune ana nuna min wariya. Ai shikenan ba
fushi zanyi ba bare na barku. Nema kuke ku nuna min ku ukun kunfi shakuwa ni dan
karo ne"


Major ya kwashe da dariya saboda yanayin muryar da Excellency din yayi magana da
ita ta ban tausayi.

"Dama ka dena damuwa nima ana nuna min amma ya na iya they are my Ladies"


Aka sake yin dariya musamman da Baban Arifah yace

62 / 99